14 – Zubar da ciki
Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Zubar da ciki.
Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Zubar da ciki.
Suka miƙa ’ya’yansu maza hadaya ’yan matansu kuma ga aljanu. Suka zub da jini marar laifi, jinin ’ya’yansu maza da mata, waɗanda suka miƙa hadaya ga gumakan Kan’ana, ƙasar kuwa ta ƙazantu ta wurin jininsu.
”“ ‘Kika kuma kwashe ’ya’yanki maza da mata waɗanda kin haifa mini kika miƙa su kamar abinci ga gumakanki. Karuwancinki bai isa ba ne? Kin kashe ’ya’yana kika kuma miƙa su ga gumaka. Cikin dukan ayyukan banƙyamarki da karuwancinki ba ki tuna da kwanakin ƙuruciyarki ba, sa’ad da kike tsirara tik, kina birgima cikin jininki.
”Gama ka halicci ciki-cikina; ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata. Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki; ayyukanka suna da banmamaki, na san da haka sosai.
”Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa. Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum. Miji da mace ya halicce su.
”“Duk wanda ya zub da jinin mutum, ta hannun mutum za a zub da jininsa; gama a cikin siffar Allah ne, Allah ya yi mutum.
”“Keɓe mini kowane ɗan fari. Ɗan fari wanda ya fara buɗe mahaifa a cikin Isra’ilawa nawa ne, ko na mutum ko na dabba.”
”Ba za ka yi kisankai ba.
”“Duk wanda ya bugi mutum har ya kashe shi, lalle a kashe shi.
”“Idan mutum biyu suna faɗa, har suka yi wa mace mai ciki rauni, har ya sa ta yi ɓari, amma wani lahani bai same ta ba, za a ci wa wanda ya yi mata raunin tara bisa ga yadda mijinta ya yanka za a biya, in dai abin da ya yanka ya yi daidai da abin da alƙalai suka tsara. Amma in akwai rauni mai tsanani, sai a ɗauki rai a maimakon rai,
”“Kada ku kāsa yin adalci ga matalauci a wurin shari’a. Ku yi nesa da ƙage. Kada ku kashe marar laifi tare da mai adalci, gama ba zan bar mugun yă tafi haka kawai ba.
”Gama ran halitta yana a cikin jinin, kuma na ba da shi gare ku don kafara a kan bagade, jini ne yake kafara saboda ran mutum.
”“ ‘Kada ku ba da wani daga cikin ’ya’yanku don a yi hadaya wa Molek, gama ba za ku ƙasƙantar da sunan Allahnku ba. Ni ne Ubangiji.
”Ubangiji ya ce wa Musa, “Faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘Duk wani mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikin Isra’ila da ya miƙa wani daga cikin ’ya’yansa wa Molek, dole sa kashe shi. Mutanen ƙasar za su jajjefe shi. Zan yi gāba da wannan mutum, zan kuma raba shi da mutanensa; gama ta wurin miƙa ’ya’yansa ga Molek, ya ƙazantar da wuri mai tsarkina, ya kuma ƙazantar da sunana mai tsarki. In mutanen ƙasar suka kau da idanunsu sa’ad da wannan mutum ya miƙa ’ya’yansa ga Molek, suka kāsa kashe shi, zan yi gāba da wannan mutum da iyalinsa, zan raba shi da kuma duk waɗanda suka bi shi cikin karuwanci ga Molek daga mutanensu.
”“ ‘Duk wanda ya kashe mutum, dole a kashe shi.
”“ ‘Kowa da ya kashe wani, za a kashe shi a matsayin mai kisankai, bisa ga shaidar shaidu. Amma kada a kashe wani bisa ga shaidar mutum ɗaya. “ ‘Kada a karɓi fansa don ran wanda ya yi kisankai, wanda ya cancanci mutuwa. Lalle ne a kashe shi.
”“ ‘Kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zama a ciki. Zub da jini yakan ƙazantar da ƙasa, ba a kuma iya yin kafara saboda wannan ƙasa da aka zub da jini, sai dai ta wurin jinin mutumin da ya zub da jinin.
”Kada ka yi kisankai.
”Ba za ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada a hanyar da suke yi ba, gama a cikin yin sujada wa allolinsu, sun yi dukan abubuwan banƙyaman da Ubangiji yake ƙi. Har ma sukan ƙone ’ya’yansu maza da mata a wuta a matsayin hadayu.
