31 – Bishara

Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Bishara.

Top 3 Mafi Muhimmanci ayoyi

Romawa 10:14-15

To, ta yaya za su kira ga wanda ba su gaskata ba? Ta yaya kuma za su gaskata wanda ba su taɓa ji ba? Ta yaya kuma za su ji ba tare da wani ya yi musu wa’azi ba? Kuma ta yaya za su yi wa’azi in ba an aike su ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Isowar masu kawo labari mai daɗi abu mai kyau ne ƙwarai!”

2 Korintiyawa 2:15-16

Don kuwa, a wurin Allah mu ƙanshin Kiristi ne cikin waɗanda ake ceto, da kuma waɗanda suke hanyar hallaka. Ga wani, mu warin mutuwa ne, amma ga wani kuwa, mu ƙanshin rai ne. Wa ya isa yă yi irin wannan aikin?

Mattiyu 10:14-15

‹Duk wanda ya ƙi marabtarku ko ya ƙi sauraron kalmominku, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku sa’ad da kuka fita gidan ko garin.› ‹Gaskiya nake gaya muku, za a fi jin tausayin Sodom da Gomorra a ranar shari’a fiye da wannan gari.›

Kowane Aya A Canonical Order – 307 sassa

Farawa 8:22

“Muddin duniya tana nan, lokacin shuki da na girbi, lokacin sanyi da na zafi, lokacin damina da na rani, dare da rana ba za su daina ba.”

Fitowa 4:1

Musa ya amsa ya ce, “In ba su gaskata ni ba, suka kuma ce, ‘ Ubangiji bai bayyana gare ka ba fa’?”

Fitowa 4:10-12

Musa ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangiji, ni ban mai iya magana ba ne, ban taɓa iya ba, ko a yanzu ma, bayan ka yi magana da ni, gama ni mai nauyin baki ne, mai nauyin harshe kuma.” Ubangiji ya ce masa, “Wa ya ba mutum bakinsa? Wa yake maishe shi kurma ko bebe? Wa yake ba shi gani ko yă makanta shi? Ashe ba Ni Ubangiji ba ne? Yanzu tafi, zan taimake ka ka yi magana, zan kuma koya maka abin da za ka faɗa.”

Fitowa 4:13-16

Amma Musa ya ce, “Ya Ubangiji, ina roƙonka, ka nemi wani ka aika.” Sai Ubangiji ya yi fushi da Musa ya ce, “Ɗan’uwanka Haruna Balawe, ba ya nan ne? Na san ya iya magana. Ya riga ya kama hanya don yă sadu da kai, zai kuma yi farin ciki sa’ad da ya gan ka. Za ka yi masa magana. Ka kuma sa masa maganata a baki; zan kuma taimake ku magana, in koya muku abin da za ku yi. Zai yi magana da mutane a madadinka, zai zama kamar bakinka, kai kuwa kamar Allah a gare shi.

Yoshuwa 1:3

Zan ba ku duk ƙasar da za ku taka, kamar yadda na yi wa Musa alkawari.

1 Tarihi 16:23-24

Ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka; ku yi shelar cetonsa kowace rana. Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, ayyukansa masu al’ajabai a cikin mutane.

Zabura 40:9-10

Na yi shelar adalcinka cikin babban taro; ba na rufe leɓunana, kamar yadda ka sani, ya Ubangiji. Ba na ɓoye adalcinka cikin zuciyata; ina maganar amincinka da cetonka. Ban ɓoye ƙaunarka da gaskiyarka a gaban taron jama’arka mai girma ba.

Zabura 71:15-18

Bakina zai ba da labarin adalcinka, zai yi maganar cetonka dukan yini, ko da yake ban san yawansa ba. Zan zo in furta in kuma yi shelar ayyukanka masu girma, ya Ubangiji Mai Iko Duka; zan yi shelar adalcinka, naka kaɗai. Tun ina yaro, ya Allah, ka koya mini har wa yau ina furta ayyukanka masu banmamaki. Ko sa’ad da na tsufa da furfura, kada ka yashe ni, ya Allah, sai na furta ikonka ga tsara mai zuwa, ƙarfinka ga dukan waɗanda suke zuwa.

Zabura 96:2-3

Ku rera ga Ubangiji, ku yabe sunansa; ku yi shelar cetonsa kowace rana. Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai, manyan ayyukansa a cikin dukan mutane.

Zabura 119:46

Zan yi maganar farillanka a gaban sarakuna ba kuwa za a kunyata ni ba,

Zabura 126:5-6

Waɗanda suka yi shuka da hawaye za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki. Shi da ya fita yana kuka, riƙe da iri don shuki, zai dawo da waƙoƙin farin ciki, ɗauke da dammuna.

Zabura 141:3

Ka sa mai tsaro a bakina, ya Ubangiji; ka yi tsaron ƙofar leɓunana.

Zabura 145:4

Tsara guda za tă yi maganar ayyukanka ga wata tsara; za su yi magana game da manyan ayyukanka.

Karin Magana 11:18

Mugun mutum kan sami albashin ƙarya amma shi da ya shuka adalci zai girbe lada tabbatacce.

Karin Magana 11:30

’Ya’yan itacen adali itacen rai ne, kuma duk mai samun rayuka mai hikima ne.

Karin Magana 15:30-33

Fuska mai fara’a takan kawo farin ciki ga zuciya, kuma labari mai daɗi na kawo lafiya ga ƙasusuwa. Duk wanda ya mai da hankali sa’ad da ake tsawata masa ba zai kasance dabam a cikin masu hikima ba. Duk waɗanda suka ƙi horon sun rena kansu ke nan, amma duk waɗanda sun yarda da gyara sukan ƙara basira. Tsoron Ubangiji yakan koya wa mutum hikima, kuma sauƙinkai kan zo kafin girmamawa.

Karin Magana 16:24

Kalmomi masu daɗi suna kama da kakin zuma, mai zaƙi ga rai da kuma warkarwa ga ƙasusuwa.

Karin Magana 17:27-28

Mutum mai sani yakan yi la’akari da amfani da kalmomi, mutum mai basira kuma natsattse ne. Ko wawa in bai buɗe bakinsa ba, za a zaci shi mai hikima ne, da kuma mai basira inda ya ƙame bakinsa.

Karin Magana 18:2

Wawa ba ya sha’awa ya sami fahimta amma abin da yake so ya yi kaɗai, shi ne ya ba da ra’ayinsa.

Karin Magana 18:6-7

Leɓunan wawa kan jawo masa faɗa, bakinsa kuma kan gayyaci dūka. Bakin wawa lalatar da kansa yake yi leɓunansa kuma tarko ne ga ransa.

Karin Magana 18:13

Duk wanda yakan ba da amsa kafin ya saurara, wannan wauta ce da kuma abin kunya.

Karin Magana 18:21

Harshe yana da ikon rai da mutuwa, kuma waɗanda suke ƙaunarsa za su ci amfaninsa.

Karin Magana 25:25

Kamar ruwan sanyi ga ran da ya gaji haka yake da jin labari mai daɗi daga ƙasa mai nisa.

Mai Hadishi 3:7

Lokacin yagewa da lokacin ɗinkewa, lokacin yin shiru da lokacin magana.

Mai Hadishi 11:4

Duk mai la’akari da iska, ba zai yi shuka ba, mai la’akari da gizagizai kuma, ba zai yi girbi ba.

Mai Hadishi 11:6

Ka shuka irinka da safe, da yamma kuma kada ka janye hannunka, gama ba ka san wanda zai yi albarka ba, ko wannan ko wancan, ko kuma duka biyunsu su yi albarka.

Mai Hadishi 12:9-10

Ba kawai Malami ya kasance mai hikima ba, amma kuma ya koyar da mutane. Ya yi tunani ya kuma yi binciken da ya tsara karin magana masu yawa. Malami ya yi bincike don yă sami kalmomin da suka dace, kuma abin da ya rubuta daidai ne da kuma gaskiya.

Ishaya 6:8

Sa’an nan na ji muryar Ubangiji tana cewa, “Wa zan aika? Wa zai tafi mana?” Sai na ce, “Ga ni! Ka aike ni!”

Ishaya 6:9-11

Ya ce, “Je ka ka faɗa wa wannan mutane, “ ‘Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba; Kome yawan dubar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.’ Ka sa zuciyar mutanen nan ta dushe; kunnuwansu su kurunce, idanunsu kuma su makance. In ba haka ba za su iya gani da idanunsu, su ji da kunnuwansu, su fahimta da zuciyarsu, su kuma juyo a kuma warkar da su.” Sa’an nan na ce, “Har yaushe, ya Ubangiji?” Ya kuma amsa, “Sai an lalatar da biranen ba kowa a ciki, sai an mai da gidaje kangwaye ƙasa kuma ta zama kango ba amfani,

Ishaya 8:20

Nemi umarnin Allah da kuma shaidar jan kunne. Duk wanda bai yi magana bisa ga wannan kalma ba, ba su da amfani.

Ishaya 11:9

Ba za su yi lahani ko su hallaka wani a dutsena mai tsarki ba, gama duniya za tă cika da sanin Ubangiji kamar yadda ruwaye suka rufe teku.

Ishaya 40:9

Kai da ka kawo labari mai daɗi wa Sihiyona, ka haura a bisa dutse. Kai da ka kawo labari mai daɗi wa Urushalima, ka tā da muryarka ka yi ihu, ka ɗaga ta, kada ka ji tsoro; faɗa wa garuruwan Yahuda, “Ga Allahnku!”

Ishaya 52:7

Me ya fi wannan kyau a kan duwatsu a ga ƙafafu na masu kawo labari mai daɗi waɗanda suke shelar salama, waɗanda suke kawo labari mai daɗi, waɗanda suke shelar ceto, waɗanda suke ce wa Sihiyona, “Allahnki yana mulki!”

Ishaya 61:1-3

Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina, domin Ubangiji ya shafe ni domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta. Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci, don in yi shelar ’yanci don ɗaurarru in kuma kunce ’yan kurkuku daga duhu don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji da kuma ranar ɗaukan fansar Allahnmu, don in ta’azantar da dukan waɗanda suke makoki, in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona, in maido musu rawani mai kyau a maimako na toka, man murna a maimako na makoki, da kuma rigar yabo a maimako na ruhun fid da zuciya. Za a ce da su itatuwan oak na adalci, shukin Ubangiji don bayyana darajarsa.

Irmiya 1:6-9

Sai na ce, “Kayya, Ubangiji Mai Iko Duka, ban iya magana ba; ni ɗan yaro ne kawai.” Amma Ubangiji ya ce mini, “Kada ka ce, ‘Ni ɗan yaro ne kawai.’ Dole ka je wurin kowane mutumin da na aike ka ka kuma faɗa abin da na umarce ka. Kada ka ji tsoronsu, gama ina tare da kai kuma zan kiyaye ka,” in ji Ubangiji. Sai Ubangiji ya miƙa hannunsa ya taɓa bakina ya ce mini, “Yanzu na sa kalmomina a bakinka.

Irmiya 16:16

“Amma yanzu zan aiko a kira masunta masu yawa su zo,” in ji Ubangiji, “za su kuma kama su. Bayan wannan zan aiko a kira mafarauta su zo, su farauce su daga kowane dutse da tudu da kuma daga kogwannin duwatsu.

Ezekiyel 3:1-4

Ya kuma ce mini, “Ɗan mutum, ka ci abin da yake a gabanka, ka ci wannan littafi; sa’an nan ka tafi ka yi magana wa gidan Isra’ila.” Saboda haka na buɗe bakina, ya kuma ba ni littafin in ci. Sai ya ce mini, “Ɗan mutum, ka ci wannan littafin da nake ba ka, ka kuma cika cikinka da shi.” Sai na ci shi, ya kuma yi zaki kamar zuma a bakina. Sa’an nan ya ce mini, “Ɗan mutum, yanzu ka tafi gidan Isra’ila ka faɗa kalmomina gare su.

Daniyel 12:3

Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar hasken samaniya, waɗanda kuma suka jagoranci waɗansu da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.

Yunana 3:1-2

Sa’an nan sai maganar Ubangiji ta zo wa Yunana sau na biyu. “Tafi babban birnin nan Ninebe, ka yi masa shelar saƙon da na ba ka.”

Yunana 3:4-10

A rana ta fari, Yunana ya kama tafiya yana ratsa birnin. Sai ya yi shela cewa, “Nan da kwana arba’in za a hallaka Ninebe?” Mutanen Ninebe kuwa suka gaskata Allah. Aka yi shela a yi azumi, sai dukansu daga babba har zuwa ƙaraminsu, suka sa tufafin makoki. Da saƙon Yunana ya kai kunnen sarkin Ninebe, sai ya tashi daga kujerar mulkinsa, ya tuɓe alkyabbarsa, ya sa rigar makoki, ya zauna cikin toka. Sai ya yi umarni a Ninebe cewa, “Bisa ga umarnin sarki da fadawansa. “Kada a bar wani mutum ko dabba, garke ko shannu, su ɗanɗana wani abu; kada a bari su ci ko su sha. Bari kowane mutum da dabba yă yafa rigunan makoki. Kowa yă roƙi Allah da gaske, kowa kuma yă bar mugayen ayyukan da yake yi. Wa ya sani? Ko Allah zai ji tausayinmu da kuma juyayinmu yă janye zafin fushinsa don kada mu hallaka.” Da Allah ya ga abin da suka yi, da kuma yadda suka juya daga mugayen hanyoyinsu sai ya ji tausayinsu, bai kawo hallaka a kansu yadda ya yi shirin yi ba.

Nahum 1:15

Duba, can a bisa duwatsu, ga ƙafafu mai kawo labari mai daɗi, wanda yake shelar salama! Ki yi bukukkuwanki, ya Yahuda, ki kuma cika wa’adodinki. Mugaye ba za su ƙara mamaye ki ba; domin za a hallaka su ƙaƙaf.

Mattiyu 3:1-2

A waɗancan kwanaki, Yohanna Mai Baftisma ya zo, yana wa’azi a Hamadan Yahudiya yana cewa, “Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”

Mattiyu 3:7-8

Amma da Yohanna ya ga Farisiyawa da Sadukiyawa da yawa suna zuwa inda yake yin baftisma, sai ya ce musu, “Ku macizai! Wa ya gargaɗe ku ku guje wa fushin nan mai zuwa? Ku yi ayyukan da suka dace da tuba.

Mattiyu 4:4

Yesu ya amsa ya ce, ‹“A rubuce yake cewa, ‘Ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah.’›‹”›

Mattiyu 4:17

Tun daga wannan lokaci, Yesu ya fara wa’azi yana cewa, ‹“Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa.”›

Mattiyu 4:19-22

Sai Yesu ya ce, ‹“Zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masu jan mutane zuwa wurina.”› Nan da nan suka bar abin kamun kifinsu suka bi shi. Da ya ci gaba daga nan, sai ya ga waɗansu ’yan’uwa guda biyu, Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna. Suna cikin jirgin ruwa tare da mahaifinsu Zebedi, suna shirya abin kamun kifinsu. Yesu ya kira su, nan take suka bar jirgin ruwan da mahaifinsu suka kuwa bi Yesu.

