26 – Gwamnati

Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Gwamnati.

Top 3 Mafi Muhimmanci ayoyi

2 Sarakuna 21:16

Ban da haka ma, Manasse ya zub da jinin marasa laifi har ya cika Urushalima daga wannan ɓangare zuwa wancan, ban da zunubin da ya sa Yahuda ta aikata, ta haka suka yi mugunta a gaban Ubangiji.

Zabura 2:1-4

Me ya sa ƙasashe suke haɗa baki mutane kuma suke ƙulla shawarwarin banza? Sarakunan duniya sun ɗauki matsayi masu mulki sun taru gaba ɗaya suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa. Suna cewa, “Bari mu tsittsinke sarƙoƙinsu, mu kuma ’yantar da kamammu daga kangin bautar Allah.” Mai zama a kursiyi a sama yana dariya; Ubangiji yana musu ba’a.

Ru’uya ta Yohanna 11:15-18

Mala’ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji muryoyi masu ƙarfi a sama da suka ce, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Kiristinsa, zai kuwa yi mulki har abada abadin.” Sai dattawan nan ashirin da huɗu da suke zaune a kursiyoyinsu a gaban Allah, suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa suka kuma yi wa Allah sujada, suna cewa, “Muna maka godiya ya Ubangiji Allah, Maɗaukaki, wanda yake a yanzu, shi ne kuma a dā, domin ka karɓi ikonka mai girma ka kuma fara mulki. Al’ummai suka yi fushi; fushinka kuwa ya zo. Lokaci ya yi don a shari’anta matattu, da kuma don sākawa wa bayinka annabawa da tsarkakanka da kuma su waɗanda suke girmama sunanka, ƙarami da babba, don kuma hallakar da waɗanda suka hallaka duniya.”

Kowane Aya A Canonical Order – 419 sassa

Farawa 2:7

Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mutum daga turɓayar ƙasa, ya kuma hura numfashin rai cikin hancinsa, mutumin kuwa ya zama rayayyen taliki.

Farawa 9:6

“Duk wanda ya zub da jinin mutum, ta hannun mutum za a zub da jininsa; gama a cikin siffar Allah ne, Allah ya yi mutum.

Farawa 10:32

Waɗannan su ne zuriyar ’ya’yan Nuhu maza bisa ga jerin zuriyarsu cikin al’ummominsu. Daga waɗannan ne al’ummomi suka bazu ko’ina a duniya bayan ambaliya.

Farawa 11:1-9

To, a lokacin, yaren mutanen duniya ɗaya ne, maganarsu kuma ɗaya ce. Yayinda mutane suke ta yin ƙaura zuwa gabas, sai suka sami fili a Shinar, suka zauna a can. Suka ce wa juna, “Ku zo, mu yi tubula, mu gasa su sosai.” Suka yi amfani da tubula a maimakon duwatsu, kwalta kuma a maimakon laka. Sa’an nan suka ce, “Ku zo, mu gina wa kanmu birni da hasumiyar da za tă kai har sammai, domin mu yi wa kanmu suna, don kada mu warwatsu ko’ina a doron ƙasa.” Sai Ubangiji ya sauko don yă ga birni da kuma hasumiyar da mutanen suke gini. Ubangiji ya ce, “Ga su, su jama’a ɗaya ce, su duka kuwa harshensu guda ne. Wannan kuwa masomi ne kawai na abin da za su iya yi, babu kuma abin da suka yi shirya yi da ba za su iya yi ba. Zo, mu sauka, mu rikitar da harshensu don kada su fahimci juna.” Saboda haka Ubangiji ya watsar da su daga wurin zuwa ko’ina a doron ƙasa, suka kuwa daina gina birnin. Shi ya sa aka kira birnin Babel, domin a can ne Ubangiji ya rikitar da harshen dukan duniya. Daga can Ubangiji ya watsar da su ko’ina a doron ƙasa.

Farawa 12:2

“Zan mai da kai al’umma mai girma, zan kuma albarkace ka; zan sa sunanka yă zama mai girma, ka kuma zama sanadin albarka.

Farawa 35:11

Sai Allah ya ce masa, “Ni ne Allah Maɗaukaki, ka yi ta haihuwa, ka kuma riɓaɓɓanya. Al’umma da tarin al’ummai za su fito daga gare ka, sarakuna kuma za su fito daga jikinka.

Farawa 41:40-44

Za ka shugabanci fadata, kuma dukan mutanena za su zama a ƙarƙashinka. Da sarauta kaɗai zan fi ka girma.” Saboda haka Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Ga shi na sa ka zama shugaban dukan ƙasar Masar.” Sa’an nan Fir’auna ya zare zoben sarauta daga yatsarsa, ya sa shi a yatsan Yusuf. Ya sanya masa rigar lallausan lilin, ya kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa. Ya sa shi ya hau keken yaƙi a matsayi mai binsa na biyu, mutane kuwa suka yi shela a gabansa suna cewa, “A ba da hanya!” Ta haka ya sa shi shugaba a kan dukan ƙasar Masar. Sa’an nan Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Ni ne Fir’auna, amma in ba tare da umarninka ba, ba wanda zai ɗaga hannu ko ƙafa a cikin dukan Masar.”

Fitowa 7:10-13

Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna, suka yi yadda Ubangiji ya umarce su. Haruna ya jefa sandansa ƙasa, a gaban Fir’auna da bayinsa, sai sandan ya zama maciji. Fir’auna kuwa ya kira masu hikima da masu sihiri, sai bokayen Masarawa ma suka yi irin abubuwan nan da bokancinsu. Kowannensu ya jefa sandansa ƙasa, ya kuwa zama maciji. Amma sandan Haruna ya haɗiye sandunansu. Duk da haka zuciyar Fir’auna ta taurare, bai kuwa saurare su ba, kamar dai yadda Ubangiji ya riga ya faɗa.

Fitowa 11:4-8

Saboda haka Musa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Wajen tsakar dare, zan ratsa dukan Masar. Kowane ɗan fari, namiji, a Masar zai mutu, daga kan ɗan fari na Fir’auna wanda zai ci gadon sarauta, har zuwa kan ɗan fari na baiwa, wadda take niƙa, da kuma dukan ’yan farin shanu. Za a yi kuka mai zafi ko’ina a Masar, irin wadda ba a taɓa yi ba, ba kuwa za a ƙara yi ba. Amma a cikin Isra’ilawa, ba karen da zai yi haushi wa mutum ko dabba.’ Ta haka za ku sani Ubangiji zai bambanta tsakanin Masar da Isra’ila. Dukan fadawan nan naka za su zo wurina, suna fāɗi a gabana suna cewa, ‘Ka fita, kai da dukan jama’arka!’ Sa’an nan zan fita.” Daga nan sai Musa ya fita daga gaban Fir’auna a husace.

Fitowa 12:29-30

Da tsakar dare, sai Ubangiji ya karkashe dukan ’ya’yan fari a ƙasar Masar, tun daga ɗan farin Fir’auna, wato, magājinsa, har zuwa ɗan fari na ɗan sarƙa da yake kurkuku, har da ’ya’yan fari na dabbobi. Fir’auna da dukan fadawansa da kuma dukan Masarawa, suka tashi a cikin daren da kuka mai zafi, aka kuma ji kukan a ko’ina a cikin ƙasar Masar, gama ba gidan da ba a yi mutuwa ba.

Fitowa 15:18

“ Ubangiji zai yi mulki har abada abadin.”

Fitowa 18:19-22

Ka kasa kunne gare ni yanzu, zan ba ka shawara, Allah kuma yă kasance tare da kai. Kai za ka zama wakilin mutane a gaban Allah, ka kuma kawo gardamansu gare shi. Ka koya musu dokokinsa da farillarsa, ka kuma nuna musu hanyar rayuwa da ayyukan da za su yi. Amma ka zaɓi mutane masu iyawa daga dukan mutane, maza masu tsoron Allah, amintattu, masu ƙin rashawa, ka sanya su shugabanni na dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma. Bari waɗannan mutane su sassanta mutane a kan ƙananan matsaloli, amma kowace babban matsala, ko bukata ta musamman, sai su kawo wurinka, ƙananan matsaloli kuma sai su yanke hukuncin da kansu. Ta haka ne za su taimaka wajen ɗaukan nauyin jama’a, don su sa aikin yă zama maka da sauƙi.

Fitowa 18:25-26

Ya zaɓi mutane masu iyawa daga cikin dukan Isra’ila, ya naɗa su shugabannin mutane, shugabanni a kan dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma. Suka yi hidimar alƙalanci na mutane a dukan lokaci. Gardandamin da suke da wuya, suka kawo wurin Musa, amma ƙananan batuttuwa, suka shari’anta a tsakaninsu.

Fitowa 19:6-7

za ku zama firistoci masu tsarki da kuma al’umma keɓaɓɓiya a gare ni.’ Waɗannan su ne kalmomin da za ka faɗa wa Isra’ilawa.” Sai Musa ya koma ya aika a kira dukan dattawan mutane, ya bayyana dukan kalmomin da Ubangiji ya umarta, ya faɗa.

Fitowa 22:28

“Kada ku yi maganar saɓo ga Allah, ko ku la’anta mai mulkin mutanenku.

Firistoci 18:24-28

“ ‘Kada ku ƙazantar da kanku da wani daga cikin waɗannan, domin haka al’umman da zan kora a gabanku suka ƙazantu. Har ƙasar ma ta ƙazantu, saboda haka na hukunta ta saboda zunubinta, ƙasar kuwa ta amayar da mazaunanta. Amma dole ku kiyaye farillaina da kuma dokokina. Kada haifaffe ɗan ƙasa da baƙin da suke zama a cikinku yă yi wani daga cikin waɗannan abubuwa banƙyama, gama mutanen da suka zauna a wannan ƙasa kafin ku sun aikata dukan waɗannan abubuwa, suka kuma ƙazantu. Kuma in kuka ƙazantar da ƙasar, za tă amayar da ku kamar yadda ta amayar da al’umman da suka riga ku.

Firistoci 20:22-24

“ ‘Ku kiyaye dukan farillaina da dokokina duka, don kada ƙasar da nake kai ku ta amayar da ku. Kada ku yi zama bisa ga al’adun al’umman da zan kora a gabanku. Domin sun aikata dukan waɗannan abubuwa, na yi ƙyamarsu. Amma na faɗa muku, “Za ku mallaki ƙasarsu, zan ba ku ita gādo, ƙasa mai zub da madara da zuma.” Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya keɓe ku daga al’ummai.

Firistoci 26:46

Waɗannan su ne farillai, da dokoki, da kuma ƙa’idodin da Ubangiji ya kafa a Dutsen Sinai, tsakaninsa da Isra’ilawa ta wurin Musa.

Maimaitawar Shari’a 17:14-17

Sa’ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kuka mallake ta, kuka kuma zauna a cikinta, sai kuka ce, “Bari mu naɗa sarki a kanmu kamar sauran al’umman da suke kewaye da mu,” ku tabbata kun naɗa sarki a kanku wanda Ubangiji Allahnku ya zaɓa ne. Dole yă zama daga cikin ’yan’uwanku. Kada ku sa baƙo a kanku, wanda ba mutumin Isra’ila ɗan’uwanku ba. Sarkin, ba zai nemi dawakai da yawa wa kansa ba, ko yă sa mutane su koma Masar don su sami ƙarin dawakai ba, gama Ubangiji ya faɗa muku, “Ba za ku ƙara koma wancan hanya kuma ba.” Sarkin ba zai auri mata masu yawa ba, in ba haka ba zuciyarsa za tă karkata. Ba zai tara azurfa da zinariya da yawa ba.

Maimaitawar Shari’a 17:18-20

Sa’ad da ya hau kursiyin mulkinsa, sai yă rubuta wa kansa a littafin kofin wannan doka da aka ɗauka daga na firistoci, waɗanda suke Lawiyawa. Zai kasance tare da shi, zai kuma karanta shi dukan kwanakin ransa, saboda yă koyi girmama Ubangiji Allahnsa, yă kuma bi dukan kalmomin wannan doka da kuma waɗannan ƙa’idodi a hankali don kada yă ɗauki kansa ya fi ’yan’uwansa, yă kuma juya daga dokar zuwa dama, ko zuwa hagu. Sa’an nan shi da kuma zuriyarsa za su daɗe suna mulki a Isra’ila.

Maimaitawar Shari’a 32:8

Sa’ad da Mafi Ɗaukaka ya ba da al’ummai gādonsu, sa’ad da ya raba dukan ’yan adam, ya kafa iyakoki wa mutane bisa ga yawan ’ya’yan Isra’ila maza.

Mahukunta 8:22-23

Isra’ilawa suka ce wa Gideyon, “Ka yi mulkinmu, kai, ɗanka da jikanka, domin ka cece mu daga hannun Midiyawa.” Amma Gideyon ya ce musu, “Ni, ko ɗana, ba za mu yi mulkinku ba. Ubangiji ne zai yi mulkinku.”

Mahukunta 17:6

A kwanakin Isra’ila ba ta da sarki; kowa yana yin abin da ya ga dama.

1 Sama’ila 8:1-3

Da Sama’ila ya tsufa, sai ya naɗa ’ya’yansa maza su zama alƙalan Isra’ila. Sunan ɗansa na fari Yowel, na biyu kuwa Abiya. Suka yi alƙalanci a Beyersheba. Amma ’ya’yansa ba su bi hanyar mahaifinsu ba. Suka mai da hankalinsu ga neman kuɗi da cin hanci, suna kuma danne gaskiya.

1 Sama’ila 8:6-7

Amma Sama’ila bai ji daɗi sa’ad da suka ce, “Ka ba mu sarki da zai bi da mu.” Sai ya yi addu’a ga Ubangiji. Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka saurari dukan maganganun da mutanen suke gaya maka. Ai, ba kai ba ne suka ƙi, ni ne suka ƙi in zama sarkinsu.

1 Sama’ila 8:9-18

Yanzu ka saurare su amma ka yi musu kashedi sosai, ka sa su san abin da sarkin da zai bi da su zai yi.” Sama’ila kuwa ya ce wa mutanen da suke roƙo yă naɗa musu sarki dukan abin da Ubangiji ya faɗa. Ya ce musu, “Ga abin da sarkin da zai yi mulkinku zai yi. Zai kwashe ’ya’yanku yă sa su yi aiki da kekunan yaƙi da dawakansa, waɗansu za su riƙa gudu a gaban keken yaƙinsa. Zai sa waɗansu su zama shugabannin mutum dubu-dubu da kuma na hamsin-hamsin. Waɗansu za su yi masa noma da girbi. Waɗansu za su ƙera masa makaman yaƙi da kayayyaki don keken yaƙinsa. Zai sa ’ya’yanku mata yin aikin turare da dafe-dafe da kuma toye-toye. Zai karɓi gonakinku mafi kyau da gonakin inabinku da gonakin zaitunku yă ba wa ma’aikatansa. Zai kuma karɓi zakan hatsinku da na inabinku yă ba shugabannin fadarsa da sauran masu hidimarsa. Zai ƙwace bayinku maza da mata, da shanunku, da jakunanku mafi kyau domin su yi masa aiki. Zai karɓi zakan dabbobinku, ku kanku za ku zama bayinsa. Sa’ad da ranar ta zo, za ku yi kuka ku nemi a fishe ku daga sarkin da kuka zaɓa, Ubangiji kuwa ba zai ji ku ba.”

1 Sama’ila 8:19-20

Amma mutanen suka ƙi jin Sama’ila, sai suka ce, “A’a, mu dai, muna son sarki yă bi da mu.” Ta haka za mu zama kamar sauran ƙasashe, mu kasance da sarkin da zai bi da mu, yă tafi tare da mu zuwa yaƙe-yaƙe.

1 Sama’ila 9:17

Da Sama’ila ya hangi Shawulu, Ubangiji ya ce masa, “Ga mutumin da na yi maka magana, shi ne zai bi da mutanena.”

1 Sama’ila 10:1

Sai Sama’ila ya ɗauki ’yar kwalabar mai, ya zuba man ɗin wa Shawulu a kansa, ya yi masa sumba yana cewa, “ Ubangiji ya keɓe ka shugaba bisa gādonsa.

1 Sama’ila 10:19

Amma yanzu kun ƙi Allahnku wanda ya cece ku daga dukan masifu da wahaloli. Kuka ce, ‘Sam, a naɗa mana sarki.’ Saboda haka yanzu sai ku zo gaban Ubangiji kabila-kabila da iyali-iyali.”

1 Sama’ila 10:24-25

Sama’ila ya ce wa dukan mutane, “Kun ga wanda Ubangiji ya zaɓa ko? Ba wani kamar sa a cikin dukan mutane.” Sai mutane suka tā da murya suka ce, “Ran sarki yă daɗe.” Sama’ila kuwa ya bayyana wa mutane ƙa’idodin sarauta. Ya rubuta su cikin littafi ya ajiye a gaban Ubangiji. Sa’an nan ya sallame mutane, kowa ya koma gidansa.

1 Sama’ila 10:26-27

Shawulu ma ya tafi gidansa a Gibeya tare da waɗansu jarumawan da Allah ya taɓa zuciyarsu. Amma waɗansu ’yan iska suka ce, “Yaya wannan mutum zai iya cetonmu?” Suka rena shi suka ƙi su kawo masa kyautai. Amma Shawulu bai ce uffam ba.

1 Sama’ila 11:6-7

Da Shawulu ya ji, sa Ruhun Allah ya sauko a kansa da iko, ya husata ƙwarai. Ya ɗauki shanu biyu, ya yayyanka su gunduwa-gunduwa, ya aika da su ko’ina a ƙasar Isra’ila ta wurin manzanni cewa, “Duk wanda bai fita ya bi Shawulu da Sama’ila ba, haka za a yi da shanunsa.” Mutanen suka ji tsoron Ubangiji suka fita gaba ɗaya kamar mutum guda.

1 Sama’ila 11:12

Sai mutane suka ce wa Sama’ila, “Su wa suka ce, ‘Shawulu zai yi mulkinmu?’ A kawo mana su mu kashe.”

1 Sama’ila 11:15

Don haka dukan mutane suka tafi Gilgal, suka tabbatar da Shawulu sarki a gaban Ubangiji. A can suka miƙa hadaya ta salama a gaban Ubangiji, Shawulu kuwa da dukan Isra’ila suka yi babban liyafa.

1 Sama’ila 12:12-15

Amma da kuka ga Nahash sarkin Ammonawa yana matsowa yă yaƙe, sai kuka ce mini, “Sam, muna so sarki yă shugabance mu.” Ko da yake Ubangiji Allahnku ne yake mulkinku. Yanzu ga sarkinku da kuka zaɓa wanda kuka nema, ga shi Ubangiji ya naɗa muku sarki. In kuka ji tsoron Ubangiji, kuka bauta masa, kuka yi masa biyayya, ba ku kuwa ƙi bin umarninsa ba, in kuma ku da sarkin da yake mulkinku kun bi Ubangiji Allahnku, to, za ku zauna lafiya. Amma in ba ku yi biyayya ga Ubangiji ba, in kuma kuka ƙi bin umarnansa, fushinsa zai zauna a kanku.

1 Sama’ila 12:19-20

Dukan mutane suka ce wa Sama’ila, “Ka yi addu’a ga Ubangiji Allahnka saboda bayinka, domin kada mu mutu, gama mun ƙara wa kanmu zunubi da muka roƙa a yi mana sarki.” Sama’ila ya ce, “Kada ku ji tsoro.” Kun yi waɗannan mugunta duk da haka kada ku bar bin Ubangiji, amma ku bauta wa Ubangiji da dukan zuciyarku.

1 Sama’ila 12:25

Amma in kuka duƙufa cikin aikin mugunta da ku da sarkinku za a hallaka ku.

1 Sama’ila 13:8-14

Ya jira har kwana bakwai bisa ga lokacin da Sama’ila ya bayar. Amma Sama’ila bai zo Gilgal ba, mutanen Shawulu suka fara watsewa. Sai ya ce, “Ku kawo mini hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama.” Sai Shawulu ya miƙa hadaya ta ƙonawa. Daidai yana gama miƙa hadaya ke nan sai Sama’ila ya iso. Shawulu kuma ya fito domin yă yi masa maraba. Sama’ila ya ce, “Me ke nan ka yi?” Shawulu ya ce, “Sa’ad da na ga mutane suna watsewa, kai kuwa ba ka zo cikin lokaci ba, ga Filistiyawa kuma suna taruwa a Mikmash, sai na yi tunani cewa, ‘Yanzu Filistiyawa za su gangaro su fāɗa mini a Gilgal, ga ni kuma ban riga na nemi nufin Ubangiji ba.’ Shi ya sa ya zama mini tilas in miƙa hadaya ta ƙonawa.” Sama’ila ya ce, “Ka yi wauta da ba ka bi umarnin da Ubangiji Allahnka ya ba ka ba. Da ka yi haka da Ubangiji ya tabbatar maka da sarautar Isra’ila har abada. Amma yanzu, masarautarka ba za tă dawwama ba, Ubangiji ya riga ya sami wani wanda zuciyarsa ke ƙauna, ya naɗa shi shugaban mutanensa gama ba ka bi umarnin Ubangiji ba.”

1 Sama’ila 15:22-23

Amma Sama’ila ya ce, “ Ubangiji yana murna da sadaka da hadaya fiye da biyayya ga maganar Ubangiji? Yin biyayya ta fi hadaya a kula kuma ta fi ƙibabbun raguna. Gama tawaye yana kama da zunubi na duba, girman kai kuma yana kama da bautar gumaka. Saboda ka ƙi maganar Ubangiji, shi ma ya ƙi ka da zaman sarki.”

1 Sama’ila 15:24-26

Sai Shawulu ya ce wa Sama’ila, “Na yi zunubi, na ƙi bin umarnin Ubangiji, na kuma ƙi bin maganarka. Na ji tsoron mutane ne shi ya sa na bi maganarsu. Yanzu fa, ina roƙonka ka yafe mini zunubina, ka koma tare da ni, domin in yi wa Ubangiji sujada.” Amma Sama’ila ya ce, “Ba zan koma tare da kai ba. Ka ƙi maganar Ubangiji, Ubangiji kuma ya ƙi ka da zama sarki a bisa Isra’ila.”

1 Sama’ila 16:13

Saboda haka Sama’ila ya ɗauko ƙahon nan da yake da mai ya shafe Dawuda a gaban ’yan’uwansa. Daga wannan rana kuwa ruhun Ubangiji ya sauko wa Dawuda da iko. Sai Sama’ila ya koma Rama.

1 Sama’ila 24:5-8

Daga baya Dawuda ya damu domin ya yanke shafin rigar Shawulu. Ya ce wa mutanensa, “ Ubangiji yă sawwaƙe in yi abu haka ga shugabana da Ubangiji ya shafe, ko in ɗaga hannuna in kashe shi, gama shi shafaffe ne na Ubangiji.” Da wannan magana Dawuda ya kwaɓi mutanensa, bai yarda su fāɗa wa Shawulu ba. Shawulu kuwa ya bar kogon ya yi tafiyarsa. Daga baya Dawuda ya fita daga kogon sai ya kira Shawulu ya ce, “Ranka yă daɗe, sarki!” Da Shawulu ya waiwaya, sai Dawuda ya rusuna da fuskarsa har ƙasa.

1 Sama’ila 24:20-22

Na sani tabbatacce za ka zama sarki. Masarautar Isra’ila za tă kahu a hannunka. Yanzu ka rantse mini da Ubangiji cewa ba za ka hallaka zuriyarta ko ka share sunana daga iyalin mahaifina ba.” Sai Dawuda ya rantse wa Shawulu. Sa’an nan Shawulu ya koma gida, amma Dawuda da mutanensa suka haura zuwa wurin ɓuya.

1 Sama’ila 26:9-12

Amma Dawuda ya ce wa Abishai, “Kada ka hallaka shi. Wa zai sa hannu a kan shafaffe na Ubangiji, har yă tsira? Muddin Ubangiji yana a raye, Ubangiji da kansa zai buge shi, ko yă mutu a lokacinsa, ko kuma yă mutu a wurin yaƙi. Amma Allah yă sawwaƙa in sa hannu a shafaffen Ubangiji, ka ɗauki māshin da butar ruwan da take kusa da kansa mu tafi.” Saboda haka Dawuda ya ɗauki māshin da butar ruwan da take kusa da Shawulu suka tafi. Ba wanda ya gan su, ba wanda ya san abin da ya faru, ba kuwa wanda ya farka, dukansu suna barci gama Ubangiji ya sa barci mai nauyi ya ɗauke su.

2 Sama’ila 1:14-16

Dawuda ya ce masa, “Yaya ba ka ji tsoro ɗaga hannu ka hallaka shafaffe na Ubangiji ba?” Sai Dawuda ya kira ɗaya daga cikin mutanensa ya ce, “Je ka kashe shi!” Haka kuwa ya buge shi, ya kuwa mutu. Gama Dawuda ya riga ya ce masa, “Alhakin jininka yana bisa kanka tun da yake da bakinka ka ce, ‘Ni ne na kashe shafaffe na Ubangiji.’ ”

2 Sama’ila 2:4

Sa’an nan mutanen Yahuda suka zo Hebron, a can kuwa suka naɗa Dawuda sarkin Yahuda. Sa’ad da aka gaya wa Dawuda cewa mutanen Yabesh Gileyad ne suka binne Shawulu,

2 Sama’ila 7:12-17

Sa’ad da kwanakinka suka ƙare, za ka huta tare da kakanninka, zan tā da zuriyarka, na cikinka, zan kuma sa mulkinsa ya kahu. Shi zai gina gida domin Sunana, zan kuwa kafa gadon sarautarsa har abada. Zan zama Ubansa, shi kuma yă zama ɗana. Idan ya yi laifi, zan yi amfani da mutane in hukunta shi. Mutane ne za su zama bulalata. Amma ba za a taɓa ɗauke ƙaunata daga gare shi yadda na ɗauke ta daga wurin Shawulu ba, shi wannan wanda na kawar daga gabanka. Gidanka da kuma masarautarka za su dawwama har abada a gabana; gadon sarautarka kuma zai kahu har abada.’ ” Natan ya gaya wa Dawuda dukan abin da Allah ya bayyana masa.

2 Sama’ila 8:15

Dawuda ya yi mulkin dukan ƙasar Isra’ila, yana yin wa dukan jama’arsa shari’ar gaskiya da adalci.

2 Sama’ila 23:3

Allah na Isra’ila ya yi magana, Dutsen Isra’ila ya ce mini, ‘Sa’ad da wani ya yi mulkin mutane da adalci, sa’ad da ya yi mulki da tsoron Allah,

1 Sarakuna 1:23

Sai aka faɗa wa sarki, “Ga annabi Natan.” Da Natan ya je gaban sarki, sai ya rusuna da fuskarsa har ƙasa.

1 Sarakuna 1:39-40

Zadok firist ya ɗauki ƙahon mai daga tenti mai tsarki, ya shafe Solomon. Sa’an nan suka busa ƙaho, sai dukan mutane suka yi ihu, suna cewa “Ran Sarki Solomon yă daɗe!” Dukan mutane kuwa suka haura suka bi shi, suna busan sarewa, suna farin ciki sosai, har ƙasa ta girgiza saboda sowa.

1 Sarakuna 3:3-4

Solomon ya ƙaunaci Ubangiji ta wurin yin tafiya bisa ga farillan mahaifinsa Dawuda, sai dai ya miƙa hadayu, ya kuma ƙone turare a wuraren nan na bisa tuddai. Sai sarki Solomon ya tafi Gibeyon don yă miƙa hadayu, gama a can ne wuri mafi muhimmanci na sujada. Solomon kuwa ya miƙa hadayun ƙonawa guda dubu a kan wannan bagade.