”Kada a sami wani a cikinku da ya miƙa ɗansa, ko ’yarsa a wuta, ko a sami mai duba, ko mai maita, ko mai fassara gaibi, ko mai sihiri,
”“La’ananne ne mutumin da ya karɓi cin hanci don yă kashe marar laifi.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!” “La’ananne ne mutumin da bai yi na’am da kalmomin wannan doka ta wurin aikata su ba.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
”A wannan rana na kira bisa sama da ƙasa a matsayin shaidu a kanku, cewa na sa a gabanku rai da mutuwa, albarku da la’anoni. Yanzu sai ku zaɓi rai, saboda ku da ’ya’yanku ku rayu
”Ya yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila har ya miƙa ɗansa hadaya a wuta, yana bin hanyoyin banƙyama na al’ummai da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa.
”Suka miƙa ’ya’yansu maza da mata hadaya ta wuta. Suka yi duba, suka yi sihiri suka kuma ba da kansu ga mugunta a gaban Ubangiji; suka sa ya yi fushi.
”Awwiyawa suka ƙera Nibhaz da Tartak, Sefarfayawa kuwa suka ƙone ’ya’yansu a wuta a matsayi hadayu ga Adrammelek da Anammelek allolin Sefarfayim.
”Ya miƙa ɗansa hadaya ta ƙonawa, ya yi sihiri da tsubu, ya tuntuɓi masu duba da masu ruhohi. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, ya sa Ubangiji ya yi fushi.
”Ya ƙone hadayu a Kwarin Ben Hinnom, ya kuma miƙa ’ya’yansa maza a cikin wuta, yana bin hanyoyi banƙyama na al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa.
”Ya miƙa ’ya’yansa maza hadaya a wuta cikin Kwarin Ben Hinnom, ya yi bokanci, ya yi duba, ya kuma yi maitanci, ya nemi shawarar mabiya da masu ruhohi. Ya yi abin da yake mugu ƙwarai a gaban Ubangiji, yana tsokanarsa yă yi fushi.
”“Da hannuwanka ka ƙera ni, kai ka halicce ni. Yanzu kuma kai za ka juya ka hallaka ni? Ka tuna cewa ka mulmula ni kamar yumɓu. Yanzu za ka mai da ni in zama ƙura kuma? Ba kai ka zuba ni kamar madara ba, na daskare kamar cuku. Ka rufe ni da tsoka da fata, ka harhaɗa ni da ƙasusuwa da jijiyoyi?
”domin na ceci matalauta waɗanda suka nemi taimako, da marasa mahaifi waɗanda ba su da wanda zai taimake su.
”Shi wanda ya yi ni a cikin uwata ba shi ne ya yi su ba? Ba shi ne ya yi mu a cikin uwayenmu ba?
”Kakan ji, ya Ubangiji sha’awar mai shan wahala; kakan ƙarfafa su, ka kuma saurari kukansu, kana kāre marayu da waɗanda aka danne, domin mutum, wanda yake na duniya kada ƙara haddasa wata razana.
”Duk da haka ka fitar da ni daga ciki; ka sa na dogara gare ka, ko ma a ƙirjin mahaifiyata. Daga haihuwa an jefa ni a kanka; daga cikin mahaifiyata kai ne Allahna.
”Ka kuɓutar da ni daga masu aikata mugunta ka kuma cece ni daga masu kisa. Duba yadda suka kwanta suna jirana! Mugaye suna ƙulle-ƙullen gāba da ni ba saboda wani dalili ko na yi wa wani zunubi ba, ya Ubangiji. Ban yi wani laifi ba, duk da haka suna a shirye su fāɗa mini. Tashi ka taimake ni; dubi halin da nake ciki!
”Uba ga marayu, mai kāre gwauraye, shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki.
”Daga haihuwa na dogara gare ka; kai ka kawo ni daga cikin mahaifiyata. Kullayaumi zan yabe ka.
”Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu; ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya. Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata; ku kuɓutar da su daga hannun mugaye. “Ba su san kome ba, ba su fahimci kome ba. Suna yawo cikin duhu; an girgiza dukan tussan duniya.