Mattiyu 4:23

Yesu ya zazzaga dukan Galili, yana koyarwa a cikin majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin sama, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiyar mutane.

Mattiyu 5:11-13

‹“Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni.› ‹Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.› ‹“Ku ne gishirin duniya, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa? Ba shi da sauran amfani, sai dai a zubar da shi mutane kuma su tattaka.›

Mattiyu 5:14-16

‹“Ku ne hasken duniya. Birnin da yake a bisan tudu ba ya ɓoyuwa.› ‹Mutane ba sa ƙuna fitila su rufe ta da murfi. A maimako, sukan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, takan kuma ba da haske ga kowa a cikin gida.› ‹Haka ma, bari haskenku yă haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su kuwa yabi Ubanku da yake cikin sama.›

Mattiyu 6:19-21

‹“Kada ku yi wa kanku ajiyar dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda kuma ɓarayi sukan fasa, su yi sata.› ‹Amma ku yi wa kanku ajiyar dukiya a sama, inda ba tsatsa da asu da za su ɓata su, inda kuma ba ɓarayin da za su fasa, su yi sata.› ‹Gama inda dukiyarka take, a nan ne fa zuciyarka za tă kasance.›

Mattiyu 8:21-22

Sai wani almajiri ya ce masa, “Ubangiji, da farko bari in je in binne mahaifina.” Amma Yesu ya ce masa, ‹“Ka bi ni, ka bar matattu su binne matattunsu.”›

Mattiyu 9:9

Da Yesu ya yi gaba daga wurin, sai ya ga wani mutum mai suna Mattiyu zaune a inda ake karɓar haraji. Ya ce masa, ‹“Bi ni.”› Mattiyu kuwa ya tashi ya bi shi.

Mattiyu 9:35

Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.

Mattiyu 9:37-38

Sai ya ce wa almajiransa, ‹“Girbi yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne.› ‹Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbi, yă aiko da ma’aikata cikin gonarsa na girbi.”›

Mattiyu 10:7-8

‹Sa’ad da kuke tafiya, ku yi wa’azi, kuna cewa, ‘Mulkin sama ya kusato.’› ‹Ku warkar da marasa lafiya, ku tā da matattu, ku tsabtacce kutare, ku kuma fitar da aljanu. A kyauta kuka samu, ku kuma bayar a kyauta.›

Mattiyu 10:9-13

‹“Kada ku riƙe wata zinariya ko azurfa ko jan ƙarfe a aljihunanku,› ‹kada ku ɗauki jaka don tafiya, ko ƙarin riga, ko takalma ko sanda; domin ma’aikaci ya cancanci hakkinsa.› ‹Kowane gari ko ƙauyen da kuka shiga, ku nemi mai mutunci a wurin, ku kuma zauna a gidansa har sai kun tashi.› ‹Da shigarku gidan, ku yi gaisuwa.› ‹In gidan na kirki ne, bari salamarku ta zauna a kansa; in kuwa ba mai kirki ba, salamarku ta komo muku.›

Mattiyu 10:14-15

‹Duk wanda ya ƙi marabtarku ko ya ƙi sauraron kalmominku, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku sa’ad da kuka fita gidan ko garin.› ‹Gaskiya nake gaya muku, za a fi jin tausayin Sodom da Gomorra a ranar shari’a fiye da wannan gari.›

Mattiyu 10:16-18

‹“Ina aikan ku kamar tumaki a cikin kyarketai. Saboda haka ku zama masu wayo kamar macizai, kuma marasa ɓarna kamar kurciyoyi.› ‹Ku yi hankali da mutane; za su miƙa ku ga majalisa su kuma yi muku bulala a majami’unsu.› ‹Saboda ni, za a ja ku zuwa gaban gwamnoni da gaban sarakuna domin ku ba da shaida a gabansu, da kuma ga Al’ummai.›

Mattiyu 10:19-20

‹Amma sa’ad da suka kama ku, kada ku damu game da abin da za ku faɗa ko kuwa yadda za ku faɗe shi. A lokacin za a ba ku abin da za ku faɗa,› ‹gama ba ku ba ne kuke magana, amma Ruhun Ubanku ne yake magana ta wurinku.›

Mattiyu 10:21-23

‹“Ɗan’uwa zai ci amanar ɗan’uwansa, a kuma kashe shi, Uba ma zai yi haka da ɗansa; ’ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su.› ‹Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya jure har ƙarshe zai sami ceto.› ‹Sa’ad da aka tsananta muku a wannan wuri, ku gudu zuwa wancan. Gaskiya nake gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan biranen Isra’ila, Ɗan Mutum zai zo.›

Mattiyu 10:32-33

‹“Duk wanda ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin sama.› ‹Amma duk wanda ya yi mūsun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi mūsun saninsa a gaban Ubana da yake cikin sama.›

Mattiyu 10:34-40

‹“Kada fa ku ɗauka na zo ne don in kawo salama a duniya. A’a, ban zo don in kawo salama ba, sai dai takobi.› ‹Gama na zo ne in sa,› ‹“ ‘gāba tsakanin mutum da mahaifinsa,› ‹’ya da mahaifiyarta,› ‹matar ɗa da surukarta,› ‹abokan gāban mutum, za su zama mutanen gidansa ne.’› ‹“Duk wanda ya fi ƙaunar mahaifinsa ko mahaifiyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba; duk kuwa wanda yake ƙaunar ɗansa ko diyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba;› ‹duk wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai dace yă zama nawa ba.› ‹Duk mai son adana ransa zai rasa shi, duk wanda kuwa ya rasa ransa saboda ni zai same shi.› ‹“Wanda ya karɓe ku, ya karɓe ni ne, wanda kuma ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne.›

Mattiyu 11:1

Bayan Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan umarni, sai ya yi gaba daga can don yă koyar yă kuma yi wa’azi a garuruwan Galili.

Mattiyu 11:5-6

‹Makafi suna gani, guragu suna tafiya, ana warkar da waɗanda suke da kuturta, kurame suna ji, ana tā da matattu, ana kuma yi wa matalauta wa’azin labari mai daɗi.› ‹Mai albarka ne mutumin da bai yi tuntuɓe ba saboda ni.”›

Mattiyu 11:12

‹Tun daga kwanakin Yohanna Mai Baftisma har yă zuwa yanzu, mulkin sama yana sha da ƙyar, fitanannu kuma sun kama mulkin sama sun riƙe gam.›

Mattiyu 12:41

‹Mutanen Ninebe za su tashi a ranar shari’a tare da wannan zamani, su kuwa hukunta shi; don sun tuba saboda wa’azin Yunana, yanzu kuwa ga wanda ya fi Yunana girma a nan.›

Mattiyu 13:3-8

Sa’an nan ya faɗa musu abubuwa da yawa cikin misalai, yana cewa, ‹“Wani manomi ya fita don yă shuka irinsa.› ‹Da yana yafa irin, waɗansu suka fāffāɗi a kan hanya, tsuntsaye kuwa suka zo suka cinye su.› ‹Waɗansu suka fāɗi a wurare mai duwatsu, inda babu ƙasa sosai, nan da nan kuwa suka tsira, da yake ƙasar ba zurfi.› ‹Sai dai da rana ta ɗaga, sai tsire-tsiren suka ƙone, suka kuma yanƙwane domin ba su da saiwa sosai.› ‹Waɗansu irin suka fāɗi a cikin ƙaya, ƙayan kuwa ta yi girma ta shaƙe su.› ‹Har yanzu, waɗansu irin suka fāffāɗi a ƙasa mai kyau, inda suka ba da amfani riɓi ɗari, sittin ko kuma talatin na abin da aka shuka.›

Mattiyu 13:18-23

‹“To, ku saurari ma’anar misali na mai shukan nan.› ‹Duk sa’ad da wani ya ji saƙo game da mulkin bai kuwa fahimce shi ba, mugun nan yakan zo yă ƙwace abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da ya fāɗi a kan hanya.› ‹Wanda ya karɓi irin da ya fāɗi a wuraren duwatsu kuwa, shi ne mutumin da yakan ji maganar, nan da nan kuwa yă karɓe ta da murna.› ‹Sai dai da yake ba shi da saiwa, yakan ɗan jima kaɗan kawai. Da wata wahala ko tsanani ya auko masa saboda maganar, nan da nan sai yă ja da baya.› ‹Wanda ya karɓi irin da ya fāɗi cikin ƙaya kuwa, shi ne mutumin da yakan ji maganar, sai dai damuwoyin rayuwan nan da jarrabar arzikin duniya sukan shaƙe shi, yă sa maganar ta kāsa amfani.› ‹Amma wanda ya karɓi irin da ya fāɗi a ƙasa mai kyau, shi ne mutumin da yakan ji maganar yă kuwa fahimce ta. Yakan ba da amfani wani riɓi ɗari, sittin, ko talatin na abin da aka shuka.”›

Mattiyu 13:31-32

Ya ba su wani misali ya ce, ‹“Mulkin sama yana kama da ƙwayar mustad, wadda mutum ya ɗauka ya shuka a gonarsa.› ‹Ko da yake ita ce mafi ƙanƙanta cikin ƙwayoyinku, duk da haka sa’ad da ta yi girma, takan zama mafi girma cikin tsire-tsiren lambu ta kuma zama itace, har tsuntsayen sararin sama su zo su yi sheƙa a rassansa.”›

Mattiyu 15:13

Ya amsa ya ce, ‹“Duk tsiron da Ubana na sama bai shuka ba, za a tumɓuke shi daga saiwoyi.›

Mattiyu 16:24-27

Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, ‹“Duk mai son bina, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa, yă bi ni.› ‹Gama duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi.› ‹Me mutum zai amfana in ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa? Ko kuwa me mutum zai bayar a bakin ransa?› ‹Gama Ɗan Mutum zai zo cikin ɗaukakar Ubansa, tare da mala’ikunsa, sa’an nan zai ba wa kowane mutum lada gwargwadon abin da ya yi.›

Mattiyu 19:29

‹Duk kuma wanda ya bar gidaje ko ’yan’uwa maza ko ’yan’uwa mata ko mahaifi ko mahaifiya ko yara ko gonaki, saboda ni, zai sami abin da ya fi haka riɓi ɗari, yă kuma gāji rai madawwami.›

Mattiyu 20:1-15

‹“Mulkin sama yana kama da wani mai gona, wanda ya fita da sassafe don yă yi hayar mutane su yi aiki a gonar inabinsa.› ‹Ya yarda yă biya su dinari guda a yini, sai ya tura su gonar inabinsa.› ‹“Wajen sa’a ta uku, ya fita sai ya ga waɗansu suna tsattsaye a bakin kasuwa ba sa kome.› ‹Ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi gonar inabina ku yi aiki, zan kuwa biya ku abin da ya dace.’› ‹Saboda haka suka tafi.› ‹“Ya sāke fita a sa’a ta shida da kuma sa’a ta tara, ya sāke yin haka.› ‹Wajen sa’a ta goma sha ɗaya, ya sāke fita, ya tarar da waɗansu har yanzu suna tsattsaye. Ya tambaye su, ‘Don me kuke yini tsattsaye a nan ba kwa kome?’› ‹“Suka amsa, ‘Don ba wanda ya ɗauke mu aiki.’› ‹“Ya ce musu, ‘Ku ma ku je ku yi aiki a gonar inabina.’› ‹“Sa’ad da yamma ta yi, sai mai gonar inabin ya ce wa wakilinsa, ‘Kira ma’aikatan, ka biya su hakkin aikinsu, fara daga waɗanda aka ɗauke su a ƙarshe har zuwa na farko.’› ‹“Ma’aikatan da ka ɗauka wajen sa’a ta goma sha ɗaya suka zo, kowannensu kuwa ya karɓi dinari guda.› ‹Saboda haka da waɗanda aka ɗauka da fari suka zo, sun zaci za su sami fiye da haka. Amma kowannensu ma ya karɓi dinari guda.› ‹Sa’ad da suka karɓa, sai suka fara yin gunaguni a kan mai gonar.› ‹Suna cewa, ‘Waɗannan mutanen da aka ɗauka a ƙarshe sun yi aikin sa’a ɗaya ne kawai, ka kuma mai da su daidai da mu da muka yini muna faman aiki, muka kuma sha zafin rana.’› ‹“Amma ya amsa wa ɗayansu ya ce, ‘Aboki, ban cuce ka ba. Ba ka yarda ka yi aiki a kan dinari guda ba?› ‹Ka karɓi hakkinka ka tafi. Ni na ga damar ba waɗannan na ƙarshe daidai da yadda na ba ka.› ‹Ba ni da ikon yin abin da na ga dama da kuɗina ne? Ko kana kishi saboda ni mai kyauta ne?’›

Mattiyu 22:2-7

‹“Mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya shirya bikin auren ɗansa.› ‹Sai ya aiki bayinsa su kira waɗanda aka gayyata zuwa bikin, amma waɗanda aka ce su zo bikin, suka ƙi zuwa.› ‹“Sai ya sāke aiken waɗansu bayi ya ce, ‘Ku ce wa waɗanda aka gayyata cewa na shirya abinci. An yanka bijimai da shanun da aka yi kiwo, kome a shirye yake. Ku zo bikin auren mana.’› ‹“Amma ba su kula ba, suka kama gabansu, ɗaya ya tafi gonarsa, ɗaya kuma ya tafi kasuwancinsa.› ‹Sauran suka kama bayinsa suka wulaƙanta su, suka kuma kashe su.› ‹Sai sarkin ya yi fushi. Ya aiki mayaƙansa suka karkashe masu kisankan nan, aka kuma ƙone birninsu.›

Mattiyu 22:8-10

‹“Sa’an nan ya ce wa bayinsa, ‘Bikin aure fa ya shiryu, sai dai mutanen da na gayyata ba su dace ba.› ‹Ku bi titi-titi ku gayyato duk waɗanda kuka gani, su zo bikin.’› ‹Saboda haka bayin suka bi titi-titi, suka tattaro duk mutanen da suka samu, masu kirki da marasa kirki, zauren bikin ya cika makil da baƙi.›

Mattiyu 24:9-11

‹“Sa’an nan za a bashe ku don a tsananta muku a kuma kashe ku, dukan al’ummai za su ƙi ku saboda ni.› ‹A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna,› ‹annabawan ƙarya da yawa za su firfito su kuma ruɗi mutane da yawa.›

Mattiyu 24:14

‹Za a kuma yi wa’azin wannan bisharar mulki a cikin dukan duniya, yă zama shaida ga dukan al’ummai, sa’an nan ƙarshen yă zo.›

Mattiyu 28:18-20

Sai Yesu ya zo wurinsu ya ce, ‹“An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa.› ‹Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikin›‹sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki,› ‹kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani.”›

Markus 1:4

Ta haka Yohanna ya zo, yana baftisma a yankin hamada, yana kuma wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai.

