06 – Jahannama
Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Jahannama.
Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Jahannama.
Teku ya ba da matattu da suke cikinsa, mutuwa da Hades kuma suka ba da matattu da suke cikinsu, aka kuma yi wa kowane mutum shari’a bisa ga abin da ya aikata. Sa’an nan aka jefar da mutuwa da kuma Hades cikin tafkin wuta. Tafkin wutar nan kuwa shi ne mutuwa ta biyu. Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a cikin littafin rai ba, an jefar da shi cikin tafkin wutar nan.
”Ba wata hadayar da za a yi don mutanen da suka yanke shawara su yi ci gaba da yin zunubi da gangan bayan sun sami sanin gaskiya. A maimakon haka za su kasance da babban fargabar hukunci da kuma ta ƙunar wuta wadda za tă cinye abokan gāban Allah.
”‹Haka zai kasance a ƙarshen zamani. Mala’iku za su zo su ware masu mugunta daga masu adalci› ‹su kuma jefa su cikin wuta mai zafi, inda za a yi kuka da cizon haƙora.”›
”Ubangiji ya amsa wa Musa, “Duk wanda ya yi mini zunubi, shi zan shafe daga littafina. Yanzu tafi, ka jagoranci mutanen zuwa inda na yi zance, mala’ikana kuma zai sha gabanku. Duk da haka sa’ad da lokaci ya yi da zan yi horo, zan hore su domin zunubinsu.”
”Ubangiji ba zai gafarce shi ba, fushinsa da kishinsa za su ƙuna a kan wannan mutum. Dukan la’anonin da aka rubuta a wannan littafi za su fāɗo a kansa, Ubangiji kuwa zai shafe sunansa daga ƙarƙashin sama.
”Gama fushina ya kama wuta, tana ci har ƙurewar zurfin lahira. Za tă cinye duniya da girbinta, tă kuma sa wuta a tussan duwatsu.
”Kamar yadda girgije yakan ɓace yă tafi, haka mutum yake shige zuwa kabari ba kuwa zai dawo ba.
”cewa an kāre mugu daga ranar bala’i, an kāre shi daga ranar fushi?
”Mugaye za su koma kabari, dukan al’umman da suka manta da Allah.
”domin ba za ka yashe ni a kabari ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.
”Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe kewaye da ni; tarkon mutuwa ya yi mini arangama.
”Hannunka zai kakkama dukan abokan gābanka; hannunka na dama zai kakkama masu ƙinka. A lokacin bayyanarka za ka sa su zama kamar wutar matoya. Cikin fushinsa Ubangiji zai haɗiye su, kuma wutarsa za tă cinye su.
”Bari mutuwa ta ɗauki abokan gābana ba labari; bari su gangara da rai zuwa cikin kabari, gama mugunta tana samun masauƙi a cikinsu.
”Bari a shafe su sarai daga littafin rai kada a kuma lissafta su tare da adalai.
”Waɗanda suke ƙin Ubangiji za su fāɗi a gabansa da rawar jiki, hukuncinsu kuma zai dawwama har abada.
”Gama ƙaunarka da girma take gare ni; kai ka cece ni daga zurfafa, daga mazaunin matattu.
”Mutum marar azanci ba zai sani ba, wawa ba zai gane ba, cewa ko da yake mugaye suna girma kamar ciyawa kuma dukan masu aikata mugunta suna haɓaka, za a hallaka su har abada.
”Waɗansu sun zauna a cikin duhu da kuma zurfin ɓacin rai, ’yan kurkuku suna wahala cikin sarƙoƙin ƙarfe, gama sun yi tayarwa a kan maganar Allah suka ƙi shawarar Mafi Ɗaukaka.
”Ubangiji yakan lura da dukan waɗanda suke ƙaunarsa, amma dukan mugaye zai hallaka su.
”Amma ba su san cewa matattu suna a can ba, cewa baƙinta suna a can cikin zurfin kabari ba.
”Mutuwa da Hallaka suna nan a fili a gaban Ubangiji, balle fa zukatan mutane!
”Hanyar rai na yin jagora ya haura wa masu hikima don ta kiyaye shi daga gangarawa zuwa kabari.
”Kada ka bar yaro ba horo; in ka yi masa horo da sanda, ba zai mutu ba. Ka hukunta shi da sanda ka ceci ransa daga mutuwa.
”Mutuwa da Hallaka ba sa ƙoshi, haka idanun mutum ba sa ƙoshi da gani.
”Yanzu an ji kome; ga ƙarshen magana. Ka ji tsoron Allah ka kuma kiyaye umarnansa, gama wannan shi ne dukan hakkin mutum. Gama Allah zai shari’anta kowane irin aiki, har da waɗanda aka yi a ɓoye, ko nagari ne, ko mugu.
”Hasken Isra’ila zai zo kamar wuta, Mai Tsarkinsu zai zama kamar wuta; a rana guda zai ƙone yă kuma cinye ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiyarsa. Darajar jejinsa da gonakinsa masu dausayi za a hallaka su ɗungum, kamar yadda ciwo yakan kashe mutum.
