29 – Aljanu

Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Aljanu.

Top 3 Mafi Muhimmanci ayoyi

2 Bitrus 2:4

Gama in har Allah bai ƙyale mala’iku sa’ad da suka yi zunubi ba, amma ya tura su cikin lahira, domin a tsare su don hukunci;

1 Timoti 4:1

Ruhu a sarari ya faɗa cewa a kwanakin ƙarshe waɗansu za su watsar da bangaskiya su bi ruhohi masu ruɗu da kuma abubuwan da aljanu suke koyarwa.

Ishaya 14:12-15

Yaya aka yi ka fāɗo daga sama Ya tauraron safiya, ɗan hasken asuba! An fyaɗa ka da ƙasa, kai da ka taɓa ƙasƙantar da al’ummai! Ka yi tunani a ranka ka ce, “Zan hau zuwa sama; zan ɗaga kursiyina sama da taurarin Allah; zan zauna a kursiyi a kan dutsen taro, a can ƙurewar saman dutse mai tsarki. Zan haura can bisa gizagizai; zan mai da kaina kamar Mafi Ɗaukaka.” Amma ga shi an gangara da kai zuwa kabari, zuwa zurfafan rami.

Kowane Aya A Canonical Order – 173 sassa

Farawa 3:1-6

To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen, “Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?” Macen ta ce wa macijin, “Za mu iya ci daga ’ya’ya itatuwa a lambun, amma Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga ’ya’yan itacen da yake tsakiyar lambu, kada kuma ku taɓa shi, in ba haka ba kuwa za ku mutu.’ ” Maciji ya ce wa macen, “Tabbatacce ba za ku mutu ba. Gama Allah ya san cewa sa’ad da kuka ci daga itacen idanunku za su buɗe, za ku kuma zama kamar Allah, ku san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu.” Sa’ad da macen ta ga ’ya’yan itacen suna da kyau don abinci, abin sha’awa ga ido, abin marmari kuma don samun hikima, sai ta tsinka ta ci, ta kuma ba da waɗansu wa mijinta wanda yake tare da ita, shi ma ya ci.

Farawa 3:13-15

Sai Ubangiji Allah ya ce wa matar, “Me ke nan kika yi?” Matar ta ce, “Macijin ne ya ruɗe ni, na kuwa ci.” Saboda haka Ubangiji Allah ya ce wa macijin, “Saboda ka yi haka, “Na la’anta ka cikin dukan dabbobi da kuma cikin dukan namun jeji! Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya turɓaya kuma za ka ci dukan kwanakin rayuwarka. Zan kuma sa ƙiyayya tsakaninka da macen, tsakanin zuriyarka da zuriyarta. Zai ragargaje kanka, kai kuma za ka sari ɗiɗɗigensa.”

Farawa 6:1-4

Sa’ad da mutane suka fara ƙaruwa a duniya, aka kuma hahhaifi musu ’ya’ya mata, sai ’ya’yan Allah maza suka ga cewa ’ya’yan mutane mata suna da bansha’awa, sai suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura. Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Ruhuna ba zai zauna a cikin mutum har abada ba, saboda shi mai mutuwa ne, kwanakinsa za su zama shekaru ɗari da arba’in ne.” Nefilimawa suna nan a duniya a waɗancan kwanaki, da kuma kwanakin da suka bi baya, a sa’ad da ’ya’yan Allah suka kwana da ’ya’yan mutane mata, suka kuma hahhaifi musu ’ya’ya. Ai, su ne jarumawan dā, mutanen da suka shahara.

Firistoci 17:7

Kada kuma su ƙara yin hadayunsu ga gumaka masu siffar bunsurai waɗanda suka bauta wa. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a gare su wa tsararraki masu zuwa.’

Firistoci 19:31

“ ‘Kada ku juya ga masu duba, ko ku nemi shawarar bokaye, gama za ku ƙazantu ta wurinsu. Ni ne Ubangiji Allahnku.

Firistoci 20:6

“ ‘Zan yi gāba da mutumin da ya juyo ga masu duba da bokaye, don yă yi karuwanci ta wurin bin su, zan kuma raba shi daga mutanensa.

Firistoci 20:27

“ ‘Namiji, ko ta macen da yake mai duba, ko maita a cikinku dole a kashe. Za ku jajjefe su da duwatsu; alhakin jininsu zai zauna a kansu.’ ”

Ƙidaya 25:2-3

waɗanda suka gayyace su zuwa wajen hadayu na allolinsu. Mutane suka ci suka kuma yi wa waɗannan alloli sujada. Ta haka Isra’ila suka sa kai a bautar gumaka Ba’al-Feyor. Ubangiji kuwa ya husata da su.

Maimaitawar Shari’a 18:10-11

Kada a sami wani a cikinku da ya miƙa ɗansa, ko ’yarsa a wuta, ko a sami mai duba, ko mai maita, ko mai fassara gaibi, ko mai sihiri, ko boka, ko mabiya, ko maye, ko mai sha’ani da matattu.

Maimaitawar Shari’a 32:17

Suka yi hadaya ga aljanu, waɗanda ba Allah ba, ga allolin da ba su sani ba, ga allolin da aka shigo da su daga baya, allolin da kakanninku ba su ji tsoronsu ba.

Mahukunta 2:11

Sai Isra’ilawa suka yi mugaye abubuwa a gaban Ubangiji suka kuma bauta Ba’al.

1 Sama’ila 5:1-7

Bayan Filistiyawa sun ƙwace akwatin alkawarin Allah, sai suka ɗauke shi daga Ebenezer suka kai shi Ashdod. Sa’an nan suka ɗauki akwatin alkawarin suka kai shi cikin haikalin gunkinsu Dagon, suka ajiye kusa da Dagon. Kashegari da safe da mutanen Ashdod suka farka sai ga Dagon ya fāɗi a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Sai suka ɗauki Dagon suka ajiye a wurin zamansa. Amma kashegari kuma da safe suka farka sai ga Dagon ya fāɗi a ƙasa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji! Kansa ya fashe, hannuwansa kuma sun kakkarye sun zube a madogarar ƙofa; jikinsa ne kaɗai ya rage. Saboda haka firistocin Dagon da waɗanda suke sujada a haikalin Dagon ba sa taka bakin ƙofar Dagon a Ashdod har wa yau. Hannun Ubangiji kuwa ya yi nauyi a bisa Ashdod da kewayenta. Ya kawo hallaka ga dukansu, ya kuma buga su da marurai. Da mutanen Ashdod suka ga abin da yake faruwa, sai suka ce, “Lalle Akwatin Alkawarin Allah na Isra’ila ba zai kasance da mu ba, domin hannunsa yana da nauyi a kanmu da bisan Dagon allahnmu.”

1 Sama’ila 16:14-16

To, fa, Ruhun Ubangiji ya riga ya rabu da Shawulu, sai mugun ruhu daga Ubangiji ya soma ba shi wahala. Ma’aikatan Shawulu suka ce masa, “Duba, ga mugun ruhu daga Allah yana ba ka wahala. Ranka yă daɗe, muna so ka ba mu izini mu tafi, mu nemo wanda ya iya kiɗan molo, domin duk sa’ad da mugun ruhun nan daga Allah ya tashi, sai yă kaɗa molon don hankalinka yă kwanta.”

1 Sama’ila 16:23

Duk lokacin da ruhun nan daga Allah ya sauko a kan Shawulu, sai Dawuda yă ɗauki molonsa yă kaɗa. Sa’an nan sauƙi yă zo wa Shawulu, mugun ruhu kuma yă rabu da shi.

1 Sama’ila 18:10

Kashegari, mugun ruhu daga Allah ya fāɗo wa Shawulu da tsanani. Yana annabci a gidansa, Dawuda kuwa yana bugan molo kamar yadda ya saba. Shawulu yana riƙe da māshi a hannunsa.

1 Sama’ila 19:9

Amma mugun ruhu daga Ubangiji ya sauko wa Shawulu yayinda yana zaune a cikin gidansa da māshi a hannunsa. Yayinda Dawuda yake bugan molo,

1 Sarakuna 11:5-7

Ya bi Ashtarot, alliyar Sidoniyawa, da Molek, allahn da aka hana na Ammonawa. Saboda haka Solomon ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji. Bai bi Ubangiji gaba ɗaya kamar yadda Dawuda mahaifinsa ya yi ba. A kan tudu, gabas da Urushalima, Solomon ya gina masujada a can domin Kemosh, allahn da aka hana na Mowab, da Molek, allahn da aka hana na Ammonawa.

1 Sarakuna 22:19-23

Mikahiya ya ci gaba, “Saboda haka ka ji maganar Ubangiji. I, na ga Ubangiji zaune a kursiyinsa tare da dukan rundunar sama tsaye kewaye da shi a dama da hagunsa. Kuma Ubangiji ya ce, ‘Wa zai ruɗi Ahab zuwa yaƙi da Ramot Gileyad, yă kuma kai shi mutuwarsa a can?’ “Wani ya ce wannan, wani ya ce wancan. A ƙarshe, wani ruhu ya zo gaba, ya tsaya a gaban Ubangiji ya ce, ‘Zan ruɗe shi.’ “Ubangiji ya yi tambaya ‘Ta wace hanya?’ Ya ce, “ ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawansa.’ “Ubangiji ya ce, ‘Za ka yi nasara a ruɗinsa. Ka tafi, ka yi haka.’ “Saboda haka yanzu Ubangiji ya sa ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawanka. Ubangiji ya zartar maka da masifa.”

2 Sarakuna 17:16-17

Suka wofinta dukan umarnan Ubangiji Allahnsu, suka yi wa kansu gumakan zubi na siffar ’yan maruƙa biyu, da kuma ginshiƙin Ashera. Suka rusuna wa rundunan taurari, suka kuma yi wa Ba’al sujada. Suka miƙa ’ya’yansu maza da mata hadaya ta wuta. Suka yi duba, suka yi sihiri suka kuma ba da kansu ga mugunta a gaban Ubangiji; suka sa ya yi fushi.

2 Sarakuna 23:24

Ban da haka, Yosiya ya kawar da masu duba, da masu maita, da allolin gidaje, da gumaka, da duk wani abin banƙyaman da ya gani a Yahuda da Urushalima. Ya yi wannan domin yă cika wa’adodin shari’a yadda suke a littafin da Hilkiya firist ya samu a haikalin Ubangiji.

1 Tarihi 10:13

Shawulu ya mutu domin rashin aminci ga Ubangiji; bai kiyaye maganar Ubangiji ba, ya ma nemi shawarar mace mai duba,

1 Tarihi 21:1

Sai Shaiɗan ya tashi gāba da Isra’ila, ya zuga Dawuda ya ƙidaya Isra’ila.

2 Tarihi 11:15

Yerobowam ya naɗa firistocinsa domin masujadan kan tudu da kuma domin gumakan nan na akuya da maraƙin da ya yi.

2 Tarihi 33:6

Ya miƙa ’ya’yansa maza hadaya a wuta cikin Kwarin Ben Hinnom, ya yi bokanci, ya yi duba, ya kuma yi maitanci, ya nemi shawarar mabiya da masu ruhohi. Ya yi abin da yake mugu ƙwarai a gaban Ubangiji, yana tsokanarsa yă yi fushi.