Markus 1:14-15

Bayan da aka sa Yohanna a kurkuku, sai Yesu ya shigo cikin Galili, yana shelar bisharar Allah. Yana cewa, ‹“Lokaci ya yi. Mulkin Allah ya yi kusa. Ku tuba, ku gaskata bishara!”›

Markus 1:16-18

Yayinda Yesu yake tafiya a gaɓar Tekun Galili, sai ya ga Siman da ɗan’uwansa Andarawus, suna jefa abin kamun kifi a cikin tafkin, domin su masunta ne. Yesu ya ce, ‹“Ku zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masuntan mutane.”› Nan da nan, suka bar abin kamun kifinsu, suka bi shi.

Markus 1:38

Yesu ya amsa ya ce, ‹“Mu je wani wuri dabam, zuwa ƙauyukan da suke kusa, don in yi wa’azi a can ma. Wannan shi ne dalilin zuwana.”›

Markus 2:14

Yana cikin tafiya, sai ya ga Lawi, ɗan Alfayus zaune a inda ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, ‹“Bi ni.”› Sai Lawi ya tashi, ya bi shi.

Markus 3:14-15

Ya naɗa sha biyu, ya kira su manzanni don su kasance tare da shi, domin kuma yă aike su yin wa’azi, don kuma su sami ikon fitar da aljanu.

Markus 4:3-12

‹“Ku saurara! Wani manomi ya fita don yă shuka irinsa.› ‹Da yana yafa irin, sai waɗansu suka fāɗi a kan hanya, tsuntsaye suka zo suka cinye su.› ‹Waɗansu suka fāɗi a wuri mai duwatsu inda babu ƙasa sosai. Nan da nan, suka tsira domin ƙasar ba zurfi.› ‹Amma da rana ta taso, sai tsire-tsiren suka ƙone, suka yanƙwane, domin ba su da saiwa.› ‹Waɗansu irin suka fāɗi a cikin ƙaya. Da suka yi girma sai ƙaya suka shaƙe su, har ya sa ba su yi ƙwaya ba.› ‹Har yanzu, waɗansu irin suka fāɗi a ƙasa mai kyau. Suka tsira, suka yi girma, suka ba da amfani, suka yi riɓi talatin-talatin, waɗansu sittin-sittin, waɗansu kuma ɗari-ɗari.”› Sai Yesu ya ce, ‹“Duk mai kunnen ji, yă ji.”› Lokacin da yake shi kaɗai, Sha Biyun, da kuma waɗanda suke kewaye da shi, suka tambaye shi game da misalan. Sai ya ce musu, ‹“An ba ku sanin asirin mulkin Allah. Amma ga waɗanda suke waje kuwa, kome sai da misalai.› ‹Saboda,› ‹“ ‘ko sun dinga duba, ba za su taɓa gane ba,› ‹kuma ko su dinga ji, ba za su taɓa fahimta ba,› ‹in ba haka ba, mai yiwuwa, su tuba, a gafarta musu!’ ”›

Markus 4:13-20

Sai Yesu ya ce musu, ‹“Ba ku fahimci wannan misali ba? Yaya za ku fahimci wani misali ke nan?› ‹Manomi yakan shuka maganar Allah.› ‹Waɗansu mutane suna kama da irin da ya fāɗi a kan hanya, inda akan shuka maganar Allah. Da jin maganar, nan da nan sai Shaiɗan yă zo yă ɗauke maganar da aka shuka a zuciyarsu.› ‹Waɗansu suna kama da irin da aka shuka a wurare masu duwatsu, sukan ji maganar Allah, sukan kuma karɓe ta nan da nan da farin ciki.› ‹Amma da yake ba su da saiwa, ba sa daɗewa. Da wahala ko tsanani ya tashi saboda maganar, nan da nan, sai su ja da baya.› ‹Har yanzu, waɗansu kamar irin da aka shuka cikin ƙaya, sukan ji maganar,› ‹amma damuwar wannan duniya, da son dukiya, da kuma kwaɗayin waɗansu abubuwa, sukan shiga, su shaƙe maganar, har su mai da ita marar amfani.› ‹Waɗansu mutane kuwa suna kama da irin da aka shuka a ƙasa mai kyau, sukan ji maganar Allah, su kuma karɓa, sa’an nan kuma su fid da amfani riɓi talatin-talatin, ko sittin-sittin, ko ɗari-ɗari.”›

Markus 4:26-29

Ya sāke cewa, ‹“Mulkin Allah yana kama da haka. Wani mutum ya yafa iri a gona.› ‹A kwana a tashi har irin yă tsiro, yă yi girma, bai kuwa santa yadda aka yi ba.› ‹Ƙasar da kanta takan ba da ƙwaya, da farko takan fid da ƙara, sa’an nan ta fid da kai, sa’an nan kan yă fid da ƙwaya.› ‹Da ƙwayan ya nuna, sai yă sa lauje yă yanka, domin lokacin girbi ya yi.”›

Markus 4:30-32

Ya kuma ce, ‹“Da me za mu kwatanta mulkin Allah, ko kuwa da wane misali za mu bayyana shi?› ‹Yana kama da ƙwayar mustad, wadda ita ce ƙwaya mafi ƙanƙanta da akan shuka a gona.› ‹Duk da haka, in aka shuka ƙwayar, sai tă yi girma, tă zama mafi girma a itatuwan lambu. Har itacen yă kasance da manyan rassa, inda tsuntsayen sararin sama sukan iya huta a inuwarsa.”›

Markus 5:19-20

Yesu bai yardar masa ba, amma ya ce, ‹“Ka tafi gida wurin iyalinka, ka gaya musu babban alherin da Ubangiji ya yi maka, da yadda ya yi maka jinƙai.”› Sai mutumin ya tafi, ya yi ta ba da labari a cikin Dekafolis a kan babban alherin da Yesu ya yi masa. Dukan mutane kuwa suka yi mamaki.

Markus 6:7-10

Ya kira Sha Biyun nan wurinsa, ya aike su biyu-biyu, ya kuma ba su iko bisa mugayen ruhohi. Ga dai umarnansa, ‹“Kada ku ɗauki kome don tafiyar, sai dai sanda ba burodi, ba jaka, ba kuɗi a ɗamararku.› ‹Ku sa takalma, amma ban da riga fiye da waɗanda kuka sa.› ‹Duk sa’ad da kuka shiga wani gida, ku zauna nan sai kun bar garin.›

Markus 6:11-12

‹In kuwa a wani wuri ba a karɓe ku, ba a kuwa saurare ku ba, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku sa’ad da kuka fita, a matsayin shaida a kansu.”› Suka fita, suna yi wa’azi, suna ce wa mutane su tuba.

Markus 7:9

Ya kuma ce musu, ‹“Kuna da hanya mai sauƙi na ajiye umarnan Allah a gefe ɗaya, don ku kiyaye al’adunku!›

Markus 8:7-9

Suna kuma da ƙananan kifaye kaɗan, ya ba da godiya dominsu, ya kuma ce wa almajiran su rarraba musu. Mutanen suka ci, suka ƙoshi. Daga baya, almajiran suka tattara gutsattsarin da suka rage cike da kwanduna bakwai. Wajen maza dubu huɗu ne suka kasance. Da ya sallame su,

Markus 8:34-37

Sai ya kira taron wurinsa tare da almajiransa ya ce, ‹“Duk wanda zai bi ni, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa yă bi ni.› ‹Domin duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, da kuma bishara, zai same shi.› ‹Me mutum zai amfana, in ya ribato duniya duka a bakin ransa?› ‹Ko kuma, me mutum zai bayar a musayar ransa?›

Markus 8:38

‹Duk wanda ya ji kunyata, da na kalmomina a wannan zamani na fasikanci da zunubi, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa lokacin da ya shiga cikin ɗaukakar Ubansa, tare da tsarkakan mala’iku.”›

Markus 10:29-30

Yesu ya amsa ya ce, ‹“Gaskiya nake gaya muku, babu wanda zai bar gida, ko ’yan’uwa maza da mata, ko mahaifiya, ko mahaifi, ko ’ya’ya, ko gonaki saboda ni, da kuma bishara,› ‹sa’an nan yă kāsa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu (na gidaje, da ’yan’uwa mata, da ’yan’uwa maza, da uwaye, da ’ya’ya, da gonaki amma tare da tsanani) a lahira kuma yă sami rai madawwami.›

Markus 13:9-10

‹“Dole ku yi zaman tsaro. Za a ba da ku ga hukuma, a kuma bulale ku a majami’u. Saboda ni kuma, za ku tsaya a gaban gwamnoni da sarakuna, domin ku ba da shaida a gabansu.› ‹Dole sai an fara yin wa’azin bishara ga dukan al’ummai.›

Markus 13:11

‹Sa’ad da aka kama ku, aka kuma kai ku don a yi muku shari’a, kada ku damu da abin da za ku faɗa. Sai dai ku faɗi abin da aka ba ku a lokacin. Gama ba ku kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne.›

Markus 13:12-13

‹“Ɗan’uwa zai ba da ɗan’uwa a kashe. Mahaifi zai ba da ɗansa. ’Ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su.› ‹Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.›

Markus 16:15-16

Ya ce, musu, ‹“Ku tafi cikin dukan duniya, ku yi wa’azin bishara ga dukan halitta.› ‹Duk wanda ya gaskata, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma duk wanda bai gaskata ba kuwa, zai hallaka.›

Markus 16:20

Sai almajiran suka fita, suka yi wa’azi ko’ina. Ubangiji kuwa ya yi aiki tare da su, ya tabbatar da maganarsa ta wurin alamu da suke biye da maganar.

Luka 1:2

kamar yadda muka karɓe su daga waɗanda tun farko shaidu ne da kuma masu hidimar bishara.

Luka 1:77

don ka sanar da mutanensa ceto, ta wurin gafarar zunubansu,

Luka 2:10

Amma mala’ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Na kawo muku labari mai daɗi na farin ciki mai yawa ne wanda zai zama domin dukan mutane.

Luka 3:3-6

Ya zaga dukan ƙasar da take kewaye da Urdun, yana wa’azin baftismar tuba don gafarar zunubai. Kamar yadda yake a rubuce a littafin annabi Ishaya. “Muryar mai kira a hamada, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa. Za a cike kowane kwari, a farfashe kowane dutse da kowane tudu. Za a miƙe hanyoyin da suka karkace, a gyaggyara hanyoyi masu gargaɗa su zama sumul. Dukan ’yan Adam kuwa za su ga ceton Allah!’ ”

Luka 3:18

Da kalmomi masu yawa Yohanna ya yi wa mutane gargaɗi, ya kuma yi musu wa’azin bishara.

Luka 4:18

‹“Ruhun Ubangiji yana kaina,› ‹domin ya shafe ni,› ‹in yi wa matalauta wa’azin bishara.› ‹Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku,› ‹in kuma buɗe idanun makafi,› ‹in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne.›

Luka 4:43

Amma ya ce, ‹“Dole in yi wa’azin bisharar mulkin Allah ga sauran garuruwa, saboda wannan ne aka aiko ni.”›

Luka 5:4-11

Da ya gama magana, sai ya ce wa Siman, ‹“Ka tuƙa jirgin zuwa inda akwai zurfi, ka saukar da abin kamun kifinka ka kama kifi.”› Siman ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, duk dare mun yi ta fama ba mu kama kome ba, amma tun da ka ce haka, zan saki abin kamun kifin.” Da suka yi haka, sai suka kama kifi da yawa, har abin kamun kifinsu suka fara tsintsinkewa. Sai suka kira abokansu a ɗaya jirgin, su zo su taimake su, suka kuwa zo. Suka cika jiragen biyu da kifi cif, har jiragen suka fara nutsewa. Da Siman Bitrus ya ga wannan, sai ya fāɗi a gaban Yesu ya ce, “Rabu da ni, Ubangiji. Ni mai zunubi ne!” Gama mamaki ya kama shi da abokansa duka, saboda yawan kifin da suka kama. Yaƙub da Yohanna, ’ya’yan Zebedi, abokan aikin Siman su ma suka yi mamaki. Sai Yesu ya ce wa Siman, ‹“Kada ka ji tsoro, daga yanzu za ka riƙa kama mutane ne.”› Sai suka jawo jiragen ruwansu zuwa gaci, suka bar kome da kome, suka bi shi.

Luka 5:27-28

Bayan wannan, sai Yesu ya fita, ya ga wani mai karɓar haraji, mai suna Lawi, yana zaune a wurin da ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, ‹“Bi ni.”› Sai Lawi ya tashi, ya bar kome da kome, ya bi shi.

Luka 6:23

‹“Ku yi farin ciki a wannan rana, ku kuma yi tsalle don murna, saboda ladarku yana da yawa a sama. Gama haka kakanninsu suka yi wa annabawa.›

Luka 7:22-23

Sai ya amsa wa almajiran Yohanna ya ce, ‹“Ku koma ku faɗa wa Yohanna abin da kuka ji, da abin da kuka gani. Makafi suna ganin gari, guragu suna tafiya, ana warkar da waɗanda suke da kuturta, kurame suna ji, ana tā da matattu, ana kuma yi wa matalauta wa’azin bishara.› ‹Mai albarka ne mutumin da bai yi shakkar bangaskiyar da yake da ita a kaina ba.”›

Luka 8:1

Bayan wannan sai Yesu ya zazzaga gari da ƙauye, yana wa’azin bisharar mulkin Allah. Sha Biyun nan kuwa suna tare da shi,

Luka 8:5-10

‹“Wani manomi ya fita domin ya shuka irinsa. Da yana watsa irin, sai waɗansu suka fāɗi a kan hanya, aka tattaka su, tsuntsayen sararin sama kuma suka cinye su.› ‹Waɗansu suka fāɗi a kan dutse, da suka tsira sai suka yanƙwane don babu ruwa a wurin.› ‹Waɗansu kuma suka fāɗi a cikin ƙaya. Da suka yi girma tare, sai ƙayan suka shaƙe su.› ‹Waɗansu kuma har yanzu, suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka yi girma, suka ba da amfani riɓi ɗari-ɗari, fiye da abin da aka shuka.”› Da faɗin haka sai ya ce, ‹“Duk mai kunnen ji, yă ji.”› Almajiransa suka tambaye shi ma’anar wannan misali. Sai ya ce, ‹“Ku ne aka ba sanin asirin mulkin Allah, amma ga sauran mutane kam, ina magana da misalai, saboda,› ‹“ ‘ko da yake suna kallo, ba za su gani ba,› ‹ko da yake suna ji, ba za su gane ba.’›

Luka 8:11-15

‹“Ga ma’anar misalin, irin, shi ne maganar Allah.› ‹Waɗanda suka fāɗi a kan hanya su ne mutanen da suka ji, amma Iblis, yakan zo ya ɗauke maganar daga zuciyarsu, don kada su gaskata, su sami ceto.› ‹Na kan dutse kuwa, su ne da jin maganar, sukan karɓa da murna, amma ba su da saiwa. Sukan gaskata na ɗan lokaci, amma lokacin gwaji, sai su ja da baya.› ‹Irin da suka fāɗi a cikin ƙaya kuwa, su ne mutanen da suka ji, amma a kwana a tashi, tunanin kayan duniya, da neman arziki, da son jin daɗi, sukan hana su ba da ’ya’ya.› ‹Amma irin da suka fāɗi a ƙasa mai kyau kuwa, su ne mutane masu kyakkyawar zuciya, mai kyau, da suka ji, suka riƙe, suka kuma jimre har suka ba da ’ya’ya.”›

Luka 8:39

‹“Koma gida, ka shaida babban alherin da Allah ya yi maka.”› Sai mutumin ya tafi yana faɗin abin da Yesu ya yi masa a duk garin.