1 Sarakuna 3:5-14

A Gibeyon, Ubangiji ya bayyana ga Solomon da dare a mafarki, Allah ya ce, “Ka roƙi abin da kake so in ba ka.” Solomon ya amsa ya ce, “Ka nuna alheri mai girma ga bawanka, mahaifina Dawuda domin ya yi aminci gare ka da adalci, ya kuma kasance da zuciya mai gaskiya. Ka ci gaba da wannan alheri mai girma gare shi, ka ba shi ɗa don yă zauna a kujerar sarautarsa a wannan rana. “Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka sa bawanka a wurin mahaifina Dawuda. Amma ni ɗan yaro ne kawai, ban kuma san yadda zan yi ayyukana ba. Bawanka yana nan a cikin mutanen da ka zaɓa, mutane masu girma, waɗanda suka wuce ƙirge, ko a lissafta. Saboda haka ka ba bawanka zuciyar ganewa, don yă shugabanci mutanenka, yă kuma iya rarrabe tsakanin abin da yake daidai da abin da ba daidai ba. Gama wa zai iya shugabance wannan mutanenka masu girma haka?” Sai Ubangiji ya ji daɗi cewa Solomon ya roƙa wannan. Saboda haka Allah ya ce masa, “Da yake ka nemi wannan ne, ba ka kuwa nemi tsawon rai ko arziki wa kanka ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, amma ka nemi ganewa a aikata gaskiya, zan yi abin da ka roƙa. Zan ba ka zuciya mai hikima da ta ganewa, har yă zama ba a taɓa samun wani kamar ka ba, ba kuwa za a taɓa samunsa ba. Ban da haka ma, zan ba ka abin da ba ka nema ba; arziki da girma, don a rayuwarka ba za ka kasance da wani kamar ka ba a cikin sarakuna. In kuma ka yi tafiya a hanyoyina, ka kuma yi biyayya da farillaina da umarnaina kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, zan ba ka tsawon rai.”

1 Sarakuna 8:22-23

Sai Solomon ya tsaya a gaban bagaden Ubangiji, a gaban dukan taron Isra’ila, ya ɗaga hannuwansa sama, ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, babu Allah kamar ka a sama can bisa, ko a ƙasa can ƙarƙashi, kai da kake kiyaye alkawarinka na ƙauna ga bayinka waɗanda suke cin gaba a hanyarka da dukan zuciyarsu.

1 Sarakuna 10:23

Sarki Solomon ya yi suna a wadata fiye da dukan sarakunan duniya.

1 Sarakuna 11:1-8

Sarki Solomon ya ƙaunaci baƙin mata. Ban da ’yar Fir’auna, ya auri Mowabawa, Ammonawa, mutanen Edom, Sidoniyawa da Hittiyawa. Sun fito daga al’ummai da Ubangiji ya ce wa Isra’ilawa, “Kada ku yi aurayya da su, domin tabbatacce za su juye zukatanku zuwa ga waɗansu alloli.” Duk da haka Solomon ya manne musu, ya nace, yana ƙaunarsu. Ya auri mata ɗari bakwai, haifaffun gidan sarauta, da kuma ƙwarƙwarai ɗari uku. Matan nan nasa suka karkatar da shi. Yayinda Solomon yake tsufa, matansa suka juye zuciyarsa ga bin waɗansu alloli, zuciyarsa kuwa ba tă bi Ubangiji Allahnsa ɗungum kamar yadda zuciyar Dawuda mahaifinsa ta kasance ba. Ya bi Ashtarot, alliyar Sidoniyawa, da Molek, allahn da aka hana na Ammonawa. Saboda haka Solomon ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji. Bai bi Ubangiji gaba ɗaya kamar yadda Dawuda mahaifinsa ya yi ba. A kan tudu, gabas da Urushalima, Solomon ya gina masujada a can domin Kemosh, allahn da aka hana na Mowab, da Molek, allahn da aka hana na Ammonawa. Ya yi haka domin dukan baƙin matansa, waɗanda suka ƙone turare suka kuma miƙa hadayu ga allolinsu.

1 Sarakuna 11:9-11

Ubangiji ya yi fushi da Solomon domin zuciyarsa ya juye daga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda ya bayyana masa sau biyu. Ko da yake ya hana Solomon bin waɗansu alloli, Solomon bai kiyaye umarnin Ubangiji ba. Saboda haka Ubangiji ya ce wa Solomon, “Da yake halinka ke nan, ba ka kuma kiyaye alkawarina, da ƙa’idodina da na umarce ka ba, tabbatacce zan yage masarautar daga gare ka, in ba da ita ga ɗaya daga cikin bayinka.

1 Sarakuna 12:12-14

Bayan kwana uku, Yerobowam da dukan mutane suka dawo wurin Rehobowam yadda sarki ya faɗa, “Ku dawo gare ni cikin kwana uku.” Sai Sarki ya amsa wa mutane da zafi. Yana ƙin shawarar da dattawa suka ba shi. Ya bi shawarar matasa, ya ce, “Mahaifina ya sa muku kaya masu nauyi; ni zan ma sa su fi haka nauyi. Mahaifina ya hore ku da bulala; ni kuwa zan hore ku da kunamai.”

1 Sarakuna 12:31-32

Yerobowam ya gina masujadai da suke kan tuddai, ya kuma naɗa firistoci barkatai daga cikin mutanen da ba na zuriyar Lawi ba. Ya kafa biki a rana ta goma sha biyar ta watan takwas, kamar bikin da ake yi a Yahuda, ya kuma miƙa hadayu a bisa bagade. Ya yi haka a Betel, yana miƙa wa siffofin maruƙan da ya yi hadayu. A Betel kuma ya naɗa firistoci a wuraren tudun da ya yi.

1 Sarakuna 13:4-5

Sa’ad da Yerobowam ya ji abin da mutumin Allah ya tā da murya ya faɗa game da bagaden Betel, sai ya miƙa hannunsa daga bagaden ya ce, “Ku kama shi!” Amma sai hannun da ya miƙa ya yanƙwane, har bai iya janye shi ba. Haka ma, bagaden ya rabu, tokarsa kuma ya zuba, bisa ga alamar da mutumin Allah ya bayar, ta wurin kalmar Ubangiji.

1 Sarakuna 13:33-34

Har ma bayan wannan, Yerobowam bai canja daga mugayen hanyoyinsa ba, amma ya ƙara naɗa firistoci domin masujadai da suke kan tuddai daga kowane irin mutane. Duk wanda ya so yă zama firist sai yă naɗa shi don aiki a masujadai da suke kan tuddai. Wannan ne zunubin gidan Yerobowam da ya kai ga fāɗuwarsa da kuma hallakarsa daga fuskar duniya.

1 Sarakuna 14:9-10

Ka aikata mugunta fiye da dukan waɗanda suka rayu kafin kai. Ka yi wa kanka waɗansu alloli, gumakan da aka yi da ƙarfe; ka tsokane ni na yi fushi, ka kuma juye mini baya. “ ‘Saboda wannan, zan kawo masifa a gidan Yerobowam. Zan yanke kowane ɗa na ƙarshe a Isra’ila, bawa ko ’yantacce. Zan ƙone gidan Yerobowam kamar yadda mutum yakan ƙone juji, sai duk ya ƙone ƙurmus.

1 Sarakuna 14:16

Zai kuma ba da Isra’ila saboda zunuban da Yerobowam ya yi, da ya kuma sa Isra’ila suka yi.”

1 Sarakuna 15:1-3

A shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yerobowam ɗan Nebat, Abiyam ya zama sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara uku. Sunan mahaifiyarsa Ma’aka ne, ’yar Abisalom. Shi ma ya aikata dukan irin zunubai da tsohonsa ya yi. Zuciyarsa ba tă bi Ubangiji Allahnsa, kamar yadda zuciyar Dawuda kakansa ta yi ba.

1 Sarakuna 15:11-14

Asa ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar yadda kakansa Dawuda ya yi. Ya kori dukan maza karuwai na masujadai daga ƙasar, ya kuma yi waje da dukan gumakan da mahaifinsa ya yi. Ya tuɓe mahaifiya mahaifiyarsa Ma’aka daga matsayinta na mahaifiyar sarauniya, gama ta gina ƙazantaccen ginshiƙin Ashera. Asa ya yanke ginshiƙin, ya kuma ƙone shi a Kwarin Kidron. Ko da yake bai cire masujadai da suke kan tuddai ba, zuciyar Asa ta kasance da aminci ɗungum ga Ubangiji dukan kwanakinsa.

1 Sarakuna 15:25-26

Nadab ɗan Yerobowam ya zama sarkin Isra’ila a shekara ta biyu ta Asa sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a bisa Isra’ila shekara biyu. Ya yi mugunta a gaban Ubangiji, yana tafiya a hanyoyin mahaifinsa da kuma cikin zunubinsa, wanda ya sa Isra’ila suka yi.

1 Sarakuna 15:30

Wannan abu ya faru saboda zunuban da Yerobowam ya yi, ya kuma sa Isra’ila ya yi, kuma saboda ya tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya yi fushi.

1 Sarakuna 15:33-34

A shekara ta uku ta Asa sarkin Yahuda, Ba’asha ɗan Ahiya ya zama sarkin dukan Isra’ila a Tirza, ya kuma yi sarauta shekara ashirin da huɗu. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, yana tafiya a hanyoyin Yerobowam da kuma cikin zunubinsa, wanda ya sa Isra’ila suka yi.

1 Sarakuna 16:4

Karnuka za su cinye waɗanda suke na Ba’asha da suka mutu a birni, tsuntsaye kuma za su cinye waɗanda suka mutu a jeji.”

1 Sarakuna 16:7

Ban da haka, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Yehu ɗan Hanani wa Ba’asha da gidansa, saboda dukan muguntar da ya aikata a gaban Ubangiji, ya tsokane shi yă yi fushi ta wurin abubuwan da ya yi, da kuma zama kamar gidan Yerobowam, da kuma domin ya hallaka gidan Yerobowam.

1 Sarakuna 16:12-13

Ta haka Zimri ya hallaka dukan iyalin Ba’asha, bisa ga maganar da Ubangiji ya yi game da Ba’asha ta wurin annabi Yehu. Wannan ya faru saboda dukan zunuban Ba’asha da waɗanda ɗansa Ela ya yi, da ya sa Isra’ila suka yi, har suka tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila, yă yi fushi ta wurin gumakansu marasa amfani.

1 Sarakuna 16:18-19

Da Zimri ya ga cewa an kame birnin, sai ya je ya shiga hasumiya fadan sarki ya sa wa fadan wuta wutar kuwa ta ƙone shi ya mutu. Wannan ya faru saboda zunuban da ya yi, ya yi mugunta a gaban Ubangiji ya kuma yi tafiya a hanyoyin Yerobowam da kuma cikin zunubin da Yerobowam ya yi da ya sa Isra’ila suka yi.

1 Sarakuna 16:25-26

Amma Omri ya yi mugunta a gaban Ubangiji, ya kuma yi zunubi fiye da dukan waɗanda suka kasance kafin shi. Ya yi tafiya a dukan hanyoyin Yerobowam ɗan Nebat da kuma cikin zunubinsa wanda ya sa Isra’ila suka yi, har suka tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila yă yi fushi ta wurin gumakansu marasa amfani.

1 Sarakuna 16:30-33

Ahab ɗan Omri ya yi mugunta sosai a gaban Ubangiji fiye da wani daga cikin waɗanda suka riga shi. Bai zama masa wani abu mai wuya ba, yă yi zunuban Yerobowam ɗan Nebat, har ma ya auri Yezebel ’yar Etba’al sarkin Sidoniyawa, ya kuma fara bauta wa Ba’al, ya yi masa sujada. Ya kafa bagade domin Ba’al a haikalin Ba’al da ya gina a Samariya. Ahab ya gina ginshiƙin Ashera, ya kuma aikata abubuwa masu yawa don yă tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila yă yi fushi fiye da dukan sarakunan Isra’ila da suka riga shi.

1 Sarakuna 18:4

Yayinda Yezebel tana kisan annabawan Ubangiji, Obadiya ya ɗauki annabawa ɗari ya ɓoye a kogwanni biyu, hamsin a kowanne, ya kuma tanada musu abinci da kuma ruwa.)

1 Sarakuna 18:17-19

Sa’ad da Ahab ya ga Iliya, sai ya ce masa, “Kai ne wannan, kai mai tā-da-na-zaune-tsaye a Isra’ila?” Iliya ya amsa, ya ce, “Ban tā-da-na-zaune-tsaye a Isra’ila ba. Amma kai da iyalin mahaifinka, ku kuka tā-da-na-zaune-tsaye. Ka ƙyale umarnai Ubangiji, ka bi Ba’al. Yanzu ka tara mutane daga dukan Isra’ila su sadu da ni a kan Dutsen Karmel. Ka kuma kawo annabawa ɗari huɗu da hamsin na Ba’al, da kuma annabawa ɗari huɗu na Ashera, waɗanda suke ci a teburin Yezebel.”

1 Sarakuna 19:1-2

Ahab fa ya faɗa wa Yezebel kome da Iliya ya yi, da yadda ya karkashe dukan annabawan da takobi. Saboda haka Yezebel ta aika da ɗan aika wa Iliya yă faɗa masa, “Bari alloli su hukunta ni da tsanani, in war haka gobe ban mai da ranka kamar na ɗaya daga cikin annabawan Ba’al ba.”

1 Sarakuna 21:17-24

Sai maganar Ubangiji ta zo wa Iliya mutumin Tishbe. Ta ce, “Gangara don ka sadu da Ahab sarkin Isra’ila, wanda yake mulki a Samariya. Yanzu yana a gonar inabin Nabot, inda ya tafi yă mallake ta. Ka ce masa, Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Ba ka kashe mutum ka kuma ƙwace kayansa ba?’ Sa’an nan ka ce masa ga abin da Ubangiji ya ce, ‘A inda karnuka suka lashe jinin Nabot, karnuka za su lashe jininka, I, naka!’ ” Ahab ya ce wa Iliya, “Wato, ka same ni kuma, abokin gābana!” Sai ya amsa ya ce, “Na same ka, domin ka sayar da kanka ga yin mugunta a gaban Ubangiji. ‘Zan kawo masifa a kanka. Zan kawar da zuriyarka, in kuma yanke daga Ahab kowane ɗa namiji na ƙarshe cikin Isra’ila, bawa ko ’yantacce. Zan mai da gidanka kamar gida Yerobowam ɗan Nebat, da na Ba’asha ɗan Ahiya, domin ka tsokane ni har na yi fushi, ka kuma sa Isra’ila ya yi zunubi.’ “Game da Yezebel kuwa Ubangiji ya ce, ‘Karnuka za su cinye Yezebel a katangar Yezireyel.’ “Karnuka za su cinye waɗanda suke na Ahab waɗanda suka mutu a cikin birni, tsuntsayen sararin sama kuma za su cinye waɗanda suka mutu a jeji.”

1 Sarakuna 21:25-29

(Babu wani mutum kamar Ahab, wanda ya ba da kansa ga aikata mugunta a gaban Ubangiji. Yezebel matarsa ce ta zuga shi. Ya yi abar ƙyama ƙwarai ta wurin bin gumaka, kamar Amoriyawan da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ila.) Sa’ad da Ahab ya ji waɗannan kalmomi, sai ya yage rigarsa, ya sa rigunan makoki, ya kuma yi azumi. Ya kwanta a kayan makoki, ya kuma yi tafiya cikin sauƙinkai. Sai maganar Ubangiji ta zo wa Iliya mutumin Tishbe, ta ce, “Ka lura da yadda Ahab ya ƙasƙantar da kansa a gabana kuwa? Domin ya ƙasƙantar da kansa, ba zan kawo wannan masifa a kwanakinsa ba, amma zan kawo ta a kan gidansa a kwanakin ɗansa.”

1 Sarakuna 22:38-39

Suka wanke keken yaƙi a tafki, a Samariya (inda karuwai suke wanka), sai karnuka suka lashe jininsa, kamar yadda maganar Ubangiji ta furta. Game da sauran ayyukan mulkin Ahab, haɗe da dukan abin da ya yi, da fadan da ya gina ya kuma shimfiɗa da hauren giwa, da biranen da ya gina, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.

1 Sarakuna 22:43-44

A cikin kome ya yi tafiya a hanyoyin mahaifinsa Asa, bai kuma kauce daga gare su ba; ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji. Amma bai rurrushe masujadai da suke kan tuddai ba, mutane kuwa suka ci gaba da miƙa hadayu suna kuma ƙone turare a can. Yehoshafat kuma ya zauna lafiya da sarkin Isra’ila.

1 Sarakuna 22:51-53

Ahaziya ɗan Ahab ya zama sarkin Isra’ila a Samariya a shekara ta goma sha bakwai ta Yehoshafat sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki a bisa Isra’ila shekaru biyu. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, domin ya yi tafiya a hanyoyin mahaifinsa da na mahaifiyarsa, da kuma a hanyoyin Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila suka yi zunubi. Ya bauta, ya kuma yi wa Ba’al sujada, ya tsokane Ubangiji, Allah na Isra’ila yă yi fushi, kamar yadda mahaifinsa ya yi.

2 Sarakuna 1:16-17

Iliya ya ce wa sarki, “Ga abin da Ubangiji ya ce, don babu Allah a Isra’ila ne wanda za ka tuntuɓa da ka aika a tuntuɓi Ba’al-Zebub, allahn Ekron? Domin ka yi haka, ba za ka tashi daga gadon da kake kwance ba, ba shakka za ka mutu!” Ya kuwa mutu yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Iliya. Da yake Ahaziya ba shi da ɗa, sai Yoram ya gāje shi, ya zama sarki a shekara ta biyu ta mulkin Yehoram, ɗan Yehoshafat, sarkin Yahuda.

2 Sarakuna 3:1-3

Yoram, ɗan Ahab ya zama sarki Isra’ila, a Samariya, a shekara ta goma sha takwas ta mulkin Yehoshafat, sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki shekara goma sha biyu. Yoram ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, amma ba kamar yadda mahaifinsa da mahaifiyarsa suka yi ba. Ya kawar da dutsen tsarkin Ba’al wanda mahaifinsa ya yi. Duk da haka ya manne wa zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta aikata, bai rabu da su ba.

2 Sarakuna 8:16-18

A shekara ta biyar ta mulkin Yoram ɗan Ahab, sarkin Isra’ila, sa’ad da Yehoshafat yake sarautar Yahuda, Yoram ɗan Yehoshafat, ya fara mulkinsa a matsayin sarkin Yahuda. Yana da shekara talatin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki na tsawon shekara takwas a Urushalima. Ya bi gurbin sarakunan Isra’ila, yadda gidan Ahab ta yi, gama ya auri ’yar Ahab. Ya yi mugunta a gaban Ubangiji.

2 Sarakuna 8:26-27

Ahaziya yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara ɗaya. Sunan mahaifiyarsa Ataliya, jikanyar Omri, sarkin Isra’ila. Ya bi gurbin gidan Ahab, ya yi mugunta a gaban Ubangiji yadda gida Ahab ta yi, gama yana da dangantaka ta aure da gidan Ahab.

2 Sarakuna 9:5-8

Da ya isa can, sai ya tarar da hafsoshin soji zaune a wuri guda. Sai ya ce, “Ina da saƙo dominka komanda.” Sai Yehu ya ce, “Wanne a cikinmu?” Sai ce, “Dominka, komanda.” Sai Yehu ya tashi ya shiga cikin gida. Sa’an nan annabin ya zuba wa Yehu mai a kā, ya ce, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Na naɗa ka sarki a bisa jama’ar Ubangiji, wato, Isra’ila. Za aka hallaka gidan Ahab maigidanka, zan kuma ɗauki fansar jinin bayina annabawa da kuma jinin dukan bayin Ubangiji da Yezebel ta zub da. Dukan gidan Ahab zai hallaka. Zan kashe dukan ’ya’yan Ahab maza a Isra’ila, bayi ko ’yantattu.

2 Sarakuna 9:30-37

Sa’an nan Yehu ya je Yezireyel. Sa’ad da Yezebel ta sami labari, sai ta sha kwalliya ta gyara gashin kanta, ta zauna tana kallo daga taga. Yayinda Yehu ya shiga ƙofa, sai ta ce, “Lafiya, kai Zimri, mai kashe maigidansa?” Sai ya ɗaga ido ya dubi tagan ya ce, “Wa yake gefena? Wane ne?” Sai bābānni biyu ko uku suka leƙo suka dube shi. Yehu ya ce musu, “Ku jefa ta ƙasa!” Sai suka jefar da ita, jininta ya fantsama a jikin bango da kuma a jikin dawakai yayinda suke tattaka ta. Yehu ya shiga ya ci, ya kuma sha. Ya ce, “Ku san yadda za ku yi da la’ananniyan nan, ku binne ta, gama ’yar sarki ce.” Amma sa’ad da suka je don su binne ta, ba su sami kome ba sai ƙoƙon kanta, ƙafafunta da kuma hannuwanta. Suka komo suka faɗa wa Yehu, wanda ya ce, “Wannan ita ce maganar da Ubangiji ya faɗa ta bakin bawansa Iliya mutumin Tishbe. A fili, a Yezireyel, karnuka za su cinye naman Yezebel. Gawar Yezebel zai zama kamar juji a ƙasa, a fili, a Yezireyel, har ba wanda zai iya cewa, ‘Wannan Yezebel ce.’ ”

2 Sarakuna 10:18-24

Sa’an nan Yehu ya tattara dukan jama’a ya ce musu, “Ahab ya bauta wa Ba’al kaɗan ne kawai; amma Yehu zai bauta masa sosai. Yanzu sai ku kira dukan annabawan Ba’al, dukan masu yin masa hidima da kuma dukan firistocinsa. Ku tabbata ba a manta da wani ba, gama zan yi wa Ba’al babbar hadaya. Duk wanda bai zo ba, a bakin ransa.” Amma Yehu yana wayo ne domin yă hallaka masu yi wa Ba’al sujada. Yehu ya ce, “Ku kira jama’a don a girmama Ba’al.” Saboda haka suka yi shela. Sa’an nan ya aika saƙo ko’ina a Isra’ila, dukan masu yi wa Ba’al hidima kuwa suka tattaru, ba mutumin da bai zo ba. Suka yi cincirindo a haikalin Ba’al har sai da ya cika makil. Sai Yehu ya ce wa mai ajiyar tufafi, “Ka kawo riguna domin dukan masu yi wa Ba’al hidima.” Sai ya fito musu da riguna. Sa’an nan Yehu da Yehonadab ɗan Rekab, suka shiga haikalin Ba’al. Yehu ya ce wa masu yi wa Ba’al sujada, “Ku dudduba ku tabbatar cewa babu wani bawan Ubangiji a nan tare da ku, sai masu hidimar Ba’al kawai.” Saboda haka suka shiga don su miƙa hadayu da kuma hadaya ta ƙonawa. To, Yehu ya riga ya ba wa mutane takwas wannan kashedi a waje cewa, “In waninku ya bar ɗaya daga cikin mutanen nan da nake danƙa a hannunku ya tsere, to, a bakin ransa.”

2 Sarakuna 10:27

Suka farfasa dutsen tsafin Ba’al, suka kuma rushe haikalin, mutane suka mai da wurin salga har yă zuwa yau.

2 Sarakuna 10:31

Duk da haka, Yehu bai mai da hankali ya kiyaye dokokin Ubangiji, Allah na Isra’ila da dukan zuciyarsa ba. Bai rabu da zunubin Yerobowam, wanda ya sa Isra’ila ta aikata ba.

2 Sarakuna 11:14

Da ta duba sai ga sarki, tsaye kusa da ginshiƙi, bisa ga al’ada. Hafsoshi da masu busa suna tsaye kusa da sarki, dukan mutanen ƙasar kuma suna farin ciki suna busa ƙahoni. Sai Ataliya ta keta tufafinta ta tā da murya tana cewa, “Kai! Wannan cin amana ne! Ai, wannan cin amana ne!”

2 Sarakuna 12:2-3

Yowash ya aikata abin da yake daidai a idon Ubangiji domin Yehohiyada firist ya koya masa. Amma fa ba a kawar da masujadan kan tuddai ba; mutane suka ci gaba da miƙa hadayu da kuma ƙona turare a kan tuddai.

2 Sarakuna 13:1-2

A shekara ta ashirin da uku ta Yowash ɗan Ahaziya, sarkin Yahuda, Yehoyahaz ɗan Yehu, ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuwa yi mulki shekaru goma sha bakwai. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji ta wurin bin zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta aikata, bai kuwa guje musu ba.

2 Sarakuna 13:10-11

A shekaru talatin da bakwai ta Yowash sarkin Yahuda, Yehowash ɗan Yehoyahaz ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuma yi mulki shekaru goma sha shida. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, bai juya ga barin zunuban Yerobowam ɗan Nebat ba, wanda ya sa Isra’ila ta aikata, ya ci gaba da yinsu.

2 Sarakuna 14:1-4

A shekara ta biyu ta mulkin Yehowash ɗan Yehoyahaz sarkin Isra’ila, Amaziya ɗan Yowash sarkin Yahuda ya fara mulki. Ya zama sarki yana da shekaru ashirin da biyar, ya kuma yi mulki a Urushalima shekaru ashirin da tara. Sunan mahaifiyarsa Yehoyaddin, mutuniyar Urushalima. Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji, sai dai ba kamar kakansa Dawuda ba. A kome dai ya bi gurbin mahaifinsa Yowash. Ba a dai kawar da masujadan kan tudu ba; mutane suka ci gaba da yin hadaya da ƙone turare a can.

2 Sarakuna 14:23-24

A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Amaziya ɗan Yowash sarkin Yahuda, Yerobowam ɗan Yehowash sarkin Isra’ila ya zama sarki a Samariya, ya kuma yi mulki na shekaru arba’in da ɗaya. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji bai kuwa kauce wa duk zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta aikata ba.

2 Sarakuna 15:1-5

A shekara ta ashirin da bakwai ta mulkin Yerobowam sarkin Isra’ila, Azariya ɗan Amaziya, sarkin Yahuda ya fara mulki. Yana da shekara goma sha shida sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyu. Sunan mahaifiyarsa Yekoliya daga Urushalima. Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji, yadda mahaifinsa Amaziya ya yi. Amma bai kawar da masujadan kan tudu ba; mutane kuwa suka yi ta yin hadaya da ƙona turare a can. Ubangiji ya sa wa sarki ciwon kuturta har mutuwarsa, ya kuma zauna a keɓe. Yotam ɗan sarki, shi ne ya gudanar da sha’anin fada, ya kuma shugabanci mutanen ƙasar.

2 Sarakuna 15:8-9

A shekara ta talatin da takwas ta mulkin Azariya sarkin Yahuda, Zakariya ɗan Yerobowam ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuma yi mulki wata shida. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda mahaifinsa ya yi. Bai bar aikata zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila suka yi ba.

2 Sarakuna 15:13-14

Shallum ɗan Yabesh ya zama sarki a shekara ta talatin da tara ta mulkin Uzziya sarkin Yahuda, ya kuma yi mulki na wata ɗaya a Samariya. Sa’an nan Menahem ɗan Gadi ya gangara daga Tirza ya haura zuwa Samariya. Ya tasam wa Shallum ɗan Yabesh a Samariya, ya kashe shi, ya kuma gāje shi.

2 Sarakuna 15:17-18

A shekara ta talatin da takwas ta mulkin Azariya sarkin Yahuda, Menahem ɗan Gadi ya zama sarkin Isra’ila, ya yi mulki a Samariya shekara goma. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. A duk tsawon mulkinsa, bai rabu da zunuban da Yerobowam ɗan Nebat ya sa Isra’ila suka aikata ba.

2 Sarakuna 15:23-24

A shekara ta hamsin ta mulkin Azariya sarkin Yahuda, Fekahiya ɗan Menahem ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuma yi mulki shekara biyu. Fekahiya ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, bai rabu da zunuban Yerobowam ɗan Nebat wanda ya sa Isra’ila ya aikata ba.

2 Sarakuna 15:27-28

A shekara ta hamsin da biyu ta mulkin Azariya sarkin Yahuda, Feka ɗan Remaliya ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya yi mulki shekara ashirin. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji. Bai kauce wa zunuban Yerobowam ɗan Nebat, wanda ya sa Isra’ila ta yi ba.

2 Sarakuna 15:32-35

A shekara ta biyu ta mulkin Feka ɗan Remaliya sarkin Isra’ila, Yotam ɗan Uzziya sarkin Yahuda ya fara mulki. Ya zama sarki yana da shekara ashirin da biyar, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Sunan mahaifiyarsa Yerusha, ’yar Zadok. Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji yadda mahaifinsa Uzziya ya yi. Duk da haka, bai kawar da masujadan kan tudu ba; mutane suka ci gaba da yin hadaya da ƙona turare a can. Yotam ya sāke gina Ƙofar Bisa ta haikalin Ubangiji.

