05 – Sama

Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Sama.

Top 3 Mafi Muhimmanci ayoyi

1 Korintiyawa 2:9

Duk da haka, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ba idon da ya taɓa gani, ba kunnen da ya taɓa ji, ba kuma zuciyar da ta taɓa tunanin abin da Allah ya shirya wa masu ƙaunarsa.”

Ru’uya ta Yohanna 22:3-5

Ba za a ƙara samun la’ana ba. Kursiyin Allah da na Ɗan Ragon zai kasance a cikin birnin, bayinsa kuma za su yi masa hidima. Za su ga fuskarsa, sunansa kuma zai kasance a goshinsu. Ba za a ƙara yin dare ba. Ba za su bukaci hasken fitila ko hasken rana ba, domin Ubangiji Allah zai haskaka su. Za su kuwa yi mulki har abada abadin.

Daniyel 12:2-3

Ɗumbun mutanen da suka yi barci cikin turɓayar duniya za su farka, waɗansu zuwa ga rai madawwami, waɗansu zuwa ga madawwamiyar kunya da kuma madawwamin ƙasƙanci. Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar hasken samaniya, waɗanda kuma suka jagoranci waɗansu da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.

Kowane Aya A Canonical Order – 183 sassa

Farawa 1:1

A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa.

Farawa 2:9

Ubangiji Allah ya kuma sa kowane irin itace ya tsira daga ƙasa, itace mai kyan gani, mai amfani kuma don abinci. A tsakiyar lambun kuwa akwai itacen rai da kuma itacen sanin abin da yake da kyau da abin da yake mugu.

Farawa 28:12

Ya yi mafarki inda ya ga wata matakalar hawa, tsaye a ƙasa, kanta ta kai sama, mala’ikun Allah kuwa suna hawa, suna sauka a kanta.

Farawa 28:17

Ya ji tsoro, ya kuma ce, “Wane irin wuri ne mai banrazana haka! Lalle wannan gidan Allah ne, kuma nan ne ƙofar sama.”

Maimaitawar Shari’a 10:14

Sammai, har da sama sammai, da duniya, da kome da yake cikinta na Ubangiji Allahnku ne.

Maimaitawar Shari’a 26:15

Ka duba ƙasa daga sama, mazauninka mai tsarki, ka albarkace mutanenka Isra’ila da kuma ƙasar da ka ba mu kamar yadda ka yi wa kakanninmu alkawari da rantsuwa, ƙasa mai zub da madara da zuma.”

1 Sarakuna 8:27

“Amma anya, Allah, za ka zauna a duniya? Sammai, har ma da saman sammai ba za tă iya riƙe ka ba, balle wannan haikalin da na gina!

1 Sarakuna 8:30

Ka ji roƙon bawanka da kuma na mutanenka Isra’ila sa’ad da suka yi addu’a, suka fuskanci wannan wuri. Ka ji daga sama, mazauninka, kuma sa’ad da ka ji, ka gafarta.

1 Tarihi 29:11

Girma da iko da ɗaukaka, da daraja da kuma nasara naka ne, ya Ubangiji, gama kome a sama da ƙasa naka ne. Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji; an kuma ɗaukaka ka a matsayin kai a bisa duka.

Nehemiya 9:6

Kai kaɗai ne Ubangiji. Kai ka yi sammai, har ma da sama sammai, da dukan rundunar taurari, da duniya da kuma dukan abin da yake cikinta, da tekuna da dukan abubuwan da suke cikinsu. Ka ba da rai ga kome, kuma rundunonin sama suna maka sujada.

Zabura 11:4

Ubangiji yana cikin haikalinsa mai tsarki; Ubangiji yana a kursiyinsa a sama. Yana kallon ’ya’yan mutane; idanunsa suna bincike su.

Zabura 16:11

Ka sanar da ni hanyar rai; za ka cika ni da farin ciki a gabanka, da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.

Zabura 20:6

Yanzu na san cewa, Ubangiji yakan cece shafaffensa. Yakan amsa masa daga samansa mai tsarki da ikon ceto na hannun damansa.

Zabura 21:4

Ya nemi ka ba shi rai, ka kuwa ba shi, tsawo kwanaki, har abada abadin

Zabura 49:9

da zai sa yă ci gaba da rayuwa har abada yă hana shi shigan kabari yă ruɓa.

Zabura 68:17

Karusan Allah ninkin dubbai goma ne da kuma dubu dubbai; Ubangiji ya zo daga Sinai ya shiga cikin haikalinsa.

Zabura 89:29

Zan kafa zuriyarsa har abada, kursiyinsa muddin sammai suna nan.

Zabura 103:11

Gama kamar yadda sammai suke can bisa duniya, haka girmar ƙaunarsa yake wa masu tsoronsa;

Zabura 103:19

Ubangiji ya kafa kursiyinsa a sama, masarautarsa kuwa na mulki a bisa duka.

Zabura 133:3

Yana kamar raɓar Hermon da take zubowa a kan Dutsen Sihiyona. Gama a can Ubangiji ya tabbatar da albarkarsa, har ma rai na har abada.

Karin Magana 12:28

A hanyar adalci akwai rai; a wannan hanya akwai rashin mutuwa.

Mai Hadishi 3:11

Ya yi kowane abu da kyau a lokacinsa. Ya kuma sa matuƙa a zukatan mutane, duk da haka sun kāsa gane abin da Allah ya yi daga farko zuwa ƙarshe.

Ishaya 6:1-3

A shekarar da Sarki Uzziya ya mutu, na ga Ubangiji zaune a kan kujerar sarauta a sama cike da ɗaukaka, zatinsa ya cika haikali. A bisansa akwai serafofi, kowanne yana da fikafikai shida. Fikafikai biyu sun rufe fuskokinsu, da biyu suka rufe ƙafafunsu, biyu kuma da su suke tashi. Suna kiran juna, “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Maɗaukaki ne; duniya ta cika da ɗaukakarsa.”

Ishaya 9:7

Game da girmar gwamnatinsa da salama babu iyaka. Zai gāji sarki Dawuda, yă yi mulki a matsayinsa, zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Maɗaukaki ne ya yi niyyar aikata wannan duka.

Ishaya 11:6

Kyarkeci zai zauna tare da ɗan rago damisa za tă kwanta tare da akuya, ɗan maraƙi da zaki da ɗan saniya za su yi kiwo tare; ɗan yaro ne zai lura da su.

Ishaya 25:8

zai haɗiye mutuwa har abada. Ubangiji Mai Iko Duka zai share hawaye daga dukan fuskoki; zai kawar da kunyar mutanensa daga dukan duniya. Ubangiji ne ya faɗa.

Ishaya 57:15

Gama abin da Maɗaukaki da kuma Mai daraja ya faɗa wanda yake raye har abada, wanda sunansa mai tsarki ne, “Ina zama a bisa da kuma a tsattsarkan wuri, amma kuma tare da shi wanda yake mai halin tuba mai tawali’u a ruhu, don in farfaɗo da ruhu mai tawali’u in kuma farfaɗo da zuciyar mai halin tuba.

Ishaya 60:19-21

Rana ba za tă ƙara zama haskenki a yini ba, balle hasken wata ya haskaka a kanki, gama Ubangiji zai zama madawwamin haskenki, Allahnki kuma zai zama ɗaukakarki. Ranarki ba za tă ƙara fāɗuwa ba watanki kuma ba zai ƙara shuɗewa ba; Ubangiji zai zama madawwamin haskenki, kwanakin baƙin cikinki za su ƙare. Sa’an nan dukan mutanenki za su zama masu adalci za su kuma mallaki ƙasar har abada. Su ne reshen da na shuka, aikin hannuwana, don nuna darajata.