”Suna kashe gwauraye da kuma baƙi; suna kisan marayu. Suna ce, “ Ubangiji ba ya gani; Allah na Yaƙub bai kula ba.” Ku mai da hankali, ku marasa azanci a cikin mutane; ku wawaye, yaushe za ku zama masu hikima?
”Zai yiwu kursiyin da ya cika da lalaci yă haɗa kai da kai, wanda yake kawo azaba ta wurin abin da ya zartar? Sun yi ƙungiya tare a kan mai adalci suka yanke wa marar laifi hukuncin mutuwa. Amma Ubangiji ya zama kagarata, Allahna kuma dutsen da nake samun mafaka. Zai sāka musu saboda zunubansu yă kuma hallaka su saboda muguntarsu; Ubangiji Allahnmu zai hallaka su.
”Suka miƙa ’ya’yansu maza hadaya ’yan matansu kuma ga aljanu. Suka zub da jini marar laifi, jinin ’ya’yansu maza da mata, waɗanda suka miƙa hadaya ga gumakan Kan’ana, ƙasar kuwa ta ƙazantu ta wurin jininsu. Suka ƙazantar da kansu ta wurin abin da suka yi; ta wurin ayyukansu suka yi karuwanci. Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da mutanensa ya ji ƙyamar gādonsa.
”Hannuwanka ne suka yi suka kuma siffanta ni; ka ba ni ganewa don in koyi umarnanka. Bari waɗanda suke tsoronka su yi farin ciki sa’ad da suke gan ni, gama na sa zuciyata a maganarka.
”’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji, yara lada ne daga gare shi.
”Gama ka halicci ciki-cikina; ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata. Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki; ayyukanka suna da banmamaki, na san da haka sosai. Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba sa’ad da aka yi ni asirce. Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya. Idanunka sun ga jikina marar fasali; dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka kafin ɗayansu yă kasance.
”Gama yana ƙarfafa ƙyamaren ƙofofinki yana kuma albarkace mutanenki a cikinki.
”In suka ce, “Zo mu tafi; mu yi kwanton ɓauna, mu nemi wani mu kashe, mu fāɗa wa marasa laifi; mu haɗiye su da rai gaba ɗaya kamar kabari, kamar waɗanda suke gangarawa zuwa rami;
”Saboda haka masifa za tă fāɗa farat ɗaya; za a hallaka shi nan da nan, ba makawa. Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi, abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi, duban reni, harshe mai ƙarya, hannuwa masu zub da jinin marar laifi,
”Ka kuɓutar da waɗanda ake ja zuwa inda za a kashe su; ka riƙe waɗanda suke tangaɗi zuwa wajen yanka. In kuka ce, “Ai, ba mu san wani abu a kai wannan ba,” shi da yake awon ba shi da zuciyar ganewa ne? Shi da yake tsare ranka bai sani ba ne? Ba zai sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya aikata ba?
”Mutumin da laifin kisa ya yi ta damunsa zai zama mai gudu don tsoro har mutuwa; kada wani ya taimake shi.
”Kamar yadda ba ka san hanyar iska ba, ko yadda aka siffanta jiki a cikin mahaifiya, haka ba za ka fahimci aikin Allah Mahaliccin dukan abubuwa ba.
”Sa’ad da kuka ɗaga hannuwanku wajen yin addu’a, zan ɓoye fuskata daga gare ku; ko da kun miƙa addu’o’i masu yawa, ba zan kasa kunne ba. Hannuwanku sun cika da jini! Ku yi wanka ku kuma tsabtacce kanku. Ku kawar da mugayen ayyukanku daga gabana; Ku daina aikata mugunta. Ku koyi yin nagarta; ku nemi adalci. Ku ƙarfafa waɗanda aka zalunta. Ku ba wa marayu hakkinsu, ku taimaki gwauruwa. Ubangiji ya ce, “Yanzu fa ku zo, bari mu dubi batun nan tare, Ko da zunubanku sun yi ja kamar garura, za su zama fari kamar ƙanƙara; ko da sun yi ja kamar mulufi, za su zama kamar ulu.
”Kaiton waɗanda suke ce da mugunta nagarta nagarta kuma mugunta, waɗanda suke mai da duhu haske haske kuma duhu, waɗanda suke mai da ɗaci zaƙi zaƙi kuma ɗaci.