”zai kuwa ji daɗin tsoron Ubangiji. Ba zai yi hukunci ta wurin abin da ya gani da idanunsa ba, ba zai kuwa yanke shawara ta wurin abin da ya ji da kunnuwansa ba; amma da adalci zai yi wa masu bukata shari’a, da gaskiya zai yanke shawarwari saboda matalautan duniya. Kamar sanda zai bugi duniya da maganar bakinsa; da numfashin leɓunansa zai yanke mugaye.
”Ku yi ihu, gama ranar Ubangiji ta yi kusa za tă zo kamar hallaka daga Maɗaukaki. Saboda wannan, hannun kowane mutum zai yi rauni, ƙarfin halin kowane mutum zai kāsa. Tsoro zai kama su, zafi da azaba za su ci ƙarfinsu; za su yi ta murɗewa kamar mace mai naƙuda. Za su dubi juna a tsorace, fuskokinsu a ɓace. Duba, ranar Ubangiji tana zuwa, muguwar rana, mai hasala da zafin fushi, don ta mai da ƙasar kango ta kuma hallakar da masu zunubi da suke cikinta. Taurarin sama da ƙungiyoyinsu ba za su ba da haskensu ba. Rana za tă yi duhu wata kuma ba zai ba da haskensa ba. Zan hukunta duniya saboda muguntarta, mugaye saboda zunubansu. Zan kawo ƙarshe ga girman kan masu taƙama in kuma ƙasƙantar da ɗaga kan marasa tausayi.
”Saboda haka zan sa sammai su yi rawar jiki; duniya kuma za tă girgiza daga inda take a fushin Ubangiji Maɗaukaki, a ranar fushinsa mai ƙuna.
”Kabari a ƙarƙashi duk ya shirya don yă sadu da kai a zuwanka; yana tā da ruhohin da suka rasu don su gaishe ka, dukan waɗanda sun taɓa zama shugabanni a duniya; ya sa suka tashi daga kujerun sarauta, dukan waɗanda suke sarakuna a kan al’ummai. Duk za su amsa, za su ce maka, “Ashe kai ma raunana ne, kamar mu; ka zama kamar mu.” An yi ƙasa da dukan alfarmarka zuwa kabari, tare da surutan garayunka; tsutsotsi sun bazu a ƙarƙashinka tsutsotsi kuma suka rufe ka.
”Yaya aka yi ka fāɗo daga sama Ya tauraron safiya, ɗan hasken asuba! An fyaɗa ka da ƙasa, kai da ka taɓa ƙasƙantar da al’ummai! Ka yi tunani a ranka ka ce, “Zan hau zuwa sama; zan ɗaga kursiyina sama da taurarin Allah; zan zauna a kursiyi a kan dutsen taro, a can ƙurewar saman dutse mai tsarki. Zan haura can bisa gizagizai; zan mai da kaina kamar Mafi Ɗaukaka.” Amma ga shi an gangara da kai zuwa kabari, zuwa zurfafan rami.
”Yanzu duk sun mutu, ba za su ƙara rayuwa ba; waɗannan ruhohin da suka rasu ba za su tashi ba. Ka hukunta su ka kuma kawo su ga hallaka; ka sa ba za a ƙara tunawa da su ba.
”Duba, Ubangiji yana fitowa daga mazauninsa don yă hukunta mutanen duniya saboda zunubansu. Duniya za tă bayyana zub da jinin da aka yi a kanta; ba za tă ƙara ɓoye waɗanda aka kashe a cikinta ba.
”Ba za a kashe ta ba dare da rana; hayaƙinta za tă yi ta tashi har abada. Daga tsara zuwa tsara za tă zama kango; babu wani da zai ƙara wucewa ta wurin.
”Gama kabari ba zai yabe ka ba, matattu ba za su rera yabonka ba; waɗanda suka gangara zuwa rami ba za su sa zuciya ga amincinka ba.
”Ga shi, Ubangiji yana zuwa da wuta, kuma kekunan yaƙinsa suna kama da guguwa; zai sauko da fushinsa da zafi, tsawatawarsa kuma da harsunan wuta. Gama da wuta da kuma takobi Ubangiji zai yi hukunci a kan dukan mutane, kuma yawanci za su kasance waɗanda Ubangiji zai kashe.
”“Za su kuma fita su ga gawawwakin mutanen da suka yi mini tayarwa; tsutsotsin da suke cinsu ba za su taɓa mutuwa ba, balle wutar da take ƙona su ta mutu, za su kuma zama abin ƙyama ga dukan mutane.”
”Gama kowane mai rai nawa ne, mahaifi da ɗa, duk nawa ne. Mutumin da ya yi zunubi shi zai mutu.
”“Sa’an nan na ci gaba da kallo saboda kalmomin fariyar da wannan ƙaho yake furtawa. Na yi ta kallo har sai da aka yanke dabbar, aka kuma hallaka jikinta a cikin wuta.
”Zai yi maganar saɓo a kan Mafi Ɗaukaka, zai kuma tsananta wa tsarkaka yă kuma yi ƙoƙarin sāke lokuta da shari’u. Za a miƙa tsarkaka a hannunsa na wani lokaci, lokuta da kuma rabin lokaci. “ ‘Amma majalisa za tă yi zama, za a karɓe ikonsa, a kuma hallaka shi gaba ɗaya har abada.
