11 – Zunubi
Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Zunubi.
Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Zunubi.
Ba wata hadayar da za a yi don mutanen da suka yanke shawara su yi ci gaba da yin zunubi da gangan bayan sun sami sanin gaskiya. A maimakon haka za su kasance da babban fargabar hukunci da kuma ta ƙunar wuta wadda za tă cinye abokan gāban Allah.
”ba su kiyaye alkawarin Allah ba suka kuma ƙi su yi rayuwa ta wurin dokarsa.
”‹Na gaya muku cewa za ku mutu cikin zunubanku; in ba ku gaskata cewa ni ne wanda na ce nake ba, lalle za ku mutu cikin zunubanku.”›
”Ubangiji Allah ya umarci mutumin ya ce, “Kana da ’yanci ka ci daga kowane itace a cikin lambun, amma kada ka ci daga itacen sanin abin da yake mai kyau da abin da yake mugu, gama a ranar da ka ci shi, lalle za ka mutu.”
”Sa’ad da macen ta ga ’ya’yan itacen suna da kyau don abinci, abin sha’awa ga ido, abin marmari kuma don samun hikima, sai ta tsinka ta ci, ta kuma ba da waɗansu wa mijinta wanda yake tare da ita, shi ma ya ci.
”Sa’an nan idanun dukansu biyu suka buɗe, suka kuma gane tsirara suke; saboda haka suka ɗinɗinka ganyayen ɓaure suka yi wa kansu sutura. Da mutumin da matarsa suka ji motsin Ubangiji Allah yana takawa a lambun a sanyin yini, sai suka ɓuya daga Ubangiji Allah a cikin itatuwan lambu. Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin ya ce, “Ina kake?” Ya ce, “Na ji ka a cikin lambu, na kuwa ji tsoro gama ina tsirara, saboda haka na ɓuya.” Sai ya ce, “Wa ya faɗa maka cewa kana tsirara? Ko dai ka ci daga itacen da na umarce ka kada ka ci ne?”
”Mutumin ya ce, “Macen da ka sa a nan tare da ni, ita ta ba ni waɗansu ’ya’ya daga itacen, na kuwa ci.” Sai Ubangiji Allah ya ce wa matar, “Me ke nan kika yi?” Matar ta ce, “Macijin ne ya ruɗe ni, na kuwa ci.”
”Ubangiji Allah ya kuma ce, “To, fa, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu. Kada a yarda yă miƙa hannunsa yă ɗiba daga itacen rai yă ci, yă kuma rayu har abada.” Saboda haka Ubangiji Allah ya kore shi daga Lambun Eden domin yă nome ƙasa wadda aka yi shi. Bayan da ya kori mutumin, sai ya sa kerubobi da takobi mai harshen wuta yana jujjuyawa baya da gaba a gabashin Lambun Eden don yă tsare hanya zuwa itacen rai.
”amma bai yi farin ciki da sadakar da Kayinu ya kawo ba. Saboda haka Kayinu ya ji fushi sosai, fuskarsa kuma ta ɓace. Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Don me kake fushi? Don me fuskarka ta ɓace? Da ka yi abin da yake daidai, ai, da ka sami karɓuwa. Amma tun da ba ka yi abin da ba daidai ba, zunubi zai yi fakonka don yă rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so yă mallake ka, amma tilas ka rinjaye shi.” To, Kayinu ya ce wa ɗan’uwansa Habila, “Mu tafi gona.” Yayinda suke a gona, sai Kayinu ya tasar wa Habila ya buge shi ya kashe.
”Ubangiji kuwa ya lura cewa muguntar mutum ta yi yawa a duniya, kuma kowane abin da yake tunani a zuciyarsa mugu ne kawai a kowanne lokaci.
”Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Kuka a kan Sodom da Gomorra ta yi yawa, zunubinsu kuma ya yi muni sosai,
”“Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli ba sai ni. Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli a siffar wani abu a sama a bisa, ko a ƙarƙashin ƙasa, ko a ƙarƙashin ruwa ba. Ba za ka durƙusa gare su, ko ka yi musu sujada ba. Gama ni, Ubangiji Allahnka mai kishi ne, nakan hukunta ’ya’ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina, amma ina nuna ƙauna ga tsara dubbai na waɗanda suke ƙaunata, suke kuma kiyaye umarnaina.
”Ba za ka yi amfani da sunan Ubangiji Allahnka a banza ba, gama Ubangiji zai hukunta duk wanda ya mai da sunansa banza.
”Ba za ka yi kisankai ba. Ba za ka yi zina ba. Ba za ka yi sata ba. Ba za ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka ba. Ba za ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba. Ba za ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, ko bawansa, ko baiwarsa, ko sansa, ko jakinsa, ko duk abin da yake na maƙwabcinka ba.”
”Musa ya ce wa mutane, “Kada ku ji tsoro, gama Allah ya zo don yă gwada ku, don ku riƙa girmama shi, don kuma kada ku yi zunubi.”
”“Duk wanda ya bugi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi. “Duk wanda ya saci mutum ya sayar da shi, ko kuwa aka iske shi a hannunsa, lalle kashe shi za a yi. “Duk wanda ya la’anta mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.
”“Duk mutumin da ya yi jima’i da dabba dole a kashe shi.
”“Kada ku baza rahoton ƙarya. Kada kuma ku haɗa baki da mugayen mutane har da ku zama munafukai ta wurin ba da shaidar ƙarya.
”Sa’ad da wani yana da laifi a kowanne cikin waɗannan hanyoyi, dole yă furta a hanyar da ya yi zunubin
”“ ‘Kada ka yi jima’i da matar maƙwabcinka ka ƙazantar da kanka tare da ita.
”“ ‘Kada ku ba da wani daga cikin ’ya’yanku don a yi hadaya wa Molek, gama ba za ku ƙasƙantar da sunan Allahnku ba. Ni ne Ubangiji.
”“ ‘Kada ka kwana da namiji kamar yadda namiji yakan kwana da ta mace, wannan abin ƙyama ne.
”“ ‘Kada ka yi jima’i da dabba ka ƙazantar da kanka. Mace ba za tă ba da kanta ga dabba don yă yi jima’i da ita ba; wannan abin ƙyama ne.
”“ ‘Duk wanda ya yi wani daga cikin waɗannan abubuwa banƙyama, dole a fid da mutumin daga cikin mutanensa.
”“ ‘Kada ku yi sata. “ ‘Kada ku yi ƙarya. “ ‘Kada ku ruɗe juna.
”“ ‘Kada ka nemi yin ramuwa, ko ka riƙe wani cikin mutanenka a zuciya, amma ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka. Ni ne Ubangiji.
”“ ‘Kada ku yi amfani da mudun ƙarya sa’ad da kuke awon tsawo, nauyi, ko yawan abu. Ku yi amfani da ma’auni na gaskiya da mudu na gaskiya, da kuma magwaji na gaskiya. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar.
”“ ‘Ku tsarkake kanku, ku kuma zama da tsarki, gama Ni ne Ubangiji Allahnku.
”Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Duk wanda ya zagi Allahnsa, alhakin zai rataya a wuyansa, duk wanda ya saɓi sunan Ubangiji, dole a kashe shi. Dole jama’a gaba ɗaya su jajjefe shi da duwatsu. Ko baƙo, ko haifaffen ɗan ƙasa, sa’ad da ya saɓi Sunan Ubangiji, dole a kashe shi.
”Duk wanda ya yi wa maƙwabcinsa rauni, sai a yi masa abin da ya yi; karaya don karaya, ido don ido, haƙori don haƙori. Kamar yadda ya yi wa wani rauni, shi ma a yi masa.
”“ ‘Amma in suka tuba daga zunubansu da zunuban kakanninsu, da cin amanar da suka yi mini, da kuma adawar da suka yi da ni,
”“Gaya wa Isra’ilawa, ‘Sa’ad da namiji ko mace ya yi wa ɗan’uwansa laifi ta kowace hanya, ta yin haka, ya yi rashin aminci ga Ubangiji, mutumin kuwa ya yi laifi ke nan
”Mutanen suka zo wurin Musa, suka ce, “Mun yi zunubi, da muka yi wa Ubangiji da kai gunaguni. Ka yi addu’a don Ubangiji yă ɗauke mana macizan nan.” Saboda haka Musa ya yi addu’a domin mutane.
”“Amma in ba ku yi haka ba, kun yi zunubi ke nan ga Ubangiji; kuma ku san cewa zunubinku zai tone ku.
”“Ba za ka kasance da waɗansu alloli a gabana ba. Ba za ka yi wa kanka gunki, ko wata siffar abin da take a sama a bisa, ko siffar abin da yake a duniya a ƙasa, ko siffar abin da yake a cikin ruwa a ƙarƙashin ƙasa ba. Ba za ka rusuna musu, ko ka yi musu sujada ba. Gama Ni, Ubangiji Allahnka, Allah ne mai kishi, nakan hukunta ’ya’ya saboda zunuban iyaye har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suka ƙi ni. Amma nakan nuna ƙauna ga dubban tsararraki na waɗanda suke ƙaunata, suke kuma kiyaye dokokina.
”Ba za ka yi amfani da sunan Ubangiji Allahnka a banza ba, gama Ubangiji zai ba wa duk mai yin amfani da sunansa a banza laifi.
”Kada ka yi kisankai. Kada ka yi zina. Kada ka yi sata. Kada ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka. Kada ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka. Kada kuma ka yi sha’awar gidan maƙwabcinka, ko gonarsa, ko bayinsa maza da mata, ko saniyarka, ko jakinsa, ko dai wani abin da yake na maƙwabtanka.”
”Sai ku yi hankali don ku yi abin da Ubangiji Allahnku ya umarce ku; kada ku juya dama ko hagu.
”Ku ƙone siffar allolinsu da wuta. Kada ku yi ƙyashin azurfa ko zinariyar da aka rufe allolin da ita, Kada ku kwashe su, don kada su zamar muku tarko, gama abin ƙyama ne ga Ubangiji Allahnku. Kada ku kawo abin ƙyama cikin gidajenku, domin kada ku zama kamar su. Gaba ɗaya ku yi ƙyamarsu, ku ƙi su, gama an ware su, sun zama domin a hallaka.
”Kada ku kasance da ma’auni iri biyu a jakarku, ɗaya babba, ɗaya ƙarami. Kada ku kasance da mudu iri biyu a jakarku, ɗaya babba, ɗaya ƙarami. Dole ku kasance da ma’aunin da kuma mudun da yake daidai, kuma na gaskiya, saboda ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku. Gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamar duk mai yi waɗannan abubuwa, da kuma mai rashin gaskiya.
”“La’ananne ne mutumin da ya sassaƙa siffa, ko ya yi zubin gunki, abar ƙyama ce ga Ubangiji, aikin hannu mai sana’a da aka kafa a ɓoye.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
”“La’ananne ne mutumin da ya yi rashin adalci ga baƙo, maraya ko gwauruwa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
”“La’ananne ne mutumin da ya kashe maƙwabcinsa a ɓoye.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
”“La’ananne ne mutumin da ya karɓi cin hanci don yă kashe marar laifi.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
”“La’ananne ne mutumin da bai yi na’am da kalmomin wannan doka ta wurin aikata su ba.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
”Amma fa, in ba ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku ba, ba ku kuma lura kun bi dukan umarnansa da ƙa’idodin da nake ba ku a yau ba, dukan la’anan nan za su zo a bisanku, su kuma same ku.
”Suka sa shi kishi saboda baƙin allolinsu, suka husata shi da gumakan banƙyamarsu. Suka yi hadaya ga aljanu, waɗanda ba Allah ba, ga allolin da ba su sani ba, ga allolin da aka shigo da su daga baya, allolin da kakanninku ba su ji tsoronsu ba.
”Amma Isra’ilawa suka ce wa Ubangiji, “Mu dai mun yi zunubi. Ka yi da mu abin da ka ga dama, amma muna roƙonka ka cece mu a yanzu.”
”A kwanakin Isra’ila ba ta da sarki; kowa yana yin abin da ya ga dama.
”Wannan zunubin samarin ya yi muni ƙwarai a gaban Ubangiji, domin sun wulaƙanta hadayar Ubangiji, ƙwarai da gaske.