Ishaya 65:17

“Ga shi, na halicci sabuwar sama da kuma sabuwar duniya. Abubuwa na dā za a manta da su, ba kuwa za a ƙara tuna da su ba.

Ishaya 66:1

Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Sama kursiyina ce, duniya kuma matashin sawuna. Ina gidan da za ku gina mini? Ina wurin hutuna zai kasance?

Ishaya 66:22

“Kamar yadda sabuwar duniya da sabuwar sama za su tabbata a gabana,” in ji Ubangiji, “haka sunanku da zuriyarku za su tabbata.

Irmiya 31:37

Ga abin da Ubangiji yana cewa, “In a iya auna sammai a kuma bincike tushen duniya a ƙarƙas to, sai in ƙi dukan zuriyar Isra’ila ke nan saboda dukan abin da suka yi,” in ji Ubangiji.

Ezekiyel 1:26-28

A bisa al’arshin a kan kawunansu akwai abin da ya yi kamar saffaya, kuma a can bisa a kan kursiyin akwai siffa kamar na mutum. Na ga daga abin da ya yi kamar kwankwasonsa zuwa bisa ya yi kamar ƙarfe mai walƙiya, sai ka ce wuta, kuma daga kwankwasonsa zuwa ƙasa ya yi kamar wuta; haske kuma mai walƙiya sosai kewaye da shi. Kamar kamannin bakan gizo a cikin gizagizai a ranar da aka yi ruwan sama, haka hasken da ya kewaye shi. Wannan shi ne kwatancin kamannin ɗaukakar Ubangiji. Sa’ad da na gani, sai na fāɗi rubda ciki, na kuma ji muryar wani tana magana.

Ezekiyel 47:12

’Ya’yan itatuwa na kowane iri za su yi girma a kowane gefen kogin. Ganyayensu ba su bushe ba, ba kuwa za su fasa yin ’ya’ya ba. Kowane wata za su ba da ’ya’ya domin ruwa daga wuri mai tsarki yana malalo musu. ’Ya’yansu za su zama abinci, ganyayensu kuma za su zama magani.”

Daniyel 2:44

“A lokacin mulkin waɗannan sarakunan, Allah na sama zai kafa mulki da ba zai taɓa rushewa ba, ba kuma za a ba ma waɗansu mutane ba. Zai ragargaje waɗannan mulkokin da kuma kawo su ga ƙarshe, amma shi wannan mulki zai dawwama har abada.

Daniyel 7:13-14

“A wahayina na dare, na ga a gabana wani kamar ɗan mutum yana saukowa tare da gizagizan sama. Ya kusaci Wannan wanda yake Tun fil azal aka kuma kai shi gabansa. Aka ba shi mulki, daraja da kuma mafificin iko; dukan mutane, da al’ummai, da mutane daga kowane harshe suka yi masa sujada. Mulkinsa kuwa dawwammamen mulki ne da ba zai ƙare ba, sarautarsa kuma ba ta taɓa lalacewa.

Daniyel 7:18

Amma tsarkaka na Mafi Ɗaukaka za su karɓi wannan sarauta, za su kuwa mallake ta har abada, I, har abada abadin.’

Daniyel 7:27

Sa’an nan za a ba da mulki, iko da girma na mulkokin da suke a ƙarƙashin dukan sammai ga tsarkaka, mutane na Mafi Ɗaukaka. Mulkinsa kuwa mulki ne marar matuƙa, kuma dukan masu mulki za su yabe shi, su kuma yi masa biyayya.’

Daniyel 12:2-3

Ɗumbun mutanen da suka yi barci cikin turɓayar duniya za su farka, waɗansu zuwa ga rai madawwami, waɗansu zuwa ga madawwamiyar kunya da kuma madawwamin ƙasƙanci. Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar hasken samaniya, waɗanda kuma suka jagoranci waɗansu da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.

Mattiyu 3:2

yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”

Mattiyu 3:12

Yana riƙe da matankaɗinsa, zai tankaɗe hatsinsa, yă kuma tattara alkamarsa a cikin rumbu, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.”

Mattiyu 4:17

Tun daga wannan lokaci, Yesu ya fara wa’azi yana cewa, ‹“Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”›

Mattiyu 5:3

‹“Masu albarka ne waɗanda suke matalauta a ruhu,› ‹gama mulkin sama nasu ne.›

Mattiyu 5:10-12

‹Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu don gani an yi adalci,› ‹gama mulkin sama nasu ne.› ‹“Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni.› ‹Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.›

Mattiyu 5:19-20

‹Duk wanda ya karya ɗaya daga cikin mafi ƙanƙanta na umarnan nan, ya kuma koya wa waɗansu su yi haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a mulkin sama. Amma duk wanda ya aikata, ya kuma koyar da waɗannan umarnai, za a kira shi mai girma a cikin mulkin sama.› ‹Gama ina faɗa muku cewa in dai adalcinku bai fi na Farisiyawa da na malaman dokoki ba, faufau, ba za ku shiga mulkin sama ba.›

Mattiyu 6:9-10

‹“To, ga yadda ya kamata ku yi addu’a.› ‹“ ‘Ubanmu wanda yake cikin sama,› ‹a tsarkake sunanka,› ‹mulkinka yă zo› ‹a aikata nufinka a duniya› ‹kamar yadda ake yi a sama.›

Mattiyu 6:13

‹Kada ka bari a kai mu cikin jarraba,› ‹amma ka cece mu daga mugun nan.›‹’›

Mattiyu 6:19-21

‹“Kada ku yi wa kanku ajiyar dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda kuma ɓarayi sukan fasa, su yi sata.› ‹Amma ku yi wa kanku ajiyar dukiya a sama, inda ba tsatsa da asu da za su ɓata su, inda kuma ba ɓarayin da za su fasa, su yi sata.› ‹Gama inda dukiyarka take, a nan ne fa zuciyarka za tă kasance.›

Mattiyu 7:13-14

‹“Ku shiga ta matsattsiyar ƙofa. Gama ƙofar zuwa hallaka faɗaɗɗiya ce mai sauƙin bi kuma, masu shiga ta cikinta kuwa suna da yawa.› ‹Amma ƙofar zuwa rai, ƙarama ce matsattsiya kuma, masu samunta kuwa kaɗan ne.›

Mattiyu 7:21

‹“Ba duk mai ce mini, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ne zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda yake aikata nufin Ubana da yake sama.›

Mattiyu 10:7

‹Sa’ad da kuke tafiya, ku yi wa’azi, kuna cewa, ‘Mulkin sama ya kusato.’›

Mattiyu 11:11

‹Gaskiya nake gaya muku. A cikin dukan waɗanda mata suka haifa, ba wani da ya taso da ya fi Yohanna Mai Baftisma girma; duk da haka mafi ƙanƙanta a mulkin sama ya fi shi girma.›

Mattiyu 13:10-11

Almajiran suka zo wurinsa suka tambaye shi, “Me ya sa kake wa mutane magana da misalai?” Ya amsa ya ce, ‹“Sanin asirin mulkin sama kam, ku aka ba wa, amma su ba a ba su ba.›

Mattiyu 13:31-32

Ya ba su wani misali ya ce, ‹“Mulkin sama yana kama da ƙwayar mustad, wadda mutum ya ɗauka ya shuka a gonarsa.› ‹Ko da yake ita ce mafi ƙanƙanta cikin ƙwayoyinku, duk da haka sa’ad da ta yi girma, takan zama mafi girma cikin tsire-tsiren lambu ta kuma zama itace, har tsuntsayen sararin sama su zo su yi sheƙa a rassansa.”›