Luka 9:1-4

Bayan da Yesu ya tara Sha Biyun wuri ɗaya, sai ya ba su iko da izini na fitar da dukan aljanu, da na warkar da cututtuka. Ya kuma aike su, su yi wa’azin mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya. Ya ce musu, ‹“Kada ku ɗauki kome don tafiyar, wato, ba sanda, ba jaka, ba burodi, ba kuɗi, ba riga na biyu.› ‹Duk gidan da kuka sauka, ku zauna nan sai kun bar garin.›

Luka 9:5-6

‹In mutane ba su karɓe ku ba, sa’ad da kun bar garinsu, ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku don shaida a kansu.”› Sai suka tashi suka shiga ƙauye zuwa ƙauye suna wa’azin bishara, suna warkar da marasa lafiya a ko’ina.

Luka 9:23-25

Sai ya ce wa dukansu, ‹“In wani zai bi ni, dole yă mūsanta kansa, ya ɗauki gicciyensa kowace rana, ya bi ni.› ‹Gama duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni zai same shi.› ‹Ina amfani, in mutum ya ribato duniya duka, amma ya rasa ransa, ko kuma ya yi hasarar ransa.›

Luka 9:26

‹Duk wanda yake jin kunyana da na kalmomina, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa sa’ad da zai zo a cikin ɗaukakarsa, da ɗaukakar Uban, da kuma ta tsarkaka mala’ikun.›

Luka 9:59-60

Ya kuma ce wa wani mutum, ‹“Ka bi ni.”› Amma mutumin ya amsa ya ce, “Ubangiji, bari in je in binne mahaifina tukuna.” Yesu ya ce masa, ‹“Ka bar matattu su binne matattunsu, amma kai, ka je ka yi shelar mulkin Allah.”›

Luka 9:61-62

Har wa yau, wani ya ce, “Zan bi ka, Ubangiji, amma ka bar ni in je in yi bankwana da iyalina tukuna.” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Babu wani da yakan sa hannunsa a garman shanu, sa’an nan ya waiwaya baya, da ya isa ya shiga hidima a cikin mulkin Allah ba.”›

Luka 10:1

Bayan haka, Ubangiji ya naɗa waɗansu mutum saba’in da biyu, ya aike su biyu-biyu, su riga shi yin gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da zai shiga.

Luka 10:2

Ya ce musu, ‹“Girbi na da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. Saboda haka, ku roƙi Ubangijin girbi ya aikar da ma’aikata zuwa gonarsa.›

Luka 10:3-4

‹Ku tafi! Ina aikan ku kamar tumaki cikin kyarketai.› ‹Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko jaka, ko takalma. Kada ma ku gai da kowa a kan hanya.›

Luka 10:10-12

‹Amma sa’ad da kuka shiga garin, kuma ba a karɓe ku ba, ku bi titi-titi ku ce,› ‹‘Ko ƙurar garinku da kuke manne a ƙafafunmu, mun karkaɗe muku. Duk da haka, ku tabbatar da wannan, “Mulkin Allah yana kusa.” ’› ‹Ina dai faɗa muku, a ranan nan, za a fi jin tausayin Sodom fiye da wannan garin.›

Luka 10:16

‹“Wanda ya saurare ku, ni yake saurara. Wanda ya ƙi ku, ni yake ƙi. Amma wanda ya ƙi ni kuwa, ya ƙi wanda ya aiko ni ne.”›

Luka 11:32

‹A ranar shari’a, mutanen Ninebe za su tashi tsaye tare da wannan zamani, su yanke wa wannan zamani hukunci. Gama sun tuba sa’ad da Yunana ya yi musu wa’azi. Ga shi yanzu, shi wanda ya fi Yunana girma, na nan.›

Luka 12:8-9

‹“Ina gaya muku, duk wanda ya shaida ni a gaban mutane, Ɗan Mutum ma zai shaida shi a gaban mala’ikun Allah.› ‹Amma wanda ya yi mūsun sanina a gaban mutane, shi ma za a yi mūsunsa a gaban mala’ikun Allah.›

Luka 12:11-12

‹“Sa’ad da an kai ku a gaban majami’u, da gaban masu mulki, da kuma gaban masu iko, kada ku damu da yadda za ku kāre kanku, ko kuma abin da za ku faɗa,› ‹gama Ruhu Mai Tsarki zai koya muku abin da ya dace ku faɗa a lokacin.”›

Luka 12:33-34

‹Ku sayar da dukiyarku, ku ba wa matalauta. Ku yi wa kanku jakar kuɗin da ba za su lalace ba. Ku yi wa kanku ajiyar dukiyar da ba za tă kare ba a sama, inda ɓarawo ba zai yi kusa ba, asu kuma ba za su iya su lalatar ba.› ‹Gama inda dukiyarku take, nan ne zuciyarku ma take.›

Luka 12:51-53

‹Kuna tsammani na zo domin in kawo salama a duniya ne? A’a! Ina gaya muku, rabuwa ne.› ‹Daga yanzu, za a iske mutum biyar a gida ɗaya sun rabu, suna gāba da juna, uku suna gāba da biyu, biyun suna gāba da ukun.› ‹Za su rarrabu. Mahaifi yana gāba da ɗan, ɗan kuma yana gāba da mahaifin. Mahaifiya tana gāba da diyar, diyar kuma tana gāba da mahaifiyar. Suruka tana gāba da matar ɗa, matar ɗa kuma tana gāba da suruka.”›

Luka 13:5

‹Ina gaya muku, a’a! Amma in ba ku tuba ba, ku ma duka za ku hallaka.”›

Luka 14:16-24

Yesu ya amsa ya ce, ‹“Wani mutum yana shirya wani babban biki, ya kuma gayyaci baƙi da yawa.› ‹Da lokacin bikin ya yi, sai ya aiki bawansa ya je ya ce wa waɗanda aka gayyata, ‘Ku zo, don an shirya kome.’› ‹“Amma sai dukansu suka fara ba da hujjoji. Na farkon ya ce, ‘Na sayi gona yanzun nan, dole in je in ga yadda take, ina roƙonka ka yi mini haƙuri.’› ‹“Wani ya ce, ‘Na sayi shanun noma guda goma yanzun nan, ina kan hanyata ke nan in gwada su, ina roƙonka, ka yi mini haƙuri.’› ‹“Har yanzu wani ya ce, ‘Na yi aure yanzun nan, don haka ni ba zan iya zuwa ba.’› ‹“Bawansa ya dawo ya gaya wa maigidansa wannan. Sai maigidan ya yi fushi, ya ba da umarni ga bawansa ya ce, ‘Ka fita da sauri, ka bi titi-titi da lungu-lungu na garin, ka kawo matalauta, da guragu, da makafi, da shanyayyu.’› ‹“Bawan ya dawo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, an yi abin da ka umarta, amma har yanzu da sauran wuri.’› ‹“Maigidan ya ce wa bawansa, ‘Ka je kan hanyoyin da layi-layi na karkara, ka sa su shigo, don gidana ya cika.’› ‹Ina gaya muku, babu ko ɗaya daga cikin mutanen nan da aka gayyata da zai ɗanɗana bikina.”›

Luka 14:26-27

‹“Duk wanda yakan zo wurina, amma bai ƙi mahaifinsa da mahaifiyarsa, da matarsa da ’ya’yansa, da ’yan’uwansa mata da maza, kai, har ma ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba.› ‹Kuma duk wanda ba yakan ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, ba zai iya zama almajirina ba.›

Luka 14:33-34

‹Haka nan fa, kowane ne a cikinku, da ba ya rabu da abin da yake da shi ba, ba zai iya zama almajirina ba.› ‹“Gishiri fa yana da kyau, amma in gishiri ya rabu da daɗin ɗanɗanonsa, ta yaya za a sāke mai da daɗin ɗanɗanonsa?›

Luka 15:7

‹Ina gaya muku, haka za a yi murna sosai a sama, a kan mai zunubi guda ɗaya da ya tuba, fiye da masu adalci tasa’in da tara, waɗanda ba su bukatan tuba.›

Luka 15:10

‹Haka, ina gaya muku, akwai murna a gaban mala’ikun Allah a kan mai zunubi guda ɗaya, da ya tuba.”›

Luka 19:10

‹Saboda Ɗan Mutum ya zo ne, domin yă nemi abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.”›

Luka 20:1

Wata rana da Yesu yana koyar da mutane, yana musu wa’azin bishara a filin haikalin, sai manyan firistoci da malaman dokoki, tare da dattawan suka zo wurinsa.

Luka 21:12-13

‹“Amma kafin duk abubuwa nan, za a kama ku a tsananta muku. Za a kai ku majami’u, da kurkuku. Za a kuma kai ku gaban sarakuna da gwamnoni, kuma dukan waɗannan saboda sunana.› ‹Wannan zai sa ku zama shaidu a gare su.›

Luka 21:14-15

‹Amma ku yi ƙuduri, wato, ku shirya zuciyarku, a kan ba za ku damu ba kafin lokacin, game da yadda za ku kāre kanku.› ‹Gama zan ba ku kalmomi, da hikima waɗanda ba ko ɗaya daga cikin maƙiyanku, za su iya tsayayya da ku, ko su ƙaryata.›

Luka 21:16-17

‹Har iyayenku, da ’yan’uwanku maza, da danginku, da abokanku ma, duk za su bashe ku, su kuma kashe waɗansunku.› ‹Duk mutane za su ƙi ku saboda ni.›

Luka 22:35-36

Sai Yesu ya tambaye, su ya ce, ‹“Lokacin da na aike ku ba tare da jakar kuɗi, ko jaka, ko takalma ba, kun rasa wani abu?”› Suka amsa, “Babu.” Ya ce musu, ‹“Amma yanzu, in kuna da jakar kuɗi, ko jaka, ku ɗauka. In kuma ba ku da takobi, ku sayar da rigarku, ku saya.›

Luka 24:47-48

‹Kuma a cikin sunansa za a yi wa’azin tuba da gafarar zunubai, ga dukan ƙasashe. Za a kuwa fara daga Urushalima.› ‹Ku ne shaidun waɗannan abubuwa.›

Yohanna 1:12-13

Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ’ya’yan Allah ’ya’yan da aka haifa ba bisa hanyar ’yan adam, ko shawarar mutum ko nufin namiji ba, sai dai haifaffu bisa ga nufin Allah.

Yohanna 1:43

Kashegari Yesu ya yanke shawara yă tafi Galili. Da ya sami Filibus sai ya ce masa, ‹“Bi ni.”›

Yohanna 3:3-8

Yesu ya amsa ya ce, ‹“Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.”› Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya za a haifi mutum sa’ad da ya tsufa? Tabbatacce ba zai sāke koma sau na biyu a cikin mahaifiyarsa don a haife shi kuma ba!” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an haife shi ta wurin ruwa da kuma Ruhu.› ‹Jiki yakan haifi jiki, amma Ruhu yana haifi ruhu.› ‹Kada ka yi mamaki da na ce, ‘Dole ne a sāke haifarku.’› ‹Iska takan hura zuwa inda take so. Kai kakan ji motsinta, sai dai ba ka iya sanin inda take fitowa ko kuwa inda za ta. Haka yake ga duk wanda aka haifa ta wurin Ruhu.”›

Yohanna 3:11-12

‹Gaskiya nake faɗa maka, muna magana a kan abin da muka sani, muka kuma shaida abin da muka gani ne, amma har yanzu kun ƙi ku karɓi shaidarmu.› ‹Na yi muku magana a kan abubuwan duniya amma ba ku gaskata ba; to, yaya za ku gaskata in na yi magana a kan abubuwan sama?›

Yohanna 3:16-21

Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami. Gama Allah bai aiki Ɗansa duniya don yă yi wa duniya hukunci ba, sai dai domin yă ceci duniya ta wurinsa. Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba. Hukuncin shi ne, Haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka so duhu a maimakon haske domin ayyukansu mugaye ne. Duk mai aikata mugunta yana ƙin haske, ba zai kuwa zo cikin haske ba don yana tsoro kada ayyukansa su tonu. Amma duk mai rayuwa bisa ga gaskiya yakan zo cikin haske, domin a gani a sarari cewa ayyukan da ya yi an yi su ne ta wurin Allah.

Yohanna 3:36

Duk wanda ya gaskata da Ɗan yana da rai madawwami, amma duk wanda ya ƙi Ɗan ba zai sami rai ba, gama fushin Allah yana nan a bisansa.”

Yohanna 4:35-38

‹Ba kukan ce, ‘Sauran wata huɗu a yi girbi ba?’ Ina gaya muku, ku ɗaga idanu ku dubi gonaki! Sun isa girbi.› ‹Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare.› ‹Karin maganan nan gaskiya ne cewa, ‘Wani da shuka, wani kuma da girbi.’› ‹Na aike ku girbin abin da ba ku yi aikinsa ba. Waɗansu sun yi aikin nan mai wahala, ku kuwa kun sami ladan aikinsu.”›

Yohanna 5:24

‹“Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ji maganata ya kuma gaskata da wanda ya aiko ni yana da rai madawwami ba za a kuma hukunta shi ba; ya riga ya ƙetare daga mutuwa zuwa rai.›

Yohanna 8:24

‹Na gaya muku cewa za ku mutu cikin zunubanku; in ba ku gaskata cewa ni ne wanda na ce nake ba, lalle za ku mutu cikin zunubanku.”›

Yohanna 8:31-32

Sai Yesu ya ce wa Yahudawan da suka gaskata da shi, ‹“In dai kun riƙe koyarwata, ku almajiraina ne da gaske.› ‹Sa’an nan za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za tă ’yantar da ku.”›

Yohanna 9:4

‹Muddin da sauran rana, dole mu yi aikin wanda ya aiko ni. Dare yana zuwa, sa’ad da ba wanda zai iya yin aiki.›

Yohanna 10:1

‹“Gaskiya nake gaya muku, mutumin da bai shiga inda ake ajiye garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya hau ta katanga, ɓarawo ne, ɗan fashi kuma.›

Yohanna 12:48-49

‹Akwai mai hukunci saboda wanda ya ƙi ni, bai kuma karɓi kalmomina ba; wannan maganar da na faɗa ita ce za tă hukunta shi a rana ta ƙarshe.› ‹Gama ba don kaina na yi magana ba, Uban da ya aiko ni shi kansa ne ya ba ni umarni a kan abin da zan faɗa da kuma yadda zan faɗe shi.›

Yohanna 14:6

Yesu ya amsa ya ce, ‹“Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina.›

Yohanna 20:31

An dai rubuta waɗannan ne don ku gaskata Yesu ne Kiristi, Ɗan Allah kuma ta wurin gaskatawa ku sami rai a cikin sunansa.