”Gama tawaye yana kama da zunubi na duba, girman kai kuma yana kama da bautar gumaka. Saboda ka ƙi maganar Ubangiji, shi ma ya ƙi ka da zaman sarki.”
”“Sa’ad da suka yi maka zunubi, gama babu wanda ba ya zunubi, ka kuwa yi fushi da su, ka kuma ba da su ga abokin gāba, wanda ya kwashe su kamammu zuwa ƙasarsa, nesa ko kusa;
”Suka miƙa ’ya’yansu maza da mata hadaya ta wuta. Suka yi duba, suka yi sihiri suka kuma ba da kansu ga mugunta a gaban Ubangiji; suka sa ya yi fushi. Saboda haka Ubangiji ya yi fushi ƙwarai da Isra’ila, ya kuma kawar da su daga gabansa. Kabilar Yahuda kaɗai aka bari,
”to, daga sama, mazauninka, sai ka ji addu’arsu da kuma roƙe-roƙensu, ka kuwa biya musu bukatunsu. Ka gafarta wa mutanenka, waɗanda suka yi maka zunubi.
”Ya miƙa ’ya’yansa maza hadaya a wuta cikin Kwarin Ben Hinnom, ya yi bokanci, ya yi duba, ya kuma yi maitanci, ya nemi shawarar mabiya da masu ruhohi. Ya yi abin da yake mugu ƙwarai a gaban Ubangiji, yana tsokanarsa yă yi fushi.
”Abin da yake faruwa ke nan da duk wanda yake mantawa da Allah; waɗanda ba su da Allah, ba su da bege.
”In na yi zunubi kana kallo na kuma ba za ka fasa ba ni horo ba don laifin da na yi.
”Ku kuma kun ishe ni da ƙarairayi; ku likitocin wofi ne, dukanku!
”Abubuwa nawa na yi waɗanda ba daidai ba, kuma zunubi ne? Ka nuna mini laifina da zunubina.
”“Mene ne mutum, har da zai zama da tsarki, ko kuma mace ta haife shi, har yă iya zama mai adalci?
”Sa’an nan sai ya zo wurin, wurin mutane ya ce, ‘Na yi zunubi, na kauce wa abin da yake daidai, amma ban samu abin da ya kamata in samu ba. Ya fanshi raina daga fāɗawa cikin rami, kuma zan rayu in ji daɗin hasken.’
”Mai farin ciki ne mutumin da ba ya aiki da shawarar mugaye ko yă yi abin da masu zunubi suke yi ko yă zauna tare da masu yin ba’a.
”Ba haka yake da mugaye ba! Su kamar yayi ne da iska take kwashewa. Saboda haka mugaye ba za su iya tsayawa a shari’a ba, balle a sami masu zunubi a taron adalai. Gama Ubangiji yana lura da yadda adalai suke yin abubuwa, amma ayyukan mugaye za su kai su ga hallaka.
”Har yaushe, ya ku mutane za ku mai da ɗaukakata abin kunya? Har yaushe za ku ƙaunaci ruɗu ku nemi allolin ƙarya? Sela
”Masu fariya ba za su iya tsaya a gabanka ba. Kana ƙin duk masu aikata abin da ba daidai ba. Kakan hallaka masu yin ƙarya. Masu kisankai da mutane masu ruɗu Ubangiji yana ƙyama.
”Cikin fariyarsa mugun mutum yakan cuci marasa ƙarfi, waɗanda yake kama cikin makircin da ya shirya. Yakan yi taƙama da ƙulle-ƙullen zuciyarsa; yana albarkaci mai haɗama yana kuma ƙin Ubangiji. Cikin ɗaga kai mutum ba ya neman Allah; cikin tunaninsa ba ya ba da wata dama saboda Allah.
”Bakinsa ya cika da zage-zage da ƙarairayi da kuma barazana; wahala da mugunta suna a ƙarƙashin harshensa.
”Wawaye sukan ce a ransu, “Ba Allah.” Sun lalace, ayyukansu kuwa mugaye ne; babu wani da yake yi abu mai kyau.
”Ka dubi wahalata da kuma azabata ka ɗauke mini dukan zunubaina.
”Mai farin ciki ne shi wanda aka gafarta masa laifofinsa, wanda aka shafe zunubansa.
”Sa’an nan na furta zunubina a gare ka ban kuwa ɓoye laifina ba. Na ce, “Zan furta laifofina ga Ubangiji.” Ka kuwa gafarta laifin zunubina. Sela
”Kalmomin bakinsa mugaye ne da kuma ruɗu; ya daina zama mai hikima da yin alheri.
”Kada ka yi fushi kada kuma ka yi hasala; kada ka tsorata, wannan yakan kai ga mugunta ne kawai.
”Na furta laifina; na damu da zunubina.
”Na ce, “Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai; ka warkar da ni, gama na yi maka zunubi.”
”Ka yi mini jinƙai, ya Allah, bisa ga ƙaunarka marar ƙarewa; bisa ga tausayinka mai girma ka shafe laifofina. Ka wanke dukan kurakuraina ka tsarkake ni daga zunubina. Gama ina sane da laifofina zunubaina kuma kullum suna a gabana. Kai kaɗai na yi wa zunubi na yi abin da yake mugu a idonka, ta haka an tabbatar kai mai gaskiya sa’ad da ka yi magana aka kuma nuna kai mai adalci ne sa’ad da ka hukunta.
”Tabbatacce ni mai zunubi ne tun haihuwa mai zunubi daga lokacin da mahaifiyata ta yi cikina.
”Ka ɓoye fuskarka daga zunubaina ka kuma shafe dukan kurakuraina. Ka halitta zuciya mai tsabta a cikina, ya Allah, ka kuma sabunta tsayayyen ruhu a cikina. Kada ka fid da ni daga gabanka ko ka ɗauke Ruhunka Mai Tsarki daga gare ni.
”Harshenka kan shirya hallaka; yana nan kamar reza mai ci, kana ta ruɗu.
”Wawa ne kawai yakan ce a zuciyarsa, “Ba Allah.” Sun lalace, kuma hanyoyinsu ba su da kyau; babu wani mai aikata abu mai kyau. Allah yana duba daga sama a kan ’ya’yan mutane yă ga ko akwai wani wanda ya gane, wani wanda yake neman Allah. Kowa ya kauce, gaba ɗaya sun lalace; babu guda da yake aikata abu mai kyau, babu ko ɗaya.
”Saboda zunuban bakunansu, saboda maganganun leɓunansu, bari a kama su cikin fariyarsu. Saboda zage-zage da ƙarairayin da suke yi,
”Ka san wautata, ya Allah; laifina ba a ɓoye yake daga gare ka ba.
”ba su kiyaye alkawarin Allah ba suka kuma ƙi su yi rayuwa ta wurin dokarsa.
”Amma suka ci gaba da yin masa zunubi, suna tayarwa a cikin hamada a kan Mafi Ɗaukaka.
”Kada ka riƙe zunubai kakanni a kanmu; bari jinƙanka yă zo da sauri yă sadu da mu, gama mun fid da zuciya sarai. Ka taimake mu, ya Allah Mai Cetonmu, saboda ɗaukakar sunanka; ka cece mu ka kuma gafarta mana zunubanmu saboda sunanka.
”Ka ajiye laifinmu a gabanka, asirin zunubanmu a hasken kasancewarka.
”Bari masu ƙaunar Ubangiji su ƙi mugunta, gama yana tsaron rayukan amintattunsa yana kuma kuɓutar da su daga hannun mugaye.
”Babu mai ruɗun da zai zauna a gidana; babu mai ƙaryan da zai tsaya a gabana.
”ba ya yin da mu gwargwadon zunubanmu ko yă sāka mana bisa ga laifofinmu. Gama kamar yadda sammai suke can bisa duniya, haka girmar ƙaunarsa yake wa masu tsoronsa; kamar yadda gabas yake daga yamma, haka ya cire laifofinmu daga gare mu.
”Mun yi zunubi, kamar yadda kakanninmu suka yi; mun yi ba daidai ba muka kuma aikata mugunta.
”amma suka yi cuɗanya da al’ummai suka ɗauki al’adunsu. Suka yi wa gumakansu sujada, waɗanda suka zama tarko gare su. Suka miƙa ’ya’yansu maza hadaya ’yan matansu kuma ga aljanu. Suka zub da jini marar laifi, jinin ’ya’yansu maza da mata, waɗanda suka miƙa hadaya ga gumakan Kan’ana, ƙasar kuwa ta ƙazantu ta wurin jininsu. Suka ƙazantar da kansu ta wurin abin da suka yi; ta wurin ayyukansu suka yi karuwanci.
”Albarka ta tabbata ga waɗanda rayuwarsu ba ta da abin zargi, waɗanda suke tafiya bisa ga dokar Ubangiji.
”Na ɓoye maganarka a cikin zuciyata don kada in yi maka zunubi.
”Ka ki dukan waɗanda suka kauce daga ƙa’idodinka, gama yaudararsu banza ne.
”Hawaye suna malalowa daga idanuna kamar rafi, gama ba a biyayya da dokarka. צ Tsade
”Ka bincike ni, ya Allah ka kuma san zuciyata; ka gwada ni ka kuma san damuwata. Duba ko akwai wani laifi a cikina, ka bishe ni a madawwamiyar hanya.
”Ɗana, in masu zunubi sun jarabce ka, kada ka yarda.
”Sakare da mutumin banza wanda yana yawo da magana banza a baki, wanda yake ƙyifce da ido, yana yi alama da ƙafafunsa yana kuma nuni da yatsotsinsa, wanda yake ƙulla mugunta da ruɗu a cikin zuciyarsa, kullum yana tā-da-na-zaune-tsaye
”Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi, abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi, duban reni, harshe mai ƙarya, hannuwa masu zub da jinin marar laifi, zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru, ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta, mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi, da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.
”Jin tsoron Ubangiji shi ne ƙin mugunta; ina ƙin girman kai da fariya, halin mugunta da kuma muguwar magana.
”Ubangiji yana ƙyamar mutane masu muguwar zuciya amma yana jin daɗin waɗanda hanyoyinsu ba su da laifi. Ka tabbata da wannan. Mugaye ba za su tafi babu hukunci ba, amma waɗanda suke masu adalci za su tafi babu hukunci.
”Akwai hanyar da ta yi kamar tana daidai ga mutum, amma a ƙarshe takan kai ga mutuwa.
”Ubangiji yana ƙyamar tunanin mugaye, amma waɗanda suke da tunani masu tsabta yakan ji daɗinsu. Mutum mai haɗama kan kawo wahala ga iyalinsa, amma wanda yake ƙin cin hanci zai rayu.
”Ubangiji yana ƙyamar dukan zuciya mai girman kai. Ka tabbata da wannan. Ba za su kuɓuta daga hukunci ba.
”Fitinannen mutum yakan zuga tashin hankali, mai gulma kuma yakan raba abokai na kusa.
”In mutum ya sāka alheri da mugunta, mugunta ba za tă taɓa barin gidansa ba.
”Baratar da mai laifi a kuma hukunta mai adalci, Ubangiji ya ƙi su biyu.
”Mai ba da shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba, kuma duk wanda ya baza ƙarairayi ba zai kuɓuta ba.
”Makircin wawa zunubi ne, mutane kuma sukan yi ƙyamar mai ba’a.
”Harshe mai faɗin ƙarya yana ƙin waɗanda yake ɓata musu rai, daɗin baki kuma yakan aikata ɓarna.
”In wani ya yi kunnuwa ƙashi ga doka ko addu’arsa ma abar ƙyama ce.
”Duk wanda ya ɓoye zunubansa ba ya taɓa cin nasara, amma duk wanda ya furta ya kuma ƙi su yakan sami jinƙai. Mai albarka ne mutumin da kullum yake jin tsoron Allah, amma duk wanda ya taurare zuciyarsa yakan shiga wahala.
”In mai mulki yana sauraran ƙarairayi, dukan ma’aikatansa za su zama mugaye.
”waɗanda sukan ɗauka su tsarkaka ne a ganinsu alhali kuwa ƙazamai ne su;
”Kada ranka yă yi saurin tashi, gama fushi yana zama a cinyar wawaye.
”Babu mai adalci a duniya wanda yake yin abin da yake daidai da bai taɓa yin zunubi ba.