Mattiyu 13:43

‹Sa’an nan masu adalci za su haskaka kamar rana a mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yă ji.”›

Mattiyu 13:44

‹“Mulkin sama yana kama da dukiyar da aka ɓoye a gona. Da wani ya same ta, sai yă sāke ɓoye ta, sa’an nan cikin farin cikinsa yă je yă sayar da duk abin da yake da shi yă sayi gonar.›

Mattiyu 13:45-46

‹“Har wa yau dai, mulkin sama yana kama da ɗan kasuwa mai neman lu’ulu’ai masu kyau.› ‹Da ya sami dutse guda mai daraja sosai, sai ya tafi ya sayar da dukan abin da yake da shi ya saye shi.›

Mattiyu 13:47-49

‹“Har yanzu, mulkin sama yana kama da abin kamun kifin da aka jefa cikin tafki yă kamo kifi iri-iri.› ‹Da abin kamun kifi ya cika, masuntan suka jawo shi gaci. Sai suka zauna suka tattara kifi masu kyau a kwanduna, amma suka zubar da marasa kyau.› ‹Haka zai kasance a ƙarshen zamani. Mala’iku za su zo su ware masu mugunta daga masu adalci›

Mattiyu 13:52

Sa’an nan ya ce musu, ‹“Saboda haka duk malamin dokokin da ya horu game da koyarwar mulkin sama, yana kama da maigida wanda yakan fitar daga ɗakin ajiyarsa sababbin dukiya da kuma tsofaffi.”›

Mattiyu 14:36

suka kuwa roƙe shi yă bar marasa lafiya su taɓa ko da gefen rigarsa kawai, duk waɗanda suka taɓa shi kuwa suka warke.

Mattiyu 16:19

‹Zan ba ka mabuɗan mulkin sama; kome ka daure a duniya zai zama a daure a sama, kome kuma ka kunce a duniya zai zama a kunce a sama.”›

Mattiyu 18:3

Sai ya ce, ‹“Gaskiya nake gaya muku, in ba kun canja kuka zama kamar ƙananan yara ba, labudda, ba za ku shiga mulkin sama ba.›

Mattiyu 18:10

‹“Ku lura, kada ku rena ɗaya daga cikin waɗannan ƙanana. Gama ina faɗa muku mala’ikunsu a sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin sama.›

Mattiyu 18:18

‹“Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka daure a duniya, za a daure a sama, duk kuma abin da kuka kunce a duniya, za a kunce shi a sama.›

Mattiyu 19:14

Yesu ya ce, ‹“Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin sama na irin waɗannan ne.”›

Mattiyu 19:16-22

To, fa, sai ga wani ya zo wurin Yesu ya tambaye shi ya ce, “Malam, wane abu mai kyau ne ya zama mini dole in yi don in sami rai madawwami?” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Don me kake tambayata game da abin da yake mai kyau? Akwai Mai kyau Ɗaya kaɗai. In kana so ka sami rai madawwami, ka kiyaye dokokin nan.”› Mutumin ya yi tambaya ya ce, “Waɗanne?” Yesu ya amsa ya ce, ‹“ ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar ƙarya,› ‹ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’›‹ka kuma ‘ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’›‹”› Saurayin ya ce, “Duk waɗannan na kiyaye. Me kuma ya rage mini?” Yesu ya amsa ya ce, ‹“In kana so ka zama cikakke, ka je, ka sayar da dukan dukiyarka ka kuma ba matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo, ka bi ni.”› Da saurayin ya ji haka, sai ya tafi rai a ɓace, don yana da arziki sosai.

Mattiyu 19:23-24

Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, ‹“Gaskiya nake gaya muku, yana da wuya mai arziki yă shiga mulkin sama.› ‹Har wa yau ina gaya muku, zai fi sauƙi raƙumi yă shiga ta kafar allura, da mai arziki yă shiga mulkin Allah.”›

Mattiyu 19:28-29

Yesu ya ce musu, ‹“Gaskiya nake gaya muku, a lokacin sabunta dukan kome, sa’ad da Ɗan Mutum ya zauna a kan kursiyinsa mai daraja, ku da kuka bi ni, ku ma za ku zauna a kan kursiyoyi goma sha biyu, kuna yi wa kabilu goma sha biyu na Isra’ila shari’a.› ‹Duk kuma wanda ya bar gidaje ko ’yan’uwa maza ko ’yan’uwa mata ko mahaifi ko mahaifiya ko yara ko gonaki, saboda ni, zai sami abin da ya fi haka riɓi ɗari, yă kuma gāji rai madawwami.›

Mattiyu 22:2-3

‹“Mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya shirya bikin auren ɗansa.› ‹Sai ya aiki bayinsa su kira waɗanda aka gayyata zuwa bikin, amma waɗanda aka ce su zo bikin, suka ƙi zuwa.›

Mattiyu 22:30-32

‹Ai, a tashin matattu, mutane ba za su yi aure ko su ba da aure ba; za su zama kamar mala’iku a sama.› ‹Amma game da tashi daga matattu na waɗanda suka mutu ba ku karanta abin da Allah ya ce muku ba ne,› ‹‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’›‹? Ai, shi ba Allah na matattu ba ne, shi Allah na masu rai ne.”›

Mattiyu 24:30

‹“A sa’an nan ne alamar dawowar Ɗan Mutum zai bayyana a sararin sama, dukan al’umman duniya kuwa za su yi kuka. Za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gizagizan sararin sama, da iko da kuma ɗaukaka mai girma.›

Mattiyu 24:35

‹Sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za tă taɓa shuɗe ba.›

Mattiyu 25:1-4

‹“A lokacin mulkin sama zai zama kamar budurwai goma waɗanda suka ɗauki fitilunsu suka fita don su taryi ango.› ‹Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuma masu hikima.› ‹Wawayen sun ɗauki fitilunsu, sai dai ba su riƙe mai ba.› ‹Masu hikimar kuwa suka riƙo tulunan mai da fitilunsu.›

Mattiyu 25:21

‹“Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’›

Mattiyu 25:34

‹“Sa’an nan Sarki zai ce wa waɗanda suke damansa, ‘Ku zo, ku da Ubana ya yi wa albarka; ku karɓi gādonku, mulkin da aka shirya muku tun halittar duniya.›

Mattiyu 25:46

‹“Sa’an nan za su tafi cikin madawwamiyar hukunci, amma masu adalci kuwa za su shiga rai madawwami.”›

Mattiyu 28:18

Sai Yesu ya zo wurinsu ya ce, ‹“An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa.›

Markus 10:14-15

Da Yesu ya ga haka, sai ya yi fushi, ya ce musu, ‹“Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne.› ‹Gaskiya nake gaya muku, duk wanda bai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.”›

Markus 10:17-22

Da Yesu ya kama hanya, sai wani mutum ya ruga da gudu ya zo wajensa, ya durƙusa a gabansa ya ce, “Malam nagari, me zan yi domin in gāji rai madawwami?” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Don me kake ce da ni mai nagarta? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai.› ‹Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, kada ka cuci wani, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’›‹”› Mutumin ya ce, “Malam, ai, tun ina yaro na kiyaye duk waɗannan.” Yesu ya kalle shi da ƙauna ya ce, ‹“Abu ɗaya ka rasa, ka tafi ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo ka bi ni.”› Da jin wannan, sai mutumin ya ɓata fuskarsa, ya tafi da baƙin ciki, gama yana da arziki sosai.