”Duba, Ubangiji yana fitowa daga mazauninsa don yă hukunta mutanen duniya saboda zunubansu. Duniya za tă bayyana zub da jinin da aka yi a kanta; ba za tă ƙara ɓoye waɗanda aka kashe a cikinta ba.
”Ga abin da Ubangiji yana cewa, shi wanda ya yi ka, wanda ya siffanta ka a cikin mahaifa, wanda kuma zai taimake ka. Kada ka ji tsoro, ya Yaƙub, bawana, Yeshurun, wanda na zaɓa.
”“Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansarka, wanda ya yi ka a cikin mahaifa. “Ni ne Ubangiji, wanda ya yi dukan abubuwa, wanda ya shimfiɗa sammai ya kuma kafa harsashen duniya da kansa,
”“Ku kasa kunne gare ni, ya ku gidan Yaƙub, dukanku waɗanda kuka rage na gidan Isra’ila, ku da na lura da ku tun da aka yi cikinku, na kuma riƙe ku tun haihuwarku.
”Ku kasa kunne gare ni, ku tsibirai; ku ji wannan, ku al’ummai masu nesa. Kafin a haife Ni Ubangiji ya kira ni; tun daga haihuwata ya ambaci sunana.
”Yanzu fa Ubangiji ya ce ya siffanta ni a cikin mahaifa don in zama bawansa don in dawo da Yaƙub gare shi in kuma tattara Isra’ila gare shi, gama an girmama ni a gaban Ubangiji Allahna kuma ne ƙarfina
”“Yana yiwuwa mahaifiya ta manta da jariri a ƙirjinta ta kuma kāsa nuna tausayi ga yaron da ta haifa? Mai yiwuwa ta manta, amma ba zan taɓa manta da ke ba! Duba, na zāna ki a tafin hannuwana; katangarki kullum suna a gabana.
”Zan kai mace har haihuwa in kuma sa ta kāsa haihu?” In ji Ubangiji. “Zan rufe mahaihuwa sa’ad da lokacin haihuwa ya yi?” In ji Allahnku.
”Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Kafin in siffanta ka a cikin ciki na san ka, kafin a haife ka, na keɓe ka; na naɗa ka ka zama annabi ga al’ummai.”
”A rigunanku mutane kan sami jinin matalauta marasa laifi, ko da yake ba ku kama su suna fasawa su shiga ba. Duk da haka kuna cewa, ‘Ba ni da laifi; ba ya fushi da ni.’ Amma zan zartar da hukunci a kanku domin kun ce, ‘Ban yi zunubi ba.’
”Sun gida masujadan Tofet a Kwarin Ben Hinnom don miƙa ’ya’yansu maza da mata a wuta, abin da ban yi umarni ba, ba kuwa yi tunaninsa ba.
”Gama sun yashe ni suka kuma mai da wannan wuri ya zama na baƙin alloli; sun ƙone hadayu a cikinsa wa allolin da ko su ko kakanninsu ko sarakunan Yahuda ba su taɓa sani ba, suka kuma cika wannan wuri da jini marasa laifi. Suka gina masujadai na kan tudu na Ba’al don su ƙona ’ya’yansu maza a cikin wuta a matsayin hadaya ga Ba’al abin da ban umarta ba, ban ambata ba, bai kuma zo mini ba. Saboda haka ku lura, kwanaki suna zuwa, in ji Ubangiji, sa’ad da mutane ba za su ƙara ce da wannan wuri Tofet ko Kwarin Ben Hinnom ba, amma za su ce da shi Kwarin Kisa. “ ‘A wannan wuri zan lalace dabarun Yahuda da na Urushalima. Zan sa a kashe su da takobi a gaban abokan gābansu, a hannuwan waɗanda suke neman ransu, zan kuma ba da gawawwakinsu su zama abinci ga tsuntsayen sararin sama da kuma namun jeji.
”Gama bai kashe ni a cikin ciki ba, da ma ya sa cikin mahaifiyata ya zama kabarina, cikinta ya fadada har abada.
”“Amma idanunka da zuciyarka sun kahu kawai a kan ƙazamar riba, da a kan zub da jinin marar laifi da kuma a kan danniya da zalunci.”
