13 – Luwaɗi

Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Luwaɗi.

Top 3 Mafi Muhimmanci ayoyi

1 Korintiyawa 6:9-11

Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ’yan daudu, ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah. Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.

Romawa 1:26-28

Saboda wannan, Allah ya yashe su ga sha’awace-sha’awacensu masu banƙyama. Har matansu suka sauya daga haɗuwar mace da miji wadda ita ce daidai bisa ga halitta zuwa haɗuwa da ’yan’uwansu mata wadda ba daidai ba. Haka ma maza suka bar al’adar kwana da mata suka tunzura cikin sha’awar kwana da juna, abin da ba daidai ba bisa ga halitta. Maza suka aikata rashin kunya da waɗansu maza, suka jawo wa kansu sakamako daidai da bauɗewarsu. Da yake ba su yi tunani cewa ya dace su riƙe sanin Allah da suke da shi ba, sai ya yashe su ga tunanin banza da wofi, su aikata abin da bai kamata a yi ba.

Firistoci 18:22-23

“ ‘Kada ka kwana da namiji kamar yadda namiji yakan kwana da ta mace, wannan abin ƙyama ne. “ ‘Kada ka yi jima’i da dabba ka ƙazantar da kanka. Mace ba za tă ba da kanta ga dabba don yă yi jima’i da ita ba; wannan abin ƙyama ne.

Kowane Aya A Canonical Order – 21 sassa

Farawa 1:27

Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa. Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum. Miji da mace ya halicce su.

Farawa 2:24

Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.

Farawa 18:20-32

Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Kuka a kan Sodom da Gomorra ta yi yawa, zunubinsu kuma ya yi muni sosai, zan gangara in ga ko abin da suka yi ya yi muni kamar yadda kukan ya zo gare ni, zan bincike.” Sai mutanen suka juya suka nufi wajen Sodom amma Ibrahim ya ci gaba da kasance a gaban Ubangiji. Sai Ibrahim ya matso wurinsa ya ce, “Za ka hallaka masu adalci tare da masu mugunta? Me zai faru in akwai mutum hamshin masu adalci a cikin birnin? Ashe, za ka hallaka shi, ba za ka cece wurin saboda mutane hamsin nan masu adalcin da suke a cikinsa ba? Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba, ka kashe masu adalci tare da masu mugunta, ka ɗauka masu adalci da masu mugunta daidai? Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba! Mai hukuncin dukan duniya ba zai aikata gaskiya ba?” Ubangiji ce, “In na sami mutum hamshin masu adalci a cikin birnin Sodom, zan bar dukan birnin saboda su.” Sai Ibrahim ya ƙara cewa, “Yanzu da na yi karambani har na yi magana da Ubangiji, ko da yake ni ba kome ba ne illa turɓaya da toka, in yawan masu adalci sun kāsa hamshin da mutum biyar fa? Za ka hallaka dukan birnin saboda rashin mutum biyar ɗin?” Ya ce, “In na sami mutum arba’in da biyar a wurin, ba zan hallaka shi ba.” Ya sāke cewa, “In mutum arba’in kaɗai aka samu a can fa?” Ya ce, “Saboda mutum arba’in ɗin, ba zan aikata ba.” Sai ya ce, “Kada Ubangiji ya yi fushi, amma bari in ƙara magana. A ce mutum talatin kaɗai aka samu a can fa?” Ya ce, “Ba zan aikata ba, in na sami mutum talatin a can.” Ibrahim ya ce, “Yanzu fa da na yi karambani har na yi magana da Ubangiji, in ashirin kaɗai aka samu a can fa?” Ya ce, “Saboda ashirin ɗin, ba zan hallaka shi ba.” Sa’an nan Ibrahim ya ce, “Kada Ubangiji yă yi fushi, amma bari in ƙara magana sau ɗaya tak. In aka sami mutum goma kaɗai a can fa?” Ubangiji ya ce, “Saboda goma nan, ba zan hallaka shi ba.”