Yohanna 21:6-11

Ya ce musu, ‹“Ku jefa abin kamun kifinku dama da jirgin ruwan, za ku samu.”› Da suka yi haka, sai suka kāsa jawo abin kamun kifin saboda yawan kifi. Sai almajirin da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, “Ai, Ubangiji ne!” Nan da nan da Siman Bitrus ya ji ya ce, “Ai, Ubangiji ne,” sai ya yafa mayafinsa (don dā ma ya tuɓe shi), ya fāɗa cikin ruwan. Sauran almajiran kuwa suka bi shi cikin jirgin ruwan, janye da abin kamun kifin cike da kifi, don ba su da nisa daga gaci, wajen yadi ɗari ne. Da suka sauka, sai suka ga garwashin wuta a can da kifi a kai, da kuma ’yan burodi. Yesu ya ce musu, ‹“Ku kawo waɗansu kifin da kuka kama yanzu.”› Sai Siman Bitrus ya hau ya jawo abin kamun kifin gaci. Ya cika da manyan kifi, 153, amma duk da yawansun nan abin kamun kifin bai tsintsinke ba.

Ayyukan Manzanni 1:8

‹Amma ku za ku karɓi iko sa’ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauka a kanku; za ku kuma zama shaiduna cikin Urushalima, da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, zuwa kuma iyakar duniya.”›

Ayyukan Manzanni 2:21

Kuma duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.’

Ayyukan Manzanni 2:38-40

Bitrus ya amsa, “Ku tuba a kuma yi muku baftisma, kowannenku a cikin sunan Yesu Kiristi domin gafarar zunubanku. Za ku kuwa karɓi kyautar Ruhu Mai Tsarki. Alkawarin dominku ne da ’ya’yanku da kuma dukan waɗanda suke da nesa, domin dukan waɗanda Ubangiji Allahnmu zai kira.” Da waɗansu kalmomi masu yawa ya gargaɗe su; ya kuma roƙe su cewa, “Ku ceci kanku daga wannan lalataccen zamani.”

Ayyukan Manzanni 2:41

Waɗanda suka yarda da saƙonsa kuwa aka yi musu baftisma, a ranar kuwa yawansu ya ƙaru da mutum kusan dubu uku.

Ayyukan Manzanni 2:47

suna yabon Allah suna kuma samun tagomashin dukan mutane. Ubangiji kuwa ya ƙara yawansu kowace rana na waɗanda suke samun ceto.

Ayyukan Manzanni 3:19-21

Saboda haka ku tuba, ku juyo ga Allah, don a shafe zunubanku, don lokutan wartsakewa su zo daga wurin Ubangiji, don kuma ya iya aika da Kiristi, wanda aka naɗa tun dā saboda ku, Yesu ke nan. Dole yă kasance a sama, sai lokaci ya yi da Allah zai mai da kome sabo, yadda ya yi alkawari tun dā ta wurin annabawansa masu tsarki.

Ayyukan Manzanni 4:4

Amma da yawa da suka ji saƙon suka gaskata, yawan mutanen kuwa ya ƙaru ya kai wajen dubu biyar.

Ayyukan Manzanni 4:12

Ba a samun ceto ta wurin wani dabam, gama babu wani suna a ƙarƙashin sama da aka ba wa mutane wanda ta wurinsa dole mu sami ceto.”

Ayyukan Manzanni 4:13

Da suka ga ƙarfin halin Bitrus da Yohanna suka kuma gane cewa su marasa ilimi ne, talakawa kuma, sai suka yi mamaki suka kuma lura cewa waɗannan mutane sun kasance tare da Yesu.

Ayyukan Manzanni 4:18-20

Sai suka sāke kiransu ciki suka kuma umarce su kada su kuskura su yi magana ko su ƙara koyarwa a cikin sunan Yesu. Amma Bitrus da Yohanna suka amsa, “Ku shari’anta da kanku ko daidai ne a gaban Allah mu yi muku biyayya maimakon Allah. Gama ba za mu iya daina yin magana game da abin da muka gani muka kuma ji ba.”

Ayyukan Manzanni 4:29-31

Yanzu, Ubangiji, ka dubi barazanansu ka kuma sa bayinka su furta maganarka da iyakar ƙarfin hali. Ka miƙa hannunka don ka warkar ka kuma yi ayyukan banmamaki da alamu masu banmamaki ta wurin sunan bawanka mai tsarki Yesu.” Bayan suka yi addu’a, sai inda suka taru ya jijjigu. Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki, suka yi ta shaidar maganar Allah babu tsoro.

Ayyukan Manzanni 4:33

Da iko mai ƙarfi manzanni suka ci gaba da shaidar tashin matattu na Ubangiji Yesu, alheri mai yawa kuwa yana bisansu duka.

Ayyukan Manzanni 5:27-29

Da suka kawo manzannin, sai suka sa su suka bayyana a gaban Majalisar don babban firist ya tuhume su. Ya ce, “Mun kwaɓe ku da gaske kada ku ƙara koyarwa cikin wannan suna, duk da haka kun cika Urushalima da koyarwarku, har ma kuna so ku ɗora mana laifin jinin mutumin nan.” Bitrus da sauran manzannin suka amsa suka ce, “Dole ne mu yi wa Allah biyayya a maimakon mutane!

Ayyukan Manzanni 5:40-42

Jawabinsa ya rinjaye su. Suka kira manzannin suka sa aka yi musu bulala. Sa’an nan suka kwaɓe su kada su ƙara magana a cikin sunan Yesu, suka kuma bar su suka tafi. Manzannin suka bar Majalisar, suna farin ciki domin an ga sun cancanta a kunyata su saboda Sunan nan. Kowace rana, a filin haikali da kuma gida-gida, ba su fasa koyarwa da kuma shelar labari mai daɗi cewa Yesu shi ne Kiristi ba.

Ayyukan Manzanni 8:4-5

Waɗanda aka wartsar suka yi ta wa’azin maganar a duk inda suka tafi. Filibus ya gangara zuwa wani birni a Samariya ya kuma yi shelar Kiristi a can.

Ayyukan Manzanni 8:12

Amma da suka gaskata da Filibus sa’ad da yake wa’azin labari mai daɗi na mulkin Allah da kuma sunan Yesu Kiristi, sai aka yi musu baftisma, maza da mata.

Ayyukan Manzanni 8:25

Sa’ad da suka yi shaidar suka kuma yi shelar maganar Ubangiji, sai Bitrus da Yohanna suka koma Urushalima, suna wa’azin bishara a ƙauyukan Samariya masu yawa.

Ayyukan Manzanni 8:35-38

Sa’an nan Filibus ya fara da wannan Nassi ɗin ya kuma faɗa masa labari mai daɗi game da Yesu. Yayinda suke cikin tafiya a kan hanya, sai suka iso wani wurin ruwa bābān nan ya ce, “Duba, ga ruwa. Me zai hana a yi mini baftisma?” Ya kuwa ba da umarni a tsai da keken yaƙin. Sa’an nan da Filibus da bābān suka gangara zuwa cikin ruwan Filibus kuwa ya yi masa baftisma.

Ayyukan Manzanni 8:40

Filibus kuwa ya fito a Azotus, ya yi ta zagawa, yana wa’azin bishara a dukan garuruwan sai da ya kai Kaisariya.

Ayyukan Manzanni 9:27-29

Amma Barnabas ya ɗauke shi ya kawo shi wurin manzanni. Ya gaya musu yadda Shawulu a kan hanyarsa ya ga Ubangiji kuma cewa Ubangiji ya yi magana da shi, da yadda a Damaskus ya yi wa’azi ba tsoro a cikin sunan Yesu. Saboda haka Shawulu ya zauna tare da su yana kai da kawowa a sake a cikin Urushalima, yana magana gabagadi a cikin sunan Ubangiji. Ya yi magana ya kuma yi muhawwara da Yahudawa masu jin Hellenanci, amma suka yi ƙoƙarin kashe shi.

Ayyukan Manzanni 10:36-37

Kun san saƙon da Allah ya aika wa mutanen Isra’ila, yana shelar labari mai daɗi na salama ta wurin Yesu Kiristi, shi ne kuwa Ubangijin kowa. Kun san abin da ya faru a dukan Yahudiya, farawa daga Galili bayan baftismar da Yohanna ya yi wa’azi,

Ayyukan Manzanni 10:42-44

Ya umarce mu mu yi wa’azi ga mutane mu kuma shaida cewa shi ne wanda Allah ya naɗa yă zama mai shari’a na masu rai da na matattu. Duk annabawa sun yi shaida game da shi cewa duk wanda ya ba da gaskiya gare shi zai sami gafarar zunubai ta wurin sunansa.” Tun Bitrus yana cikin faɗin waɗannan kalmomi, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauka wa duk waɗanda suka ji saƙon.

Ayyukan Manzanni 11:1

Manzanni da ’yan’uwa ko’ina a Yahudiya suka ji cewa Al’ummai ma sun karɓi maganar Allah.

Ayyukan Manzanni 11:13-14

Ya kuma gaya mana yadda wani mala’ika ya bayyana a gidansa ya ce masa, ‘Ka aika zuwa Yoffa a kira Siman wanda ake ce da shi Bitrus. Zai kawo maka saƙo wanda ta wurinsa kai da dukan iyalinka za ku sami ceto.’

Ayyukan Manzanni 11:18

Sa’ad da suka ji haka, ba su ƙara yin faɗa ba, suka kuma ɗaukaka Allah, suna cewa, “To, fa, har Al’ummai ma Allah ya sa suka tuba zuwa rai.”

Ayyukan Manzanni 11:20-21

Amma waɗansunsu kuwa, mutane daga Saifurus da Sairin, suka je Antiyok suka fara yi wa Hellenawa magana su ma, suna ba da labari mai daɗi game da Ubangiji Yesu. Hannun Ubangiji kuwa yana tare da su, mutane da yawan gaske kuwa suka gaskata suka juya ga Ubangiji.

Ayyukan Manzanni 13:24

Kafin zuwan Yesu, Yohanna ya yi wa’azin tuba da baftisma ga dukan mutanen Isra’ila.

Ayyukan Manzanni 13:32

“Muna gaya muku labari mai daɗi cewa abin da Allah ya yi wa kakanninmu alkawari,

Ayyukan Manzanni 13:44

A ranar Asabbaci na biye kusan dukan birnin suka taru don su ji maganar Ubangiji.

Ayyukan Manzanni 13:46-47

Sai Bulus da Barnabas suka amsa musu gabagadi, suka ce, “Ya zama mana dole mu yi muku maganar Allah da farko. Da yake kun ƙi ta ba ku kuma ga kun cancanci rai madawwami ba, to, za mu juya ga Al’ummai. Gama abin da Allah ya umarce mu ke nan cewa, “ ‘Na sa ka zama haske ga Al’ummai, don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.’”

Ayyukan Manzanni 13:48-49

Sa’ad da Al’ummai suka ji haka, sai suka yi farin ciki suka ɗaukaka maganar Ubangiji; kuma duk waɗanda aka zaɓa don samun rai madawwami, suka gaskata. Maganar Ubangiji kuwa ta bazu a dukan yankin.

Ayyukan Manzanni 13:50-51

Amma Yahudawa suka zuga waɗansu mata masu tsoron Allah masu martaba da kuma waɗansu maza masu matsayi a gari. Suka tā da tsanani ga Bulus da Barnabas, suka kore su daga yankinsu. Saboda haka suka karkaɗe ƙurar ƙafafunsu don shaidar a kansu suka kuwa tafi Ikoniyum.

Ayyukan Manzanni 14:1-2

A Ikoniyum Bulus da Barnabas suka shiga majami’ar Yahudawa yadda suka saba. A can suka yi magana gabagadi har Yahudawa da Al’ummai masu yawa suka gaskata. Amma Yahudawan da suka ƙi ba da gaskata, suka zuga Al’ummai suka sa ɓata tsakaninsu da ’yan’uwa.

Ayyukan Manzanni 14:3

Bulus da Barnabas kuwa suka daɗe sosai a can, suna magana gabagadi saboda Ubangiji, wanda kuwa ya tabbatar da saƙon alherinsa ta wurinsa su su aikata ayyuka da alamu masu banmamaki.

Ayyukan Manzanni 14:15

“Ya ku mutane, don me kuke yin haka? Ai, mu ma mutane ne kawai, ’yan adam ne kamar ku. Mun kawo muku labari mai daɗi ne, muna gaya muku ku juya daga waɗannan abubuwa banza, ku juyo ga Allah mai rai, wanda ya yi sama da ƙasa da teku da kuma dukan abin da yake cikinsu.

Ayyukan Manzanni 14:21-22

Suka yi wa’azin Labari mai daɗi a wannan birni, suka kuma sami almajirai da yawa. Sai suka koma Listira, Ikoniyum da kuma Antiyok, suna gina almajirai suna kuma ƙarfafa su su tsaya da gaske cikin bangaskiya. Suka ce, “Sai da shan wahaloli masu yawa za mu shiga mulkin Allah.”

Ayyukan Manzanni 15:7

Bayan aka yi muhawwara da sosai, sai Bitrus ya miƙe tsaye ya yi musu jawabi ya ce, “’Yan’uwa, kun san cewa a kwanakin baya Allah ya yi zaɓe a cikinku don Al’ummai su ji daga leɓunana saƙon bishara su kuma gaskata.

Ayyukan Manzanni 16:6-10

Bulus da abokan tafiyarsa suka zazzaga dukan yankin Firjiya da Galatiya, don Ruhu Mai Tsarki ya hana su yin wa’azi a lardin Asiya. Da suka isa kan iyakar Misiya, suka yi ƙoƙari su shiga Bitiniya, amma Ruhun Yesu bai yarda musu ba. Saboda haka suka ratsa Misiya suka zo Toruwas. Da dare Bulus ya ga wahayin wani mutumin Makidoniya yana tsaye yana roƙonsa cewa, “Ka zo Makidoniya ka taimake mu.” Bayan Bulus ya ga wahayin, muka shirya nan take mu tashi zuwa Makidoniya, mun tabbata cewa, Allah ya kira mu mu yi musu wa’azin bishara.

Ayyukan Manzanni 16:29-31

Mai gadin kurkukun ya kira a kawo fitilu, ya ruga ciki ya fāɗi yana rawan jiki a gaban Bulus da Sila. Sai ya fito da su waje ya kuma tambaye su ya ce, “Ranku yă daɗe, me zan yi domin in sami ceto?” Suka amsa suka ce, “Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka sami ceto, kai da iyalinka.”