”Ga abin da Ubangiji yana cewa, “An ji murya daga Rama, makoki da kuka mai zafi, Rahila tana kuka domin ’ya’yanta ta kuma ƙi a ta’azantar da ita domin ’ya’yanta ba su.”
”Sun gina masujadai kan tudu wa Ba’al a Kwarin Ben Hinnom don su miƙa ’ya’yansu maza da mata hadaya ga Molek, ko da yake ban taɓa umarce su ba, bai kuma zo mini cewa su yi abin banƙyama irin wannan ba ta haka suka sa Yahuda ya yi zunubi.
”“ ‘Kika kuma kwashe ’ya’yanki maza da mata waɗanda kin haifa mini kika miƙa su kamar abinci ga gumakanki. Karuwancinki bai isa ba ne? Kin kashe ’ya’yana kika kuma miƙa su ga gumaka. Cikin dukan ayyukan banƙyamarki da karuwancinki ba ki tuna da kwanakin ƙuruciyarki ba, sa’ad da kike tsirara tik, kina birgima cikin jininki. “ ‘Kaito! Kaitonki, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Bugu da ƙari a kan dukan waɗansu muguntarki,
”Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kin zubar da dukiyarki kika bayyana tsiraicinki cikin fasikancinki da kwartayenki, kuma saboda dukan gumakan banƙyamarki, kuma saboda kin ba su jinin ’ya’yansu, saboda haka zan tattara dukan kwartayenki, waɗanda kike jin daɗinsu, waɗanda kike ƙauna da waɗanda kike ƙi. Zan tattara su gāba da ke daga dukan kewaye zan kuma tuɓe ki a gabansu, za su kuwa ga dukan tsiraicinki. Zan hukunta ki da hukuncin matan da suke zina da kuma waɗanda suke zub da jini; zan kawo hakkin jini na fushina da kuma fushin kishina.
”Gama kowane mai rai nawa ne, mahaifi da ɗa, duk nawa ne. Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu.
”Sa’ad da kuka miƙa kyautai naku, hadayar ’ya’yanku maza a wuta, kuna cin gaba da ƙazantar da kanku da duka gumakanku har wa yau. Zan bari ku nemi shawarata, ya gidan Isra’ila? Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, ba zan bari ku nemi shawarata ba.
”gama sun yi zina kuma jinin yana a hannuwansu. Sun yi zina da gumakansu; har suka miƙa ’ya’yansu da suka haifa mini, su zama musu abinci. Sun kuma yi mini wannan. A lokaci guda sun ƙazantar da wuri mai tsarkina suka ɓata Asabbataina. A ranar da suka miƙa ’ya’yansu ga gumakansu, sai suka shiga wuri mai tsarkina suka kuma ƙazantar da shi. Abin da suka yi a gidana ke nan.
”Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Ammon, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba. Don ya tsaga cikin matan Gileyad masu juna biyu don kawai yă ƙwace ƙasar.
”Da Hiridus ya gane cewa Masanan nan sun yi masa wayo, sai ya husata ƙwarai, ya yi umarni cewa a karkashe dukan ’yan yara maza da suke a Betlehem da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, bisa ga lokacin da ya sami labarin daga Masanan nan.
”‹“Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā cewa, ‘Kada ka yi kisankai;›‹kuma duk wanda ya yi kisankai za a hukunta shi.’›
”‹Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta.›
”‹Duk kuma wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan a cikin sunana ya karɓe ni ne.›
”‹In hannunka ko ƙafarka yana sa ka zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da hannu ko ƙafa ɗaya da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu da a jefar da kai cikin madawwamiyar wuta da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu.› ‹In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da ido ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta da idanunka biyu.› ‹“Ku lura, kada ku rena ɗaya daga cikin waɗannan ƙanana. Gama ina faɗa muku mala’ikunsu a sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin sama.›
”‹Haka ma Ubanku da yake cikin sama ba ya so ko ɗaya daga cikin ƙananan nan yă ɓace.›
”Yesu ya ce, ‹“Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin sama na irin waɗannan ne.”›
”‹Gama daga ciki, daga zuciyar mutane, mugayen tunani suke fitowa, fasikanci, sata, kisankai, zina,›
”‹Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, kada ka cuci wani, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’›‹”›
”gama zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba kuwa zai taɓa shan ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun haihuwa.