”Ɗumbun mutanen da suka yi barci cikin turɓayar duniya za su farka, waɗansu zuwa ga rai madawwami, waɗansu zuwa ga madawwamiyar kunya da kuma madawwamin ƙasƙanci.
”“Tabbatacce rana tana zuwa; za tă yi ƙuna kamar wutar maƙera. Dukan masu girman kai da kowane mai aikata mugunta zai zama ciyawa, wannan rana mai zuwa za tă ƙone su. Babu saiwa ko reshen da za a bar musu,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.
”Amma da Yohanna ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa suna zuwa inda yake yin baftisma, sai ya ce musu, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa fushin nan mai zuwa?
”An riga an sa bakin gatari a gindin itatuwa, kuma duk itacen da bai ba da ’ya’ya masu kyau ba, za a sare shi a jefa cikin wuta.
”Yana riƙe da matankaɗinsa, zai tankaɗe hatsinsa, yă kuma tattara alkamarsa a cikin rumbu, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.”
”‹“Kun dai ji an faɗa wa mutanen dā cewa, ‘Kada ka yi kisankai;›‹kuma duk wanda ya yi kisankai za a hukunta shi.’› ‹Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗan’uwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗan’uwansa ‘ Raka,’›‹za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta.›
”‹In idonka na dama yana sa ka yin zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.› ‹In kuma hannunka na dama yana sa ka yin zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka rasa ɗaya daga cikin gaɓoɓin jikinka, da a jefa jikinka ɗungum a cikin jahannama ta wuta.›
”‹“Ku shiga ta matsattsiyar ƙofa. Gama ƙofar zuwa hallaka faɗaɗɗiya ce mai sauƙin bi kuma, masu shiga ta cikinta kuwa suna da yawa.› ‹Amma ƙofar zuwa rai, ƙarama ce matsattsiya kuma, masu samunta kuwa kaɗan ne.›
”‹Duk itacen da ba ya ba da ’ya’ya masu kyau sai a sare shi a jefa cikin wuta.› ‹Ta haka, ta wurin aikinsu za ku gane su.”›
”‹“Ba duk mai ce mini, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ne zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda yake aikata nufin Ubana da yake sama.› ‹Da yawa za su ce mini a wannan rana, ‘Ubangiji, Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, ba kuma a cikin sunanka ne muka fitar da aljanu, muka yi abubuwan banmamaki da yawa ba?’› ‹Sa’an nan zan ce musu a fili, ‘Ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!’›
”‹Amma za a jefar da ’ya’yan mulki waje, zuwa cikin baƙin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.”›
”‹Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta.›
”‹Mutumin kirki yakan fito da abubuwa masu kyau daga ajiyar da aka a yi cikinsa, mugun mutum kuwa yakan fito da mugayen abubuwa daga cikin muguntar da aka yi ajiya a cikinsa.› ‹Amma ina gaya muku cewa mutane za su ba da lissafi a ranar shari’a a kan kowace kalmar banza da suka faɗa.› ‹Gama ta wurin kalmominka za a kuɓutar da kai, kuma ta wurin kalmominka za a hukunta ka.”›
”‹Gonar kuwa ita ce duniya, irin nan mai kyau kuwa suna a matsayin ’ya’yan mulkin. Ciyayin nan kuma su ne ’ya’yan mugun nan,› ‹abokin gāban da yake shuka su kuwa, Iblis ne. Lokacin girbi kuma shi ne ƙarshen zamani, masu girbin kuwa su ne mala’iku.› ‹“Kamar yadda aka tattara ciyayin aka kuma ƙone a wuta, haka zai zama a ƙarshen zamani.› ‹Ɗan Mutum zai aiki mala’ikunsa, su kuwa cire daga mulkinsa kome da yake jawo zunubi da kuma duk masu aikata mugunta.› ‹Za su jefa su cikin wuta mai zafi, inda za a yi kuka da cizon haƙora.›
”‹Haka zai kasance a ƙarshen zamani. Mala’iku za su zo su ware masu mugunta daga masu adalci› ‹su kuma jefa su cikin wuta mai zafi, inda za a yi kuka da cizon haƙora.”›
”‹Ina kuwa gaya maka, kai ne Bitrus,›‹a kan wannan dutse zan gina ikkilisiyata, kuma ƙofofin Hades›‹ba za su rinjaye ta ba.›
”‹Me mutum zai amfana in ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa? Ko kuwa me mutum zai bayar a bakin ransa?› ‹Gama Ɗan Mutum zai zo cikin ɗaukakar Ubansa, tare da mala’ikunsa, sa’an nan zai ba wa kowane mutum lada gwargwadon abin da ya yi.›
”Sai ya ce, ‹“Gaskiya nake gaya muku, in ba kun canja kuka zama kamar ƙananan yara ba, labudda, ba za ku shiga mulkin sama ba.›
