08 – Yesu
Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Yesu.
Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Yesu.
Ta wurinsa aka halicci dukan abu, abubuwan da suke cikin sama da abubuwan da suke a duniya, waɗanda ake gani, da waɗanda ba a gani, ko kursiyoyi ko ikoki ko masu mulki ko hukumomi; an halicci dukan abu ta wurinsa da kuma dominsa ne. Ya kasance kafin dukan abu, kuma a cikinsa ne dukan abubuwa suke a harhaɗe.
”Za tă haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, gama shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.” Duk wannan ya faru ne, don a cika abin da Ubangiji ya faɗi ta bakin annabin cewa, “Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, kuma za a kira shi Immanuwel” (wanda yake nufin “Allah tare da mu”).
”Sai na duba na kuma ji muryar mala’iku masu yawa, yawansu kuwa ya kai dubu dubbai, da kuma dubu goma sau dubu goma. Suka kewaye kursiyin da halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan. Da babbar murya suka rera, “Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka kashe, don yă sami iko da wadata da hikima da ƙarfi da girma da ɗaukaka da kuma yabo!” Sa’an nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa, “Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon yabo da girma da ɗaukaka da iko, sun tabbata har abada abadin!” Sai halittu huɗun nan masu rai suka ce, “Amin”, dattawan kuma suka fāɗi suka yi sujada.
”Zan kuma sa ƙiyayya tsakaninka da macen, tsakanin zuriyarka da zuriyarta. Zai ragargaje kanka, kai kuma za ka sari ɗiɗɗigensa.”
”sai Ishaku ya yi tambaya, ya ce wa mahaifinsa Ibrahim, “Baba?” Ibrahim ya ce masa, “Na’am ɗana!” Ishaku ya ce, “Ga dai wuta, ga kuma itace, amma ina ɗan ragon hadaya ta ƙonawa?” Ibrahim ya amsa ya ce, “Ɗana, Allah kansa zai tanada ɗan ragon hadayar ƙonawa.” Sai su biyu suka ci gaba da tafiya.
”Allah ya ce wa Musa, “NI NE wanda NINE. Abin da za ka faɗa wa Isra’ilawa ke nan cewa, ‘NI NE, ya aiko ni wurinku.’ ”
”“In mutum ya yi zunubi, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, ko da yake bai sani ba, shi mai laifi ne. Za a kuwa nemi hakki daga gare shi. Zai kawo wa firist rago daga garke, marar lahani. Za a kimanta tamanin rago daidai da tamanin hadaya don laifi. Firist kuwa zai yi kafara don kuskuren da mutumin ya yi ba da saninsa ba, za a gafarta masa.
”Na san wanda zai fanshe ni yana nan da rai, kuma a ƙarshe zai tsaya a kan duniya.
”Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni? Me ya sa ka yi nisa da cetona, ka yi nesa daga kalmomin nishina?
”An zubar da ni kamar ruwa, kuma dukan ƙasusuwana sun fiffito daga mahaɗai. Zuciyata ta zama kaki; ta narke a cikina. Ƙarfina ya bushe kamar kasko, harshena kuma ya manne wa dasashina na sama; ka kwantar da ni a ƙurar mutuwa. Karnuka sun kewaye ni; ƙungiyar mugaye sun sa ni a tsaka, sun soki hannuwana da ƙafafuna. Zan iya ƙirga ƙasusuwana; mutane suna farin ciki a kaina. Sun raba rigunana a tsakaninsu suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigunana.
”Cikin hannuwanka na miƙa ruhuna; ka cece ni, ya Ubangiji Allah na gaskiya.
”yakan tsare dukan ƙasusuwansa, ba ko ɗayansu da zai karye.
”Har abokina na kurkusa, wanda na amince da shi, wanda muke cin abinci tare, ya juya yana gāba da ni.
”Bari sunansa yă dawwama har abada; bari yă ci gaba muddin rana tana nan. Dukan al’ummai za su sami albarka ta wurinsa, za su kuma ce da shi mai albarka.
”Zan kuma naɗa shi ɗan farina, mafi ɗaukaka cikin sarakunan duniya.
”Zabura Dutsen da magina suka ƙi ya zama mai amfani;
”Wane ne ya taɓa haura zuwa sama ya dawo? Wane ne ya tattara iska a tafin hannuwansa? Wane ne ya nannaɗe ruwaye a cikin rigarsa? Wane ne ya kafa dukan iyakokin duniya? Mene ne sunansa, da kuma sunan ɗansa? Faɗa mini in ka sani!
”A shekarar da Sarki Uzziya ya mutu, na ga Ubangiji zaune a kan kujerar sarauta a sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika haikali. A bisansa akwai serafofi, kowanne yana da fikafikai shida. Fikafikai biyu sun rufe fuskokinsu, da biyu suka rufe ƙafafunsu, biyu kuma da su suke tashi. Suna kiran juna, “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Maɗaukaki ne; duniya ta cika da ɗaukakarsa.”
”Saboda haka Ubangiji kansa zai ba ku alama. Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, za tă kuwa kira shi Immanuwel. In ya yi girma har ya isa yanke shawara don kansa, madara da zuma ne abincinsa. Amma kafin yaron yă isa yanke shawara yă ƙi abin da yake mummuna, yă zaɓi abin da yake nagari, ƙasashen sarakunan nan biyu da kuke tsoro za su zama kango.
”Mutanen da suke tafiya cikin duhu sun ga babban haske; a kan waɗanda suke zama a ƙasar inuwar mutuwa haske ya haskaka.
”Gama a gare mu an haifa mana yaro, a gare mu an ba da ɗa, gwamnati za tă kasance a kafaɗarsa. Za a ce da shi Mashawarci Mai Banmamaki, Allah Maɗaukaki Uban Madawwami, Sarkin Salama. Game da girmar gwamnatinsa da salama babu iyaka. Zai gāji sarki Dawuda, yă yi mulki a matsayinsa, zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Maɗaukaki ne ya yi niyyar aikata wannan duka.
”Toho zai fito daga kututturen Yesse; daga saiwarsa Reshe zai ba da ’ya’ya. Ruhun Ubangiji zai kasance a kansa, Ruhun hikima da na fahimta, Ruhun shawara da na iko, Ruhun sani da na tsoron Ubangiji,
”Ba za su yi lahani ko su hallaka wani a dutsena mai tsarki ba, gama duniya za tă cika da sanin Ubangiji kamar yadda ruwaye suka rufe teku. A wannan rana Saiwar Yesse zai miƙe kamar tuta don mutanenta; al’ummai za su tattaru wurinsa, wurin hutunsa kuma zai zama mai daraja.
”Sa’an nan idanun makafi za su buɗe kunnuwan kurame kuma su ji. Sa’an nan guragu za su yi tsalle kamar barewa, bebaye kuma su yi sowa don farin ciki. Ruwa zai kwararo daga jeji rafuffuka kuma a cikin hamada.
”“Ga bawana, wanda na ɗaukaka, zaɓaɓɓen nan nawa wanda nake jin daɗi; Zan sa Ruhuna a cikinsa zai kuwa kawo adalci ga al’ummai.
”“Ga abin da Ubangiji yana cewa, Sarki da kuma Mai Fansar Isra’ila, Ubangiji Maɗaukaki. Ni ne farko ni ne kuma ƙarshe; in ban da ni babu wani Allah.
”Na ba da bayana ga masu dūkana, kumatuna ga masu jan gemuna; ban ɓoye fuskata daga masu ba’a da masu tofa mini miyau ba.
”Duba, bawana zai aikata abubuwa da hikima; za a tā da shi a kuma ɗaga shi da ɗaukaka ƙwarai. Kamar dai yadda aka kasance da mutane masu yawa waɗanda suka giggice sa’ad da suka gan shi, kamanninsa ya lalace ƙwarai fiye da na kowane mutum siffarsa kuma ta yi muni fiye da yadda ta mutum take, haka zai ba al’ummai masu yawa mamaki, sarakuna kuma za su riƙe bakunansu don mamaki. Gama abin da ba a faɗa musu ba, shi za su gani, kuma abin da ba su ji ba, shi za su fahimta.
”Wa ya gaskata saƙonmu kuma ga wa hannun Ubangiji ya bayyana? Ya yi girma kamar dashe marar ƙarfi, kamar saiwa kuma daga ƙeƙasasshiyar ƙasa. Ba shi da kyan gani ko wani makamin da zai ja hankalinmu, babu wani abin da yake da shi da zai sa mu yi sha’awarsa. Mutane suka rena shi suka ƙi shi, mutum ne cike da baƙin ciki, ya kuma saba da wahala. Kamar wanda mutane suna ɓuya fuskokinsu daga gare shi aka rena shi aka yi banza da shi. Tabbatacce ya ɗauki cututtukanmu ya kuma daure da baƙin cikinmu duk da haka muka ɗauka Allah ya hukunta shi ne, ya buge shi ya kuma sa ya sha azaba. Amma aka yi masa rauni saboda laifofinmu, aka ƙuje shi saboda kurakuranmu; hukuncin da ya kawo mana salama ya kasance a kansa, kuma ta wurin mikinsa ya sa muka warke. Dukanmu, muna kama da tumakin da suka ɓata, kowannenmu ya kama hanyarsa; Ubangiji kuwa ya sa hukunci ya auko a kansa hukuncin da ya wajaba a kanmu. Aka wulaƙanta shi aka kuma yi masa azaba, duk da haka bai buɗe bakinsa ba; aka kai shi kamar ɗan rago zuwa wurin yanka, kuma kamar tunkiya a gaban masu askinta tana shiru, haka bai buɗe bakinsa ba. Da wulaƙanci da kuma hukunci aka ɗauke shi aka tafi. Wa kuwa zai yi maganar zuriyarsa? Gama an kawar da shi daga ƙasar masu rai; saboda laifin mutanena aka kashe shi. Aka yi jana’izarsa tare da mugaye, aka binne shi tare da masu arziki, ko da yake bai taɓa yin wani tashin hankali ba, ko a sami ƙarya a bakinsa. Duk da haka nufin Ubangiji ne a ƙuje shi yă kuma sa yă sha wahala, kuma ko da yake Ubangiji ya sa ransa ya zama hadaya don zunubi, zai ga zuriyarsa zai kuma kawo masa tsawon rai, nufin Ubangiji kuma zai yi nasara a hannunsa. Bayan wahalar ransa, zai ga hasken rai, ya kuma gamsu; ta wurin saninsa bawana mai adalci zai ’yantar da mutane masu yawa, zai kuma ɗauki laifofinsu. Saboda haka zan ba shi rabo tare da manya, zai kuma raba ganima tare da masu ƙarfi, domin ya ba da ransa har mutuwa, aka kuma lissafta shi tare da masu laifofi. Gama ya ɗauki zunubin mutane masu yawa, ya kuma yi roƙo saboda laifofinsu.
”Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina, domin Ubangiji ya shafe ni domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta. Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci, don in yi shelar ’yanci don ɗaurarru in kuma kunce ’yan kurkuku daga duhu don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji da kuma ranar ɗaukan fansar Allahnmu, don in ta’azantar da dukan waɗanda suke makoki, in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona, in maido musu rawani mai kyau a maimako na toka, man murna a maimako na makoki, da kuma rigar yabo a maimako na ruhun fid da zuciya. Za a ce da su itatuwan oak na adalci, shukin Ubangiji don bayyana darajarsa.
”“Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan tā da wa Dawuda Reshen adalci, Sarki wanda zai yi mulki da hikima ya kuma yi abin da yake gaskiya da kuma daidai a ƙasar.
”“Lokaci yana zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan yi sabon alkawari da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda. Ba zai zama kamar alkawarin da na yi da kakanni kakanninsu ba sa’ad da na kama su da hannu na bishe su daga Masar, domin sun take alkawarina, ko da yake na zama miji a gare su,” in ji Ubangiji. “Ga alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila bayan wannan lokaci,” in ji Ubangiji. “Zan sa dokata a tunaninsu in kuma rubuta ta a zukatansu. Zan zama Allahnsu, za su kuma zama mutanena. Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabci ba, ko ya koya wa ɗan’uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji,’ domin duk za su san ni, daga ƙaraminsu har zuwa babba,” in ji Ubangiji. “Gama zan gafarta muguntarsu ba zan kuwa ƙara tuna da zunubansu ba.”
”“A lokacin mulkin waɗannan sarakunan, Allah na sama zai kafa mulki da ba zai taɓa rushewa ba, ba kuma za a ba ma waɗansu mutane ba. Zai ragargaje waɗannan mulkokin da kuma kawo su ga ƙarshe, amma shi wannan mulki zai dawwama har abada.
”Sai Sarki Nebukadnezzar ya miƙe tsaye, cike da mamaki ya tambayi mashawartansa, “Shin ba mutum uku ba ne muka daure muka jefa cikin wutar?” Suka amsa, “Tabbatacce haka yake ya sarki.” Sai ya ce, “Ku duba ina ganin mutum huɗu suna tafiya suna yawo a cikin wutar, a sake kuma babu abin da ya same su, na huɗun sai ka ce ɗan alloli.”
”“Ina cikin dubawa, “sai aka ajiye kursiyoyi, sai ga wani wanda yake tun fil azal ya zauna a mazauninsa. Rigarsa ta yi fari fat kamar ƙanƙara; gashin kansa sun yi fari kamar ulu. Kursiyinsa kuma harshen wuta, dukan ƙafafun kursiyin masu kama da keken yaƙin, wuta ne. Kogin wuta yana gudu, yana fitowa daga gabansa. Dubun dubbai sun yi masa hidima; dubu goma sau dubu goma sun tsaya a gabansa. Aka zauna don shari’a, aka kuma buɗe littattafai.
”“A wahayina na dare, na ga a gabana wani kamar ɗan mutum yana saukowa tare da gizagizan sama. Ya kusaci Wannan wanda yake Tun fil azal aka kuma kai shi gabansa. Aka ba shi mulki, daraja da kuma mafificin iko; dukan mutane, da al’ummai, da mutane daga kowane harshe suka yi masa sujada. Mulkinsa kuwa dawwammamen mulki ne da ba zai ƙare ba, sarautarsa kuma ba ta taɓa lalacewa.
”“Sai ka sani ka kuma fahimci wannan; Tun daga sa’ad da aka kafa doka don a maido a kuma sāke gina Urushalima har sai Shafaffen nan, mai mulki, ya zo, za a yi shekara arba’in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da mafaka. Bayan shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu, za a datse Shafaffen nan zai kuma kasance ba shi da kome. Mutanen mai mulkin za su zo su hallaka birnin da kuma wuri mai tsarki. Ƙarshen zai zo kamar rigyawa. Yaƙi zai ci gaba har ƙarshe, a kuma hallakar kamar yadda aka ƙaddara.
”“Amma ke, Betlehem ta Efrata, ko da yake ke ƙarama ce daga cikin zuriyarki a Yahuda, daga cikinki wani zai zo domina wanda zai yi mulkin Isra’ila, wanda asalinsa tun fil azal ne.”
”Zai tsaya yă yi kiwon garkensa da ƙarfin Ubangiji, cikin girman sunan Ubangiji Allahnsa. Za su kuma zauna lafiya, gama girmansa za tă kai har ƙarshen duniya.
”‘Ɗaukakar gidan nan na yanzu za tă fi ɗaukakar gidan nan na dā,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. ‘A wannan wuri kuma zan ba da salama,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.”
”Ki yi murna ƙwarai, ya Diyar Urushalima! Ki yi sowa, Diyar Urushalima! Duba, ga sarkinki yana zuwa wurinki, mai adalci yana kuma da ceto, mai tawali’u yana kuma hawan jaki, yana a kan ɗan aholaki, a kan ’yar jaka.