”Yanzu an ji kome; ga ƙarshen magana. Ka ji tsoron Allah ka kuma kiyaye umarnansa, gama wannan shi ne dukan hakkin mutum. Gama Allah zai shari’anta kowane irin aiki, har da waɗanda aka yi a ɓoye, ko nagari ne, ko mugu.
”Ku yi wanka ku kuma tsabtacce kanku. Ku kawar da mugayen ayyukanku daga gabana; Ku daina aikata mugunta.
”Ubangiji ya ce, “Yanzu fa ku zo, bari mu dubi batun nan tare, Ko da zunubanku sun yi ja kamar garura, za su zama fari kamar ƙanƙara; ko da sun yi ja kamar mulufi, za su zama kamar ulu.
”Amma za a karye ’yan tawaye da masu zunubi, waɗanda suka rabu da Ubangiji kuma za su hallaka.
”Fuskokinsu shaidu ne a kansu; suna nuna zunubinsu a fili kamar yadda Sodom ya yi; ba sa ma ɓoye shi. Kaitonsu! Sun jawo wa kansu masifa.
”Kaiton waɗanda suke ce da mugunta nagarta nagarta kuma mugunta, waɗanda suke mai da duhu haske haske kuma duhu, waɗanda suke mai da ɗaci zaƙi zaƙi kuma ɗaci. Kaiton waɗanda suke tsammani suna da hikima da kuma wayo a idonsu.
”Saboda haka kamar yadda harshen wuta yakan lashe kara kuma kamar yadda busasshiyar ciyawa takan ƙone ƙurmus a cikin wuta, haka saiwarsu za su ruɓa iska kuma ta hura furanninsu kamar ƙura; gama sun ƙi dokar Ubangiji Maɗaukaki suka kuma ƙyale maganar Mai Tsarkin nan na Isra’ila.
”Zan hukunta duniya saboda muguntarta, mugaye saboda zunubansu. Zan kawo ƙarshe ga girman kan masu taƙama in kuma ƙasƙantar da ɗaga kan marasa tausayi.
”Waɗannan mutane masu tawaye, ’ya’ya masu ruɗu, ’ya’yan da ba sa niyya su saurara ga umarnan Ubangiji.
”Gama wawa maganar wauta yakan yi, zuciyarsa ta cika da mugunta, yana aikata abubuwan rashin sanin Allah yana baza kurakurai game da Ubangiji; yana barin mayunwata da yunwa ya kuma hana masu ƙishirwa ruwan sha. Matakan mazambaci mugaye ne, yana ƙulla mugayen shirye-shirye don yă hallaka talakawa da ƙarairayi, ko sa’ad da roƙon mai bukata da gaskiya ne.
”“Ni kaɗai ne na shafe laifofinku, saboda sunana, ban kuma ƙara tunawa da zunubanku ba. Ku tunashe ni abin da ya riga ya wuce, bari mu yi muhawwara wannan batu tare; ku kawo hujjarku na nuna rashin laifinku.
”Amma aka yi masa rauni saboda laifofinmu, aka ƙuje shi saboda kurakuranmu; hukuncin da ya kawo mana salama ya kasance a kansa, kuma ta wurin mikinsa ya sa muka warke. Dukanmu, muna kama da tumakin da suka ɓata, kowannenmu ya kama hanyarsa; Ubangiji kuwa ya sa hukunci ya auko a kansa hukuncin da ya wajaba a kanmu.
”Su karnuka ne masu kwaɗayi; ba su taɓa ƙoshi. Su makiyaya ne marasa ganewa; duk sun nufi inda suka ga dama, kowa yana nemar wa kansa riba.
”Wane ne kuke yi wa ba’a? Ga wa kuke masa gwalo kuna kuma fitar da harshe? Ashe, ku ba tarin ’yan tawaye ba ne, zuriyar maƙaryata?
”Amma laifofinku sun raba ku da Allahnku; zunubanku sun ɓoye fuskarsa daga gare ku, saboda kada yă ji. Gama hannuwanku sun ƙazantu da jini, yatsotsinku kuma da alhaki. Leɓunanku suna faɗin ƙarairayi, harshenku kuma yana raɗar mugayen abubuwa. Babu wani mai ce a yi adalci; babu wani mai nema a dubi al’amarinsa da mutunci. Sun dogara a gardandamin banza suna ƙarairayi; suna ɗaukar cikin ɓarna, su haifi mugunta.
”Dukanmu mun zama kamar wanda yake marar tsabta, kuma dukan ayyukanmu masu adalci sun zama kamar ƙazaman tsummoki; duk mun zama kamar busasshen ganye, kamar iska haka zunubanmu sukan share mu.
”Ko da yake ka wanke kanka da sabulu ka yi amfani da sabulu mai yawa, duk da haka har yanzu tabon laifinka yana nan a gabana,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.
”Ki dai yarda da laifinki kin yi wa Ubangiji Allahnki tawaye, kin watsar da alheranki ga baƙin alloli a ƙarƙashin kowane itace mai duhuwa, ba ki kuwa yi mini biyayya ba,’ ” in ji Ubangiji.
”Bari mu kwanta mu sha kunya, bari kuma kunyarmu ta rufe mu. Mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi, da mu da kakanninmu; daga ƙuruciyarmu har yă zuwa yau ba mu yi wa Ubangiji Allahnmu biyayya ba.”
”Ya Urushalima, ki wanke mugunta daga zuciyarki ki sami ceto. Har yaushe za ki zauna riƙe da mugayen tunani?
”Suna jin kunyar halinsu na banƙyama? A’a, ba sa jin kunya sam; ba su ma san yadda za su soke kai ba. Saboda haka za su fāɗi tare da fāɗaɗɗu; za a hamɓarar da su sa’ad da na hukunta su,” in ji Ubangiji.
”Ki ji, ya duniya. Zan kawo masifa a kan waɗannan mutane, sakayyar ƙulle-ƙullensu, domin ba su saurari maganata ba suka kuma ƙi dokata.
”Amma ga shi, kuna dogara ga maganganu na ruɗami marasa amfani. “ ‘Za ku yi sata da kisa, ku yi zina da rantsuwar ƙarya, kuna ƙone turare wa Ba’al kuna kuma bin waɗansu allolin da ba ku sani ba, sa’an nan ku zo ku tsaya a gabana a wannan gida, wanda ake kira da Sunana, kuna cewa, “An cece mu,” mun dace mu aikata waɗannan abubuwa banƙyama?
”To, me ya sa waɗannan mutane suka kauce? Me ya sa Urushalima kullum take kaucewa? Sun manne wa ƙarya; suka ƙi su dawo.
”Na saurara sosai, amma ba su faɗi wata maganar kirki ba. Ba wanda ya tuba daga muguntarsa, sai ma cewa yake, “Me na yi?” Kowa ta kai-ta-kai yake kamar dokin da ya kutsa kai a fagen fama.
”“Sun tanƙwasa harshensu kamar baka, don su harba ƙarya; ba da gaskiya ba ne suke nasara a cikin ƙasar. Sukan tashi daga wannan zunubi zuwa wancan; ba su san ni ba,” in ji Ubangiji. “Ka yi hankali da abokanka; kada ka amince da ’yan’uwanka. Gama kowane ɗan’uwa munafuki ne, kowane aboki kuma mai kushe ne. Aboki kan ruɗi aboki, ba mai faɗar gaskiya. Sun koya wa harshensu faɗar ƙarya; sun gajiyar da kansu da yin zunubi.
”Harshensu kibiya ce mai dafi; yana magana da ruɗu. Da bakinsa kowa yana maganar alheri da maƙwabcinsa, amma a zuciyarsa ya sa masa tarko.
”Ubangiji ya ce, “Domin sun bar dokata, wadda na sa a gabansu; ba su yi biyayya da ni ko su bi dokata ba. A maimako, sun bi taurin zuciyarsu; suka bi Ba’al, yadda kakanninsu suka koya musu.”
”Ko da yake zunubanmu suna ba da shaida a kanmu, Ya Ubangiji, ka yi wani abu saboda sunanka. Gama jan bayanmu ya yi yawa; mun yi maka zunubi.
”Ya Ubangiji, mun gane da muguntarmu da kuma laifin kakanninmu; tabbatacce mun yi maka zunubi.
”Zuciya ta fi kome ruɗu ta fi ƙarfin warkewa. Wa zai iya gane ta?
”A cikin annabawan Urushalima kuma na ga wani abin bantsoro. Suna zina suna kuma rayuwar ƙarya. Sun ƙarfafa hannuwa masu aikata mugunta, domin kada wani ya juya daga muguntarsa. Dukansu sun yi kama da Sodom a gare ni; mutanen Urushalima sun yi kama da Gomorra.”
”Sau da sau na aiki bayina annabawa, waɗanda suka ce, ‘Kada ku yi wannan abin ƙyama da na ƙi!’
”Sa’ad da Ubangiji bai iya jurewa da mugayen ayyukanku da kuma abubuwa banƙyama da kuka aikata ba, sai ƙasarku ta zama abin la’ana da kufai babu mazauna yadda yake a yau.
”Amma gidan Isra’ila ba sa niyya su saurare ka domin ba sa niyya su saurare ni, gama dukan gidan Isra’ila sun taurare suna kuma kin ji.
”Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kin zubar da dukiyarki kika bayyana tsiraicinki cikin fasikancinki da kwartayenki, kuma saboda dukan gumakan banƙyamarki, kuma saboda kin ba su jinin ’ya’yansu,
”“ ‘To, fa, ga zunubin ’yar’uwarki Sodom. Ita da ’ya’yanta mata sun yi girman kai, sun ƙoshi fiye da kima kuma ba su kula da wani abu ba; ba su taimaki matalauta da kuma masu bukata ba.
”Gama kowane mai rai nawa ne, mahaifi da ɗa, duk nawa ne. Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu.
”Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu. Ɗa ba zai sami rabo a laifin mahaifi ba, mahaifi ba zai sami rabo a laifi ɗa ba. Adalcin adali zai zama nasa, muguntar mugu za tă koma kansa.
”“Amma in mugun mutum ya juya daga dukan zunubin da ya aikata ya kuma kiyaye dukan ƙa’idodina ya kuwa yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba. Babu laifin da ya yi da za a tuna da su. Saboda abubuwan adalcin da ya aikata, zai rayu. Ina jin daɗin mutuwar mugu ne? In ji Ubangiji Mai Iko Duka. A maimako, ban fi jin daɗi sa’ad da suka juyo daga hanyoyinsu suka rayu ba?
”“Amma in mai adalci ya juya daga adalcinsa ya yi zunubi ya kuma aikata abubuwa masu banƙyamar da mugun mutum ke aikatawa, zai rayu? Babu abubuwan adalcin da ya aikata da za a tuna da su. Saboda rashin amincinsa da kuma saboda zunubai da ya yi, zai mutu.
”In mai adalci ya juye daga adalcinsa ya yi zunubi, zai mutu saboda wannan; saboda zunubin da ya yi, zai mutu.
”Amma in mugun mutum ya juye daga muguntarsa ya kuma yi abin da yake daidai da kuma gaskiya, zai ceci ransa. Domin ya lura da dukan laifofin da ya yi ya kuma juye daga gare su, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba.
”“Saboda haka, ya gidan Isra’ila, zan hukunta ku, kowa bisa ga hanyarsa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tuba! Ku juye daga dukan laifofinku; sa’an nan zunubi ba zai zama sanadin fāɗuwarku ba. Ku raba kanku da dukan laifofin da kuka yi, ku sami sabuwar zuciya da sabon ruhu. Don me za ku mutu, ya gidan Isra’ila? Gama ba na jin daɗin mutuwar wani, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Ku tuba don ku rayu!
”A can za ku tuna da halinku da kuma dukan ayyukanku waɗanda kuka ɓata kanku da su, za ku kuwa ji ƙyamar kanku saboda mugayen abubuwan da kuka aikata.
”In adali ya juye daga adalcinsa ya yi mugunta, zai mutu saboda haka. Kuma in mugu ya juye daga muguntarsa ya aikata abin da yake gaskiya da kuma daidai, zai rayu ta yin haka.