Markus 12:25-26

‹Sa’ad da matattu suka tashi, ba za su yi aure ba, ba kuwa za a ba da su ga aure ba. Za su zama kamar yadda mala’iku suke a cikin sama.› ‹Game da tashin matattu kuwa, ashe, ba ku karanta a cikin littafin Musa ba, game da labarin ɗan kurmin nan mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, yadda Allah ya yi magana da shi ya ce, ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’?›

Luka 6:20-23

Da ya dubi almajiransa, sai ya ce, ‹“Masu albarka ne ku da kuke matalauta,› ‹gama mulkin Allah naku ne.› ‹Masu albarka ne ku da kuke jin yunwa yanzu,› ‹gama za ku ƙoshi.› ‹Masu albarka ne ku da kuke kuka yanzu,› ‹gama za ku yi dariya.› ‹Masu albarka ne sa’ad da mutane suka ƙi ku,› ‹suka ware ku, suka zage ku,› ‹suna ce da ku mugaye,› ‹saboda Ɗan Mutum.› ‹“Ku yi farin ciki a wannan rana, ku kuma yi tsalle don murna, saboda ladarku yana da yawa a sama. Gama haka kakanninsu suka yi wa annabawa.›

Luka 8:10

Sai ya ce, ‹“Ku ne aka ba sanin asirin mulkin Allah, amma ga sauran mutane kam, ina magana da misalai, saboda,› ‹“ ‘ko da yake suna kallo, ba za su gani ba,› ‹ko da yake suna ji, ba za su gane ba.’›

Luka 10:20

‹Duk da haka, kada ku yi farin ciki da cewa, kun sha ƙarfin ruhohi, amma ku yi farin ciki, domin an rubuta sunayenku a sama.”›

Luka 10:25-28

Wata rana, sai wani masanin dokoki ya miƙe tsaye don yă gwada Yesu. Ya tambaya ya ce, “Malam, me zan yi don in gāji rai madawwami?” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Me aka rubuta a cikin Doka? Yaya kake karanta ta?”› Sai ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan ƙarfinka, da kuma dukan hankalinka’; kuma, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ ” Yesu ya ce, ‹“Ka amsa daidai. Ka yi haka, kuma za ka rayu.”›

Luka 12:31-34

‹Amma ku nemi mulkinsa, za a kuwa ƙara muku waɗannan abubuwa.› ‹“Ya ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, gama ya gamshi Ubanku ya ba ku mulkin.› ‹Ku sayar da dukiyarku, ku ba wa matalauta. Ku yi wa kanku jakar kuɗin da ba za su lalace ba. Ku yi wa kanku ajiyar dukiyar da ba za tă kare ba a sama, inda ɓarawo ba zai yi kusa ba, asu kuma ba za su iya su lalatar ba.› ‹Gama inda dukiyarku take, nan ne zuciyarku ma take.›

Luka 15:7

‹Ina gaya muku, haka za a yi murna sosai a sama, a kan mai zunubi guda ɗaya da ya tuba, fiye da masu adalci tasa’in da tara, waɗanda ba su bukatan tuba.›

Luka 16:25-26

‹“Amma Ibrahim ya ce, ‘Ka tuna fa ɗana, a lokacin da kake duniya, ka sami abubuwa masu kyau naka, Lazarus kuwa ya sami munanan abubuwa. Amma yanzu ya sami ta’aziyya a nan, kai kuwa kana shan azaba.› ‹Ban da wannan duka ma, tsakaninmu da kai, akwai wani babban rami da aka yi, yadda waɗanda suke son ƙetarewa daga nan zuwa wurinku, ba za su iya ba, kuma ba mai iya ƙetarewa daga wurinku zuwa wurinmu.’›

Luka 18:16-17

Amma Yesu ya kira yaran a wurinsa ya ce, ‹“Ku bar yara ƙanana su zo wurina. Kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne.› ‹Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ba zai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.”›

Luka 18:18-27

Wani mai mulki ya tambayi Yesu ya ce, “Malam managarci, me zan yi don in gāji rai madawwami?” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Don me kake kira na managarci? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai.› ‹Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”› Mutumin ya ce, “Ai, tun ina ƙarami, na kiyaye duka waɗannan.” Da Yesu ya ji haka, sai ya ce masa, ‹“Akwai abu ɗaya har yanzu da ya rage maka. Ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, sa’an nan za ka sami dukiya a sama. Bayan haka, ka zo ka bi ni.”› Da jin haka, sai ya ɓata rai, domin shi mai arziki ne sosai. Yesu ya kalle shi ya ce, ‹“Yana da wuya fa, masu arziki su shiga mulkin Allah!› ‹Tabbatacce, zai fi sauƙi raƙumi ya shiga ta kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.”› Waɗanda suka ji wannan suka yi tambaya suka ce, “To, wa zai iya samun ceto?” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Abin da ba ya yiwuwa ga mutane, mai yiwuwa ne ga Allah.”›

Luka 18:29-30

Yesu ya ce musu, ‹“Gaskiya nake gaya muku, ba wanda ya bar gida, ko mata, ko ’yan’uwa maza, ko iyaye, ko yara, saboda mulkin Allah,› ‹da zai kāsa samun riɓi mai yawa, a wannan zamani, ya kuma sami rai madawwami a zamani mai zuwa.”›

Luka 23:42-43

Sai ya ce, “Yesu, ka tuna da ni sa’ad da ka shiga mulkinka.” Yesu ya amsa, ya ce masa, ‹“Gaskiya nake faɗa maka, yau ɗin nan, za ka kasance tare da ni, a mulkina a sama.”›

Yohanna 1:51

Sai ya ƙara da cewa, ‹“Gaskiya nake gaya muku, za ku ga sama a buɗe, mala’ikun Allah kuma suna hawa suna kuma sauka a kan Ɗan Mutum.”›

Yohanna 3:3-6

Yesu ya amsa ya ce, ‹“Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.”› Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya za a haifi mutum sa’ad da ya tsufa? Tabbatacce ba zai sāke koma sau na biyu a cikin mahaifiyarsa don a haife shi kuma ba!” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an haife shi ta wurin ruwa da kuma Ruhu.› ‹Jiki yakan haifi jiki, amma Ruhu yana haifi ruhu.›

Yohanna 3:12-16

‹Na yi muku magana a kan abubuwan duniya amma ba ku gaskata ba; to, yaya za ku gaskata in na yi magana a kan abubuwan sama?› ‹Ba wanda ya taɓa hawa zuwa sama sai wanda ya sauka daga sama, wato, Ɗan Mutum.› ‹Kamar dai yadda Musa ya ɗaga maciji a hamada, haka dole ne a ɗaga Ɗan Mutum,› ‹don duk mai gaskata da shi ya sami rai madawwami.”› Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami.

Yohanna 3:36

Duk wanda ya gaskata da Ɗan yana da rai madawwami, amma duk wanda ya ƙi Ɗan ba zai sami rai ba, gama fushin Allah yana nan a bisansa.”