”Sai Ubangiji ya ce mini, “Jefar da shi cikin ma’aji,” Lada mai kyau da aka yi cinikina ne! Saboda haka sai na ɗauki azurfa talatin ɗin na jefa su cikin gidan Ubangiji don a sa cikin ma’aji.
”“Zan kuma zubo wa gidan Dawuda da mazaunan Urushalima ruhun alheri da na addu’a. Za su dube ni, wannan da suka soke shi, za su kuma yi makoki dominsa kamar yadda mutum yakan yi makokin mutuwar ɗansa tilo, su kuma yi baƙin ciki ƙwarai kamar yadda mutum yakan yi baƙin ciki don ɗan fari.
”In wani ya tambaye shi, ‘Waɗanne miyaku ne haka a jikinka?’ Zai amsa yă ce, ‘Miyakun da aka yi mini a gidan abokaina ne.’ “Tashi, ya takobi, gāba da makiyayina, mutumin da yake kusa da ni sosai!” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Kashe makiyayin, sai tumakin su watse, in kuma tayar wa ƙananan.
”Tarihin da aka rubuta game da asalin Yesu Kiristi ɗan Dawuda, ɗan Ibrahim.
”Yaƙub ya haifi Yusuf, mijin Maryamu, wadda ta haifi Yesu, wanda ake kira Kiristi.
”Ta haka akwai zuriya goma sha huɗu ke nan duka-duka daga lokacin Ibrahim zuwa lokacin Dawuda, goma sha huɗu kuma daga Dawuda zuwa bauta a Babilon, goma sha huɗu kuma daga bauta a Babilon zuwa Kiristi.
”Ga yadda haihuwar Yesu Kiristi ta kasance. An yi alkawarin auren mahaifiyarsa Maryamu, ga Yusuf. Amma tun kafin su zama miji da mata, sai aka tarar Maryamu tana da ciki, ta wurin Ruhu Mai Tsarki.
”Za tă haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, gama shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.” Duk wannan ya faru ne, don a cika abin da Ubangiji ya faɗi ta bakin annabin cewa, “Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, kuma za a kira shi Immanuwel” (wanda yake nufin “Allah tare da mu”).
”Amma bai kwana da ita ba, sai bayan da ta haifi ɗan. Ya kuwa sa masa suna Yesu.
”Bayan an haifi Yesu a Betlehem, a Yahudiya, a zamanin Sarki Hiridus, sai waɗansu Masana, daga gabas suka zo Urushalima suka yi tambaya suka ce, “Ina shi wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Gama mun ga tauraronsa a gabas mun kuwa zo ne domin mu yi masa sujada.” Da Sarki Hiridus ya ji wannan, sai hankalinsa ya tashi haka ma na dukan Urushalima. Bayan ya kira dukan manyan firistoci da malaman dokoki na mutane wuri ɗaya, sai ya tambaye su inda za a haifi Kiristi. Suka amsa suka ce, “A Betlehem ne, cikin Yahudiya, gama haka annabin ya rubuta. “ ‘Amma ke Betlehem, a cikin ƙasar Yahuda, ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin masu mulki a Yahuda ba, gama daga cikinki mai mulki zai zo, wanda zai zama makiyayin mutanena Isra’ila.’”
”Suka shiga gidan, suka kuwa ga yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka durƙusa har ƙasa, suka yi masa sujada. Sa’an nan suka kunce dukiyarsu, suka miƙa masa kyautai na zinariya da na turare da na mur.
”“Ina muku baftisma da ruwa domin tuba. Amma wani yana zuwa a bayana wanda ya fi ni iko, wanda ko takalmansa ma ban isa in ɗauka ba. Zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da kuma wuta. Yana riƙe da matankaɗinsa, zai tankaɗe hatsinsa, yă kuma tattara alkamarsa a cikin rumbu, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.”
”Sai Yesu ya zo daga Galili, ya je Urdun don Yohanna yă yi masa baftisma. Amma Yohanna ya so yă hana shi, yana cewa, “Ina bukata ka yi mini baftisma, yaya kake zuwa wurina?” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Bari yă zama haka yanzu; ya dace mu yi haka don mu cika dukan adalci.”› Sa’an nan Yohanna ya yarda. Nan da nan da aka yi wa Yesu baftisma, sai ya fito daga ruwa. A wannan lokaci sama ya buɗe, sai ya ga Ruhun Allah yana saukowa kamar kurciya ya kuwa sauka a kansa. Sai murya daga sama ta ce, “Wannan shi ne Ɗana wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai.”
”Sa’an nan Ruhu ya kai Yesu cikin hamada don Iblis yă gwada shi. Bayan ya yi azumi yini arba’in da kuma dare arba’in, sai ya ji yunwa.
”Tun daga wannan lokaci, Yesu ya fara wa’azi yana cewa, ‹“Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”›
”Yesu ya zazzaga dukan Galili, yana koyarwa a cikin majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin sama, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiyar mutane. Labarinsa ya bazu ko’ina a Suriya, mutane kuwa suka kawo masa dukan waɗanda suke fama da cututtuka iri-iri, da waɗanda suke da zafin ciwo, da masu aljanu, da waɗanda suke masu farfaɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su. Taron mutane mai yawa daga Galili, Dekafolis, Urushalima, Yahudiya da kuma yankin hayin Urdun suka bi shi.
”‹“Kada ku yi tsammani na zo ne domin in kawar da Doka ko kuma Annabawa; ban zo domin in kawar da su ba ne, sai dai domin in ciccika su.›
”‹“Saboda haka, ina gaya muku, kada ku damu game da rayuwarku, game da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha; ko kuma game da jikinku, game da abin da za ku sa. Ashe, rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba?›
”‹“Ba duk mai ce mini, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ne zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda yake aikata nufin Ubana da yake sama.›
”Sai Yesu ya amsa ya ce, ‹“Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.”›
”Mutanen suka yi mamaki suka ce, “Wane irin mutum ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa suna masa biyayya!”
”Sane da tunaninsu, Yesu ya ce, ‹“Me ya sa kuke da mugun tunani a zuciyarku?›
”‹Amma don ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.”› Sai ya ce wa shanyayyen, ‹“Tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.”›
”Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.
”Sai ya kira almajiransa goma sha biyu wurinsa ya kuma ba su iko su fitar aljanu, su kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.
”‹Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya jure har ƙarshe zai sami ceto.›
”‹“Duk wanda ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin sama.› ‹Amma duk wanda ya yi mūsun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi mūsun saninsa a gaban Ubana da yake cikin sama.›
”‹“Kada fa ku ɗauka na zo ne don in kawo salama a duniya. A’a, ban zo don in kawo salama ba, sai dai takobi.› ‹Gama na zo ne in sa,› ‹“ ‘gāba tsakanin mutum da mahaifinsa,› ‹’ya da mahaifiyarta,› ‹matar ɗa da surukarta,›
”‹“Duk wanda ya fi ƙaunar mahaifinsa ko mahaifiyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba; duk kuwa wanda yake ƙaunar ɗansa ko diyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba;› ‹duk wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai dace yă zama nawa ba.›
”‹Ɗan Mutum ya zo yana ciye-ciye, yana shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama da kuma mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ Amma akan tabbatar da hikima ta wurin ayyukanta.”›
”‹“Dukan kome Ubana ya danƙa mini. Ba wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban, sai dai Ɗan da kuma waɗanda Ɗan ya so yă bayyana musu shi.›
”‹“Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu.› ‹Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku.› ‹Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”›
”‹Gama Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabbaci.”›
”Cikin sunansa al’ummai za su dogara.”
”Sai aka kawo masa wani bebe kuma makaho mai aljani, Yesu kuwa ya warkar da shi, har ya iya magana ya kuma sami ganin gari. Dukan mutane suka yi mamaki, suka ce, “Wannan Ɗan Dawuda ne kuwa?”
”Yesu kuwa ya san tunaninsu sai ya ce musu, ‹“Duk mulkin da yake gāba da kansa zai lalace, kuma duk birni ko gidan da yake rabe gāba da kansa ba zai ɗore ba.›
”‹Amma in ina fitar da aljanu ta wurin Ruhun Allah ne, to, fa, mulkin Allah ya zo muku ke nan.›
”‹Gama kamar yadda Yunana ya yi yini uku da kuma dare uku a cikin wani babban kifi, haka Ɗan Mutum zai yi yini uku da kuma dare uku a cikin ƙasa.›
”‹Ai, duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda yake cikin sama, shi ne ɗan’uwana da ’yar’uwata da kuma mahaifiyata.”›
”‹Ɗan Mutum zai aiki mala’ikunsa, su kuwa cire daga mulkinsa kome da yake jawo zunubi da kuma duk masu aikata mugunta.›
”Sai ya umarci mutanen su zazzauna a kan ciyawa. Da ya ɗauki burodi biyar da kifin biyun nan ya dubi sama, ya yi godiya ya kuma kakkarya burodin. Sa’an nan ya ba wa almajiransa, almajiran kuwa suka ba wa mutane. Duk suka ci suka ƙoshi, almajiran kuwa suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu. Yawan waɗanda suka ci, sun yi wajen maza dubu biyar, ban da mata da yara.
”Wajen tsaro na huɗu na dare, sai Yesu ya nufe su, yana takawa a kan tafkin. Sa’ad da almajiran suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai tsoro ya kama su. Suka yi ihu don tsoro suka ce, “Fatalwa ce.”
”Waɗanda suke cikin jirgin ruwan kuwa suka yi masa sujada, suna cewa, “Gaskiya kai Ɗan Allah ne.”
”Da mutanen wurin suka gane da Yesu, sai suka kai labari a ko’ina a ƙauyukan da suke kewaye. Mutane suka kawo masa dukan marasa lafiyarsu suka kuwa roƙe shi yă bar marasa lafiya su taɓa ko da gefen rigarsa kawai, duk waɗanda suka taɓa shi kuwa suka warke.
”Taron mutane mai girma kuwa suka zo wurinsa, suna kawo masa guragu, makafi, shanyayyu, kurame da dai waɗansu da yawa, suka kuwa kwantar da su a gabansa; ya kuma warkar da su.
”Sa’an nan ya ɗauki burodi guda bakwai da kuma kifayen nan, da ya yi godiya, sai ya kakkarya su ya ba wa almajiran, su kuma suka ba wa mutane. Duk kuwa suka ci, suka ƙoshi. Daga baya almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna bakwai. Yawan waɗanda suka ci kuwa, maza dubu huɗu ne, ban da mata da yara.
”Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Kiristi, Ɗan Allah mai rai.”
”Sa’an nan ya gargaɗe almajiransa cewa kada su faɗa wa kowa shi ne Kiristi.
”Tun daga wannan lokaci Yesu ya fara bayyana wa almajiransa cewa dole yă tafi Urushalima yă sha wahaloli da yawa a hannun dattawa, manyan firistoci da kuma malaman dokoki, dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.
”‹Gama Ɗan Mutum zai zo cikin ɗaukakar Ubansa, tare da mala’ikunsa, sa’an nan zai ba wa kowane mutum lada gwargwadon abin da ya yi.›
”A can aka sāke kamanninsa a gabansu. Fuskarsa ta haskaka kamar rana, tufafinsa kuwa suka zama fari fat suna walƙiya.
”Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije mai haske ya rufe su, sai wata murya daga cikin girgijen ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai. Ku saurare shi!”
”Da suka taru a Galili, sai ya ce musu, ‹“Za a bashe Ɗan Mutum, a hannun mutane.› ‹Za su kashe shi, a rana ta uku kuma za a tashe shi.”› Almajiran kuwa suka cika da baƙin ciki.
”‹“Ku lura, kada ku rena ɗaya daga cikin waɗannan ƙanana. Gama ina faɗa muku mala’ikunsu a sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin sama.›
”‹Gama inda mutum biyu ko uku suka taru cikin sunana, a can ma ina tare da su.”›
”Yesu ya amsa ya ce, ‹“In kana so ka zama cikakke, ka je, ka sayar da dukan dukiyarka ka kuma ba matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo, ka bi ni.”›
”‹“Za mu haura zuwa Urushalima, za a kuma bashe Ɗan Mutum ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa› ‹za su kuma bashe shi ga Al’ummai su yi masa ba’a, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma a tashe shi!”›
”‹kamar yadda Ɗan Mutum bai zo don a bauta masa ba, sai dai don yă yi bauta, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”›
”Wani babban taron mutane suka shimfiɗa mayafansu a kan hanya, yayinda waɗansu suka sassari rassan itatuwa suka shisshimfiɗa a kan hanya. Taron mutanen da suke gabansa da kuma waɗanda suke binsa a baya suka yi ihu suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Hosanna a cikin sama!”
”Yesu ya shiga filin haikali, ya kuma kori duk masu saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur masu canjin kuɗi da kuma kujerun masu sayar da tattabarai. Ya ce musu, ‹“A rubuce yake, ‘Za a ce da gidana, gidan addu’a,’›‹amma kuna mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ”› Makafi da guragu suka zo wurinsa a haikali, ya kuwa warkar da su. Amma da manyan firistoci da malaman dokoki suka ga abubuwan banmamakin da ya yi, yara kuma suna ihu a filin haikali suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda,” sai fushi ya kama su.
”Yesu ya ce musu, ‹“Ashe, ba ku taɓa karanta a cikin Nassi cewa,› ‹“ ‘Dutsen da magina suka ƙi shi› ‹ne ya zama dutsen kusurwar gini.› ‹Ubangiji ne ya aikata wannan,› ‹kuma abin mamaki ne a idanunmu’?› ‹“Saboda haka, ina gaya muku cewa za a karɓe mulkin Allah daga gare ku, a ba wa mutanen da za su ba da amfani.› ‹Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Amma duk wanda dutsen nan ya fāɗi a kansa, za a murƙushe shi.”›
”Yayinda Farisiyawa suke a tattare wuri ɗaya, sai Yesu ya tambaye su, ‹“Me kuke tsammani game da Kiristi? Ɗan wane ne shi?”› Suka amsa suka ce, “Ɗan Dawuda.” Ya ce musu, ‹“To, ta yaya Dawuda ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ya kira shi ‘Ubangiji’? Gama ya ce,› ‹“ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,› ‹“Zauna a hannun damana,› ‹sai na sa abokan gābanka› ‹su zama matashin sawunka.” ’› ‹To, in Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji,’ yaya zai zama ɗansa?”› Ba wanda ya iya tanka masa, daga wannan rana kuwa ba wanda ya sāke yin karambanin yin masa wata tambaya.