”‹“Amma duk wanda ya sa ɗaya daga cikin ƙananan nan da suka gaskata da ni ya yi zunubi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku.›
”‹In hannunka ko ƙafarka yana sa ka zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da hannu ko ƙafa ɗaya da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu da a jefar da kai cikin madawwamiyar wuta da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu.› ‹In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da ido ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta da idanunka biyu.›
”‹“Amma da sarkin ya shigo don yă ga baƙin, sai ya ga wani can da ba ya sanye da kayan auren.› ‹Ya yi tambaya ya ce, ‘Aboki, yaya ka shigo nan ba tare da rigar aure ba?’ Mutumin ya rasa ta cewa.› ‹“Sai sarkin ya ce wa fadawa, ‘Ku daure shi hannu da ƙafa, ku jefar da shi waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’›
”‹“Ku macizai! ’Ya’yan macizai! Ta yaya za ku tsere wa hukuncin jahannama ta wuta?›
”‹Maigidan zai farfasa masa jiki da bulala, yă kuma ba shi wuri tare da munafukai, inda za a yi kuka da cizon haƙora.›
”‹“Amma yayinda suke kan tafiya garin sayen mai, sai ango ya iso. Budurwai da suke a shirye, suka shiga wajen bikin auren tare da shi. Aka kuma kulle ƙofa.› ‹“An jima can, sai ga sauran sun iso. Suka ce, ‘Ranka yă daɗe! Ranka yă daɗe! Ka buɗe mana ƙofa!’› ‹“Amma ya amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, ban san ku ba.’›
”‹Ku jefar da banzan bawan nan waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’›
”‹“Sa’ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa, tare da dukan mala’iku, zai zauna a kursiyinsa cikin ɗaukakar sama.› ‹Za a tara dukan al’ummai a gabansa, zai kuma raba mutane dabam-dabam yadda makiyayi yakan ware tumaki daga awaki.› ‹Zai sa tumaki a damansa, awaki kuma a hagunsa.›
”‹“Sa’an nan zai ce wa waɗanda suke a hagunsa, ‘Ku rabu da ni, la’anannu, zuwa cikin madawwamiyar wutar da aka shirya don Iblis da mala’ikunsa.› ‹Gama da nake jin yunwa, ba ku ba ni abinci ba, da nake jin ƙishirwa, ba ku ba ni abin sha ba,› ‹da na yi baƙunci, ba ku karɓe ni ba, da nake bukatar tufafi, ba ku yi mini sutura ba, da na yi rashin lafiya kuma ina a kurkuku, ba ku lura da ni ba.’› ‹“Su ma za su amsa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka cikin yunwa ko ƙishirwa ko baƙo ko cikin bukatar tufafi ko cikin rashin lafiya ko cikin kurkuku, ba mu taimake ka ba?’› ‹“Zai amsa, yă ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ba ku yi mini ba ke nan.’› ‹“Sa’an nan za su tafi cikin madawwamiyar hukunci, amma masu adalci kuwa za su shiga rai madawwami.”›
”‹Amma duk wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki, ba za a taɓa gafara masa ba. Ya aikata madawwamin zunubi ke nan.”›
”‹Me mutum zai amfana, in ya ribato duniya duka a bakin ransa?› ‹Ko kuma, me mutum zai bayar a musayar ransa?›
”‹“Idan kuma wani yă sa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan yara masu gaskatawa da ni yă yi laifi, zai fiye masa a rataya wani babban dutsen niƙa a wuyarsa, a jefa shi cikin teku.› ‹In hannunka yana sa ka yin zunubi, yanke shi. Ai, gwamma ka shiga rai da hannu ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta, inda ba a iya kashe wutar ba, da hannuwanka biyu.› ‹In kuma ƙafarka tana sa ka yin zunubi, yanke ta. Ai, gwamma ka shiga rai da ƙafa ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da ƙafafunka biyu.› ‹In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi. Ai, gwamma ka shiga mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da idanu biyu,› ‹inda› ‹“ ‘tsutsotsinsu ba sa mutuwa,› ‹wutar kuma ba a iya kashewa.’›
”‹Duk wanda ya gaskata, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma duk wanda bai gaskata ba kuwa, zai hallaka.›
”Matankaɗinsa yana a hannunsa don yă tankaɗe sussukarsa ya kuma tattara alkama cikin rumbunsa, amma zai ƙone yayin da wutar da ba a iya kashewa.”
”Yesu ya tambaye shi, ‹“Mene ne sunanka?”› Sai ya amsa, “Tuli,” gama aljanu masu ɗumbun yawa ne suna cikinsa. Suka yi ta roƙonsa kada yă umarce su su shiga ramin Abis.