”Kun dogara ga takobinku, kuka aikata abubuwan banƙyama, kowannenku kuma ya ƙazantar da matar maƙwabcinsa. Kuna gani za ku mallaki ƙasar?’
”Akwai la’ana ce kawai, yin ƙarya da kisa, yin sata da zina; sun wuce gona da iri, kisankai a kan kisankai.
”Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Yahuda, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Gama sun ƙi bin dokar Ubangiji ba su kuma yi biyayya da ƙa’idodinsa ba, domin allolin ƙarya sun ruɗe su, allolin da kakanninsu suka bauta.
”Zan kuɓutar da mutumin da yake da ma’auni na rashin gaskiya, da kuma buhun ma’aunan ƙarya? Attajiranta masu fitina ne; mutanenta kuma maƙaryata ne harsunansu kuwa suna yaudara.
”“Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
”Za tă haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, gama shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.”
”Mutane suka zo wurinsa daga Urushalima da dukan Yahudiya da kuma dukan yankin Urdun. Suna furta zunubansu, ya kuma yi musu baftisma a Kogin Urdun.
”‹“Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā cewa, ‘Kada ka yi kisankai;›‹kuma duk wanda ya yi kisankai za a hukunta shi.’› ‹Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗan’uwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗan’uwansa ‘ Raka,’›‹za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta.›
”‹“Kun dai ji an faɗa, ‘Kada ka yi zina.’› ‹Amma ina gaya muku, duk wanda ya dubi mace, sa’an nan ya yi sha’awarta a zuci, ya riga ya yi zina ke nan da ita a zuciyarsa.› ‹In idonka na dama yana sa ka yin zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.› ‹In kuma hannunka na dama yana sa ka yin zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.›
”‹“An kuma faɗa, ‘Duk wanda ya saki matarsa, dole yă ba ta takardar saki.’› ‹Amma ina gaya muku, duk wanda ya saki matarsa in ba a kan laifin zina ba, ya sa ta zama mazinaciya ke nan, kuma duk wanda ya auri macen da mijinta ya sake, shi ma yana zina ne.›
”‹Saboda haka sai ku zama cikakku, yadda Ubanku na sama yake cikakke.›
”‹Kada ka bari a kai mu cikin jarraba,› ‹amma ka cece mu daga mugun nan.›‹’›
”‹Gama in kuna yafe wa mutane sa’ad da suka yi muku laifi, Ubanku da yake cikin sama ma zai gafarta muku.› ‹Amma in ba kwa yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku ma ba zai gafarta muku zunubanku ba.›
”‹Haka ma kowane itace mai kyau yakan ba da ’ya’ya masu kyau, kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau.› ‹Itace mai kyau ba ya ba da munanan ’ya’ya, haka kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau.› ‹Duk itacen da ba ya ba da ’ya’ya masu kyau sai a sare shi a jefa cikin wuta.› ‹Ta haka, ta wurin aikinsu za ku gane su.”›
”‹“Ba duk mai ce mini, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ne zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda yake aikata nufin Ubana da yake sama.› ‹Da yawa za su ce mini a wannan rana, ‘Ubangiji, Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, ba kuma a cikin sunanka ne muka fitar da aljanu, muka yi abubuwan banmamaki da yawa ba?’› ‹Sa’an nan zan ce musu a fili, ‘Ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!’›
”‹Saboda haka ina gaya muku, za a gafarta wa mutane kowane zunubi da kuma saɓo, amma saɓo game da Ruhu, ba za a gafarta ba.› ‹Duk wanda ya zargi Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya zargi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, ko a wannan zamani ko a zamani mai zuwa.›
”‹Amma ina gaya muku cewa mutane za su ba da lissafi a ranar shari’a a kan kowace kalmar banza da suka faɗa.› ‹Gama ta wurin kalmominka za a kuɓutar da kai, kuma ta wurin kalmominka za a hukunta ka.”›
”‹Gama daga zuciya ne mugayen tunani, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar ƙarya, ɓatan suna, suka fitowa.›
”‹Me mutum zai amfana in ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa? Ko kuwa me mutum zai bayar a bakin ransa?›
”‹“Amma duk wanda ya sa ɗaya daga cikin ƙananan nan da suka gaskata da ni ya yi zunubi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku.›
”‹In hannunka ko ƙafarka yana sa ka zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da hannu ko ƙafa ɗaya da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu da a jefar da kai cikin madawwamiyar wuta da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu.› ‹In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da ido ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta da idanunka biyu.›
”‹“In ɗan’uwanka ya yi maka laifi, ka je ka nuna masa laifinsa, tsakaninku biyu kaɗai. In ya saurare ka, ka maido da ɗan’uwanka ke nan.› ‹Amma in bai saurare ka ba, ka je tare da mutum ɗaya ko biyu, domin ‘a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.’› ‹In kuwa ya ƙi yă saurare su, sai ka gaya wa ikkilisiya; in kuma ya ƙi yă saurari ikkilisiya ma, ka yi da shi kamar marar sanin Allah ko mai karɓar haraji.›
”Sai Bitrus ya zo wurin Yesu ya yi masa tambaya ya ce, “Ubangiji, sau nawa zan yafe wa ɗan’uwana sa’ad da ya yi mini zunubi? Har sau bakwai?” Yesu amsa ya ce, ‹“Ina gaya maka, ba sau bakwai ba, amma sau saba’in da bakwai.›
”‹“Haka Ubana da yake cikin sama zai yi da kowannenku, in ba ku yafe wa ’yan’uwanku daga zuciyarku ba.”›
”‹Ina faɗa muku cewa duk wanda ya saki matarsa, sai dai a kan rashin aminci a cikin aure, ya kuwa auri wata, ya yi zina ke nan.”›
”To, fa, sai ga wani ya zo wurin Yesu ya tambaye shi ya ce, “Malam, wane abu mai kyau ne ya zama mini dole in yi don in sami rai madawwami?” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Don me kake tambayata game da abin da yake mai kyau? Akwai Mai kyau Ɗaya kaɗai. In kana so ka sami rai madawwami, ka kiyaye dokokin nan.”› Mutumin ya yi tambaya ya ce, “Waɗanne?” Yesu ya amsa ya ce, ‹“ ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar ƙarya,› ‹ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’›‹ka kuma ‘ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’›‹”›
”‹“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan wanke bayan kwaf da kwano, amma a ciki, cike suke da zalunci da sonkai.›
”‹Saboda ƙaruwar mugunta, ƙaunar yawanci za tă yi sanyi,›
”‹Wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubai.›
”‹Ku yi tsaro, ku kuma yi addu’a, don kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.”›
”Ta haka Yohanna ya zo, yana baftisma a yankin hamada, yana kuma wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai. Dukan ƙauyukan Yahudiya da dukan mutanen Urushalima suka fiffito zuwa wurinsa. Suna furta zunubansu, ya kuwa yi musu baftisma a Kogin Urdun.
”Yana cewa, ‹“Lokaci ya yi. Mulkin Allah ya yi kusa. Ku tuba, ku gaskata bishara!”›
”Ya ci gaba, ‹“Abin da yake fitowa daga mutum ne yake ƙazantar da shi.› ‹Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina,› ‹kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen sha’awa, kishi, ɓata suna, girman kai da kuma wauta.› ‹Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ƙazantar da mutum.”›
”‹In hannunka yana sa ka yin zunubi, yanke shi. Ai, gwamma ka shiga rai da hannu ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta, inda ba a iya kashe wutar ba, da hannuwanka biyu.›
”‹In kuma ƙafarka tana sa ka yin zunubi, yanke ta. Ai, gwamma ka shiga rai da ƙafa ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da ƙafafunka biyu.›
”‹In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi. Ai, gwamma ka shiga mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da idanu biyu,› ‹inda› ‹“ ‘tsutsotsinsu ba sa mutuwa,› ‹wutar kuma ba a iya kashewa.’›
”Da Yesu ya kama hanya, sai wani mutum ya ruga da gudu ya zo wajensa, ya durƙusa a gabansa ya ce, “Malam nagari, me zan yi domin in gāji rai madawwami?” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Don me kake ce da ni mai nagarta? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai.› ‹Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, kada ka cuci wani, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’›‹”›
”‹A duk lokacin da kuke tsaye cikin addu’a, in kuna riƙe da wani mutum a zuciyarku, ku gafarta masa, domin Ubanku da yake sama shi ma yă gafarta muku zunubanku.”›
”‹Ku yi tsaro, ku kuma yi addu’a, domin kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.”›
”don ka sanar da mutanensa ceto, ta wurin gafarar zunubansu,
”Ya zaga dukan ƙasar da take kewaye da Urdun, yana wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai.
”Yesu ya amsa musu ya ce, ‹“Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya.› ‹Ban zo don in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi zuwa ga tuba.”›
”‹“Saboda haka ina gaya maka, zunubanta masu yawa, an gafarta mata, gama ƙaunarta mai yawa ce. Amma wanda aka gafarta wa kaɗan kuwa, yakan nuna ƙauna kaɗan.”› Sai Yesu ya ce mata, ‹“An gafarta miki zunubanki.”› Sauran baƙin suka fara ce wa juna, “Wane ne wannan, wanda har yake gafarta zunubai?”
”‹Na kan dutse kuwa, su ne da jin maganar, sukan karɓa da murna, amma ba su da saiwa. Sukan gaskata na ɗan lokaci, amma lokacin gwaji, sai su ja da baya.›
”‹Ka gafarta mana zunubanmu,› ‹kamar yadda mu ma ke gafarta wa duk wanda ya yi mana laifi.› ‹Kada ka bari a kai mu cikin jarraba.’ ”›
”‹Ina gaya muku, haka za a yi murna sosai a sama, a kan mai zunubi guda ɗaya da ya tuba, fiye da masu adalci tasa’in da tara, waɗanda ba su bukatan tuba.›
”‹Haka, ina gaya muku, akwai murna a gaban mala’ikun Allah a kan mai zunubi guda ɗaya, da ya tuba.”›
”‹“Sai ya ce, ‘A’a, ya uba, Ibrahim, in dai wani ya tashi daga matattu ya je wurinsu, za su tuba.’› ‹“Amma ya ce masa, ‘In ba su saurari Musa da Annabawa ba, kai, ko da wani ya tashi daga matattu ma, ba za su saurare shi ba.’ ”›
”‹Saboda haka, ku lura da kanku.› ‹“In ɗan’uwanka ya yi zunubi, ka kwaɓe shi. In ya tuba, ka gafarta masa.› ‹In ya yi maka laifi sau bakwai a rana ɗaya, ya kuma dawo sau bakwai ɗin a wurinka, yana cewa, ‘Na tuba,’ sai ka gafarta masa.”›
”‹“Amma mai karɓar harajin ya tsaya daga nesa. Bai ma iya ɗaga kansa sama ba, sai ya buga ƙirjinsa, yana cewa, ‘Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi ne.’›
”Wani mai mulki ya tambayi Yesu ya ce, “Malam managarci, me zan yi don in gāji rai madawwami?” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Don me kake kira na managarci? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai.› ‹Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”›
”‹Kuma a cikin sunansa za a yi wa’azin tuba da gafarar zunubai, ga dukan ƙasashe. Za a kuwa fara daga Urushalima.›
”Kashegari Yohanna ya ga Yesu yana zuwa wajensa sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah mai ɗauke zunubin duniya!
”‹Kamar dai yadda Musa ya ɗaga maciji a hamada, haka dole ne a ɗaga Ɗan Mutum,› ‹don duk mai gaskata da shi ya sami rai madawwami.”› Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa. Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba. Hukuncin shi ne, Haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka so duhu a maimakon haske domin ayyukansu mugaye ne. Duk mai aikata mugunta yana ƙin haske, ba zai kuwa zo cikin haske ba don yana tsoro kada ayyukansa su tonu. Amma duk mai rayuwa bisa ga gaskiya yakan zo cikin haske, domin a gani a sarari cewa ayyukan da ya yi an yi su ne ta wurin Allah.