”‹Ba kuwa za a kira ku ‘malam’ ba, gama kuna da Malami ɗaya ne, Kiristi.›
”‹“Sa’an nan za a bashe ku don a tsananta muku a kuma kashe ku, dukan al’ummai za su ƙi ku saboda ni.›
”‹Gama kamar yadda walƙiya take wulgawa walai daga gabas zuwa yamma, haka dawowar Ɗan Mutum zai kasance.›
”‹“A sa’an nan ne alamar dawowar Ɗan Mutum zai bayyana a sararin sama, dukan al’umman duniya kuwa za su yi kuka. Za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gizagizan sararin sama, da iko da kuma ɗaukaka mai girma.›
”‹Sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za tă taɓa shuɗe ba.›
”‹“Sa’ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa, tare da dukan mala’iku, zai zauna a kursiyinsa cikin ɗaukakar sama.› ‹Za a tara dukan al’ummai a gabansa, zai kuma raba mutane dabam-dabam yadda makiyayi yakan ware tumaki daga awaki.› ‹Zai sa tumaki a damansa, awaki kuma a hagunsa.› ‹“Sa’an nan Sarki zai ce wa waɗanda suke damansa, ‘Ku zo, ku da Ubana ya yi wa albarka; ku karɓi gādonku, mulkin da aka shirya muku tun halittar duniya.›
”Yayinda suke cikin cin abinci, Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ya kuma kakkarya, ya ba wa almajiransa yana cewa, ‹“Ku karɓa ku ci; wannan jikina ne.”› Sa’an nan ya ɗauki kwaf, ya yi godiya, ya kuma ba su, yana cewa, ‹“Ku shassha daga cikinsa, dukanku.› ‹Wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubai.› ‹Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabin nan ba har sai ranar da zan sha shi sabo tare da ku a mulkin Ubana.”›
”Sai ya ce musu, ‹“Raina yana cike da baƙin ciki har kamar zan mutu. Ku dakata a nan, ku kuma yi tsaro tare da ni.”›
”‹Kuna tsammani ba zan iya kira Ubana, nan take kuwa yă aiko mini fiye da rundunar mala’iku goma sha biyu ba?› ‹Amma ta yaya za a cika Nassin da ya ce dole haka yă faru?”›
”Amma Yesu ya yi shiru. Sai babban firist ya ce masa, “Na haɗa ka da Allah mai rai. Faɗa mana in kai ne Kiristi, Ɗan Allah.” Sai Yesu ya amsa ya ce, ‹“I, haka yake yadda ka faɗa. Sai dai ina gaya muku duka, nan gaba, za ku ga Ɗan Mutum zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gizagizan sama.”›
”Sai suka tottofa masa miyau a fuskarsa, suka kuma bubbuge shi da hannuwansu. Waɗansu kuma suka mammare shi suka ce, “Yi mana annabci, Kiristi. Wa ya buge ka?”
”Ana cikin haka, Yesu kuwa yana tsaye a gaban gwamna, sai gwamnan ya tambaye shi, “Kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya ce, ‹“I, haka ne, kamar yadda ka faɗa.”›
”Saboda haka da taron suka taru, sai Bilatus ya tambaye su ya ce, “Wane ne a cikinsu kuke so in sakar muku. Barabbas ko Yesu wanda ake kira Kiristi?”
”Bilatus ya yi tambaya, “To, me zan yi da Yesu wanda ake kira Kiristi?” Duka suka ce, “A gicciye shi!”
”Suka tuɓe shi, suka yafa masa wata jar riga. Suka kuma tuƙa wani rawanin ƙaya, suka sa masa a kā. Suka sa sanda a hannun damansa. Suka durƙusa a gabansa, suka yi masa ba’a, suna cewa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!” Suka tattofa masa miyau, suka karɓe sandan, suka yi ta ƙwala masa shi a kai. Bayan sun yi masa ba’a, sai suka tuɓe masa rigar, suka sa masa nasa tufafin. Sai suka tafi da shi, domin su gicciye shi.
”Bisa da kansa kuwa, an kafa rubutun zargin da aka yi masa, da ya ce, Wannan shi ne Yesu Sarkin Yahudawa.
”Haka ma, manyan firistoci da malaman dokoki da kuma dattawa, suka yi ta yin masa ba’a, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! In shi ne Sarkin Isra’ila! To, yă sauko daga kan gicciyen nan, mu kuwa mu gaskata shi. Ya dogara ga Allah. Bari Allah yă cece shi yanzu, in yana sonsa, domin ya ce, ‘Ni Ɗan Allah ne.’ ”
”Wajen sa’a ta tara, Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, ‹“Eloi, Eloi,› ‹lama sabaktani?”› (Wato, ‹“Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”›).
”Da Yesu ya sāke ɗaga murya da ƙarfi, sai ya saki ruhunsa. A daidai wannan lokaci, sai labulen haikali ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa ta jijjiga, duwatsu kuma suka farfashe. Kaburbura suka bubbuɗe, jikunan tsarkaka da yawa kuwa cikin waɗanda da suka mutu, suka tashi. Suka firfito daga kaburbura, sa’an nan bayan tashin Yesu daga matattu, suka shiga birni mai tsarki, suka bayyana ga mutane da yawa. Da jarumin nan tare da waɗanda suke tsaron Yesu, suka ga girgizar ƙasa, da kuma abin da ya faru, sai tsoro ya kama su, suka kuma ce, “Gaskiya, wannan Ɗan Allah ne!”
”Sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa. Don wani mala’ikan Ubangiji ya sauka daga sama, ya je kabarin, ya gungurar da dutsen, ya kuma zauna a kai. Kamanninsa yana kama da walƙiya, tufafinsa kuma fari fat kamar dusan ƙanƙara. Masu gadin kabarin kuma suka ji tsoro ƙwarai, suka yi rawan jiki, suka zama kamar matattu. Mala’ikan ya ce wa matan, “Kada ku ji tsoro, domin na san cewa kuna neman Yesu wanda aka gicciye ne. Ai, ba ya nan, ya tashi kamar yadda ya faɗa. Ku zo ku ga inda ya kwanta. Sai ku tafi da sauri ku gaya wa almajiransa cewa, ‘Ya tashi daga matattu, ya kuma ya sha gabanku zuwa Galili. Can za ku gan shi.’ Ga shi na faɗa muku.”
”Kwaram, sai ga Yesu ya gamu da su ya ce, ‹“Gaisuwa.”› Sai suka zo kusa da shi, suka rungumi ƙafafunsa, suka yi masa sujada. Sai Yesu ya ce musu, ‹“Kada ku ji tsoro, ku tafi ku gaya wa ’yan’uwana, su tafi Galili. A can za su gan ni.”›
”Sai Yesu ya zo wurinsu ya ce, ‹“An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa.› ‹Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikin›‹sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki,› ‹kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani.”›
”Farkon bishara game da Yesu Kiristi, Ɗan Allah.
”Ina muku baftisma da ruwa, amma shi zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.”
”A lokacin, Yesu ya zo daga Nazaret na Galili, Yohanna kuwa ya yi masa baftisma a Urdun. Da Yesu yana fitowa daga ruwan, sai ya ga sama ya buɗe, Ruhu kuma yana saukowa a kansa kamar kurciya. Sai murya ta fito daga sama ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, da kai kuma nake fari ciki ƙwarai.” Nan da nan, sai Ruhu ya kai shi cikin hamada, ya kuma kasance a hamada kwana arba’in, Shaiɗan yana gwada shi. Yana tare da namomin jeji, mala’iku kuma suka yi masa hidima.
”Suka tafi Kafarnahum. Da ranar Asabbaci ta kewayo, sai Yesu ya shiga majami’a ya fara koyarwa. Mutane suka yi mamakin koyarwarsa, domin ya koyar da su kamar wanda yake da iko, ba kamar malaman dokoki ba. Nan take, sai wani mutum mai mugun ruhu a majami’arsu, ya ɗaga murya ya ce, “Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki nan na Allah!” Yesu ya tsawata masa ya ce, ‹“Yi shiru! Fita daga cikinsa!”› Sai mugun ruhun ya jijjiga mutumin da ƙarfi, ya fita daga jikinsa da ihu. Dukan mutane suka yi mamaki, suna tambayar juna suna cewa, “Mene ne haka? Tabɗi! Yau ga sabuwar koyarwa kuma da iko! Yana ma ba wa mugayen ruhohi umarni, suna kuma yin masa biyayya.” Labari game da shi ya bazu nan da nan ko’ina a dukan yankin Galili.
”Yesu kuwa ya warkar da marasa lafiya da yawa da suke da cututtuka iri-iri. Ya kuma fitar da aljanu da yawa, amma bai yarda aljanun suka yi magana ba, don sun san wane ne shi.
”A maimakon haka, sai ya fita, ya fara magana a sake, yana baza labarin. Saboda haka, Yesu bai ƙara iya shiga cikin gari a fili ba, sai dai ya kasance a wuraren da ba kowa. Duk da haka, mutane suka yi ta zuwa wurinsa daga ko’ina.
”Duk inda ya shiga, cikin ƙauyuka, birane ko karkara, sai su kwantar da marasa lafiya a bakin kasuwa. Suka roƙe shi yă bari su taɓa gefen rigarsa kawai, kuma duk waɗanda suka taɓa shi kuwa, suka warke.
”Sai ya yi tambaya ya ce, ‹“Amma ku fa, wa kuke ce da ni?”› Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Kiristi.”
”Sai ya fara koya musu cewa, dole Ɗan Mutum yă sha wahaloli da yawa, dattawa, manyan firistoci da malaman dokoki kuma su ƙi shi. Dole kuma a kashe shi, bayan kwana uku kuma, yă tashi.
”gama yana koya wa almajiransa. Ya ce musu, ‹“Za a ci amanar Ɗan Mutum, a ba da shi ga hannun mutane. Za su kashe shi, bayan kwana uku kuma zai tashi.”›
”Suna haurawa a hanyarsu zuwa Urushalima ke nan, Yesu yana a gaba, almajiran suna bin sa suna mamaki, waɗanda suke bi kuma suna ji tsoro. Ya sāke kai Sha Biyun nan gefe, ya gaya musu abin da zai faru da shi. Ya ce, ‹“Za mu haura zuwa Urushalima, za a bashe Ɗan Mutum, ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa, a kuma ba da shi ga Al’ummai,› ‹waɗanda za su yi masa ba’a, su tofa masa miyau, su yi masa bulala, su kuma kashe shi. Bayan kwana uku kuma yă tashi.”›
”‹Gama ko Ɗan Mutum ma, bai zo domin a bauta masa ba, amma don yă yi bauta, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”›
”Da suka kai Urushalima, sai Yesu ya shiga filin haikalin, ya fara korar waɗanda suke saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur na masu musayar kuɗi, da kujerun masu sayar da tattabaru, ya kuma hana kowa yă ratsa da a filin haikali ɗauke da kayan ciniki. Da yake koya musu, sai ya ce, ‹“Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira gidana, gidan addu’a na dukan al’ummai ba’?›‹Amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’›‹”› Manyan firistoci da malaman dokoki suka ji wannan, sai suka fara neman hanyar da za su kashe shi, gama suna jin tsoronsa, saboda dukan taron suna mamakin koyarwarsa.
”Yayinda Yesu yake koyarwa a filin haikalin, sai ya yi tambaya ya ce, ‹“Yaya malaman dokoki suke cewa Kiristi ɗan Dawuda ne?›
”‹Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.›
”‹“Sa’an nan, mutane za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin gizagizai da iko, da ɗaukaka mai girma.›
”‹Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.›
”Yayinda suke cin abinci, sai Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya, ya ba wa almajiransa, yana cewa, ‹“Ku karɓa, wannan jikina ne.”› Sai kuma ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, ya kuma miƙa musu, dukansu suka sha daga ciki. Sai ya ce musu, ‹“Wannan jinina ne na alkawari, wanda aka zubar da shi saboda mutane da yawa.›
”Amma Yesu ya yi shiru, bai kuwa amsa ba. Babban firist ya sāke tambayarsa ya ce, “Kai ne Kiristi, Ɗan Mai Albarka?” Yesu ya ce, ‹“Ni ne. Za ku kuwa ga Ɗan Mutum yana zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a cikin gizagizan sama.”›
”Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa ya ce, ‹“I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.”›
”Suka sa masa wata riga mai ruwan shunayya, suka kuma tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa. Sai suka fara ce masa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!” Suka dinga bugunsa a kā da sanda, suka tattofa masa miyau. Suka durƙusa suka yi masa bangirma na ba’a. Bayan da suka gama yin masa ba’a, suka tuɓe rigar mai ruwan shunayyar, suka sa masa nasa tufafi. Sai suka tafi da shi don a gicciye shi.
”Akwai rubutu na zarginsa, da ya ce, Sarkin Yahudawa. Suka gicciye ’yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗayan kuma a hagunsa.
”Bari wannan Kiristi, wannan Sarkin Isra’ila, yă sauko yanzu daga gicciye, don mu ga mu kuma gaskata.” Waɗanda aka gicciye tare da shi ma suka zazzage shi.
”A daidai sa’a ta tara na rana, sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, ‹“Eloi, Eloi, lama sabaktani?”› (Wato, ‹“Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”›).
”Da murya mai ƙarfi, Yesu ya ja numfashinsa na ƙarshe. Labulen haikali kuwa ya yage kashi biyu, daga sama har ƙasa. Da jarumin da yake tsaye a gaban Yesu ya ji muryarsa, ya kuma ga yadda ya mutu, sai ya ce, “Gaskiya, wannan mutum Ɗan Allah ne!”
”Da suna shiga cikin kabarin, sai suka ga wani saurayi sanye da farar riga, yana zaune a hannun dama, sai suka firgita. Ya ce, “Kada ku firgita. Kuna neman Yesu Banazare wanda aka gicciye ne. Ya tashi! Ba ya nan. Ku dubi inda aka kwantar da shi. Amma ku tafi ku gaya wa almajiransa da kuma Bitrus cewa, ‘Ya sha gabanku zuwa Galili. Can za ku gan shi, kamar yadda ya faɗa muku.’ ” Da rawan jiki da kuma ruɗewa, matan suka fita a guje daga kabarin. Ba su kuwa gaya wa kowa ba, don suna tsoro. [Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko da waɗansu shaidu na dā ba su da ayoyi 9-20.]
”Bayan Ubangiji Yesu ya yi musu magana, sai aka ɗauke shi zuwa sama, ya kuma zauna a hannun dama na Allah. Sai almajiran suka fita, suka yi wa’azi ko’ina. Ubangiji kuwa ya yi aiki tare da su, ya tabbatar da maganarsa ta wurin alamu da suke biye da maganar.
”Ga shi za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa, za ki kuma ba shi suna Yesu. Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi gadon sarautar kakansa Dawuda, zai yi mulkin gidan Yaƙub har abada, mulkinsa kuma ba zai taɓa ƙare ba.”
”Maryamu ta tambayi mala’ikan ta ce, “Yaya wannan zai yiwu, da yake ni budurwa ce?” Mala’ikan ya amsa ya ce, “Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, ikon Maɗaukaki kuma zai rufe ke. Saboda haka, Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah.
”ta kuwa haifi ɗanta na fari. Ta nannaɗe shi a zane ta kuma kwantar da shi cikin wani kwami, don ba su sami ɗaki a masauƙi ba.
”Yau a birnin Dawuda an haifa muku Mai Ceto; shi ne Kiristi Ubangiji. Wannan zai zama alama a gare ku. Za ku tarar da jariri a nannaɗe a zane kwance a kwami.” Ba labari sai ga taron rundunar sama suka bayyana tare da mala’ikan, suna yabon Allah suna cewa, “Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama, a duniya kuma salama ga mutane waɗanda tagomashinsa yake bisansu.”
”Sa’an nan Siman ya sa musu albarka ya ce wa Maryamu mahaifiyarsa, “An ƙaddara yaron nan yă zama sanadin fāɗuwa da tashin mutane da yawa a Isra’ila, zai kuma zama alamar da mutane ba za su so ba, ta haka za a fallasa tunanin zukatan mutane da yawa. Ke ma, takobi zai soki zuciyarki.”
”Sa’ad da ake wa dukan mutane baftisma, sai aka yi wa Yesu shi ma. Da yana cikin addu’a, sai sama ya buɗe, Ruhu Mai Tsarki kuma ya sauko masa a wata siffa, kamar kurciya. Sai murya ta fito daga sama, ta ce, “Kai ne Ɗana, wanda nake ƙauna, kai ne kuma kana faranta mini zuciya ƙwarai.”