Ayuba 1:6-12

Wata rana mala’iku suka kawo kansu gaban Ubangiji, Shaiɗan shi ma ya zo tare da su. Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Daga ina ka fito?” Shaiɗan ya amsa wa Ubangiji ya ce, “Daga yawo a duniya ina kai da kawowa a cikinta.” Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ko ka ga bawana Ayuba? A cikin duniya babu wani kamar sa; shi marar laifi ne, adali kuma, mutum ne mai tsoron Allah, ba ruwansa da mugunta.” Sai Shaiɗan ya amsa ya ce, “Haka kawai Ayuba yake tsoron Allah? Ba ka kāre shi da iyalinsa gaba ɗaya da duk mallakarsa ba? Ka Albarkaci ayyukan hannunsa yadda dabbobinsa duk sun cika ko’ina. Ka ɗan miƙa hannunka ka raba shi da duk abin da yake da shi, ba shakka zai la’anta ka kana ji, kana gani.” Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, duk abin da yake da shi yana hannunka, amma kada ka taɓa shi, shi kansa.” Sai Shaiɗan ya bar Ubangiji.

Ayuba 2:1-7

Wata rana kuma mala’iku suka sāke kawo kansu gaban Ubangiji, sai Shaiɗan shi ma ya zo tare da su yă nuna kansa a gabansa. Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Daga ina ka fito?” Shaiɗan ya amsa wa Ubangiji ya ce, “Daga yawo a duniya ina kai da kawowa a cikinta.” Sai Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Ko ka ga bawana Ayuba? A cikin duniya babu wani kamar sa; shi marar laifi ne, adali kuma, mutum ne mai tsoron Allah ba ruwansa da mugunta. Kuma har yanzu bai fasa zama mai aminci ba duk da wahalar da ka sa na bari ka ba shi ba tare da wani dalili ba.” Shaiɗan ya amsa ya ce, “Fata don fata! Mutum zai iya rabuwa da duk abin da yake da shi domin ransa. Ka ɗan taɓa lafiyar jikinsa ka gani ba shakka zai la’anta ka kana ji kana gani.” Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, duk abin da yake da shi yana hannunka, amma kada ka taɓa shi, shi kansa.” Sai Shaiɗan ya bar Ubangiji, ya je ya sa wa Ayuba ƙuraje masu zafi a jikinsa daga tafin ƙafafunsa har zuwa kansa.

Zabura 106:37-38

Suka miƙa ’ya’yansu maza hadaya ’yan matansu kuma ga aljanu. Suka zub da jini marar laifi, jinin ’ya’yansu maza da mata, waɗanda suka miƙa hadaya ga gumakan Kan’ana, ƙasar kuwa ta ƙazantu ta wurin jininsu.

Ishaya 14:9-11

Kabari a ƙarƙashi duk ya shirya don yă sadu da kai a zuwanka; yana tā da ruhohin da suka rasu don su gaishe ka, dukan waɗanda sun taɓa zama shugabanni a duniya; ya sa suka tashi daga kujerun sarauta, dukan waɗanda suke sarakuna a kan al’ummai. Duk za su amsa, za su ce maka, “Ashe kai ma raunana ne, kamar mu; ka zama kamar mu.” An yi ƙasa da dukan alfarmarka zuwa kabari, tare da surutan garayunka; tsutsotsi sun bazu a ƙarƙashinka tsutsotsi kuma suka rufe ka.

Ishaya 14:12-15

Yaya aka yi ka fāɗo daga sama Ya tauraron safiya, ɗan hasken asuba! An fyaɗa ka da ƙasa, kai da ka taɓa ƙasƙantar da al’ummai! Ka yi tunani a ranka ka ce, “Zan hau zuwa sama; zan ɗaga kursiyina sama da taurarin Allah; zan zauna a kursiyi a kan dutsen taro, a can ƙurewar saman dutse mai tsarki. Zan haura can bisa gizagizai; zan mai da kaina kamar Mafi Ɗaukaka.” Amma ga shi an gangara da kai zuwa kabari, zuwa zurfafan rami.

Ishaya 14:16-17

Waɗanda suka gan ka sun zura maka ido, suna tunani abin da zai same ka. “Wannan mutumin ne ya girgiza duniya ya kuma sa mulkoki suka razana, mutumin da ya mai da duniya ta zama hamada, wanda ya tumɓuke biranenta bai kuma bar kamammunsa suka tafi ba?”

Ishaya 14:29

Kada ku yi farin ciki, dukanku Filistiyawa, cewa sandar da ta buge ku ta karye; daga saiwar wannan maciji wani mugun maciji mai dafi zai taso, ’ya’yansa za su zama wani maciji masu dafi mai tashi sama.

Ishaya 27:1

A wannan rana, Ubangiji zai yi hukunci da takobi, takobinsa mai tsanani, mai ƙarfi da kuma mai muguwar ɓarna, zai hukunta dodon ruwa macijin nan da ya kanannaɗe, dodon ruwa macijin nan mai murɗewa; zai kashe dodon nan na teku.

Ishaya 30:6

Allah ya faɗa game da dabbobin Negeb cewa, Ta cikin ƙasa mai wahala da mai hatsari inda zakoki da zakanya, inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke, jakadu na ɗaukan arzikinsu a kan jakuna, dukiyarsu a kan raƙuma, zuwa ƙasan nan marar riba,

Irmiya 50:2

“Ka yi shela ka kuma furta a cikin al’ummai, ka tā da tuta ka kuma furta; kada ku ɓoye kome, amma ku ce, ‘Za a ci Babilon da yaƙi; za a kunyata Bel, Marduk ya cika da tsoro. Siffofinta za su sha kunya gumakanta za su cika da tsoro.’

Ezekiyel 28:12-15

“Ɗan mutum, ka yi makoki domin sarkin Taya ka kuma ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Ka kasance hatimin cikakke, cike da hikima da cikakke a kyau. Ka kasance a Eden, a lambun Allah; aka yi maka ado da kowane dutse mai daraja, yakutu, tofaz, da zumurrudu, kirisolit, onis da yasfa, saffaya, turkuwoyis da beril. Tsare-tsare da shirye-shiryenka an yi su da zinariya ne; a ranar da aka halicce ka an shirya su. An shafe ka kamar kerub mai tsaro, gama haka na naɗa ka. Kana a tsattsarkan dutsen Allah; ka yi tafiya a tsakiyar duwatsun wuta. Ka kasance marar laifi cikin dukan hanyoyinka daga ranar da aka halicce ka sai da aka sami mugunta a cikinka.

Ezekiyel 28:16-19

Ta wurin yawan kasuwancinka ka cika da rikici, ka kuma yi zunubi. Saboda haka na kore ka da kunya daga dutsen Allah, na kore ka, ya kerub mai tsaro, daga cikin duwatsun wuta. Zuciyarka ta cika da alfarma saboda kyanka, ka kuma lalace hikimarka saboda darajarka. Saboda haka na jefar da kai zuwa ƙasa; na sa ka zama abin kallo a gaban sarakuna. Ta wurin yawan zunubanka da kasuwancinka na cuta ka ƙazantar da wuri mai tsarkinka. Saboda haka na sa wuta ta fito daga cikinka, ta cinye ka, na maishe ka toka a bisa ƙasa a kan idon dukan waɗanda suke kallonka. Dukan al’umman da suka san ka sun giggice saboda masifar da ta auko maka; ka zo ga mummunar ƙarshe ba za ka ƙara kasancewa ba har abada.’ ”

Daniyel 10:12-13

Sai ya ci gaba da cewa, “Kada ka ji tsoro, Daniyel. Gama tun daga ran da ka fara sa zuciya ga neman ganewa, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allahnka, an ji addu’arka, amsar addu’arka ce ta kawo ni. Amma mai mulkin masarautar Farisa ya tsare ni har kwana ashirin da ɗaya. Sai da Mika’ilu, ɗaya daga cikin manya shugabanni, ya zo ya taimake ni, saboda an tsare ni a can tare da sarkin Farisa.

Daniyel 10:20-21

Sai ya ce mini, “Ka san abin da ya kawo ni gare ka? Ba da jimawa ba zan koma in yi yaƙi da mai mulkin Farisa, kuma idan na tafi, mai mulkin Hellenawa zai taso; amma da farko zan faɗa maka abin da aka rubuta a cikin Littafin Gaskiya (Babu wanda ya taimake ni yaƙi da waɗannan sai dai Mika’ilu, sarkinku.

Zakariya 3:1-2

Sa’an nan ya nuna mini Yoshuwa babban firist a tsaye a gaban mala’ikan Ubangiji, Shaiɗan kuma yana tsaye a damansa don yă tuhume shi. Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “ Ubangiji ya tsawata maka, Shaiɗan! Ubangiji wanda ya zaɓi Urushalima, ya tsawata maka! Ashe, mutumin nan ba shi ne sandar da take ƙonewa da aka ciro daga cikin wuta ba?”

Zakariya 13:2

“A ranan nan, zan kawar da sunayen gumaka daga ƙasar, ba kuwa za a ƙara tunawa da su ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan kawar da annabawa da kuma ruhu marar tsabta daga ƙasar.

Mattiyu 4:1-11

Sa’an nan Ruhu ya kai Yesu cikin hamada don Iblis yă gwada shi. Bayan ya yi azumi yini arba’in da kuma dare arba’in, sai ya ji yunwa. Sai mai gwajin ya zo wurinsa ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka ce wa duwatsun nan su zama burodi.” Yesu ya amsa ya ce, ‹“A rubuce yake cewa, ‘Ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah.’›‹”› Sai Iblis ya kai shi birni mai tsarki, ya kai shi can wuri mafi tsayi duka na haikali. Ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, yi tsalle ka sauka ƙasa. Gama a rubuce yake, “ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai, za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’” Yesu ya amsa masa ya ce, ‹“A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’›‹”› Har wa yau, Iblis ya kai shi bisa wani dutse mai tsawo sosai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu. Ya ce, “Zan ba ka dukan wannan, in za ka durƙusa ka yi mini sujada.” Sai Yesu ya ce masa, ‹“Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake, ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’›‹”› Sa’an nan Iblis ya bar shi, mala’iku kuwa suka zo suka yi masa hidima.

Mattiyu 4:24

Labarinsa ya bazu ko’ina a Suriya, mutane kuwa suka kawo masa dukan waɗanda suke fama da cututtuka iri-iri, da waɗanda suke da zafin ciwo, da masu aljanu, da waɗanda suke masu farfaɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.

Mattiyu 7:21-23

‹“Ba duk mai ce mini, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ne zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda yake aikata nufin Ubana da yake sama.› ‹Da yawa za su ce mini a wannan rana, ‘Ubangiji, Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, ba kuma a cikin sunanka ne muka fitar da aljanu, muka yi abubuwan banmamaki da yawa ba?’› ‹Sa’an nan zan ce musu a fili, ‘Ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!’›

Mattiyu 8:16

Da yamma ta yi, aka kawo masa masu aljanu da yawa, ya kuwa fitar da ruhohin ta wurin magana, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya.