Yohanna 4:14

‹amma duk wanda ya sha ruwan da zan ba shi, ba zai ƙara jin ƙishirwa ba. Tabbatacce, ruwan da zan ba shi, zai zama masa maɓuɓɓugan ruwa da yake ɓuɓɓugowa har yă zuwa rai madawwami.”›

Yohanna 5:24

‹“Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ji maganata ya kuma gaskata da wanda ya aiko ni yana da rai madawwami ba za a kuma hukunta shi ba; ya riga ya ƙetare daga mutuwa zuwa rai.›

Yohanna 5:28-29

‹“Kada ku yi mamakin wannan, gama lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke cikin kaburbura za su ji muryarsa› ‹su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta za su tashi zuwa ga rai, waɗanda kuma suka aikata mugunta za su tashi zuwa ga hukunci.›

Yohanna 5:39

‹Kuna ta nazarin Nassosi da himma don kuna tsammani ta wurinsu ne kuna samun rai madawwami. Nassosin nan ne suke ba da shaida a kaina,›

Yohanna 6:27

‹Kada ku yi aiki saboda abincin da yake lalacewa, sai dai saboda abinci mai dawwama har yă zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. A kansa ne Allah Uba ya sa hatimin amincewarsa.”›

Yohanna 6:40

‹Gama nufin Ubana shi ne, duk wanda yake duban Ɗan, ya kuma gaskata shi zai sami rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.”›

Yohanna 6:47

‹Gaskiya nake gaya muku, wanda ya gaskata yana da rai madawwami.›

Yohanna 6:51

‹Ni ne burodin rai mai saukowa daga sama. Duk wanda ya ci wannan burodi, zai rayu har abada. Wannan burodin shi ne jikina, da zan bayar don duniya ta sami rai.”›

Yohanna 6:54

‹Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana da rai madawwami. Ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.›

Yohanna 6:68

Sai Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Ubangiji wajen wa za mu tafi? Kai ne da kalmomin rai madawwami.

Yohanna 10:28

‹Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.›

Yohanna 11:25-27

Yesu ya ce mata, ‹“Ni ne tashin matattu da kuma rai. Duk wanda ya gaskata da ni zai rayu, ko ya mutu;› ‹kuma duk wanda yake raye ya kuma gaskata da ni ba zai taɓa mutuwa ba. Kin gaskata wannan?”› Sai ta ce masa, “I, Ubangiji, na gaskata kai ne Kiristi, Ɗan Allah, mai zuwa cikin duniya.”

Yohanna 12:25

‹Duk mai ƙaunar ransa, zai rasa shi, duk mai ƙin ransa a wannan duniya, zai kiyaye shi har yă zuwa rai madawwami.›

Yohanna 14:2-3

‹A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa; da a ce ba haka ba ne, da na gaya muku. Za ni can don in shirya muku wuri.› ‹In kuwa na tafi na shirya muku wuri, sai in dawo in ɗauke ku ku kasance tare da ni don ku kasance inda nake.›

Yohanna 17:1-3

Bayan da Yesu ya faɗi wannan, sai ya dubi sama ya yi addu’a ya ce, ‹“Uba, lokaci ya yi. Ka ɗaukaka Ɗanka, don Ɗanka yă ɗaukaka ka.› ‹Gama ka ba shi iko bisa dukan mutane domin yă ba da rai madawwami ga duk waɗanda ka ba shi.› ‹Rai madawwami kuwa shi ne, su san ka, Allah makaɗaici mai gaskiya, da kuma Yesu Kiristi, wanda ka aiko.›

Yohanna 18:36

Yesu ya ce, ‹“Mulkina ba na duniyan nan ba ne. Da na duniyan nan ne da bayina sun yi yaƙi su hana Yahudawa kama ni. Amma fa mulkina daga wani waje ne.”›

Ayyukan Manzanni 7:49

“ ‘Sama ne kursiyina, duniya kuma wurin ajiye tafin ƙafata. Wane irin gida za ka gina mini? Ko kuwa ina wurin hutuna zai kasance? In ji Ubangiji.

Ayyukan Manzanni 13:48

Sa’ad da Al’ummai suka ji haka, sai suka yi farin ciki suka ɗaukaka maganar Ubangiji; kuma duk waɗanda aka zaɓa don samun rai madawwami, suka gaskata.

Ayyukan Manzanni 14:22

suna gina almajirai suna kuma ƙarfafa su su tsaya da gaske cikin bangaskiya. Suka ce, “Sai da shan wahaloli masu yawa za mu shiga mulkin Allah.”

Ayyukan Manzanni 28:31

Ya yi wa’azin mulkin Allah yana kuma koyarwa game da Ubangiji Yesu Kiristi, gabagadi ba tare da wani abu ya hana shi ba.

Romawa 2:7

Ga waɗanda ta wurin naciya suna yin nagarta suna neman ɗaukaka, girma da rashin mutuwa, su za a ba su rai madawwami.

Romawa 5:21

domin, kamar yadda zunubi ya yi mulki cikin mutuwa, haka ma alheri yă yi mulki ta wurin adalci yă kuwa kawo rai madawwami ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu.

Romawa 6:22-23

Amma a yanzu da aka ’yantar da ku daga zunubi kuka kuma zama bayi ga Allah, ribar da kuka samu tana kai ga zaman tsarki, ƙarshenta kuwa rai madawwami ne. Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

Romawa 10:13

gama, “Duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.”

1 Korintiyawa 2:9

Duk da haka, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ba idon da ya taɓa gani, ba kunnen da ya taɓa ji, ba kuma zuciyar da ta taɓa tunanin abin da Allah ya shirya wa masu ƙaunarsa.”

1 Korintiyawa 15:42-49

Haka ne tashin matattu zai kasance. Abin da aka shuka yakan ruɓe, abin da aka tā da shi kuma ba ya ruɓewa; akan shuka shi cikin ƙasƙanci, a kuma tā da shi cikin ɗaukaka, akan shuka shi da rashin ƙarfi, a kuma tā da shi da ƙarfi; akan shuka shi da jiki na mutuntaka, a kuma tā da shi da jikin ruhaniya. In akwai jiki na mutuntaka, to, lalle akwai jikin ruhaniya ma. Haka yake a rubuce cewa, “Adamu, mutumin farko ya zama mai rai”; Adamu na ƙarshe kuwa ruhu ne mai ba da rai. Ba jikin ruhaniya ne ya zo da farko ba, na mutuntakan ne, daga baya kuma sai na ruhaniya. Mutumin farko daga turɓaya ce ya fito, mutum na biyu kuwa daga sama ne ya fito. Kamar yadda mutumin turɓaya yake, haka ma waɗanda suke na turɓaya. Kuma kamar yadda mutumin sama yake, haka ma waɗanda suke na sama. Kamar dai yadda muka ɗauki siffar mutumin turɓaya, haka kuma za mu ɗauki siffar mutumin sama.

1 Korintiyawa 15:50-56

Ina sanar da ku, ’yan’uwa, cewa nama da jini ba za su gāji mulkin Allah ba, haka ma ruɓa ba zai gāji rashin ruɓa ba. Ku saurara, in gaya muku wani asiri. Ba dukanmu ne za mu yi barci ba, sai dai duk za a sauya kamanninmu farat ɗaya, cikin ƙyaftawar ido, da busan ƙaho na ƙarshe. Gama za a busa ƙaho, za a tā da matattu da jiki irin da ba ya ruɓewa, za a kuma sauya kamanninmu. Gama dole mai ruɓa yă maye wa mai ruɓan nan, marar mutuwa kuma yă maye wa mai mutuwan nan. Sa’ad da mai ruɓan nan ya maye marar ruɓan nan, mai mutuwa kuma ya maye marar mutuwan nan, sa’an nan ne karin maganar da yake a rubuce zai zama gaskiya cewa, “An haɗiye mutuwa cikin nasara.” “Ya ke mutuwa, ina nasararki? Ya ke mutuwa, ina dafinki?” Zunubi ne yake ba wa mutuwa dafi, Doka kuma take ba wa zunubi iko.