”Yesu ya koma Galili cikin ikon Ruhu. Labarinsa kuwa ya bazu ko’ina a ƙauyuka. Ya yi ta koyarwa a majami’unsu, kowa kuwa ya yabe shi.
”Aka kuwa ba shi naɗaɗɗen littafin annabi Ishaya. Da ya buɗe, sai ya sami wurin da aka rubuta, ‹“Ruhun Ubangiji yana kaina,› ‹domin ya shafe ni,› ‹in yi wa matalauta wa’azin bishara.› ‹Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku,› ‹in kuma buɗe idanun makafi,› ‹in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne.› ‹In yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji.”› Sai ya naɗe naɗaɗɗen littafin ya mayar wa mai hidimar, ya kuma zauna. Dukan idanun waɗanda suke a majami’ar, suka koma a kansa. Sai ya fara ce musu, ‹“A yau, Nassin nan, ya cika a kunnenku.”›
”Suka yi ta mamakin koyarwarsa, domin saƙonsa yana da iko. A cikin majami’ar, akwai wani mutum mai aljani, wani mugun ruhu. Mutumin ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki na Allah!” Yesu ya tsawata masa da ƙarfin cewa, ‹“Yi shiru! Ka fita daga cikinsa!”› Sai aljanin ya fyaɗa mutumin da ƙasa a gabansu duka, sa’an nan ya fita, ya bar shi ba wani rauni. Dukan mutanen suka yi mamaki, suka ce wa junansu, “Wace irin koyarwa ce haka? Da ƙarfi da iko, yana ba wa mugayen ruhohin umarni suna kuma fita!”
”Bugu da ƙari, aljanu suka fiffita daga cikin mutane da yawa suna ihu suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne!” Amma ya kwaɓe su, ya hana su magana, don sun san cewa shi ne Kiristi.
”Da ya gama magana, sai ya ce wa Siman, ‹“Ka tuƙa jirgin zuwa inda akwai zurfi, ka saukar da abin kamun kifinka ka kama kifi.”› Siman ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, duk dare mun yi ta fama ba mu kama kome ba, amma tun da ka ce haka, zan saki abin kamun kifin.” Da suka yi haka, sai suka kama kifi da yawa, har abin kamun kifinsu suka fara tsintsinkewa. Sai suka kira abokansu a ɗaya jirgin, su zo su taimake su, suka kuwa zo. Suka cika jiragen biyu da kifi cif, har jiragen suka fara nutsewa. Da Siman Bitrus ya ga wannan, sai ya fāɗi a gaban Yesu ya ce, “Rabu da ni, Ubangiji. Ni mai zunubi ne!”
”Yesu ya san abin da suke tunani, sai ya yi tambaya ya ce, ‹“Don me kuke tunanin waɗannan abubuwa a zukatanku?›
”‹Masu albarka ne sa’ad da mutane suka ƙi ku,› ‹suka ware ku, suka zage ku,› ‹suna ce da ku mugaye,› ‹saboda Ɗan Mutum.›
”‹“Amma ku fa, wa, kuke ce da ni?”› Bitrus ya amsa ya ce, “Kiristi na Allah.” Yesu ya gargaɗe su da ƙarfi, kada su gaya wa kowa wannan magana. Ya sāke cewa, ‹“Dole ne Ɗan mutum ya sha wahaloli da yawa, dattawa, da manyan firistoci, da malaman dokoki kuma su ƙi shi, kuma dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a tā da shi da rai.”›
”‹“Ubana ya danƙa mini dukan kome. Ba wanda ya san Ɗan sai Uban, kuma ba wanda ya san Uban, sai Ɗan, da kuma waɗanda Ɗan ya zaɓa ya bayyana musu shi.”›
”‹“Ina gaya muku, duk wanda ya shaida ni a gaban mutane, Ɗan Mutum ma zai shaida shi a gaban mala’ikun Allah.› ‹Amma wanda ya yi mūsun sanina a gaban mutane, shi ma za a yi mūsunsa a gaban mala’ikun Allah.›
”Sai ya kai Sha Biyun gefe ɗaya, ya ce musu, ‹“Za mu Urushalima, kuma dukan abin da annabawa suka rubuta a kan Ɗan Mutum zai cika.› ‹Za a ba da shi ga Al’ummai, za su yi masa ba’a, su zage shi, su tofa masa miyau,› ‹za su yi masa bulala, su kuma kashe shi. A rana ta uku kuma zai tashi.”›
”‹Saboda Ɗan Mutum ya zo ne, domin yă nemi abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.”›
”Sai ya shiga filin haikali, ya fara korar masu sayar da kaya. Ya ce musu, ‹“A rubuce, yake cewa, ‘Gidana, zai zama gidan addu’a,’›‹amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ”› Kowace rana, ya yi ta koyarwa a haikalin. Amma manyan firistoci, da malaman dokoki, da shugabannin mutane, suna ƙoƙarin kashe shi. Amma ba su sami hanyar yin haka ba, domin kalmominsa sun kama hankalin dukan mutanen.
”Yesu ya zura musu ido ya ce, ‹“To, mene ne ma’anar abin da aka rubuta cewa,› ‹“ ‘Dutsen da magina suka ƙi,› ‹shi ne kuwa ya zama dutsen kan ginin’›, ‹Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Kuma in dutsen nan ya fāɗi a kan wani, zai murƙushe shi.”›
”‹Duk mutane za su ƙi ku saboda ni.›
”‹A lokacin ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin girgije, da iko, da ɗaukaka mai girma.›
”‹Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.›
”Sai ya ɗauki burodi ya yi godiya, ya kakkarya ya ba su, da cewa, ‹“Wannan jikina ne, da aka bayar dominku. Ku riƙa yin haka don tunawa da ni.”› Haka kuma, bayan abincin, ya ɗauki kwaf ruwan inabi ya ce, ‹“Wannan kwaf ruwan inabi shi ne, na sabon alkawari cikin jinina, da aka zubar dominku.›
”‹Ku ne kuka tsaya tare da ni a gwaje-gwajen da na sha.› ‹Daidai kamar yadda Ubana ya ba ni mulki, haka ni ma nake ba ku.› ‹Saboda ku ci, ku sha a teburina a cikin mulkina. Kuma ku zauna a kan gadon sarauta, ku yi wa kabilu goma sha biyu na Isra’ila shari’a.›
”Domin tsananin azaba, sai ya ƙara himma cikin addu’a, zuffansa kuma na ɗigowa ƙasa kamar jini.
”‹Amma daga yanzu, Ɗan Mutum zai zauna a hannun dama na Allah Mai Iko.”› Sai dukansu suka yi tambaya suka ce, “Wato, kai Ɗan Allah ke nan?” Ya amsa ya ce, ‹“Kun faɗa daidai, ni ne.”›
”Sai Bilatus ya tambayi Yesu ya ce, “Kai ne sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa ya ce, ‹“I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.”›
”Da suka isa wurin da ake kira “Ƙoƙon Kai,” nan suka gicciye shi, tare da masu laifin nan, ɗaya a hannun damansa, ɗayan kuma a hagunsa. Yesu ya ce, ‹“Ya Uba ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.”› Suka rarraba tufafinsa ta wurin jefa ƙuri’a.
”Bisa da shi kuma akwai rubutun da ya ce, Wannan shi ne Sarkin Yahudawa.
”Sai ya ce, “Yesu, ka tuna da ni sa’ad da ka shiga mulkinka.” Yesu ya amsa, ya ce masa, ‹“Gaskiya nake faɗa maka, yau ɗin nan, za ka kasance tare da ni, a mulkina a sama.”›
”Yanzu kuwa wajen sa’a ta shida ne, kuma duhu ya rufe ko’ina a ƙasar, har zuwa sa’a ta tara, domin rana ta daina haskakawa. Labulen da yake cikin haikali kuma ya yage kashi biyu. Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, ‹“Ya Uba, na danƙa ruhuna a hannunka.”› Da ya faɗi haka, sai ya ja numfashi na ƙarshe.
”Yayinda suna cikin tunani a kan wannan, nan take, ga waɗansu mutum biyu tsaye kusa da su, sanye da kaya masu ƙyalli, kamar walƙiya. A cikin tsoro, matan suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa, amma mutanen suka ce musu, “Me ya sa kuke neman mai rai a cikin matattu? Ba ya nan, ya tashi! Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana tare da ku a Galili cewa,
”Sai ya fara bayyana musu daga Musa da dukan Annabawa, abin da dukan Nassi ya faɗa a kansa.”
”Ya ce musu, ‹“Wannan shi ne abin da na gaya muku tun ina tare da ku cewa, dole a cika kome da aka rubuta game da ni, a cikin Dokar Musa, da Annabawa, da kuma Zabura.”› Sai ya wayar da tunaninsu don su fahimci Nassi. Ya ce musu, ‹“Wannan shi ne abin da aka rubuta, cewa dole Kiristi yă sha wahala, a rana ta uku kuma yă tashi daga matattu.› ‹Kuma a cikin sunansa za a yi wa’azin tuba da gafarar zunubai, ga dukan ƙasashe. Za a kuwa fara daga Urushalima.›
”Yana cikin sa musu albarka, sai ya rabu da su. Aka ɗauke shi zuwa cikin sama. Sai suka yi masa sujada, suka koma Urushalima cike da murna sosai.
”Tun farar farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne. Yana nan tare da Allah tun farar farawa. Ta wurin Kalman ne aka halicci dukan abubuwa. In ba tare da shi ba, babu abin da aka yi wanda aka yi.
”Yana a duniya, kuma ko da yake an yi duniya ta wurinsa ne, duniya ba tă gane shi ba. Ya zo wurin abin da yake nasa, amma nasa ɗin ba su karɓe shi ba. Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ’ya’yan Allah ’ya’yan da aka haifa ba bisa hanyar ’yan adam, ko shawarar mutum ko nufin namiji ba, sai dai haifaffu bisa ga nufin Allah. Kalman ya zama mutum, ya kuwa zauna a cikinmu. Muka ga ɗaukakarsa, ɗaukaka ta wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaici, wanda ya zo daga wurin Uba, cike da alheri da gaskiya.
”Gama an ba da doka ta wurin Musa; alheri da gaskiya kuwa sun zo ne ta wurin Yesu Kiristi.
”Kashegari Yohanna ya ga Yesu yana zuwa wajensa sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah mai ɗauke zunubin duniya!
”Da ya ga Yesu yana wucewa, sai ya ce, “Ku ga, ga Ɗan Rago na Allah!”
”Abu na fari da Andarawus ya yi shi ne ya sami ɗan’uwansa Siman ya gaya masa cewa, “Mun sami Almasihu” (wato, Kiristi).
”Sai Natanayel ya ce, “Rabbi, kai Ɗan Allah ne. Kai ne Sarkin Isra’ila.”
”Nan kusa kuwa akwai tulunan ruwa shida na dutse a ajiye, irin da Yahudawa suke amfani da su don tsarkakewa bisa ga al’ada, kowace kan ci gallon kusan ashirin zuwa talatin. Sai Yesu ya ce wa bayin, ‹“Ku ciccika tulunan da ruwa.”› Suka kuwa ciccika su fal. Sa’an nan ya ce musu, ‹“Yanzu ku ɗiba ku kai wa uban bikin.”› Suka yi haka. Uban bikin kuwa ya ɗanɗana ruwan da aka juya ya zama ruwan inabi. Bai san daga ina ya fito ba, ko da yake bayin da suka ɗiba ruwan sun sani. Sai ya kira angon waje ɗaya ya ce, “Kowa yakan kawo ruwan inabi mafi kyau da fari, sa’an nan marar kyan bayan baƙin sun sha da yawa; amma ka ajiye ruwan inabi mafi kyau sai yanzu.”
”Saboda haka ya tuƙa bulala ta igiyoyi, ya kori duka daga filin haikali, har da tumaki da shanu; ya watsar da kuɗin masu canjin, ya birkice teburansu. Ga masu sayar da tattabaru kuwa ya ce, ‹“Ku kwashe waɗannan daga nan! Don me za ku mai da gidan Ubana kasuwa!”› Sai almajiransa suka tuna cewa a rubuce yake, “Himma saboda gidanka zai cinye ni.” Sai Yahudawa suka tambaye shi, “Wace abar banmamaki za ka nuna mana ka tabbatar mana ikonka na yin duk waɗannan?” Yesu ya amsa musu ya ce, ‹“Ku rushe wannan haikali, zan kuwa sāke tā da shi cikin kwana uku.”›
”‹Na yi muku magana a kan abubuwan duniya amma ba ku gaskata ba; to, yaya za ku gaskata in na yi magana a kan abubuwan sama?› ‹Ba wanda ya taɓa hawa zuwa sama sai wanda ya sauka daga sama, wato, Ɗan Mutum.› ‹Kamar dai yadda Musa ya ɗaga maciji a hamada, haka dole ne a ɗaga Ɗan Mutum,› ‹don duk mai gaskata da shi ya sami rai madawwami.”› Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa. Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba.
”“Wannan da ya zo daga sama ya fi kowa; wannan da ya zo daga ƙasa na ƙasa ne, yana kuma magana kamar wanda ya zo daga ƙasa ne. Wannan da ya zo daga sama ya fi kowa.
”Uban yana ƙaunar Ɗan ya kuma danƙa kome a hannuwansa. Duk wanda ya gaskata da Ɗan yana da rai madawwami, amma duk wanda ya ƙi Ɗan ba zai sami rai ba, gama fushin Allah yana nan a bisansa.”