Mattiyu 8:28-33

Da ya isa ɗayan gefen a yankin Gadarenawa (ko kuwa Gerasenawa), sai ga mutum biyu masu aljanu suna fitowa daga kaburbura suka tarye shi. Su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bin wannan hanya. Suka yi ihu suka ce, “Me ya haɗa ka da mu, Ɗan Allah?” Ka zo ne nan don ka ji mana kafin lokaci yă yi? Nesa kaɗan da su kuwa akwai babban garken aladu da yake kiwo. Aljanun suka roƙi Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.” Ya ce musu, ‹“Ku tafi!”› Sai suka fita suka shiga cikin aladun, dukan garken kuwa ya gangara a guje daga kan tudun zuwa cikin tafkin aladun kuma suka mutu a cikin ruwa. Masu kiwon aladun suka ruga, suka je cikin gari suka ba da labarin dukan wannan, haɗe da abin da ya faru da mutanen nan masu aljanu.

Mattiyu 9:32-34

Yayinda suke fitowa, sai aka kawo wa Yesu wani mutum mai aljani, da ba ya iya magana. Sa’ad da aka fitar da aljanin kuwa, sai beben ya yi magana. Taron suka yi mamaki suka ce, “Ba a taɓa ganin irin wannan abu a Isra’ila ba.” Amma Farisiyawa suka ce, “Ai, da ikon sarkin aljanu yake fitar da aljanu.”

Mattiyu 10:1

Sai ya kira almajiransa goma sha biyu wurinsa ya kuma ba su iko su fitar aljanu, su kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.

Mattiyu 10:8

‹Ku warkar da marasa lafiya, ku tā da matattu, ku tsabtacce kutare, ku kuma fitar da aljanu. A kyauta kuka samu, ku kuma bayar a kyauta.›

Mattiyu 12:22-23

Sai aka kawo masa wani bebe kuma makaho mai aljani, Yesu kuwa ya warkar da shi, har ya iya magana ya kuma sami ganin gari. Dukan mutane suka yi mamaki, suka ce, “Wannan Ɗan Dawuda ne kuwa?”

Mattiyu 12:24-32

Amma da Farisiyawa suka ji haka, sai suka ce, “Ahab, da Be’elzebub sarkin aljanu ne kaɗai, wannan mutum yake fitar da aljanu.” Yesu kuwa ya san tunaninsu sai ya ce musu, ‹“Duk mulkin da yake gāba da kansa zai lalace, kuma duk birni ko gidan da yake rabe gāba da kansa ba zai ɗore ba.› ‹In Shaiɗan yana fitar da Shaiɗan, ai, ya rabu yana gāba da kansa ke nan. Yaya kuwa mulkinsa zai ɗore?› ‹In kuwa ta wurin Be’elzebub nake fitar da aljanu, to, ta wa mutanenku suke fitar da su? Saboda haka, su ne za su zama alƙalanku.› ‹Amma in ina fitar da aljanu ta wurin Ruhun Allah ne, to, fa, mulkin Allah ya zo muku ke nan.› ‹“Ko kuwa, yaya wani zai iya shiga gidan mai ƙarfi yă ƙwace masa kaya ba tare da ya fara daure mai ƙarfin nan tukuna ba? Sa’an nan zai iya washe gidansa.› ‹“Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni ne, kuma wanda ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi.› ‹Saboda haka ina gaya muku, za a gafarta wa mutane kowane zunubi da kuma saɓo, amma saɓo game da Ruhu, ba za a gafarta ba.› ‹Duk wanda ya zargi Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya zargi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, ko a wannan zamani ko a zamani mai zuwa.›

Mattiyu 12:43-45

‹“Sa’ad da mugun ruhu ya fita daga mutum, yakan bi wuraren da ba ruwa yana neman hutu, ba ya kuwa samu.› ‹Sa’an nan yakan ce, ‘Zan koma gidan da na bari.’ Sa’ad da ya iso, ya tarar da gidan ba kowa a ciki, shararre, kuma a kintse.› ‹Sai yă je yă ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, su kuwa zo su shiga su zauna a can. Ƙarshen mutumin nan fa zai fi farkonsa muni. Haka zai zama ga wannan mugun zamani.”›

Mattiyu 13:19

‹Duk sa’ad da wani ya ji saƙo game da mulkin bai kuwa fahimce shi ba, mugun nan yakan zo yă ƙwace abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da ya fāɗi a kan hanya.›

Mattiyu 13:24-28

Yesu ya ba su wani misali. ‹“Mulkin sama yana kama da wani da ya shuka iri mai kyau a cikin gonarsa.› ‹Amma yayinda kowa yake barci, abokin gābansa ya zo ya yafa ciyayi a cikin alkamar, ya tafi abinsa.› ‹Sa’ad da alkamar ta tashi ta yi kawuna, sai ciyayin ma suka bayyana.› ‹“Bayin mai gonar suka zo wurinsa suka ce, ‘Ranka yă daɗe, ashe, ba iri mai kyau ka shuka a gonarka ba? To, ina ciyayin nan suka fito?’› ‹“Sai ya ce, ‘Abokin gāba ne ya yi wannan.’› ‹“Bayin suka tambaye shi suka ce, ‘Kana so mu je mu tuttumɓuke su?’›

Mattiyu 13:38-40

‹Gonar kuwa ita ce duniya, irin nan mai kyau kuwa suna a matsayin ’ya’yan mulkin. Ciyayin nan kuma su ne ’ya’yan mugun nan,› ‹abokin gāban da yake shuka su kuwa, Iblis ne. Lokacin girbi kuma shi ne ƙarshen zamani, masu girbin kuwa su ne mala’iku.› ‹“Kamar yadda aka tattara ciyayin aka kuma ƙone a wuta, haka zai zama a ƙarshen zamani.›

Mattiyu 16:19

‹Zan ba ka mabuɗan mulkin sama; kome ka daure a duniya zai zama a daure a sama, kome kuma ka kunce a duniya zai zama a kunce a sama.”›

Mattiyu 16:21-23

Tun daga wannan lokaci Yesu ya fara bayyana wa almajiransa cewa dole yă tafi Urushalima yă sha wahaloli da yawa a hannun dattawa, manyan firistoci da kuma malaman dokoki, dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi. Bitrus ya ja shi gefe ya fara tsawata masa yana cewa, “Sam, Ubangiji! Wannan ba zai taɓa faruwa da kai ba!” Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, ‹“Rabu da ni, Shaiɗan! Kai abin sa tuntuɓe ne a gare ni; ba ka tunanin al’amuran Allah, sai dai al’amuran mutane.”›

Mattiyu 17:15-18

Ya ce, “Ubangiji, ka yi wa ɗana jinƙai. Yana da farfaɗiya yana kuma shan wahala ƙwarai. Ya sha fāɗuwa cikin wuta ko ruwa. Na kuma kawo shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba.” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Ya ku zamani marasa bangaskiya da kuma masu taurinkai, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe kuma zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron a nan.”› Yesu ya tsawata wa aljanin, ya kuwa rabu da yaron, nan take yaron ya warke.

Mattiyu 18:18

‹“Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka daure a duniya, za a daure a sama, duk kuma abin da kuka kunce a duniya, za a kunce shi a sama.›

Mattiyu 23:33

‹“Ku macizai! ’Ya’yan macizai! Ta yaya za ku tsere wa hukuncin jahannama ta wuta?›

Mattiyu 25:41

‹“Sa’an nan zai ce wa waɗanda suke a hagunsa, ‘Ku rabu da ni, la’anannu, zuwa cikin madawwamiyar wutar da aka shirya don Iblis da mala’ikunsa.›

Markus 1:13

ya kuma kasance a hamada kwana arba’in, Shaiɗan yana gwada shi. Yana tare da namomin jeji, mala’iku kuma suka yi masa hidima.

Markus 1:21-27

Suka tafi Kafarnahum. Da ranar Asabbaci ta kewayo, sai Yesu ya shiga majami’a ya fara koyarwa. Mutane suka yi mamakin koyarwarsa, domin ya koyar da su kamar wanda yake da iko, ba kamar malaman dokoki ba. Nan take, sai wani mutum mai mugun ruhu a majami’arsu, ya ɗaga murya ya ce, “Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki nan na Allah!” Yesu ya tsawata masa ya ce, ‹“Yi shiru! Fita daga cikinsa!”› Sai mugun ruhun ya jijjiga mutumin da ƙarfi, ya fita daga jikinsa da ihu. Dukan mutane suka yi mamaki, suna tambayar juna suna cewa, “Mene ne haka? Tabɗi! Yau ga sabuwar koyarwa kuma da iko! Yana ma ba wa mugayen ruhohi umarni, suna kuma yin masa biyayya.”

Markus 1:32-34

A wannan yamma, bayan fāɗuwar rana, mutane suka kawo wa Yesu dukan marasa lafiya, da masu aljanu. Duk garin ya taru a ƙofar gidan. Yesu kuwa ya warkar da marasa lafiya da yawa da suke da cututtuka iri-iri. Ya kuma fitar da aljanu da yawa, amma bai yarda aljanun suka yi magana ba, don sun san wane ne shi.

Markus 1:39

Sai ya tafi ko’ina a Galili, yana wa’azi a majami’unsu, yana kuma fitar da aljanu.

Markus 3:11-12

Duk sa’ad da mugayen ruhohi suka gan shi, sai fāɗi a gabansa, su ɗaga murya, su ce, “Kai Ɗan Allah ne.” Amma yakan tsawata musu, kada su shaida ko wane ne shi.

Markus 3:14-15

Ya naɗa sha biyu, ya kira su manzanni don su kasance tare da shi, domin kuma yă aike su yin wa’azi, don kuma su sami ikon fitar da aljanu.

Markus 3:22-30

Malaman dokokin da suka zo daga Urushalima suka ce, “Ai, yana da Be’elzebub! Da ikon sarkin aljanu yake fitar da aljanu.” Sai Yesu ya kira su, ya yi musu magana da misalai ya ce, ‹“Yaya Shaiɗan zai fitar da Shaiɗan?› ‹In mulki yana gāba da kansa, wannan mulki ba zai tsaya ba.› ‹In gida yana gāba da kansa, wannan gida ba zai tsaya ba.› ‹In kuwa Shaiɗan yana gāba da kansa, ya kuma rabu biyu, ba zai tsaya ba, ƙarshensa ya zo ke nan.› ‹Tabbatacce, ba mai shiga gidan mai ƙarfi yă kwashe dukiyarsa, sai bayan ya daure mai ƙarfin, sa’an nan zai iya yin fashin gidansa.› ‹Gaskiya nake gaya muku, za a gafarta duk zunubai da kuma saɓon mutane suka yi.› ‹Amma duk wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki, ba za a taɓa gafara masa ba. Ya aikata madawwamin zunubi ke nan.”› Ya faɗi haka domin suna cewa, “Yana da mugun ruhu.”