2 Sarakuna 16:1-4

A shekara ta goma sha bakwai ta mulkin Feka ɗan Remaliya, Ahaz ɗan Yotam sarkin Yahuda ya fara mulki. Ahaz ya zama sarki yana da shekara ashirin, ya kuma yi mulki shekara goma sha shida a Urushalima ba kamar Dawuda mahaifinsa ba. Ahaz bai yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji Allahnsa ba. Ya yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila har ya miƙa ɗansa hadaya a wuta, yana bin hanyoyin banƙyama na al’ummai da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa. Ya miƙa hadaya, ya kuma ƙona turare a masujadan tudu, da kan tuddai, da kuma a ƙarƙashin kowane babban itace.

2 Sarakuna 17:1-2

A shekara ta goma sha biyu ta mulkin Ahaz sarkin Yahuda, Hosheya ɗan Ela ya zama sarkin Isra’ila a Samariya, ya kuma yi mulki na shekara tara. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, amma ba kamar na sarakunan Isra’ilan da suka riga shi ba.

2 Sarakuna 18:1-6

A shekara ta uku ta mulkin Hosheya ɗan Ela sarkin Isra’ila, Hezekiya ɗan Ahaz sarkin Yahuda ya fara mulki. Yana da shekara ashirin da biyar da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara ashirin da tara a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Abiya ’yar Zakariya. Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji yadda kakansa Dawuda ya yi. Ya kawar da masujadan kan tudu, ya farfasa keɓaɓɓun duwatsu, ya sassare ginshiƙan Ashera. Ya fashe macijin tagullan da Musa ya yi, gama har zuwa lokacin nan Isra’ilawa suna ƙona turare gare shi. (An ba shi suna Nehushtan.) Hezekiya ya dogara ga Ubangiji, Allah na Isra’ila. Ba a yi wani kamar sa ba cikin dukan sarakunan Yahuda; ko kafin shi, ko kuma bayansa. Ya manne wa Ubangiji, bai fasa binsa ba; ya yi biyayya da dokokin da Ubangiji ya ba wa Musa.

2 Sarakuna 18:14-16

Sai Hezekiya sarkin Yahuda ya aika saƙo ga sarkin Assuriya a Lakish cewa, “Na yi laifi, ka janye daga gare ni, zan kuma biya ka duk abin da ake bukata daga gare ni.” Sarkin Assuriya ya karɓi talenti ɗari uku na azurfa, da talenti talatin na zinariya daga hannun Hezekiya sarkin Yahuda. Ya zama kuwa cewa, Hezekiya ya bayar da dukan azurfan da suke a haikalin Ubangiji da kuma a ma’ajin fadan sarki. A wannan lokaci ne Hezekiya sarkin Yahuda ya ɓaɓɓalle zinariyan da aka dalaye ƙofofi da madogaran ƙofofin haikalin Ubangiji, ya ba sarkin Assuriya.

2 Sarakuna 20:13-17

Hezekiya ya karɓi jakadun, ya nuna musu dukan abin da yake a ɗakunan ajiyarsa, azurfa, zinariya, kayan ƙanshi da mai, wurin ajiye makamansa da kuma dukan abin da aka samu a ɗakin ajiyarsa. Babu wani abu a fadansa ko a dukan mulkinsa da Hezekiya bai nuna musu ba. Sai annabi Ishaya ya tafi wurin Sarki Hezekiya ya tambaye shi ya ce, “Me mutanen nan suka ce, kuma daga ina suka fito?” Sai Hezekiya ya ce, “Daga ƙasa mai nisa. Daga Babilon.” Annabin ya yi tambaya, “Me suka gani a fadanka?” Hezekiya ya ce, “Ba abin da yake a ma’ajina da ban nuna musu ba.” Sai Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ka ji kalmar Ubangiji. Lokaci yana zuwa da za a kwashe kome a fadanka da kuma dukan abubuwan da kakanninka suka tara har yă zuwa yau, a kai su Babilon. Ba abin da za a rage, in ji Ubangiji.

2 Sarakuna 21:1-7

Manasse yana da shekara goma sha biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki shekara hamsin da biyar a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hefziba. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, ya bi munanan al’adun al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa. Ya sāke gina masujadan da mahaifinsa Hezekiya ya rurrushe. Ya kuma gina wa Ba’al bagadai. Ya kafa ginshiƙin Ashera kamar yadda Ahab sarkin Isra’ila ya yi. Ya durƙusa wa dukan rundunan taurari ya yi musu sujada. Ya gina bagadai a haikalin Ubangiji, wurin da Ubangiji ya ce, “A Urushalima ne zan sa Sunana.” Cikin filaye biyu na haikalin Ubangiji kuwa, ya gina bagadai na dukan rundunan taurari. Ya miƙa ɗansa hadaya ta ƙonawa, ya yi sihiri da tsubu, ya tuntuɓi masu duba da masu ruhohi. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, ya sa Ubangiji ya yi fushi. Ya ɗauki siffar ginshiƙin Asherar da ya yi, ya sa a haikalin da Ubangiji ya ce wa Dawuda da ɗansa Solomon, “A cikin wannan haikali, da kuma cikin Urushalima inda na zaɓa daga kabilan Isra’ila, zan sa Sunana har abada.

2 Sarakuna 21:16

Ban da haka ma, Manasse ya zub da jinin marasa laifi har ya cika Urushalima daga wannan ɓangare zuwa wancan, ban da zunubin da ya sa Yahuda ta aikata, ta haka suka yi mugunta a gaban Ubangiji.

2 Sarakuna 21:19-22

Amon yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki shekara biyu a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Meshullemet ’yar Haruz; ita mutuniyar Yotba ce. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, yadda Manasse mahaifinsa ya yi. Ya bi duk gurbin mahaifinsa a kome, ya yi sujada ga gumakan da mahaifinsa ya yi wa, ya kuma durƙusa musu. Ya rabu da Ubangiji Allah na kakanninsa, bai kuwa yi tafiya a hanyar Ubangiji ba.

2 Sarakuna 22:1-2

Yosiya yana da shekara takwas sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara talatin da ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Yedida ’yar Adahiya; mutuniyar Bozkat. Ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji ya kuma bi dukan gurbin kakansa Dawuda, bai bauɗe hagu ko dama ba.

2 Sarakuna 22:8-13

Hilkiya babban firist ya ce wa Shafan magatakarda, “Na sami Littafin Doka a haikalin Ubangiji.” Sai ya ba wa Shafan, shi kuma ya karanta. Sa’an nan Shafan ya koma wurin sarki ya ce masa, “Hafsoshinka sun kwashe kuɗin da suke a haikalin Ubangiji, suka ba wa masu aiki da masu lura da haikalin.” Sa’an nan Shafan magatakarda ya ce wa sarki, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Sai Shafan ya karanta shi a gaban sarki. Da sarki ya ji kalmomin Littafin Doka, sai ya kece tufafinsa. Ya ba da waɗannan umarnai ga Hilkiya firist, da Ahikam ɗan Shafan, da Akbor ɗan Mikahiya, da Shafan magatakarda, da kuma Asahiya mai hidimar sarki, ya ce, “Ku je, ku nemi nufin Ubangiji saboda ni da saboda jama’a da kuma saboda dukan Yahuda game da abin da wannan littafi da aka samo ya ƙunsa. Fushin Ubangiji mai girma ne a kanmu domin kakanninmu ba su kiyaye kalmomin littafin nan ba; ba su aikata bisa ga abin da yake a rubuce game da mu ba.”

2 Sarakuna 23:12-14

Ya rushe bagadan da sarakunan Yahuda suka kafa a kan ɗakin sama kusa da ɗakin sama na Ahaz, da kuma bagadai biyu da Manasse ya gina a filaye biyu na haikalin Ubangiji. Ya kawar da su daga can, ya farfashe su, ya zubar da tarkacen a Kwarin Kidron. Sarkin kuma ya lalatar da masujadan kan tuddan da suke gabas da Urushalima, kudu da Tudun Hallaka, waɗanda Solomon sarkin Isra’ila ya gina don Ashtarot, ƙazantacciyar alliyar Sidoniyawa, da Kemosh ƙazantaccen allah na Mowab, da kuma Molek allahn banƙyama na mutanen Ammon. Yosiya ya farfashe keɓaɓɓun duwatsu, ya rurrushe ginshiƙan Asheransu, ya baza ƙasusuwan mutane a can.

2 Sarakuna 23:24-26

Ban da haka, Yosiya ya kawar da masu duba, da masu maita, da allolin gidaje, da gumaka, da duk wani abin banƙyaman da ya gani a Yahuda da Urushalima. Ya yi wannan domin yă cika wa’adodin shari’a yadda suke a littafin da Hilkiya firist ya samu a haikalin Ubangiji. Babu wani sarki kafin Yosiya, ko kuma a bayansa, wanda ya juya ga Ubangiji da dukan zuciyarsa, da dukan ransa, da dukan ƙarfinsa bisa ga shari’ar Musa, kamar yadda ya yi. Duk da haka, Ubangiji bai huce daga zafin fushinsa wanda ya ƙuna game da Yahuda saboda abin da Manasse ya aikata don yă tozarta shi ba.

2 Sarakuna 23:31-32

Yehoyahaz yana da shekara ashirin da uku sa’ad da ya zama sarki. Ya yi mulki na wata uku a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hamutal ’yar Irmiya; mutuniyar Libna. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji, yadda kakanninsa suka yi.

2 Sarakuna 23:36-37

Yehohiyakim yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara goma sha ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Zebuda ’yar Fedahiya, mutuniyar Ruma. Ya kuma aika mugunta a gaban Ubangiji yadda kakanninsa suka yi.

2 Sarakuna 24:8-9

Yehohiyacin yana da shekara goma sha takwas da ya zama sarki, ya kuma yi mulki wata uku a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Nehushta ’yar Elnatan, mutuniyar Urushalima. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda mahaifinsa ya yi.

2 Sarakuna 24:13-16

Yadda Ubangiji ya faɗa, Nebukadnezzar ya kwashe dukan dukiyar haikalin Ubangiji, da ta fadan sarki, ya kuma kwashe dukan kayan zinariyar da Solomon sarkin Isra’ila ya ƙera domin haikalin Ubangiji. Ya kwashi dukan mutanen Urushalima zuwa bauta, ya kwashi dukan fadawa, da mayaƙa, da masu sana’a, da maƙera, yawansu ya kai dubu goma. Ba wanda ya ragu, sai matalautan ƙasar. Nebukadnezzar ya ɗauki Yehohiyacin ya kai bauta a Babilon. Ya kuma kwashe mahaifiyar sarki, da matansa, da fadawansa, da manyan mutanen ƙasar daga Urushalima ya kai Babilon. Sarkin Babilon kuma ya kwashe dukan mayaƙa dubu bakwai, ƙarfafu, shiryayyu don yaƙi, da masu sana’a, da maƙera dubu ɗaya, ya kai Babilon.

2 Sarakuna 24:18-20

Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara goma sha ɗaya a Urushalima. Sunan mahaifiyarsa Hamutal ’yar Irmiya; mutuniyar Libna. Ya aikata mugunta a gaban Ubangiji yadda Yehohiyakim ya yi. Saboda fushin Ubangiji ne dukan waɗannan abubuwa suka faru da Urushalima, da kuma Yahuda, a ƙarshe kuma ya kawar da su daga fuskarsa.

2 Sarakuna 25:6-7

Aka kama shi, aka kai shi gaban sarkin Babilon a Ribla, inda aka yanke masa hukunci. Suka kashe ’ya’yan Zedekiya a gabansa, sa’an nan aka ƙwaƙule idanunsa. Suka daure shi da sarƙar tagulla, suka kai shi Babilon.

1 Tarihi 10:13-14

Shawulu ya mutu domin rashin aminci ga Ubangiji; bai kiyaye maganar Ubangiji ba, ya ma nemi shawarar mace mai duba, bai kuwa nemi nufin Ubangiji ba. Saboda haka Ubangiji ya kashe shi, ya miƙa mulkin ga Dawuda ɗan Yesse.

1 Tarihi 11:1-2

Dukan Isra’ila fa suka taru wurin Dawuda a Hebron suka ce, “Mu jiki da jininka ne. A dā, ko a lokacin da Shawulu yake sarki, ai, kai ne kake shugabantar Isra’ila a yaƙe-yaƙe. Kuma Ubangiji Allahnka ya ce maka, ‘Za ka zama makiyayin mutanena Isra’ila, za ka kuma zama mai mulkinsu.’ ”

1 Tarihi 28:4-5

“Duk da haka Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya zaɓe ni daga dukan iyalina don in zama sarki bisa Isra’ila har abada. Ya zaɓi Yahuda a matsayin shugaba, kuma daga gidan Yahuda ya zaɓi iyalina, daga ’ya’yan mahaifina maza kuwa ya gamsu ya mai da ni sarki bisa dukan Isra’ila. Cikin dukan ’ya’yana maza, Ubangiji kuwa ya ba ni su da yawa, ya zaɓi ɗana Solomon yă zauna a kujerar mulkin Ubangiji a bisa Isra’ila.

1 Tarihi 28:6-8

Ya ce mini, ‘Solomon ɗanka shi ne wanda zai gina gidana da filayen da suke kewaye da shi, gama na zaɓe shi yă zama ɗana, ni kuma zan zama mahaifinsa. Zan kafa mulkinsa har abada in bai kauce ga kiyaye umarnaina da dokokina ba, yadda ake yi a wannan lokaci.’ “Saboda haka yanzu ina umartanku a gaban dukan Isra’ila da na taron jama’ar Ubangiji, da kuma a kunnuwan Allahnmu. Ku yi hankali ku kiyaye dukan umarnan Ubangiji Allahnku don ku mallaki wannan kyakkyawar ƙasa ku kuma bar wa zuriyarku gādo har abada.

1 Tarihi 29:26-28

Dawuda ɗan Yesse ya zama sarki a bisa dukan Isra’ila. Ya yi mulki a bisa Isra’ila shekaru arba’in, shekaru bakwai a Hebron da kuma shekaru talatin da uku a Urushalima. Ya mutu a kyakkyawar tsufa, bayan ya more dogon rai, wadata da girma. Ɗansa Solomon ya gāje shi a matsayin sarki.

2 Tarihi 1:1-4

Solomon ɗan Dawuda ya kafa kansa sosai a bisa masarautarsa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi ya kuma sa ya zama mai girma sosai. Sai Solomon ya yi magana ga dukan Isra’ila, ga shugabannin mayaƙa dubu-dubu da shugabannin mayaƙa ɗari-ɗari, ga alƙalai da kuma ga dukan shugabanni a Isra’ila, kawunan iyalai, Solomon tare da dukan taron suka tafi masujadan kan tudu a Gibeyon, gama Tentin Sujadar Allah yana can, wanda Musa bawan Ubangiji ya yi a hamada. Dawuda ya riga ya haura da akwatin alkawarin Allah daga Kiriyat Yeyarim zuwa inda ya shirya dominsa, domin yă kafa masa tenti a Urushalima.

2 Tarihi 6:12-14

Sa’an nan Solomon ya tsaya a gaban bagaden Ubangiji a gaban dukan taron Isra’ila ya ɗaga hannuwansa sama. Dā ma ya riga ya gina dakalin tagulla, mai tsawo kamu biyar, fāɗi kamu biyar da kuma tsayi kamu uku, ya kuma sa shi a tsakiyar filin waje. Ya tsaya a kan dakalin ya kuma durƙusa a gaban dukan taron Isra’ila ya buɗe hannuwansa sama. Ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, babu Allah kamar ka a sama da kuma ƙasa, kai da kake kiyaye alkawarinka na ƙauna tare da bayinka waɗanda suke cin gaba da zuciya ɗaya a hanyarka.

2 Tarihi 7:1-5

Sa’ad da Solomon ya gama yin addu’a, sai wuta ya sauko daga sama ya cinye hadaya ta ƙonawa da kuma sadakokin, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika haikalin. Firistoci ba su iya shiga haikalin Ubangiji ba domin ɗaukakar Ubangiji ta cika shi. Sa’ad da dukan Isra’ilawa suka ga wutar na saukowa, ɗaukakar Ubangiji kuma tana a bisa haikalin, sai suka durƙusa a dakali da fuskokinsu a ƙasa, suka yi sujada suka kuma yi godiya ga Ubangiji suna cewa, “ Ubangiji mai alheri ne, ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.” Sai sarki da dukan mutanen suka miƙa hadayu a gaban Ubangiji. Sarki Solomon kuwa ya miƙa hadayar bijimai dubu ashirin da biyu da kuma tumaki da awaki dubu ɗari da dubu ashirin. Ta haka sarki da dukan mutane suka keɓe haikalin Allah.

2 Tarihi 7:12-14

sai Ubangiji ya bayyana gare shi a daren ya ce, “Na ji addu’arka na kuma zaɓi wannan wuri don kaina, a matsayin haikali don hadayu. “Sa’ad da na kulle sammai don kada a yi ruwan sama ko na umarci fāri su cinye amfanin ƙasar ko kuwa na aika da annoba a cikin mutanena, in mutanena, waɗanda ake kira da sunana, sun ƙasƙantar da kansu, suka kuma yi addu’a, suka nemi fuskata, suka kuma juye daga mugayen hanyoyinsu, zan ji daga sama in kuma gafarta zunubinsu in kuwa warkar da ƙasarsu.

2 Tarihi 12:13-14

Sarki Rehobowam ya kafa kansa daram a Urushalima, ya kuma ci gaba a matsayin sarki. Yana da shekara arba’in da ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara goma sha bakwai a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga dukan kabilan Isra’ila wanda zai sa Sunansa. Sunan mahaifiyarsa Na’ama ce, ita mutuniyar Ammon ce. Ya aikata mugunta domin bai sa zuciyarsa ga neman Ubangiji ba.

2 Tarihi 13:17

Abiya da mutanensa suka kashe su sosai, har mutum dubu ɗari biyar suka mutu a cikin jarumawan Isra’ila.

2 Tarihi 13:20

Yerobowam bai sāke yin ƙarfi a zamanin Abiya ba. Ubangiji ya buge shi ya kuma mutu.

2 Tarihi 14:2-5

Asa ya yi abin da yake da kyau da kuma daidai a gaban Ubangiji Allahnsa. Ya kawar da baƙin bagade da masujadai bisa tudu, ya farfashe keɓaɓɓun duwatsu, ya kuma sassare ginshiƙan Ashera. Ya umarci Yahuda su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu, su kuma yi biyayya da dokoki da kuma umarnansa. Ya kawar da masujadan kan tudu da bagadan turare a kowane gari a Yahuda, masarautar kuwa ta zauna lafiya a ƙarƙashinsa.

2 Tarihi 15:17

Ko da yake bai kawar da masujadan kan tudu daga Isra’ila ba, zuciyar Asa ta cika da bin Ubangiji dukan kwanakinsa.

2 Tarihi 16:10

Sai Asa ya yi fushi sosai da mai duban saboda wannan; ya yi fushi ƙwarai har ya sa aka jefa shi a kurkuku. A lokaci guda kuma Asa ya fara gwada wa mutane azaba.

2 Tarihi 16:12

A shekara ta talatin da tara ta mulkinsa, Asa ya kamu da wata cuta a ƙafarsa. Ko da yake cutar ta yi tsanani, duk d haka ma a cikin ciwonsa bai nemi taimako daga Ubangiji ba, sai dai daga likitoci.

2 Tarihi 17:3-6

Ubangiji kuwa yana tare da Yehoshafat domin a shekarunsa na farko-farko ya yi tafiya a hanyoyin da kakansa Dawuda ya bi. Bai nemi shawarar Ba’al ba amma ya nemi Allah na kakansa ya kuma bi umarnansa a maimakon ayyukan da Isra’ila ke yi. Ubangiji ya kafa mulkin a ƙarƙashin ikonsa; dukan Yahuda kuwa suka kawo kyautai wa Yehoshafat, ta haka ya yi arziki sosai da kuma girma. Zuciyarsa ta duƙufa ga hanyoyin Ubangiji, bugu da ƙari, ya kawar masujadan kan tudu da ginshiƙan Ashera daga Yahuda.

2 Tarihi 18:18-22

Mikahiya ya ci gaba, “Saboda haka sai ka ji maganar Ubangiji. Na ga Ubangiji yana zama a kan kursiyinsa tare da dukan rundunar sama tsaye a damansa da hagunsa. Ubangiji kuwa ya ce, ‘Wa zai ruɗe Ahab sarki Isra’ila zuwa yaƙi da Ramot Gileyad da kuma zuwa mutuwarsa a can?’ “Wani ya ba da wata shawara, wani kuma wata dabam. A ƙarshe, wani ruhu ya zo gaba, ya tsaya a gaban Ubangiji ya ce, ‘Zan ruɗe shi.’ “ Ubangiji ya yi tambaya, ‘Ta wace hanya?’ “Ya ce, ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawansa.’ “ Ubangiji ya ce, ‘Za ka yi nasara a ruɗinsa. Ka tafi, ka yi haka.’ “To yanzu, Ubangiji ya sa ruhun ruɗu a bakunan waɗannan annabawanka. Ubangiji ya ƙayyade masifa dominka.”

2 Tarihi 18:23-27

Sai Zedekiya ɗan Kena’ana ya haura ya mari Mikahiya a fuska. Ya ce, “Ta wace hanya ce ruhun Ubangiji ya fita daga gare ni ya zo ya yi magana da kai?” Mikahiya ya amsa ya ce, “Za ka gane a ranar da ka je ka ɓuya a can cikin ɗaki.” Sa’an nan sarkin Isra’ila ya umarta, “Ɗauki Mikahiya ku aika da shi zuwa ga Amon mai mulkin birni da kuma ga Yowash ɗan sarki, ku ce ga abin da sarki ya ce, ‘Ku jefa wannan mutum a kurkuku kada kuma ku ba shi wani abu sai dai burodi da ruwa har sai na dawo lafiya.’ ” Mikahiya ya furta ya ce, “Idan har ka dawo lafiya, to, Ubangiji bai yi magana ta wurina ba.” Ya kuma ƙara da cewa, “Dukanku mutane, ku lura da maganata!”

2 Tarihi 18:33-34

Amma wani ya harba kibiya haka kawai, sai kibiyar ta sami sarki Ahab na Isra’ila a kafaɗa tsakanin rigar yaƙinsa na ƙarfe da ƙarfen ƙirjinsa. Sai sarki ya ce wa mai tuƙan keken yaƙi, “Juya ka fitar da ni daga wurin yaƙin. An ji mini rauni.” Duk yini yaƙi ya yi ta cin gaba, sarkin Isra’ila kuwa ya jingina kansa a cikin keken yaƙinsa yana duban Arameyawa har yamma. Sa’an nan a fāɗuwar rana sai ya mutu.

2 Tarihi 20:35-37

Daga baya, Yehoshafat sarkin Yahuda ya haɗa kai da Ahaziya sarkin Isra’ila, wanda yake da laifin mugunta. Ya yarda da shi su gina jiragen ruwan kasuwanci. Bayan aka gina waɗannan a Eziyon Geber, Eliyezer ɗan Dodabahu na Maresha ya yi annabci a kan Yehoshafat cewa, “Domin ka haɗa kai da Ahaziya, Ubangiji zai hallaka abin da ka yi.” Jiragen ruwan kuwa suka farfashe, ba a kuwa iya sa su je kasuwanci ba.

2 Tarihi 21:5-6

Yehoram yana da shekara talatin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara takwas. Ya yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila, kamar yadda gidan Ahab ta yi, gama ya auri ’yar Ahab. Ya aikata mugayen ayyuka a idon Ubangiji.

2 Tarihi 21:16-19

Ubangiji ya sa Filistiyawa da Larabawa waɗanda suke zama kusa da Kushawa su yi gāba da Yehoram Suka yaƙi Yahuda, suka kai masa hari, suka kwashe dukan abubuwa masu kyau da suka samu a fadan sarki, tare da ’ya’yansa maza da kuma matansa. Ba wanda aka bari, sai dai Ahaziya autansa. Bayan dukan wannan, sai Ubangiji ya sa wa Yehoram cuta marar warkarwa ta ciki. Cikin lokaci, a ƙarshen shekara ta biyu, sai hanjin cikinsa suka fito saboda cutar, ya kuma mutu cikin tsananin zafi. Mutanensa suka hura wuta don girmama shi, kamar yadda suka yi wa kakanninsa.

2 Tarihi 22:2-4

Ahaziya yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara guda. Sunan mahaifiyarsa Ataliya ce, jikanyar Omri. Shi ma ya yi tafiya a hanyoyin gidan Ahab, gama mahaifiyarsa ta ƙarfafa shi yă yi abin da ba shi da kyau. Ya aikata mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, yadda gidan Ahab ta yi, gama bayan mutuwar mahaifinsa, sai gidan Ahab ta zama masu ba shi shawara, shawarar da ta kai shi ga lalacewa.

2 Tarihi 22:9

Ya kuma sa aka nemi Ahaziya. Aka kamo shi sa’ad da ya ɓuya a Samariya, suka kawo shi wurin Yehu, suka kashe shi, suka binne shi, gama sun ce, “Shi jikan Yehoshafat ne, wanda ya nemi Ubangiji da dukan zuciyarsa.” Ta haka babu wani a gidan Ahaziya da yake da ƙarfin cin gaba da mulkin.

2 Tarihi 23:12-13

Sa’ad da Ataliya ta ji surutun mutane suna gudu suna yabon sarki, sai ta tafi wurinsu a haikalin Ubangiji. Ta duba, a can kuwa ga sarki, tsaye kusa da ginshiƙinsa a mashigi. Manyan sojoji da masu bushe-bushe suna kusa da sarki, dukan mutanen ƙasar kuwa suna farin ciki suna busa ƙahoni, mawaƙa kuma da kayan kiɗi suna bi da yabo. Sai Ataliya ta yage rigunanta ta yi ihu tana cewa, “Cin amanar ƙasa! Cin amanar ƙasa!”

2 Tarihi 23:16-18

Sa’an nan Yehohiyada ya yi alkawari cewa shi da mutane da kuma sarki za su zama mutanen Ubangiji. Dukan mutane suka tafi haikalin Ba’al suka rurrushe shi. Suka farfashe bagadan da gumakan, suka kuma kashe Mattan firist na Ba’al a gaban bagadan. Sa’an nan Yehohiyada ya sa aikin lura da haikalin Ubangiji a hannuwan firistoci, waɗanda suke Lawiyawan da Dawuda ya ba su aikin haikali don su miƙa hadayun ƙonawa na Ubangiji kamar yadda yake a rubuce a Dokar Musa, da farin ciki da kuma rerawa, kamar yadda Dawuda ya umarta.

2 Tarihi 24:1-2

Yowash yana da shekara goma sha bakwai sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi sarauta a Urushalima shekara arba’in. Sunan mahaifiyarsa Zibiya ce; ita daga Beyersheba. Yowash ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji duka shekarun Yehohiyada firist.

2 Tarihi 24:20-22

Sai Ruhun Allah ya sauko a kan Zakariya ɗan Yehohiyada firist. Ya tsaya a gaban mutane ya ce, “Ga abin da Allah ya ce, ‘Me ya sa ba ku yi biyayya da umarnan Ubangiji ba? Ba za ku yi nasara ba. Domin kun yashe Ubangiji, shi ma ya yashe ku.’ ” Amma suka yi masa maƙarƙashiya, kuma ta wurin umarnin sarki suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu a filin haikalin Ubangiji. Sarki Yowash bai tuna da alherin da Yehohiyada mahaifin Zakariya ya nuna masa ba, sai ya kashe ɗansa, wanda ya ce yayinda yake mutuwa, “Bari Ubangiji yă dubi wannan yă kuma sāka maka.”

2 Tarihi 25:1-2

Amaziya yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara ashirin da tara. Sunan mahaifiyarsa Yehoyaddin ce; ita daga Urushalima ne. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, amma ba da dukan zuciyarsa ba.