”Yesu ya amsa ya ce, ‹“Kowa ya sha wannan ruwa, zai sāke jin ƙishirwa,› ‹amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba. Tabbatacce, ruwan da zan ba shi, zai zama masa maɓuɓɓugan ruwa da yake ɓuɓɓugowa har yă zuwa rai madawwami.”›
”Macen ta ce, “Na san cewa Almasihu” (da ake ce da shi Kiristi) “yana zuwa. Sa’ad da ya zo kuwa, zai bayyana mana kome.” Sai Yesu ya ce, ‹“Ni mai maganan nan da ke, Ni ne shi.”›
”Don haka Yahudawa suka ƙara nema su kashe shi; ba don yă karya Asabbaci kawai ba, har ma yana ce Allah Ubansa ne, yana mai da kansa daidai da Allah. Sai Yesu ya ba su wannan amsa cewa, ‹“Gaskiya nake gaya muku, Ɗan ba ya iya yin kome da kansa; yana yin abin da ya ga Ubansa yake yi ne kawai, gama duk abin da Uban yake yi shi ne Ɗan ma yake yi.› ‹Gama Uban yana ƙaunar Ɗan yana kuma nuna masa duk abin da yake yi. I, za ku kuwa yi mamaki, gama zai nuna masa abubuwan da suka fi waɗannan girma.› ‹Gama kamar yadda Uban yake tā da matattu yake kuma ba su rai, haka ma Ɗan yake ba da rai ga wanda ya ga dama.› ‹Bugu da ƙari, Uban ba ya hukunta kowa, sai dai ya danƙa dukan hukunci a hannun Ɗan,› ‹don kowa yă girmama Ɗan kamar yadda yake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan ba ya girmama Uban, da ya aiko shi ke nan.› ‹“Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ji maganata ya kuma gaskata da wanda ya aiko ni yana da rai madawwami ba za a kuma hukunta shi ba; ya riga ya ƙetare daga mutuwa zuwa rai.›
”‹Gaskiya nake gaya muku, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya zo sa’ad da matattu za su ji muryar Ɗan Allah waɗanda kuwa suka ji za su rayu.› ‹Gama kamar yadda Uban yana da rai a cikinsa, haka ya sa Ɗan yă kasance da rai a cikin kansa.› ‹Ya kuma ba shi iko yă hukunta domin shi Ɗan Mutum ne.› ‹“Kada ku yi mamakin wannan, gama lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke cikin kaburbura za su ji muryarsa› ‹su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta za su tashi zuwa ga rai, waɗanda kuma suka aikata mugunta za su tashi zuwa ga hukunci.›
”Sa’an nan Yesu ya furta cewa, ‹“Ni ne burodin rai. Wanda ya zo wurina ba zai taɓa jin yunwa ba, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai taɓa jin ƙishirwa ba.›
”‹Gama na sauko daga sama ba don in cika nufin kaina ba sai dai don in cika nufin shi wanda ya aiko ni.›
”‹Ni ne burodin rai mai saukowa daga sama. Duk wanda ya ci wannan burodi, zai rayu har abada. Wannan burodin shi ne jikina, da zan bayar don duniya ta sami rai.”›
”Sai Yesu ya ce musu, ‹“Gaskiya nake gaya muku, sai kun ci naman jikin Ɗan Mutum kuka kuma sha jininsa, ba za ku kasance da rai a cikinku ba.› ‹Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana da rai madawwami. Ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.› ‹Gama naman jikina abinci ne na gaskiya jinina kuma abin sha ne na gaskiya.› ‹Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana cikina, ni kuma ina cikinsa.›
”Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan koyarwa tana da wuya. Wa zai iya yarda da ita?” Da yake ya san almajiransa suna gunaguni game da wannan, sai Yesu ya ce musu, ‹“Wannan ya ɓata muku rai ne?› ‹Me za ku ce ke nan, in kuka gan Ɗan Mutum yana hawa zuwa inda yake dā!› ‹Ruhu ne yake ba da rai; jikin kam, ba ya amfana kome. Kalmomin da na faɗa muku, Ruhu ne, da kuma rai.›
”Ya ci gaba da cewa, ‹“Shi ya sa na faɗa muku cewa ba mai iya zuwa wurina, sai dai Uba ya yardar masa.”›
”Daga wannan lokaci da yawa daga cikin almajiransa suka ja da baya, suka daina bin sa. Sai Yesu ya tambayi Sha Biyun, ‹“Ku ma za ku tafi ne?”› Sai Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Ubangiji wajen wa za mu tafi? Kai ne da kalmomin rai madawwami.
”Yesu ya amsa ya ce, ‹“Koyarwata ba tawa ba ce, ta fito ne daga wurin wanda ya aiko ni.› ‹Duk wanda ya zaɓi yin nufin Allah, zai gane ko koyarwata daga Allah ce, ko kuwa don kaina ne nake magana.› ‹Mai magana don kansa, neman ɗaukakar kansa yake yi. Amma mai neman ɗaukakar wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, ba kuwa rashin gaskiya a gare shi.›
”Sa’ad da Yesu ya sāke magana da mutanen, sai ya ce, ‹“Ni ne hasken duniya. Duk wanda ya bi ni ba zai yi tafiya cikin duhu ba, sai dai yă sami hasken rayuwa.”›
”‹Amma ko da zan yi shari’a, shari’ata daidai ce, don ba ni kaɗai ba ne. Ina tare da Uba da ya aiko ni.›
”‹Ni ne nake shaidar kaina, Uba da ya aiko ni kuma yana shaidata.”›
”Amma ya ci gaba da cewa, ‹“Ku daga ƙasa kuke; ni kuwa daga bisa ne. Ku na duniyan nan ne; ni kuwa ba na duniyan nan ba ne.› ‹Na gaya muku cewa za ku mutu cikin zunubanku; in ba ku gaskata cewa ni ne wanda na ce nake ba, lalle za ku mutu cikin zunubanku.”›
”Saboda haka Yesu ya ce, ‹“Sa’ad da kuka ɗaga Ɗan Mutum, a sa’an nan ne za ku san cewa ni ne wannan da na ce nake. Ni kuwa ba na yin kome ni kaɗai, sai in dai faɗi abin da Uba ya koya mini.› ‹Wanda kuwa ya aiko ni yana tare da ni; bai bar ni ni kaɗai ba, domin kullum ina aikata abin da ya gamshe shi.”›
”Yesu ya amsa ya ce, ‹“Gaskiya nake gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne!”›
”Yesu ya ji labari cewa sun kore shi, da ya same shi kuwa, sai ya ce, ‹“Ka gaskata da Ɗan Mutum?”› Sai mutumin ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, wane ne shi? Gaya mini, don in gaskata da shi.” Yesu ya ce, ‹“Yanzu ka gan shi; tabbatacce ma, shi ne yake magana da kai.”› Sai mutumin ya ce, “Ubangiji, na gaskata,” ya kuma yi masa sujada.
”Saboda haka Yesu ya sāke cewa, ‹“Gaskiya nake gaya muku, ni ne ƙofar tumakin.›
”‹“Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yakan ba da ransa domin tumakin.›
”‹“Ni ne makiyayi mai kyau; na san tumakina, tumakina kuma sun san ni,› ‹kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uba, ina kuwa ba da raina domin tumakin.› ‹Ina da waɗansu tumaki da ba na wannan garken ba ne. Dole ne in kawo su su ma. Za su saurari muryata, za su kasance garke guda ɗaya, makiyayi guda kuma.› ‹Abin da ya sa Ubana yake ƙaunata ke nan, domin ina ba da raina, in ɗauko shi kuma.› ‹Ba mai karɓe mini rai, ina dai ba da shi. Ina da iko in ba da shi, ina da iko in ɗauko shi kuma. Wannan umarni kuwa daga wurin Ubana na karɓo shi.”›
”Yesu ya amsa ya ce, ‹“Na faɗa muku, amma ba ku gaskata ba. Ayyukan da nake yi cikin sunan Ubana su suke nuna ko wane ne ni.› ‹Amma ba ku gaskata ba domin ku ba tumakina ba ne.› ‹Tumakina sukan saurari muryata; na sansu, suna kuma bi na.› ‹Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.› ‹Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba mai ƙwace su daga hannun Ubana.› ‹Da ni da Uba ɗaya ne.”›
”‹Da ni da Uba ɗaya ne.”› Sai Yahudawa suka sāke ɗebo duwatsu don su jajjefe shi, amma Yesu ya ce musu, ‹“Na nuna muku ayyukan alheri masu yawa da Uba ya aiko ni in yi, a kan wanne kuke so ku jajjefe ni?”› Yahudawa suka amsa suka ce, “Ai, ba don wani daga cikin waɗannan ayyukan alheri ne muke so mu jajjefe ka ba, amma don saɓon da kake yi, kai da kake mutum kawai, kana mai da kanka Allah.”
”‹Amma in su nake yi, ko ba ku gaskata ni ba, to, ku gaskata ayyukan, don ku sani, ku kuma gane, Uban yana cikina, ni kuma ina cikin Uban.”›
”Yesu ya ce mata, ‹“Ni ne tashin matattu da kuma rai. Duk wanda ya gaskata da ni zai rayu, ko ya mutu;› ‹kuma duk wanda yake raye ya kuma gaskata da ni ba zai taɓa mutuwa ba. Kin gaskata wannan?”› Sai ta ce masa, “I, Ubangiji, na gaskata kai ne Kiristi, Ɗan Allah, mai zuwa cikin duniya.”
”Yesu ya yi kuka.
”Sa’ad da ya faɗa haka, sai Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, ‹“Lazarus, ka fito!”› Sai mamacin ya fito, hannuwansa da ƙafafunsa a daure da ƙyallayen lilin, fuskarsa kuwa an naɗe da mayafi. Yesu ya ce musu, ‹“Ku tuɓe kayan bizo, ku bar shi yă tafi.”›
”Kashegari babban taron da suka zo Bikin suka sami labari cewa Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima. Sai suka ɗaɗɗauko rassan dabino suka fiffita taryensa, suna ɗaga murya suna cewa, “Hosanna!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Mai albarka ne Sarkin Isra’ila!”
”Yesu ya amsa ya ce, ‹“Lokaci ya yi da za a ɗaukaka Ɗan Mutum.›
”‹Uba, ka ɗaukaka sunanka!”› Sai wata murya ta fito daga sama ta ce, “Na riga na ɗaukaka shi, zan kuma ƙara ɗaukaka shi.”
”‹Amma ni, sa’ad da aka ɗaga ni daga ƙasa, zan ja dukan mutane gare ni.”› Ya faɗa haka ne don yă nuna irin mutuwar da zai yi.
”Ishaya ya faɗi haka ne, saboda ya hangi ɗaukakar Yesu, ya kuwa yi magana a kansa.
”‹Akwai mai hukunci saboda wanda ya ƙi ni, bai kuma karɓi kalmomina ba; wannan maganar da na faɗa ita ce za tă hukunta shi a rana ta ƙarshe.› ‹Gama ba don kaina na yi magana ba, Uban da ya aiko ni shi kansa ne ya ba ni umarni a kan abin da zan faɗa da kuma yadda zan faɗe shi.›
”Ana gab da Bikin Ƙetarewa. Yesu kuwa ya san cewa lokaci ya yi da zai bar wannan duniya, yă koma wurin Uba. Da yake ya ƙaunaci waɗanda suke nasa a duniya, yanzu kuwa ya nuna musu cikakkiyar ƙaunarsa.
”Da ya tafi, sai Yesu ya ce, ‹“Yanzu ne aka ɗaukaka Ɗan Mutum aka kuma ɗaukaka Allah a cikinsa.› ‹In kuwa Allah ya sami ɗaukaka a cikin Ɗan, Allah kuwa zai ɗaukaka Ɗan zuwa ga zatinsa, zai kuma ɗaukaka shi nan take.›
”Yesu ya amsa ya ce, ‹“Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina.› ‹Da kun san ni, da za ku san Ubana ma. Daga yanzu, kun san shi kun kuma gan shi.”›
”‹Ba ka gaskata cewa ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina ba? Kalmomin da nake gaya muku ba na kaina ba ne. Ai, Uban da yake raye a cikina ne yake aikinsa.› ‹Ku gaskata ni sa’ad da na ce ina cikin Uba, Uba kuma yana cikina. Ko kuwa ku gaskata ni saboda ayyukan banmamakin su kansu.›
”‹Gaskiya nake gaya muku, duk wanda yake da bangaskiya gare ni, zai yi abubuwan da ni nake yi. Zai ma yi abubuwa masu girma fiye da waɗannan, don zan tafi wurin Uba.› ‹Kuma zan yi duk abin da kuka roƙa cikin sunana, don Ɗan ya kawo ɗaukaka ga Uban.› ‹Za ku iya roƙe ni kome a cikin sunana, zan kuwa yi.› ‹“In kuna ƙaunata za ku yi biyayya da umarnina.›
”‹A ranan nan za ku sani ina cikin Uba, ku kuma kuna cikina, ni kuma ina cikinku.›
”‹Wanda ba ya ƙaunata ba zai yi biyayya da koyarwata ba. Waɗannan kalmomin da kuke ji ba nawa ba ne; na Uba ne da ya aiko ni.›
”‹“Kun dai ji na ce, ‘Zan tafi in kuma sāke dawo wurinku.’ In har kuna ƙaunata, za ku yi farin ciki cewa za ni wurin Uba, domin kuwa Uban ya fi ni.›
”‹“Ni ne kuringar inabi na gaskiya, Ubana kuwa shi ne manomin.›
”‹“Ni ne kuringar inabin; ku ne kuma rassan. In mutum ya kasance a cikina ni kuma a cikinsa, zai ba da ’ya’ya da yawa; in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba.› ‹Duk wanda bai kasance a cikina ba, yana kamar reshen da aka jefar yă bushe; irin waɗannan rassan ne akan tattara, a jefa cikin wuta a ƙone.› ‹In kun kasance a cikina kalmomina kuma suka kasance a cikinku, ku roƙi kome da kuke so, za a kuwa ba ku.›
”‹“Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, fa, ku kasance cikin ƙaunata.› ‹In kuka yi biyayya da umarnaina, za ku kasance a cikin ƙaunata, kamar dai yadda na yi biyayya da umarnan Ubana na kuma kasance a cikin ƙaunarsa.› ‹Na gaya muku wannan domin murnata ta kasance a cikinku, murnanku kuma ta zama cikakkiya.›
”‹Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku.› ‹Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa.›
”‹“In duniya ta ƙi ku, ku san cewa ta fara ƙin na ne.›
”‹Wanda ya ƙi ni ya ƙi ya ƙi Ubana ma.›
”‹Zai kawo ɗaukaka gare ni ta wurin ɗaukan abin da yake nawa, ya bayyana muku.› ‹Duk abin da yake na Uba nawa ne. Shi ya sa na ce, ‘Ruhun zai ɗauko daga abin da yake nawa, yă bayyana muku.’ ”›
”Yanzu mun gane cewa ka san kome ba sai wani ya tambaye ka ba. Wannan ya sa muka gaskata ka fito daga Allah.”
”‹Amma lokaci na zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansa. Za ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka ba ni kaɗai ba ne, gama Ubana yana tare da ni.› ‹“Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”›
”Bayan da Yesu ya faɗi wannan, sai ya dubi sama ya yi addu’a ya ce, ‹“Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka, don Ɗanka yă ɗaukaka ka.› ‹Gama ka ba shi iko bisa dukan mutane domin yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi.› ‹Rai madawwami kuwa shi ne, su san ka, Allah makaɗaici mai gaskiya, da kuma Yesu Kiristi, wanda ka aiko.› ‹Na ɗaukaka ka a duniya ta wurin gama aikin da ka ba ni.› ‹Yanzu ya Uba, ka ɗaukaka ni a gabanka da ɗaukakar da dā nake da ita tun kafin a kafa duniya.›
”‹Ina addu’a dominsu. Ba domin duniya nake addu’a ba, amma domin waɗanda ka ba ni, gama su naka ne.› ‹Duk abin da nake da shi naka ne, kuma duk abin da kake da shi nawa ne. Na kuwa sami ɗaukaka ta wurinsu.›
”‹“Yanzu ina zuwa wurinka, sai dai na faɗi waɗannan abubuwa ne tun ina a duniya domin farin ciki yă zama cikakke a cikinsu.› ‹Na gaya musu maganarka duniya kuwa ta ƙi su, don su ba na duniya ba ne yadda ni ma ba na duniya ba ne.›
”‹Ina so dukansu su zama ɗaya, ya Uba, kamar yadda kake a cikina, ni kuwa a cikinka. Haka su ma bari su zauna cikinmu, domin duniya ta gaskata cewa kai ka aiko ni.› ‹Na ba su ɗaukakar da ka ba ni, don su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya.› ‹Ni a cikinsu kai kuma a cikina. Bari su kasance da cikakken haɗinkai, domin duniya ta san cewa kai ka aiko ni. Ka kuwa ƙaunace su yadda ka ƙaunace ni.› ‹“Uba, ina so waɗanda ka ba ni su kasance tare da ni a inda nake, su kuma ga ɗaukakata, ɗaukakar da ka ba ni domin kana ƙaunata kafin halittar duniya.›
”Suka amsa suka ce, “Yesu Banazare.” Yesu ya ce, ‹“Ni ne shi.”› (Yahuda kuwa wanda ya bashe shi yana nan tsaye tare da su.) Da Yesu ya ce, ‹“Ni ne shi,”› sai suka ja da baya suka fāɗi a ƙasa.