Markus 4:14-15

‹Manomi yakan shuka maganar Allah.› ‹Waɗansu mutane suna kama da irin da ya fāɗi a kan hanya, inda akan shuka maganar Allah. Da jin maganar, nan da nan sai Shaiɗan yă zo yă ɗauke maganar da aka shuka a zuciyarsu.›

Markus 5:2-19

Da Yesu ya sauka daga jirgin ruwa, sai wani mutum mai mugun ruhu ya fito daga kaburbura, ya tarye shi. Wannan mutumin ya mai da kaburbura gidansa. Kuma ba wanda ya iya daure shi, ko da sarƙa ma. Gama an sha daure shi hannu da ƙafa da sarƙa, amma yakan tsintsinke sarƙar, yă kuma karye ƙarafan da suke ƙafafunsa. Ba wanda yake da ƙarfin da zai iya yă riƙe shi. Dare da rana, sai yă dinga kuka yana ƙuƙƙuje jikinsa da duwatsu a cikin kaburbura da kan tuddai. Da ya hangi Yesu daga nesa, sai ya ruga da gudu, ya zo ya durƙusa a gabansa. Ya yi ihu da babbar murya ya ce, “Ina ruwanka da ni Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ka rantse da Allah cewa ba za ka ba ni azaba ba!” Gama Yesu ya riga ya ce masa, ‹“Ka fita daga jikin mutumin nan, kai mugun ruhu!”› Sai Yesu ya tambaye shi ya ce, ‹“Mene ne sunanka?”› Sai ya amsa ya ce, “Sunana Lejiyon, wato, ‘Tuli,’ domin muna da yawa.” Sai ya yi ta roƙon Yesu, kada yă kore su daga wurin. A kan tudun da yake nan kusa kuwa, akwai wani babban garken aladu, suna kiwo. Sai aljanun suka roƙi Yesu, suka ce, “Tura mu cikin aladun nan, ka bari mu shiga cikinsu.” Ya kuwa yarda musu, sai mugayen ruhohin suka fita suka shiga cikin aladun. Garken kuwa, yana da kusan aladu dubu biyu, suka gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, suka nutse. Masu kiwon aladun kuwa suka ruga da gudu zuwa cikin gari da ƙauyuka, suka ba da wannan labari. Sai mutanen suka fito, domin su ga abin da ya faru. Da suka kai wajen Yesu, sai suka ga mutumin da dā yake da tulin aljanun yana zaune a wurin, sanye da tufafi kuma cikin hankalinsa, sai suka ji tsoro. Waɗanda suka ga abin da ya faru, suka ba da labarin abin da ya faru da mai aljanun, da kuma aladun. Sai mutane suka fara roƙon Yesu yă bar yankinsu. Yesu yana kan shiga cikin jirgin ruwa ke nan, sai mutumin da dā yake da aljanun ya roƙa yă bi shi. Yesu bai yardar masa ba, amma ya ce, ‹“Ka tafi gida wurin iyalinka, ka gaya musu babban alherin da Ubangiji ya yi maka, da yadda ya yi maka jinƙai.”›

Markus 6:7

Ya kira Sha Biyun nan wurinsa, ya aike su biyu-biyu, ya kuma ba su iko bisa mugayen ruhohi.

Markus 6:12-13

Suka fita, suna yi wa’azi, suna ce wa mutane su tuba. Suka fitar da aljanu da yawa, suka shafa wa marasa lafiya da yawa mai, suka kuwa warkar da su.

Markus 7:25-30

Da jin labarinsa, sai wata mace wadda ƙaramar diyarta tana da mugun ruhu, ta zo ta durƙusa a gabansa. Macen kuwa mutuniyar Hellenawa ce, an haife ta a Funisiya a Suriya. Ta roƙi Yesu yă fitar da aljani da yake jikin diyarta. Yesu ya ce mata, ‹“Da farko, bari ’ya’ya su ci su ƙoshi tukuna, gama ba daidai ba ne, a ɗauki burodin yara a jefa wa karnukansu.”› Ta amsa, ta ce, “I, Ubangiji, ko karnuka ma da suke ƙarƙashin tebur, sukan ci burbuɗin da suke fāɗuwa daga abincin yara.” Sai ya ce mata, ‹“Saboda irin wannan amsa, ki tafi, aljanin ya rabu da diyarki.”› Ta tafi gida, ta tarar da diyarta kwance a gado, aljanin kuwa ya fita.

Markus 8:31-33

Sai ya fara koya musu cewa, dole Ɗan Mutum yă sha wahaloli da yawa, dattawa, manyan firistoci da malaman dokoki kuma su ƙi shi. Dole kuma a kashe shi, bayan kwana uku kuma, yă tashi. Ya yi wannan zance a sarari. Sai Bitrus ya jawo shi gefe, ya fara tsawata masa. Amma da Yesu ya juya ya dubi almajiransa, sai ya tsawata wa Bitrus ya ce, ‹“Tashi daga nan Shaiɗan! Ba ka da al’amuran Allah a zuciyarka, sai na mutane.”›

Markus 9:17-29

Wani mutum a cikin taron ya amsa ya ce, “Malam, na kawo maka ɗana mai wani ruhun da yake hana shi magana. Duk lokacin da mugun ruhun ya kama shi, yakan jefa shi a ƙasa. Bakinsa yakan yi kumfa, yă cije haƙorarsa, yakan sa jikinsa ya sandare, yă zama da ƙarfi. Na roƙi almajiranka su fitar da ruhun, amma ba su iya ba.” Yesu ya ce, ‹“Ya ku zamani marar bangaskiya, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron.”› Sai suka kawo shi. Da ruhun ya ga Yesu, nan da nan sai ya buge yaron da farfaɗiya. Ya fāɗi a ƙasa, yana birgima, bakinsa yana kumfa. Yesu ya tambayi mahaifin yaron ya ce, ‹“Tun yaushe yake haka?”› Ya ce, “Tun yana ƙarami. Ya sha jefa shi cikin wuta, ko ruwa don yă kashe shi. Amma in za ka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimake mu.” Yesu ya ce, ‹“ ‘In za ka iya’? Ai, kome mai yiwuwa ne ga wanda ya gaskata.”› Nan da nan mahaifin yaron ya faɗa da ƙarfi ya ce, “Na gaskata, ka taimake ni in sha kan rashin bangaskiyata!” Da Yesu ya ga taron suna zuwa can a guje, sai ya tsawata wa mugun ruhun ya ce, ‹“Kai ruhun kurma, da na bebe, na umarce ka, ka fita daga cikinsa, kada kuma ka ƙara shigarsa.”› Sai ruhun ya yi ihu, ya buge shi da ƙarfi da farfaɗiya, ya fita. Yaron ya kwanta kamar matacce, har mutane da yawa suka ce, “Ai, ya mutu.” Amma Yesu ya kama shi a hannu ya ɗaga, ya kuwa tashi tsaye. Da Yesu ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi a ɓoye, suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da shi ba?” Ya amsa ya ce, ‹“Sai da addu’a›‹kaɗai irin wannan yakan fita.”›

Markus 16:9

Da Yesu ya tashi daga matattu da safe, a ranar farko ta mako, ya fara bayyana ga Maryamu Magdalin, wadda ya fitar da aljanu bakwai daga cikinta.

Markus 16:16-17

‹Duk wanda ya gaskata, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma duk wanda bai gaskata ba kuwa, zai hallaka.› ‹Waɗannan alamu za su kasance tare da waɗanda suka gaskata. A cikin sunana za su fitar da aljanu, za su yi magana da sababbin harsuna.›

Luka 4:1-13

Yesu kuwa cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dawo daga Urdun, Ruhu kuma ya kai shi cikin hamada, inda kwana arba’in, Iblis ya gwada shi. Bai ci kome ba a cikin kwanakin nan, a ƙarshensu kuwa ya ji yunwa. Iblis ya ce masa, “In kai Ɗan Allah ne, ka faɗa wa wannan dutse yă zama burodi.” Yesu ya amsa ya ce, ‹“A rubuce yake, ‘Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba.’›‹”› Iblis ya kai shi can kan wani wuri mai tsawo, ya nunnuna masa a ƙyiftawar ido dukan mulkokin duniya. Ya ce masa, “Zan ba ka dukan ikonsu da darajarsu, gama ni aka danƙa wa, kuma zan bai wa duk wanda na ga dama. Saboda haka in ka yi mini sujada, dukan wannan zai zama naka.” Yesu ya amsa ya ce, ‹“A rubuce yake, ‘Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta wa.’›‹”› Sai Iblis, ya kai shi Urushalima ya sa ya tsaya a kan wuri mafi tsayi na haikali ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka yi tsalle daga nan zuwa ƙasa. Gama a rubuce yake, “ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai, su kiyaye ka da kyau; za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’” Yesu ya amsa ya ce, ‹“An ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’›‹”› Da Iblis ya gama dukan wannan gwajin, ya bar shi sai lokacin da wata dama ta samu.

Luka 4:32-36

Suka yi ta mamakin koyarwarsa, domin saƙonsa yana da iko. A cikin majami’ar, akwai wani mutum mai aljani, wani mugun ruhu. Mutumin ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki na Allah!” Yesu ya tsawata masa da ƙarfin cewa, ‹“Yi shiru! Ka fita daga cikinsa!”› Sai aljanin ya fyaɗa mutumin da ƙasa a gabansu duka, sa’an nan ya fita, ya bar shi ba wani rauni. Dukan mutanen suka yi mamaki, suka ce wa junansu, “Wace irin koyarwa ce haka? Da ƙarfi da iko, yana ba wa mugayen ruhohin umarni suna kuma fita!”

Luka 4:40-41

Rana tana fāɗuwa, sai mutane suka yi ta kawo wa Yesu dukan waɗanda suke da cuta iri-iri, sai ya ɗibiya wa kowannensu hannuwansa, ya warkar da su. Bugu da ƙari, aljanu suka fiffita daga cikin mutane da yawa suna ihu suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne!” Amma ya kwaɓe su, ya hana su magana, don sun san cewa shi ne Kiristi.

Luka 6:18

waɗanda suka zo domin su ji shi, a kuma warkar da cututtukansu. Waɗanda suke fama da mugayen ruhohi kuwa aka warkar da su.

Luka 7:21

A daidai lokacin nan, Yesu ya warkar da mutane da yawa masu ciwo, masu cututtuka, da kuma masu mugayen ruhohi. Ya kuma ba makafi da yawa ganin gari.

Luka 8:2

da kuma waɗansu mata waɗanda aka warkar da su daga cututtukansu, da kuma mugayen ruhohi. Cikinsu akwai Maryamu (wadda ake kira Magdalin) wadda aljanu bakwai suka fito daga cikinta.