”Daga baya Yesu ya same shi a haikali ya ce masa, ‹“Ga shi, ka warke. Ka daina yin zunubi, in ba haka ba wani abin da ya fi wannan muni zai iya samunka.”›
”suka kuma ce wa Yesu, “Malam, an kama wannan mace tana zina. A cikin Doka Musa ya umarce mu, mu jajjefe irin waɗannan mata. To, me ka ce?” Sun yi wannan tambaya ce don su sa masa tarko, don su sami hanyar zarge shi. Amma Yesu ya sunkuya ya fara rubutu a ƙasa da yatsarsa. Da suka ci gaba da yin masa tambayoyi, sai ya miƙe tsaye ya ce musu, ‹“In da wani a cikinku da ba shi da zunubi, sai yă fara jifanta da dutse.”› Sai ya sāke sunkuyawa ya kuma yi rubutu a ƙasa. Da jin haka, waɗanda suka ji sai suka fara tashi daga wurin ɗaya-ɗaya, tun daga babbansu har ya zuwa ƙaraminsu, sai da aka bar Yesu kaɗai, tare da macen tsaye a wurin. Sai Yesu ya miƙe tsaye ya tambaye ta ya ce, ‹“Mace, ina suke? Ba wanda ya hukunta ki?”› Ta ce, “Ba kowa, ranka yă daɗe.” Sai Yesu ya ce, ‹“Haka ni ma ban hukunta ki ba. Ki tafi, ki daina rayuwar zunubi.”›
”‹Na gaya muku cewa za ku mutu cikin zunubanku; in ba ku gaskata cewa ni ne wanda na ce nake ba, lalle za ku mutu cikin zunubanku.”›
”Yesu ya amsa ya ce, ‹“Gaskiya nake gaya muku, duk mai yin zunubi bawan zunubi ne.›
”Mun san cewa Allah ba ya sauraron masu zunubi. Yakan saurari mai tsoronsa mai aikata nufinsa.
”‹Akwai mai hukunci saboda wanda ya ƙi ni, bai kuma karɓi kalmomina ba; wannan maganar da na faɗa ita ce za tă hukunta shi a rana ta ƙarshe.›
”‹“In kuna ƙaunata za ku yi biyayya da umarnina.›
”‹Sa’ad da ya zo kuwa, zai kā da duniya a kan zunubi da adalci da kuma hukunci,› ‹a kan zunubi, domin mutane ba su gaskata da ni ba;› ‹a kan adalci, domin zan tafi wurin Uba, inda ba za ku ƙara ganina ba;› ‹a kan hukunci kuma, domin an yanke hukunci a kan mai mulkin duniyan nan.›
”Bitrus ya amsa, “Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki.
”Saboda haka ku tuba, ku juyo ga Allah, don a shafe zunubanku, don lokutan wartsakewa su zo daga wurin Ubangiji,
”“Ku mutane masu taurinkai, da zukata da kuma kunnuwa marasa kaciya! Kuna kama da kakanninku. Kullum kuna tsayayya da Ruhu Mai Tsarki!
”Ka tuba daga wannan mugunta ka kuma yi addu’a ga Ubangiji. Wataƙila zai gafarta maka don irin tunanin da yake a zuciyarka.
”Yanzu me kake jira? Ka tashi, a yi maka baftisma, a wanke zunubanka, ta wurin kira bisa ga sunansa.’
”Ana bayyana fushin Allah daga sama a kan dukan rashin sanin Allah da kuma muguntar mutanen da suke danne gaskiya ta wurin muguntarsu,
”Saboda haka Allah ya yashe su ga mugayen sha’awace-sha’awacen zukatansu ga fasikanci don a ƙasƙantar da jikunansu ga yin abin kunya. Sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, suka kuma yi wa abubuwan da aka halitta sujada suna bauta musu a maimakon Mahalicci, wanda ake yabo har abada. Amin. Saboda wannan, Allah ya yashe su ga sha’awace-sha’awacensu masu banƙyama. Har matansu suka sauya daga haɗuwar mace da miji wadda ita ce daidai bisa ga halitta zuwa haɗuwa da ’yan’uwansu mata wadda ba daidai ba. Haka ma maza suka bar al’adar kwana da mata suka tunzura cikin sha’awar kwana da juna, abin da ba daidai ba bisa ga halitta. Maza suka aikata rashin kunya da waɗansu maza, suka jawo wa kansu sakamako daidai da bauɗewarsu.
”Da yake ba su yi tunani cewa ya dace su riƙe sanin Allah da suke da shi ba, sai ya yashe su ga tunanin banza da wofi, su aikata abin da bai kamata a yi ba. Sun cika da kowace irin ƙeta, mugunta, kwaɗayi, da tunanin banza da wofi. Suka kuma cika da kishi, kisankai, faɗa, ruɗu, da kuma riƙo a zuci. Su masu gulma ne, da masu ɓata suna, masu ƙin Allah, masu rashin kunya, masu girman kai, masu rigima; sukan ƙaga hanyoyin yin mugunta; suna rashin biyayya ga iyayensu; su marasa hankali ne, marasa bangaskiya, marasa ƙauna, marasa tausayi. Ko da yake sun san dokar adalcin Allah cewa masu aikata irin waɗannan abubuwa sun cancanci mutuwa, duk da haka ba cin gaba da aikata waɗannan abubuwa kaɗai suke yi ba, har ma suna goyon bayan masu yinsu.
”Saboda haka, kai da kake ba wa wani laifi, ba ka da wata hujja, gama a duk lokacin da kake ba wa wani laifi, kana hukunta kanka ne, domin kai da kake ba wa wani laifi kai ma kana aikata waɗannan abubuwa.
”Amma ga waɗanda suke sonkai waɗanda suke ƙin gaskiya suke kuma bin mugunta, akwai fushi da haushi dominsu. Akwai wahala da baƙin ciki ga duk mutumin da yake aikata mugunta, da farko Yahudawa, sa’an nan Al’ummai,
”Wannan zai faru a ranar da Allah ta wurin Yesu Kiristi zai shari’anta ɓoyayyun abubuwan da mutane suka yi, yadda bisharata ta furta.
”To, me za mu ce ke nan? Mun fi su ke nan? Ina, ko kaɗan! Mun riga mun zartar cewa da Yahudawa da Al’ummai duk suna a ƙarƙarshin zunubi. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Babu wani mai adalci, babu ko ɗaya; babu wani mai fahimta, babu wani mai neman Allah. Duk sun kauce gaba ɗaya, sun zama marasa amfani; babu wani mai aikata nagarta, babu ko ɗaya.”
”“Babu tsoron Allah a idanunsu.” Yanzu mun san cewa dukan abin da doka ta ce, tana magana ne ga waɗanda suke ƙarƙarshin doka, saboda a rufe kowane baki; dukan duniya kuma ta ba da lissafin kanta a gaban Allah.
”Saboda haka babu wanda Allah zai ce da shi mai adalci ta wurin kiyaye doka kawai; a maimako, ta wurin doka ne muke sane da zunubi.
”gama duka sun yi zunubi suka kuma kāsa ga ɗaukakar Allah, an kuma kuɓutar da su kyauta ta wurin alherinsa bisa ga aikin fansar da ya zo ta wurin Yesu Kiristi. Allah ya miƙa Yesu Kiristi a matsayin hadayar kafara, ta wurin bangaskiya cikin jininsa. Ya yi haka domin yă nuna adalcinsa, domin a cikin haƙurinsa bai hukunta zunuban da aka aikata a dā ba
”“Masu albarka ne waɗanda aka gafarta laifofinsu, waɗanda aka kuma rufe zunubansu.
”Amma Allah ya nuna mana ƙaunarsa a wannan. Tun muna masu zunubi tukuna, Kiristi ya mutu dominmu. Da yake yanzu mun sami zama marasa laifi ta wurin jininsa, ashe kuwa za a cece mu daga fushin Allah ta wurinsa!
”Saboda haka, kamar yadda zunubi ya shigo duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuma ta wurin zunubi, ta haka kuwa mutuwa ta shafi dukan mutane, domin dukan mutane sun yi zunubi. Gama kafin a ba da doka, zunubi yana nan a duniya. Amma ba a lissafin zunubi inda babu doka.
”An ba da dokar don mu ga yadda laifi yake da girma. Amma da zunubi ya ƙaru, sai alheri ya ƙaru sosai, domin, kamar yadda zunubi ya yi mulki cikin mutuwa, haka ma alheri yă yi mulki ta wurin adalci yă kuwa kawo rai madawwami ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu.
”Me za mu ce ke nan? Za mu ci gaba da yin zunubi domin alheri yă haɓaka? Sam, ko kaɗan! Mun mutu ga zunubi; ta yaya za mu ci gaba da rayuwa a cikinsa kuma? Ko ba ku sani ba cewa dukanmu da aka yi wa baftisma a cikin Kiristi Yesu an yi mana baftismar ne zuwa cikin mutuwarsa?
”Saboda haka, an binne mu da shi ke nan, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa, domin kamar yadda aka tā da Kiristi daga matattu ta wurin ɗaukakar Uba, haka mu ma mu yi zaman sabuwar rayuwa. In kuwa mun zama ɗaya tare da shi haka a cikin mutuwarsa, tabbatacce mu ma za mu zama ɗaya tare da shi cikin tashinsa daga matattu. Gama mun san cewa an gicciye halayenmu na dā tare da shi domin a kawar da jikin nan mai zunubi don kada mu ƙara zama bayi ga zunubi domin duk wanda ya mutu an ’yantar da shi daga zunubi ke nan.
”domin duk wanda ya mutu an ’yantar da shi daga zunubi ke nan. To, in mun mutu tare da Kiristi, mun gaskata cewa za mu rayu tare da shi kuma. Gama mun san cewa da yake an tā da Kiristi daga matattu, ba zai sāke mutuwa ba; mutuwa ba ta da sauran iko a kansa. Mutuwar da ya yi, ya mutu ne sau ɗaya tak, saboda yă shafe zunubi, amma rayuwar da yake yi, yana yi ne cikin tarayya da Allah. Haka ku ma, ku ɗauke kanku matattu ne ga ikon zunubi amma rayayyu cikin tarayya da Allah cikin Kiristi Yesu.
”Saboda haka kada ku bar zunubi yă mallaki jikin nan naku mai mutuwa yă sa ku zama masu biyayya ga mugayen sha’awace-sha’awacensa. Kada ku miƙa gaɓoɓin jikinku ga zunubi a matsayin kayan aikin mugunta, sai dai ku miƙa kanku ga Allah, a matsayin waɗanda aka fitar da su daga mutuwa zuwa rai; ku kuma miƙa gaɓoɓin jikinku gare shi a matsayin kayan aikin adalci. Gama zunubi ba zai zama maigidanku ba, domin ba kwa ƙarƙashin doka, sai dai ƙarƙashin alheri.
”Me za mu ce ke nan? Za mu ci gaba yin zunubi domin ba ma ƙarƙashin doka sai dai ƙarƙashin alheri? Sam, ko kaɗan! Ba ku sani ba cewa sa’ad da kuka miƙa kanku ga wani don ku yi masa biyayya a matsayin bayi, ko ku bayi ne ga zunubi, wanda yake kai ga mutuwa, ko kuwa ga biyayya, wadda take kai ga adalci, ashe, ba kun zama bayi ga wannan da kuke yi wa biyayya ba ke nan?
”Amma godiya ga Allah don ko da yake a dā ku bayi ne ga ikon zunubi, da dukan zuciyarku kun yi biyayya ga irin koyarwar da aka danƙa muku. An ’yanta ku daga zunubi, kun kuma zama bayi ga aikin adalci. Ina magana ne kamar mutane saboda kun raunana a jikinku. Kamar yadda kuka saba miƙa gaɓoɓin jikinku a bautar abubuwan ƙazanta da mugun aiki a kan mugun aiki, saboda haka yanzu sai ku miƙa su bayi ga aikin adalci mai kai ga zaman tsarki.
”Sa’ad da kuke bayin zunubi, ba ruwanku da aikin adalci. Wace riba ce kuka samu a lokacin, daga abubuwan nan da yanzu suka zama muku abin kunya? Ƙarshen irin abubuwan nan dai, mutuwa ne!