2 Tarihi 25:27

Sa’ad da Amaziya ya bar bin Ubangiji, aka shirya masa maƙarƙashiya a Urushalima, sai ya gudu zuwa Lakish, amma suka aiki mutane suka bi shi zuwa Lakish, a can suka kashe shi.

2 Tarihi 26:3-5

Uzziya yana da shekara goma sha shida sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyu. Sunan mahaifiyarsa Yekoliya ce; ita daga Urushalima ce. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar dai yadda mahaifinsa Amaziya ya yi. Ya nemi Allah a kwanakin Zakariya, wanda ya koyar da shi a tsoron Allah. Muddin ya nemi Ubangiji, Allah ya ba shi nasara.

2 Tarihi 26:16-21

Amma bayan Uzziya ya zama mai iko, sai ɗaga kai ya kai shi ga fāɗuwa. Bai yi aminci ga Ubangiji Allahnsa ba, ya kuma shiga haikalin Ubangiji don yă ƙone turare a bagaden turare. Azariya firist tare da waɗansu firistoci tamanin na Ubangiji masu ƙarfin hali suka bi shi ciki. Suka kalubalance shi suka ce, “Ba daidai ba ne, Uzziya, ka ƙone turare ga Ubangiji. Wannan aikin firistoci zuriyar Haruna ne, waɗanda aka tsarkake don ƙone turare. Ka bar wuri mai tsarki, gama ka kasance marar aminci; kuma Ubangiji Allah ba zai girmama ka ba.” Uzziya wanda yake da farantin wuta a hannunsa a shirye don ƙone turare, ya husata. Yayinda yake fushi da firistocin a gabansu a gaban bagaden turare a haikalin Ubangiji, sai kuturta ta faso a goshinsa. Sa’ad da Azariya babban firist da dukan sauran firistoci suka dube shi, sai suka ga cewa yana da kuturta a goshinsa, saboda haka suka gaggauta tunkuɗa shi waje nan da nan. Tabbatacce, shi kansa ma ya yi marmari yă bar wurin domin Ubangiji ya buge shi. Sarki Uzziya ya kasance da kuturta har ranar mutuwarsa. Ya zauna a gidan da aka ware, da kuturci, aka kuma ware shi daga haikalin Ubangiji. Yotam ɗansa ya lura da fadan ya kuma yi mulkin mutanen ƙasar.

2 Tarihi 27:1-2

Yotam yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Sunan mahaifiyarsa Yerusha, ’yar Zadok. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar yadda mahaifinsa Uzziya ya yi, sai dai bai kutsa cikin haikalin Ubangiji kamar mahaifinsa ba. Mutane kuwa, suka ci gaba da aikata ayyukan lalaci.

2 Tarihi 28:1-3

Ahaz yana da shekara ashirin sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Ba kamar Dawuda kakansa ba, bai yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji ba. Ya yi tafiya a hanyoyin sarakunan Isra’ila ya kuma yi zubin gumaka domin a bauta wa Ba’al. Ya ƙone hadayu a Kwarin Ben Hinnom, ya kuma miƙa ’ya’yansa maza a cikin wuta, yana bin hanyoyi banƙyama na al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa.

2 Tarihi 28:22-25

Cikin lokacin wahalarsa Sarki Ahaz ya ƙara zama marar aminci ga Ubangiji. Ya miƙa hadayu ga allolin Damaskus, waɗanda suka ci shi a yaƙi; gama ya yi tunani, “Da yake allolin sarakunan Aram sun taimake su, zan miƙa hadayu domin su taimake ni.” Amma suka zama sanadin fāɗuwarsa da kuma fāɗuwar dukan Isra’ila. Ahaz ya tattara kayayyaki daga haikalin Allah ya kwashe su. Ya kulle ƙofofin haikalin Ubangiji ya kakkafa bagadai a kowace kusurwa a titin Urushalima. A kowane gari a Yahuda, ya gina masujadan kan tudu don ƙone hadayu ga waɗansu alloli, ya kuma tsokane Ubangiji Allah na kakanninsa ya yi fushi.

2 Tarihi 29:1-3

Hezekiya yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara ashirin da tara. Sunan mahaifiyarsa Abiya, ’yar Zakariya. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar dai yadda kakansa Dawuda ya yi. A wata na farkon a farkon shekarar mulkinsa, ya buɗe ƙofofin haikalin Ubangiji ya gyara su.

2 Tarihi 32:20-23

Sarki Hezekiya da annabi Ishaya ɗan Amoz suka yi kuka cikin addu’a ga sama game da wannan. Sai Ubangiji ya aiki mala’ika, wanda ya karkashe dukan jarumawa da shugabanni da kuma hafsoshi a sansanin sarkin Assuriyawa. Saboda haka sai sarkin Assuriya ya janye zuwa ƙasarsa da kunya. Da ya shiga haikalin Allahnsa, sai waɗansu a cikin ’ya’yansa maza suka yanka shi da takobi. Ta haka Ubangiji ya ceci Hezekiya da mutanen Urushalima daga hannun Sennakerib sarkin Assuriya da kuma daga hannun dukan sauran. Ya magance su a kowane gefe. Yawanci mutane suka kawo hadayun ƙonawa zuwa Urushalima wa Ubangiji da kuma kyautai masu daraja wa Hezekiya sarkin Yahuda. Daga lokacin zuwa gaba dukan ƙasashe suka girmama shi.

2 Tarihi 32:31

Amma da masu mulkin Babilon suka aika da jakadu su tambaye shi game alamar da ta faru a ƙasar, Allah ya rabu da shi don yă gwada shi don yă kuma san kome da yake cikin zuciyarsa.

2 Tarihi 33:1-9

Manasse yana da shekara ashirin sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara hamsin da biyar. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji, yana bin ayyukan banƙyama na al’umman da Ubangiji ya kora a gaban Isra’ilawa. Ya sāke gina masujadan kan tudun da mahaifinsa Hezekiya ya rurrushe; ya tā da bagadan Ba’al, ya kuma gina ginshiƙan Ashera. Ya rusuna wa dukan rundunonin taurari, ya kuma yi musu sujada. Ya gina bagadai cikin haikalin Ubangiji, waɗanda Ubangiji ya ce, “Sunana zai kasance cikin Urushalima har abada.” Cikin filayen haikalin Ubangiji, ya gina bagadai ga dukan rundunonin taurari. Ya miƙa ’ya’yansa maza hadaya a wuta cikin Kwarin Ben Hinnom, ya yi bokanci, ya yi duba, ya kuma yi maitanci, ya nemi shawarar mabiya da masu ruhohi. Ya yi abin da yake mugu ƙwarai a gaban Ubangiji, yana tsokanarsa yă yi fushi. Ya ɗauki siffar da aka sassaƙa wadda ya yi, ya sa ta a cikin haikalin Allah, wanda Allah ya ce wa Dawuda da kuma ɗansa Solomon, “Cikin wannan haikali da kuma cikin Urushalima, wanda na zaɓa daga cikin kabilan Isra’ila, zan sa Sunana har abada. Ba zan ƙara bari ƙafafun Isra’ilawa su bar ƙasar da na ba wa kakanninku ba, in dai suka yi hankali ga yin kome da na umarce su game da duka dokoki, ƙa’idodi da kuma farillai da na bayar ta wurin Musa.” Amma Manasse ya sa Yahuda da mutanen Urushalima suka kauce, har suka aikata mugunta fiye da al’umman da Ubangiji ya hallaka a gaban Isra’ilawa.

2 Tarihi 33:10-13

Ubangiji ya yi magana da Manasse da mutanensa, amma ba su kula ba. Saboda haka Ubangiji ya kawo manyan hafsoshin mayaƙan sarkin Assuriya a kansu, waɗanda suka ɗauki Manasse a matsayi ɗan kurkuku, suka sa ƙugiya a hancinsa, suka daure shi da sarƙoƙin tagulla suka kuma kai shi Babilon. Cikin wahalarsa ya nemi tagomashin Ubangiji Allahnsa ya kuma ƙasƙantar da kansa sosai a gaban Allah na kakanninsa. Da ya yi addu’a gare shi, sai Ubangiji ya taɓu da tubansa, ya kuma saurari roƙonsa; saboda haka ya dawo da shi Urushalima da kuma zuwa mulkinsa. Sa’an nan Manasse ya san cewa Ubangiji shi ne Allah.

2 Tarihi 33:15-17

Ya fid da baƙin alloli, ya kuma fid da siffofi daga haikalin Ubangiji, haka ma dukan bagadan da ya gina a kan tudun haikali da kuma cikin Urushalima, ya zubar da su a bayan birni. Sa’an nan ya gyara bagaden Ubangiji ya kuma miƙa hadayun salama da kuma hadayun godiya a bagaden, ya kuma faɗa wa Yahuda su bauta wa Ubangiji, Allah na Isra’ila. Mutane dai suka ci gaba da miƙa hadayu a masujadai kan tudu, amma wa Ubangiji Allahnsu kaɗai.

2 Tarihi 33:21-23

Amon yana da shekara ashirin da biyu sa’ad da ya zama sarki, ya yi mulki a Urushalima shekara biyu. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji kamar yadda mahaifinsa Manasse ya yi. Amon ya bauta ya kuma miƙa hadayu ga dukan gumakan da Manasse ya yi. Amma ba kamar mahaifinsa Manasse ba, bai ƙasƙantar da kansa a gaban Ubangiji ba; Amon ya ƙara laifinsa.

2 Tarihi 34:1-4

Yosiya yana da shekara goma sha takwas sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara talatin da ɗaya. Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji ya kuma yi tafiya a hanyoyin kakansa Dawuda, ba tare da juye dama ko hagu ba. A shekara ta takwas ta mulkinsa, yayinda yake matashi, sai ya fara neman Allah na kakansa Dawuda. A shekara ta goma sha biyunsa ya fara tsabtacce Yahuda da Urushalima daga masujadan kan tudu, ginshiƙan Ashera, sassaƙaƙƙun gumaka da kuma siffofin da aka yi zubi. A ƙarƙashin umarninsa aka rurrushe bagadan Ba’al, ya kuma tumɓuke bagadan ƙona turare waɗanda suke a bisansu, ya farfashe ginshiƙan Ashera da kuma sassaƙaƙƙun siffofi. Ya ragargaza waɗannan kucu-kucu, ya barbaɗa su a kan kaburburan waɗanda suka miƙa musu hadayu.

2 Tarihi 34:15-21

Hilkiya ya ce wa Shafan magatakarda, “Na sami Littafin Doka a cikin haikalin Ubangiji.” Sai ya ba wa Shafan. Sa’an nan Shafan ya ɗauki littafin zuwa wurin sarki, ya faɗa masa, “Manyan ma’aikatanka suna yin kome da aka sa su. Mun ɗauke kuɗin da an ajiye a haikalin Ubangiji muka ba wa masu aiki da waɗanda suke lura da su.” Sa’an nan Shafan magatakarda ya sanar da sarki ya ce, “Hilkiya firist ya ba ni wani littafi.” Sai Shafan ya karanta daga cikinsa a gaban sarki. Da sarki ya ji kalmomin Doka, sai ya yage rigunansa. Ya ba da waɗannan umarnai ga Hilkiya, Ahikam ɗan Shafan, Abdon ɗan Mika, Shafan magatakarda da kuma Asahiya mai hidimar sarki. Ya ce, “Ku tafi ku nemi nufin Ubangiji saboda ni da kuma saboda raguwa a Isra’ila da Yahuda game da abin da aka rubuta a wannan littafin da aka samu. Fushin Ubangiji mai girma ne da aka zuba a kanmu domin kakanninmu ba su kiyaye maganar Ubangiji ba; ba su aikata bisa ga dukan abin da yake a rubuce a wannan littafi ba.”

2 Tarihi 34:24-27

‘Ga abin da Ubangiji ya ce zai kawo masifa a wannan wuri da mutanensa, dukan la’anar da aka rubuta a cikin littafin da aka karanta a gaban sarkin Yahuda. Domin sun yashe ni suka kuma ƙone turare wa waɗansu alloli, suka tsokane ni in yi fushi ta wurin dukan abin da hannuwansu suka yi, fushina zai zuba a kan wannan wuri, ba kuma za a kwantar da shi ba.’ Ku faɗa wa sarkin Yahuda, wanda ya aike ku ku nemi nufin Ubangiji, ‘Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yake cewa game da kalmomin da ka ji. Domin zuciyarka mai tuba ce, ka kuma ƙasƙantar da kanka a gaban Allah sa’ad da ka ji abin da ya yi magana a kan wannan wuri da mutanensa, domin kuma ka ƙasƙantar da kanka a gabana, ka yage rigunanka ka kuma yi kuka a gabana, na ji ka, in ji Ubangiji.

2 Tarihi 34:31-33

Sai sarkin ya miƙe tsaye a inda yake, ya sabunta alkawari a gaban Ubangiji, don yă bi Ubangiji yă kiyaye umarnansa, ƙa’idodinsa da kuma farillansa da dukan zuciyarsa da kuma dukan ransa, ya kuma yi biyayya da kalmomin alkawarin da aka rubuta a cikin wannan littafi. Sa’an nan ya sa kowa a Urushalima da Benyamin ya yi alkawari ga wannan; mutanen Urushalima suka aikata wannan bisa ga alkawarin Allah, Allah na kakanninsu. Yosiya ya fitar da dukan gumakan banƙyama daga dukan yankunan Isra’ilawa, ya kuma sa dukan waɗanda suke a Isra’ila su bauta wa Ubangiji Allahnsu. Muddin ransa, ba su fasa bin Ubangiji Allah na kakanninsu ba.

2 Tarihi 36:2

Yehoyahaz yana da shekara ashirin da uku sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima wata uku.

2 Tarihi 36:5

Yehohiyakim yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnsa.

2 Tarihi 36:9

Yehohiyacin yana da shekara goma sha takwas sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima wata uku da kwana goma. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji.

2 Tarihi 36:10

Da bazara, Sarki Nebukadnezzar ya aika a kawo Yehohiyacin, aka kuma kawo shi Babilon, tare da kayayyaki masu daraja daga haikalin Ubangiji, sai Sarki Nebukadnezzar ya naɗa kawunsa Zedekiya, sarki a bisa Yahuda da Urushalima.

2 Tarihi 36:11-14

Zedekiya yana da shekara ashirin da ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha ɗaya. Ya yi abin da yake mugu a gaban Ubangiji Allahnsa kuma bai ƙasƙantar da kansa a gaban Irmiya annabi, wanda ya yi magana kalmar Ubangiji ba. Ya tayar wa Sarki Nebukadnezzar, wanda ya sa ya yi rantsuwa da sunan Allah. Ya zama mai kunnen ƙashi da kuma taurin zuciya, bai kuwa juye ga Ubangiji, Allah na Isra’ila ba. Bugu da ƙari, dukan shugabannin firistoci da mutane suka ƙara zama marasa aminci, suna bin dukan abubuwan banƙyama na al’ummai, suka ƙazantar da haikalin Ubangiji, wanda ya tsarkake a Urushalima.

2 Tarihi 36:16-21

Amma suka yi wa ’yan saƙon Allah ba’a, suka rena maganarsa, suka yi wa annabawansa dariyar reni, har sai da fushin Ubangiji ya tasar a kan mutanensa babu makawa. Ya bashe su ga sarkin Babiloniyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a wuri mai tsarki, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka ga Nebukadnezzar. Nebukadnezzar ya kwashe dukan kayayyaki daga haikalin Allah, babba da ƙarami, da ma’ajin haikalin Ubangiji da kuma ma’ajin sarki da na fadawansa zuwa Babilon. Suka cinna wa haikalin Allah wuta, suka rurrushe katangar Urushalima; suka ƙone dukan fada, suka kuma lalace kome mai amfani da yake can. Waɗanda ba a kashe ba kuwa Nebukadnezzar ya kwashe su, ya kai Babilon, suka zama bayinsa da na ’ya’yansa maza har zuwa kahuwar mulkin Farisa. Ƙasar ta more hutun Asabbacinta; a dukan lokacin zamanta kango ta huta, har sai da shekaru saba’in nan suka cika bisa ga maganar Ubangiji da Irmiya ya faɗi.

2 Tarihi 36:22-23

Don a cika maganar da Ubangiji ya yi ta wurin Irmiya, a shekara farko ta Sairus sarkin Farisa, sai Ubangiji ya motsa zuciyar Sairus na Farisa don yă yi shela a dukan masarautarsa, ya kuma sa shi a rubuce cewa, “Ga abin da Sairus sarkin Farisa ya ce, “ ‘ Ubangiji Allah na sama, ya ba ni dukan mulkokin duniya, ya kuma naɗa ni in gina masa haikali a Urushalima a Yahuda. Duk wani na mutanensa a cikinku, bari yă haura yă tafi, bari kuma Ubangiji Allahnsa yă kasance tare da shi.’ ”

Ezra 1:1-3

A shekara ta farko ta mulkin sarkin Farisa, wato, sarki Sairus, domin a cika maganar Ubangiji da aka yi ta bakin Irmiya, sai Ubangiji ya taɓa zuciyar Sairus sarkin Farisa ya yi shela a duk fāɗin ƙasarsa, ya kuma rubuta cewa, “Ga abin da Sairus sarkin Farisa yake shela, “ ‘ Ubangiji Allah na sama ya ba ni iko in yi mulkin duniya duka, ya kuma zaɓe ni in gina masa haikali a Urushalima cikin Yahuda. Duk wanda yake nasa a cikinku bari Allahnsa yă kasance tare da shi, bari yă tafi Urushalima cikin Yahuda yă gina haikalin Ubangiji, Allah na Isra’ila, Allah wanda yake a Urushalima.

Ezra 10:14

Bari shugabanninmu su yi wani abu a madadin mutane duka, sa’an nan sai duk wanda ya san ya auri baƙuwar mace a garuruwanmu, sai yă zo nan a lokacin da aka shirya tare da dattawa da alƙalan kowane gari, har sai Allah ya huce fushinsa mai zafi da yake kanmu.”

Esta 3:1-4

Bayan waɗannan al’amura, sai Sarki Zerzes ya girmama Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, ya ɗaukaka shi, ya kuma ba shi matsayi mafi girma fiye da na dukan sauran hakiman. Dukan masu hidimar da suke a ƙofar sarki suka riƙa durƙusa suna ba wa Haman girma, gama sarki ya ba da umarni a yi masa haka. Amma Mordekai bai durƙusa ya ba shi girma ba. Sa’an nan masu hidimar da suke a ƙofar sarki suka tambaye Mordekai, “Me ya sa ba ka yin biyayya da umarnin sarki?” Kowace rana suna masa magana, amma ya ƙi yă yi. Saboda haka, suka faɗa wa Haman game da wannan don su ga ko za a jure da halin Mordekai, gama ya faɗa musu cewa shi mutumin Yahuda ne.

Esta 3:12-15

Sa’an nan aka kira magatakardun sarki a rana ta goma sha uku na wata na fari. Suka rubuta dukan umarnin Haman a irin rubutun kowane lardi, kuma cikin harshen kowane mutane, zuwa ga shugabannin mahukuntai na sarki, da gwamnonin larduna dabam-dabam, da kuma hakiman mutane dabam-dabam. Aka rubuta waɗannan a sunan Sarki Zerzes da kansa, aka kuma hatimce da zobensa. Aka aika ’yan-kada-tă-kwana da saƙoni zuwa dukan lardunan sarki da umarni a hallaka, a karkashe, a kuma kawar da dukan Yahudawa, manya da ƙanana, mata da yara, a kuma washe kayayyakinsu. Za a ba da kofin rubutun a matsayin doka a kowane lardi, a kuma sanar da mutanen kowace al’umma, domin su zauna da shiri don wannan rana. Bisa ga umarnin sarki, sai ’yan-kada-tă-kwana, suka tafi da sauri. Aka ba da umarni a mazaunin masarauta da yake a Shusha. Sai Sarki da Haman suka zauna don su sha, amma birnin Shusha ya ruɗe.

Esta 5:1-3

A rana ta uku, Esta ta sanya rigunanta na sarauta, ta tafi ta tsaya a harabar fada, a gaban zaure sarki. Sarki yana zaune a kan gadon sarautarsa a zauren, yana fuskantar ƙofar shiga. Sa’ad da ya ga Sarauniya Esta tsaye a harabar, sai ya ji daɗin ganinta, ya miƙa mata sandan sarauta na zinariya da take hannunsa. Sai Esta ta matsa kusa ta taɓa kan sandan. Sai sarki ya ce mata, “Me kike so, Sarauniya Esta? Mene ne roƙonki? Kai, ko rabin masarautata ce, za a ba ki.”

Ayuba 9:24

Lokacin da ƙasa ta faɗa a hannun mugaye, yakan rufe idanun masu shari’a. In ba shi ba wa zai yi wannan?

Ayuba 34:17

Maƙiyin gaskiya zai iya yin mulki? Za ka iya ba mai gaskiya, Maɗaukaki laifi?

Ayuba 34:18

Ba shi ne ya ce wa sarakuna, ‘Ba ku da amfani ba,’ ya ce wa manya ‘Ku mugaye ne,’

Zabura 2:1-4

Me ya sa ƙasashe suke haɗa baki mutane kuma suke ƙulla shawarwarin banza? Sarakunan duniya sun ɗauki matsayi masu mulki sun taru gaba ɗaya suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa. Suna cewa, “Bari mu tsittsinke sarƙoƙinsu, mu kuma ’yantar da kamammu daga kangin bautar Allah.” Mai zama a kursiyi a sama yana dariya; Ubangiji yana musu ba’a.

Zabura 2:6-11

“Na kafa Sarkina a kan kursiyi a kan Sihiyona, dutsena mai tsarki.” Sarki ya yi shelar umarnin Ubangiji. Ubangiji ya ce mini, “Kai Ɗana ne; yau na zama Mahaifinka. Ka tambaye ni zan kuwa sa al’ummai su zama gādonka, iyakokin duniya su zama mallakarka. Za ka yi mulkinsu da sandan ƙarfe; za ka farfashe su kucu-kucu kamar tukunyar laka.” Saboda haka, ku sarakuna, ku yi wayo; ku shiga hankalinku, ku masu mulkin duniya. Ku bauta wa Ubangiji da tsoro ku kuma yi farin ciki kuna rawar jiki.

Zabura 9:17-20

Mugaye za su koma kabari, dukan al’umman da suka manta da Allah. Amma har abada ba za a manta da mai bukata ba, ba kuwa sa zuciyar mai wahala zai taɓa hallaka. Ka tashi, ya Ubangiji, kada ka bar wani yă yi nasara; bari a hukunta al’ummai a gabanka. Ka buge su da rawar jiki, ya Ubangiji; bari al’ummai su sani su mutane ne kurum. Sela

Zabura 10:16

Ubangiji Sarkin har abada abadin ne; al’ummai za su hallaka daga ƙasarsa.

Zabura 11:5

Ubangiji yana bincike adalai, amma ransa yana ƙi mugaye da masu son rikici.

Zabura 22:27-28

Dukan iyakokin duniya za su tuna su kuma juya ga Ubangiji, kuma dukan iyalan al’ummai za su rusuna a gabansa, gama mulki na Ubangiji ne kuma yana mulki a bisa al’ummai.

Zabura 24:10

Wane ne shi, wannan Sarkin ɗaukaka? Ubangiji Maɗaukaki, shi ne Sarkin ɗaukaka. Sela

Zabura 33:10-12

Ubangiji yakan soke shirye-shiryen al’ummai; yakan wofintar da manufofin mutane. Amma shirye-shiryen Ubangiji kan tsaya daram har abada, manufofin zuciyarsa kuwa har dukan zamanai. Mai farin ciki ce al’ummar da Allah ne Ubangijinta, mutanen da ya zaɓa don gādonsa.

Zabura 47:2-8

Ubangiji Mafi Ɗaukaka mai banmamaki ne, Sarki ne mai girma a bisa dukan duniya! Ya rinjayi al’ummai a ƙarƙashinmu, mutane kuma a ƙarƙashin ƙafafunmu. Ya zaɓar mana gādonmu, abar taƙamar Yaƙub, wanda yake ƙauna. Sela Allah ya haura a cikin sowa ta farin ciki, Ubangiji ya haura a cikin ƙarar ƙahoni. Ku rera yabai ga Allah, ku rera yabai; ku rera yabai ga Sarkinmu, ku rera yabai. Gama Allah shi ne Sarkin dukan duniya; ku rera zabura ta yabo gare shi. Allah yana mulki a bisa al’ummai; Allah yana zama a kan kursiyinsa mai tsarki.

Zabura 95:3

Gama Ubangiji Allah mai girma ne, babban Sarki a bisa dukan alloli.

Zabura 98:6

tare da bushe-bushe da karar ƙahon rago, ku yi sowa don farin ciki a gaban Ubangiji, Sarki.

Zabura 102:15

Al’ummai za su ji tsoron sunan Ubangiji, dukan sarakunan duniya za su girmama ɗaukakarka.

Karin Magana 8:15-16

Ta wurina sarakuna suke mulki masu mulki kuma suke yin dokokin da suke da adalci; ta wurina sarakuna suke mulki, da kuma dukan manyan mutanen da suke mulkin duniya.

Karin Magana 14:34-35

Adalci yakan ɗaukaka al’umma, amma zunubi kan kawo kunya ga kowane mutane. Sarki yakan yi murna a kan bawa mai hikima, amma bawa marar kunya kan jawo fushinsa.

Karin Magana 16:10-15

Leɓunan sarki kan yi magana kamar ta wurin ikon Allah, kuma bai kamata bakinsa ya yi kuskure a yanke shari’a ba. Ma’aunai da magwajin gaskiya daga Ubangiji ne; dukan ma’aunai da suke cikin jaka yinsa ne. Sarakuna suna ƙyamar abin da ba shi da kyau, gama an kafa kujerar sarauta ta wurin adalci ne. Sarakuna sukan ji daɗi leɓuna masu yin gaskiya; sukan darjanta mutumin da yake faɗin gaskiya. Fushin sarki ɗan saƙon mutuwa ne, amma mai hikima yakan faranta masa rai. Sa’ad da fuskar sarki ta haska, yana nufin rai ke nan; tagomashinsa yana kamar girgijen ruwa a bazara.

Karin Magana 19:10-12

Bai dace da wawa ya yi rayuwa cikin jin daɗi ba, haka ya fi muni bawa ya yi mulki a kan sarki! Hikimar mutum kan ba shi haƙuri; ɗaukakarsa ce ya ƙyale laifi. Fushin sarki yana kama da rurin zaki, amma tagomashinsa yana kama da raba a kan ciyawa.

Karin Magana 20:2

Fushin sarki yana kama da rurin zaki; duk wanda ya sa shi fushi zai rasa ransa.

Karin Magana 20:8

Sa’ad da sarki ya zauna kan kujerarsa don yă yi shari’a, yakan ga dukan mugunta da idanunsa.

Karin Magana 21:1

A hannun Ubangiji zuciyar sarki kamar ruwan rafi ne wanda yake bi da shi duk inda ya so.

Karin Magana 24:21-22

Ka ji tsoron Ubangiji da kuma sarki, ɗana, kuma kada ka haɗa kai da masu tayarwa, gama za a tura waɗannan biyu zuwa hallaka nan da nan, kuma wa ya sani irin bala’in da za su iya kawowa?

Karin Magana 25:2-7

Ɗaukakar Allah ce a ɓoye batun; a bayyana batun kuwa ɗaukakar sarakuna ne. Kamar yadda sammai suna can bisa duniya kuma tana da zurfi, haka zukatan sarakuna suka wuce a bincika. Ka tace azurfa sai kayan su fito don maƙerin azurfa; ka cire mugaye daga gaban sarki, kursiyinsa kuwa zai kahu ta wurin adalci. Kada ka ɗaukaka kanka a gaban sarki, kada kuma ka nemi wa kanka wuri a cikin manyan mutane; gara ya ce maka, “Ka hauro nan,” da a ƙasƙantar da kai a gaban wani mai makami. Abin da ka gani da idanunka

Karin Magana 28:15-16

Kamar rurin zaki ko sanɗar beyar haka mugun mutum mai mulki a kan mutane marasa ƙarfi yake. Mugu mai mulki ba shi da azanci, amma duk wanda yake ƙin ƙazamar riba yakan yi tsawon rai.