Farawa 19:1-11

Mala’ikun nan biyu suka iso Sodom da yamma. Lot kuwa yana zama a hanyar shiga birnin. Da ya gan su, sai ya tashi don yă tarye su, ya kuma rusuna da fuskarsa har ƙasa. Ya ce, “Ranku yă daɗe, ina roƙonku ku ratsa zuwa gidan bawanku. Ku wanke ƙafafunku, ku kwana, sa’an nan ku kama hanyarku da sassafe.” Suka ce, “A’a, za mu kwana a dandali.” Amma ya nace musu ƙwarai, sai suka tafi tare da shi, suka kuma shiga gidansa. Ya shirya musu abinci, ya gasa burodi marasa yisti, suka ci. Kafin suka shiga barci, sai ga dukan mutane, ƙanana da manya daga kowane ɓangare na birnin Sodom, suka kewaye gidan. Suka kira Lot, suka ce, “Ina mutanen da suka zo wurinka a daren nan? Fito mana da su waje domin mu kwana da su.” Lot ya fita daga cikin gida, ya rufe ƙofar a bayansa. Ya je wurin mutanen ya ce musu, “A’a, abokaina kada ku yi wannan mummunan abu. Duba, ina da ’ya’ya mata biyu waɗanda ba su taɓa sanin namiji ba, bari in kawo muku su ku yi kome da kuke so da su. Amma kada ku taɓa waɗannan mutane, gama su baƙina ne kuma dole in tsare su.” Sai mutanen birnin suka amsa, “Ba mu wuri! Wannan mutum ya zo nan kamar baƙo, ga shi yanzu yana so yă zama alƙali! Za mu wulaƙanta ka fiye da su.” Suka ci gaba da matsa wa Lot lamba, suka matsa kusa domin su fasa ƙofar. Amma mutanen da suke ciki suka miƙa hannunsu, suka ja Lot zuwa cikin gida, suka rufe ƙofar. Sai suka bugi mutanen da suke a bakin ƙofar gidan da makanta, ƙanana da manya duka, har suka gajiyar da kansu, suna lalluba inda ƙofar take.

Farawa 19:12-17

Mutanen nan biyun suka ce wa Lot, “Kana da wani a nan, ko surukai, ko ’ya’ya maza ko mata, ko kuwa wani dai a cikin birni wanda yake naka? Ka fitar da su daga nan, gama za mu hallaka wannan wuri. Kukan da aka yi ga Ubangiji game da mutanen birnin nan ya yi yawa sosai, ya sa har ya aiko mu domin mu hallaka birnin.” Saboda haka Lot ya tafi ya yi magana da surukansa waɗanda suka yi alkawari za su aure ’ya’yansa mata. Ya ce, “Ku yi sauri ku fita daga wannan wuri, gama Ubangiji yana gab da hallaka birnin.” Amma surukansa suka ɗauka wasa yake yi. Gari na wayewa, sai mala’ikun nan suka ƙarfafa Lot suna cewa, “Yi sauri! Ka ɗauki matarka da ’ya’yanka biyu mata waɗanda suke a nan, don kada a shafe ku sa’ad da ake hukunta birnin.” Da yana jan jiki, sai mutanen suka kama hannunsa da hannuwan matarsa da na ’ya’yansa biyu mata, suka kai su bayan birni, gama Ubangiji ya nuna musu jinƙai. Da suka fitar da su, sai ɗaya daga cikin mala’ikun ya ce, “Ku gudu domin ranku; kada ku duba baya, kada kuma ku tsaya ko’ina cikin kwarin! Ku gudu zuwa cikin duwatsu, don kada a hallaka ku!”

Farawa 19:24

Sai Ubangiji ya yi ta zuba kibiritu a bisa Sodom da Gomorra daga sama.

Farawa 19:26

Amma matar Lot ta waiwaya baya, ta kuma zama ginshiƙin gishiri.

Firistoci 18:22-23

“ ‘Kada ka kwana da namiji kamar yadda namiji yakan kwana da ta mace, wannan abin ƙyama ne. “ ‘Kada ka yi jima’i da dabba ka ƙazantar da kanka. Mace ba za tă ba da kanta ga dabba don yă yi jima’i da ita ba; wannan abin ƙyama ne.

Firistoci 20:13

“ ‘In mutum ya kwana da mutum kamar yadda ake kwana da mace, su biyun sun yi abin ƙyama. Dole a kashe su, alhakin jininsu zai zauna a kansu.

Maimaitawar Shari’a 22:5

Kada mace ta sa suturar maza, kada kuma namiji ya sa suturar mata, gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamar duk mai yin haka.

Mattiyu 19:4-6

Ya amsa ya ce, ‹“Ba ku taɓa karantawa ba ne cewa, a farkon halitta, Mahalicci ‘ya yi su namiji da ta mace,’› ‹ya kuma ce, ‘Saboda wannan dalili, namiji zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa yă manne wa matarsa, biyun kuwa su zama jiki guda’?› ‹Ta haka, ba sa ƙara zama biyu, sai dai ɗaya. Saboda haka abin da Allah ya haɗa fa, kada mutum yă raba.”›

Markus 10:6-9

‹Amma a farkon halitta, Allah ya ‘halicce su miji da mace.’› ‹‘Saboda wannan dalili, mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa,› ‹su biyun kuma za su zama jiki ɗaya.’›‹Saboda haka, su ba mutum biyu ba ne, amma mutum ɗaya.› ‹Domin haka, abin da Allah ya haɗa, kada mutum yă raba.”›

Luka 15:10

‹Haka, ina gaya muku, akwai murna a gaban mala’ikun Allah a kan mai zunubi guda ɗaya, da ya tuba.”›

Ayyukan Manzanni 3:19

Saboda haka ku tuba, ku juyo ga Allah, don a shafe zunubanku, don lokutan wartsakewa su zo daga wurin Ubangiji,