”Amma a yanzu da aka ’yantar da ku daga zunubi kuka kuma zama bayi ga Allah, ribar da kuka samu tana kai ga zaman tsarki, ƙarshenta kuwa rai madawwami ne. Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
”Gama sa’ad da halin mutuntaka yake mulkinmu, sha’awace-sha’awacen zunubi waɗanda dokar ta zuga sun yi ta aiki a jikunanmu, don mu ba da amfani wa mutuwa. Amma yanzu, ta wurin mutuwa ga abin da dā ya daure mu, an sake mu daga dokar saboda mu yi hidima a sabuwar hanyar Ruhu, ba a tsohuwar hanyar rubutaccen ƙa’ida ba.
”Me za mu ce ke nan? Dokar zunubi ce? Sam, ko kaɗan! Tabbatacce ai, da ban san mene ne zunubi ba in ba ta wurin doka ba. Gama da ban san mene ne ƙyashi yake ba tabbatacce in ba don doka ta ce, “Kada ka yi ƙyashi ba.” Amma zunubi, da ya sami dama ta wurin umarnin nan, ya haifar a cikina kowane halin ƙyashi iri-iri. Gama in babu doka, zunubi matacce ne. Dā kam ina da rai sa’ad da ban san doka ba; amma da umarni ya zo, sai zunubi ya zaburo da rai na kuma mutu. Na gane cewa wannan umarnin da aka nufa ya kawo rai, a gaskiya ya jawo mutuwa ce. Gama zunubi, da ya sami dama ta wurin umarni, sai ya ruɗe ni, kuma ta wurin umarnin kuwa ya kashe ni.
”Amma zunubi, da ya sami dama ta wurin umarnin nan, ya haifar a cikina kowane halin ƙyashi iri-iri. Gama in babu doka, zunubi matacce ne.
”Abin nan da yana mai kyau, zai kawo mini mutuwa? Ko kaɗan! Amma domin zunubi ya bayyana kansa a matsayin zunubi, sai ya haifar da mutuwa a cikina ta wurin abin da yake mai kyau, domin ta wurin umarnin nan zunubi ya fito da matuƙar muninsa.
”Mun san cewa doka aba ce ta ruhu; amma ni ba na ruhu ba ne, an sayar da ni a matsayin bawa ga zunubi. Ban gane abin da nake yi ba. Don abin da nakan so yi, ba shi nakan yi ba, sai dai abin da nake ƙi, shi nake yi. In kuma na yi abin da ba na son yi, na yarda da cewa dokar aba ce mai kyau. Kamar dai yadda yake, ba ni kaina nake yinsa ba, sai dai zunubin da yake zaune a cikina ne. Gama na san cewa babu wani abin kirkin da yake zaune a cikina, wato, a mutuntakata. Gama sha’awar yin abu mai kyau kam ina da ita, sai dai ikon yin ne fa babu. Gama abin da nake yi ba shi ne abu mai kyau da nake so in yi ba; a’a, mugun da ba na so in yi, shi ne nake ci gaba da yi. To, in na yi abin da ba na so in yi, ba ni ba ne nake yinsa, sai dai zunubin nan da yake zaune a cikina.
”Saboda haka na gane wannan ƙa’ida ce take aiki a cikina. Sa’ad da nake so in yi abu mai kyau, sai in ga cewa mugun nan ne nake yi. Gama a ciki-cikina ina farin cikin da dokar Allah; amma ina ganin wata doka tana aiki a gaɓoɓin jikina, tana yaƙi da dokar hankalina, tana kuma sa in zama ɗaurarren dokar zunubin da take aiki a gaɓoɓin jikina. Kaitona! Wane ne zai cece ni daga wannan jiki mai mutuwa? Godiya ga Allah ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu! Saboda haka fa, ni kaina a cikin hankalina, ni bawa ne ga dokar Allah, amma a mutuntaka, ni bawa ne ga dokar zunubi.
”Saboda haka, yanzu babu hukunci don waɗanda suke cikin Kiristi Yesu, gama ta wurin Kiristi Yesu dokar Ruhu mai ba da rai ta ’yantar da ni daga Dokar Musa. Gama abin da dokar ba tă iya yi saboda kāsawar mutuntaka ba, Allah ya yi shi sa’ad da ya aiko da Ɗansa a kamannin mutum mai zunubi, don yă zama hadaya ta zunubi. Ta haka, ya hukunta zunubi a cikin mutum mai zunubi. Ya yi haka domin yă cika bukatun adalcin doka a cikinmu, mu da ba ma rayuwa bisa ga mutuntaka, sai dai bisa ga Ruhu. Waɗanda suke rayuwa bisa ga mutuntaka sun kafa hankulansu a kan sha’awace-shawa’acen jiki; amma waɗanda suke rayuwa bisa ga Ruhu sun kafa hankulansu a kan abubuwan da Ruhu yake so. Ƙwallafa rai ga al’amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga al’amuran Ruhu kuwa rai ne da salama; hankalin mai zunubi na gāba da Allah. Ba ya biyayya da dokar Allah, ba kuwa zai iya yin haka ba. Waɗanda mutuntaka yake mulkinsu ba za su iya su gamshi Allah ba.
”Saboda haka ’yan’uwa, muna da hakki, amma ba na wanda za mu yi rayuwar mutuntaka da yake so ba. Gama in kuna rayuwa bisa ga mutuntaka, za ku mutu; amma in ta wurin Ruhu kuka kashe ayyukan jikin nan, za ku rayu.
”Wannan kuwa shi ne alkawarina da su sa’ad da na ɗauke musu zunubansu.”
”Dole ƙauna tă zama ta gaskiya. Ku ƙi duk abin da yake mugu; ku manne wa abin da yake nagari.
”Umarnan nan, “Kada ka yi zina.” “Kada ka yi kisankai.” “Kada ka yi sata.” “Kada kuma ka yi ƙyashi.” Da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”
”Bari mu tafiyar da al’amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa ba, ba cikin fasikanci da rashin kunya ba, ba kuma cikin faɗa da kishi ba. A maimakon haka, ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Kiristi, kada kuma ku yi tunani game da yadda za ku gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka.
”Kai kuwa, don me kake ganin laifin ɗan’uwanka? Ko kuma don me kake rena ɗan’uwanka? Gama duk za mu tsaya a gaban kujerar shari’ar Allah.
”Amma wanda yake da shakka yakan jawo wa kansa hukunci ne in ya ci, domin yana ci ne ba bisa ga bangaskiya ba; kuma duk abin da bai zo daga bangaskiya ba zunubi ne.
”Ina roƙonku, ’yan’uwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su. Gama irin waɗannan mutane ba sa bautar Ubangijinmu Kiristi, sai dai cikinsu. Ta wurin yaudara da kuma daɗin baki, suna ruɗin marasa wayo.
”Ashe, ba ku sani ba cewa ku kanku haikalin Allah ne, Ruhun Allah kuma yana zaune a cikinku? Duk wanda ya ɓata haikalin Allah, Allah zai ɓata shi, don haikalin Allah mai tsarki ne, ku ne kuwa haikalin nan.
”Na rubuta muku cikin wasiƙata, kada ku yi haɗa kai da masu aikin lalata. Ko kusa, ba na nufin fasikai marasa bi, ko makwaɗaita da mazambata, ko matsafa, don in haka ne, sai yă zama dole ku fita daga duniya. Yanzu dai ina rubuta muku cewa kada ku haɗa kai da duk mai kiran kansa ɗan’uwa, amma yana fasikanci, ko kwaɗayi, ko bautar gumaka, ko ɓata suna, ko mashayi, ko mazambaci. Kada ku ko ci abinci da irin wannan mutum. Me zai kai yin hukunci ga waɗanda ba ’yan ikkilisiya ba. Ai, waɗanda suke ’yan ikkilisiya ne za ku hukunta. Allah zai hukunta waɗanda ba namu ba. “Ku yi waje da irin mugun mutumin nan daga cikinku.”
”Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ’yan daudu, ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah. Haka waɗansu a cikinku ma suke a dā. Amma an wanke ku, an tsarkake ku, aka kuma sa kuka zama marasa laifi cikin sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma ta wurin Ruhun Allahnmu.
”Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubai da mutum yakan aikata suna waje da jikinsa, amma mai yin fasikanci, yana ɗaukar alhalin jikinsa ne. Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne; saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku.
”Kada fa mu yi fasikanci yadda waɗansunsu suka yi, har a rana guda mutane dubu ashirin da uku a cikinsu suka mutu. Kada mu gwada Kiristi yadda waɗansunsu suka yi, har macizai suka kakkashe su. Kada kuma ku yi gunaguni yadda waɗansunsu suka yi, har mala’ika mai hallakarwa ya hallaka su. Waɗannnan abubuwa sun same su ne, domin su zama abubuwan koyi, aka kuma rubuta su domin a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana. Saboda haka in kana tsammani kana tsaye ne, to, ka yi hankali kada ka fāɗi!
”Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.
”Gama abu farko mafi muhimmancin da na karɓo shi ne na ba ku cewa Kiristi ya mutu domin zunubanmu bisa ga Nassi, cewa an binne shi an kuma tashe shi a rana ta uku bisa ga Nassi,
”Kada fa a ruɗe ku, “Ajiyar mugayen abokai yana ɓata hali mai kyau.” Ku koma cikin hankalinku yadda ya kamata, ku kuma daina yin zunubi, gama akwai waɗansu da ba su san Allah ba, na faɗi wannan ne don ku kunyata.
”Zunubi ne yake ba wa mutuwa dafi, Doka kuma take ba wa zunubi iko.
”Gama dole dukanmu mu bayyana a gaban kujerar shari’ar Kiristi, domin kowannenmu yă karɓi ladan aikin da ya yi a wannan jiki, ko mai kyau ne ko marar kyau.
”Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi kamar hadayar zunubi saboda mu, domin mu sami adalcin Allah ta wurinsa.
”Da yake muna da waɗannan alkawura, ya ku ƙaunatattu, sai mu tsarkake kanmu daga kowane abu da yake ƙazantar da jiki, da ruhu, mu zama da cikakken tsarki, saboda bangirma ga Allah.
”Gama ina tsoro, in na zo, in tarar da ku dabam da yadda nake so, ku ma ku tarar da ni dabam da yadda kuke so. Ina tsoro kada yă zama akwai faɗa, da kishi, da fushi mai zafi, da tsattsaguwa, da ɓata suna, da gulma, da girman kai, da hargitsi. Ina tsoro kada sa’ad da na sāke zuwa, Allahna zai ƙasƙantar da ni a gabanku, kuma in yi baƙin ciki saboda waɗanda suka yi zunubi a dā, ba su kuma tuba daga aikin ƙazanta, da na fasikanci, da kuma lalata da suka sa kansu a ciki ba.
”Amma Nassi ya kulle kome a ƙarƙashin ikon zunubi, domin abin da aka yi alkawarin nan, da ake bayar ta wurin bangaskiya a cikin Yesu Kiristi, a ba da shi ga waɗanda suka gaskata.
”Saboda haka ina ce muku, ku yi rayuwa ta wurin Ruhu, ba za ku kuwa gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka ba. Gama mutuntaka yana son abin da Ruhu yake ƙi, Ruhu kuma yana son abin da mutuntaka yake ƙi. Waɗannan biyu kuwa gāba suke da juna, har ku kāsa yin abin da kuke so. Amma in Ruhu ne yake bishe ku, ba ku a ƙarƙashin Doka ke nan.
”Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata; bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya, da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.
”Waɗanda suke na Kiristi Yesu, sun gicciye mutuntaka tare da abubuwan da mutum yake marmari da kuma sha’awace-sha’awacensa. Da yake muna rayuwa ta Ruhu ne, bari mu ci gaba da al’amuranmu ta wurin Ruhu.
”’Yan’uwa, in an kama wani yana cikin yin zunubi, ku da kuke masu ruhaniya ya kamata ku komo da shi a kan hanya a hankali. Amma ku lura da kanku, domin kada maimakon dawowa da ɗan’uwanku, ku ma ku fāɗi cikin jarraba.
”Kada a ruɗe ku. Ba a yi wa Allah ba’a. Mutum yakan girbe abin da ya shuka ne. Wanda ya yi shuki don yă gamshi mutuntakarsa, daga wannan mutuntaka zai girbi hallaka. Wanda ya yi shuki domin yă gamshi Ruhu, daga Ruhu zai girbi rai madawwami.