Ayyukan Manzanni 17:2-4

Kamar yadda ya saba, Bulus ya shiga majami’ar, ranakun Asabbaci uku ya yi ta yin muhawwara da su daga cikin Nassosi, yana musu bayani da tabbatarwa cewa dole Kiristi ya sha wahala ya kuma tashi daga matattu. Ya kuma ce, “Wannan Yesu da nake sanar muku shi ne Kiristi.” Waɗansu Yahudawa suka amince suka kuma bi Bulus da Sila, haka ma Hellenawa da yawa masu tsoron Allah da kuma manyan mata ba kaɗan ba.

Ayyukan Manzanni 17:11

Bereyawa kuwa sun fi Tessalonikawa hankali, gama sun karɓi saƙon da marmari ƙwarai, suka kuma yi ta yin bincike Nassosi kowace rana su ga ko abin da Bulus ya faɗa gaskiya ne.

Ayyukan Manzanni 17:22-31

Sai Bulus ya miƙe tsaye a tsakiyar taron Areyofagus ya ce, “Ya ku mutanen Atens! Na dai lura cewa ta kowace hanya ku masu addini ne ƙwarai. Gama sa’ad da nake zagawa, na lura da kyau da abubuwan da kuke bauta wa, har ma na tarar da wani bagade da wannan rubutu, Ga Allahn da ba a sani ba. To, abin nan da kuke yi wa sujada a matsayin abin da ba ku sani nan ba shi ne zan sanar da ku. “Allahn da ya halicci duniya da kome da yake cikinta shi ne Ubangijin sama da ƙasa, ba ya kuma zama a haikalin da aka gina da hannuwa. Ba a kuma yin masa hidima da hannun mutum, sai ka ce mai bukatan wani abu, domin shi kansa ne ke ba wa dukan mutane rai da numfashi da kuma kome. Daga mutum ɗaya, ya halicci kowace al’ummar mutane, don su zauna a duk duniya; shi ne kuma ya ƙaddara lokuta bisa ga tsarinsu da kuma inda za su kasance. Allah ya yi wannan domin mutane su neme shi mai yiwuwa kuma su lalluba su same shi, ko da yake ba shi da nisa daga kowannenmu. ‘Gama a cikinsa ne muke rayuwa muke motsi muka kuma kasance.’ Yadda waɗansu mawaƙanku suka ce, ‘Mu zuriyarsa ce.’ “Saboda haka da yake mu zuriyar Allah ce, kada mu yi tsammani cewa kamannin Allah yana kama da zinariya ko azurfa ko dutse, siffar da mutum ya ƙago ta wurin dabararsa. A dā Allah ya kawar da Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu ya umarci dukan mutane a ko’ina su tuba. Gama ya sa ranar da zai yi wa duniya shari’a da adalci ta wurin mutumin da ya naɗa. Ya riga ya ba da tabbacin wannan ga dukan mutane ta wurin tā da shi daga matattu.”

Ayyukan Manzanni 18:24-26

Ana cikin haka sai wani mutumin Yahuda mai suna Afollos, ɗan ƙasar Alekzandariya, ya zo Afisa. Shi masani ne, yana da cikakken sani na Nassosi. An horar da shi a hanyar Ubangiji, ya kuma himma ƙwarai a magana, ya kuma yi koyarwa game da Yesu, daidai, ko da yake baftismar Yohanna ce kaɗai ya sani. Sai ya fara magana gabagadi a majami’a. Sa’ad da Firiskila da Akwila suka ji shi, sai suka gayyace shi gidansu suka ƙara bayyana masa hanyar Allah sosai.

Ayyukan Manzanni 19:8-10

Bulus ya shiga majami’a ya yi magana gabagadi a can na watanni uku, yana muhawwara yana kuma rinjayarsu game da mulkin Allah. Amma waɗansunsu suka taurara; suka ƙi su gaskata kuma a gaban jama’a suka yi baƙar magana game da Hanyar. Bulus kuwa ya bar su. Ya tafi tare da almajirai ya dinga tattaunawa da su kullum a babban ɗakin jawabi na Tirannus. Wannan ya ci gaba har shekara biyu, sai da ya sa dukan Yahudawa da Hellenawa da suke zaune a lardin Asiya suka ji maganar Ubangiji.

Ayyukan Manzanni 20:20-24

Kun san cewa ban yi wata-wata yin muku wa’azi game da duk abin da zai amfane ku ba amma na koyar da ku a fili da kuma gida-gida. Na yi shela ga Yahudawa da Hellenawa cewa dole su juye ga Allah cikin tuba su kuma amince da Ubangijinmu Yesu. “Yanzu kuma Ruhu ya tilasta ni, za ni Urushalima, ba tare da sanin abin da zai faru da ni a can ba. Na dai san cewa a kowace birni Ruhu Mai Tsarki yakan gargaɗe ni cewa kurkuku da shan wuya suna jirana. Amma ni ban ɗauki raina a bakin kome ba, in dai zan iya gama tserena in kuma kammala aikin da Ubangiji Yesu ya ba ni aikin shaida bisharar alherin Allah.

Ayyukan Manzanni 22:15

Za ka zama mai shaidarsa ga dukan mutane game da abin da ka gani ka kuma ji.

Ayyukan Manzanni 23:11

Kashegari da dare Ubangiji ya tsaya kusa da Bulus ya ce, ‹“Ka yi ƙarfin hali! Don kamar yadda ka yi shaida game da ni a Urushalima, haka kuma lalle, za ka yi shaidata a Roma.”›

Ayyukan Manzanni 26:16

‹Yanzu ka tashi, ka tsaya da ƙafafunka. Na bayyana a gare ka don in naɗa ka bawa da kuma mai shaidar abin da ka gani game da ni da kuma abin da zan nuna maka.›

Ayyukan Manzanni 26:18

‹ka buɗe idanunsu su kuwa juyo daga duhu zuwa haske, daga mulkin Shaiɗan kuma zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai da kuma matsayi a cikin waɗanda aka tsarkake ta wurin bangaskiya a cikina.’›

Ayyukan Manzanni 26:22-23

Amma na sami taimakon Allah har yă zuwa yau. Yanzu ga ni a tsaye a nan, ina shaida ga babba da yaro. Ba na faɗin kome fiye da abin da annabawa da Musa suka ce zai faru, cewa Kiristi zai sha wahala, kuma a matsayin wanda yake na fari da zai tashi daga matattu, zai yi shelar haske ga mutanensa da kuma Al’ummai.”

Ayyukan Manzanni 28:30-31

Shekaru biyu cif Bulus ya zauna a can a gidansa na haya yana marabtar duk wanda ya je wurinsa. Ya yi wa’azin mulkin Allah yana kuma koyarwa game da Ubangiji Yesu Kiristi, gabagadi ba tare da wani abu ya hana shi ba.

Romawa 1:8

Da farko, ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Kiristi saboda ku duka, gama ana ba da labarin bangaskiyarku a ko’ina a duniya.

Romawa 1:14-16

Ina da hakki ga Hellenawa da waɗanda ba Hellenawa ba, ga masu hikima da kuma marasa azanci. Shi ya sa na yi himma sosai in yi muku wa’azin bishara ku ma da kuke a Roma. Ba na jin kunyar bishara, gama ita ikon Allah ne domin ceton kowa da ya gaskata, da farko ga Yahudawa, sa’an nan ga Al’ummai.

Romawa 5:8

Amma Allah ya nuna mana ƙaunarsa a wannan. Tun muna masu zunubi tukuna, Kiristi ya mutu dominmu.

Romawa 6:23

Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

Romawa 10:9-13

Cewa in ka furta da bakinka, “Yesu Ubangiji ne,” ka kuma gaskata a zuciyarka cewa Allah ya tā da shi daga matattu, za ka sami ceto. Gama da zuciyarka ce kakan gaskata a kuma kuɓutar da kai, da bakinka ne kuma kake furta a kuma cece ka. Kamar yadda Nassi ya ce, “Duk wanda ya gaskata da shi ba zai taɓa shan kunya ba.” Gama ba bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa yana kuma ba da albarka a yalwace ga duk masu kira gare shi, gama, “Duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.”

Romawa 10:14-15

To, ta yaya za su kira ga wanda ba su gaskata ba? Ta yaya kuma za su gaskata wanda ba su taɓa ji ba? Ta yaya kuma za su ji ba tare da wani ya yi musu wa’azi ba? Kuma ta yaya za su yi wa’azi in ba an aike su ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Isowar masu kawo labari mai daɗi abu mai kyau ne ƙwarai!”

Romawa 10:16

Amma ba dukan Isra’ilawa ne suka karɓi labari mai daɗin nan ba. Gama Ishaya ya ce, “Ubangiji, wa ya gaskata saƙonmu?”

Romawa 10:17-18

Saboda haka, bangaskiya takan zo ne ta wurin jin saƙo, akan ji saƙon kuma ta wurin maganar Kiristi. Amma ina tambaya, “Ba su ji ba ne? Tabbatacce sun ji. “Muryarsu ta tafi ko’ina a cikin duniya, kalmominsu kuma har iyakar duniya.”

Romawa 15:19

ta wurin ikon alamu da ayyukan banmamaki, da kuma ikon Ruhun Allah. Ta haka daga Urushalima har yă zuwa kewayen Illirikum, na yi wa’azin bisharar Kiristi.

Romawa 16:25-26

Ɗaukaka ta tabbata ga mai ikon ƙarfafa ku bisa ga bisharata, bisa ga wa’azin Yesu Kiristi, wadda ta gare ta ne aka bayyana asirin nan da yake ɓoye tun fil azal, amma yanzu kuwa aka bayyana, aka kuma sanar ta wurin rubuce-rubucen annabawa bisa ga umarnin Allah madawwami, domin dukan al’ummai su gaskata su kuma yi masa biyayya

1 Korintiyawa 1:17-19

Gama Kiristi bai aike ni yin baftisma ba, sai dai wa’azin bishara ba da kalmomin hikimar mutum ba, domin kada gicciyen Kiristi ya rasa ikonsa. Gama saƙon gicciye wauta ne ga waɗanda suke hallaka, amma a gare mu, mu da ake ceto, ikon Allah ne. Gama a rubuce yake cewa, “Zan rushe hikimar mai hikima, basirar mai azanci kuma zan rikita shi.”

1 Korintiyawa 1:21-25

Gama tun da a cikin hikimar Allah, duniya a cikin hikimarta ba tă san shi ba, Allah ya ji daɗin ceton waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin wautar wa’azin bishara. Yahudawa suna so su ga alama, Hellenawa kuma suna neman hikima, amma mu, muna wa’azin Kiristi wanda aka gicciye ne, wanda ya zama dutsen tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga Al’ummai, amma ga su waɗanda Allah ya kira, Yahudawa da Hellenawa, Kiristi ikon Allah ne, da kuma hikimar Allah. Gama wautar Allah ta fi hikimar mutum, kuma rashin ƙarfin Allah ya fi ƙarfin mutum.

1 Korintiyawa 2:1-5

Da na zo wurinku ’yan’uwa, ban zo da iya magana ko wani mafificin hikima yayinda na yi muku shelar shaida game da Allah ba. Don na ƙudura a raina sa’ad da nake tare da ku cewa ba zan mai da hankali ga kome ba sai dai Yesu Kiristi wanda aka gicciye. Na zo wurinku cikin rashin ƙarfi da tsoro, da rawan jiki ƙwarai. Saƙona da wa’azina ba su zo cikin hikima da kalmomin lallashi ba, sai dai da nuna ikon Ruhu, domin kada bangaskiyarku ta dogara a kan hikimar mutane, sai dai a kan ikon Allah.

1 Korintiyawa 2:6-9

Duk da haka, muna sanar da saƙon hikima cikin waɗanda suka balaga, amma ba hikima irin ta wannan zamani ba ne, ko kuwa irin ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda za su shuɗe ba. A’a, muna magana ne a kan asirin hikimar Allah, hikimar da tun dā, take a ɓoye, wadda Allah ya ƙaddara domin ɗaukakarmu, tun kafin farkon zamanai. Ba ko ɗaya daga cikin masu mulkin wannan zamani da ya fahimce ta, gama da a ce sun fahimce ta, da ba su gicciye Ubangiji mai ɗaukaka ba. Duk da haka, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ba idon da ya taɓa gani, ba kunnen da ya taɓa ji, ba kuma zuciyar da ta taɓa tunanin abin da Allah ya shirya wa masu ƙaunarsa.”

1 Korintiyawa 2:10-13

Amma Allah ya bayyana mana shi ta wurin Ruhunsa. Ruhu yana bincika dukan abubuwa, har ma da abubuwa masu zurfi na Allah. Wane ne a cikin mutane ya san tunanin mutum, in ba ruhun mutumin da yake cikinsa ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah. Ba mu karɓi ruhun duniya ba, sai dai Ruhun da yake daga Allah, domin mu fahimci abin da Allah ya ba mu hannu sake. Wannan shi ne abin da muke sanarwa, ba da kalmomin da muka koya ta wurin hikimar mutum ba, amma da kalmomin da Ruhu yake koyarwa, muna faɗin gaskiya ta ruhaniya da kalmomin ruhaniya.

1 Korintiyawa 2:14-16

Mutumin da ba shi da Ruhu, ba ya yarda da abubuwan da suka fita daga Ruhun Allah, domin wauta ce a gare shi. Ba kuwa zai fahimce su ba, domin ta Ruhu ne ake fahimtarsu. Mutumin ruhaniya yakan gwada dukan abubuwa, amma shi kansa ba ya ƙarƙashin shari’ar mutum. “Wa ya taɓa sanin hankalin Ubangiji, har da zai koya masa?” Amma muna da tunani iri na Kiristi ne.

1 Korintiyawa 3:1-2

’Yan’uwa, ban iya yi muku magana kamar masu ruhaniya ba, sai dai kamar masu halin mutuntaka, jarirai cikin bin Kiristi kawai. Na ba ku madara ba abinci mai tauri ba, domin ba ku balaga ba a lokacin. Kai, har yanzu ma, ba ku balaga ba.

1 Korintiyawa 3:6-9

Ni na shuka iri, Afollos kuma ya yi banruwa, amma Allah ne ya sa irin ya yi girma. Don haka, da wanda ya yi shuki, da wanda ya yi banruwa, ba a bakin kome suke ba, sai dai Allah kaɗai, mai sa abubuwa su yi girma. Mutumin da ya yi shuki, da mutumin da ya yi banruwa nufinsu ɗaya ne, kuma kowannensu zai sami lada gwargwadon aikinsa. Gama mu abokan aiki ne na Allah; ku kuwa gonar ce ta Allah, ginin Allah kuma.