Luka 8:11-12

‹“Ga ma’anar misalin, irin, shi ne maganar Allah.› ‹Waɗanda suka fāɗi a kan hanya su ne mutanen da suka ji, amma Iblis, yakan zo ya ɗauke maganar daga zuciyarsu, don kada su gaskata, su sami ceto.›

Luka 8:27-39

Da Yesu ya sauka daga jirgin, sai ga wani mutum mai aljanu daga garin. Mutumin ya daɗe bai sa tufafi ba, kuma ba ya zama a gida. Yana zama a cikin kaburbura. Da ya ga Yesu, sai mutumin ya ɗaga murya da ƙarfi, ya fāɗi a gabansa, yana ihu cewa, “Ina ruwanka da ni, Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ina roƙonka, kada ka ba ni wahala!” Gama Yesu ya riga ya umarci mugun ruhun ya fita daga mutumin. Sau da yawa mugun ruhun ya sha kamunsa. Ko da yake akan daure shi hannu da ƙafa, da sarƙa, a kuma yi gadinsa, amma yakan tsinke sarƙoƙinsa, aljanun kuma su kore shi zuwa wuraren kaɗaici, inda ba kowa. Yesu ya tambaye shi, ‹“Mene ne sunanka?”› Sai ya amsa, “Tuli,” gama aljanu masu ɗumbun yawa ne suna cikinsa. Suka yi ta roƙonsa kada yă umarce su su shiga ramin Abis. A wurin kuwa, akwai babban garken aladu da suke kiwo a gefen tudu. Aljanun suka roƙi Yesu ya bar su, su shiga cikin aladun, ya kuwa yardar musu. Da aljanun suka fita daga cikin mutumin, sai suka shiga cikin aladun. Garken kuma ya gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, kuma suka nutse. Da masu kiwon aladun suka ga abin da ya faru, sai suka ruga da gudu zuwa garin da kewaye suka kai labari. Mutanen kuma suka fito don su ga abin da ya faru. Da suka iso wurin Yesu, sai suka tarar da mutumin da aljanun suka fita daga cikinsa, yana zaune kusa da Yesu sanye da tufafi, kuma cikin hankalinsa, sai tsoro ya kama su. Waɗanda suka ga abin da faru, suka gaya wa mutanen yadda aka warkar da mai aljanun. Sai dukan mutanen yankin Gerasenawa suka roƙi Yesu ya bar su, don sun tsorata sosai. Sai Yesu ya shiga jirgin ruwa ya tafi. Mutumin da aka fitar da aljanun daga cikinsa, ya roƙi Yesu don yă tafi tare da shi, amma Yesu ya sallame shi ya ce, ‹“Koma gida, ka shaida babban alherin da Allah ya yi maka.”› Sai mutumin ya tafi yana faɗin abin da Yesu ya yi masa a duk garin.

Luka 9:1

Bayan da Yesu ya tara Sha Biyun wuri ɗaya, sai ya ba su iko da izini na fitar da dukan aljanu, da na warkar da cututtuka.

Luka 9:38-43

Sai wani mutum daga cikin taron ya yi kira da ƙarfi ya ce, “Malam, ina roƙonka, ka dubi ɗan nan nawa, gama shi ne kaɗai nake da shi. Wani ruhu yakan kama shi, sai ya yi ihu farar ɗaya. Yakan sa shi farfaɗiya, har bakinsa ya yi kumfa. Da ƙyar yake barinsa, yana kuwa kan hallakar da shi. Na roƙi almajiranka su fitar da shi, amma ba su iya ba.” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Ya karkataccen zamani marar bangaskiya, har yaushe ne zan kasance tare da ku, ina kuma haƙuri da ku? Kawo yaronka nan.”› Yaron yana kan zuwa ke nan, sai aljanin ya buga shi ƙasa, cikin farfaɗiya. Amma Yesu ya kwaɓe mugun ruhun, ya warkar da yaron, sai ya miƙa shi ga mahaifinsa. Duk suka yi mamakin girman Allah.

Luka 10:17-20

Mutum saba’in da biyun nan suka dawo da murna, suka ce, “Ubangiji, har mun sha ƙarfin aljanu ma a cikin sunanka.” Sai ya amsa ya ce, ‹“Na ga Shaiɗan ya fāɗi daga sama kamar walƙiya.› ‹Na ba ku iko da za ku tattaka macizai, da kunamai, ku kuma shawo kan dukan ikon abokin gāba, kuma ba wani lahani da zai same ku.› ‹Duk da haka, kada ku yi farin ciki da cewa, kun sha ƙarfin ruhohi, amma ku yi farin ciki, domin an rubuta sunayenku a sama.”›

Luka 11:14-20

Sa’ad da Yesu yake fitar da wani beben aljani daga wani mutum, da aljanin ya fita, sai mutumin wanda da bebe ne, ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki. Amma waɗansunsu suka ce, “Ai, da ikon Be’elzebub, sarkin aljanu ne, yake fitar da aljanu.” Waɗansu kuma suka gwada shi, ta wurin neman yă nuna musu wata alama daga sama. Yesu kuwa ya san tunaninsu, sai ya ce musu, ‹“Duk mulkin da yake gāba da kansa, zai lalace, kuma gidan da yake gaba da kansa zai rushe.› ‹In Shaiɗan yana gāba da kansa, yaya mulkinsa zai tsaya? Ina faɗin haka domin kun ce, da ikon Be’elzebub nake fitar da aljanu.› ‹In da ikon Be’elzebub nake fitar da su, to, da ikon wa masu binku suke fitar da su? Saboda haka, za su zama alƙalanku ke nan.› ‹Amma in da ikon Allah ne ni nake fitar da aljanu, ashe, mulkin Allah ya zo muku ke nan.›

Luka 11:21-26

‹“Sa’ad da mutum mai ƙarfi, wanda yake da makamai yana gadin gidan kansa, an tsare lafiyar dukiyarsa ke nan.› ‹Amma in wani wanda ya fi shi ƙarfi, ya faɗa masa ya kuma sha ƙarfinsa, yakan ƙwace makaman da mutumin ke dogara da su, ya kuma rarraba ganima.› ‹“Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni, wanda kuma ba ya tarawa da ni, watsarwa yake yi.› ‹“Lokacin da mugun ruhu ya fita daga mutum, sai ya bi ta wuraren da ba mutane, yana neman hutu, amma ya kāsa samu, sai ya ce, ‘Zan koma gidan da na bari.’› ‹Sa’ad da ya koma, ya tarar da gidan a share da tsabta, kuma a shirye.› ‹Sai ya je ya ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, sai su shiga su zauna a wurin. Ƙarshen wannan mutum kuwa zai fi farkonsa muni.”›

Luka 13:11

a wurin kuwa, akwai wata mace wadda aljani ya gurgunta, har na shekaru goma sha takwas. Duk ta tanƙware, ba ta ma iya miƙewa ko kaɗan.

Luka 13:16

‹Ashe, bai kamata a ’yantar da macen nan, diyar zuriyar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya daure, har shekara goma sha takwas, a ranar Asabbaci, daga abin da ya daure ta ba?”›

Luka 22:3-4

Shaiɗan kuwa ya shiga Yahuda, wanda ake kira Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun. Sai Yahuda ya je ya tattauna da manyan firistoci, da ma’aikatan ’yan gadin haikali, a kan yadda zai ba da Yesu a gare su.

Luka 22:31-32

‹“Siman, Siman, Shaiɗan ya nemi izini ya sheƙe ka›‹kamar alkama.› ‹Amma na yi maka addu’a, Siman, domin kada bangaskiyarka ta kāsa. Bayan ka juyo, ka ƙarfafa ’yan’uwanka.”›

Yohanna 8:44

‹Ku na ubanku ne, Iblis, kuna kuwa so ku aikata abin da ubanku yake so. Shi mai kisankai ne tun farko. Ba ruwansa da gaskiya, gama gaskiya ba ta cikinsa. Yayinda yake ƙarya, yana yin halinsa ne, gama shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.›

Yohanna 10:19-21

Saboda waɗannan kalmomi fa, sai ɓaraka ta sāke shiga cikin Yahudawa. Da yawa daga cikinsu suka ce, “Yana da aljani, yana kuma hauka. Don me za ku saurare shi?” Amma waɗansu suka ce, “Kai, waɗannan kalmomi ba na mai aljani ba ne. Anya, aljani yana iya buɗe idanun makaho?”

Yohanna 13:2

Ana cikin cin abincin yamma, Iblis kuwa ya riga ya zuga Yahuda Iskariyot, ɗan Siman yă bashe Yesu.

Yohanna 13:26-27

Yesu ya amsa ya ce, ‹“Shi ne wanda zan ba shi gutsurin burodin nan sa’ad da na tsoma cikin kwanon.”› Da ya tsoma gutsurin burodin, sai ya ba wa Yahuda Iskariyot, ɗan Siman. Nan take bayan Yahuda ya karɓi burodin, sai Shaiɗan ya shige shi. Sai Yesu ya ce masa, ‹“Abin nan da kake niyyar yi, ka yi shi maza.”›

Ayyukan Manzanni 5:3-4

Sai Bitrus ya ce, “Ananiyas, ta yaya Shaiɗan ya cika zuciyarka haka da ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya ka kuma ajiye wa kanka sauran kuɗin da ka karɓa na filin? Ba naka ba ne kafin ka sayar da shi? Bayan da ka sayar da shi kuma, kuɗin ba naka ba ne? Me ya sa ka yi tunanin yin irin wannan abu? Ba mutum ne ka yi wa ƙarya ba, Allah ne ka yi masa.”

Ayyukan Manzanni 5:16

Jama’a ma suka tattaru daga garuruwa kewaye da Urushalima suna kawo marasa lafiyarsu da kuma waɗanda mugayen ruhohi suke damun su, dukansu kuwa suka warke.

Ayyukan Manzanni 8:7

Mugayen ruhohi suka fiffito suna kururuwa daga cikin mutane da yawa, shanyayyu da guragu masu yawa suka sami warkarwa.

Ayyukan Manzanni 10:38

yadda Allah ya shafe Yesu Banazare da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da kuma yadda ya zaga ko’ina yana aikata alheri yana kuma warkar da dukan waɗanda suke ƙarƙashin ikon Iblis, domin Allah yana tare da shi.

Ayyukan Manzanni 13:8-12

Amma Elimas mai sihirin nan (domin ma’anar sunansa ke nan) ya yi hamayya da maganarsu ya kuma yi ƙoƙari ya juyar da muƙaddas ɗin daga bangaskiya. Sai Shawulu, wanda kuma ake kira Bulus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya kafa wa Elimas ido ya ce, “Kai ɗan Iblis ne abokin gāban dukan abin da yake daidai! Kana cike da kowane irin ruɗi da munafunci. Ba za ka daina karkata hanyoyin da suke daidai na Ubangiji ba? Ga shi hannun Ubangiji yana gāba da kai. Za ka makance, kuma ba za ka ga rana ba har na wani lokaci.” Nan take, hazo da duhu suka sauko a kansa, ya yi ta lallubawa, yana neman wanda zai yi masa jagora. Sa’ad da muƙaddas ɗin ya ga abin da ya faru, sai ya ba da gaskiya, gama ya yi mamaki a kan da koyarwa game Ubangiji.