”‹Ina amfani, in mutum ya ribato duniya duka, amma ya rasa ransa, ko kuma ya yi hasarar ransa.›
”‹Ke kuma Kafarnahum, kina tsammani za ki sami ɗaukaka ne? A’a, za a hallaka ki.› ‹“Wanda ya saurare ku, ni yake saurara. Wanda ya ƙi ku, ni yake ƙi. Amma wanda ya ƙi ni kuwa, ya ƙi wanda ya aiko ni ne.”›
”‹Amma zan nuna muku wanda za ku ji tsoronsa. Ku ji tsoron wanda, bayan da ya kashe jikin, yana da iko ya jefa ku cikin jahannama ta wuta. I, ina gaya muku, ku ji tsoronsa.›
”‹Ina gaya muku, a’a! Amma in ba ku tuba ba, ku ma duka za ku hallaka.›
”Sai wani ya tambaye shi ya ce, “Ya Ubangiji, shin, wai mutane kima ne kawai za su sami ceto?” Ya ce musu, ‹“Ku yi matuƙar ƙoƙari ku shiga ta matsattsiyar ƙofa, domin ina faɗa muku, mutane da yawa za su yi ƙoƙarin shiga, amma ba za su iya ba.› ‹Da zaran maigidan ya tashi ya rufe ƙofar, za ku tsaya a waje kuna ƙwanƙwasawa, kuna roƙo cewa, ‘Ranka yă daɗe, buɗe mana ƙofa.’› ‹“Amma shi zai amma ya ce, ‘Ni ban san ku, ko inda kuka fito ba.’› ‹“Sa’an nan za ku ce, ‘Haba, mu da muka ci, muka sha tare da kai, har ka yi koyarwa a cikin titi-titi namu.’› ‹“Amma shi zai amma ya ce, ‘Ban san ku, ko inda kuka fito ba. Ku rabu da ni, dukan ku masu aikata mugunta!’› ‹“Za a yi kuka a can, da cizon haƙora, sa’ad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, da dukan annabawa a mulkin Allah, amma ku kuwa, za a jefar da ku a waje.›
”‹“An yi wani mutum mai arziki wanda yakan sa tufafi masu ruwan shunayya, da kuma na lallausan lilin, yana kuma cikin rayuwar jin daɗi kullum.› ‹A ƙofar gidansa kuma akan ajiye wani mai bara, mai suna Lazarus, wanda jikinsa duk gyambuna ne.› ‹Shi kuwa yakan yi marmarin cin abin da yakan fāɗi daga tebur na mai arzikin nan. Har karnuka ma sukan zo su lashe gyambunansa.› ‹“Ana nan, sai mai baran ya mutu, kuma mala’iku suka ɗauke shi zuwa gefen Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi.› ‹A cikin jahannama ta wuta, inda yana shan azaba, ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim can nesa, da kuma Lazarus a gefensa.› ‹Sai ya yi masa kira ya ce, ‘Baba, Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiki Lazarus ya sa ɗan yatsarsa a ruwa, ya ɗiga mini a harshe saboda in ji sanyi, domin ina shan azaba cikin wannan wuta.’› ‹“Amma Ibrahim ya ce, ‘Ka tuna fa ɗana, a lokacin da kake duniya, ka sami abubuwa masu kyau naka, Lazarus kuwa ya sami munanan abubuwa. Amma yanzu ya sami ta’aziyya a nan, kai kuwa kana shan azaba.› ‹Ban da wannan duka ma, tsakaninmu da kai, akwai wani babban rami da aka yi, yadda waɗanda suke son ƙetarewa daga nan zuwa wurinku, ba za su iya ba, kuma ba mai iya ƙetarewa daga wurinku zuwa wurinmu.’› ‹“Ya amsa ya ce, ‘To, ina roƙonka, ya uba, ka aiki Lazarus zuwa gidan mahaifina,› ‹gama ina da ’yan’uwana biyar maza. Bari yă ba su gargaɗi, don kada su ma su zo wurin nan mai azaba.’› ‹“Ibrahim ya amsa ya ce, ‘Suna da Musa da Annabawa, ai, sai su saurare su.’› ‹“Sai ya ce, ‘A’a, ya uba, Ibrahim, in dai wani ya tashi daga matattu ya je wurinsu, za su tuba.’› ‹“Amma ya ce masa, ‘In ba su saurari Musa da Annabawa ba, kai, ko da wani ya tashi daga matattu ma, ba za su saurare shi ba.’ ”›
”Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa. Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba. Hukuncin shi ne, Haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka so duhu a maimakon haske domin ayyukansu mugaye ne. Duk mai aikata mugunta yana ƙin haske, ba zai kuwa zo cikin haske ba don yana tsoro kada ayyukansa su tonu.
”Duk wanda ya gaskata da Ɗan yana da rai madawwami, amma duk wanda ya ƙi Ɗan ba zai sami rai ba, gama fushin Allah yana nan a bisansa.”
”‹“Kada ku yi mamakin wannan, gama lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke cikin kaburbura za su ji muryarsa› ‹su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta za su tashi zuwa ga rai, waɗanda kuma suka aikata mugunta za su tashi zuwa ga hukunci.›
”‹Duk wanda bai kasance a cikina ba, yana kamar reshen da aka jefar yă bushe; irin waɗannan rassan ne akan tattara, a jefa cikin wuta a ƙone.›
”gama ba za ka bar ni cikin kabari ba, ba kuwa za ka yarda Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.
”Ganin abin da yake gaba, ya yi magana a kan tashin Kiristi daga matattu cewa, ba a bar shi a kabari ba, jikinsa kuma bai ruɓa ba.