1 Korintiyawa 3:10-15

Ta wurin alherin da Allah ya ba ni, na kafa tushen gini kamar ƙwararren magini, wani kuma dabam yana gini a kai. Amma kowa yă lura da yadda yake gini. Gama babu wanda zai iya kafa wani tushen gini dabam da wanda aka riga aka kafa, wanda yake Yesu Kiristi. In wani ya yi gini a kan tushen ginin nan da zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja, itace, ciyawa ko kara, aikin zai bayyana kansa, domin za a nuna shi a sarari a Ranar. Wuta ce za tă bayyana aikin, wutar kuwa za tă gwada ingancin aikin kowa. In abin da kowane mutum ya gina ya tsaya, zai sami lada. In ya ƙone, zai yi hasara, amma zai sami ceto, sai dai kamar wanda ya bi ta tsakiyar wuta ne.

1 Korintiyawa 9:16

Duk da haka, sa’ad da ina wa’azin bishara, ba na taƙama, domin tilas ne a gare ni in yi wa’azi. Kaitona, in ban yi wa’azin bishara ba!

1 Korintiyawa 9:17-18

In na yi wa’azi da yardar rai, ina da lada; in ba da yardar rai ba, ina dai cika amana da aka danƙa mini ne. To, mene ne ladana? Ladana kaɗai shi ne, in yi wa’azin bishara, in kuma yi shi a kyauta, yadda ba zan yi amfani da ’yancina cikin wa’azin ba.

1 Korintiyawa 9:19-22

Ko da yake ina da ’yanci ba na kuma ƙarƙashin kowa, na mai da kaina bawa ga kowa, domin in rinjayi mutane da yawa. Ga Yahudawa na zama kamar mutumin Yahuda, domin in rinjayi Yahudawa. Ga waɗanda suke ƙarƙashin doka kuma, na zama kamar wanda yake ƙarƙashin Dokar (ko da yake ni kaina ba na ƙarƙashin Doka), domin in rinjayi waɗanda suke ƙarƙashin Doka. Ga waɗanda ba su da Dokar kuwa, na zama kamar wanda ba shi da Dokar (ko da yake ba ni da ’yanci daga dokar Allah, amma ina ƙarƙashin dokar Kiristi), domin in rinjayi waɗanda ba su da dokar. Ga waɗanda ba su da ƙarfi, na zama marar ƙarfi, domin in rinjayi waɗanda ba su da ƙarfi. Na zama dukan abu ga dukan mutane, domin ko ta yaya in zai yiwu, in ceci waɗansu.

1 Korintiyawa 13:2-3

In ina da baiwar annabci, ina kuma iya fahimtar dukan asirai da dukan ilimi, in kuma ina da bangaskiyar da zan iya kawar da manyan duwatsu, amma ba ni da ƙauna, ni ba kome ba ne. In na ba wa matalauta dukan abin da nake da shi, na kuma miƙa jikina a ƙone, amma ba ni da ƙauna, ban yi riban kome ba.

1 Korintiyawa 15:1-2

To, ’yan’uwa, ina so in tuna muku da bisharar da na yi muku wa’azinta, wadda kuka karɓa, wadda kuma kuka yanke shawara ku tsaya a kai. Ta wurin wannan bisharar ce kuka sami ceto, muddin kuna riƙe da wa’azin da na yi muku kam-kam. In ba haka ba, kun gaskata a banza ke nan.

1 Korintiyawa 15:10-11

Amma bisa ga alherin Allah, na zama abin da nake, alherinsa zuwa gare ni kuwa bai zama a banza ba. A’a, na yi aiki fiye da dukansu, duk da haka, ba ni ba ne, sai dai alherin Allah da yake tare da ni ne. To, ko ni ne, ko su ne, wannan shi ne abin da muke wa’azi, shi ne kuma abin da kuka gaskata.

1 Korintiyawa 15:36-37

Kai, marar azanci! Abin da kuka shuka ba zai tsira ba sai ya mutu. Sa’ad da kuke shuki, ba tsiron da zai yi girma ba ne kuka shuka, ƙwayar ce kawai, ko ta alkama ko kuma na wani irin dabam.

2 Korintiyawa 2:14-16

Amma godiya ga Allah, wanda kullum yake bi da mu da nasara cikin Kiristi, kuma ta wurinmu, yana baza ƙanshin nan na sanin Kiristi a ko’ina. Don kuwa, a wurin Allah mu ƙanshin Kiristi ne cikin waɗanda ake ceto, da kuma waɗanda suke hanyar hallaka. Ga wani, mu warin mutuwa ne, amma ga wani kuwa, mu ƙanshin rai ne. Wa ya isa yă yi irin wannan aikin?

2 Korintiyawa 2:17

Ba ma tallar maganar Allah don riba yadda waɗansu mutane da yawa suke yi. A maimakon haka, muna magana cikin Kiristi a gaban Allah da gaskiya, kamar mutanen da aka aika daga Allah.

2 Korintiyawa 3:7-11

To, in hidimar da ta kawo mutuwa, wadda an rubuta a kan allon dutse, ta zo da ɗaukaka har Isra’ilawa suka kāsa duban fuskar Musa saboda tsananin haskenta, ko da yake mai shuɗewa ce, ashe, hidimar Ruhu ba za tă fi wannan ɗaukaka ba? In hidimar da take jawo wa mutane hukunci tana da ɗaukaka haka, to, lalle, hidimar da take kawo adalci za tă fi ta ɗaukaka nesa! Gama abin da dā take da ɗaukaka, ba ta da ɗaukaka a yanzu, in aka kwatantata da mafificiyar ɗaukaka ta yanzu. In kuma aba mai shuɗewa ta zo da ɗaukaka, ashe, abin da yake dawwammame, lalle ne yă kasance da ɗaukakar da ta fi haka nesa!

2 Korintiyawa 3:12

Da yake muna da bege irin wannan, to, muna da ƙarfin zuciya sosai ke nan.

2 Korintiyawa 5:18-19

Duk wannan kuwa daga Allah ne, wanda ya sulhunta mu da kansa ta wurin Kiristi, ya kuma ba mu hidimar sulhu, wato, Allah ya sulhunta duniya zuwa kansa ta wurin Kiristi, ba ya lissafta zunuban mutane a kansu. Ya kuma danƙa mana saƙon sulhu.

2 Korintiyawa 5:20

Saboda haka, mu jakadu ne na Kiristi, sai ka ce Allah kansa yake magana ta wurinmu. Muna roƙonku a madadin Kiristi. Ku sulhuntu da Allah.

2 Korintiyawa 6:2

Gama ya ce, “A lokacin samun alherina, na ji ka, a ranar samun ceto kuma, na taimake ka.” Ina gaya muku, yanzu ne lokacin samun alherin Allah, yanzu ne ranar samun ceto.

2 Korintiyawa 6:3

Ba ma sa abin tuntuɓe wa kowa, domin kada hidimarmu ta zama abin zargi.

2 Korintiyawa 7:10

Baƙin ciki irin na tsoron Allah yana kai ga tuban da yake kawo ceto, ba ya kuma kawo baƙin ciki, amma baƙin ciki irin na duniya yakan kawo mutuwa.

2 Korintiyawa 9:6

Ku tuna fa, duk wanda ya yi shuki kaɗan zai girbe kaɗan, kuma duk wanda ya yi shuki da yawa, zai girbe a yalwace.

2 Korintiyawa 9:10

To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, yă riɓanya shi, yă kuma albarkaci ayyukanku na alheri da yawa.

2 Korintiyawa 10:16

Saboda mu iya yin wa’azin bishara a yankunan da suke gaba da ku. Gama ba ma so mu yi taƙama game da aikin da aka riga aka yi a sashen wani.

2 Korintiyawa 11:7

Laifi ke nan ne na yi da na ƙasƙantar da kaina, don a ɗaga ku zuwa babban matsayi ta wurin yin muku wa’azin bisharar Allah kyauta?

Galatiyawa 1:8-9

Amma ko mu, ko mala’ika daga sama ya yi wa’azin wata bishara dabam da wadda muka yi muku, bari yă zama la’ananne har abada! Kamar yadda muka riga muka faɗa, haka yanzu ma ina ƙara cewa in wani yana muku wa’azin wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, bari yă zama la’ananne har abada!

Galatiyawa 1:10-11

Za a ce, ina ƙoƙarin neman amincewar mutane ne, ko amincewa ta Allah? Ko kuwa ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne? Da a ce har yanzu ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne, ai, da ban zama bawan Kiristi ba. Ina so ku sani ’yan’uwa, cewa bisharar da nake wa’azi, ba mutum ne ya ƙago ta ba.

Galatiyawa 2:20

An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne nake raye ba, Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina.

Galatiyawa 6:7-8

Kada a ruɗe ku. Ba a yi wa Allah ba’a. Mutum yakan girbe abin da ya shuka ne. Wanda ya yi shuki don yă gamshi mutuntakarsa, daga wannan mutuntaka zai girbi hallaka. Wanda ya yi shuki domin yă gamshi Ruhu, daga Ruhu zai girbi rai madawwami.

Afisawa 2:17

Ya zo ya yi muku wa’azin salama; ku da kuke nesa da shi, ya kuma yi wa waɗanda suke kusa.

Afisawa 4:11-14

Saboda haka Kiristi kansa ya ba wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu su zama annabawa, waɗansu su zama masu wa’azi, waɗansu kuma su zama fastoci, da kuma malamai. Ya yi haka don yă shirya mutanensa saboda ayyukan hidima, don a gina jikin Kiristi. Wannan zai ci gaba har sai mun zama ɗaya a cikin bangaskiya da kuma ta wurin fahimtarmu na Ɗan Allah. Sa’an nan za mu zama balagaggu, kamar yadda Kiristi yake, mu kuma zama gaba ɗaya cikakku kamar sa. An yi wannan kuwa don kada mu koma zama kamar yara, muna ta canja zukatanmu game da abin da muka gaskata don kawai wani ya faɗa mana wani abu dabam, ko domin wani ya yi wayo ya ruɗe mu, ya sa ƙarya ta zama kamar gaskiya.

Afisawa 5:2

ku kuma yi rayuwar ƙauna, kamar yadda Kiristi ya ƙaunace mu, har ya ba da kansa dominmu a matsayin sadaka mai ƙanshi da kuma hadaya ga Allah.

Afisawa 6:19-20

Ku kuma yi addu’a domina, don duk sa’ad da na buɗe bakina, in sami kalmomi babu tsoro, don in sanar da asirin bishara, wadda nake jakadanta cikin sarƙoƙi. Ku yi addu’a don in iya yin shelarta babu tsoro, yadda ya kamata in yi.

Filibbiyawa 1:14-18

Saboda sarƙoƙina, yawancin ’yan’uwa cikin Ubangiji sun sami ƙarfafawa su yi maganar Allah gabagadi da kuma babu tsoro. Gaskiya ce cewa waɗansu suna yin wa’azin Kiristi saboda kishi da neman faɗa, amma waɗansu da nufi mai kyau suke yi. Na biye suna yin haka cikin ƙauna, da sanin cewa an sa ni a nan ne domin kāriyar bishara. Na farin dai suna wa’azin Kiristi da sonkai ne, ba da zuciya ɗaya ba, a sonsu, su wahalar da ni a cikin sarƙoƙi. Me kuma? Ta ko yaya dai, ko da gangan, ko da gaske, ana shelar Kiristi. Domin wannan kuwa ina farin ciki. I, zan kuwa ci gaba da farin ciki,

Kolossiyawa 1:23-28

Sai ku ci gaba cikin bangaskiyarku, kuna tsaye a kafe kuma tsayayyu, ba tare da gusawa daga begen da kuka ji daga bishara ba. Wannan ita ce bisharar da kuka ji wadda aka yi shelarta ga kowace halittar da take ƙarƙashin sama, wadda kuma ni Bulus, na zama mai hidimarta. Yanzu, ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, don ta wurin wuyan nan zan cika abin da ya rage na wuyar da Kiristi ya sha saboda jikinsa, wato, ikkilisiya. Na zama mai hidimar ikkilisiya bisa ga aikin nan da Allah ya ba ni amana saboda ku, domin in sanar da maganar Allah sosai. Wannan magana da nake gaya muku asiri ne da yake a ɓoye tun zamanai masu yawa, wanda yanzu aka bayyana ga tsarkaka. Su ne Allah ya so yă sanar da yadda irin yalwar ɗaukakar asirin nan take a cikin al’ummai, asirin nan kuwa shi ne Kiristi a cikinku, begen ɗaukakar da za a bayyana. Saboda haka ko’ina muka tafi, muna shela, muna gargaɗi, muna kuma koyar da kowa da dukan hikima, don mu miƙa kowa cikakke a cikin Kiristi.

Kolossiyawa 3:24

Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa.

Kolossiyawa 4:3-6

Ku kuma yi mana addu’a, mu ma, don Allah yă buɗe ƙofa saboda saƙonmu, don mu iya yin shelar asirin Kiristi, wanda saboda shi nake cikin sarƙoƙi. Ku yi addu’a yadda zan yi shelarsa, yadda ya kamata. Ku zama masu hikima a yadda kuke ma’amala da waɗanda suke ba masu bi ba; ku kuma yi amfani da kowane zarafi. Bari maganarku kullum ta zama da ladabi da kuma daɗin ji, domin ku san amsar da ta dace ku ba wa kowa.

1 Tessalonikawa 1:5-6

domin bishararmu ba tă zo gare ku da kalmomi kawai ba, amma da iko, da Ruhu Mai Tsarki, da kuma cikakken tabbaci. Kun san irin rayuwar da muka yi a cikinku don amfaninku. Har kuka zama masu koyi da mu da kuma Ubangiji; duk da tsananin wahala, kuka karɓi saƙon nan da farin ciki wanda Ruhu Mai Tsarki ya bayar.

1 Tessalonikawa 2:2-9

Mun riga mun sha wahala, aka kuma zage mu a Filibbi, kamar yadda kuka sani, amma da taimakon Allahnmu muka yi ƙarfin hali muka sanar muku bishararsa duk da matsananciyar gāba. Gama roƙon da muke yi bai fito daga kuskure ko munafunci ba, ba kuwa ƙoƙari muke yi mu yaudare ku ba. A maimako haka, muna magana ne kamar mutanen da Allah ya amince yă danƙa musu amanar wannan bishara. Ba ma ƙoƙari mu gamshi mutane sai dai Allah, mai auna zukatanmu. Kun san ba ma taɓa yin daɗin baki ko mu yi ƙoƙarin kasance da halin kwaɗayin da muke ɓoyewa, Allah shi ne shaidarmu. Ba ma neman yabo daga wurin mutane, ko a gare ku, ko ga waɗansu. A matsayinmu na manzannin Kiristi da mun so, da mun nawaita muku, amma muka kasance masu sauƙinkai a cikinku, kamar yadda mahaifiya take lura da ƙananan ’ya’yanta. Muka ƙaunace ku ƙwarai har muka ji daɗin bayyana muku, ba bisharar Allah kaɗai ba amma har rayukanmu ma, domin kun zama ƙaunatattu a gare mu. Ba shakka kuna iya tunawa, ’yan’uwa, famarmu da kuma wahalarmu; mun yi aiki dare da rana don kada mu zama nauyi wa wani yayinda muke muku wa’azin bisharar Allah.