Karin Magana 29:2-4

Sa’ad da masu adalci suke cin nasara, mutane kan yi farin ciki sa’ad da mugaye suke mulki, mutane kan yi nishi. Duk mai ƙaunar hikima kan kawo wa mahaifinsa farin ciki, amma wanda yake ma’amala da karuwai kan lalatar da dukiyarsa. Ta wurin yin adalci sarki kan sa ƙasa tă yi ƙarƙo amma duk mai haɗama don cin hanci kan rushe ƙasar.

Karin Magana 29:12-14

In mai mulki yana sauraran ƙarairayi, dukan ma’aikatansa za su zama mugaye. Matalauci da azzalumi suna da wannan abu ɗaya. Ubangiji ne yake ba dukansu gani. In sarki yana hukunta talakawa da adalci kursiyinsa kullum zai kasance lafiya.

Karin Magana 31:4-5

“Ba na sarakuna ba ne, ya Lemuwel, ba na sarakuna ba ne su sha ruwan inabi, ba na masu mulki ba ne su yi marmarin barasa, don kada su sha su manta da abin da doka ta umarta, su hana wa waɗanda aka danne hakkinsu.

Mai Hadishi 8:2-4

Ka yi biyayya da umarnin sarki, na ce, saboda alkawarin da ka yi a gaban Allah. Kada ka yi hanzarin tashi daga gaban sarki. Kada ka kāre abin da ba daidai ba, gama zai iya yin duk abin da ya ga dama. Da yake maganar sarki ita ce mafificiya, wa zai iya ce masa, “Me kake yi?”

Mai Hadishi 10:20

Kada ka zagi sarki ko da a cikin tunaninka ne, ko ka zagi mai arziki ko da a ɗakin kwananka ne, gama tsuntsun sararin sama zai iya ɗauki maganarka, tsuntsu mai fikafikai zai sanar da abin da ka ce.

Ishaya 1:7-10

Ƙasarku ta zama kufai, an ƙone biranenku da wuta; baƙi suna ƙwace gonakinku a idanunku, ta zama kango kamar sa’ad da baƙi suka rushe ta. An bar diyar Sihiyona kamar rumfar mai ƙumu a gonar inabi, kamar bukka a gonar kabewa, kamar birnin da aka kewaye da yaƙi. Da ba a ce Ubangiji Maɗaukaki ya bar mana raguwar masu rai ba, da mun zama kamar Sodom, da mun zama kamar Gomorra. Ku saurari maganar Ubangiji, ku masu mulkin Sodom; ku kasa kunne ga dokar Allahnmu, ku mutanen Gomorra!

Ishaya 1:13-14

Ku daina kawo hadayu marasa amfani! Turarenku abin ƙyama ne gare ni. Ina ƙin bukukkuwanku na Sabon Wata, da na ranakun Asabbaci, da taronku na addini, ba zan iya jure wa mugun taronku ba. Bukukkuwanku na Sabon Wata da na tsarkakan ranaku na ƙi su. Sun zama mini kaya; na gaji da ɗaukansu.

Ishaya 2:4

Zai shari’anta tsakanin al’ummai zai kuma sulhunta faɗar mutane masu yawa. Za su mai da takubansu su zama garemani māsunsu su zama wuƙaƙen askin itatuwa. Al’umma ba za tă ƙara ɗauki takobi a kan al’umma ba, ba kuwa za su ƙara yin horarwar yaƙi.

Ishaya 8:12

“Kada ka kira wani abu makirci game da kome da waɗannan mutane suke kira makirci; kada ji tsoron abin da suke tsoro, kada kuma ka firgita game da shi.

Ishaya 9:6-7

Gama a gare mu an haifa mana yaro, a gare mu an ba da ɗa, gwamnati za tă kasance a kafaɗarsa. Za a ce da shi Mashawarci Mai Banmamaki, Allah Maɗaukaki Uban Madawwami, Sarkin Salama. Game da girmar gwamnatinsa da salama babu iyaka. Zai gāji sarki Dawuda, yă yi mulki a matsayinsa, zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Maɗaukaki ne ya yi niyyar aikata wannan duka.

Ishaya 13:19-20

Babilon, kayan daraja na mulkoki, abin fariyar Babiloniyawa, Allah zai kaɓantar da ita kamar yadda ya yi da Sodom da Gomorra. Ba za ƙara kasance da mazauna kuma ba ko a yi zama a cikinta dukan zamanai; Ba wani mutumin Arab da zai kafa tentinsa a can, ba makiyayin da zai taɓa kiwon garkensa a can.

Ishaya 14:4-5

za ku yi wa sarkin Babilon wannan ba’a. Mai danniya ya zo ga ƙarshe! Dubi yadda fushinsa ya ƙare! Ubangiji ya karye sandar mugaye, sandan mulkin masu mulki,

Ishaya 24:5-6

Duniya ta ƙazantu ta wurin mutanenta sun ƙi yin biyayya da dokoki, sun keta farillai suka kuma karya madawwamin alkawari. Saboda haka la’ana za tă auko wa duniya; dole mutanenta su ɗauki hakkin laifinsu. Saboda haka aka ƙone mazaunan duniya, kuma kaɗan ne kurum suka rage.

Ishaya 32:1

Duba, sarki zai yi mulki cikin adalci masu mulki kuma su yi mulki da adalci.

Ishaya 33:22

Gama Ubangiji ne alƙalinmu, Ubangiji ne mai ba mu dokoki, Ubangiji ne sarkinmu; shi ne wanda zai cece mu.

Ishaya 44:28

wanda ya yi zancen Sairus ya ce, ‘Shi ne makiyayina zan kuma cika dukan abin da na gan dama; zai yi zancen Urushalima cewa, “Bari a sāke gina ta,” game da haikali kuma cewa, “Bari a kafa harsashinsa.” ’

Ishaya 45:1

“Ga abin da Ubangiji ya faɗa wa shafaffensa, ga Sairus, wanda hannun damansa yana riƙe da shi don yă ci al’ummai a gabansa ya kuma tuɓe makaman sarakuna, don yă buɗe ƙofofi a gabansa don kada a kulle ƙofofi.

Ishaya 60:12

Gama al’umma ko masarautar da ba tă bauta miki ba, za tă hallaka; za tă lalace sarai.

Irmiya 1:10

Duba, yau na naɗa ka a kan al’ummai da mulkoki don ka tumɓuke ka kuma rusar, ka hallaka ka kuma kakkaɓe, ka gina ka kuma shuka.”

Irmiya 5:11

Gidan Isra’ila da gidan Yahuda sun zama marasa aminci gaba ɗaya gare ni” in ji Ubangiji.

Irmiya 5:15

Ya gidan Isra’ila,” in ji Ubangiji, “Ina kawo al’umma daga nesa a kanku al’umma ce ta tun dā mai ƙarfin hali, mutane ne da ba ku san harshensu ba, waɗanda ba za ku fahimci abin da suke faɗa ba.

Irmiya 6:13

“Daga ƙarami zuwa babba, dukansu masu haɗama ne don riba; har da annabawa da firistoci, dukansu suna aikata rashin gaskiya.

Irmiya 10:10

Amma Ubangiji shi ne Allah na gaskiya; shi ne Allah mai rai, madawwamin sarki. Sa’ad da ya yi fushi, ƙasa takan girgiza; al’ummai ba sa iya jure da hasalarsa.

Irmiya 12:17

Amma duk al’ummar da ba tă saurara ba, zan tumɓuke ta ɗungum in kuma hallaka ta,” in ji Ubangiji.

Irmiya 18:5-10

Sai maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ya gidan Isra’ila, ashe, ba zan yi da ku yadda mai ginin tukwanen nan yake yi ba?” In ji Ubangiji. “Kamar yumɓu a hannun mai ginin tukwane, haka kuke a hannuna, ya gidan Isra’ila. A duk lokacin da na yi shela cewa za a tumɓuke, a kakkarya a kuma hallaka wata al’umma ko mulki, in wannan al’ummar da na yi wa gargaɗi ta tuba daga muguntarta, sai in janye in kuma fasa kawo mata masifar da na yi niyya aukar mata. In kuma wani lokaci na yi shela cewa za a gina wata al’umma ko mulki a kuma kafa ta, in ta yi mugunta a gabana ba tă kuwa yi mini biyayya ba, sai in janye alherin da na yi niyya in yi mata.

Irmiya 25:26-27

da kuma dukan sarakunan arewa, nesa da kuma kusa, bi da bi, dukan mulkokin duniya. Bayan dukansu kuma, sai sarkin Sheshak ma yă sha. “Sa’an nan na faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ku sha, ku bugu ku kuma yi amai, ku fāɗi, kada kuma ku ƙara tashi saboda takobin da zan aiko muku.’

Irmiya 25:32-36

Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Duba! Masifa tana yaɗuwa daga al’umma zuwa al’umma; hadari mai girma yana tasowa daga iyakar duniya.” A lokacin waɗanda Ubangiji ya kashe za su kasance a ko’ina, daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Ba za a yi kuka dominsu, ba za a tattara su don a binne ba, amma za su zama kamar juji da an tsiba a ƙasa. Ku yi kuka ku kuma yi makoki, ku makiyaya; ku yi ta birgima a ƙura, ku shugabannin garke. Gama lokacin da za a yanka ku ya zo; za ku fāɗi ku kuma farfasa kamar tukunyar yumɓu mai kyau. Makiyaya ba za su sami wurin da za su gudu su tafi ba, shugabannin garke ba za su sami wurin kuɓuta ba. Ji kukan makiyaya, kururuwan shugabannin garke, gama Ubangiji yana hallaka wurin kiwo.

Irmiya 29:7

Haka kuma, ku nemi zaman salama da cin gaba a birnin da aka kai ku zaman bauta. Ku yi addu’a ga Ubangiji saboda birnin, domin in ya ci gaba, ku ma za ku ci gaba.”

Irmiya 50:23

Dubi yadda aka karya aka kuma ragargaza gudumar dukan duniya! Dubi yadda Babilon ta zama kufai a cikin al’ummai!

Irmiya 51:6-7

“Ku gudu daga cikin Babilon! Bari kowa yă ceci ransa! Kada a hallaka saboda zunubanta. Gama lokaci ne don ramuwar Ubangiji, zai sāka mata bisa ga alhakinta. Babilon ta zama ƙoƙon zinariya a hannun Ubangiji, ta sa dukan duniya ta yi maye. Ƙasashe sun sha ruwan inabinta, saboda haka yanzu sun haukace.

Irmiya 51:53

Ko da Babilon za tă kai sararin sama ne, ta gina kagaranta mai ƙarfi, duk da haka zan aiki masu hallakarwa a kanta,” in ji Ubangiji.

Irmiya 51:57-58

Zan sa mahukuntanta da masu hikimarta, gwamnoninta, shugabanninta da sojojinta su sha su bugu; za su dinga yin barcin da ba za su farka ba,” in ji Sarkin, mai suna Ubangiji Maɗaukaki. Ni Ubangiji Maɗaukaki, na ce, “Za a baje katangan nan na Babilon mai kauri za a kuma ƙone dogayen ƙyamarenta da wuta; mutane sun wahalar da kansu a banza, al’umma sun yi wahala kawai domin wutar lalata.”

Daniyel 2:21

Yana sāke lokuta, yana tuɓe sarakuna yana kuma naɗa waɗansu. Yana ba da hikima ga masu hikima kuma ilimi ga masu basira.

Daniyel 2:36-45

“Wannan shi ne mafarkin, yanzu kuma za mu fassara ta wa sarki. Ya, sarki, kai ne sarkin sarakuna. Allah na sama ya ba ka iko da girma da suna; a cikin hannunka ya sanya ɗan adam, da namun jeji da tsuntsayen sama. A duk inda suke zaune, ya maishe ka ka yi mulki a bisansu kai ne kan zinariyan nan na siffar. “A bayanka, za a yi wani mulki, wanda bai kai naka ba. A gaba kuma, za a yi mulki na uku wanda yake na tagulla, zai yi mulkin dukan duniya. A ƙarshe, za a yi mulki na huɗu, mai ƙarfi kamar ƙarfe, Da yake baƙin ƙarfe yakan kakkarya, ya ragargaje abubuwa, haka nan wannan mulki zai ragargaje sauran mulkoki Ka kuma ga an yi ƙafafun da yatsotsin da baƙin ƙarfe gauraye da yumɓu, wato, mulkin zai rabu, amma zai kasance da ƙarfi kamar na baƙin ƙarfe da yake gauraye da yumɓu. Kamar yadda yatsotsin rabi na ƙarfe rabi kuma na yumɓu ne, haka wannan mulki zai zama rabi mai ƙarfi rabi kuma marar ƙarfi. Kamar dai yadda ka ga ƙarfen ya gauraye da yumɓu, haka mutanen za su zama a gauraye amma ba za su haɗu da juna ba, kamar yadda baƙin ƙarfe da yumɓu ba su haɗuwa. “A lokacin mulkin waɗannan sarakunan, Allah na sama zai kafa mulki da ba zai taɓa rushewa ba, ba kuma za a ba ma waɗansu mutane ba. Zai ragargaje waɗannan mulkokin da kuma kawo su ga ƙarshe, amma shi wannan mulki zai dawwama har abada. Wannan shi ne ma’anar wannan wahayin da ka gani na dutsen da aka yanko daga jikin tsaunin, amma ba da hannun ɗan adam ba, dutsen da ya ragargaza ƙarfen, da tagullar, da yumɓun da azurfar da kuma zinariyar. “Allah mai girma ya nuna wa sarki abin da zai faru nan gaba. Mafarkin gaskiya ne, fassararsa kuma abin dogara ne.”

Daniyel 2:46-49

Sai sarki Nebukadnezzar ya fāɗi da fuskarsa har ƙasa a gaban Daniyel domin ya girmama shi ya kuma umarta a miƙa hadaya da kuma hadayar ƙonawa ta turare ga Daniyel. Sarki ya kuma ce wa Daniyel, “Tabbatacce Allahnka shi ne Allahn alloli da kuma Sarkin sarakuna da mai bayyana asirai, gama ka iya bayyana wannan asiri.” Sai sarki ya ɗora Daniyel a babban matsayi ya kuma sanya shi mai mulki a kan dukan yankin ƙasar Babilon; ya kuma ɗora shi yă zama mai kula da duk masu hikima. Bugu da ƙari, bisa ga bukatar Daniyel sai sarki yă naɗa Shadrak da Meshak da Abednego su zama masu kula da harkokin lardin Babilon, amma Daniyel kuma ya tsaya a fadar sarki.

Daniyel 3:1-7

Sarki Nebukadnezzar ya yi gunkin zinariya, tsawonsa kamu tasa’in, fāɗinsa kuma kamu tara ne, ya kafa shi a filin Dura a yankin Babilon. Sa’an nan ya aika a kira hakimai da wakilai da gwamnoni da mashawarta, da ma’aji, da alƙalai, da marubutan kotu, da dukan sauran ma’aikatan yankunan, suka hallara domin a rusuna wa wannan siffar da ya kafa. Saboda haka sai hakimai, da wakilai da gwamnoni, mashawarta da ma’aji da alƙalai, da marubutan alƙalai, da kuma dukan ma’aikatan yankunan suka tattaru domin kaddamar da siffar da Nebukadnezzar ya kafa, suka kuma tsaya a gabansa. Sai mai shela ya daga murya da ƙarfi ya ce, “Wannan shi ne abin da aka umarce ku ku yi, ya ku mutane da al’umma da kowane yare. Da zarar kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya da goge da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe ku rusuna ku yi sujada ga wannan gunkin da sarki Nebukadnezzar ya kafa. Duk wanda bai rusuna ya yi sujada ba, nan take za a jefa shi a cikin tendarun wuta.” Saboda haka, da zarar suka ji karar ƙaho, da sarewa, garaya da goge da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe da kowane irin kaɗe-kaɗe kowane mutum da ko wace al’umma da kowane irin yare suka sunkuya suka yi sujada ga wannan siffa ta zinariya da sarki Nebukadnezzar ya kafa.

Daniyel 3:8-15

A wannan lokaci sai waɗansu masanan taurari suka zo gaba suka yi karar Yahudawa. Suka ce wa sarki Nebukadnezzar, “Ran sarki yă daɗe, Ya sarki, ka fitar da doka, cewa duk wanda ya ji karar ƙaho, da sarewa, da garayu da goge, da molo da algaita da kowane irin kayan kaɗe-kaɗe da bushe-bushe sai yă rusuna yă yi sujada ga siffar zinariya, kuma cewa duk wanda bai rusuna ya yi sujadar ba za a jefa shi cikin tanderun wuta. Amma sai ga waɗansu Yahudawa waɗanda ka ɗora su a kan harkokin yankin Babilon, wato, Shadrak, Meshak da Abednego waɗanda ba su kula da umarninka ba, ya sarki. Ba su bauta wa allolin ba balle su yi sujada ga gunkin zinariya da ka kafa.” Cikin fushi da hasala, Nebukadnezzar ya aika a kira Shadrak, Meshak da Abednego. Aka kawo waɗannan mutane a gaban sarki, sai Nebukadnezzar ya ce musu, “Gaskiya ne Shadrak, Meshak da Abednego, cewa kun ƙi ku bauta wa alloli kuka kuma ƙi yi sujada ga gunkin da na kafa? Yanzu sa’ad da kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, in kuna a shirye ku rusuna ƙasa ku yi wa wannan gunkin da na yi sujada, to, da kyau. Amma in ba ku yi sujada ba, za a je fa ku yanzu a cikin tanderun wutar nan. In ga kowane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”

Daniyel 3:16-23

Sai Shadrak, Meshak da Abednego suka amsa wa sarki suka ce, “Ya Nebukadnezzar, ba mu bukata mu kāre kanmu a gabanka a kan wannan batu. In an jefa mu cikin tanderun wutar nan, Allahn da muke bauta wa zai iya cetonmu daga ita, kuma ya sarki, zai cece mu daga hannunka. Amma ko da bai cece mu ba, muna so ka sani, ya sarki; cewa ba za mu bauta wa allolinka ba ko kuma mu yi sujada ga gunkin zinariyar da ka kafa ba.” Sai Nebukadnezzar ya husata da Shadrak, Meshak da Abednego, sai al’amuransa a kansu ya canja. Sai ya umarta a ƙara zuga wutar har sau bakwai domin tă yi zafi fiye da yadda take a dā. Kuma ya umarci waɗansu ƙarfafan sojoji a cikin rundunarsa su daure Shadrak, Meshak da Abednego su jefa su cikin tanderun wutar. Waɗannan mutanen suna sanye da riguna, da wanduna, da rawani da waɗansu kayan sawa, aka daure su, aka jefa su cikin tanderun wuta. Sarki ya ba da umarnin da gaggawa kuma wutar ta yi zafi ƙwarai har harshen wutar ya kashe sojojin nan da suka ɗauki Shadrak, Meshak da Abednego, waɗannan mutane uku kuma a daure, suka fāɗa cikin tanderun wutar.

Daniyel 3:24-27

Sai Sarki Nebukadnezzar ya miƙe tsaye, cike da mamaki ya tambayi mashawartansa, “Shin ba mutum uku ba ne muka daure muka jefa cikin wutar?” Suka amsa, “Tabbatacce haka yake ya sarki.” Sai ya ce, “Ku duba ina ganin mutum huɗu suna tafiya suna yawo a cikin wutar, a sake kuma babu abin da ya same su, na huɗun sai ka ce ɗan alloli.” Sai Nebukadnezzar ya matsa kusa da ƙofar tanderun wutar ya yi kira da ƙarfi, “Shedrak, Meshak da Abednego, bayin Allah Mafi Ɗaukaka ku fito! Ku zo nan!” Sai Shadrak, Meshak da Abednego suka fita daga cikin wutar, Sa’an nan hakimai, da wakilai, da gwamnoni da masu ba wa sarki shawara suka kewaya su. Suka ga wutar ba tă yi musu wani lahani a jikinsu ba, babu ko gashin kansu da ya ƙuna; ko warin wuta ma ba su yi ba.

Daniyel 3:28-30

Sa’an nan Nebukadnezzar ya ce, “Yabo ya tabbata ga Allahn Shadrak, Meshak da Abednego wanda ya aiko da mala’ikansa ya ceci bayinsa da suka dogara matuƙa a gare shi, suka ki bin umarnin sarki kuma su na a shirye domin su ba da ransu da suka ƙi bauta ko su yi sujada ga wani allah sai dai Allahnsu. Domin haka ina ba da doka cewa duk mutane da kowace al’umma ko kowane yaren da ya ce wani abu mummuna a kan Allahn Shadrak, Meshak da Abednego za a yanka shi gunduwa-gunduwa kuma gidansu zai zama wurin zuba shara, domin babu wani allahn da zai iya ceto ta irin wannan hanya.” Sa’an nan sarki ya ƙara wa su Shadrak, Meshak da Abednego girma a yankin Babilon.

Daniyel 4:1-3

Daga sarki Nebukadnezzar. Zuwa ga mutane da al’ummai da kuma kowane yare, da suke zama a duniya. Salama mai yawa ta tabbata a gare ku! Ina murna in shaida muku game da alamu da al’ajabai waɗanda Allah Mafi Ɗaukaka ya yi ta wurina. Alamunsa da girma suke, ayyukansa da girma suke! Mulkinsa mulki ne na har abada; sarautarsa kuma za tă dawwama daga zamani zuwa zamani.

Daniyel 4:17

“ ‘An sanar da wannan matsayi ne ta bakin ’yan saƙo, masu tsarki ne kuwa suka sanar da hukuncin, domin masu rai su sani Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a bisa kowane mulkin mutane, yakan kuma ba wa duk wanda ya ga dama, yakan sanya talaka yă zama sarki.’

Daniyel 4:25

Za a kore ka daga cikin mutane, za ka kuma zauna cikin namun jeji; za ka ci ciyawa kamar shanu, za ka jiƙe da raɓa har shekara bakwai cif sa’an nan za ka sani cewa Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.

Daniyel 4:27

Saboda haka, ya sarki, ina roƙonka ka karɓi shawarar da zan ba ka; ka furta zunubanka ta wurin yin abin da yake daidai. Ka bar muguntarka, ka aikata alheri ga waɗanda ake wulaƙantawa, wataƙila za a ƙara tsawon kwanakinka da salama.”

Daniyel 4:28-33

Duk wannan kuwa ya faru da sarki Nebukadnezzar. Bayan wata goma sha biyu, a sa’ad da sarki yake takawa a bisan saman ɗakin fadar Babilon, sai ya ce, “Ba wannan ita ce Babilon babba da na gina domin wurin zaman sarautar Babilon, da ikona kuma domin ɗaukakar darajata ba?” Tun kalmomin suna cikin bakinsa sai ya ji murya daga sama tana cewa, “Wannan shi ne abin da aka zartar a kanka, Sarki Nebukadnezzar. An karɓe ikon mulkinka. Za a kore ka daga cikin mutane za ka kuma yi rayuwa tare da namun jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa har shekara bakwai cif, sa’an nan za ka gane Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.” Nan da nan abin da aka faɗa a kan Nebukadnezzar tabbatarsa ya cika. Aka kore shi daga cikin mutane ya kuma shiga cin ciyawa kamar shanu. Jikinsa ya jiƙe da raɓa, har gashinsa ya yi tsawo kamar fikafikan gaggafa, kumbarsa kuma suka yi tsawo kamar na tsuntsu.

Daniyel 4:34-37

A ƙarshen waɗannan kwanaki, ni, Nebukadnezzar, na ɗaga idanuna sama, sai hankalina ya komo mini. Na kuwa yabi Maɗaukaki, na girmama shi, na ɗaukaka shi wanda yake rayayye har abada. Mulkinsa dawwammamen mulki ne; sarautarsa ta dawwama daga zamani zuwa zamani. Dukan mutanen duniya ba a bakin kome suke ba. Yakan yi abin da ya gamshe shi da ikokin sama da kuma na mutanen duniya. Babu mai hana shi ko yă ce masa; “Me ka yi?” A lokacin nan hankalina ya komo mini, sai aka mayar mini da masarautata mai daraja, da martabata, da girmana. ’Yan majalisata da fadawana suka nemo ni. Aka maido ni kan gadon sarautata da daraja fiye da ta dā. Yanzu ni, Nebukadnezzar, ina yabon Sarkin sama, ina waƙa ina kuma darjanta shi, saboda dukan abin da ya yi mini, mai kyau ne kuma dukan hanyoyinsa gaskiya ne. Kuma duk masu tafiya da girman kai zai ƙasƙantar da su.

Daniyel 5:11

Akwai wani mutum a masarautarka wanda yake da ruhun alloli masu tsarki a cikinsa. A zamanin mahaifinka an gane cewa yana da basira da hazaka da hikima kamar na alloli. Sarki Nebukadnezzar mahaifinka, mahaifinka sarki, na ce, ya naɗa shugaban masu dabo, da masu sihiri, masanan taurari da kuma masu duba.

Daniyel 5:18-21

“Ya sarki, Allah Mafi Ɗaukaka ya ba mahaifinka Nebukadnezzar sarauta, da girma, da ɗaukaka, da martaba. Saboda irin matsayin da ya ba shi, dukan mutane da al’ummai da kuma dukan harsuna suka ji tsoronsa suka yi rawar jiki a gabansa. Bisa ga ganin damarsa yakan kashe wani, ya bar wani da rai, haka kuma yakan ɗaukaka wani, ya ƙasƙantar da wani. Amma da lokacin da zuciyarsa ta cika da girman kai ta kuma taurare, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa. Aka kore shi daga cikin mutane aka kuma ba shi tunani irin na dabba; ya yi zama tare da jakunan jeji, ya kuma ci ciyawa kamar shanu; jikinsa kuma ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.

Daniyel 5:22-31

“Amma kai ɗansa, Ya Belshazar, ba ka ƙasƙantar da kanka ba, ko da yake ka san wannan duka. A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa. Saboda haka ya aiko da hannun da ya yi rubutun nan. “Wannan shi ne rubutun da aka yi, Mene, mene, tekel, farsin “Abin da kalmomin nan suke nufi shi ne, “Mene, Allah ya ƙayyade yawan kwanakin mulkinka ya kuma kawo su ga ƙarshe. “Tekel, An kuma auna ka a ma’auni aka tarar ka kāsa. “Feres, An raba mulkinka aka ba wa Medes da Farisa.” Sai Belshazar ya umarta, aka sa wa Daniyel riga mai shunayya, aka sa sarƙar zinariya a wuyansa, aka kuma yi shela, cewa yanzu shi ne na uku a cikin masu mulkin ƙasar. A wannan dare aka kashe Belshazar, sarkin Babiloniyawa, Dariyus mutumin Medes kuwa ya karɓi mulkin, yana da shekara sittin da biyu.

Daniyel 6:1-9

Ya gamshi Dariyus ya naɗa muƙaddasai 120 su yi shugabanci a duk fāɗin masarautar, ya naɗa mutum uku a bisa waɗannan muƙaddasan, Daniyel yana ɗaya daga cikin mutum ukun nan. Sai aka sa muƙaddasan nan a ƙarƙashin waɗannan uku ɗin domin kada sarki ya yi hasarar kome. To, Daniyel dai ya yi ficce a cikin shugabannin nan uku har da muƙaddasan ma, saboda waɗansu halaye nagari da yake da su, wanda ya sa sarki ya yi shiri ya ɗora shi a kan dukan mulkinsa. A kan haka, shugabannin nan uku da muƙaddasan nan suka yi ƙoƙari su sami wani laifi a kan Daniyel a yadda yake tafiyar da aikin shugabancinsa, amma ba su samu ba. Ba su same shi da wani laifin cin hanci ba, domin shi amintacce ne kuma babu wani aibi a kansa ko rashin kula. A ƙarshe waɗannan mutane suka ce; “Ba za mu taɓa samun wani laifin da za mu kama Daniyel da shi ba, sai dai ko abin ya shafi dokar Allahnsa.” Saboda haka shugabannin nan suka haɗu da muƙaddasan nan suka tafi wurin sarki a ƙungiyance suka ce, “Ya Sarki Dariyus, ranka yă daɗe! Shugabannin masarauta, da masu mulki, da muƙaddasai, da mashawarta da gwamnoni duk sun amince cewa sarki yă kafa doka yă kuma yi umarni cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda ya yi addu’a ga wani allah ko mutum, in ba a gare ka ba, ya sarki, jefa shi cikin kogon zakoki. Yanzu, ya sarki, sai ka yi umarni ka kuma yi shi a rubuce saboda kada a canja shi, bisa ga dokar Medes da Farisa, waɗanda ba a iya sokewa.” Sai Sarki Dariyus ya ba da umarnin a rubuce.