”A cikinsa muka sami fansa ta wurin jininsa, wato, yafewar zunubanmu. Kiristi ya yi wannan saboda yawan alherin Allah
”Ku kam, a dā ku matattu ne saboda laifofinku da kuma zunubanku. Kun yi rayuwa kamar yadda sauran mutanen duniya suke yi, cike da zunubi, kuna biyayya ga sarki masu ikon sarari sama, wato, ruhun nan da yanzu yake aiki a cikin masu ƙin biyayya ga Allah. Dukanmu a dā mun yi irin rayuwan nan a cikinsu, muna bin kwaɗayi da sha’awace-sha’awacen jikunanmu da tunaninmu. Kamar sauran mutane, mun cancanci fushin Allah.
”To, ina dai faɗa muku, ina kuma nace faɗa muku a cikin Ubangiji, cewa kada ku ci gaba da yin rayuwa kamar yadda Al’ummai suke yi, masu banzan tunani. Suna a cikin duhu a fahimtarsu, kuma a rabe suke daga ran Allah saboda jahilcin da yake cikinsu ta dalilin taurarewar zukatansu. Ba sa damu da wani abu ko mai kyau ko marar kyau. Rayukansu sun cika da kowace irin ƙazanta da haɗama.
”sai ku tuɓe tsohon mutumin nan naku da kuma rayuwarku ta dā, wadda take lalacewa saboda sha’awace-sha’awacen da suke ruɗe ku. A maimakon haka, bari Ruhu yă sabunta tunaninku da kuma halayenku. Ku sanya sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah, halin nan kuwa, yă bayyana cikin adalci, da zaman tsarki.
”Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta.
”Kada a ma ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata, ko kwaɗayi a tsakaninku, domin bai dace da mutane masu tsarki na Allah ba. Haka ma bai kamata a sami datti, ƙazamar magana, ko zancen banza a cikinku ba, domin ba su dace ba, a maimakon haka sai ku yi ta yin godiya. Ku dai tabbata, ba wani mai fasikanci, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayin (wanda shi da mai bautar gumaka ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Kiristi da na Allah. Kada wani yă ruɗe ku da kalmomin wofi, gama saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake zuwa a kan marasa biyayya.
”Ku yi nesa da ayyukan duhun da mutane suke yi, a maimakon haka, ku tona su. Gama abin kunya ne a ma faɗi abubuwan da marasa biyayya suke yi a ɓoye.
”Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu.
”A dā kuna a ware da Allah, kuka kuma zama abokan gāba a cikin tunaninku saboda mugun halinku. Amma Ɗansa ya zama mutum ya kuma mutu. Saboda haka Allah ya yi sulhu da ku, yanzu kuwa ya bar ku ku tsaya a gabansa da tsarki, marasa aibi, da kuma marasa abin zargi.
”Saboda haka, sai ku fid da duk wani abin da yake kawo sha’awa a zukatanku, fasikanci, ƙazanta, sha’awa, muguwar sha’awa, da kuma kwaɗayi wanda shi ma bautar gumaka ne. Gama fushin Allah zai sauko a kan masu aikata waɗannan. Dā kun yi waɗannan abubuwa, sa’ad da rayuwar tana cikin duniya mai wannan hali. Amma yanzu dole ku raba kanku da dukan ire-iren abubuwan nan. Ku daina fushi, ku daina ƙiyayya da ƙeta. Ku bar ɓatan suna da kuma ƙazamar magana daga leɓunanku. Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun tuɓe tsohon halinku tare da ayyukansa
”Duk wanda ya yi laifi, za a sāka masa don laifinsa, babu sonkai.
”Nufin Allah ne a tsarkake ku, cewa ku guje wa fasikanci; don kowannenku yă koya yadda zai ƙame kansa a hanyar da take mai tsarki, mai mutunci kuma,
”Gama Allah bai kira mu ga zaman marasa tsarki ba, sai dai ga zaman tsarki. Saboda haka, duk wanda ya ƙi wannan umarni ba mutum ne ya ƙi ba sai ko Allah, wanda ya ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.
”amma ku gwada kome, ku riƙe abin da yake mai kyau, ku ƙi kowace mugunta. Bari Allah da kansa, Allah na salama, yă tsarkake ku sarai. Bari dukan ruhunku, ranku, da kuma jikinku su zama marar aibi a dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi.
”Zai hukunta waɗanda ba su san Allah ba da kuma waɗanda ba su yi biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu ba.
”Mun kuma san cewa an yi doka ba domin masu adalci ba sai dai masu tawaye, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai, da masu zina da kuma da maza masu kwana da maza, ko mata masu kwana da mata, da masu cinikin bayi da masu ƙarya da kuma masu shaidar ƙarya, da kuma duk wani abin da ya saɓa wa sahihiyar koyarwa,
”Ga wata magana tabbatacciya wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa. Kiristi Yesu ya zo duniya domin ceton masu zunubi, wanda nake mafi muni a cikinsu. Amma saboda wannan dalilin ne aka nuna mini jinƙai domin ta wurina, mafi zunubi duka, Kiristi Yesu yă iya bayyana matuƙar haƙurinsa a matsayin misali ga waɗanda za su gaskata shi su kuma sami rai madawwami.
”Amman waɗannan dattawa waɗanda suke yin zunubi kuwa sai ka kwaɓe su a gaban jama’a, don saura su ji tsoro.
”Zunuban waɗansu mutane a fili suke, suna shan gabansu zuwa hukunci; zunuban waɗansu kuwa sukan bi su a baya.
”Mutanen da suke son yin arziki sukan fāɗi cikin jarraba, su fāɗa a tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka. Gama son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Waɗansu mutane, don tsananin son kuɗi, sun bauɗe daga bangaskiya suka kuma jawo wa kansu da baƙin ciki iri-iri.
”Mutane za su zama masu son kansu, masu son kuɗi, masu taƙama, masu girman kai, masu zage-zage, marasa biyayya ga iyayensu, marasa godiya, marasa tsarki, marasa ƙauna, marasa gafartawa, masu ɓata sunayen waɗansu, marasa kamunkai, masu ƙeta, marasa ƙaunar nagarta, masu cin amana, marasa hankali, waɗanda sun cika da ɗaga kai, masu son jin daɗi a maimakon ƙaunar Allah suna riƙe da siffofin ibada, amma suna mūsun ikonta. Kada wani abu yă haɗa ka da su. Irin su ne suke saɗaɗawa su shiga gidaje suna rinjayar mata marasa ƙarfin hali, waɗanda zunubai suka sha kansu, mugayen sha’awace-sha’awace kuma sun ɗauke hankulansu, kullum suna koyo amma ba sa taɓa iya yarda da gaskiya.
”Mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu.
”Sun ɗauka cewa sun san Allah, amma ta wurin ayyukansu suna mūsunsa. Sun zama abin ƙyama, marasa biyayya, ba su ma isa su yi aiki nagari ba.
”A wani lokaci can baya mu ma wawaye ne, marasa biyayya, aka ruɗe mu, sha’awace-sha’awace da kwaɗayi iri-iri suka daure mu, muka yi zaman ƙiyayya da kishi, aka ƙi mu, mu kuma muka ƙi juna.
”Domin shi kansa ya sha wahala sa’ad da aka gwada shi, yana iya taimakon waɗanda ake yi wa gwaji.
”Sai dai ku ƙarfafa juna kullum, muddin akwai lokacin da ana ce da shi Yau, don kada waninku yă zama mai taurin zuciya ta wurin ruɗun zunubi.
”Kamar yadda aka faɗa cewa, “Yau, in kuka ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a tawayen nan.”
”Gama babban firist da muke da shi ba marar juyayin kāsawarmu ba ne, amma muna da wanda aka gwada ta kowace hanya, kamar dai yadda akan yi mana, duk da haka bai yi zunubi ba.
”gama ta wurin hadayan nan guda ɗaya ya kammala har abada waɗanda ake tsarkake. Ruhu Mai Tsarki ma ya yi mana shaida game da wannan. Da farko ya ce, “Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su bayan wannan lokaci, in ji Ubangiji. Zan sa dokokina a cikin zukatansu, in kuma rubuta su a kan zukatansu.” Sai ya ƙara da cewa, “Zunubansu da kurakuransu ba zan ƙara tunawa da su ba.” In an gafarta zunubai, babu sauran bukatar miƙa hadaya.
”Ba wata hadayar da za a yi don mutanen da suka yanke shawara su yi ci gaba da yin zunubi da gangan bayan sun sami sanin gaskiya. A maimakon haka za su kasance da babban fargabar hukunci da kuma ta ƙunar wuta wadda za tă cinye abokan gāban Allah. Duk wanda ya ƙi ya kiyaye dokar Musa akan kashe shi ba tausayi, a kan shaidar mutum biyu ko uku. Wane irin hukunci mai tsanani ne kuke tsammani zai dace da mutumin da ya nuna rashin bangirma ga Ɗan Allah, wanda ya yi banza da jinin nan na alkawarin da ya tsarkake shi, wanda kuma ya zargi Ruhun alheri? Gama mun san shi, wannan wanda ya ce, “Ramuwa tawa ce; zan rama,” da kuma, “Ubangiji zai yi wa mutanensa hukunci.” Abu mai matuƙar bantsoro ne a fāɗa cikin hannuwan Allah mai rai.
”Saboda haka, da yake muna kewaye da irin wannan taron shaidu mai girma, sai mu yar da duk abin da yake hana mu da kuma zunubin da yake saurin daure mu, mu kuma yi tseren da aka sa a gabanmu da nacewa.
”Cikin famanku da zunubi, ba ku yi tsayayya har ga zub da jininku ba tukuna.
”Ku yi iyakacin ƙoƙari ku yi zaman lafiya da kowa, ku kuma zama masu tsarki; gama in ban da tsarki ba babu wanda zai ga Ubangiji.
”Aure yă zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci.
”Mai albarka ne mutumin da yake daurewa cikin gwaji, gama bayan ya yi nasara da gwajin, zai sami rawanin rai wanda Allah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa. Sa’ad da aka jarrabci mutum, kada yă ce, “Allah ne yake jarrabtarsa.” Gama ba ya yiwuwa a jarrabci Allah da mugunta, shi kuma ba ya jarrabtar kowa; amma akan jarrabce kowane mutum sa’ad da muguwar sha’awarsa ta janye shi ta kuma rinjaye shi. Sa’an nan, bayan da sha’awar ta yi ciki, takan haifi zunubi; zunubi kuwa, sa’ad da ya balaga yakan haifi mutuwa. Kada a ruɗe ku, ’yan’uwana ƙaunatattu.
”Saboda haka, ku rabu da ƙazamin hali da kuma kowace irin mugunta ku kuma yi na’am da maganar da aka shuka a cikinku da tawali’u, wadda za tă iya cetonku. Kada ku zama masu ji kawai, ku ruɗi kanku. A maimakon haka ku zama masu yin abin da ta ce.
”Gama duk wanda ya kiyaye dukan doka amma ya yi tuntuɓe a kan abu ɗaya kaɗai, ya zama mai laifin karya dukansu ke nan.
”Me yake jawo faɗace-faɗace da gardandami a tsakaninku? Ashe, ba sha’awace-sha’awacenku da suke yaƙi a zukatanku ba ne? Kukan nemi abu ku rasa, sai ku yi kisa da ƙyashi. In kuka rasa abin da kuke nema sai ku shiga yin gardama da faɗa. Kukan rasa ne, domin ba ku roƙi Allah ba.
”Ku mazinata, ba ku san cewa abokantaka da duniya gāba ce da Allah ba? Duk wanda ya zaɓa yă zama abokin duniya ya zama abokin gāban Allah ke nan. Ko kuna tsammani a banza ne Nassi ya ce ruhun da ya sa yă zauna a cikinmu yana kishi sosai? Amma yakan ba mu alheri a yalwace. Shi ya sa Nassi ya ce, “Allah yana gāba da masu girman kai amma yakan ba da alheri ga masu tawali’u.” Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah. Ku yi tsayayya da Iblis, zai kuwa guje ku. Ku matso kusa da Allah shi kuwa zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ku masu zunubi, ku kuma tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu. Ku yi baƙin ciki, ku yi makoki ku kuma yi kuka. Ku mai da dariyarku ta zama makoki, farin cikinku kuma yă zama ɓacin zuciya. Ku ƙasƙantar da kanku a gaban Ubangiji, zai kuwa ɗaukaka ku.