2 Korintiyawa 4:17-18

Don wannan ’yar wahalar tamu mai saurin wucewa, ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci. Domin ba abubuwan da ido yake gani ne muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa. Gama abubuwan da ake gani masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne.

2 Korintiyawa 5:1-2

Yanzu mun san cewa in an hallaka tentin duniyan nan da muke ciki, muna da wani gini daga Allah, madawwamin gida a sama, wanda ba da hannuwan mutum ne suka gina shi ba. Kafin nan muna nishi, da marmari a yi mana sutura da gidanmu na sama,

2 Korintiyawa 5:8

Ina cewa muna da tabbaci, za mu fi so mu rabu da jikin nan, mu kuma kasance a sama tare da Ubangiji.

2 Korintiyawa 12:2-4

Na san wani a cikin Kiristi wanda shekaru goma sha huɗu da suka wuce an ɗauke zuwa sama ta uku. Ko a cikin jiki ne, ko kuwa ba a cikin jiki ba, ni dai ban sani ba, Allah ne ya sani. Na kuma san cewa wannan mutum, ko a cikin jiki ne, ko kuma ba a cikin jiki ba, ni dai ban sani ba, amma Allah ne ya sani, an ɗauke shi ne zuwa aljanna. Ya ji waɗansu abubuwa waɗanda ba zai iya faɗarsu da kalmomi ba, abubuwan da ba a ba wa mutum damar faɗi.

Galatiyawa 6:7-8

Kada a ruɗe ku. Ba a yi wa Allah ba’a. Mutum yakan girbe abin da ya shuka ne. Wanda ya yi shuki don yă gamshi mutuntakarsa, daga wannan mutuntaka zai girbi hallaka. Wanda ya yi shuki domin yă gamshi Ruhu, daga Ruhu zai girbi rai madawwami.

Afisawa 1:3

Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ya kawo mana kowace albarka ta ruhaniya daga sama.

Afisawa 2:19

Don haka, yanzu ku ba baƙi ba ne, ku kuma ba bare ba ne. Ku ’yan ƙasa ne tare da mutanen Allah, iyalin gidan Allah kuma.

Filibbiyawa 1:21-23

Gama a gare ni, rai Kiristi ne, mutuwa kuma riba ce. In zan ci gaba da rayuwa a cikin jiki, wannan zai zama aiki mai amfani a gare ni. Duk da haka me zan zaɓa? Ban sani ba! Na rasa wanda zan zaɓa cikin biyun nan. Ina sha’awa in yi ƙaura in zauna tare da Kiristi, wannan kuwa ya fi kyau nesa ba kusa ba;

Filibbiyawa 3:20-21

Amma mu ’yan mulkin sama ne. Muna kuma jira zuwan Mai Ceto daga can, Ubangiji Yesu Kiristi, shi ne mai ikon kawo dukan abubuwa ƙarƙashin mulkinsa. Ta wurin ikon nan nasa zai sāke jikin nan namu na ƙasƙanci, yă mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka.

Kolossiyawa 1:13

Gama ya riga ya cece mu daga mulkin duhu ya kuma kawo mu cikin mulkin Ɗan da yake ƙauna,

Kolossiyawa 3:2

Ku sa hankulanku a kan abubuwan sama, ba kan abubuwan duniya ba.

1 Tessalonikawa 2:12

muna ƙarfafa ku, muna ta’azantar da ku, muna kuma gargaɗe ku ku yi rayuwar da za tă cancanci Allah, wanda ya kira ku zuwa mulkinsa da kuma ɗaukakarsa.

2 Tessalonikawa 1:7

yă kuma sauƙaƙa muku ku da kuke wahala, har ma da mu. Wannan zai faru sa’ad da aka bayyana Ubangiji Yesu daga sama cikin wuta mai ci tare da mala’ikunsa masu iko.

1 Timoti 1:16-17

Amma saboda wannan dalilin ne aka nuna mini jinƙai domin ta wurina, mafi zunubi duka, Kiristi Yesu yă iya bayyana matuƙar haƙurinsa a matsayin misali ga waɗanda za su gaskata shi su kuma sami rai madawwami. Bari girma da ɗaukaka su tabbata har abada abadin ga Sarki madawwami, wanda ba ya mutuwa, wanda ba a ganinsa, wanda kuma shi ne kaɗai Allah! Amin.

1 Timoti 4:8

Gama horon jiki yana da amfani, amma tsoron Allah yana da amfani ga kowane abu, yana da albarka ga rai na yanzu da kuma rai mai zuwa.

1 Timoti 6:7

Gama ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu fita daga cikinta da kome ba.

1 Timoti 6:12

Ka yi fama, kyakkyawar fama ta bangaskiya. Ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira saboda shi, sa’ad da ka yi kyakkyawar shaida a gaban shaidu masu yawa.

1 Timoti 6:18-19

Ka umarce su su yi nagarta, su wadatu cikin ayyuka nagari, su kuma zama masu bayarwa hannu sake da kuma masu niyyar yin taimako. Ta haka za su ajiye wa kansu dukiya a matsayin tushen mai ƙarfi don tsara mai zuwa, don su riƙi rai wanda yake na tabbatacce.

2 Timoti 1:10

amma yanzu an bayyana ta ta wurin bayyanuwar Mai Cetonmu, Kiristi Yesu, wanda ya hallaka mutuwa ya kuma kawo rai da rashin mutuwa a sarari ta wurin bishara.

2 Timoti 4:18

Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun hari yă kuma kai ni mulkinsa na sama lafiya. A gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin.

Titus 1:2

duk wannan kuwa saboda begen nan ne ga rai madawwami da Allah ya yi alkawari tun fil azal, shi wanda ƙarya ba ta a gare shi,

Titus 3:7

wannan fa domin an kuɓutar da mu ne ta wurin alherinsa, don mu zama magāda masu begen ga rai madawwami.

Ibraniyawa 1:8

Amma game da Ɗan ya ce, “Kursiyinka, ya Allah, zai kasance har abada abadin, adalci kuma zai zama sandan mulkinka.

Ibraniyawa 4:9

Har yanzu, akwai wani hutun Asabbacin da ya rage domin mutanen Allah;

Ibraniyawa 5:9

kuma da aka mai da shi cikakke, sai ya zama hanyar samun madawwamin ceto ga dukan waɗanda suke masa biyayya.

Ibraniyawa 9:23-24

Waɗannan abubuwa hotuna ne kawai na abin da yake a sama, dole kuma a tsarkake su ta wurin waɗannan ƙa’idodi. Amma dole a tsarkake ainihin abubuwa na sama da wani abu mafi kyau. Gama Kiristi bai shiga wani wuri tsattsarka da mutum ya yi ba, wanda yake hoto ne kawai na gaskataccen, a’a sama kanta ya shiga, domin yă bayyana a gaban zatin Allah a yanzu saboda mu.

Ibraniyawa 11:16

A maimako, suna marmarin wata ƙasa mafi kyau, ta sama. Saboda haka Allah ba ya kunya a kira shi Allahnsu, domin ya riga ya shirya musu birni.

Ibraniyawa 12:22-23

Sai dai kun zo ne ga Dutsen Sihiyona, ga Urushalima ta sama, birnin Allah mai rai. Kun zo ga dubu dubban mala’ikun da suke cikin taron farin ciki, kun zo ga ikkilisiyar ɗan fari, waɗanda sunayensu suna a rubuce a sama. Kun zo ga Allah, alƙalin dukan mutane, kun kuma zo ga ruhohin mutane masu adalci da aka mai da su cikakku.

Ibraniyawa 13:14

Gama a nan ba mu da dawwammamen birni, sai dai muna zuba ido a kan birnin nan mai zuwa.