Daniyel 6:10-15

To, da Daniyel ya ji labarin cewa an fitar da doka, sai ya tafi gidansa a ɗakinsa na sama inda tagogin ɗakin suke duban wajen Urushalima. Sau uku yakan durƙusa yă yi addu’a yana yin godiya ga Allahnsa, kamar yadda ya saba yi. Sai waɗannan mutane suka tafi a ƙungiyance suka kuma iske Daniyel yana addu’a yana roƙon Allah yă taimake shi. Sai suka tafi wurin sarki suka yi masa magana game da dokar mulkinsa, suka ce, “Ashe, ba ka yi doka cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda aka tarar yana addu’a ga wani allah ko mutum in ba kai ba, ya sarki, za ka jefa shi a cikin ramin zakoki ba?” Sarki ya amsa ya ce, “Dokar tana nan daram bisa ga dokar Medes da Farisa, waɗanda ba a iya sokewa.” Sai suka ce wa sarki, “Daniyel ɗin nan, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda aka kwaso daga Yahuda, bai kula da kai ba, ya sarki, balle fa dokar da ka yi. Har yanzu yana addu’a sau uku a rana.” Da sarki ya ji haka, sai ya damu sosai, ya ƙudura yă ceci Daniyel, ya yi ta fama har fāɗuwar rana yadda zai yi yă kuɓutar da shi. Sai mutanen nan suka je wurin sarki a ƙungiyance suka ce masa, “Ka tuna, ya sarki; cewa bisa ga dokar Medes da Farisa, babu umarni ko dokar da sarki ya yi da za a iya sokewa.”

Daniyel 6:16-18

Saboda haka sai sarki ya ba da umarni suka kuma kawo Daniyel suka jefa shi cikin ramin zakoki. Sarki ya ce wa Daniyel, “Bari Allahn nan wanda kake bauta masa kullum, yă cece ka!” Aka kawo dutsen aka rufe bakin ramin, sa’an nan sarki ya hatimce shi da zobensa da kuma zoban manyan mutanensa, don kada wani yă canja yanayin Daniyel. Sa’an nan sarki ya koma fadarsa ya kwana bai ci ba, kuma babu wata liyafar da aka kawo masa. Ya kuma kāsa barci.

Daniyel 6:19-23

Gari yana wayewa, sai sarki ya tashi ya hanzarta zuwa ramin zakoki. Da ya yi kusa da ramin zakokin, sai ya kira Daniyel da muryar mai cike da damuwa ya ce, “Daniyel bawan Allah mai rai, ko Allahn nan naka wanda kake bauta wa kullum, ya iya cetonka daga zakoki?” Sai Daniyel ya amsa ya ce, “Ran sarki, yă daɗe! Allahna ya aiko da mala’ikansa, ya kuwa rufe bakunan zakoki. Ba su yi mini rauni ba, gama an same ni marar laifi ne a gabansa. Ban kuwa taɓa yin wani abu marar kyau a gabanka ba, ya sarki.” Sai sarki ya cika da murna ƙwarai, ya kuma yi umarni a ciro Daniyel daga ramin zakoki. Kuma da aka fito da Daniyel daga ramin, ba a sami wani rauni a jikinsa ba, domin ya dogara ga Allahnsa.

Daniyel 6:24-28

Sai sarki ya umarta, a kawo mutanen nan da suka yi wa Daniyel maƙarƙashiya, a tura su, da ’ya’yansu, da matansu cikin ramin zakoki. Kafin ma su kai ƙurewar ramin, sai zakoki suka hallaka su suka yayyage su, suka yi kaca-kaca da su. Sa’an nan Sarki Dariyus ya rubuta wa dukan mutane, da al’ummai da kuma mutanen dukan harsunan a duk fāɗin ƙasar. “Bari yă yi nasara sosai! “Na fitar da doka cewa a cikin dukan iyakar ƙasar mulkina, dole mutane su ji tsoro su kuma girmama Allah na Daniyel. “Gama shi ne Allah mai rai kuma madawwami ne har abada; ba za a taɓa lalace masarautarsa ba, mulkinsa kuma ba za tă taɓa ƙarewa ba Yakan kuɓutar ya kuma ceci; yana yin alamu da al’ajabai a sama da kuma a duniya. Shi ya ceci Daniyel daga ikon zakoki.” Daniyel kuwa ya bunkasa a lokacin mulkin Dariyus da kuma mulkin Sairus na Farisa.

Daniyel 7:14

Aka ba shi mulki, daraja da kuma mafificin iko; dukan mutane, da al’ummai, da mutane daga kowane harshe suka yi masa sujada. Mulkinsa kuwa dawwammamen mulki ne da ba zai ƙare ba, sarautarsa kuma ba ta taɓa lalacewa.

Daniyel 7:17-18

‘Waɗannan manyan dabbobi huɗu, Masarautai ne huɗu waɗanda za su taso a duniya. Amma tsarkaka na Mafi Ɗaukaka za su karɓi wannan sarauta, za su kuwa mallake ta har abada, I, har abada abadin.’

Daniyel 7:19-20

“Sa’an nan kuma sai na so in san ma’anar wannan dabba ta huɗu, wadda ta yi dabam da sauran dabbobin da suke da matuƙar bantsoro, da take da haƙoran ƙarfe da kuma farcen tagulla, dabbar ta ragargaje ta cinye abin da ta kama, ta kuma tattaka duk abin da ya rage a ƙarƙashin ƙafafunta. Na kuma so in gane game da ƙahonin nan guda goma da suke a kanta da kuma game da ƙahon nan da ya fito, wanda aka tumɓuke ƙahoni uku a gabansa, ƙahon nan da yake da idanu da bakin da yake furta manyan maganganun fariya, wanda ya yi kamar ya fi sauran girma.

Daniyel 7:23-24

“Sai ya ba ni wannan bayani, ‘Dabbar nan ta huɗu, ita ce mulki na huɗu da zai bayyana a duniya. Zai bambanta da dukan sauran mulkoki, zai kuma cinye dukan duniya, yă tattake ta, yă kuma ragargaje ta. Ƙahonin nan goma, sarakuna ne goma waɗanda za su taso daga wannan mulki. Bayansu kuma, wani sarki zai taso, wanda ya sha dabam da waɗanda suka riga shi. Zai rinjayi sarakunan nan uku.

Daniyel 7:25-26

Zai yi maganar saɓo a kan Mafi Ɗaukaka, zai kuma tsananta wa tsarkaka yă kuma yi ƙoƙarin sāke lokuta da shari’u. Za a miƙa tsarkaka a hannunsa na wani lokaci, lokuta da kuma rabin lokaci. “ ‘Amma majalisa za tă yi zama, za a karɓe ikonsa, a kuma hallaka shi gaba ɗaya har abada.

Daniyel 7:27

Sa’an nan za a ba da mulki, iko da girma na mulkokin da suke a ƙarƙashin dukan sammai ga tsarkaka, mutane na Mafi Ɗaukaka. Mulkinsa kuwa mulki ne marar matuƙa, kuma dukan masu mulki za su yabe shi, su kuma yi masa biyayya.’

Daniyel 11:27

Sarakunan nan biyu sun sa mugunta a ransu. Za su zauna a tebur guda su yi ta shara wa juna ƙarya, amma a banza, gama lokacin da aka ƙayyade bai yi ba tukuna.

Daniyel 12:1

“A wannan lokaci Mika’ilu, babban mai mulki wanda yake kāre mutanenka, zai tashi. Za a yi lokacin matsananciyar wahala wanda ba a taɓa yi tun farkon ƙasashe har zuwa yanzu. Amma a lokacin da mutanenka, kowane mutum wanda aka sami sunansa a rubuce a cikin littafin, za a cece shi.

Hosiya 8:4

Suna naɗa sarakuna, ba da izinina ba; sun zaɓa shugabanni ba da yardanta ba. Da azurfa da zinariya sun ƙera gumaka wa kansu wanda zai kai zuwa ga hallakarsu.

Hosiya 13:9-11

“An hallaka ku, ya Isra’ila, domin kun tayar mini, kun tayar wa mai taimakonku. Ina sarkinku, da zai cece ku? Ina masu mulkinku cikin dukan garuruwanku, waɗanda kuka ce, ‘Ba mu sarki da shugabanni’? Saboda haka cikin fushina na ba ku sarki, kuma cikin hasalata na ɗauke shi.

Yunana 3:5-8

Mutanen Ninebe kuwa suka gaskata Allah. Aka yi shela a yi azumi, sai dukansu daga babba har zuwa ƙaraminsu, suka sa tufafin makoki. Da saƙon Yunana ya kai kunnen sarkin Ninebe, sai ya tashi daga kujerar mulkinsa, ya tuɓe alkyabbarsa, ya sa rigar makoki, ya zauna cikin toka. Sai ya yi umarni a Ninebe cewa, “Bisa ga umarnin sarki da fadawansa. “Kada a bar wani mutum ko dabba, garke ko shannu, su ɗanɗana wani abu; kada a bari su ci ko su sha. Bari kowane mutum da dabba yă yafa rigunan makoki. Kowa yă roƙi Allah da gaske, kowa kuma yă bar mugayen ayyukan da yake yi.

Mika 3:1-3

Sa’an nan na ce, “Ku kasa kunne, ku shugabannin Yaƙub, ku masu mulkin gidan Isra’ila. Ya kamata ku san shari’a, ku da kuke ƙin abu mai kyau kuke ƙaunar mugunta, ku da kuke feɗe mutanena kuke tuge nama daga ƙasusuwansu; ku da kuke cin naman mutanena, ku feɗe fatar jikinsu kuke kakkarya ƙasusuwansu, kuke yayyanka su gunduwa-gunduwa kamar naman da za a toya, kamar naman da za a sa a dafa.”

Mika 3:9-10

Ku ji wannan, ku shugabannin gidan Yaƙub, ku masu mulkin gidan Isra’ila, ku da kuke ƙyamar gaskiya, kuka karkatar duk abin da yake na gaskiya; kuka gina Sihiyona ta wurin zub da jini, Urushalima kuma ta wurin mugunta.

Mika 4:3

Zai shari’anta tsakanin mutane yă kuma sulhunta tsakanin manyan al’ummai nesa da kuma kusa. Har su mai da takubansu su zama garemani, māsunsu kuma su zama wuƙaƙen askin itace. Al’umma ba za tă ɗauki takobi gāba da wata al’umma ba, ko a yi horarwa don yaƙi.

Mika 5:2

“Amma ke, Betlehem ta Efrata, ko da yake ke ƙarama ce daga cikin zuriyarki a Yahuda, daga cikinki wani zai zo domina wanda zai yi mulkin Isra’ila, wanda asalinsa tun fil azal ne.”

Zakariya 14:9

Ubangiji zai sama sarki bisa dukan duniya. A ranan nan za a kasance da Ubangiji ɗaya, ba wani suna kuma sai nasa.

Zakariya 14:16-19

Sa’an nan waɗanda suka tsira daga cikin al’umman da suka yaƙe Urushalima za su haura shekara-shekara su yi wa Sarki, Ubangiji Maɗaukaki sujada, su kuma yi Bikin Tabanakul. In waɗansu mutanen da suke duniya ba su haura Urushalima suka yi wa Sarki, Ubangiji Maɗaukaki sujada ba, ba za su sami ruwan sama ba. In mutanen Masar ba su haura sun yi sujada ba, ba za su sami ruwan sama ba. Ubangiji zai kawo masu bala’in da ya aika wa al’umman da ba su haura sun yi Bikin Tabanakul ba. Wannan ne zai zama hukuncin Masar da kuma na dukan al’umman da ba su haura sun yi Bikin Tabanakul ba.

Mattiyu 2:1-6

Bayan an haifi Yesu a Betlehem, a Yahudiya, a zamanin Sarki Hiridus, sai waɗansu Masana, daga gabas suka zo Urushalima suka yi tambaya suka ce, “Ina shi wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Gama mun ga tauraronsa a gabas mun kuwa zo ne domin mu yi masa sujada.” Da Sarki Hiridus ya ji wannan, sai hankalinsa ya tashi haka ma na dukan Urushalima. Bayan ya kira dukan manyan firistoci da malaman dokoki na mutane wuri ɗaya, sai ya tambaye su inda za a haifi Kiristi. Suka amsa suka ce, “A Betlehem ne, cikin Yahudiya, gama haka annabin ya rubuta. “ ‘Amma ke Betlehem, a cikin ƙasar Yahuda, ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin masu mulki a Yahuda ba, gama daga cikinki mai mulki zai zo, wanda zai zama makiyayin mutanena Isra’ila.’”

Mattiyu 2:13-15

Bayan sun tafi, sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana ga Yusuf a mafarki ya ce, “Tashi, ka ɗauki yaron da mahaifiyarsa, ku gudu zuwa Masar. Ku zauna a can sai na gaya muku, gama Hiridus zai nemi yaron don yă kashe.” Sai Yusuf ya tashi, ya ɗauki yaron da mahaifiyarsa da dad dare suka tafi Masar, inda ya zauna har sai da Hiridus ya mutu. Ta haka kuwa aka cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabin cewa, “Daga Masar na kira ɗana.”

Mattiyu 2:16

Da Hiridus ya gane cewa Masanan nan sun yi masa wayo, sai ya husata ƙwarai, ya yi umarni cewa a karkashe dukan ’yan yara maza da suke a Betlehem da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, bisa ga lokacin da ya sami labarin daga Masanan nan.

Mattiyu 4:8-10

Har wa yau, Iblis ya kai shi bisa wani dutse mai tsawo sosai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu. Ya ce, “Zan ba ka dukan wannan, in za ka durƙusa ka yi mini sujada.” Sai Yesu ya ce masa, ‹“Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake, ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’›‹”›

Mattiyu 6:24

‹“Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu. Ko dai yă ƙi ɗaya, yă ƙaunaci ɗaya, ko kuwa yă yi aminci ga ɗaya, sa’an nan yă rena ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah, ku kuma bauta wa kuɗi gaba ɗaya.”›

Mattiyu 7:12

‹Saboda haka, duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Doka da koyarwar Annabawa sun ƙunsa.›

Mattiyu 10:17-20

‹Ku yi hankali da mutane; za su miƙa ku ga majalisa su kuma yi muku bulala a majami’unsu.› ‹Saboda ni, za a ja ku zuwa gaban gwamnoni da gaban sarakuna domin ku ba da shaida a gabansu, da kuma ga Al’ummai.› ‹Amma sa’ad da suka kama ku, kada ku damu game da abin da za ku faɗa ko kuwa yadda za ku faɗe shi. A lokacin za a ba ku abin da za ku faɗa,› ‹gama ba ku ba ne kuke magana, amma Ruhun Ubanku ne yake magana ta wurinku.›

Mattiyu 10:23

‹Sa’ad da aka tsananta muku a wannan wuri, ku gudu zuwa wancan. Gaskiya nake gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan biranen Isra’ila, Ɗan Mutum zai zo.›

Mattiyu 14:1-2

A lokacin nan sarki Hiridus ya ji labarin Yesu, sai ya ce wa fadawansa, “Wannan Yohanna Mai Baftisma ne; ya tashi daga matattu! Shi ya sa abubuwan banmamakin nan suke faruwa ta wurinsa.”

Mattiyu 14:3-11

To, dā Hiridus ya kama Yohanna ya daure, ya kuma sa shi cikin kurkuku saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa Filibus, gama Yohanna ya dinga ce masa, “Ba daidai ba ne ka aure ta.” Hiridus ya so yă kashe Yohanna, amma yana jin tsoron mutane, don sun ɗauka shi annabi ne. A bikin tuna da ranar haihuwar Hiridus, diyar Hiridiyas ta yi musu rawa ta kuma gamsar da Hiridus ƙwarai, har ya yi alkawari da rantsuwa cewa zai ba ta duk abin da ta roƙa. Da mahaifiyarta ta zuga ta, sai ta ce, “Ba ni a cikin kwanon nan, kan Yohanna Mai Baftisma.” Sarki ya yi baƙin ciki, amma saboda rantsuwarsa da kuma baƙinsa, sai ya ba da umarni a ba ta abin da ta roƙa ya kuma sa aka yanke kan Yohanna a kurkuku. Aka kawo kansa cikin kwano aka ba yarinyar, ita kuma ta kai wa mahaifiyarta.

Mattiyu 17:24-27

Bayan Yesu da almajiransa suka isa Kafarnahum, sai masu karɓan harajin rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, “Malaminku ba ya biyan harajin haikali ne?” Ya amsa ya ce “I, yana biya.” Da Bitrus ya shiga gida, Yesu ne ya fara magana. Ya ce masa, ‹“Me ka gani, Siman? Daga wurin wane ne sarakunan duniya suke karɓar kuɗin shiga da kuma haraji, daga wurin ’ya’yansu ne ko kuwa daga wurin waɗansu?”› Bitrus ya amsa ya ce, “Daga wurin waɗansu.” Yesu ya ce masa, ‹“Wato, an ɗauke wa ’ya’yan ke nan.› ‹Amma don kada mu ɓata musu rai, ka je tafki ka jefa ƙugiyarka. Ka ɗauki kifin da ka fara kama; ka buɗe bakinsa, za ka sami shekel guda. Ka kawo ka ba su, harajina da naka ke nan.”›

Mattiyu 22:17-21

To, ka gaya mana, a ra’ayinka? Ya dace a biya Kaisar haraji ko a’a?” Amma Yesu da yake ya san mugun nufinsu, sai ya ce, ‹“Ku munafukai, don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko?› ‹Ku nuna mini kuɗin da ake biyan haraji da shi.”› Sai suka kawo masa dinari, sai ya tambaye su ya ce, ‹“Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne?”› Suka amsa, “Na Kaisar ne.” Sai ya ce musu, ‹“Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”›

Mattiyu 23:34

‹Saboda haka ina aika muku da annabawa, da masu hikima da malamai. Waɗansunsu za ku kashe ku kuma gicciye; waɗansu kuma za ku yi musu bulala a majami’unku kuna kuma binsu gari-gari.›

Mattiyu 24:6-9

‹Za ku ji labarin yaƙe-yaƙe da kuma jita-jitarsu, sai dai ku lura kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru, amma ƙarshen tukuna.› ‹Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki yă tasar wa mulki. Za a yi yunwa da girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam.› ‹Dukan waɗannan fa, mafarin azabar naƙudar haihuwa ne.› ‹“Sa’an nan za a bashe ku don a tsananta muku a kuma kashe ku, dukan al’ummai za su ƙi ku saboda ni.›

Mattiyu 26:59-60

Sai manyan firistoci da ’yan majalisa duka suka yi ta neman shaidar ƙarya a kan Yesu, don su sami dama su kashe shi. Amma ba su sami ko ɗaya ba, ko da yake masu shaidar ƙarya da yawa sun firfito. A ƙarshe, biyu suka zo gaba,

Mattiyu 26:67-68

Sai suka tottofa masa miyau a fuskarsa, suka kuma bubbuge shi da hannuwansu. Waɗansu kuma suka mammare shi suka ce, “Yi mana annabci, Kiristi. Wa ya buge ka?”

Mattiyu 27:11-14

Ana cikin haka, Yesu kuwa yana tsaye a gaban gwamna, sai gwamnan ya tambaye shi, “Kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya ce, ‹“I, haka ne, kamar yadda ka faɗa.”› Da manyan firistoci da dattawa suka zarge shi, bai ba da amsa ba. Sai Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Ba ka jin shaidar da suke kawowa a kanka?” Amma Yesu bai ce uffam game da ko ɗaya daga cikin zargin da suka yi masa ba. Har gwamna ya yi mamaki ƙwarai.

Mattiyu 27:27-31

Sai sojojin gwamna suka ɗauki Yesu suka kai shi Fadar mai mulki, sa’an nan suka tara dukan kamfanin sojoji kewaye da shi. Suka tuɓe shi, suka yafa masa wata jar riga. Suka kuma tuƙa wani rawanin ƙaya, suka sa masa a kā. Suka sa sanda a hannun damansa. Suka durƙusa a gabansa, suka yi masa ba’a, suna cewa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!” Suka tattofa masa miyau, suka karɓe sandan, suka yi ta ƙwala masa shi a kai. Bayan sun yi masa ba’a, sai suka tuɓe masa rigar, suka sa masa nasa tufafin. Sai suka tafi da shi, domin su gicciye shi.

Mattiyu 27:37

Bisa da kansa kuwa, an kafa rubutun zargin da aka yi masa, da ya ce, Wannan shi ne Yesu Sarkin Yahudawa.

Mattiyu 27:42

“Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! In shi ne Sarkin Isra’ila! To, yă sauko daga kan gicciyen nan, mu kuwa mu gaskata shi.

Mattiyu 28:18

Sai Yesu ya zo wurinsu ya ce, ‹“An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa.›

Markus 1:14-15

Bayan da aka sa Yohanna a kurkuku, sai Yesu ya shigo cikin Galili, yana shelar bisharar Allah. Yana cewa, ‹“Lokaci ya yi. Mulkin Allah ya yi kusa. Ku tuba, ku gaskata bishara!”›

Markus 6:14-16

Sarki Hiridus ya ji wannan labari, gama sunan Yesu ya bazu a ko’ina. Waɗansu suna cewa, “An tashe Yohanna Mai Baftisma daga matattu ne, shi ya sa yana da ikon yin ayyukan banmamakin nan.” Waɗansu suka ce, “Ai, Iliya ne.” Har wa yau waɗansu suka ce, “Ai, annabi ne, kamar ɗaya daga cikin annabawan dā.” Amma da Hiridus ya ji haka, sai ya ce, “Ai, Yohanna ne, mutumin da na yanke masa kai, shi ne ya tashi daga matattu!”

Markus 6:17-28

Gama Hiridus da kansa ya ba da umarni a kama Yohanna, ya kuma sa aka daure shi, aka sa shi a kurkuku. Ya yi haka saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa Filibus, wadda ya aura. Gama Yohanna ya yi ta ce wa Hiridus, “Ba daidai ba ne bisa ga doka, ka ɗauki matar ɗan’uwanka.” Saboda haka, Hiridiyas ta ƙulla munafunci game da Yohanna, ta kuma so ta kashe shi. Amma ba tă iya ba, domin Hiridus yana jin tsoron Yohanna, ya kuma kāre shi sosai, da sanin cewa shi mutum ne mai adalci da kuma mai tsarki. Duk sa’ad da Hiridus ya saurari Yohanna, yakan damu ƙwarai, duk da haka, yakan so yă ji shi. A ƙarshe, ta sami zarafi. A ranar murnar haihuwar Hiridus, ya yi biki domin hakimansa, da shugabannin sojojinsa, da kuma manyan mutanen Galili. Sa’ad da diyar Hiridiyas ta shigo, ta kuma yi rawa, sai ta gamshi Hiridus tare da baƙinsa. Sai Sarkin ya ce wa yarinyar, “Ki tambaye ni kome da kike so, ni kuwa zan ba ki.” Ya yi mata alkawari da rantsuwa cewa, “Duk abin da kika roƙa, zan ba ki, ko da rabin mulkina ne.” Sai ta fita ta ce wa mahaifiyarta, “Me zan roƙa?” Ta ce, “Kan Yohanna Mai Baftisma.” Nan da nan, sai yarinyar ta yi hanzari zuwa wajen sarki da roƙon, “Ina so ka ba ni kan Yohanna Mai Baftisma a cikin tasa, yanzu-yanzu nan.” Sai sarki ya yi baƙin ciki ƙwarai, amma saboda rantsuwar da kuma baƙinsa, bai so yă hana ta ba. Nan take, sai ya aiki mai aiwatar da kisa da umarni ya kawo kan Yohanna. Mutumin ya je ya yanke kan Yohanna a kurkuku. Ya kuma kawo kan a tasa ya ba yarinyar. Ita kuma ta ba wa mahaifiyarta.

Markus 12:14-17

Suka zo wurinsa suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci. Ba ka bin ra’ayin mutane, don ba ka nuna bambanci. Amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya. Daidai ne a biya wa Kaisar haraji, ko babu? Mu biya ko kada mu biya?” Amma Yesu ya san munafuncinsu, sai ya yi tambaya ya ce, ‹“Don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko? Ku kawo mini dinari in ga.”› Suka kawo masa kuɗin, sai ya tambaye, su ya ce, ‹“Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne wannan?”› Suka ce, “Na Kaisar.” Sai Yesu ya ce musu, ‹“Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku ba wa Allah kuma abin da yake na Allah.”› Suka yi mamakinsa ƙwarai.

Markus 13:7-8

‹Sa’ad da kuka ji labarun yaƙe-yaƙe da jita-jitar yaƙe-yaƙe, kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru. Amma ƙarshen tukuna.› ‹Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki kuma yă tasar wa mulki. Za a yi girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam, a kuma yi yunwa. Waɗannan dai mafarin azabar naƙuda.›

Markus 13:9-11

‹“Dole ku yi zaman tsaro. Za a ba da ku ga hukuma, a kuma bulale ku a majami’u. Saboda ni kuma, za ku tsaya a gaban gwamnoni da sarakuna, domin ku ba da shaida a gabansu.› ‹Dole sai an fara yin wa’azin bishara ga dukan al’ummai.› ‹Sa’ad da aka kama ku, aka kuma kai ku don a yi muku shari’a, kada ku damu da abin da za ku faɗa. Sai dai ku faɗi abin da aka ba ku a lokacin. Gama ba ku kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne.›

Markus 14:53-56

Suka kai Yesu wajen babban firist, sai dukan manyan firistoci, dattawa da kuma malaman dokoki suka taru. Bitrus ya bi shi daga nesa, har cikin filin gidan babban firist. A can, ya zauna tare da masu gadi, yana jin ɗumin wuta. Manyan firistoci da dukan ’yan Majalisa, suka shiga neman shaidar laifin da za a tabbatar a kan Yesu, domin su kashe shi. Amma ba su sami ko ɗaya ba. Da yawa suka ba da shaidar ƙarya a kansa, amma shaidarsu ba tă zo ɗaya ba.

Markus 14:63-65

Babban firist ya yage tufafinsa, ya yi ce, “Ina dalilin neman waɗansu shaidu kuma? Kun dai ji saɓon. Me kuka gani?” Duka suka yanke masa hukuncin kisa. Sai waɗansu suka fara tattofa masa miyau, suka rufe masa idanu, suka bubbuge shi da hannuwansu, suka ce, “Yi annabci!” Masu gadin kuma suka ɗauke shi, suka yi masa duka.

Markus 15:1-5

Da sassafe, sai manyan firistoci da dattawa, da malaman dokoki, da dukan Majalisa, suka yanke shawara. Suka daure Yesu, suka kai shi, suka miƙa shi ga Bilatus. Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kai ne Sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa ya ce, ‹“I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.”› Manyan firistoci suka zarge shi a kan abubuwa da yawa. Don haka Bilatus ya sāke tambayarsa ya ce, “Ba za ka amsa ba? Dubi abubuwa da yawa da suke zarginka da su.” Amma har yanzu, Yesu bai ba da amsa ba, Bilatus ya yi mamaki.

Markus 15:9

Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kuna so in sakar muku Sarkin Yahudawa?”

Markus 15:12-13

Bilatus ya tambaye su ya ce, “To, me zan yi da wanda kuke ce da shi, sarkin Yahudawa?” Suka yi ihu, suka ce, “A gicciye shi!”