Ayyukan Manzanni 16:16-19

Wata rana muna tafiya zuwa wurin yin addu’a, sai muka sadu da wata baranya mai ruhun aljani mai duba. Takan samo wa mutanenta kuɗi da yawa, duban da take yi. Wannan yarinya kuwa ta bi Bulus da kuma sauranmu, tana ihu tana cewa, “Waɗannan mutane bayin Allah Mafi Ɗaukaka ne, suna sanar da ku hanyar ceto.” Ta yi ta faɗin haka har kwanaki masu yawa. A ƙarshe Bulus ya damu ƙwarai sai ya juya ya ce wa aljanin, “A cikin sunan Yesu Kiristi na umarce ka, ka rabu da ita!” Nan take aljanin ya rabu da ita. Da iyayengijin baranyar suka ga hanyar samun kuɗinsu ta toshe, sai suka kama Bulus da Sila suka ja su zuwa cikin kasuwa don su fuskanci hukuma.

Ayyukan Manzanni 19:11-12

Allah ya yi ayyukan banmamakin da suka wuce misali ta hannu Bulus, har ma ana kai hankicif da adikan da suka taɓa jikinsa wa marasa lafiya, suka kuwa warke daga cututtukansu mugayen ruhohi kuma suka rabu da su.

Ayyukan Manzanni 19:13-16

Waɗansu Yahudawa masu yawo gari-gari suna fitar da mugayen ruhohi suka yi ƙoƙari su yi amfani da sunan Ubangiji Yesu a kan waɗanda suke da aljanu. Suna cewa, “A cikin sunan Yesu wanda Bulus yake wa’azi, na umarce ku, ku fito.” ’Ya’ya bakwai maza na Sikeba, wani babban firist na Yahudawa, suna yin haka. Wata rana mugun ruhu ya amsa musu ya ce, “Yesu kam na sani, Bulus kuma na sani, amma ku kuma su wane ne?” Sai mutumin da yake da mugun ruhun ya fāɗa musu ya sha ƙarfinsu duka. Ya yi musu dūkan tsiya har suka fita a guje daga gidan tsirara jini yana zuba.

Ayyukan Manzanni 19:19

Waɗansu masu yin sihiri suka kawo naɗaɗɗun littattafansu wuri ɗaya suka kuwa ƙone su a gaban jama’a. Sa’ad da aka lissafta yawan kuɗin naɗaɗɗun littattafan nan, sai jimillar ta kai darik dubu hamsin.

Ayyukan Manzanni 26:17-18

‹Zan tsirar da kai daga mutanenka da kuma daga Al’ummai. Ina aikan ka zuwa gare su domin› ‹ka buɗe idanunsu su kuwa juyo daga duhu zuwa haske, daga mulkin Shaiɗan kuma zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai da kuma matsayi a cikin waɗanda aka tsarkake ta wurin bangaskiya a cikina.’›

Romawa 8:38-39

Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

Romawa 11:4

Wace amsa ce Allah ya ba shi? “Na keɓe wa kaina dubu bakwai waɗanda ba su yi wa Ba’al sujada ba.”

Romawa 16:20

Allah na salama zai tattake Shaiɗan ba da daɗewa ba yă kuma sa shi a ƙarƙashin sawunku. Alherin Ubangijinmu Yesu kuma yă kasance tare da ku.

1 Korintiyawa 5:5

Ku miƙa irin wannan mutum ga Shaiɗan, don a hallaka halin nan na mutuntaka, ruhunsa kuma yă sami ceto a ranar da Ubangiji zai dawo.

1 Korintiyawa 7:5

Kada ku ƙi kwana da juna sai ko kun yarda a junanku kuma na ɗan lokaci, don ku himmantu ga addu’a. Sa’an nan ku sāke haɗuwa don kada Shaiɗan yă jarrabce ku saboda rashin ƙamewarku.

1 Korintiyawa 10:20-22

A’a, ina nufin akan miƙa hadayun da masu bautar gumaka suka wa aljanu ne, ba Allah ba. Ba na so ku zama ɗaya da aljanu. Ba zai yiwu ku sha daga kwaf na Ubangiji ku kuma sha daga kwaf na aljanu ba, ba ya yiwuwa ku ci a teburin Ubangiji, ku kuma ci a teburin aljanu. Ashe, so muke mu tsokani Ubangiji ya yi kishi? Mun fi shi ƙarfi ne?

2 Korintiyawa 2:11

don kada Shaiɗan yă rinjaye mu. Da yake muna sane da dabarunsa.

2 Korintiyawa 4:3-4

Ko da bishararmu a rufe take, tana a rufe ne ga waɗanda suke hallaka. Allahn zamanin nan ya makanta hankulan marasa ba da gaskiya, yadda har ba za su iya ganin hasken bishara ta ɗaukakar Kiristi ba, wanda yake kamannin Allah.

2 Korintiyawa 6:15

Wace daidaituwa ce tsakanin Kiristi da Iblis? Me ya haɗa mai bi da marar bi?

2 Korintiyawa 10:4-5

Makaman da muke yaƙi da su, ba makamai na duniya ba ne. Sai dai na ikon Allah ne, masu rushe wuraren mafaka masu ƙarfi. Muna ka da masu gardama da kowane tunanin ɗaga kai da yake kafa kansa gāba da sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Kiristi.

2 Korintiyawa 11:3

Sai dai ina tsoro kada yă zama, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa’u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Kiristi.

2 Korintiyawa 11:13-15

Gama irin waɗannan mutane manzannin ƙarya ne, ma’aikata ne masu ruɗi, sun ɓad da kamanni kamar su manzannin Kiristi ne. Ba abin mamaki ba ne, gama Shaiɗan kansa ma yana ɓad da kamanni kamar shi mala’ikan haske ne. Don haka, ba abin mamaki ba ne, in bayin Shaiɗan sun ɓad da kamanni kamar su bayin adalci ne. A ƙarshe, za a sāka musu gwargwadon ayyukansu.

2 Korintiyawa 12:7

Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni.

Afisawa 1:21

Yanzu yana mulki a kan dukan masu sarauta, da masu iko, da masu ƙarfi, da kuma masu mulki. Yana mulkin kome a wannan duniya, zai kuma yi mulkin duniya mai zuwa.

Afisawa 2:2

Kun yi rayuwa kamar yadda sauran mutanen duniya suke yi, cike da zunubi, kuna biyayya ga sarki masu ikon sarari sama, wato, ruhun nan da yanzu yake aiki a cikin masu ƙin biyayya ga Allah.

Afisawa 3:10

Nufinsa shi ne, yanzu, ta wurin ikkilisiya, a sanar da hikima iri dabam-dabam na Allah ga masu mulki, da masu iko a samaniya.

Afisawa 4:26-27

“Cikin fushinku kada ku yi zunubi.” Kada ku bar rana ta fāɗi kuna fushi, kada kuma ku ba wa Iblis dama.

Afisawa 6:11-13

Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa, don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan. Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama. Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge.

Afisawa 6:16

Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kibiyoyin wutar Mugun nan da ita.

Kolossiyawa 2:15

Bayan ya ƙwace makaman ikoki da hukumomi, ya kunyata su a sarari, ya ci nasara a bisansu ta wurin gicciye.

1 Tessalonikawa 2:18

Gama mun so mu zo wurinku, tabbatacce ni, Bulus, na yi ƙoƙari sau da sau, amma Shaiɗan ya hana mu.

2 Tessalonikawa 2:3-10

Kada ku bar wani yă ruɗe ku ko ta yaya, gama wannan rana ba za tă zo ba sai an yi tawayen nan an kuma bayyana mutumin tawayen nan, mutumin da aka ƙaddara ga hallaka. Zai yi gāba yă kuma ɗaukaka kansa a bisa kome da ya shafe sunan Allah, ko kuma ake yi wa sujada, domin yă kafa kansa a haikalin Allah, yana shelar kansa a kan shi Allah ne. Ba ku tuna ba cewa sa’ad da nake tare da ku nakan gaya muku waɗannan abubuwa? Yanzu kuwa kun san abin da yake hana shi, wannan yana faruwa ne don a bayyana shi a daidai lokaci. Gama ikon asirin tawaye ya riga ya fara aiki; sai dai wannan da yake hana shi zai ci gaba da yin haka sai an kau da shi. Sa’an nan za a bayyana mai tawayen, Ubangiji Yesu kuwa zai hamɓare shi da numfashin bakinsa yă kuma hallaka shi da darajar dawowarsa. Zuwan mai tawayen nan zai zama ta wurin aikin Shaiɗan da aka bayyana cikin kowane irin ayyukan banmamaki, alamu da abubuwan banmamaki na ƙarya, da kuma cikin kowace irin muguntar da take ruɗin waɗanda suke hallaka. Sun hallaka ne domin sun ƙi su ƙaunaci gaskiya don su sami ceto.

2 Tessalonikawa 3:3

Ubangiji mai aminci ne, zai ƙarfafa ku, yă kuma tsare ku daga mugun nan.

1 Timoti 1:20

Cikinsu kuwa akwai Himenayus da Alekzanda, waɗanda na miƙa ga Shaiɗan don su horo su bar yin saɓo.

1 Timoti 3:6-7

Kada yă zama sabon tuba, in ba haka zai zama mai girman kai yă kuma fāɗa cikin irin hukuncin da ya fāɗo wa Iblis. Dole kuma yă kasance da shaida mai kyau ga waɗanda suke na waje, don kada yă zama abin kunya yă kuma fāɗa cikin tarkon Iblis.

1 Timoti 4:1

Ruhu a sarari ya faɗa cewa a kwanakin ƙarshe waɗansu za su watsar da bangaskiya su bi ruhohi masu ruɗu da kuma abubuwan da aljanu suke koyarwa.

1 Timoti 5:15

Waɗansu dai sun riga sun bauɗe sun bi Shaiɗan.

2 Timoti 1:7

Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai.

2 Timoti 2:26

su kuma dawo cikin hankulansu su kuɓuta daga tarkon Iblis, wanda ya sa suka zama kamammu don su aikata nufinsa.

Ibraniyawa 2:14

Da yake ’ya’yan suna da nama da jini, shi ma sai ya ɗauki kamanninsu na mutum domin ta wurin mutuwarsa yă hallaka wanda yake riƙe da ikon mutuwa, wato, Iblis

Yaƙub 2:19

Ka gaskata cewa Allah ɗaya ne. To, da kyau! Ai, ko aljanu ma sun gaskata wannan, har da rawan jiki.

Yaƙub 3:14-15

Amma in kuna cike da mugun kishi da kuma sonkai a cikin zukatanku, kada ku yi taƙama game da wannan, ko ku danne gaskiya. Irin wannan “hikima” ba daga sama ta sauko ba, ta duniya ce, ta rashin ruhaniya, ta Iblis kuma.

Yaƙub 4:7

Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah. Ku yi tsayayya da Iblis, zai kuwa guje ku.

1 Bitrus 5:8

Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye.