”Ana bayyana fushin Allah daga sama a kan dukan rashin sanin Allah da kuma muguntar mutanen da suke danne gaskiya ta wurin muguntarsu, gama abin da ana iya sani game da Allah a bayyane yake a gare su, domin Allah ya bayyana musu shi. Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja. Gama ko da yake sun san Allah, ba su ɗaukaka shi a matsayin Allah ko su gode masa ba, sai dai tunaninsu ya zama banza, zukatansu masu wauta kuma suka duhunta. Ko da yake sun ɗauka su masu hikima ne, sai suka zama wawaye,
”Amma saboda taurinkanka da zuciyarka marar tuba, kana tara wa kanka fushi a ranar fushin Allah, sa’ad da za a bayyana hukuncinsa mai adalci. Allah, “Zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikin da ya yi.” Ga waɗanda ta wurin naciya suna yin nagarta suna neman ɗaukaka, girma da rashin mutuwa, su za a ba su rai madawwami. Amma ga waɗanda suke sonkai waɗanda suke ƙin gaskiya suke kuma bin mugunta, akwai fushi da haushi dominsu.
”Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
”Saboda haka, yanzu babu hukunci don waɗanda suke cikin Kiristi Yesu, gama ta wurin Kiristi Yesu dokar Ruhu mai ba da rai ta ’yantar da ni daga Dokar Musa.
”Kada ku yi ramuwa, abokaina, sai dai ku bar wa Allah. Gama a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce; zan kuwa sāka,” in ji Ubangiji.
”A rubuce yake cewa, “ ‘Muddin ina raye,’ in ji Ubangiji, ‘kowace gwiwa za tă durƙusa a gabana; kowane harshe kuma zai furta wa Allah.’ ” Don haka kowannenmu zai ba da lissafin kansa ga Allah.
”Gama dole dukanmu mu bayyana a gaban kujerar shari’ar Kiristi, domin kowannenmu yă karɓi ladan aikin da ya yi a wannan jiki, ko mai kyau ne ko marar kyau. To, da yake mun san ko mene tsoron Ubangiji yake, muna ƙoƙari mu rinjaye mutane. Yadda muke kuwa, yana sane a sarari ga Allah, ina kuma fata yana nan a sarari a lamirinku.
”Duk wanda ya yi laifi, za a sāka masa don laifinsa, babu sonkai.
”Zai hukunta waɗanda ba su san Allah ba da kuma waɗanda ba su yi biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu ba. Za a hukunta su da madawwamiyar hallaka a kuma kau da su daga gaban Ubangiji da kuma daga ɗaukakar ikonsa
”Kamar dai yadda aka ƙaddara wa mutum yă mutu sau ɗaya, bayan haka kuma sai shari’a,
”Ba wata hadayar da za a yi don mutanen da suka yanke shawara su yi ci gaba da yin zunubi da gangan bayan sun sami sanin gaskiya. A maimakon haka za su kasance da babban fargabar hukunci da kuma ta ƙunar wuta wadda za tă cinye abokan gāban Allah.
”Wane irin hukunci mai tsanani ne kuke tsammani zai dace da mutumin da ya nuna rashin bangirma ga Ɗan Allah, wanda ya yi banza da jinin nan na alkawarin da ya tsarkake shi, wanda kuma ya zargi Ruhun alheri? Gama mun san shi, wannan wanda ya ce, “Ramuwa tawa ce; zan rama,” da kuma, “Ubangiji zai yi wa mutanensa hukunci.” Abu mai matuƙar bantsoro ne a fāɗa cikin hannuwan Allah mai rai.
”Gama Kiristi ya mutu domin zunubi sau ɗaya tak, mai adalci saboda marasa adalci, don yă kawo ku ga Allah. An kashe shi a cikin jiki, amma an rayar da shi a Ruhu, ta wurin wanda kuma ya tafi ya yi wa ruhohin da suke a kurkuku wa’azi
”Amma a dā akwai annabawan ƙarya a cikin mutane, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku. A ɓoye za su shigar da karkataccen koyarwa mai hallaka, har ma su yi mūsun Ubangiji mai iko duka wanda ya saye su suna kawo wa kansu hallaka farat ɗaya. Da yawa za su bi hanyoyinsu na rashin kunya su kuma sa a rena hanyar gaskiya. Cikin kwaɗayinsu waɗannan malaman ƙarya za su cuce ku da tatsuniyoyin da suka ƙaga. Hukuncinsu yana a rataye a kansu tun da daɗewa, hallakarsu kuma ba ta barci.
”Gama in har Allah bai ƙyale mala’iku sa’ad da suka yi zunubi ba, amma ya tura su cikin lahira, domin a tsare su don hukunci; in har bai ƙyale duniya ta dā ba sa’ad da ya kawo ambaliya a kan mutanenta marasa tsoron Allah, amma ya kiyaye Nuhu, mai wa’azin adalci, da kuma waɗansu bakwai; in har ya hukunta biranen Sodom da Gomorra ta wurin ƙone su suka zama toka, ya kuma maishe su misali na abin da zai faru da marasa tsoron Allah; in kuwa har ya ceci Lot, mai adalci, wanda ya damu ainun da ƙazamar rayuwar mutane marasa bin doka; (adon kuwa abin da adalin nan ya yi, ya kuma gani, sa’ad da yake a cikinsu, sai kowace rana yakan ji ciwon aikinsu na kangara a zuciyarsa mai adalci) in haka ne, to, Ubangiji ya san yadda zai ceci mutane masu tsoron Allah daga gwaje-gwaje, yă kuma tsare marasa adalci don ranar hukunci, har yă zuwa ranar shari’a. Wannan gaskiya ce musamman ga waɗanda suke bin sha’awace-sha’awacen lalaci na mutuntaka, suna kuma rena masu mulki. Da ƙarfin hali da kuma girman kai, waɗannan mutane ba sa tsoro kawo zargin ɓata sunan talikan sama; duk da haka ko mala’iku ma da suka fi su ƙarfi suka kuma fi su iko, ba sa kawo irin wannan zargi na ɓata suna game da waɗannan talikai a gaban Ubangiji.