Markus 15:15-20

Don son yă faranta wa taron rai, sai Bilatus ya sakar musu Barabbas. Ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye. Sojojin suka tafi da Yesu cikin fadar gwamna (wato, Firetoriyum), suka kira dukan kamfanin sojoji wuri ɗaya. Suka sa masa wata riga mai ruwan shunayya, suka kuma tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa. Sai suka fara ce masa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!” Suka dinga bugunsa a kā da sanda, suka tattofa masa miyau. Suka durƙusa suka yi masa bangirma na ba’a. Bayan da suka gama yin masa ba’a, suka tuɓe rigar mai ruwan shunayyar, suka sa masa nasa tufafi. Sai suka tafi da shi don a gicciye shi.

Markus 15:26

Akwai rubutu na zarginsa, da ya ce, Sarkin Yahudawa.

Markus 15:32

Bari wannan Kiristi, wannan Sarkin Isra’ila, yă sauko yanzu daga gicciye, don mu ga mu kuma gaskata.” Waɗanda aka gicciye tare da shi ma suka zazzage shi.

Luka 1:32-33

Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi gadon sarautar kakansa Dawuda, zai yi mulkin gidan Yaƙub har abada, mulkinsa kuma ba zai taɓa ƙare ba.”

Luka 2:1-3

A waɗancan kwanaki, Kaisar Augustus ya ba da doka cewa ya kamata a yi ƙidaya a dukan masarautar Roma. (Wannan ce ƙidaya ta fari da aka yi a lokacin da Kwiriniyus yake gwamnar Suriya.) Sai kowa ya koma garinsa don a rubuta shi.

Luka 3:1-2

A shekara ta goma sha biyar ta mulkin Kaisar Tiberiyus, a lokacin Buntus Bilatus ne gwamnar Yahudiya, Hiridus kuma yana sarautar Galili, ɗan’uwansa Filibus yana sarautar Ituriya da Tarakunitis, Lisaniyas kuma yana sarautar Abiline. A lokacin ne Annas da Kayifas suke manyan firistoci. Sai maganar Allah ta zo wa Yohanna, ɗan Zakariya a hamada.

Luka 3:19-20

Amma da Yohanna ya tsawata wa Hiridus mai mulki saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa, da kuma dukan sauran mugayen abubuwan da ya yi, Hiridus dai ya ƙara ɓata al’amarin. Ya sa a kulle Yohanna a kurkuku.

Luka 9:7-9

Yanzu fa, Hiridus mai sarauta ya ji labarin dukan abubuwan da suke faruwa. Sai ya rikice, don waɗansu mutane suna cewa, Yohanna Mai Baftisma ne ya tashi daga matattu, waɗansu kuma suna cewa, annabi Iliya ne ya sāke bayyana. Waɗansu kuma har wa yau, suna cewa, ɗaya daga cikin annabawa na dā ne, ya tashi. Amma Hiridus ya ce, “Yohanna dai na yanke kansa, amma wanne mutum ne nake jin labarin abubuwan nan a kansa?” Sai ya yi ƙoƙari ya ga Yesu.

Luka 11:49-50

‹Saboda haka, Allah a cikin hikimarsa ya ce, ‘Zan aika musu da annabawa da manzanni. Za su kashe waɗansu, su kuma tsananta wa waɗansu.’› ‹Saboda haka, alhakin jinin dukan annabawa da aka kashe, tun farkon duniya, yana kan wannan zamani,›

Luka 12:58

‹Yayinda kake kan hanyar zuwa kotu da maƙiyinka, ka yi matuƙar ƙoƙari ku shirya tun kuna kan hanya. In ba haka ba, zai kai ka gaban alƙali, alƙali kuma ya miƙa ka ga ɗan sanda, ɗan sanda kuma ya jefa ka a kurkuku.›

Luka 16:13

‹“Babu wani bawa mai iya bauta wa iyayengiji biyu ba. Ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗayan, ko kuwa ya dāge ga yi wa ɗaya bauta, sa’an nan ya rena ɗayan. Ba za ku iya ku bauta wa Allah tare da bauta wa Mammon (wato, Kuɗi) a lokaci ɗaya ba.”›

Luka 19:26-27

‹“Ya amsa ya ce, ‘Ina gaya muku, duk wanda yake da abu, za a ƙara masa. Amma wanda ba shi da shi kuwa, ko abin da yake da shi ma, za a karɓe.› ‹Amma waɗannan abokan gābana, waɗanda ba su so in zama sarkinsu ba, ku kawo su nan, ku karkashe su, a gabana.’ ”›

Luka 20:22-25

Daidai ne mu biya haraji ga Kaisar, ko babu?” Ya gane makircinsu, sai ya ce musu, ‹“Nuna mini dinari. Hoton wane ne, kuma rubutun wane ne a kai?”› Suka amsa, “Na Kaisar.” Sai ya ce musu, ‹“Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”›

Luka 21:12

‹“Amma kafin duk abubuwa nan, za a kama ku a tsananta muku. Za a kai ku majami’u, da kurkuku. Za a kuma kai ku gaban sarakuna da gwamnoni, kuma dukan waɗannan saboda sunana.›

Luka 22:30

‹Saboda ku ci, ku sha a teburina a cikin mulkina. Kuma ku zauna a kan gadon sarauta, ku yi wa kabilu goma sha biyu na Isra’ila shari’a.›

Luka 22:63-67

Mutanen da suke gadin Yesu suka fara masa ba’a da dūka. Suka rufe masa idanu suna tambaya cewa, “Ka yi annabci! Wa ya mare ka?” Suka kuma yi masa waɗansu baƙaƙen maganganu masu yawa. Da gari ya waye, sai majalisar dattawa na mutane, da manyan firistoci, da malaman dokoki, suka taru wuri ɗaya. Sai aka kawo Yesu a gabansu. Suka ce, “Ka faɗa mana, ko kai ne Kiristi?” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Ko na gaya muku, ba za ku gaskata ni ba,›

Luka 23:2-4

Suka fara zarginsa suna cewa, “Mun sami wannan mutum yana rikitar da al’ummarmu. Yana hana a biya haraji ga Kaisar. Yana kuma cewa, shi Kiristi ne, sarki kuma.” Sai Bilatus ya tambayi Yesu ya ce, “Kai ne sarkin Yahudawa?” Yesu ya amsa ya ce, ‹“I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.”› Sai Bilatus ya sanar wa manyan firistoci da taron ya ce, “Ni fa, ban sami wani ainihin abin zargi game wannan mutum nan ba.”

Luka 23:36-38

Sojoji su ma, suka zo suka yi masa ba’a. Suka miƙa masa ruwan tsami. Suka ce, “In kai ne sarkin Yahudawa, ka ceci kanka mana.” Bisa da shi kuma akwai rubutun da ya ce, Wannan shi ne Sarkin Yahudawa.

Yohanna 1:17

Gama an ba da doka ta wurin Musa; alheri da gaskiya kuwa sun zo ne ta wurin Yesu Kiristi.

Yohanna 1:49

Sai Natanayel ya ce, “Rabbi, kai Ɗan Allah ne. Kai ne Sarkin Isra’ila.”

Yohanna 3:1-3

Akwai wani Bafarisiye mai suna Nikodimus, wani ɗan majalisar Yahudawa. Ya zo wurin Yesu da dad dare ya ce, “Rabbi, mun sani kai malami ne daga Allah. Gama ba wanda zai iya yin waɗannan abubuwan banmamaki da kake yi in Allah ba ya tare da shi.” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.”›

Yohanna 5:16

To, domin Yesu yana yin waɗannan abubuwa a ranar Asabbaci, sai Yahudawa suka tsananta masa.

Yohanna 6:15

Da Yesu ya gane suna shirin su ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa kan dutsen shi kaɗai.

Yohanna 12:12-13

Kashegari babban taron da suka zo Bikin suka sami labari cewa Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima. Sai suka ɗaɗɗauko rassan dabino suka fiffita taryensa, suna ɗaga murya suna cewa, “Hosanna!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!” “Mai albarka ne Sarkin Isra’ila!”

Yohanna 18:33-39

Sai Bilatus ya koma cikin fada, ya kira Yesu ya tambaye shi, “Shin, kai ne sarkin Yahudawa?” Yesu ya yi tambaya ya ce, ‹“Wannan ra’ayin kanka ne, ko waɗansu ne suka yi maka magana game da ni?”› Bilatus ya amsa ya ce, “Ni mutumin Yahuda ne? Ai, mutanenka ne da kuma manyan firistoci suka bashe ka gare ni. Me ka yi?” Yesu ya ce, ‹“Mulkina ba na duniyan nan ba ne. Da na duniyan nan ne da bayina sun yi yaƙi su hana Yahudawa kama ni. Amma fa mulkina daga wani waje ne.”› Sai Bilatus ya ce, “To, wato, kai sarki ne!” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Haka yake, ni sarki ne yadda ka faɗa. Tabbatacce, saboda wannan dalili ne aka haife ni, kuma don wannan ne na zo duniya, domin in shaidi gaskiya. Duk wanda yake gefen gaskiya yakan saurare ni.”› Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Mece ce gaskiya?” Amma fa kuna da wata al’ada in lokacin Bikin Ƙetarewa ya yi, nakan sakar muku da ɗan kurkuku ɗaya. To, kuna so in sakar muku ‘sarkin Yahudawa’?”

Yohanna 19:3

Suka yi ta zuwa wurinsa suna cewa, “Ranka yă daɗe, sarkin Yahudawa!” Suna ta marinsa a fuska.

Yohanna 19:8-12

Da Bilatus ya ji haka, sai tsoro ya ƙara kama shi, sai ya sāke koma cikin fada. Ya tambayi Yesu, “Daga ina ka fito?” Amma Yesu bai amsa masa ba. Bilatus ya ce, “Ba za ka yi mini magana ba? Ba ka san cewa ina da ikon sakinka, ko gicciye ka ba?” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Ba ka da wani iko a kaina, in ba a ba ka daga sama ba. Saboda haka wanda ya bashe ni gare ka, ya fi na zunubi.”› Daga nan fa, Bilatus ya yi nemi yă saki Yesu, sai dai Yahudawa suka yi ta ihu suna cewa, “In ka saki wannan mutum, kai ba abokin Kaisar ba ne. Duk wanda ya ɗauka kansa a matsayin sarki, ai, yana gāba da Kaisar ne.”

Yohanna 19:14-15

Ranar Shirye-shiryen Makon Bikin Ƙetarewa ce kuwa, wajen sa’a ta shida. Sai Bilatus ya ce wa Yahudawa, “Ga sarkinku.” Amma suka yi ihu suka ce, “A yi da shi! A yi da shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce, “A! In gicciye sarkinku?” Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Mu dai, ba mu da wani sarki sai Kaisar.”

Yohanna 19:19-22

Bilatus ya sa aka rubuta wata sanarwa aka kafa a kan gicciyen. Abin da aka rubuta kuwa shi ne, Yesu Banazare, Sarkin Yahudawa. Yahudawa da yawa suka karanta wannan sanarwa, gama inda aka gicciye Yesu yana kusa da birni. An kuwa rubuta sanarwar da Arameyanci, Romanci da kuma Girik. Sai manyan firistocin Yahudawa suka ce, “A’a! Kada ka rubuta, ‘Sarkin Yahudawa,’ ka dai rubuta, wannan mutum ya ce shi sarkin Yahudawa ne.” Bilatus ya amsa ya ce, “Abin da na rubuta, na rubuta.”

Ayyukan Manzanni 4:18-21

Sai suka sāke kiransu ciki suka kuma umarce su kada su kuskura su yi magana ko su ƙara koyarwa a cikin sunan Yesu. Amma Bitrus da Yohanna suka amsa, “Ku shari’anta da kanku ko daidai ne a gaban Allah mu yi muku biyayya maimakon Allah. Gama ba za mu iya daina yin magana game da abin da muka gani muka kuma ji ba.” Bayan ƙarin barazana sai suka bar su su tafi. Ba su iya yanke shawara yadda za a hore su ba, domin dukan mutane suna yabon Allah saboda abin da ya faru.

Ayyukan Manzanni 4:23-29

Da aka sake su, Bitrus da Yohanna suka koma wajen mutanensu suka ba da labarin duk abin da manyan firistoci da dattawa suka faɗa musu. Sa’ad da suka ji wannan, sai suka ɗaga muryoyinsu gaba ɗaya cikin addu’a ga Allah, suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kai ka halicci sama da ƙasa da kuma teku, da kome da yake cikinsu. Ka yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki ta bakin bawanka, kakanmu Dawuda cewa, “ ‘Don me ƙasashe suke fushi, mutane kuma suke ƙulla shawara a banza? Sarakunan duniya sun ja dāgā, masu mulki kuma sun taru gaba ɗaya, suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa.’ Tabbatacce Hiridus da Buntus Bilatus suka haɗu tare da Al’ummai da kuma mutanen Isra’ila a wannan birni ce don su ƙulla gāba da bawanka mai tsarki Yesu, wanda ka shafe. Sun aikata abin da ikonka da kuma nufinka ya riga ya shirya tuntuni zai faru. Yanzu, Ubangiji, ka dubi barazanansu ka kuma sa bayinka su furta maganarka da iyakar ƙarfin hali.

Ayyukan Manzanni 5:17-18

Sai babban firist da dukan abokan aikinsa, waɗanda suke na ƙungiyar Sadukiyawa suka cika da kishi. Suka kama manzannin suka sa su a kurkukun da ake sa kowa da kowa.

Ayyukan Manzanni 5:19-29

Amma da dare wani mala’ikan Ubangiji ya buɗe ƙofofin kurkukun ya fitar da su. Ya ce, “Ku je ku tsaya a filin haikali ku sanar wa mutane cikakken saƙon wannan sabon rai.” Da gari ya waye, sai suka shiga filin haikali, yadda aka faɗa musu, suka kuwa fara koyar da mutane. Sa’ad da babban firist da abokan aikinsa suka iso, sai suka kira Majalisa gaba ɗaya dukan dattawan Isra’ila, suka kuma aika kurkuku a zo da manzannin. Amma da dogarawan suka iso kurkukun, ba su same su a can ba. Saboda haka suka dawo suka ba da labari, suka ce, “Mun iske kurkukun a kulle sosai, da masu gadi suna tsaye a bakin ƙofofin; amma da muka buɗe su, sai muka tarar ba kowa a ciki.” Da jin wannan labari, sai shugaban masu gadin haikali da manyan firistocin suka ruɗe, suna tunanin abin da wannan al’amari zai zama. Sai wani ya zo ya ce, “Ga shi! Mutanen da kuka sa a kurkuku suna tsaye a filin haikali suna koya wa mutane.” Da wannan, shugaban ya tafi tare da dogarawansa suka kawo manzannin. Sun kawo su amma fa ba ƙarfi da yaji ba, don suna tsoro kada mutane su jajjefe su da duwatsu. Da suka kawo manzannin, sai suka sa su suka bayyana a gaban Majalisar don babban firist ya tuhume su. Ya ce, “Mun kwaɓe ku da gaske kada ku ƙara koyarwa cikin wannan suna, duk da haka kun cika Urushalima da koyarwarku, har ma kuna so ku ɗora mana laifin jinin mutumin nan.” Bitrus da sauran manzannin suka amsa suka ce, “Dole ne mu yi wa Allah biyayya a maimakon mutane!

Ayyukan Manzanni 5:41

Manzannin suka bar Majalisar, suna farin ciki domin an ga sun cancanta a kunyata su saboda Sunan nan.

Ayyukan Manzanni 12:1-5

Kusan a wannan lokaci ne Sarki Hiridus ya kama waɗansu da suke na ikkilisiya, da niyya ya tsananta musu. Ya sa aka kashe Yaƙub, ɗan’uwan Yohanna, da takobi. Sa’ad da ya ga wannan ya faranta wa Yahudawa rai, sai ya kama Bitrus shi ma. Wannan ya faru kwanakin Bikin Burodi Marar Yisti. Bayan ya kama shi, sai ya sa shi a kurkuku, ya danƙa shi a hannun soja hurhuɗu kashi huɗu, don su yi gadinsa. Hiridus ya yi niyyar ya yi masa shari’a a gaban mutane bayan Bikin Ƙetarewa. Saboda haka aka tsare Bitrus a kurkuku, amma ikkilisiya ta nace da addu’a ga Allah dominsa.

Ayyukan Manzanni 12:6-17

A daren da in gari ya waye da Hiridus yake niyyar kawo shi domin a yi masa shari’a, Bitrus yana barci tsakanin sojoji biyu, daure da sarƙoƙi biyu, masu gadi kuma suna bakin ƙofa. Ba zato ba tsammani sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana haske kuma ya haskaka a ɗakin. Ya bugi Bitrus a gefe ya kuma tashe shi ya ce, “Maza, ka tashi!” Sarƙoƙin kuwa suka zube daga hannuwansa. Sa’an nan mala’ikan ya ce masa, “Ka sa rigunarka da takalmanka.” Bitrus kuwa ya sa. Mala’ikan ya faɗa masa cewa, “Ka yafa mayafinka ka bi ni.” Bitrus ya bi shi suka fita kurkukun, amma bai ma san cewa abin da mala’ikan yake yi tabbatacce ne ba; yana tsammani wahayi yake gani. Suka wuce masu gadi na fari da na biyu, suka kuma isa ƙofar ƙarfe ta shiga birni. Ƙofar kuwa ta buɗe musu da kanta, suka kuma wuce. Sa’ad da suka yi tafiya tsawon wani titi, nan take mala’ikan ya bar shi. Sai Bitrus ya dawo hankalinsa ya ce, “Yanzu na sani ba shakka Ubangiji ne ya aiki mala’ikansa yă cece ni daga hannun Hiridus da kuma dukan mugun fatan Yahudawa.” Da ya gane haka, sai ya tafi gidan Maryamu uwar Yohanna, wanda ake kuma kira Markus, inda mutane da yawa suka taru suna addu’a. Bitrus ya ƙwanƙwasa ƙofar waje, sai wata mai aiki a gidan da ake kira Roda ta zo tă ji ko wane ne. Da ta gane muryar Bitrus, ta cika da murna ta gudu ta koma ba tare da ta buɗe ƙofar ba, sai ta koma a guje ta ce da ƙarfi, “Ga Bitrus a bakin ƙofa!” Sai suka ce mata, “Kina hauka.” Da ta nace cewa shi ne, sai suka ce, “To, lalle, mala’ikansa ne.” Amma Bitrus ya yi ta ƙwanƙwasawa. Da suka buɗe ƙofar suka kuma gan shi, sai suka yi mamaki. Bitrus ya yi musu alama da hannunsa su yi shiru sai ya bayyana yadda Ubangiji ya fitar da shi daga kurkuku. Ya ce, “Ku gaya wa Yaƙub da kuma ’yan’uwa game da wannan,” sa’an nan ya tashi ya tafi wani wuri.

Ayyukan Manzanni 12:18-19

Da safe, hargitsin da ya tashi tsakanin sojojin ba ƙarami ba ne, a kan abin da ya sami Bitrus. Bayan Hiridus ya neme shi bai same shi ba, sai ya tuhumi masu gadin, ya kuma ba da umarni a kashe su.

Ayyukan Manzanni 12:20-23

Yana da rashin jituwa da mutanen Taya da na Sidon; sai suka haɗa kai suka nemi ganawa da shi. Bayan suka sami goyon bayan Bilastus, amintaccen bawan sarki, sai suka nemi salama, domin sun dogara ga ƙasar sarkin don samun abincinsu. A ranar da aka shirya Hiridus, sanye da kayan sarautarsa, ya zauna a gadon sarautarsa ya kuma ya wa mutanen jawabi. Suka tā da murya suka ce, “Wannan muryar wani allah ne, ba ta mutum ba.” Nan take, domin Hiridus bai yi wa Allah yabo ba, wani mala’ikan Ubangiji ya buge shi, tsutsotsi kuwa suka cinye shi ya kuma mutu.

Ayyukan Manzanni 16:22-24

Sai taron suka fāɗa wa Bulus da Sila gaba ɗaya, alƙalan kuwa suka yi umarni a tuɓe su a kuma yi musu dūka. Bayan an yi musu bulala sosai, sai aka jefa su cikin kurkuku, aka umarci mai gadin kurkukun yă tsare su da kyau. Da karɓan irin umarnan nan, sai ya sa su can cikin ɗakin kurkuku na ciki-ciki, kuma ya ɗaura ƙafafunsu a turu.

Ayyukan Manzanni 16:25-30

Wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu’a suna rera waƙoƙi ga Allah, sauran ’yan kurkuku kuwa suna sauraronsu. Ba zato ba tsammani sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa har tushen ginin kurkukun ya jijjiga. Nan da nan sai duk ƙofofin kurkukun suka bubbuɗe, sarƙoƙin kowa kuma suka ɓaɓɓalle. Mai gadin kurkukun ya farka daga barci, sa’ad da ya ga ƙofofin kurkukun a buɗe, sai ya zāre takobinsa yana shirin kashe kansa domin ya ɗauka ’yan kurkukun sun gudu. Amma Bulus ya yi ihu ya ce, “Kada ka yi wa kanka lahani! Dukanmu muna nan!” Mai gadin kurkukun ya kira a kawo fitilu, ya ruga ciki ya fāɗi yana rawan jiki a gaban Bulus da Sila. Sai ya fito da su waje ya kuma tambaye su ya ce, “Ranku yă daɗe, me zan yi domin in sami ceto?”

Ayyukan Manzanni 16:35-40

Da gari ya waye, sai alƙalan suka aika ma’aikatansu wajen mai gadin kurkukun da umarni cewa, “Ka saki mutanen nan.” Sai mai gadin kurkukun ya gaya wa Bulus cewa, “Alƙalai sun ba da umarni a sake ku kai da Sila. Yanzu sai ku tafi. Ku sauka lafiya.” Amma Bulus ya ce wa ma’aikatan, “Sun yi mana dūka a fili ba tare da shari’a ba, ko da yake mu ’yan ƙasar Roma ne, suka kuma jefa mu cikin kurkuku. Yanzu suna so su fitar da mu a ɓoye? A’a! Sai dai su zo da kansu su rako mu waje.” Sai ma’aikatan suka faɗa wa alƙalan wannan, da suka ji cewa Bulus da Sila Romawa ne, sai suka ji tsoro. Sai suka zo don su roƙe su, suka yi musu rakiya daga kurkukun, suna roƙonsu su bar birnin. Bayan Bulus da Sila suka fita daga kurkukun, sai suka tafi gidan Lidiya, inda suka sadu da ’yan’uwa suka kuma ƙarfafa su. Sa’an nan suka tafi.

Ayyukan Manzanni 17:6-8

Amma da ba su same su ba, sai suka ja Yason da waɗansu ’yan’uwa zuwa gaban mahukuntan birnin, suna ihu suna cewa, “Waɗannan mutanen da suke tā da fitina ko’ina a duniya sun iso nan, Yason kuwa ya karɓe su a gidansa. Dukansu suna karya dokokin Kaisar, suna cewa akwai wani sarki, wanda ake kira Yesu.” Da suka ji haka, sai hankalin taron da na mahukuntan birnin ya tashi.

Ayyukan Manzanni 17:26

Daga mutum ɗaya, ya halicci kowace al’ummar mutane, don su zauna a duk duniya; shi ne kuma ya ƙaddara lokuta bisa ga tsarinsu da kuma inda za su kasance.

Ayyukan Manzanni 22:24-30

sai shugaban ƙungiyar sojan ya umarta a kai Bulus a barikin soja. Ya ba da umarni a yi masa bulala a kuma tambaye shi abin da ya sa mutane suke masa ihu haka. Suna kwantar da shi ke nan domin a yi masa bulala, sai Bulus ya ce wa jarumin da yake tsaye a nan, “Ashe, daidai ne bisa ga doka a yi wa ɗan ƙasar Roma bulala wanda ba a ma tabbatar da laifi a kansa ba?” Da jarumin ya ji haka sai ya je wurin shugaban ƙungiyar sojan ya ce masa, “Me kake so yi ne? Wannan mutum ɗan ƙasar Roma ne.” Sai shugaban ƙungiyar sojan ya je ya tambayi Bulus ya ce, “Faɗa mini, kai ɗan ƙasar Roma ne?” Bulus ya ce, “I.” Sai shugaban ƙungiyar sojan ya ce, “Sai da na biya kuɗi mai yawa kafin in zama ɗan ƙasa.” Bulus ya ce, “Ni kuwa an haife ni ɗan ƙasa.” Waɗanda dā suke shirin yin masa tambayoyi suka ja da baya nan da nan. Shugaban ƙungiyar sojan kansa ya tsorata da ya fahimci cewa ya sa wa Bulus, ɗan ƙasar Roma sarƙa. Kashegari da yake shugaban ƙungiyar sojan ya so yă tabbatar da ainihin abin da ya sa Yahudawa suke zargin Bulus, sai ya sake shi ya kuwa umarci manyan firistoci da dukan Majalisar su taru. Sa’an nan ya kawo Bulus ya sa ya tsaya a gabansu.

Ayyukan Manzanni 23:1-5

Bulus ya zuba wa Majalisar ido ya ce, “’Yan’uwana, na cika aikina ga Allah cikin lamiri mai kyau har yă zuwa yau.” Da jin wannan Ananiyas babban firist ya umarci waɗanda suke tsaye kusa da Bulus su buge bakinsa. Sai Bulus ya ce masa, “Allah zai buge ka, kai farin bango! Ka zauna a can kana hukunta ni bisa ga doka, ga shi kai kanka kana ƙetare dokar ta wurin ba da umarni a buge ni!” Waɗanda suke tsaye kusa da Bulus kuwa suka ce masa, “Babban firist na Allah za ka zaga?” Bulus ya amsa ya ce, “’Yan’uwa, ai, ban san cewa shi ne babban firist ba; gama yana a rubuce cewa, ‘Kada ka yi mugun magana game da mai mulkin mutanenka.’”

Ayyukan Manzanni 23:6-10

Bulus, da ya gane cewa waɗansu daga cikinsu Sadukiyawa ne sauran kuma Farisiyawa ne, sai ya ɗaga murya a Majalisar ya ce, “’Yan’uwana, ni Bafarisiye ne, ɗan Farisiyawa. Ana mini shari’a saboda begen da nake da shi a kan tashin matattu.” Da ya faɗi haka, sai gardama ta tashi tsakanin Farisiyawa da Sadukiyawa, taron kuwa ya rabu biyu. (Sadukiyawa suna cewa babu tashin matattu, babu mala’iku ko ruhohi. Amma Farisiyawa kuwa sun tsaya a kan cewa duk akwai.) Aka yi babbar hayaniya. Waɗansu daga cikin malaman dokokin da suke Farisiyawa suka miƙe tsaye suka yi gardama mai ƙarfi suna cewa, “Ba mu sami wani laifi a wurin mutumin nan ba. A ce wani ruhu ko mala’ika ne ya yi masa magana fa?” Gardamar kuwa ta yi tsanani har shugaban ƙungiyar sojan ya ji tsoro za su yayyage Bulus. Ya umarci sojoji su tafi su ƙwace shi ƙarfi da yaji daga wurinsu su kawo shi cikin barikin soja.

Ayyukan Manzanni 25:6-12

Bayan ya yi kwanaki takwas ko goma tare da su, sai ya gangara zuwa Kaisariya, kashegari kuma ya kira a yi zaman kotu ya kuma umarta a kawo Bulus a gabansa. Da Bulus ya bayyana, sai Yahudawan da suka gangaro daga Urushalima suka tsaya kewaye shi, suna kawo ƙarar masu tsanani da yawa a kansa, waɗanda ba su iya tabbatarwa ba. Sa’an nan Bulus ya kāre kansa ya ce, “Ban aikata wani laifi game da dokokin Yahudawa ko game da haikali ko kuma game da Kaisar ba.” Festus, da yake yana so yă yi wa Yahudawa alfarma, sai ya ce wa Bulus, “Ka yarda ka je Urushalima a yi maka shari’a a can a gabana a kan waɗannan zarge?” Bulus ya amsa ya ce, “Yanzu ina tsaye a gaban kotun Kaisar, inda ya kamata a yi mini shari’a. Ban yi wani laifi ga Yahudawa ba, kai da kanka ma ka san da haka sarai. In kuwa ina da wani laifin da ya isa kisa, ban ƙi in mutu ba. Amma in ƙarar da waɗannan Yahudawa suka kawo a kaina ba gaskiya ba ne, ba wanda yake da iko ya ba da ni a gare su. Na ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar!” Bayan Festus ya yi shawara da majalisarsa sai ya ce, “Ka ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar. To, ga Kaisar kuwa za ka tafi!”