2 Bitrus 2:4

Gama in har Allah bai ƙyale mala’iku sa’ad da suka yi zunubi ba, amma ya tura su cikin lahira, domin a tsare su don hukunci;

1 Yohanna 2:18-22

’Ya’yana ƙaunatattu, waɗannan su ne kwanakin ƙarshe; kuma kamar yadda kuka ji cewa magabcin Kiristi yana zuwa, ko yanzu ma abokan gāban Kiristi da yawa sun zo. Ta haka muka san cewa kwanakin ƙarshe sun iso. Waɗannan masu gāba da Kiristi suna cikinmu a dā, amma sun bar mu, don tun dā ma su ba namu ba ne. Ai, da su namu ne, da har yanzu suna tare da mu. Amma sun bar mu, wannan ya nuna a fili cewa su ba namu ba ne. Amma ku kam, kuna da shafewa daga wurin Mai Tsarkin nan, kuma dukanku kun san gaskiya. Ina rubuta muku ba domin ba ku san gaskiya ba ne, a’a, sai dai domin kun santa, kun kuma san cewa babu yadda ƙarya za tă fito daga gaskiya. Wane ne maƙaryaci? Ai, shi ne mutumin da yake mūsun cewa Yesu shi ne Kiristi. Irin wannan mutum shi ne magabcin Kiristi, ya yi mūsun Uban da kuma Ɗan.

1 Yohanna 3:8-10

Duk mai aikata abin da yake zunubi shi na Iblis ne, domin Iblis mai aikata zunubi ne tun farko. Dalilin da ya sa Ɗan Allah ya bayyana kuwa shi ne don yă rushe aikin Iblis. Babu haifaffe na Allah da zai ci gaba da yin zunubi, domin iri na Allah yana a cikinsa; ba zai iya ci gaba da yin zunubi ba, domin haifaffe ne na Allah. Ta haka muka san waɗanda suke ’ya’yan Allah da kuma waɗanda suke ’ya’yan Iblis. Duk wanda ba ya yin abin da yake daidai, ba ɗan Allah ba ne; haka ma wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa.

1 Yohanna 4:1

Abokaina ƙaunatattu, ba kowane ruhu za ku gaskata ba, sai dai ku gwada ruhohi don ku ga ko daga Allah ne, domin annabawan ƙarya da yawa sun fito duniya.

1 Yohanna 4:2-3

Ga yadda za ku gane Ruhun Allah, duk ruhun da ya yarda cewa Yesu Kiristi ya zo cikin jiki, to, daga Allah yake. Amma duk ruhun da bai yarda da Yesu ba, ba daga Allah ba ne, ruhun magabcin Kiristi ne, wanda kuka ji yana zuwa, har ma ya riga ya shigo duniya.

1 Yohanna 5:19

Mun san cewa mu ’ya’yan Allah ne, duniya duka kuwa tana hannun Mugun.

2 Yohanna 1:7-11

Masu ruɗi da yawa, waɗanda ba su yarda da zuwan Yesu Kiristi cikin jiki ba, sun riga sun fito a duniya. Duk irin mutumin nan mai ruɗi ne kuma magabcin Kiristi. Ku lura don kada ku yi hasarar aikin da kuka yi, sai dai ku sami cikakken lada. Duk mutumin da bai tsaya a kan koyarwar Kiristi ba, amma ya yi ƙari a kanta, mutumin nan ba shi da Allah. Amma wanda ya tsaya a kan koyarwar Kiristi, yana da Uban da kuma Ɗan. Duk wanda ya zo wurinku bai kuma kawo koyarwan nan ba, kada ku karɓe shi a gidanku ko ku marabce shi. Duk wanda ya karɓe shi yana tarayya da mugun aikinsa ke nan.

Yahuda 1:6

Haka ma mala’ikun da ba su riƙe matsayinsu na iko ba, waɗanda suka bar ainihin mazauninsu, su ne ya tsare a duhu daure da dawwammamun sarƙoƙi don hukunci ta babbar Ranan nan.

Yahuda 1:9

Kai, ko Mika’ilu babban shugaban mala’iku ma, sa’ad da yake mūsu da Iblis game da gawar Musa, bai yi garajen ɗora masa laifi da baƙar magana ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka!”

Ru’uya ta Yohanna 2:9-10

‹Na san wahalarka da kuma talaucinka, duk da haka kai mai arziki ne! Na san ɓata suna da waɗannan suke yi maka waɗannan da suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, su dai majami’ar Shaiɗan ne.› ‹Kada ka ji tsoron wahalar da kake gab da sha. Ina gaya maka, Iblis zai sa waɗansunku a kurkuku don yă gwada ku. Za ku sha tsanani na kwana goma. Ka yi aminci ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka rawanin rai.›

Ru’uya ta Yohanna 2:13

‹Na san inda kake da zama, inda Shaiɗan yana da gadon sarautarsa. Duk da haka ka riƙe sunana da gaske. Ba ka yi mūsun bangaskiyarka gare ni ba, har ma a kwanakin Antifas, amintaccen mashaidina, wanda aka kashe a birninku, inda Shaiɗan yake zama.›

Ru’uya ta Yohanna 2:24

‹Yanzu, ina ce wa sauranku da kuke a Tiyatira, ku da ba ku riƙe da koyarwarta ba kuma ba ku koyi abin da suke kira zurfafan asiran Shaiɗan, ‘Ba zan ƙara muku wani nauyi ba.›

Ru’uya ta Yohanna 3:9

‹Zan sa waɗanda suke na majami’ar Shaiɗan, waɗanda suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, sai dai maƙaryata, zan sa su zo su fāɗi a ƙasa a gabanka su kuma shaida cewa na ƙaunace ka.›

Ru’uya ta Yohanna 9:1-11

Mala’ika na biyar ya busa ƙahonsa, sai na ga tauraron da ya fāɗo duniya daga sararin sama. Aka ba wa tauraron mabuɗin ramin Abis. Da ya buɗe Abis ɗin, sai hayaƙi ya taso daga cikin kamar hayaƙin matoya mai girma. Hayaƙin nan daga Abis ya duhunta rana da sararin sama. Daga cikin hayaƙin kuwa fāri suka fito zuwa cikin duniya aka kuma ba su iko irin na kunaman duniya. Aka faɗa musu kada su yi wa ciyawa na duniya lahani ko wani tsiro ko itace, sai dai su yi wa mutanen da ba su da hatimin Allah a goshinsu kaɗai lahani. Ba a ba su iko su kashe su ba, sai dai su ba su azaba na watanni biyar. Azabar da suka sha kuwa ya yi kamar ta harbin kunama sa’ad da ta harbi mutum. Cikin waɗannan kwanakin mutane za su nemi mutuwa, amma ba za su samu ba; za su yi marmarin mutuwa, amma mutuwa za tă ɓace musu. Kamannin fārin nan kuwa yana kama da dawakan da aka shirya don yaƙi. A kawunansu kuwa da wani abu da ya yi kamar rawanin zinariya, fuskokinsu kuma sun yi kamar fuskokin mutane. Gashin kansu ya yi kamar gashin kan mata, haƙoransu kuma sun yi kamar haƙoran zakoki. Suna da sulkuna kamar sulkunan ƙarfe, ƙarar fikafikansu kuma ta yi kamar motsin dawakai da kekunan yaƙi masu yawa da suke rugawa zuwa yaƙi. Suna da wutsiyoyi da ƙari kamar kunamai, kuma a wutsiyoyinsu suna da iko su ba wa mutane azaba na wata biyar. Suna da sarkin da yake mulki a bisansu wanda yake mala’ikan Abis, wanda sunansa a harshen Yahudawa shi ne Abaddon, da harshen Hellenawa kuwa shi ne, Afolliyon.

Ru’uya ta Yohanna 9:20

Sauran ’yan Adam da ba a kashe ta wajen waɗannan annobai ba kuwa har wa yau ba su tuba daga aikin hannuwansu ba; ba su daina bauta wa aljanu, da gumakan zinariya, azurfa, tagulla, dutse da na itace, gumakan da ba sa iya gani ko ji ko tafiya ba.

Ru’uya ta Yohanna 11:7

To, da suka gama shaidarsu, dabbar da takan fito daga Abis za tă kai musu hari, tă kuwa sha ƙarfinsu tă kuma kashe su.

Ru’uya ta Yohanna 12:3-4

Sai wata alama ta bayyana a sama, wani babban jan maciji mai kawuna bakwai da ƙahoni goma da rawani bakwai a kan kawunansa. Wutsiyarsa ta share kashi ɗaya bisa uku na taurari daga sararin sama ta kuma zubar da su ƙasa. Ƙaton jan macijin ya tsaya a gaban macen wadda take gab da haihuwa, don yă cinye ɗanta nan take bayan an haife shi.

Ru’uya ta Yohanna 12:7-12

Aka kuwa yi yaƙi a sama. Mika’ilu da mala’ikunsa yaƙi macijin, maciji da mala’ikunsa su ma suka mai da martani. Amma macijin nan ba shi da isashen ƙarfi, har suka rasa matsayinsu a sama. Aka jefar da ƙaton jan macijin ƙasa, tsohon maciji nan da ake kira Iblis, ko Shaiɗan, wanda ya ɓad da dukan duniya. Aka jefar da shi ƙasa, tare da mala’ikunsa a duniya. Sa’an nan na ji babbar murya daga sama tana cewa, “Yanzu ceto da iko da mulkin Allahnmu, da kuma ikon Kiristinsa. Gama mai zargin ’yan’uwanmu, wanda yake zarginsu a gaban Allahnmu dare da rana, an jefar da shi ƙasa. Sun ci nasara a kansa ta wurin jinin Ɗan Ragon da ta wurin kalmar shaidarsu; ba su ƙaunaci rayukansu sosai har da za su ja da baya daga mutuwa. Saboda haka ku yi farin ciki, ku sammai, da ku da kuke zaune a cikinsu! Amma kaiton duniya da kuma teku, gama Iblis ya sauko gare ku! Ya cika da fushi, domin ya san cewa lokacinsa ya rage kaɗan.”

Ru’uya ta Yohanna 12:13-17

Sa’ad da macijin ya ga an jefar da shi a duniya, sai ya fafari macen nan da ta haifi ɗa namiji. Sai aka ba wa macen fikafikai biyu na babban gaggafa, don ta tashi sama zuwa inda aka shirya mata a hamada, inda za a lura da ita na ɗan lokaci, lokuta da rabin lokaci, inda macijin ba zai iya kaiwa ba. Sa’an nan daga bakinsa macijin ya kwarara ruwa kamar kogi, don ruwan ya cimma matan yă kuma kwashe ta tare da ambaliya. Amma ƙasa ta taimaki macen ta wurin buɗe bakinta ta kuma shanye ruwan kogin da macijin ya kwarara daga bakinsa. Sai macijin ya yi fushi da macen ya kuma koma wajen sauran zuriyarta don yă yaƙe su waɗannan waɗanda suke biyayya da umarnan Allah suke kuma riƙe da shaidar Yesu.