Romawa 1:24-32

Saboda haka Allah ya yashe su ga mugayen sha’awace-sha’awacen zukatansu ga fasikanci don a ƙasƙantar da jikunansu ga yin abin kunya. Sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, suka kuma yi wa abubuwan da aka halitta sujada suna bauta musu a maimakon Mahalicci, wanda ake yabo har abada. Amin. Saboda wannan, Allah ya yashe su ga sha’awace-sha’awacensu masu banƙyama. Har matansu suka sauya daga haɗuwar mace da miji wadda ita ce daidai bisa ga halitta zuwa haɗuwa da ’yan’uwansu mata wadda ba daidai ba. Haka ma maza suka bar al’adar kwana da mata suka tunzura cikin sha’awar kwana da juna, abin da ba daidai ba bisa ga halitta. Maza suka aikata rashin kunya da waɗansu maza, suka jawo wa kansu sakamako daidai da bauɗewarsu. Da yake ba su yi tunani cewa ya dace su riƙe sanin Allah da suke da shi ba, sai ya yashe su ga tunanin banza da wofi, su aikata abin da bai kamata a yi ba. Sun cika da kowace irin ƙeta, mugunta, kwaɗayi, da tunanin banza da wofi. Suka kuma cika da kishi, kisankai, faɗa, ruɗu, da kuma riƙo a zuci. Su masu gulma ne, da masu ɓata suna, masu ƙin Allah, masu rashin kunya, masu girman kai, masu rigima; sukan ƙaga hanyoyin yin mugunta; suna rashin biyayya ga iyayensu; su marasa hankali ne, marasa bangaskiya, marasa ƙauna, marasa tausayi. Ko da yake sun san dokar adalcin Allah cewa masu aikata irin waɗannan abubuwa sun cancanci mutuwa, duk da haka ba cin gaba da aikata waɗannan abubuwa kaɗai suke yi ba, har ma suna goyon bayan masu yinsu.

1 Korintiyawa 6:9-11

Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ’yan daudu, ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah. Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.

1 Timoti 1:9-10

Mun kuma san cewa an yi doka ba domin masu adalci ba sai dai masu tawaye, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai, da masu zina da kuma da maza masu kwana da maza, ko mata masu kwana da mata, da masu cinikin bayi da masu ƙarya da kuma masu shaidar ƙarya, da kuma duk wani abin da ya saɓa wa sahihiyar koyarwa,

2 Bitrus 2:4-10

Gama in har Allah bai ƙyale mala’iku sa’ad da suka yi zunubi ba, amma ya tura su cikin lahira, domin a tsare su don hukunci; in har bai ƙyale duniya ta dā ba sa’ad da ya kawo ambaliya a kan mutanenta marasa tsoron Allah, amma ya kiyaye Nuhu, mai wa’azin adalci, da kuma waɗansu bakwai; in har ya hukunta biranen Sodom da Gomorra ta wurin ƙone su suka zama toka, ya kuma maishe su misali na abin da zai faru da marasa tsoron Allah; in kuwa har ya ceci Lot, mai adalci, wanda ya damu ainun da ƙazamar rayuwar mutane marasa bin doka; (adon kuwa abin da adalin nan ya yi, ya kuma gani, sa’ad da yake a cikinsu, sai kowace rana yakan ji ciwon aikinsu na kangara a zuciyarsa mai adalci) in haka ne, to, Ubangiji ya san yadda zai ceci mutane masu tsoron Allah daga gwaje-gwaje, yă kuma tsare marasa adalci don ranar hukunci, har yă zuwa ranar shari’a. Wannan gaskiya ce musamman ga waɗanda suke bin sha’awace-sha’awacen lalaci na mutuntaka, suna kuma rena masu mulki. Da ƙarfin hali da kuma girman kai, waɗannan mutane ba sa tsoro kawo zargin ɓata sunan talikan sama;

2 Bitrus 3:9

Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani yă hallaka, sai dai kowa yă kai ga tuba.

Yahuda 1:6-8

Haka ma mala’ikun da ba su riƙe matsayinsu na iko ba, waɗanda suka bar ainihin mazauninsu, su ne ya tsare a duhu daure da dawwammamun sarƙoƙi don hukunci ta babbar Ranan nan. Haka ma Sodom da Gomorra da garuruwan da suke kewaye da su, waɗanda su ma suka ba da kansu ga fasikanci da muguwar sha’awar jiki, sun zama misalin waɗanda suke shan hukuncin madawwamiyar wuta. Haka yake da masu mafarke-mafarken nan, gama sun ƙazantar da jikunansu, suka ƙi bin masu mulki, suna ɓata sunan talikan sararin sama.

Ru’uya ta Yohanna 21:8

Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.”

Hausa - Hausa - HA

HA'BSS - Budadden Littafi Mai Tsarki Biblica - 2020

This Bible text is from Biblica Open Hausa Contemporary Bible 2020
https://open.bible/bibles/hausa-biblica-text-bible/
provided by: Biblica Inc, available by Creative Commons CC-BY-SA-4.0,
and this new compilation is shared as www.creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0.
Languages are made available to you by www.ipedge.net