”Yesu ya ce, ‹“Mulkina ba na duniyan nan ba ne. Da na duniyan nan ne da bayina sun yi yaƙi su hana Yahudawa kama ni. Amma fa mulkina daga wani waje ne.”› Sai Bilatus ya ce, “To, wato, kai sarki ne!” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Haka yake, ni sarki ne yadda ka faɗa. Tabbatacce, saboda wannan dalili ne aka haife ni, kuma don wannan ne na zo duniya, domin in shaidi gaskiya. Duk wanda yake gefen gaskiya yakan saurare ni.”›
”Sai sojojin suka tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa a kā, suka kuma yafa masa wata riga mai ruwan shunayya. Suka yi ta zuwa wurinsa suna cewa, “Ranka yă daɗe, sarkin Yahudawa!” Suna ta marinsa a fuska.
”Yahudawa dai suka nace suna cewa, “Mu fa muna da doka, kuma bisa ga dokar dole yă mutu domin ya mai da kansa Ɗan Allah.”
”Ranar Shirye-shiryen Makon Bikin Ƙetarewa ce kuwa, wajen sa’a ta shida. Sai Bilatus ya ce wa Yahudawa, “Ga sarkinku.” Amma suka yi ihu suka ce, “A yi da shi! A yi da shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce, “A! In gicciye sarkinku?” Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Mu dai, ba mu da wani sarki sai Kaisar.”
”Bilatus ya sa aka rubuta wata sanarwa aka kafa a kan gicciyen. Abin da aka rubuta kuwa shi ne, Yesu Banazare, Sarkin Yahudawa. Yahudawa da yawa suka karanta wannan sanarwa, gama inda aka gicciye Yesu yana kusa da birni. An kuwa rubuta sanarwar da Arameyanci, Romanci da kuma Girik. Sai manyan firistocin Yahudawa suka ce, “A’a! Kada ka rubuta, ‘Sarkin Yahudawa,’ ka dai rubuta, wannan mutum ya ce shi sarkin Yahudawa ne.” Bilatus ya amsa ya ce, “Abin da na rubuta, na rubuta.”
”Bayan haka, sanin cewa an cika kome, kuma domin a cika Nassi, sai Yesu ya ce, ‹“Ina jin ƙishirwa.”›
”Da ya tsotsi abin sha ɗin, sai Yesu ya ce, ‹“An gama.”› Da wannan fa, ya sunkuyar da kansa ya saki ruhunsa.
”sai ta ga waɗansu mala’iku biyu saye da fararen tufafi, zaune a inda dā gawar Yesu take, ɗaya wajen kai ɗayan kuma wajen ƙafafu. Suka tambaye ta cewa, “Mace, don me kike kuka?” Ta ce, “Sun ɗauke Ubangijina, ban kuma san inda suka ajiye shi ba.” Da ta faɗin haka, sai ta juya ta ga Yesu tsaye, sai dai ba tă gane cewa Yesu ne ba. Sai ya ce, ‹“Mace, don me kike kuka? Wa kike nema?”› Ta yi tsammani shi ne mai aikin lambun, sai ta ce, “Ranka yă daɗe, in kai ne ka ɗauke shi, gaya mini inda ka ajiye shi, in je in ɗauke shi.” Yesu ya ce mata, ‹“Maryamu.”› Sai ta juya wajensa ta ɗaga murya ta ce da Arameyanci, “ Rabboni!” (Wanda yake nufin “Malam”).
”Da Yamman ranar farko ta mako, sa’ad da almajiran suna tare, ƙofofi kuma suna a kulle saboda tsoron Yahudawa, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, ‹“Salama tă kasance tare da ku!”›
”Bayan mako guda, har wa yau almajiransa suna cikin gidan, Toma kuwa yana tare da su. Ko da yake ƙofofi suna kulle, sai ga Yesu ya zo ya tsaya a tsakiyarsu ya ce, ‹“Salama tă kasance tare da ku!”› Sa’an nan ya ce wa Toma, ‹“Sa yatsarka nan; dubi hannuwana. Miƙa hannunka ka sa a gefena. Ka daina shakka ka gaskata.”› Toma ya ce masa, “Ya Ubangijina da Allahna!”
”Yesu ya yi waɗansu abubuwan banmamaki da yawa a gaban almajiransa da ba a rubuta a wannan littafi ba. An dai rubuta waɗannan ne don ku gaskata Yesu ne Kiristi, Ɗan Allah kuma ta wurin gaskatawa ku sami rai a cikin sunansa.
”Ya ce musu, ‹“Ku jefa abin kamun kifinku dama da jirgin ruwan, za ku samu.”› Da suka yi haka, sai suka kāsa jawo abin kamun kifin saboda yawan kifi. Sai almajirin da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, “Ai, Ubangiji ne!” Nan da nan da Siman Bitrus ya ji ya ce, “Ai, Ubangiji ne,” sai ya yafa mayafinsa (don dā ma ya tuɓe shi), ya fāɗa cikin ruwan.
”Yesu ya yi waɗansu abubuwa da yawa kuma. Da a ce an rubuta kowannensu, na tabbata ko duniya duka ba za tă sami wuri saboda littattafan da za a rubuta ba.
”Bayan wahalarsa, ya bayyana kansa ga waɗannan mutane ya kuma ba da tabbatattun alamu masu yawa cewa yana da rai. Ya bayyana a gare su har kwana arba’in ya kuma yi musu magana game da mulkin Allah.
”Bayan ya faɗi wannan, sai aka ɗauke shi sama a idanunsu sai wani girgije ya rufe shi daga ganinsu. Suna zuba ido a bisa, zuwa cikin sararin sama yayinda yake tafiya, nan da nan, sai ga mutane biyu saye da fararen riguna tsaye kusa da su. Sai suka ce, “Mutanen Galili, don me kuke tsaye a nan kuna duban sararin sama? Wannan Yesu, wanda aka ɗauke daga gare ku zuwa sama, zai komo daidai yadda kuka ga ya tafi sama.”
”“Mutanen Isra’ila, ku saurari wannan. Yesu Banazare shi ne mutumin da Allah ya tabbatar muku ta wurin mu’ujizai, ayyukan banmamaki, da kuma alamu, waɗanda Allah ya yi a cikinku ta wurinsa, kamar yadda ku kanku kuka sani. An ba da wannan mutum gare ku bisa ga nufin Allah da kuma rigyasaninsa, ku kuma tare da taimakon mugayen mutane, kuka kashe shi ta wurin kafa shi a kan gicciye.
”Ganin abin da yake gaba, ya yi magana a kan tashin Kiristi daga matattu cewa, ba a bar shi a kabari ba, jikinsa kuma bai ruɓa ba.
”An ɗaukaka shi zuwa ga hannun dama na Allah, ya karɓi alkawarin Ruhu Mai Tsarki daga Uba, ya kuma zubo abin da yanzu kuke gani kuke kuma ji.
”“Saboda haka bari dukan Isra’ila su tabbatar da wannan. Allah ya mai da wannan Yesu, da kuka gicciye, Ubangiji da kuma Kiristi.”
”Kuka kashe tushen rai, amma Allah ya tashe shi daga matattu. Mu shaidu ne ga wannan.
”to, sai ku san wannan, ku da dukan mutanen Isra’ila cewa da sunan Yesu Kiristi Banazare, wanda kuka gicciye amma wanda Allah ya tasar daga matattu ne, wannan mutum yake tsaye a gabanku lafiyayye. Shi ne, “ ‘dutsen da ku magina kuka ƙi, wanda kuwa ya zama dutsen kusurwar gini.’ Ba a samun ceto ta wurin wani dabam, gama babu wani suna a ƙarƙashin sama da aka ba wa mutane wanda ta wurinsa dole mu sami ceto.”
”Allahn kakanninmu ya tā da Yesu daga matattu, wanda kuka kashe ta wurin ratayewa a bisan itace. Allah ya ɗaukaka shi zuwa hannun damansa a matsayin Yerima da Mai Ceto don yă kawo tuba da gafarar zunubai ga Isra’ila.
”Amma Istifanus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dubi sama ya kuma ga ɗaukakar Allah, da Yesu kuma tsaye a hannun dama na Allah. Ya ce, “Ga shi, na ga sama a buɗe da kuma Ɗan Mutum tsaye a hannun dama na Allah.”
”Bābān yana karanta wannan Nassin, “An ja shi kamar tunkiya zuwa mayanka, kuma kamar ɗan rago a hannun mai askin gashinsa yake shiru, haka kuwa bai buɗe bakinsa ba.
”Kun san saƙon da Allah ya aika wa mutanen Isra’ila, yana shelar labari mai daɗi na salama ta wurin Yesu Kiristi, shi ne kuwa Ubangijin kowa.
”yadda Allah ya shafe Yesu Banazare da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da kuma yadda ya zaga ko’ina yana aikata alheri yana kuma warkar da dukan waɗanda suke ƙarƙashin ikon Iblis, domin Allah yana tare da shi.
”amma Allah ya tashe shi daga matattu a rana ta uku, ya sa kuma aka gan shi. Ba dukan mutane ne suka gan shi ba, amma ta wurin shaidun da Allah ya riga ya zaɓa, ta wurinmu da muka ci muka kuma sha tare da shi bayan tashinsa daga matattu. Ya umarce mu mu yi wa’azi ga mutane mu kuma shaida cewa shi ne wanda Allah ya naɗa yă zama mai shari’a na masu rai da na matattu. Duk annabawa sun yi shaida game da shi cewa duk wanda ya ba da gaskiya gare shi zai sami gafarar zunubai ta wurin sunansa.”
”yana musu bayani da tabbatarwa cewa dole Kiristi ya sha wahala ya kuma tashi daga matattu. Ya kuma ce, “Wannan Yesu da nake sanar muku shi ne Kiristi.”
”cewa Kiristi zai sha wahala, kuma a matsayin wanda yake na fari da zai tashi daga matattu, zai yi shelar haske ga mutanensa da kuma Al’ummai.”
”game da Ɗansa. Wanda bisa ga mutuntakarsa, zuriyar Dawuda ne. Wanda bisa ga Ruhun tsarki, an shaida shi da iko cewa shi Ɗan Allah ne ta wurin tashinsa daga matattu. Wannan bishara kuwa game da Yesu Kiristi Ubangijinmu ne.
”Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi,
”Amma Allah ya nuna mana ƙaunarsa a wannan. Tun muna masu zunubi tukuna, Kiristi ya mutu dominmu. Da yake yanzu mun sami zama marasa laifi ta wurin jininsa, ashe kuwa za a cece mu daga fushin Allah ta wurinsa! Gama in kuwa, sa’ad da muke abokan gāban Allah, aka sulhunta mu da shi ta wurin mutuwar Ɗansa, ashe, da yake an sulhunta mu, za mu sami ceto ta wurin ransa! Ba ma haka yake kawai ba, har muna farin ciki da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa yanzu muka sami sulhu.
”To, in mun mutu tare da Kiristi, mun gaskata cewa za mu rayu tare da shi kuma. Gama mun san cewa da yake an tā da Kiristi daga matattu, ba zai sāke mutuwa ba; mutuwa ba ta da sauran iko a kansa. Mutuwar da ya yi, ya mutu ne sau ɗaya tak, saboda yă shafe zunubi, amma rayuwar da yake yi, yana yi ne cikin tarayya da Allah. Haka ku ma, ku ɗauke kanku matattu ne ga ikon zunubi amma rayayyu cikin tarayya da Allah cikin Kiristi Yesu.
”Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
”Saboda haka, yanzu babu hukunci don waɗanda suke cikin Kiristi Yesu, gama ta wurin Kiristi Yesu dokar Ruhu mai ba da rai ta ’yantar da ni daga Dokar Musa. Gama abin da dokar ba tă iya yi saboda kāsawar mutuntaka ba, Allah ya yi shi sa’ad da ya aiko da Ɗansa a kamannin mutum mai zunubi, don yă zama hadaya ta zunubi. Ta haka, ya hukunta zunubi a cikin mutum mai zunubi.
”Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi?
”Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
”Kakannin-kakannin nan kuma nasu ne, Kiristi kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo ya tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome! Amin.
”Cewa in ka furta da bakinka, “Yesu Ubangiji ne,” ka kuma gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tā da shi daga matattu, za ka sami ceto.
”Saboda wannan ne Kiristi ya mutu, ya kuma sāke rayuwa domin yă zama Ubangiji na matattu da na masu rai.
”Gama Kiristi bai aike ni yin baftisma ba, sai dai wa’azin bishara ba da kalmomin hikimar mutum ba, domin kada gicciyen Kiristi ya rasa ikonsa. Gama saƙon gicciye wauta ne ga waɗanda suke hallaka, amma a gare mu, mu da ake ceto, ikon Allah ne.
”amma mu, muna wa’azin Kiristi wanda aka gicciye ne, wanda ya zama dutsen tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga Al’ummai, amma ga su waɗanda Allah ya kira, Yahudawa da Hellenawa, Kiristi ikon Allah ne, da kuma hikimar Allah.
”Saboda Allah ne kuke cikin Kiristi Yesu, shi wanda ya zama hikima a gare mu daga Allah. Kiristi shi ne adalcinmu, da tsarkinmu, da kuma fansarmu.
”Don na ƙudura a raina sa’ad da nake tare da ku cewa ba zan mai da hankali ga kome ba sai dai Yesu Kiristi wanda aka gicciye.
”Ba ko ɗaya daga cikin masu mulkin wannan zamani da ya fahimce ta, gama da a ce sun fahimce ta, da ba su gicciye Ubangiji mai ɗaukaka ba.
”Saboda haka sa’ad da kun taru ikon Ubangijinmu Yesu kuma yana nan, ni ma ina tare da ku.
”Ku kawar da tsohon yisti don ku zama kamar sabon curi da aka yi babu yisti yadda dai kuke. Gama an miƙa Kiristi Ɗan Ragon Bikin Ƙetarewarmu.
”duk da haka a gare mu dai akwai Allah ɗaya kaɗai, Uba, wanda dukan abubuwa suke daga gare shi, wanda kuma saboda shi ne muke rayuwa, kuma akwai Ubangiji ɗaya, Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa ne aka yi dukan abu, ta wurinsa ne kuma muke rayuwa.
”Saboda haka, ina gaya muku cewa ba wani mai magana da ikon Ruhun Allah da zai ce, “Yesu la’ananne ne,” haka kuma ba wanda zai ce, “Yesu Ubangiji ne,” sai wanda Ruhu Mai Tsarki yake bi da shi.
”To, ku jikin Kiristi ne, kowannenku kuwa gaɓarsa ne. A cikin ikkilisiya, da farko dai Allah ya zaɓa waɗansu ya naɗa su su zama manzanni, na biyu annabawa, na uku malamai, sa’an nan masu yin ayyukan banmamaki, sai masu baiwar warkarwa, da masu taimakon waɗansu, da masu baiwar gudanarwa, sa’an nan kuma masu magana da harsuna iri-iri.
”Gama abu farko mafi muhimmancin da na karɓo shi ne na ba ku cewa Kiristi ya mutu domin zunubanmu bisa ga Nassi, cewa an binne shi an kuma tashe shi a rana ta uku bisa ga Nassi, cewa ya bayyana ga Bitrus, sa’an nan ga Sha Biyun. Bayan haka, ya bayyana ga fiye da ɗari biyar daga cikin ’yan’uwa a lokaci guda. Yawancinsu kuwa suna nan da rai, ko da yake waɗansu sun riga sun yi barci.