2 Tessalonikawa 1:10

a ranar da zai dawo don a ɗaukaka shi a cikin mutanensa masu tsarki, yă kuma zama abin banmamaki ga dukan waɗanda suka gaskata. Wannan ya haɗa har da ku, domin kun gaskata shaidar da muka yi muku.

2 Tessalonikawa 2:14-15

Ya kira ku ga wannan ta wurin bishararmu, don ku sami rabo a cikin ɗaukakar Ubangijinmu Yesu Kiristi. Saboda haka fa, ’yan’uwa, sai ku tsaya daram ku riƙe koyarwar da muka miƙa muku, ko ta wurin maganar baki ko kuma ta wurin wasiƙa.

1 Timoti 6:12

Ka yi fama, kyakkyawar fama ta bangaskiya. Ka riƙi rai madawwamin nan, wanda aka kira saboda shi, sa’ad da ka yi kyakkyawar shaida a gaban shaidu masu yawa.

2 Timoti 1:8-12

Saboda haka kada ka ji kunyar ba da shaida game da Ubangijinmu, ko kuwa ka ji kunyata, ni da nake ɗan sarƙa saboda shi. Sai dai ka haɗa kai tare da ni cikin shan wahala saboda bishara ta wurin ikon Allah, wanda ya cece mu ya kuma kira mu ga rayuwar tsarki ba saboda wani abin da muka yi ba sai dai saboda nufinsa da kuma alherinsa. An ba mu wannan alheri cikin Kiristi Yesu tun fil azal, amma yanzu an bayyana ta ta wurin bayyanuwar Mai Cetonmu, Kiristi Yesu, wanda ya hallaka mutuwa ya kuma kawo rai da rashin mutuwa a sarari ta wurin bishara. A wannan bishara ce, aka naɗa ni mai shela da manzo da kuma malami. Shi ya sa nake shan wahalar da nake sha. Duk da haka ba na jin kunya, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata cewa yana iya kiyaye abin da na danƙa masa amana don wancan rana.

2 Timoti 2:2

Abubuwan da ka ji na faɗa a gaban shaidu masu yawa kuwa ka danƙa wa amintattun mutane waɗanda su ma za su iya koya wa waɗansu.

2 Timoti 2:10-12

Saboda haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton da yake cikin Kiristi Yesu, tare da madawwamiyar ɗaukaka. Ga wata magana tabbatacciya, “In muka mutu tare da shi, za mu rayu tare da shi; in muka jimre, za mu yi mulki tare da shi. In muka yi mūsunsa, shi ma zai yi mūsunmu;

2 Timoti 2:14-16

Ka riƙa tuna masu da haka, ka kuma gama su da Allah, kada su yi jayayya a kan maganganu, don ba ta da wani amfani, sai ɓad da masu ji kawai take yi. Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka gabatar da kanka a gaban Allah a matsayin wanda aka amince da shi, ma’aikaci wanda ba shi da dalilin jin kunya wanda kuma yake fassara kalmar gaskiya daidai. Ka yi nesa da maganganun banza na rashin tsoron Allah, gama waɗanda suka mai da hankali ga yin waɗannan za su ƙara zama marasa tsoron Allah.

2 Timoti 4:2-5

Ka yi wa’azin Maganar Allah, ka zama a shirye a kullum, ko da zarafi, ko babu zarafi, ka yi gyara, ka kwaɓe, ka kuma ƙarfafa, da matuƙar haƙuri da koyarwa cikin natsuwa. Gama lokaci yana zuwa da mutane ba za su jure da sahihiyar koyarwa ba. A maimako, don cimma burinsu, za su taro wa kansu malamai masu yawa, domin su faɗi abin da kunnuwansu masu ƙaiƙayi suke so su ji. Za su juye kunnuwansu daga gaskiya zuwa ga jin tatsuniyoyi. Amma kai, ka natsu cikin kowane hali, ka jure shan wahala, ka yi aikin mai bishara, ka cika dukan ayyukan hidimarka.

2 Timoti 4:17

Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya kuma ba ni ƙarfi, don ta wurina a yi cikakkiyar shelar saƙon har Al’ummai duka su ji. Aka kuma cece ni daga bakin zaki.

Titus 2:11

Gama alherin Allah mai kawo ceto ya bayyana ga dukan mutane.

Filemon 1:6-8

Ina addu’a ka zama mai ƙwazo cikin shaida bangaskiyarka, domin ka sami cikakken fahimta ta kowane abin da yake nagarin da muke da shi cikin Kiristi. Ƙaunarka ta sa ni farin ciki ƙwarai ta kuma ƙarfafa ni, domin kai, ɗan’uwa, ka wartsake zukatan tsarkaka. Saboda haka, ko da yake cikin Kiristi ina iya yin ƙarfin hali in umarce ka ka yi abin da ya kamata,

Ibraniyawa 4:1-3

Saboda haka, da yake alkawarin shiga hutunsa yana nan har yanzu, sai mu yi hankali kada waninku yă kāsa shiga. Gama mu ma mun ji an yi mana wa’azin bishara, kamar yadda su ma suka ji; sai dai saƙon da suka ji ba tă amfane su ba, domin waɗanda suka ji ba su karɓe shi da bangaskiya ba. Mu kam da muka gaskata mu ne muka shiga wannan hutu, kamar yadda Allah ya ce, “Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ” Allah ya faɗa haka ko da yake ya riga ya kammala aikinsa tun halittar duniya.

Ibraniyawa 4:12-13

Maganar Allah tana da rai, tana kuma da ƙarfin aiki. Ta fi kowane takobi mai baki biyu kaifi. Maganarsa takan ratsa har ciki-ciki, tana raba rai da ruhu, gaɓoɓi da kuma ɓargon ƙashi; har sai ta tone ainihi wane ne muke. Babu wani abu cikin dukan halittar da yake ɓoye daga fuskar Allah. Kowane abu a buɗe yake yana kuma a shimfiɗe a idanun wanda dole mu ba da lissafi a gare shi.

Ibraniyawa 10:35

Saboda haka kada ku yar da tabbacinku; za a sāka muku a yalwace.

Ibraniyawa 11:6

In ba tare da bangaskiya ba kuwa, ba ya yiwuwa a gamshi Allah, domin duk mai zuwa wurin Allah dole yă gaskata cewa yana nan, kuma shi ne yakan sāka wa waɗanda suke nemansa da gaske.

Yaƙub 1:5

In waninku ya rasa hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi.

Yaƙub 1:26

In wani ya ɗauki kansa mai addini ne duk da haka bai ƙame harshensa ba, ruɗin kansa yake yi addininsa kuwa banza ne.

Yaƙub 5:19-20

’Yan’uwana, in waninku ya kauce daga gaskiya, wani kuma ya komo da shi, sai yă tuna da wannan. Duk wanda ya komo da mai zunubi daga kaucewarsa, zai cece shi daga mutuwa, yă kuma rufe zunubai masu ɗumbun yawa.

1 Bitrus 1:12

Aka bayyana musu cewa ba kansu ne suke bauta wa ba sai ku, sa’ad da suka yi maganar abubuwan da aka faɗa muku ta wurin waɗanda suka yi muku wa’azin bishara, ta wurin Ruhu Mai Tsarki wanda aka aika daga sama. Ko mala’iku ma suna marmari su ga waɗannan abubuwa.

1 Bitrus 1:23-25

Gama an sāke haihuwarku, ba da iri da yake lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, ta wurin rayayyiya da kuma madawwamiyar maganar Allah. Gama, “Dukan mutane kamar ciyawa suke, darajarsu kuma kamar furannin jeji ne; ciyawa takan yanƙwane furannin kuma su kakkaɓe, amma maganar Ubangiji tana nan har abada.” Wannan kuwa ita ce kalmar da aka yi muku wa’azi.

1 Bitrus 2:2-3

Kamar sababbin jarirai, ku yi marmarin madara zalla ta ruhaniya, domin ta wurinta za ku yi girma cikin cetonku, yanzu da kuka ɗanɗana alherin Ubangiji.

1 Bitrus 2:7-8

A gare ku da kuka gaskata, wannan dutse mai daraja ne. Amma ga waɗanda ba su gaskata ba, “Dutsen da magina suka ƙi ya zama dutsen kusurwar gini, kuma, “Dutse ne da yake sa mutane tuntuɓe kuma fā ne da yake sa su fāɗi.” Sun yi tuntuɓe domin sun ƙi su yi biyayya da saƙon, wanda kuma yake abin da aka ƙaddara musu.

1 Bitrus 2:9

Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki.

1 Bitrus 3:15-16

Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi, tare da lamiri mai kyau, saboda waɗanda suke maganganun banza a kan kyawawan ayyukanku cikin Kiristi su ji kunya da irin ɓata suna da suke yi.

2 Bitrus 1:16

Ba mu bi tatsuniyoyin da aka ƙaga da wayo sa’ad da muka gaya muku game da ikon Ubangijinmu Yesu Kiristi da zuwansa ba, sai dai mu shaidu ne na ɗaukakarsa mai girma da muka gani da ido.

2 Bitrus 3:9

Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani yă hallaka, sai dai kowa yă kai ga tuba.

1 Yohanna 1:9

In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci.

1 Yohanna 3:9-10

Babu haifaffe na Allah da zai ci gaba da yin zunubi, domin iri na Allah yana a cikinsa; ba zai iya ci gaba da yin zunubi ba, domin haifaffe ne na Allah. Ta haka muka san waɗanda suke ’ya’yan Allah da kuma waɗanda suke ’ya’yan Iblis. Duk wanda ba ya yin abin da yake daidai, ba ɗan Allah ba ne; haka ma wanda ba ya ƙaunar ɗan’uwansa.

1 Yohanna 4:6

Mu daga Allah ne, kuma duk wanda ya san Allah yakan saurare mu. Amma duk wanda ba daga Allah ba, ba ya sauraronmu. Ta haka ne muke gane Ruhun gaskiya, da kuma ruhun ƙarya.

1 Yohanna 5:9-11

Tun da yake mukan yarda da shaida mutane, ai, shaidar Allah ta fi ƙarfi. Wannan ita ce shaidar Allah, wato, ya shaidi Ɗansa. Duk wanda ya gaskata da Ɗan Allah, yana da shaidan nan a zuciyarsa. Duk wanda bai gaskata da Allah ba kuwa ya mai da shi maƙaryaci, domin bai gaskata shaidar da Allah ya bayar game da Ɗansa ba. Wannan kuwa ita ce shaidar; cewa Allah ya ba mu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Ɗansa.

Ru’uya ta Yohanna 1:2

wanda ya shaida dukan abin da ya gani, wato, maganar Allah da kuma shaidar Yesu Kiristi.

Ru’uya ta Yohanna 3:20

‹Ga ni! Ina tsaye a bakin ƙofa, ina ƙwanƙwasawa. Duk wanda ya ji muryata ya kuma buɗe ƙofar, zan shiga in kuma ci tare da shi, shi kuma tare da ni.›

Ru’uya ta Yohanna 7:10

Suka tā da murya da ƙarfi suna cewa, “Ceto na Allahnmu ne, wanda yake zaune a bisan kursiyi, da kuma na Ɗan Ragon.”

Ru’uya ta Yohanna 11:3-6

Zan kuma ba wa shaiduna nan biyu iko, za su kuwa yi annabci na kwanaki 1,260, saye da gwadon makoki.” Waɗannan su ne itatuwan zaitun biyu da kuma alkukai biyu da suke tsaye a gaban Ubangijin duniya. Duk wanda ya yi ƙoƙari yin musu lahani, wuta za tă fito daga bakunansu ta cinye abokan gābansu. Haka ne duk mai niyyar yin musu lahani zai mutu. Waɗannan mutane suna da iko su kulle sararin sama don kada a yi ruwan sama a lokacin da suke annabci; suna kuma da iko su juye ruwaye su zama jini su kuma bugi duniya da kowace irin annoba a duk lokacin da suke so.

Ru’uya ta Yohanna 11:7-11

To, da suka gama shaidarsu, dabbar da takan fito daga Abis za tă kai musu hari, tă kuwa sha ƙarfinsu tă kuma kashe su. Gawawwakinsu za su kasance a kwance a titin babban birni, wanda a misalce ake kira Sodom da Masar, inda kuma aka gicciye Ubangijinsu. Kwana uku da rabi mutane daga kowace jama’a, kabila, harshe da kuma al’umma za su yi ta kallon gawawwakinsu su kuma ƙi binne su. Mazaunan duniya za su ƙyaface su kuma yi biki ta wurin aika kyautai wa juna, domin waɗannan annabawan nan biyu ne suka azabtar da mazaunan duniya. Amma bayan kwana uku da rabi ɗin numfashin rai daga Allah ya shige su, suka kuwa tashi tsaye, tsoro kuma ya kama waɗanda suka gan su.

Ru’uya ta Yohanna 12:11

Sun ci nasara a kansa ta wurin jinin Ɗan Ragon da ta wurin kalmar shaidarsu; ba su ƙaunaci rayukansu sosai har da za su ja da baya daga mutuwa.

Ru’uya ta Yohanna 12:17

Sai macijin ya yi fushi da macen ya kuma koma wajen sauran zuriyarta don yă yaƙe su waɗannan waɗanda suke biyayya da umarnan Allah suke kuma riƙe da shaidar Yesu.

Ru’uya ta Yohanna 14:5

Ba a sami ƙarya a bakunansu ba; su kuma marasa aibi ne.

Ru’uya ta Yohanna 19:1

Bayan wannan sai na ji abin da ya yi kamar ƙasaitaccen taron mutane a sama, suna cewa, “Halleluya! Ceto da ɗaukaka da iko sun tabbata ga Allahnmu,

Ru’uya ta Yohanna 19:9-10

Sai mala’ikan ya ce mini, “Rubuta, ‘Masu albarka ne waɗanda aka gayyace su zuwa bikin auren Ɗan Ragon!’ ” Sai ya ƙara da cewa, “Waɗannan su ne kalmomin Allah da gaske.” Da wannan sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada. Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni ma abokin bauta ne da kai da kuma ’yan’uwanka waɗanda suke riƙe da shaidar Yesu. Ka yi wa Allah sujada! Domin shaidar Yesu ita ce ruhun annabci.”

Ru’uya ta Yohanna 20:4

Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu.

Ru’uya ta Yohanna 22:12

‹“Ga shi, ina zuwa da wuri! Ladan da zan bayar yana tare da ni, kuma zan ba wa kowa gwargwadon abin da ya yi.›

Hausa - Hausa - HA

HA'BSS - Budadden Littafi Mai Tsarki Biblica - 2020

This Bible text is from Biblica Open Hausa Contemporary Bible 2020
https://open.bible/bibles/hausa-biblica-text-bible/
provided by: Biblica Inc, available by Creative Commons CC-BY-SA-4.0,
and this new compilation is shared as www.creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0.
Languages are made available to you by www.ipedge.net