Ayyukan Manzanni 25:20-21

Na rasa yadda zan bincike irin abubuwan nan; saboda haka na yi tambaya ko zai yarda ya tafi Urushalima a yi masa shari’a a can game da waɗannan zargi. Da Bulus ya ɗaukaka ƙara zuwa gaban Babban Sarki sai na umarta a tsare shi har kafin in aika shi zuwa ga Kaisar.”

Ayyukan Manzanni 26:25-32

Bulus ya amsa ya ce, “Ba na hauka, ya mafifici Festus. Abin da nake faɗi gaskiya ne da kuma mai kyau. Sarki ya san waɗannan abubuwa, ina kuma iya yin magana da shi a sake. Na tabbata cewa ba ɗaya daga cikin waɗannan da ya kuɓuce saninsa, domin ba a ɓoye aka yi shi ba. Sarki Agiriffa ka gaskata da annabawa? Na san ka gaskata.” Sai Agiriffa ya ce wa Bulus, “Kana tsammani cewa a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kana so ka mai da ni Kirista?” Bulus ya amsa ya ce, “Ko a ɗan lokaci, ko a lokaci mai yawa, ina addu’a ga Allah cewa, ba kai kaɗai ba amma duk waɗanda suke saurare ni a yau su zama abin da nake, sai dai ban da sarƙoƙin nan.” Sai sarki ya tashi, haka kuma gwamna da Bernis da kuma waɗanda suke zaune tare da su. Suka bar ɗakin, kuma yayinda suke magana da juna, sai suka ce, “Wannan mutum ba ya yin kome da ya isa kisa ko dauri.” Sai Agiriffa ya ce wa Festus, “Da ba don wannan mutum ya ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar ba da an sake shi.”

Ayyukan Manzanni 27:23-24

Jiya da dare wani mala’ikan Allahn da nake nasa nake kuma bauta wa ya tsaya kusa da ni ya ce, ‘Kada ka ji tsoro, Bulus. Lalle za ka tsaya a gaban Kaisar a yi maka shari’a; Allah kuma cikin alherinsa ya ba ka dukan rayukan mutanen da suke tafiya tare da kai.’

Ayyukan Manzanni 28:16-19

Da muka isa Roma, sai aka yarda wa Bulus yă zauna shi kaɗai, tare da sojan da zai yi gadinsa. Bayan kwana uku sai ya kira taron shugabannin Yahudawa. Da suka taru, Bulus ya ce musu, “’Yan’uwana, ko da yake ban yi wa mutanenmu wani laifi ba ko kuma wani abu game da al’adun kakanninmu, aka kama ni a Urushalima aka kuma ba da ni ga Romawa. Suka tuhume ni suka kuma so su sake ni, domin ba a same ni da wani laifin da ya cancanci kisa ba. Amma da Yahudawa suka ƙi, sai ya zama mini dole in ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar ba don ina da wani zargin da zan kawo game da mutanena ba.

Romawa 13:1-7

Dole kowa yă yi biyayya ga masu mulki, gama babu wani iko sai ko in Allah ya yarda. Duk hukumomin da muke su, naɗin Allah ne. Saboda haka, duk wanda ya yi tawaye ga hukuma yana yin tawaye da abin da Allah ya naɗa ne, waɗanda kuwa suke aikata haka, za su jawo wa kansu hukunci. Gama masu mulki ba abin tsoro ba ne ga waɗanda suke yin abin da yake daidai, sai dai ga waɗanda suke aikata laifi. Kana so ka rabu da jin tsoron wanda yake mulki? To, sai ka aikata abin da yake daidai, zai kuwa yabe ka. Gama shi bawan Allah ne don kyautata rayuwarka. Amma in ka aikata mugunta, to, sai ka ji tsoro, don ba a banza ne shugaba yake ɗaukan takobinsa ba. Shi fa bawan Allah ne, ta wurinsa ne fushin Allah yakan hukunta masu laifi. Saboda haka, dole a yi biyayya ga hukumomi, ba don gudun horo kawai ba amma don lamirinku. Shi ne ma ya sa kuke biyan haraji, gama hukumomin nan bayin Allah ne, waɗanda suke ba da dukan lokacinsu don aikin shugabanci. Ku ba wa kowa hakkinsa. In kuna da bashin haraji, sai ku biya; in kuɗin shiga ne, ku biya kuɗin shiga; in ladabi ne, ku yi ladabi; in kuma girmamawa ne, ku ba da girma.

1 Korintiyawa 2:6-8

Duk da haka, muna sanar da saƙon hikima cikin waɗanda suka balaga, amma ba hikima irin ta wannan zamani ba ne, ko kuwa irin ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda za su shuɗe ba. A’a, muna magana ne a kan asirin hikimar Allah, hikimar da tun dā, take a ɓoye, wadda Allah ya ƙaddara domin ɗaukakarmu, tun kafin farkon zamanai. Ba ko ɗaya daga cikin masu mulkin wannan zamani da ya fahimce ta, gama da a ce sun fahimce ta, da ba su gicciye Ubangiji mai ɗaukaka ba.

1 Korintiyawa 6:12

“Ina da dama in yi kome,” sai dai ba kome ba ne yake da amfani. “Ina da dama in yi kome” sai dai ba abin da zai mallake ni.

1 Korintiyawa 10:23

“Ana da dama a yi kome” sai dai ba kome ba ne yake da amfani. “Ana da dama a yi kome” sai dai ba kome ba ne mai ginawa.

1 Korintiyawa 15:24-25

Sa’an nan sai ƙarshen ta zo, sa’ad da zai miƙa wa Allah Uba mulki, bayan ya hallaka dukan sarauta, mulki da iko. Gama dole yă yi mulki har sai ya sa dukan abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa.

Galatiyawa 3:28-29

Babu bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, bawa da ’yantacce, namiji da ta mace, gama dukanku ɗaya ne cikin Kiristi Yesu. In kuwa ku na Kiristi ne, to, ku zuriyar Ibrahim ne, magāda kuma bisa ga alkawarin nan.

Galatiyawa 4:30-31

Amma me Nassi ya ce? Nassi ya ce, “Kori macen nan ’yar aikin gida da ɗanta don ɗan mace ’yar aikin gida ba zai taɓa raba gādo tare da ɗa na ainihin matarka ba.” Saboda haka, ’yan’uwa, mu ba ’ya’yan mace ’yar aikin gida ba ne, amma na ainihin matan gidan ne.

Galatiyawa 5:1

Saboda ’yanci ne Kiristi ya ’yantar da mu. Sai ku tsaya daram, kada ku yarda ku sāke komawa ƙarƙashin nauyin bauta.

Galatiyawa 5:14

Dukan doka an taƙaita a cikin umarni ɗaya ne cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”

Galatiyawa 5:22-23

Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.

Afisawa 1:21-22

Yanzu yana mulki a kan dukan masu sarauta, da masu iko, da masu ƙarfi, da kuma masu mulki. Yana mulkin kome a wannan duniya, zai kuma yi mulkin duniya mai zuwa. Allah ya sa kome a ƙarƙashin ikonsa, ya kuma ba shi iko a kan kome don amfanin ikkilisiya.

Afisawa 2:12

Ku kuma tuna a lokacin ba ku san Kiristi ba. A ware kuke daga mutanen Isra’ila, ba ku kuma da dangantaka da alkawaran da Allah ya yi da su. Kun yi zama a duniyan nan babu bege kuma babu Allah.

Afisawa 2:19

Don haka, yanzu ku ba baƙi ba ne, ku kuma ba bare ba ne. Ku ’yan ƙasa ne tare da mutanen Allah, iyalin gidan Allah kuma.

Afisawa 6:12

Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama.

Filibbiyawa 2:9-11

Saboda haka Allah ya ɗaukaka shi zuwa mafificin wuri ya kuma ba shi sunan da ya fi dukan sunaye, don a sunan Yesu kowace gwiwa za tă durƙusa, a sama da a ƙasa da kuma a ƙarƙashin ƙasa, kowane harshe kuma yă furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne, don ɗaukakar Allah Uba.

Filibbiyawa 3:20

Amma mu ’yan mulkin sama ne. Muna kuma jira zuwan Mai Ceto daga can, Ubangiji Yesu Kiristi,

Kolossiyawa 1:16

Ta wurinsa aka halicci dukan abu, abubuwan da suke cikin sama da abubuwan da suke a duniya, waɗanda ake gani, da waɗanda ba a gani, ko kursiyoyi ko ikoki ko masu mulki ko hukumomi; an halicci dukan abu ta wurinsa da kuma dominsa ne.

Kolossiyawa 2:8

Ku lura kada wani yă ruɗe ku da ilimin banza da wofi. Wannan koyarwa ta mutane ce kawai. Ta fito daga ikokin wannan duniya ne ba daga Kiristi ba.

1 Timoti 1:8-10

Mun san cewa doka tana da kyau in an yi amfani da ita yadda ya kamata. Mun kuma san cewa an yi doka ba domin masu adalci ba sai dai masu tawaye, da marasa biyayya, da marasa bin Allah, da masu zunubi, da marasa tsarkaka, da masu saɓon Allah, da masu kashe iyaye maza da mata, da masu kisankai, da masu zina da kuma da maza masu kwana da maza, ko mata masu kwana da mata, da masu cinikin bayi da masu ƙarya da kuma masu shaidar ƙarya, da kuma duk wani abin da ya saɓa wa sahihiyar koyarwa,

1 Timoti 1:17

Bari girma da ɗaukaka su tabbata har abada abadin ga Sarki madawwami, wanda ba ya mutuwa, wanda ba a ganinsa, wanda kuma shi ne kaɗai Allah! Amin.

1 Timoti 2:1-2

Da farko dai, ina gargaɗe ku cewa a yi roƙe-roƙe, ana addu’o’i, ana yin addu’a a madadin waɗansu da kuma a yi godiya saboda kowane mutum da sarakuna da dukan masu mulki, domin mu zauna lafiya, rai kuma kwance, muna bin Allah sosai a cikin natsuwa.

1 Timoti 6:15

wanda Allah zai kawo a daidai lokaci, Allah, mai albarka wanda yake kaɗai Mai Mulki, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji,

2 Timoti 2:12

in muka jimre, za mu yi mulki tare da shi. In muka yi mūsunsa, shi ma zai yi mūsunmu;

Titus 3:1-2

Ka tuna wa mutane su zama masu biyayya ga masu mulki da kuma hukumomi, su zama masu biyayya suna kuma a shirye su yi kowane abin da yake mai kyau, kada su zama masu ɓata sunan kowa, su zama masu salama da kulawa, su kuma zama masu matuƙar tawali’u ga dukan mutane.

Ibraniyawa 1:8

Amma game da Ɗan ya ce, “Kursiyinka, ya Allah, zai kasance har abada abadin, adalci kuma zai zama sandan mulkinka.

Ibraniyawa 8:1-2

Abin da muke magana a nan shi ne, muna da irin wannan babban firist, wanda ya zauna a hannun dama na kursiyin Maɗaukaki a sama, wanda yake hidima a cikin wuri mai tsarki, tabanakul na gaskiya wanda Ubangiji ne ya kafa, ba mutum ba.

Ibraniyawa 11:36-38

Waɗansu suka sha ba’a da bulala, har da dauri da sarƙa, da kuma jefa su cikin kurkuku. Aka jajjefe su da duwatsu; aka raba su biyu da zarto; aka kashe su da takobi. Suka yi ta yawo saye da fatun tumaki da na awaki, suka yi zaman rashi, suka sha tsanani da kuma wulaƙanci duniya ba tă ma cancanci su zauna a cikinta ba. Suka yi ta yawo a cikin hamada da a kan duwatsu, da cikin kogwanni da kuma cikin ramummuka.

Ibraniyawa 13:17

Ku yi wa shugabanninku biyayya ku kuma miƙa kanku ga ikonsu. Suna lura da ku kuma za su ba da lissafi a gaban Allah. Saboda haka kada ku sa su yi fushi saboda aikinsu, ku sa su yi farin ciki. In ba haka ba za su iya taimakonku ba ko kaɗan.

1 Bitrus 2:9

Amma ku zaɓaɓɓu ne, ƙungiyar firistocin babban Sarki, al’umma mai tsarki, jama’a mallakar Allah, domin ku shaida yabon shi wanda ya kira ku daga cikin duhu zuwa haskensa mai banmamaki.

1 Bitrus 2:11-18

Abokaina ƙaunatattu, ina roƙonku, a matsayin bare da kuma baƙi a duniya, ku rabu da sha’awace-sha’awacen zunubin da suke yaƙi da ranku. Ku yi irin rayuwa mai kyau a cikin masu bautar gumaka, yadda ko da sun zarge ku da yin laifi, za su iya ganin ayyukanku nagari, su ɗaukaka Allah a ranar da zai ziyarce mu. Saboda Ubangiji, ku yi biyayya ga kowace hukumar da aka kafa cikin mutane, ko ga sarki, a matsayi wanda ya fi iko, ko ga gwamnoni, waɗanda ya aika domin su hukunta masu laifi su kuma yabi masu aikata abin da yake daidai. Gama nufin Allah ne cewa ta wurin yin nagarta za ku toshe jahilcin marasa azanci. Ku yi rayuwa kamar mutanen da aka ’yantar, sai dai kada ku yi amfani da ’yancinku a matsayin hujjar aikata mugunta; ku yi rayuwa kamar bayin Allah. Ku nuna ladabin da ya dace ga kowa. Ku ƙaunaci ’yan’uwantakar masu bi, ku ji tsoron Allah, ku girmama sarki. Bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku da matuƙar ladabi, ba kawai ga waɗanda suke da kirki da masu sauƙinkai ba, amma har ga masu zafin rai ma.

2 Bitrus 2:6-8

in har ya hukunta biranen Sodom da Gomorra ta wurin ƙone su suka zama toka, ya kuma maishe su misali na abin da zai faru da marasa tsoron Allah; in kuwa har ya ceci Lot, mai adalci, wanda ya damu ainun da ƙazamar rayuwar mutane marasa bin doka; (adon kuwa abin da adalin nan ya yi, ya kuma gani, sa’ad da yake a cikinsu, sai kowace rana yakan ji ciwon aikinsu na kangara a zuciyarsa mai adalci)

2 Bitrus 2:10-11

Wannan gaskiya ce musamman ga waɗanda suke bin sha’awace-sha’awacen lalaci na mutuntaka, suna kuma rena masu mulki. Da ƙarfin hali da kuma girman kai, waɗannan mutane ba sa tsoro kawo zargin ɓata sunan talikan sama; duk da haka ko mala’iku ma da suka fi su ƙarfi suka kuma fi su iko, ba sa kawo irin wannan zargi na ɓata suna game da waɗannan talikai a gaban Ubangiji.

1 Yohanna 3:4

Duk mai yin zunubi yana karya doka ne; tabbatacce, zunubi, karya doka ne.

Yahuda 1:8

Haka yake da masu mafarke-mafarken nan, gama sun ƙazantar da jikunansu, suka ƙi bin masu mulki, suna ɓata sunan talikan sararin sama.

Ru’uya ta Yohanna 1:4-6

Daga Yohanna, Zuwa ga ikkilisiyoyi bakwai da suke a lardin Asiya. Alheri da salama gare ku daga shi wanda yake a yanzu, wanda yake a dā, da kuma wanda zai zo, da kuma daga ruhohi bakwai da suke a gaban kursiyinsa, da kuma daga Yesu Kiristi, wanda yake amintaccen shaida, ɗan farin daga tashin matattu, da kuma mai mulkin sarakunan duniya. Gare shi wanda yake ƙaunarmu wanda kuma ya ’yantar da mu daga zunubanmu ta wurin jininsa, ya kuma mai da mu masarauta da firistoci don mu yi wa Allahnsa da Ubansa hidima, a gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin! Amin.

Ru’uya ta Yohanna 3:21

‹Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon zama tare da ni a kursiyina, kamar yadda na ci nasara, kuma ina zaune tare da Ubana a kursiyinsa.›

Ru’uya ta Yohanna 4:2-6

Nan da nan sai ga ni cikin Ruhu, a can a gabana kuwa ga kursiyi a cikin sama da wani zaune a kansa. Wannan mai zama a can kuwa yana da kamannin dutsen yasfa da karneliya. Bakan gizo, mai kama da zumurrudu, ya kewaye kursiyin. Kewaye da kursiyin kuwa akwai waɗansu kursiyoyi ashirin da huɗu, zaune a kansu kuwa dattawa ashirin da huɗu ne. Suna saye da fararen tufafi suna kuma da rawanin zinariya a kawunansu. Daga kursiyin hasken walƙiya yana ta fitowa, da ƙararraki da kuma tsawa. A gaban kursiyin, fitilu bakwai suna ci. Waɗannan ne ruhohi bakwai na Allah. Haka kuma a gaban kursiyin akwai wani abu mai kama da tekun gilashi, yana ƙyalli kamar madubi. A tsakiya kuwa, kewaye da kursiyin, akwai halittu huɗu masu rai, cike kuma suna da idanu gaba da baya.

Ru’uya ta Yohanna 4:9-10

Duk lokacin da halittu masu ran nan suka rera ɗaukaka, girma da kuma godiya ga wannan wanda yake zaune a kan kursiyin da kuma wanda yake mai rai har abada abadin, sai dattawa ashirin da huɗun nan su fāɗi a ƙasa a gaban wannan wanda yake zaune a kursiyin, su yi sujada wa wannan wanda yake da rai har abada abadin. Sukan ajiye rawaninsu a gaban kursiyin suna cewa,

Ru’uya ta Yohanna 5:10-13

Ka mai da su masarauta da kuma firistoci, don su yi wa Allahnmu hidima, kuma za su yi mulki a duniya.” Sai na duba na kuma ji muryar mala’iku masu yawa, yawansu kuwa ya kai dubu dubbai, da kuma dubu goma sau dubu goma. Suka kewaye kursiyin da halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan. Da babbar murya suka rera, “Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka kashe, don yă sami iko da wadata da hikima da ƙarfi da girma da ɗaukaka da kuma yabo!” Sa’an nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa, “Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon yabo da girma da ɗaukaka da iko, sun tabbata har abada abadin!”

Ru’uya ta Yohanna 7:9-11

Bayan wannan sai na duba, can a gabana kuwa ga wani taro mai girma, wanda ba mai iya ƙirgawa, daga kowace al’umma, kabila, mutane da kuma harshe, suna tsaye a gaban kursiyin da kuma gaban Ɗan Ragon nan. Suna saye da fararen tufafi suna kuma riƙe da rassan dabino a hannuwansu. Suka tā da murya da ƙarfi suna cewa, “Ceto na Allahnmu ne, wanda yake zaune a bisan kursiyi, da kuma na Ɗan Ragon.” Dukan mala’iku suna tsaye kewaye da kursiyin da kuma kewaye da dattawan tare da halittu huɗun nan masu rai. Suka fāɗi da fuskokinsu ƙasa a gaban kursiyin suka kuma yi wa Allah sujada,

Ru’uya ta Yohanna 7:15

Saboda haka, “suna a gaban kursiyin Allah suna masa hidima dare da rana a cikin haikalinsa; kuma wannan mai zaune a kursiyin zai shimfiɗa tentinsa a bisansu.

Ru’uya ta Yohanna 11:15-18

Mala’ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji muryoyi masu ƙarfi a sama da suka ce, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Kiristinsa, zai kuwa yi mulki har abada abadin.” Sai dattawan nan ashirin da huɗu da suke zaune a kursiyoyinsu a gaban Allah, suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa suka kuma yi wa Allah sujada, suna cewa, “Muna maka godiya ya Ubangiji Allah, Maɗaukaki, wanda yake a yanzu, shi ne kuma a dā, domin ka karɓi ikonka mai girma ka kuma fara mulki. Al’ummai suka yi fushi; fushinka kuwa ya zo. Lokaci ya yi don a shari’anta matattu, da kuma don sākawa wa bayinka annabawa da tsarkakanka da kuma su waɗanda suke girmama sunanka, ƙarami da babba, don kuma hallakar da waɗanda suka hallaka duniya.”

Ru’uya ta Yohanna 13:1-2

Macijin kuwa ya tsaya a bakin teku. Sai na ga wata dabba tana fitowa daga teku. Tana da ƙahoni goma da kawuna bakwai, da kuma rawani goma a ƙahoninta, a kowane kai kuwa akwai sunan saɓo. Dabbar da na gani ta yi kamar damisa, amma tana da ƙafafu kamar na beyar, bakinta kuma ya yi kamar na zaki. Macijin nan ya ba wa dabbar ƙarfinsa da gadon sarautarsa da kuma ikonsa mai girma.

Ru’uya ta Yohanna 14:8

Mala’ika na biyu ya biyo yana cewa, “Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi, wadda ta sa dukan al’ummai suka sha ruwan inabin hauka na zinanta.”

Ru’uya ta Yohanna 16:19-20

Babban birnin ya rabu kashi uku, biranen al’ummai kuma suka rurrushe. Allah ya tuna da Babilon Mai Girma ya kuma ba ta kwaf cike da ruwan inabin fushinsa. Kowane tsibiri ya gudu ba a kuwa ƙara ganin duwatsu ba.

Ru’uya ta Yohanna 17:1-2

Ɗaya daga cikin mala’iku bakwai masu ɗauke da kwanoni bakwai nan, ya zo ya ce mini, “Zo, zan nuna maka hukuncin babbar karuwan nan da take zaune a bisan ruwaye masu yawa. Da ita ce sarakunan duniya suka yi zina mazaunan duniya kuma suka bugu da ruwan inabin zinace zinacenta.”

Ru’uya ta Yohanna 17:9-13

“Wannan yana bukata hankali da kuma hikima. Kawuna bakwai nan tuddai bakwai ne da macen take zama a kai. Sarakuna bakwai ne kuma. Biyar sun fāɗi, ɗaya yana nan, ɗayan kuma bai zo ba tukuna; amma sa’ad da ya zo, zai kasance na ɗan lokaci. Dabbar da a dā ta taɓa kasancewa, amma yanzu ba ta, ita ce sarki na takwas. Ita ɗaya ce cikin bakwai ɗin, kuma tana tafiya zuwa ga hallakarta. “Ƙahonin nan goma da ka gani sarakuna goma ne da ba su riga sun karɓi mulki ba, amma waɗanda na sa’a guda za su karɓi iko a matsayin sarakuna tare da dabbar. Suna da manufa guda za su kuma ba wa dabbar ikonsu da kuma sarautarsu.

Ru’uya ta Yohanna 17:14-18

Za su yi yaƙi da Ɗan Ragon, sai dai Ɗan Ragon zai ci nasara a bisansu domin shi ne Ubangijin iyayengiji, Sarkin sarakuna, tare da shi kuwa kirayayunsa, zaɓaɓɓunsa da kuma amintattu masu binsa za su kasance.” Sa’an nan mala’ikan ya ce mini, “Ruwayen da ka gani, inda karuwan take zama, jama’a ce, taro masu yawa, al’ummai da kuma harsuna. Dabbar da kuma ƙahoni goma da ka gani za su ƙi jinin karuwar. Za su kai ta ga hallaka su kuma bar ta tsirara; za su ci namanta su kuma ƙone ta da wuta. Gama Allah ya sa a zukatansu su cika nufinsa ta wurin yarda su ba wa dabbar ikonsu tă yi mulki, sai lokacin da kalmomin Allah sun cika. Macen da ka gani ita ce babban birnin da yake mulki a bisan sarakunan duniya.”

Ru’uya ta Yohanna 18:2-3

Ya yi kira da babbar murya ya ce, “Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi. Ta zama gidan aljanu da kuma wurin zaman kowace irin mugun ruhu, wurin zaman kowane irin tsuntsu marar tsabta da mai banƙyama. Gama dukan al’ummai sun sha ruwan inabin haukan zinace zinacenta. Sarakunan duniya sun yi zina tare da ita, attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.”

Ru’uya ta Yohanna 18:9-10

“Sa’ad da sarakunan duniya da suka yi zina da ita suka kuma yi tarayya cikin jin daɗinta suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi kuka da makoki saboda ita. Don tsoron ganin azabarta za su tsaya daga nesa, su yi kuka suna cewa, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma. Ya ke Babilon, birni mai iko! Cikin sa’a guda hallakarki ta zo!’

Ru’uya ta Yohanna 18:21

Sa’an nan wani mala’ika mai ƙarfi ya ɗauki dutse kamar girman babban dutsen niƙa ya jefa cikin teku ya ce, “Da wannan irin giggitawa za a jefar da birnin Babilon mai girma ƙasa, ba za a ƙara ganin ta ba.

Ru’uya ta Yohanna 19:15

Daga bakinsa takobi mai kaifi ya fito. Da shi zai karkashe al’ummai. “Zai yi mulkinsu da sandan sarautar ƙarfe.” Yana tattake wurin matsin ruwan inabi na fushin Allah Maɗaukaki.

Ru’uya ta Yohanna 19:16

A rigarsa da kuma a cinyarsa akwai wannan suna a rubuce, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji.

Ru’uya ta Yohanna 19:17-19

Na kuma ga wani mala’ika tsaye a cikin rana, wanda ya yi kira da babbar murya ga dukan tsuntsaye da suke tashi sama a tsakiyar sararin sama cewa, “Ku zo, ku taru don babban bikin nan na Allah, don ku ci naman sarakuna, jarumawa, da kuma manyan mutane, na dawakai da mahayansu, da kuma naman dukan mutane, ’yantacce da bawa, babba da yaro.” Sa’an nan na ga dabbar da sarakunan duniya da mayaƙansu sun taru don su yi yaƙi da wannan wanda yake kan farin dokin da kuma mayaƙansa.

Ru’uya ta Yohanna 20:6

Masu albarka da kuma tsarki ne waɗanda suke da rabo a tashin matattu na farko. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kansu, sai dai za su zama firistocin Allah da kuma na Kiristi za su kuma yi mulki tare da shi na shekaru dubu.

Ru’uya ta Yohanna 20:11-13

Sa’an nan na ga babban farin kursiyi da kuma wannan da yake zama a kansa. Duniya da sararin sama kuwa suka ɓace daga gabansa, babu wuri kuwa dominsu. Sai na ga matattu, babba da yaro tsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne littafin rai. Aka yi wa matattu shari’a bisa ga abin da suka aikata yadda yake a rubuce a cikin littattafai. Teku ya ba da matattu da suke cikinsa, mutuwa da Hades kuma suka ba da matattu da suke cikinsu, aka kuma yi wa kowane mutum shari’a bisa ga abin da ya aikata.

Ru’uya ta Yohanna 21:5-6

Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. “Ina yin kome sabo!” Sai ya ce, “Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma.” Ya ce mini, “An gama. Ni ne Alfa da kuma Omega, na Farko da kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi abin sha kyauta daga maɓulɓular ruwan rai.

Ru’uya ta Yohanna 22:1-5

Sai mala’ikan ya nuna mini kogin ruwan rai, mai ƙyalli kamar madubi, yana gangarawa daga kursiyin Allah da na Ɗan Ragon, yana bin tsakiyar babban titi na birnin. A kowane gefen kogin akwai itacen rai mai ba da ’ya’ya goma sha biyu, yana ba da ’ya’yansa kowane wata. Ganyayen itacen kuwa saboda warkar da al’ummai ne. Ba za a ƙara samun la’ana ba. Kursiyin Allah da na Ɗan Ragon zai kasance a cikin birnin, bayinsa kuma za su yi masa hidima. Za su ga fuskarsa, sunansa kuma zai kasance a goshinsu. Ba za a ƙara yin dare ba. Ba za su bukaci hasken fitila ko hasken rana ba, domin Ubangiji Allah zai haskaka su. Za su kuwa yi mulki har abada abadin.

Hausa - Hausa - HA

HA'BSS - Budadden Littafi Mai Tsarki Biblica - 2020

This Bible text is from Biblica Open Hausa Contemporary Bible 2020
https://open.bible/bibles/hausa-biblica-text-bible/
provided by: Biblica Inc, available by Creative Commons CC-BY-SA-4.0,
and this new compilation is shared as www.creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0.
Languages are made available to you by www.ipedge.net