”Waɗannan mutane maɓulɓulai ne babu ruwa da kuma hazon da guguwar iska take kora. An shirya matsanancin duhu dominsu.
”Ta wurin wannan magana ce aka ajiye sammai da ƙasa na yanzu domin wuta, an ajiye su kuma don ranar hukunci da hallaka ta mutane marasa tsoron Allah.
”Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani yă hallaka, sai dai kowa yă kai ga tuba.
”Duk mai ƙin ɗan’uwansa mai kisankai ne, kun kuma san cewa ba mai kisankan da yake da rai madawwami a cikinsa.
”Wannan kuwa ita ce shaidar; cewa Allah ya ba mu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Ɗansa. Duk wanda yake da Ɗan, yana da rai; wanda kuwa ba shi da Ɗan Allah, ba shi da rai.
”Na faɗa haka ne domin waɗansu mutanen da aka rubuta hukuncinsu tun dā sun shiga cikinku a ɓoye. Su fa marasa tsoron Allah ne. Su ne waɗanda suka mai da alherin Allahnmu ya zama dalilin yin fasikanci, suna kuma mūsun Yesu Kiristi wanda shi ne Makaɗaici Mai Iko Duka da kuma Ubangijinmu.
”Haka ma mala’ikun da ba su riƙe matsayinsu na iko ba, waɗanda suka bar ainihin mazauninsu, su ne ya tsare a duhu daure da dawwammamun sarƙoƙi don hukunci ta babbar Ranan nan. Haka ma Sodom da Gomorra da garuruwan da suke kewaye da su, waɗanda su ma suka ba da kansu ga fasikanci da muguwar sha’awar jiki, sun zama misalin waɗanda suke shan hukuncin madawwamiyar wuta.
”Waɗannan mutane sun zama kamar ƙazanta a taronku na soyayya, suna ta ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro. Su masu kiwo ne da suke ciyar da kansu kawai. Su kamar hadari ne da babu ruwa da iska take kori. Su kamar itatuwa ne, marasa ’ya’ya da rani, waɗanda aka tumɓuke, ko kamar itatuwan da aka tumɓuke suka kuma mutu ƙurmus. Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da tumbatsan kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu yawo barkatai, waɗanda aka ajiye mugun duhu saboda su har abada.
”ku cece waɗansu ta wurin fizge su daga wuta. Ga waɗansu kuma ku ji tausayinsu, amma tare da tsoro, har ma ku yi ƙyamar tufafin da suka ɓata da ayyukansu na jiki.
”‹Ni ne Rayayye, dā na mutu, ga shi kuwa ina a raye har abada abadin! Ina kuma riƙe da mabuɗan mutuwa da na Hades.›
”‹Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara mutuwa ta biyu ba za tă cuce shi ba ko kaɗan.›
”Mala’ika na biyar ya busa ƙahonsa, sai na ga tauraron da ya fāɗo duniya daga sararin sama. Aka ba wa tauraron mabuɗin ramin Abis. Da ya buɗe Abis ɗin, sai hayaƙi ya taso daga cikin kamar hayaƙin matoya mai girma. Hayaƙin nan daga Abis ya duhunta rana da sararin sama.
”Mala’ika na uku ya biyo su ya ce da babbar murya, “Duk wanda ya yi wa dabban nan da siffarta sujada ya kuma sami alamarta a goshi ko a hannu, shi ma zai sha ruwan inabin fushin Allah, wanda aka zuba da duk ƙarfinsa a kwaf fushinsa. Za a ba shi azaba da farar wuta mai ci a gaban tsarkakan mala’iku da na Ɗan Ragon. Hayaƙin azabarsu kuwa zai dinga tashi har abada abadin. Kuma babu hutu dare ko rana wa waɗanda suke wa dabbar da siffarta sujada, ko kuwa ga duk wanda ya sami alamar sunanta.”
”Dabbar da a dā ta taɓa kasancewa, amma yanzu ba ta, ita ce sarki na takwas. Ita ɗaya ce cikin bakwai ɗin, kuma tana tafiya zuwa ga hallakarta.
”Ya yi kira da babbar murya ya ce, “Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi. Ta zama gidan aljanu da kuma wurin zaman kowace irin mugun ruhu, wurin zaman kowane irin tsuntsu marar tsabta da mai banƙyama. Gama dukan al’ummai sun sha ruwan inabin haukan zinace zinacenta. Sarakunan duniya sun yi zina tare da ita, attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.”