”Da Elizabet ta ji gaisuwar Maryamu, sai jaririn da yake a cikinta ya yi motsi. Elizabet kuma ta cika da Ruhu Mai Tsarki. Sai ta ɗaga murya da ƙarfi ta ce, “Ke mai albarka ce a cikin mata. Mai albarka ne kuma ɗan da za ki haifa! Me ya sa na sami wannan tagomashi har da mahaifiyar Ubangijina za tă zo wurina? Da jin gaisuwarki, sai jaririn da yake cikina ya yi motsi don murna.
”(yadda yake a rubuce a Dokar Ubangiji cewa, “Kowane ɗan fari, za a keɓe shi ga Ubangiji”),
”‹Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”›
”‹Me ya sa ba kwa gane da maganata? Don ba kwa iya jin abin da nake faɗi.› ‹Ku na ubanku ne, Iblis, kuna kuwa so ku aikata abin da ubanku yake so. Shi mai kisankai ne tun farko. Ba ruwansa da gaskiya, gama gaskiya ba ta cikinsa. Yayinda yake ƙarya, yana yin halinsa ne, gama shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.› ‹Amma domin ina faɗin gaskiya, ba kwa gaskata!›
”‹Macen da za tă haihu takan yi naƙuda domin lokacinta ya yi; amma sa’ad da ta haihu, sai ta manta da wahalar domin farin ciki an haifi jariri a duniya.›
”Da yake ba su yi tunani cewa ya dace su riƙe sanin Allah da suke da shi ba, sai ya yashe su ga tunanin banza da wofi, su aikata abin da bai kamata a yi ba. Sun cika da kowace irin ƙeta, mugunta, kwaɗayi, da tunanin banza da wofi. Suka kuma cika da kishi, kisankai, faɗa, ruɗu, da kuma riƙo a zuci. Su masu gulma ne, da masu ɓata suna, masu ƙin Allah, masu rashin kunya, masu girman kai, masu rigima; sukan ƙaga hanyoyin yin mugunta; suna rashin biyayya ga iyayensu; su marasa hankali ne, marasa bangaskiya, marasa ƙauna, marasa tausayi. Ko da yake sun san dokar adalcin Allah cewa masu aikata irin waɗannan abubuwa sun cancanci mutuwa, duk da haka ba cin gaba da aikata waɗannan abubuwa kaɗai suke yi ba, har ma suna goyon bayan masu yinsu.
”Kada hakkin kowa yă zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan. Umarnan nan, “Kada ka yi zina.” “Kada ka yi kisankai.” “Kada ka yi sata.” “Kada kuma ka yi ƙyashi.” Da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.” Ƙauna ba ta cutar da maƙwabci. Saboda haka ƙauna cika Doka ce.
”Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne;
”Amma sa’ad da Allah, wanda ya keɓe ni daga mahaifa ya kira ni ta wurin alherinsa, ya kuma gamshe shi yă bayyana Ɗansa a cikina, domin in yi wa’azinsa cikin Al’ummai. Ban nemi shawarar wani mutum ba.
”amma muka kasance masu sauƙinkai a cikinku, kamar yadda mahaifiya take lura da ƙananan ’ya’yanta.
”Sa’an nan za su iya su koya wa mata masu ƙuruciya su ƙaunaci mazansu da ’ya’yansu,
”Kamar yadda jikin da babu ruhu matacce ne, haka ma bangaskiyar da babu ayyuka matacciya ce.
”Dubi irin ƙaunar da Uba ya ƙaunace mu da ita mana, har ana ce da mu ’ya’yan Allah! Haka kuwa muke! Dalilin da ya sa duniya ba tă san mu ba shi ne, don ba tă san shi ba.
”Kada ku zama kamar Kayinu, wanda ya zama na mugun nan, ya kuma kashe ɗan’uwansa. Me ya sa ya kashe shi? Domin ayyukansa mugaye ne, na ɗan’uwansa kuma na adalci ne.
”Duk mai ƙin ɗan’uwansa mai kisankai ne, kun kuma san cewa ba mai kisankan da yake da rai madawwami a cikinsa.
”Suka yi kira da babbar murya suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarki da kuma Mai Gaskiya, sai yaushe za ka shari’anta mazaunan duniya ka kuma ɗauki mana fansar jininmu?”
”Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.”
”