”’Yan’uwa, kada ku ɓata wa juna suna. Duk wanda ya zargi ɗan’uwansa ko ya ɗora masa laifi, yana gāba da doka ne yana kuma yin mata shari’a ke nan. In kuwa ka ɗora wa shari’a laifi, kai ba mai binta ba ne, mai ɗora mata laifi ne. Akwai Mai ba da doka da kuma Alƙali guda ɗaya tak, shi ne yake da ikon ceto da kuma hallakarwa. Amma kai, wane ne da za ka hukunta maƙwabcinka?
”Saboda haka, duk wanda ya san abu mai kyan da ya kamata yă yi, bai kuwa yi ba, ya yi zunubi ke nan.
”sai yă tuna da wannan. Duk wanda ya komo da mai zunubi daga kaucewarsa, zai cece shi daga mutuwa, yă kuma rufe zunubai masu ɗumbun yawa.
”Kamar ’ya’ya masu biyayya, kada ku bi mugayen sha’awace-sha’awacen da dā kuke da su sa’ad da kuke rayuwa a cikin jahilci. Amma kamar yadda wanda ya kira ku yake mai tsarki, haka ku ma sai ku kasance masu tsarki cikin dukan abubuwan da kuke yi; gama a rubuce yake cewa, “Ku zama masu tsarki, domin ni mai tsarki ne.”
”Saboda haka, ku rabu da kowace ƙeta da dukan ruɗu, munafunci, kishi, da kuma kowace irin ɓata suna.
”Abokaina ƙaunatattu, ina roƙonku, a matsayin bare da kuma baƙi a duniya, ku rabu da sha’awace-sha’awacen zunubin da suke yaƙi da ranku.
”Shi kansa ya ɗauki zunubanmu a jikinsa a kan itace, domin mu mutu ga zunubai mu kuma rayu ga adalci; ta wurin raunukansa ne kuka sami warkarwa. Gama dā kuna kama da tumakin da suka ɓace, amma yanzu kun dawo ga Makiyayi da kuma Mai lura da rayukanku.
”Gama Kiristi ya mutu domin zunubi sau ɗaya tak, mai adalci saboda marasa adalci, don yă kawo ku ga Allah. An kashe shi a cikin jiki, amma an rayar da shi a Ruhu,
”Saboda haka, da yake Kiristi ya sha wahala a jikinsa, sai ku ma ku yi wa kanku ɗamara da irin wannan hali, gama wanda ya sha wahala a jikinsa ya gama da zunubi ke nan. Ta haka, ba ya sauran rayuwarsa a kan mugayen sha’awace-sha’awacen jiki, sai dai nufin Allah. Gama kun ɓata lokaci sosai a dā kuna yin abubuwan da masu bauta gumaka suka zaɓa su yi, kuna rayuwa cikin lalata, sha’awace-sha’awace, buguwa, shashanci, shaye-shaye da kuma bautar gumaka masu banƙyama.
”Cikin kwaɗayinsu waɗannan malaman ƙarya za su cuce ku da tatsuniyoyin da suka ƙaga. Hukuncinsu yana a rataye a kansu tun da daɗewa, hallakarsu kuma ba ta barci. Gama in har Allah bai ƙyale mala’iku sa’ad da suka yi zunubi ba, amma ya tura su cikin lahira, domin a tsare su don hukunci;
”in haka ne, to, Ubangiji ya san yadda zai ceci mutane masu tsoron Allah daga gwaje-gwaje, yă kuma tsare marasa adalci don ranar hukunci, har yă zuwa ranar shari’a. Wannan gaskiya ce musamman ga waɗanda suke bin sha’awace-sha’awacen lalaci na mutuntaka, suna kuma rena masu mulki. Da ƙarfin hali da kuma girman kai, waɗannan mutane ba sa tsoro kawo zargin ɓata sunan talikan sama;
”Idanunsu sun cike da zina, ba sa ƙoshi da yin zunubi; suna jarrabtar waɗanda ba tsayayyu ba; gwanaye ne a kan kwaɗayi, la’anannun iri!
”A kansu karin maganan nan gaskiya ce, “Kare ya koma kan amansa,” da kuma, “Alade da aka yi wa wanka, ya koma birgimarsa cikin laka.”
”Da farko dai, dole ku fahimci wannan cewa a kwanakin ƙarshe masu ba’a za su zo suna ba’a, suna bin mugayen sha’awace-sha’awacensu.
”In muka ce muna zumunci da shi amma muna tafiya cikin duhu, ƙarya muke yi, kuma ba ma rayuwa bisa ga gaskiya. Amma in muna tafiya cikin haske, yadda yake cikin haske, muna da zumunci da juna ke nan, kuma jinin Yesu, Ɗansa, yana tsarkake mu daga dukan zunubi. In muka ce ba mu da zunubi, muna ruɗin kanmu ne, gaskiya kuwa ba ta cikinmu. In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci. In muka ce ba mu yi zunubi ba, mun mai da shi maƙaryaci ke nan, maganarsa kuwa ba ta da wuri a cikinmu.
”’Ya’yana ƙaunatattu, ina rubuta muku wannan ne don kada ku yi zunubi. Amma in wani ya yi zunubi, muna da wani wanda yake magana da Uba don taimakonmu, wato, Yesu Kiristi, Mai Adalci. Shi ne hadayar kafara saboda zunubanmu, kuma ba don namu kaɗai ba amma har ma da zunuban duniya duka. Ta haka za mu tabbata cewa mun san shi in muna yin biyayya da umarnansa. Mutumin da ya ce, “Na san shi,” amma ba ya yin abin da ya umarta, maƙaryaci ne, gaskiya kuwa ba ta cikinsa. Amma in wani ya yi biyayya da maganarsa, ƙaunar Allah ta zama cikakkiya ke nan a cikinsa. Ta haka muka san cewa muna cikinsa. Duk wanda ya ce yana rayuwa a cikinsa dole yă yi tafiya kamar yadda Yesu ya yi.
”Amma duk wanda yake ƙin ɗan’uwansa, cikin duhu yake, yana kuma tafiya cikin duhu ke nan; bai ma san inda za shi ba, domin duhun ya makanta shi.
”Ina rubuta muku, ’ya’yana ƙaunatattu, domin an gafarta muku zunubanku saboda sunansa.
”Kada ku ƙaunaci duniya, ko wani abin da yake cikinta. In wani yana ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa. Gama duk abin da yake na duniya, kamar sha’awace-sha’awacen mutuntaka, sha’awar idanunsa, da kuma taƙama da abin da yake da shi, yake kuma yi, ba daga wurin Uba suke fitowa ba sai dai daga duniya. Duniya da sha’awace-sha’awacenta suna shuɗewa, amma mutumin da yake aikata nufin Allah, zai rayu har abada.
”Duk mai yin zunubi yana karya doka ne; tabbatacce, zunubi, karya doka ne. Sai dai kun san cewa Kiristi ya bayyana ne domin yă ɗauke zunubanmu. A cikinsa kuwa babu zunubi. Ba mai rayuwa a cikinsa da yake cin gaba da yin zunubi. Kowa da yake aikata zunubi, bai taɓa ganinsa ba, bai ma san shi ba. ’Ya’yana ƙaunatattu, kada ku yarda wani yă ruɗe ku. Duk mai yin abin da yake daidai mai adalci ne, yadda Kiristi yake mai adalci. Duk mai aikata abin da yake zunubi shi na Iblis ne, domin Iblis mai aikata zunubi ne tun farko. Dalilin da ya sa Ɗan Allah ya bayyana kuwa shi ne don yă rushe aikin Iblis. Babu haifaffe na Allah da zai ci gaba da yin zunubi, domin iri na Allah yana a cikinsa; ba zai iya ci gaba da yin zunubi ba, domin haifaffe ne na Allah. Ta haka muka san waɗanda suke ’ya’yan Allah da kuma waɗanda suke ’ya’yan Iblis. Duk wanda ba ya yin abin da yake daidai, ba ɗan Allah ba ne; haka ma wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa.
”Duk mai ƙin ɗan’uwansa mai kisankai ne, kun kuma san cewa ba mai kisankan da yake da rai madawwami a cikinsa.
”In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa?
”Wannan ita ce ƙauna, wato, ba mu ne muka ƙaunaci Allah ba, sai dai shi ne ya ƙaunace mu, ya kuma aiko Ɗansa yă zama hadaya ta kafara saboda zunubanmu.
”Kowa ya ga ɗan’uwansa yana yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba, sai yă yi masa addu’a. Ta dalilin mai addu’an nan kuwa, Allah zai ba da rai ga mai yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba. Akwai zunubin da yakan kai ga mutuwa. Ban ce a yi addu’a domin wannan ba. Duk rashin adalci, zunubi ne, amma akwai waɗansu zunuban da ba sa kai ga mutuwa. Mun san cewa kowane haifaffe na Allah ba ya cin gaba da yin zunubi; kasancewarsa haifaffe na Allah ita takan kāre shi, mugun kuwa ba zai iya cuce shi ba.
”Duk mutumin da bai tsaya a kan koyarwar Kiristi ba, amma ya yi ƙari a kanta, mutumin nan ba shi da Allah. Amma wanda ya tsaya a kan koyarwar Kiristi, yana da Uban da kuma Ɗan. Duk wanda ya zo wurinku bai kuma kawo koyarwan nan ba, kada ku karɓe shi a gidanku ko ku marabce shi. Duk wanda ya karɓe shi yana tarayya da mugun aikinsa ke nan.
”don yă yi wa kowa shari’a, yă kuma hukunta duk marasa tsoron Allah game da dukan ayyukansu na rashin tsoron Allah da suka aikata ta hanyar rashin tsoron Allah, da kuma dukan baƙaƙen kalmomin da masu zunubi marasa tsoron Allah suka faɗa game da shi.”
”Waɗannan mutane dai, gunaguni gare su, kullum ganin laifin waɗansu suke yi. Muguwar sha’awa ce kaɗai tunaninsu. Sun cika da banzar magana ta yabon kansu. Suna ruɗin mutane da zaƙin baki don samun ribar kansu.
”‹Saboda haka ka tuba! In ba haka ba, zan zo wajenka ba da daɗewa ba in yaƙe su da takobin bakina.›
”‹Na ba ta lokaci tă tuba daga fasikancinta, amma ba ta da niyya.›
”‹Na san ayyukanka, ba ka da sanyi ba ka kuma da zafi. Na so da kai ɗaya ne daga ciki, ko sanyi, ko zafi!› ‹Amma domin kana tsaka-tsaka ba zafi ba, ba kuma sanyi ba, ina dab da tofar da kai daga bakina.›
”Ba su kuma tuba daga kisankansu, sihirinsu, fasikancinsu ko kuma daga sace-sacensu ba.
”Sai na ji wata murya daga sama ta ce, “Ku fita daga cikinta, mutanena, don kada zunubanta su shafe ku, don kada wata annobarta ta same ku; gama zunubanta sun yi tsororuwa sun kai sama. Allah kuma ya tuna da laifofinta.
”Sa’an nan na ga babban farin kursiyi da kuma wannan da yake zama a kansa. Duniya da sararin sama kuwa suka ɓace daga gabansa, babu wuri kuwa dominsu. Sai na ga matattu, babba da yaro tsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne littafin rai. Aka yi wa matattu shari’a bisa ga abin da suka aikata yadda yake a rubuce a cikin littattafai.
”Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.”
”Babu wani abu marar tsarkin da zai taɓa shiga cikin birnin, babu kuma wani mai aikata abin kunya ko ruɗi da zai shiga, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a cikin littafin rai na Ɗan Ragon.
”Duk mai yin laifi yă ci gaba da yin laifi; duk mai aikata ƙazanta yă ci gaba da aikata ƙazanta. Duk mai aikata abin da yake daidai, yă ci gaba da aikata abin da yake daidai. Kuma duk wanda yake mai tsarki, yă ci gaba da yin abin da yake da tsarki.”
”‹Waɗanda suke waje kuwa karnuka ne, masu sihiri, masu fasikanci, masu kisankai, masu bautar gumaka, da duk wanda yake ƙaunar ƙarya yake kuma aikata ta.›
”