”Amma tabbatacce, an tā da Kiristi daga matattu, nunan fari kuwa cikin waɗanda suka yi barci. Da yake mutuwa ta zo ta wurin mutum, haka tashin matattu ma ya zo ta wurin mutum. Kamar yadda duka suka mutu cikin Adamu, haka duka za su rayu cikin Kiristi. Sai dai kowa da lokacinsa. Kiristi ne nunan fari; sa’an nan sa’ad da ya dawo; za a tā da waɗanda suke nasa. Sa’an nan sai ƙarshen ta zo, sa’ad da zai miƙa wa Allah Uba mulki, bayan ya hallaka dukan sarauta, mulki da iko. Gama dole yă yi mulki har sai ya sa dukan abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa. Abokin gāba na ƙarshen da za a hallaka kuwa, shi ne mutuwa. Gama ya “sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.” To, da aka ce an sa “kome” a ƙarƙashinsa, a fili yake cewa ba a haɗa da Allah a ciki ba, shi wannan da ya sa kome a ƙarƙashin Kiristi. Sa’ad da ya yi haka, sa’an nan Ɗan kansa yă koma a ƙarƙashin shi wanda ya sa kome a ƙarƙashinsa, domin Allah yă zama kome da kome.
”Amma aka sa hankulansu suka dushe, gama har yă zuwa yau akwai lulluɓin nan a duk sa’ad da ake karatun tsohon alkawari. Ba a kawar da shi ba, sai a cikin Kiristi ne kaɗai ake kawar da shi.
”Ko da bishararmu a rufe take, tana a rufe ne ga waɗanda suke hallaka. Allahn zamanin nan ya makanta hankulan marasa ba da gaskiya, yadda har ba za su iya ganin hasken bishara ta ɗaukakar Kiristi ba, wanda yake kamannin Allah. Gama ba wa’azin kanmu muke yi ba, sai dai na Yesu Kiristi, a kan shi ne Ubangiji, mu kuma bayinku saboda Yesu. Domin shi Allah wanda ya ce, “Bari haske yă haskaka daga duhu,” ya sa haskensa ya haskaka a cikin zukatanmu, don yă ba mu hasken sanin ɗaukakar Allah a fuskar Kiristi.
”Gama dole dukanmu mu bayyana a gaban kujerar shari’ar Kiristi, domin kowannenmu yă karɓi ladan aikin da ya yi a wannan jiki, ko mai kyau ne ko marar kyau.
”Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon al’amari ya shuɗe, sabon ya zo!
”Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi kamar hadayar zunubi saboda mu, domin mu sami adalcin Allah ta wurinsa.
”Gama kun san alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi cewa ko da yake shi mawadaci ne, duk da haka, ya zama matalauci saboda ku, domin ta wurin talaucinsa, ku zama mawadata.
”An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne nake raye ba, Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina.
”Kiristi ya fanshe mu daga la’anar Doka ta wurin zama la’ana saboda mu, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda aka rataye a kan itace.”
”Amma da lokacin da aka tsara ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffe daga mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka, domin yă fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, saboda mu sami cikakken matsayin zaman ’ya’ya.
”Ina ta roƙo cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhun hikima da na ganewa, domin ku san shi da kyau. Ina kuma addu’a cewa zuciyarku tă waye don ku gane ko mene ne sa zuciyan nan da ya kira ku a kansa, ku kuma san darajar dukiyan nan wadda take ta mutanen Allah, wato, albarkunsa. Ina addu’a ku san girman ikon Allah wanda ya wuce misali, wanda yake namu. Ikon da yake aiki a cikinmu, ɗaya ne da ikon nan da ya tā da Kiristi daga matattu, ya kuma sa ya zauna a hannun damansa a cikin mulkin samaniya. Yanzu yana mulki a kan dukan masu sarauta, da masu iko, da masu ƙarfi, da kuma masu mulki. Yana mulkin kome a wannan duniya, zai kuma yi mulkin duniya mai zuwa. Allah ya sa kome a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma ba shi iko a kan kome don amfanin ikkilisiya. Kuma ikkilisiya ce jikinsa; ta kuma cika da Kiristi, wanda ya cika kome ta kowace hanya.
”Ku gini ne wanda manzanni da annabawa suke tushensa, Kiristi kuma shi ne dutse mafi muhimmanci na ginin. Ta wurinsa ne dukan ginin yake a haɗe, shi ne kuma yake sa ginin yă yi girma, yă zama haikali mai tsarki domin Ubangiji. Ku ma sashe ne na wannan ginin da Kiristi ya yi inda Allah yake zaune ta wurin Ruhunsa.
”Shi wannan da ya sauka ɗin, shi ne kuma ya hau zuwa can sama, kai, gaba da sammai, don mulkinsa yă cika duniya gaba ɗaya.)
”Ya kamata kullum ƙauna tă sa mu faɗa gaskiya. Ta haka za mu yi girma a kowace hanya, mu kuma zama kamar Kiristi, wanda yake kan dukan jiki. Shi ne ya haɗe jiki duka, ya kuma sa dukan gaɓoɓin jiki suna aiki daidai, yayinda kowace gaɓa take aikinta cikin ƙauna.
”Ku zama masu koyi da Allah, kamar ƙaunatattun ’ya’ya, ku kuma yi rayuwar ƙauna, kamar yadda Kiristi ya ƙaunace mu, har ya ba da kansa dominmu a matsayin sadaka mai ƙanshi da kuma hadaya ga Allah.
”gama mu gaɓoɓin jikinsa ne.
”A cikin dangantakarku da juna, ya kamata halayenku su zama kamar na Kiristi Yesu. Wanda, ko da yake cikin ainihin surar Allah yake, bai mai da daidaitakansa nan da Allah wani abin riƙewa kam-kam ba, amma ya mai da kansa ba kome ba, yana ɗaukan ainihin surar bawa, aka yi shi cikin siffar mutum. Aka kuma same shi a kamannin mutum, ya ƙasƙantar da kansa ya kuma zama mai biyayya wadda ta kai shi har mutuwa, mutuwar ma ta gicciye! Saboda haka Allah ya ɗaukaka shi zuwa mafificin wuri ya kuma ba shi sunan da ya fi dukan sunaye, don a sunan Yesu kowace gwiwa za tă durƙusa, a sama da a ƙasa da kuma a ƙarƙashin ƙasa, kowane harshe kuma yă furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne, don ɗaukakar Allah Uba.
”Ina so in san Kiristi da ikon tashinsa daga matattu da kuma zumuncin tarayya cikin shan wahalarsa, in kuma zama kamar sa a cikin mutuwarsa, yadda kuma ko ta yaya, in kai ga tashin nan daga matattu.
”Gama ya riga ya cece mu daga mulkin duhu ya kuma kawo mu cikin mulkin Ɗan da yake ƙauna, wanda ta wurinsa muka sami fansa da kuma gafarar zunubai. Kiristi shi ne surar da ake gani na Allah wanda ba a iya gani, ɗan fari a kan dukan halitta. Ta wurinsa aka halicci dukan abu, abubuwan da suke cikin sama da abubuwan da suke a duniya, waɗanda ake gani, da waɗanda ba a gani, ko kursiyoyi ko ikoki ko masu mulki ko hukumomi; an halicci dukan abu ta wurinsa da kuma dominsa ne. Ya kasance kafin dukan abu, kuma a cikinsa ne dukan abubuwa suke a harhaɗe. Shi ne kuma kan ikkilisiya, wadda take jikinsa. Shi ne mafari da kuma na farko da ya tashi daga matattu, domin a cikin kowane abu yă zama mafifici. Gama Allah ya ji daɗi yă sa dukan cikarsa ta kasance a cikin Kiristi, ta wurin Kiristi ne ya komar da kome zuwa ga kansa. Ya kawo salama ga abubuwan da suke ƙasa da abubuwan da suke sama, ta wurin jinin Kiristi da ya zubar a kan gicciye.
”Manufata ita ce a ƙarfafa su su kuma zama ɗaya a cikin ƙauna. Ina so su kasance da cikakken ƙarfin hali domin suna da cikakken fahimtar asirin Allah, wato, Kiristi kansa, a cikinsa ne aka ɓoye dukkan dukiya ta hikima da ta sani.
”Gama a cikin Kiristi cikin jiki dukkan cikar Allahntaka take tabbata, an kuma mai da ku cikakku a cikin Kiristi, wanda yake shi ne kai a kan kowane iko da kuma hukuma.
”Bayan ya ƙwace makaman ikoki da hukumomi, ya kunyata su a sarari, ya ci nasara a bisansu ta wurin gicciye.
”Da yake an tashe ku tare da Kiristi, sai ku sa zukatanku a kan abubuwan da suke sama, inda Kiristi yake zaune a hannun dama na Allah.
”Gama Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya tsakanin Allah da mutane, shi ne kuwa Kiristi Yesu, wanda ya ba da kansa fansa domin dukan mutane, shaidar da aka bayar a daidai lokaci.
”Ba shakka, asirin addini da girma yake. Ya bayyana cikin jiki, Ruhu ya nuna shi adali ne, mala’iku suka gan shi, aka yi wa’azinsa cikin al’ummai, aka gaskata shi a duniya, aka ɗauke shi sama cikin ɗaukaka.
”ka kiyaye wannan umarni ba tare da wani aibi ko abin zargi ba har yă bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda Allah zai kawo a daidai lokaci, Allah, mai albarka wanda yake kaɗai Mai Mulki, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji, wanda shi kaɗai ne marar mutuwa wanda kuma yake zaune cikin hasken da ba ya kusatuwa, wanda babu wanda ya taɓa gani ko zai iya gani. A gare shi girma da iko su tabbata har abada. Amin.
”A gaban Allah da kuma Kiristi Yesu, wanda zai yi wa masu rai da matattu shari’a, saboda kuma bayyanuwarsa da mulkinsa, ina ba ka umarni.
”yayinda muke sauraron begenmu mai albarka bayyanuwar ɗaukakar Allahnmu mai girma da kuma Mai Cetonmu, Yesu Kiristi,
”A dā Allah ya yi wa kakanni-kakanninmu magana ta bakin annabawa a lokuta dabam-dabam da kuma a hanyoyi iri-iri, amma a waɗannan kwanaki a ƙarshe ya yi magana da mu ta wurin Ɗansa, wanda ya naɗa magājin dukan abubuwa, wanda kuma ta wurinsa ya halicci duniya. Ɗan shi ne hasken ɗaukakar Allah, shi ne kuma ainihin kamanninsa, yana riƙe da dukan abubuwa ta wurin kalmarsa mai iko. Bayan ya yi tsarkakewa don zunubai, sai ya zauna a hannun daman Maɗaukaki a sama.
”Gama ga wane daga cikin mala’ikun Allah ya taɓa cewa, “Kai Ɗana ne; yau na zama Uba a gare ka”? Ko kuwa, “Zan zama Ubansa, shi kuma zai zama Ɗana”? Haka kuma, sa’ad da Allah ya kawo ɗan farinsa a duniya ya ce, “Bari dukan mala’ikun Allah su yi masa sujada.”
”Amma game da Ɗan ya ce, “Kursiyinka, ya Allah, zai kasance har abada abadin, adalci kuma zai zama sandan mulkinka. Ka ƙaunaci abin da yake daidai, ka kuma ƙi mugunta; saboda haka Allah, Allahnka, ya ɗora ka a bisan abokan zamanka, ta wurin shafan da ya yi maka da man farin ciki.” Ya kuma ce, “Tun da farko, ya Ubangiji, ka kafa tushen duniya, sammai kuma aikin hannuwanka ne. Su za su hallaka, amma kai kana nan; dukansu za su tsufa kamar riga. Za ka naɗe su kamar mayafi, kamar riga za su sauya. Amma kai ba za ka canja ba, shekarunka kuma ba za su taɓa ƙarewa ba.”
”Domin shi kansa ya sha wahala sa’ad da aka gwada shi, yana iya taimakon waɗanda ake yi wa gwaji.
”Saboda haka, ’yan’uwa tsarkaka, waɗanda suke da rabo a kiran nan na sama, ku kafa tunaninku a kan Yesu, manzo da kuma babban firist wanda muke shaidawa.
”Saboda haka, da yake muna da babban firist mai girma wanda ya ratsa sama, Yesu Ɗan Allah, bari mu riƙe bangaskiyan nan wadda muke shaidawa da ƙarfi. Gama babban firist da muke da shi ba marar juyayin kāsawarmu ba ne, amma muna da wanda aka gwada ta kowace hanya, kamar dai yadda akan yi mana, duk da haka bai yi zunubi ba.
”A lokacin da Yesu ya yi rayuwa a duniya, ya yi addu’o’i da roƙe-roƙe tare da kuka mai zafi da kuma hawaye ga wannan wanda yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa ji shi saboda tsananin bangirman da ya yi. Ko da yake shi ɗa ne, ya yi biyayya ta wurin shan wahala kuma da aka mai da shi cikakke, sai ya zama hanyar samun madawwamin ceto ga dukan waɗanda suke masa biyayya. Allah kuwa ya naɗa shi yă zama babban firist, bisa ga tsarin Melkizedek.
”amma Yesu ba zai mutu ba, don haka zai zama firist har abada. Saboda haka ya iya ba da ceto gaba ɗaya ga masu zuwa wurin Allah ta wurinsa, gama kullum a raye yake saboda yă yi roƙo dominsu. Irin wannan babban firist ne muke bukata, shi mai tsarki ne, marar aibi, mai tsabta, ba kamar mu masu zunubi ba sam. An ɗaukaka shi fiye da kome a sama. Ba ya bukata yă yi ta miƙa hadayu kowace rana saboda zunubansa, sa’an nan saboda zunuban mutane kamar sauran firistoci. Ya miƙa hadaya sau ɗaya tak, sa’ad da ya miƙa kansa. Gama doka takan naɗa babban firist a cikin mutane masu kāsawa; amma rantsuwar da ta zo bayan dokar, ta naɗa Ɗan, wanda aka mai da shi cikakke har abada.
”Abin da muke magana a nan shi ne, muna da irin wannan babban firist, wanda ya zauna a hannun dama na kursiyin Maɗaukaki a sama,
”Gama da a ce alkawari na fari ba shi da wani laifi, da ba sai an sāke neman wani ba. Amma Allah ya sami mutane da laifi ya ce, “Ina gaya muku lokaci yana zuwa, sa’ad da zan yi sabon alkawari da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda.
”Ta wurin kira wannan alkawari “sabo,” ya mai da na farin tsoho ke nan; abin da yake tsoho yana kuma daɗa tsufa, zai shuɗe nan ba da daɗewa ba.
”Sa’ad da Kiristi ya zo a matsayin babban firist na kyawawan abubuwan da suka riga suka kasance a nan, ya bi ta cikin tabanakul mafi girma da kuma mafi cikakke wanda ba mutum ne ya yi ba, wato, ba na wannan halitta ba. Bai shiga ta wurin jinin awaki da na maruƙa ba; amma ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak ta wurin jininsa, bayan ya samo madawwamiyar fansa.
”Saboda haka Kiristi shi ne matsakancin sabon alkawari, don waɗanda aka kira su sami madawwamin gādon da aka yi alkawari, yanzu da ya mutu a matsayin mai fansa don yă ’yantar da su daga zunuban da aka aikata a ƙarƙashin alkawari na farko. Sa’ad da wani ya yi alkawari game da gādonsa, dole a tabbatar da mutuwar wanda ya yi ta, domin alkawarin gādo yana aiki ne kawai bayan mai yinsa ya mutu, ba ya taɓa aiki yayinda mai yinsa yana da rai. Shi ya sa alkawari na farko bai fara aiki ba sai da aka zub da jini.
”Tabbatacce, doka ta bukaci a tsabtacce kusa kowane abu da jini, kuma in ba tare da zub da jini ba babu gafara.
”Gama Kiristi bai shiga wani wuri tsattsarka da mutum ya yi ba, wanda yake hoto ne kawai na gaskataccen, a’a sama kanta ya shiga, domin yă bayyana a gaban zatin Allah a yanzu saboda mu.