Ru’uya ta Yohanna 13:1-10

Macijin kuwa ya tsaya a bakin teku. Sai na ga wata dabba tana fitowa daga teku. Tana da ƙahoni goma da kawuna bakwai, da kuma rawani goma a ƙahoninta, a kowane kai kuwa akwai sunan saɓo. Dabbar da na gani ta yi kamar damisa, amma tana da ƙafafu kamar na beyar, bakinta kuma ya yi kamar na zaki. Macijin nan ya ba wa dabbar ƙarfinsa da gadon sarautarsa da kuma ikonsa mai girma. Ɗaya daga cikin kawunan dabbar ya yi kamar yana da raunin da zai iya kashe shi, amma raunin nan da zai iya kashe shi ya riga ya warke. Dukan duniya ta yi mamaki ta kuma bi dabbar. Mutane suka yi wa macijin sujada domin ya ba wa dabbar ikonsa, suka yi wa dabbar sujada, suka kuma yi tambaya cewa, “Wane ne yake kama da dabban nan? Wa zai iya yaƙe ta?” Aka ba wa dabbar baki don ta faɗi kalmomin girman kai da na saɓo ta kuma yi amfani da ikonta har watanni arba’in da biyu. Ta buɗe bakinta don tă yi wa Allah saɓo, ta kuma ɓata sunansa da kuma mazauninsa da na waɗanda suke zama a sama. Aka ba ta iko tă yaƙi tsarkaka tă kuma ci nasara a kansu. Aka kuma ba ta iko bisa kowace kabila, jama’a, harshe da kuma al’umma. Dukan mazaunan duniya za su yi wa dabbar sujada, dukan waɗanda ba a rubuta sunayensu a cikin littafin ran da yake na Ɗan Ragon da aka yanka tun kafin halittar duniya ba. Duk mai kunne ji, bari yă ji. Duk wanda aka ƙaddara ga bauta, ga bauta zai tafi. Duk wanda aka ƙaddara za a kashe da takobi, da takobin za a kashe shi. Wannan yana bukata haƙuri da aminci a gefen tsarkaka.

Ru’uya ta Yohanna 13:11-18

Sai na ga wata dabba tana fitowa daga ƙasa. Tana da ƙahoni biyu kamar ɗan rago, amma ta yi magana kamar maciji. Ta mori dukan ikon dabban nan ta fari a madadinta, ta sa duniya da mazaunanta su yi wa dabba ta farin nan sujada, wadda aka warkar mata da raunin nan da zai iya kashe ta. Ta kuma yi manyan ayyuka da kuma alamu masu banmamaki, har ta sa wuta ta sauko daga sama zuwa ƙasa a gaban idon mutane. Saboda alamun nan da aka ba ta iko tă yi a madadin dabban nan ta fari, sai ta ruɗi mazaunan duniya. Ta umarce su su kafa siffa don girmama dabbar da aka ji mata rauni da takobi duk da haka ta rayu. Aka ba ta iko tă ba da numfashi ga siffar dabban nan ta fari, don tă yi magana tă kuma sa a kashe duk waɗanda suka ƙi yi wa siffar sujada. Ta kuma tilasta wa kowa, manya da yara, mawadata da matalauta, ’yantattu da bayi, don a yi musu alama a hannun dama ko a goshi, don kada kowa yă saya ko yă sayar, sai dai yana da alamar, wadda take sunan dabbar ko kuma lambar sunanta. Wannan yana bukata hikima. Duk mai hankali, sai yă lissafta lambar dabbar, gama lamban nan ta mutum ne. Lambarta kuwa ita ce 666.

Ru’uya ta Yohanna 14:9-11

Mala’ika na uku ya biyo su ya ce da babbar murya, “Duk wanda ya yi wa dabban nan da siffarta sujada ya kuma sami alamarta a goshi ko a hannu, shi ma zai sha ruwan inabin fushin Allah, wanda aka zuba da duk ƙarfinsa a kwaf fushinsa. Za a ba shi azaba da farar wuta mai ci a gaban tsarkakan mala’iku da na Ɗan Ragon. Hayaƙin azabarsu kuwa zai dinga tashi har abada abadin. Kuma babu hutu dare ko rana wa waɗanda suke wa dabbar da siffarta sujada, ko kuwa ga duk wanda ya sami alamar sunanta.”

Ru’uya ta Yohanna 16:10

Mala’ika na biyar ya juye kwanonsa a bisan gadon sarautar dabbar, mulkinta kuwa ya zama duhu. Mutane suka yi ta cizon bakinsu saboda azaba

Ru’uya ta Yohanna 16:13-14

Sa’an nan na ga mugayen ruhohi guda uku da suka yi kamar kwaɗi; suka fito daga bakin macijin nan, da kuma daga bakin dabbar, da kuma daga bakin annabin ƙaryan nan. Su ruhohin aljanu ne da suke aikata abubuwan banmamaki, sukan je wurin sarakunan dukan duniya, don su tattara su don yaƙi a babbar ranar Allah Maɗaukaki.

Ru’uya ta Yohanna 17:1-7

Ɗaya daga cikin mala’iku bakwai masu ɗauke da kwanoni bakwai nan, ya zo ya ce mini, “Zo, zan nuna maka hukuncin babbar karuwan nan da take zaune a bisan ruwaye masu yawa. Da ita ce sarakunan duniya suka yi zina mazaunan duniya kuma suka bugu da ruwan inabin zinace zinacenta.” Sa’an nan mala’ikan ya ɗauke ni cikin Ruhu zuwa hamada. A can na ga mace zaune a kan wata jan dabbar da aka rufe da sunayen saɓo tana kuma da kawuna bakwai da ƙahoni goma. Macen tana saye da tufafi masu ruwan ja da shunayya, tana ƙyalli da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai. Tana riƙe da kwaf na zinariya a hannunta, cike da abubuwa masu banƙyama da kuma ƙazantar zinace zinacenta. Sunan da aka rubuta a goshinta asiri ne, Babilon mai girma mahaifiyar karuwai da kuma na abubuwa masu banƙyama na duniya. Na ga cewa macen ta bugu da jinin tsarkaka, jinin waɗanda suka shaida Yesu. Da na gan ta, sai na yi mamaki ƙwarai. Sa’an nan mala’ikan ya ce mini, “Don me kake mamaki? Zan bayyana maka asirin macen nan da dabbar da take hawa, wadda take da kawuna bakwai da ƙahoni goma.

Ru’uya ta Yohanna 17:8-13

Dabbar da ka gani, a dā ta taɓa kasancewa, a yanzu, ba ta, za tă kuma fito daga Abis zuwa ga hallakarta. Mazaunan duniya waɗanda ba a rubuta sunayensu a littafin rai tun kafin halittar duniya ba za su yi mamaki sa’ad da suka ga dabbar, domin a dā ta taɓa kasancewa, yanzu kuwa ba ta, duk da haka za tă dawo. “Wannan yana bukata hankali da kuma hikima. Kawuna bakwai nan tuddai bakwai ne da macen take zama a kai. Sarakuna bakwai ne kuma. Biyar sun fāɗi, ɗaya yana nan, ɗayan kuma bai zo ba tukuna; amma sa’ad da ya zo, zai kasance na ɗan lokaci. Dabbar da a dā ta taɓa kasancewa, amma yanzu ba ta, ita ce sarki na takwas. Ita ɗaya ce cikin bakwai ɗin, kuma tana tafiya zuwa ga hallakarta. “Ƙahonin nan goma da ka gani sarakuna goma ne da ba su riga sun karɓi mulki ba, amma waɗanda na sa’a guda za su karɓi iko a matsayin sarakuna tare da dabbar. Suna da manufa guda za su kuma ba wa dabbar ikonsu da kuma sarautarsu.

Ru’uya ta Yohanna 17:14-18

Za su yi yaƙi da Ɗan Ragon, sai dai Ɗan Ragon zai ci nasara a bisansu domin shi ne Ubangijin iyayengiji, Sarkin sarakuna, tare da shi kuwa kirayayunsa, zaɓaɓɓunsa da kuma amintattu masu binsa za su kasance.” Sa’an nan mala’ikan ya ce mini, “Ruwayen da ka gani, inda karuwan take zama, jama’a ce, taro masu yawa, al’ummai da kuma harsuna. Dabbar da kuma ƙahoni goma da ka gani za su ƙi jinin karuwar. Za su kai ta ga hallaka su kuma bar ta tsirara; za su ci namanta su kuma ƙone ta da wuta. Gama Allah ya sa a zukatansu su cika nufinsa ta wurin yarda su ba wa dabbar ikonsu tă yi mulki, sai lokacin da kalmomin Allah sun cika. Macen da ka gani ita ce babban birnin da yake mulki a bisan sarakunan duniya.”

Ru’uya ta Yohanna 18:2

Ya yi kira da babbar murya ya ce, “Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi. Ta zama gidan aljanu da kuma wurin zaman kowace irin mugun ruhu, wurin zaman kowane irin tsuntsu marar tsabta da mai banƙyama.

Ru’uya ta Yohanna 19:19-21

Sa’an nan na ga dabbar da sarakunan duniya da mayaƙansu sun taru don su yi yaƙi da wannan wanda yake kan farin dokin da kuma mayaƙansa. Amma aka kama dabbar tare da annabin ƙaryan nan wanda ya aikata alamu masu banmamaki a madadinta. Da waɗannan alamun ne ya ruɗe waɗanda suka sami alamar dabbar suka kuma bauta wa siffarta. Aka jefa dukansu biyu da rai cikin tafkin wuta ta da farar wuta mai ci. Sauran kuma aka kashe su da takobin da ya fito daga bakin wannan wanda yake kan dokin. Dukan tsuntsaye kuwa suka ci namansu iyakar iyawarsu.

Ru’uya ta Yohanna 20:1-3

Na kuma ga wani mala’ika yana saukowa daga sama, yana da mabuɗin Abis yana kuma riƙe da ƙaton sarƙa a hannunsa. Ya kama macijin, wannan tsohon maciji, wanda yake shi ne Iblis, ko kuwa Shaiɗan, aka kuma ɗaura shi har shekara dubu. Ya jefa shi cikin Abis, ya kuma kulle ya sa hatimi a kansa, don a hana kada yă ƙara ruɗin al’ummai, sai shekarun nan dubu sun cika. Bayan wannan, dole a sake shi na ɗan lokaci.

Ru’uya ta Yohanna 20:7-9

Sa’ad da shekaru dubun nan suka cika, za a saki Shaiɗan daga kurkukun da yake, zai kuma fito don yă ruɗi al’ummai da suke a kursuyoyi huɗu na duniya, Gog da Magog, yă tattara su don yaƙi. Yawansu kuwa ya yi kamar yashi a bakin teku. Suka mamaye duk fāɗin duniya suka kuma kewaye sansanin mutanen Allah, birnin da yake ƙauna. Amma wuta ta fito daga sama ta cinye su.

Ru’uya ta Yohanna 20:10

Aka jefa Iblis da ya ruɗe su cikin tafkin farar wuta, inda aka jefa dabban nan da annabin ƙaryan nan. Za a ba su azaba dare da rana har abada abadin.

Hausa - Hausa - HA

HA'BSS - Budadden Littafi Mai Tsarki Biblica - 2020

This Bible text is from Biblica Open Hausa Contemporary Bible 2020
https://open.bible/bibles/hausa-biblica-text-bible/
provided by: Biblica Inc, available by Creative Commons CC-BY-SA-4.0,
and this new compilation is shared as www.creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0.
Languages are made available to you by www.ipedge.net