1 Bitrus 1:4

da kuma cikin gādon da ba zai taɓa lalacewa, ɓacewa ko koɗewa ba, ajiyayye a sama dominku,

1 Bitrus 3:22

wanda ya tafi sama, yana kuma a hannun dama na Allah, mala’iku, mulkoki da kuma masu iko suna masa biyayya.

2 Bitrus 1:10-11

Saboda haka ’yan’uwana, ku ƙara aniya wajen tabbatar da kiranku da zaɓenku da aka yi. Gama in kuka yi waɗannan abubuwa, ba za ku taɓa fāɗuwa ba, za ku sami kyakkyawar marabta cikin madawwamin mulkin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi.

2 Bitrus 3:13

Amma bisa ga alkawarinsa muna zuba ido ga sabuwar sama da kuma sabuwar ƙasa, inda adalci zai yi zama.

1 Yohanna 1:1-2

Wannan da ya kasance tun farko, wanda muka ji, wanda muka gani da idanunmu, wanda muka duba, hannuwanmu kuma suka taɓa, wannan ne muke shela game da Kalman rai. Wannan Rai ya bayyana, muka kuwa gan shi, muka kuma shaida shi, muna kuwa yin muku shelar wannan rai madawwami, wanda dā yake tare da Uba, ya kuma bayyana a gare mu.

1 Yohanna 2:17

Duniya da sha’awace-sha’awacenta suna shuɗewa, amma mutumin da yake aikata nufin Allah, zai rayu har abada.

1 Yohanna 2:25

Wannan shi ne abin da ya yi mana alkawari, wato, rai madawwami.

1 Yohanna 3:2

Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ’ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake.

1 Yohanna 5:11-13

Wannan kuwa ita ce shaidar; cewa Allah ya ba mu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Ɗansa. Duk wanda yake da Ɗan, yana da rai; wanda kuwa ba shi da Ɗan Allah, ba shi da rai. Ina rubuta waɗannan abubuwa gare ku, ku da kuka gaskata sunan Ɗan Allah domin ku san kuna da rai madawwami.

1 Yohanna 5:20

Mun san cewa Ɗan Allah ya zo duniya, ya kuma ba mu ganewa domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna cikinsa, shi da yake Allah na gaskiya wato, cikin Ɗansa Yesu Kiristi. Shi ne Allah na gaskiya da kuma rai na har abada.

Yahuda 1:21

Ku zauna cikin ƙaunar Allah yayinda kuke jira jinƙan Ubangijinmu Yesu Kiristi don yă kawo ku ga rai madawwami.

Ru’uya ta Yohanna 2:7

‹Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon ci daga itacen rai, da yake cikin aljannar Allah.›

Ru’uya ta Yohanna 3:5

‹Wanda ya ci nasara, kamar su, za a sanya masa fararen tufafi. Ba zan taɓa share sunansa daga cikin littafin rai ba, sai dai zan shaida sunansa a gaban Ubana da mala’ikunsa.›

Ru’uya ta Yohanna 3:21

‹Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon zama tare da ni a kursiyina, kamar yadda na ci nasara, kuma ina zaune tare da Ubana a kursiyinsa.›

Ru’uya ta Yohanna 4:1-4

Bayan wannan sai na duba, a can kuma a gabana ga ƙofa a buɗe a sama. Sai muryar da na ji da fari da take magana da ni mai kama da busar ƙaho ta ce, ‹“Hauro nan, zan kuma nuna maka abin da lalle zai faru bayan wannan.”› Nan da nan sai ga ni cikin Ruhu, a can a gabana kuwa ga kursiyi a cikin sama da wani zaune a kansa. Wannan mai zama a can kuwa yana da kamannin dutsen yasfa da karneliya. Bakan gizo, mai kama da zumurrudu, ya kewaye kursiyin. Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyoyi ashirin da huɗu, zaune a kansu kuwa dattawa ashirin da huɗu ne. Suna saye da fararen tufafi suna kuma da rawanin zinariya a kawunansu.

Ru’uya ta Yohanna 4:5-8

Daga kursiyin hasken walƙiya yana ta fitowa, da ƙararraki da kuma tsawa. A gaban kursiyin, fitilu bakwai suna ci. Waɗannan ne ruhohi bakwai na Allah. Haka kuma a gaban kursiyin akwai wani abu mai kama da tekun gilashi, yana ƙyalli kamar madubi. A tsakiya kuwa, kewaye da kursiyin, akwai halittu huɗu masu rai, cike kuma suna da idanu gaba da baya. Halitta ta fari tana kama da zaki, ta biyun kuwa tana kama da bijimi, ta ukun kuma tana da fuska kamar ta mutum, ta huɗun kuma tana kama da gaggafa mai tashi sama. Kowace a cikin halittu huɗu masu rai ɗin nan tana da fikafikai guda shida, tana kuma cike da idanu a ko’ina, har ma ƙarƙashin fikafikanta. Dare da rana ba sa fasa cewa, “ ‘Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki shi ne Ubangiji Allah Maɗaukaki,’ wanda yake a dā, wanda yake a yanzu, wanda kuma yake nan gaba.”

Ru’uya ta Yohanna 4:9-11

Duk lokacin da halittu masu ran nan suka rera ɗaukaka, girma da kuma godiya ga wannan wanda yake zaune a kan kursiyin da kuma wanda yake mai rai har abada abadin, sai dattawa ashirin da huɗun nan su fāɗi a ƙasa a gaban wannan wanda yake zaune a kursiyin, su yi sujada wa wannan wanda yake da rai har abada abadin. Sukan ajiye rawaninsu a gaban kursiyin suna cewa, “Ya Ubangijinmu da Allahnmu, ka cancanci ɗaukaka da girma da iko, domin ka halicci dukan abubuwa, kuma ta wurin nufinka aka halicce su suka kuma kasance.”

Ru’uya ta Yohanna 5:10-11

Ka mai da su masarauta da kuma firistoci, don su yi wa Allahnmu hidima, kuma za su yi mulki a duniya.” Sai na duba na kuma ji muryar mala’iku masu yawa, yawansu kuwa ya kai dubu dubbai, da kuma dubu goma sau dubu goma. Suka kewaye kursiyin da halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan.

Ru’uya ta Yohanna 7:9-12

Bayan wannan sai na duba, can a gabana kuwa ga wani taro mai girma, wanda ba mai iya ƙirgawa, daga kowace al’umma, kabila, mutane da kuma harshe, suna tsaye a gaban kursiyin da kuma gaban Ɗan Ragon nan. Suna saye da fararen tufafi suna kuma riƙe da rassan dabino a hannuwansu. Suka tā da murya da ƙarfi suna cewa, “Ceto na Allahnmu ne, wanda yake zaune a bisan kursiyi, da kuma na Ɗan Ragon.” Dukan mala’iku suna tsaye kewaye da kursiyin da kuma kewaye da dattawan tare da halittu huɗun nan masu rai. Suka fāɗi da fuskokinsu ƙasa a gaban kursiyin suka kuma yi wa Allah sujada, suna cewa, “Amin! Yabo da ɗaukaka, da hikima da godiya da girma da iko da ƙarfi sun tabbata ga Allahnmu har abada abadin. Amin!”