”haka aka miƙa Kiristi hadaya sau ɗaya domin yă ɗauke zunuban mutane masu yawa; zai kuma bayyana sau na biyu, ba don yă ɗauki zunubi ba, sai dai don yă kawo ceto ga waɗanda suke jiransa.
”Amma da Kiristi ya miƙa hadaya ɗaya ta dukan lokaci saboda zunubai, sai ya zauna a hannun dama na Allah.
”Saboda haka, ’yan’uwa, da yake muna da wannan tabbaci na shiga Wuri Mafi Tsarki ta wurin jinin Yesu, ta wurin sabuwa, rayayyiyar hanya kuma wadda aka buɗe mana ta labulen nan, wato, jikinsa, da yake kuma muna da babban firist mai mulkin gidan Allah,
”Bari mu kafa idanunmu a kan Yesu, tushe da kuma kammalar bangaskiyarmu, wanda ya jure kunyar gicciye da aka yi masa, domin ya san cewa daga baya zai yi farin ciki ya yi haka. Yanzu kuma yana zaune a hannun dama na kursiyin Allah. Ku lura da wannan wanda ya jure da irin hamayyan nan daga masu zunubi, don kada ku gaji, har ku fid da zuciya.
”Kun zo ga Yesu, mai yin sulhu na sabon alkawari, da kuma ga jinin da aka yayyafa wanda yake magana mafi kyau fiye da jinin Habila.
”Yesu Kiristi ba ya sākewa, shi ne a jiya, shi ne a yau, shi ne kuma har abada.
”Bari Allah na salama, wanda ta wurin jinin madawwamin alkawari ya tā da Ubangijinmu Yesu daga matattu, wannan Makiyayin tumaki mai girma, yă kintsa ku da kowane abu mai kyau domin aikata nufinsa, bari kuma yă aikata abin da zai gamshe shi cikinmu, ta wurin Yesu Kiristi, a gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada. Amin.
”’Yan’uwana, a matsayinmu cikin Ubangiji Yesu Kiristi maɗaukaki, kada ku nuna bambanci.
”Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi! Cikin jinƙansa mai girma ya ba mu sabuwar haihuwa cikin bege mai rai ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu, da kuma cikin gādon da ba zai taɓa lalacewa, ɓacewa ko koɗewa ba, ajiyayye a sama dominku, ku waɗanda ta wurin bangaskiya ake kiyayewa ta wurin ikon Allah har yă zuwa ceton da yake a shirye da za a bayyana a ƙarshen lokaci.
”sai dai an fanshe ku da jini mai daraja na Kiristi, ɗan rago marar aibi ko lahani. An zaɓe shi kafin halittar duniya, amma an bayyana shi a zamanin ƙarshe saboda ku. Ta gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya tā da shi daga matattu, aka kuma ɗaukaka shi, ta haka bari bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.
”Da kuka zo gare shi, rayayyen Dutse, da mutane suka ƙi amma Allah ya zaɓa, kuma mai daraja a gare shi ku ma, a matsayinku na duwatsu masu rai, ana gina ku ga zama gidan ruhaniya don ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, kuna miƙa hadayun ruhaniya, abin karɓa ga Allah ta wurin Yesu Kiristi. Gama a cikin Nassi an ce, “Ga shi, na kafa dutse a Sihiyona, zaɓaɓɓen dutse na kusurwar gini mai daraja, wanda kuma ya dogara gare shi ba zai taɓa kunyata ba.”
”A gare ku da kuka gaskata, wannan dutse mai daraja ne. Amma ga waɗanda ba su gaskata ba, “Dutsen da magina suka ƙi ya zama dutsen kusurwar gini, kuma, “Dutse ne da yake sa mutane tuntuɓe kuma fā ne da yake sa su fāɗi.” Sun yi tuntuɓe domin sun ƙi su yi biyayya da saƙon, wanda kuma yake abin da aka ƙaddara musu.
”Ga wannan ne aka kira ku, domin Kiristi ya sha wahala dominku, ya bar muku gurbin da ya kamata ku bi. “Bai taɓa yin laifi ba sam, ba a kuma sami ƙarya a bakinsa ba.” Sa’ad da suka zazzage shi, bai rama ba; sa’ad da ya sha wahala, bai yi barazana ba. A maimakon haka, ya miƙa kansa ga wanda yake shari’ar adalci. Shi kansa ya ɗauki zunubanmu a jikinsa a kan itace, domin mu mutu ga zunubai mu kuma rayu ga adalci; ta wurin raunukansa ne kuka sami warkarwa. Gama dā kuna kama da tumakin da suka ɓace, amma yanzu kun dawo ga Makiyayi da kuma Mai lura da rayukanku.
”Gama Kiristi ya mutu domin zunubi sau ɗaya tak, mai adalci saboda marasa adalci, don yă kawo ku ga Allah. An kashe shi a cikin jiki, amma an rayar da shi a Ruhu,
”ruwan nan kuwa kwatancin baftisma ne da yanzu ya cece ku ku ma, ba kawar da dauda daga jiki ba, sai dai yin alkawari na lamiri mai kyau ga Allah. Ya cece ku ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu, wanda ya tafi sama, yana kuma a hannun dama na Allah, mala’iku, mulkoki da kuma masu iko suna masa biyayya.
”Siman Bitrus, bawa da kuma manzon Yesu Kiristi, Zuwa ga waɗanda ta wurin adalcin Allahnmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi sun sami bangaskiya mai daraja irin tamu. Alheri da salama su zama naku a yalwace ta wurin sanin Allah da Yesu Ubangijinmu.
”za ku sami kyakkyawar marabta cikin madawwamin mulkin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi.
”Ba mu bi tatsuniyoyin da aka ƙaga da wayo sa’ad da muka gaya muku game da ikon Ubangijinmu Yesu Kiristi da zuwansa ba, sai dai mu shaidu ne na ɗaukakarsa mai girma da muka gani da ido. Gama ya sami girma da ɗaukaka daga Allah Uba sa’ad da murya ta zo masa daga Mafificiyar Ɗaukaka cewa, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; da shi nake jin daɗi ƙwarai.”
”Sai dai ku yi girma cikin alheri da sanin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi. A gare shi ɗaukaka ta tabbata yanzu da har abada! Amin.
”’Ya’yana ƙaunatattu, ina rubuta muku wannan ne don kada ku yi zunubi. Amma in wani ya yi zunubi, muna da wani wanda yake magana da Uba don taimakonmu, wato, Yesu Kiristi, Mai Adalci. Shi ne hadayar kafara saboda zunubanmu, kuma ba don namu kaɗai ba amma har ma da zunuban duniya duka.
”Sai dai kun san cewa Kiristi ya bayyana ne domin yă ɗauke zunubanmu. A cikinsa kuwa babu zunubi.
”Mun san cewa Ɗan Allah ya zo duniya, ya kuma ba mu ganewa domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna cikinsa, shi da yake Allah na gaskiya wato, cikin Ɗansa Yesu Kiristi. Shi ne Allah na gaskiya da kuma rai na har abada.
”Gare shi kuma, shi da yake kaɗai Allah Mai Cetonmu, ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu, bari ɗaukaka, daraja, iko da mulki, su tabbata a gare shi, tun farkon zamanai, yanzu, da har abada abadin! Amin.
”Daga Yohanna, Zuwa ga ikkilisiyoyi bakwai da suke a lardin Asiya. Alheri da salama gare ku daga shi wanda yake a yanzu, wanda yake a dā, da kuma wanda zai zo, da kuma daga ruhohi bakwai da suke a gaban kursiyinsa, da kuma daga Yesu Kiristi, wanda yake amintaccen shaida, ɗan farin daga tashin matattu, da kuma mai mulkin sarakunan duniya. Gare shi wanda yake ƙaunarmu wanda kuma ya ’yantar da mu daga zunubanmu ta wurin jininsa, ya kuma mai da mu masarauta da firistoci don mu yi wa Allahnsa da Ubansa hidima, a gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin! Amin. “Duba, yana zuwa cikin gizagizai, kowane ido kuwa zai gan shi, har da waɗanda suka soke shi”; dukan mutanen duniya kuwa “za su yi makoki dominsa.” Bari yă zama haka nan! Amin.
”“Ni ne Alfa da kuma Omega,” in ji Ubangiji Allah, “wanda yake a yanzu, wanda yake a dā, da kuma wanda zai zo, Maɗaukaki.”
”wadda ta ce, ‹“Rubuta a cikin naɗaɗɗen littafi abin da ka gani ka kuma aika ta zuwa ga ikkilisiyoyi bakwai, zuwa Afisa, Simirna, Fergamum, Tiyatira, Sardis, Filadelfiya, da kuma Lawodiseya.”›
”Sai na juya don in ga muryar da take magana da ni. Da na juya kuwa sai na ga alkukan fitilu bakwai na zinariya. A tsakiyar alkukan kuwa akwai wani “kama da ɗan mutum,” saye da rigar da ya kai har ƙafafunsa da kuma ɗamarar zinariya daure a ƙirjinsa. Kansa da kuma gashin fari ne fat kamar ulu, fari kamar dusar ƙanƙara, idanunsa kuwa kamar harshen wuta. Sawunsa sun yi kamar tagullar da take haske cikin matoya, muryarsa kuma ta yi kamar muryar ruwaye masu gudu. A hannunsa na dama ya riƙe taurari bakwai, daga bakinsa kuwa takobi mai kaifi biyu ya fito. Fuskarsa ta yi kamar rana mai haskakawa da dukan haskenta.
”Sa’ad da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa sai ka ce matacce. Sai ya ɗibiya hannunsa na dama a kaina ya ce, ‹“Kada ka ji tsoro. Ni ne Farko da kuma Ƙarshe.› ‹Ni ne Rayayye, dā na mutu, ga shi kuwa ina a raye har abada abadin! Ina kuma riƙe da mabuɗan mutuwa da na Hades.›
”Sai ɗaya daga cikin dattawan ya ce mini, “Kada ka yi kuka! Duba, Zakin kabilar Yahuda, da kuma Tushen Dawuda ya ci nasara. Ya iya buɗe naɗaɗɗen littafin da hatimansa bakwai.” Sa’an nan na ga Ɗan Rago, yana kamar an yanka, tsaye a tsakiyar kursiyin, halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan an sun kewaye shi. Yana da ƙahoni bakwai da idanu bakwai, waɗanda suke ruhohi bakwai na Allah da aka aika cikin dukan duniya.
”Suka rera sabuwar waƙa, “Ka cancanci ka karɓi naɗaɗɗen littafin ka kuma buɗe hatimansa, domin an kashe ka, da jininka kuma ka sayi mutane wa Allah, daga kowace kabila da harshe da mutane da kuma al’umma.
”Sai na duba na kuma ji muryar mala’iku masu yawa, yawansu kuwa ya kai dubu dubbai, da kuma dubu goma sau dubu goma. Suka kewaye kursiyin da halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan. Da babbar murya suka rera, “Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka kashe, don yă sami iko da wadata da hikima da ƙarfi da girma da ɗaukaka da kuma yabo!” Sa’an nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa, “Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon yabo da girma da ɗaukaka da iko, sun tabbata har abada abadin!” Sai halittu huɗun nan masu rai suka ce, “Amin”, dattawan kuma suka fāɗi suka yi sujada.
”Bayan wannan sai na duba, can a gabana kuwa ga wani taro mai girma, wanda ba mai iya ƙirgawa, daga kowace al’umma, kabila, mutane da kuma harshe, suna tsaye a gaban kursiyin da kuma gaban Ɗan Ragon nan. Suna saye da fararen tufafi suna kuma riƙe da rassan dabino a hannuwansu. Suka tā da murya da ƙarfi suna cewa, “Ceto na Allahnmu ne, wanda yake zaune a bisan kursiyi, da kuma na Ɗan Ragon.” Dukan mala’iku suna tsaye kewaye da kursiyin da kuma kewaye da dattawan tare da halittu huɗun nan masu rai. Suka fāɗi da fuskokinsu ƙasa a gaban kursiyin suka kuma yi wa Allah sujada,
”Gama Ɗan Ragon da yake a tsakiyar kursiyin zai zama makiyayinsu; ‘zai bi da su zuwa ga maɓulɓular ruwan rai.’ ‘Allah kuwa zai share dukan hawaye daga idanunsu.’ ”
”Mala’ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji muryoyi masu ƙarfi a sama da suka ce, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Kiristinsa, zai kuwa yi mulki har abada abadin.”
”Sun ci nasara a kansa ta wurin jinin Ɗan Ragon da ta wurin kalmar shaidarsu; ba su ƙaunaci rayukansu sosai har da za su ja da baya daga mutuwa.
”Sai na duba, can a gabana kuwa ga Ɗan Rago, tsaye a kan Dutsen Sihiyona, tare da shi akwai kuma mutane 144,000 waɗanda suke da sunansa da sunan Ubansa a rubuce a goshinsu.
”Na duba, can gabana kuwa ga farin girgije, zaune kuma a kan girgijen kuwa ga wani da ya yi kamar “ɗan mutum” tare da rawanin zinariya a kansa da kuma lauje mai kaifi a hannunsa.
”Za su yi yaƙi da Ɗan Ragon, sai dai Ɗan Ragon zai ci nasara a bisansu domin shi ne Ubangijin iyayengiji, Sarkin sarakuna, tare da shi kuwa kirayayunsa, zaɓaɓɓunsa da kuma amintattu masu binsa za su kasance.”
”Sai na ga sama a buɗe can kuwa a gabana ga farin doki, sunan mahayinsa Mai Aminci da Mai Gaskiya ne. Da adalci yake shari’a yake kuma yaƙi. Idanunsa sun yi kamar harshen wuta, a kansa kuwa akwai rawani masu yawa. Yana da suna rubuce a kansa da babu wanda ya sani sai dai shi. Yana saye da rigar da aka tsoma a jini, sunansa kuwa Kalman Allah ne. Mayaƙan sama suna biye da shi, suna hawan fararen dawakai, saye da fararen tufafi masu tsabta na lallausan lilin. Daga bakinsa takobi mai kaifi ya fito. Da shi zai karkashe al’ummai. “Zai yi mulkinsu da sandan sarautar ƙarfe.” Yana tattake wurin matsin ruwan inabi na fushin Allah Maɗaukaki. A rigarsa da kuma a cinyarsa akwai wannan suna a rubuce, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji.
”Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. “Ina yin kome sabo!” Sai ya ce, “Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma.” Ya ce mini, “An gama. Ni ne Alfa da kuma Omega, na Farko da kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi abin sha kyauta daga maɓulɓular ruwan rai.
”Ba za a ƙara samun la’ana ba. Kursiyin Allah da na Ɗan Ragon zai kasance a cikin birnin, bayinsa kuma za su yi masa hidima.
”‹“Ga shi, ina zuwa da wuri! Ladan da zan bayar yana tare da ni, kuma zan ba wa kowa gwargwadon abin da ya yi.› ‹Ni ne Alfa da kuma Omega, na Fari da kuma na Baya, Farko da kuma Ƙarshe.›
”‹“Ni, Yesu, na aiko mala’ikana ya ba ka wannan shaida saboda ikkilisiyoyi. Ni ne Tushe da kuma Zuriyar Dawuda, da kuma Tauraron Asubahi mai haske.”›
”Shi da ya shaida waɗannan abubuwa ya ce, ‹“I, ina zuwa da wuri.”› Amin. Zo, Ubangiji Yesu! Alherin Ubangiji Yesu yă kasance tare da mutanen Allah. Amin.
”