”Hasken fitila ba zai ƙara haskakawa a cikinki ba. Ba za a ƙara jin muryar ango da amarya a cikinki ba. Attajiranki, dā su ne manyan mutanen duniya. Ta wurin sihirinki, dukan ƙasashe sun kauce. A cikinta aka sami jinin annabawa, da na tsarkaka, da kuma na dukan waɗanda aka kashe a duniya.”
”gama hukuncinsa daidai ne, mai adalci kuma. Ya hukunta babbar karuwan nan wadda ta ɓata duniya da zinace zinacenta. Ya rama jinin bayinsa a kanta.” Suka sāke tā da murya suka ce, “Halleluya! Hayaƙin yake fitowa daga wurinta ya yi ta tashi sama har abada abadin.”
”Yana saye da rigar da aka tsoma a jini, sunansa kuwa Kalman Allah ne. Mayaƙan sama suna biye da shi, suna hawan fararen dawakai, saye da fararen tufafi masu tsabta na lallausan lilin. Daga bakinsa takobi mai kaifi ya fito. Da shi zai karkashe al’ummai. “Zai yi mulkinsu da sandan sarautar ƙarfe.” Yana tattake wurin matsin ruwan inabi na fushin Allah Maɗaukaki.
”Na kuma ga wani mala’ika tsaye a cikin rana, wanda ya yi kira da babbar murya ga dukan tsuntsaye da suke tashi sama a tsakiyar sararin sama cewa, “Ku zo, ku taru don babban bikin nan na Allah, don ku ci naman sarakuna, jarumawa, da kuma manyan mutane, na dawakai da mahayansu, da kuma naman dukan mutane, ’yantacce da bawa, babba da yaro.”
”Amma aka kama dabbar tare da annabin ƙaryan nan wanda ya aikata alamu masu banmamaki a madadinta. Da waɗannan alamun ne ya ruɗe waɗanda suka sami alamar dabbar suka kuma bauta wa siffarta. Aka jefa dukansu biyu da rai cikin tafkin wuta ta da farar wuta mai ci. Sauran kuma aka kashe su da takobin da ya fito daga bakin wannan wanda yake kan dokin. Dukan tsuntsaye kuwa suka ci namansu iyakar iyawarsu.
”Na kuma ga wani mala’ika yana saukowa daga sama, yana da mabuɗin Abis yana kuma riƙe da ƙaton sarƙa a hannunsa. Ya kama macijin, wannan tsohon maciji, wanda yake shi ne Iblis, ko kuwa Shaiɗan, aka kuma ɗaura shi har shekara dubu. Ya jefa shi cikin Abis, ya kuma kulle ya sa hatimi a kansa, don a hana kada yă ƙara ruɗin al’ummai, sai shekarun nan dubu sun cika. Bayan wannan, dole a sake shi na ɗan lokaci.
”Sa’ad da shekaru dubun nan suka cika, za a saki Shaiɗan daga kurkukun da yake, zai kuma fito don yă ruɗi al’ummai da suke a kursuyoyi huɗu na duniya, Gog da Magog, yă tattara su don yaƙi. Yawansu kuwa ya yi kamar yashi a bakin teku. Suka mamaye duk fāɗin duniya suka kuma kewaye sansanin mutanen Allah, birnin da yake ƙauna. Amma wuta ta fito daga sama ta cinye su. Aka jefa Iblis da ya ruɗe su cikin tafkin farar wuta, inda aka jefa dabban nan da annabin ƙaryan nan. Za a ba su azaba dare da rana har abada abadin.
”Sa’an nan na ga babban farin kursiyi da kuma wannan da yake zama a kansa. Duniya da sararin sama kuwa suka ɓace daga gabansa, babu wuri kuwa dominsu. Sai na ga matattu, babba da yaro tsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne littafin rai. Aka yi wa matattu shari’a bisa ga abin da suka aikata yadda yake a rubuce a cikin littattafai. Teku ya ba da matattu da suke cikinsa, mutuwa da Hades kuma suka ba da matattu da suke cikinsu, aka kuma yi wa kowane mutum shari’a bisa ga abin da ya aikata. Sa’an nan aka jefar da mutuwa da kuma Hades cikin tafkin wuta. Tafkin wutar nan kuwa shi ne mutuwa ta biyu. Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a cikin littafin rai ba, an jefar da shi cikin tafkin wutar nan.
”Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.”
”Duk mai yin laifi yă ci gaba da yin laifi; duk mai aikata ƙazanta yă ci gaba da aikata ƙazanta. Duk mai aikata abin da yake daidai, yă ci gaba da aikata abin da yake daidai. Kuma duk wanda yake mai tsarki, yă ci gaba da yin abin da yake da tsarki.”
”Ina yin wa duk wanda ya ji kalmomin annabcin wannan littafi gargaɗi. Duk wanda ya ƙara wani abu a kansu, Allah zai ƙara masa annoban da aka bayyana a littafin nan. Duk wanda kuma ya yi ragi a kalmomi daga littafin annabcin nan, Allah zai ɗauke rabonsa na itacen rai da kuma na birnin nan mai tsarki, waɗanda aka bayyana a littafin nan.
”