Ru’uya ta Yohanna 7:15-17

Saboda haka, “suna a gaban kursiyin Allah suna masa hidima dare da rana a cikin haikalinsa; kuma wannan mai zaune a kursiyin zai shimfiɗa tentinsa a bisansu. ‘Ba za su sāke jin yunwa ba; ba za su kuma sāke jin ƙishirwa ba. Rana ba za tă buga su ba,’ ko kuma kowane irin zafin ƙuna. Gama Ɗan Ragon da yake a tsakiyar kursiyin zai zama makiyayinsu; ‘zai bi da su zuwa ga maɓulɓular ruwan rai.’ ‘Allah kuwa zai share dukan hawaye daga idanunsu.’ ”

Ru’uya ta Yohanna 11:19

Sa’an nan aka buɗe haikalin Allah da yake a sama, kuma a cikin haikalinsa aka ga akwatin alkawarinsa. Sai kuwa ga walƙiya, ƙararraki, tsawa, girgizar ƙasa, da kuma ƙanƙara masu girma.

Ru’uya ta Yohanna 12:7-8

Aka kuwa yi yaƙi a sama. Mika’ilu da mala’ikunsa yaƙi macijin, maciji da mala’ikunsa su ma suka mai da martani. Amma macijin nan ba shi da isashen ƙarfi, har suka rasa matsayinsu a sama.

Ru’uya ta Yohanna 19:9

Sai mala’ikan ya ce mini, “Rubuta, ‘Masu albarka ne waɗanda aka gayyace su zuwa bikin auren Ɗan Ragon!’ ” Sai ya ƙara da cewa, “Waɗannan su ne kalmomin Allah da gaske.”

Ru’uya ta Yohanna 20:11

Sa’an nan na ga babban farin kursiyi da kuma wannan da yake zama a kansa. Duniya da sararin sama kuwa suka ɓace daga gabansa, babu wuri kuwa dominsu.

Ru’uya ta Yohanna 21:1-4

Sa’an nan na ga sabon sama da sabuwar duniya, gama sama na farko da duniya ta farko sun shuɗe, babu kuma wani teku. Na ga Birni Mai Tsarki, sabuwar Urushalima tana saukowa daga sama, daga Allah, a shirye kamar amaryar da aka yi mata ado mai kyau saboda mijinta. Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu. Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe.”

Ru’uya ta Yohanna 21:5-9

Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. “Ina yin kome sabo!” Sai ya ce, “Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma.” Ya ce mini, “An gama. Ni ne Alfa da kuma Omega, na Farko da kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi abin sha kyauta daga maɓulɓular ruwan rai. Duk wanda ya ci nasara zai gāji dukan wannan, zan kuma zama Allahnsa, shi kuma zai zama ɗana. Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.” Ɗaya daga cikin mala’ikun nan bakwai masu kwanonin nan bakwai cike da annoban nan bakwai na ƙarshe, ya zo ya ce mini “Zo, zan nuna maka amaryar, matar Ɗan Ragon.”

Ru’uya ta Yohanna 21:10-14

Ya kuwa ɗauke ni cikin Ruhu zuwa wani babban dutse mai tsayi, ya kuma nuna mini Birni Mai Tsarki, Urushalima, tana saukowa daga sama, daga Allah. Ya haskaka da ɗaukakar Allah, haskensa kuwa ya yi kamar lu’ulu’u mai daraja sosai, kamar yasfa, yana ƙyalƙyali kamar madubi. Yana da babbar katanga mai tsayi, mai ƙofofi goma sha biyu, da kuma mala’iku goma sha biyu a ƙofofin. A bisa ƙofofin an rubuta sunayen kabilu goma sha biyu na Isra’ila. Akwai ƙofofi uku a gabas, uku a arewa, uku a kudu, uku kuma a yamma. An gina katangar birnin a kan tushen gini goma sha biyu, a kansu kuwa akwai sunayen manzannin sha biyu na Ɗan Ragon.

Ru’uya ta Yohanna 21:15-21

Mala’ikan da ya yi magana da ni yana da sandan awo na zinariya don awon birnin, ƙofofinsa, da kuma katangarsa. Birnin murabba’i ne, tsayinsa daidai ne da fāɗinsa. Ya auna birnin da sandarsa ya kuwa sami mil 1,400 (wajen kilomita 2,200) tsawonsa, fāɗinsa da kuma tsayinsa daidai suke. Ya auna katangarsa ya kuma sami ƙaurinta kamun 144, bisa ga ma’aunin mutum, wanda mala’ikan ya yi amfani da shi. An yi katangar da yasfa, birnin kuma da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi. Tushen ginin katangar birnin kuwa an yi masa adon da kowane irin dutse mai daraja. Tushe na farko an yi shi yasfa, na biyu saffaya, na uku agat, na huɗu zumurrudu, na biyar onis, na shida yakutu, na bakwai kirisolit, na takwas beril, na tara tofaz, na goma kirisofuras, na goma sha ɗaya yasin, na goma sha biyu kuma ametis. Ƙofofi goma sha biyun nan lu’ulu’ai goma sha biyu ne, kowace ƙofa an yi ta da lu’ulu’u guda. Babban titin birnin kuwa an yi shi da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi.

Ru’uya ta Yohanna 21:22-27

Ban ga haikali a cikin birnin ba, domin Ubangiji Allah Maɗaukaki da kuma Ɗan Ragon ne haikalin birnin. Birnin ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi, gama ɗaukakar Allah tana ba shi haske, Ɗan Ragon kuwa shi ne fitilar birnin. Al’ummai za su yi tafiya cikin hasken birnin, sarakunan duniya kuma za su kawo darajarsu cikin birnin. Ba za a taɓa rufe ƙofofin birnin da rana ba, gama ba za a yi dare a can ba. Za a kawo ɗaukaka da girmar al’ummai a cikin birnin. Babu wani abu marar tsarkin da zai taɓa shiga cikin birnin, babu kuma wani mai aikata abin kunya ko ruɗi da zai shiga, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a cikin littafin rai na Ɗan Ragon.

Ru’uya ta Yohanna 22:1-5

Sai mala’ikan ya nuna mini kogin ruwan rai, mai ƙyalli kamar madubi, yana gangarawa daga kursiyin Allah da na Ɗan Ragon, yana bin tsakiyar babban titi na birnin. A kowane gefen kogin akwai itacen rai mai ba da ’ya’ya goma sha biyu, yana ba da ’ya’yansa kowane wata. Ganyayen itacen kuwa saboda warkar da al’ummai ne. Ba za a ƙara samun la’ana ba. Kursiyin Allah da na Ɗan Ragon zai kasance a cikin birnin, bayinsa kuma za su yi masa hidima. Za su ga fuskarsa, sunansa kuma zai kasance a goshinsu. Ba za a ƙara yin dare ba. Ba za su bukaci hasken fitila ko hasken rana ba, domin Ubangiji Allah zai haskaka su. Za su kuwa yi mulki har abada abadin.

Ru’uya ta Yohanna 22:14

‹“Masu albarka ne waɗanda suka wanke tufafinsu, don su sami izinin ci daga itacen rai su kuma shiga birnin ta ƙofofi.›

Ru’uya ta Yohanna 22:17

Ruhu da kuma amarya suna cewa, “Zo!” Duk wanda ya ji kuwa, yă ce, “Zo!” Duk mai jin ƙishirwa, yă zo; duk mai bukata kuma, yă ɗibi ruwan rai kyauta.

Hausa - Hausa - HA

HA'BSS - Budadden Littafi Mai Tsarki Biblica - 2020

This Bible text is from Biblica Open Hausa Contemporary Bible 2020
https://open.bible/bibles/hausa-biblica-text-bible/
provided by: Biblica Inc, available by Creative Commons CC-BY-SA-4.0,
and this new compilation is shared as www.creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0.
Languages are made available to you by www.ipedge.net