18 – Malaman ƙarya

Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Malaman ƙarya.

Top 3 Mafi Muhimmanci ayoyi

2 Bitrus 2:1-3

Amma a dā akwai annabawan ƙarya a cikin mutane, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku. A ɓoye za su shigar da karkataccen koyarwa mai hallaka, har ma su yi mūsun Ubangiji mai iko duka wanda ya saye su suna kawo wa kansu hallaka farat ɗaya. Da yawa za su bi hanyoyinsu na rashin kunya su kuma sa a rena hanyar gaskiya. Cikin kwaɗayinsu waɗannan malaman ƙarya za su cuce ku da tatsuniyoyin da suka ƙaga. Hukuncinsu yana a rataye a kansu tun da daɗewa, hallakarsu kuma ba ta barci.

2 Bitrus 3:16

Haka yake rubutu cikin dukan wasiƙunsa, yana magana a cikinsu a kan waɗannan al’amura. Wasiƙunsa sun ƙunshi waɗansu abubuwa masu wuyar fahimta, waɗanda jahilai da kuma waɗanda ba tsayayyu ba ne suke murɗe ma’anarsu, kamar yadda suke yi da sauran Nassosi, ta haka suke jawo wa kansu hallaka.

Maimaitawar Shari’a 18:20

Amma duk annabin da ya ɗauka cewa yana magana da sunana a kan wani abin da ban umarce shi ya faɗa ba, ko kuwa wani annabin da ya yi magana da sunan waɗansu alloli, dole a kashe shi.”

Kowane Aya A Canonical Order – 328 sassa

Farawa 3:1-5

To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen, “Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?” Macen ta ce wa macijin, “Za mu iya ci daga ’ya’ya itatuwa a lambun, amma Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga ’ya’yan itacen da yake tsakiyar lambu, kada kuma ku taɓa shi, in ba haka ba kuwa za ku mutu.’ ” Maciji ya ce wa macen, “Tabbatacce ba za ku mutu ba. Gama Allah ya san cewa sa’ad da kuka ci daga itacen idanunku za su buɗe, za ku kuma zama kamar Allah, ku san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu.”

Farawa 3:13-15

Sai Ubangiji Allah ya ce wa matar, “Me ke nan kika yi?” Matar ta ce, “Macijin ne ya ruɗe ni, na kuwa ci.” Saboda haka Ubangiji Allah ya ce wa macijin, “Saboda ka yi haka, “Na la’anta ka cikin dukan dabbobi da kuma cikin dukan namun jeji! Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya turɓaya kuma za ka ci dukan kwanakin rayuwarka. Zan kuma sa ƙiyayya tsakaninka da macen, tsakanin zuriyarka da zuriyarta. Zai ragargaje kanka, kai kuma za ka sari ɗiɗɗigensa.”

Fitowa 20:5-6

Ba za ka durƙusa gare su, ko ka yi musu sujada ba. Gama ni, Ubangiji Allahnka mai kishi ne, nakan hukunta ’ya’ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina, amma ina nuna ƙauna ga tsara dubbai na waɗanda suke ƙaunata, suke kuma kiyaye umarnaina.

Fitowa 23:1-2

“Kada ku baza rahoton ƙarya. Kada kuma ku haɗa baki da mugayen mutane har da ku zama munafukai ta wurin ba da shaidar ƙarya. “Kada ku yi abin da ba daidai ba, don galibin mutane suna yin haka. Sa’ad da kuke ba da shaida a gaban shari’a, kada ku ba da shaidar ƙarya a kauce wa gaskiya don ku faranta wa taron jama’a rai.

Firistoci 19:11

“ ‘Kada ku yi sata. “ ‘Kada ku yi ƙarya. “ ‘Kada ku ruɗe juna.

Firistoci 19:16-17

“ ‘Kada ku yi ta yawo kuna yaɗa ƙarya a cikin mutanenku. “ ‘Kada ku yi wani abin da zai sa ran maƙwabcinku cikin hatsari. Ni ne Ubangiji. “ ‘Kada ka yi ƙiyayyar ɗan’uwanka a zuciya. Ka tsawata wa maƙwabcinka da gaske don kada ka sami rabo cikin laifinsa.

Ƙidaya 23:19

Allah ba mutum ba ne, da zai yi ƙarya, shi ba ɗan mutum ba ne, da zai canja tunaninsa. Yana maganar abin da ba zai iya aikata ba ne? Yakan kuma yi alkawarin da ba zai iya cikawa ba?

Maimaitawar Shari’a 4:3

Da idanunku, kun ga abin da Ubangiji ya yi a Ba’al-Feyor. Yadda Ubangiji Allahnku ya hallaka waɗansu daga cikinku waɗanda suka yi wa Ba’al-Feyor sujada,

Maimaitawar Shari’a 5:32

Sai ku yi hankali don ku yi abin da Ubangiji Allahnku ya umarce ku; kada ku juya dama ko hagu.

Maimaitawar Shari’a 8:2-3

Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku a dukan hanya, a cikin hamada waɗannan shekaru arba’in, don yă ƙasƙantar da ku, yă kuma gwada ku don yă san abin da yake a zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa, ko babu. Ya ƙasƙantar da ku, ya bar ku da yunwa, sa’an nan ya ciyar da ku da Manna, wadda ku, ko kakanninku, ba su sani ba, ta haka ne ya sa kuka sani cewa, ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba, amma ta wurin kowace kalmar da ta fito daga bakin Ubangiji.

Maimaitawar Shari’a 8:5-6

Sai ku sani fa a cikin zuciyarku cewa kamar yadda mutum kan horar da ɗansa, haka Ubangiji Allahnku ke horar da ku. Ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, kuna tafiya cikin hanyoyinsa, kuna kuma girmama shi.

Maimaitawar Shari’a 11:16

Ku yi hankali, kada a ruɗe ku har ku bauta wa alloli, ku kuma yi musu sujada,

Maimaitawar Shari’a 12:32

Ku lura, ku aikata dukan abin da na umarce ku; kada ku ƙara, kada ku rage daga cikin.

Maimaitawar Shari’a 13:1-3

In wani annabi ko mai mafarkai, ya bayyana a cikinku, ya kuma yi muku shelar wata alama mai banmamaki ko al’ajabi, in kuwa alamar, ko al’ajabin da annabin ya yi faɗin ya faru, ya kuma ce, “Bari mu bi waɗansu alloli (allolin da ba ku sani ba) mu kuma yi musu sujada,” kada ku saurari kalmomin wannan annabi ko mai mafarki. Ubangiji Allahnku yana gwada ku ne don yă sani ko kuna ƙaunarsa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku.

Maimaitawar Shari’a 18:20

Amma duk annabin da ya ɗauka cewa yana magana da sunana a kan wani abin da ban umarce shi ya faɗa ba, ko kuwa wani annabin da ya yi magana da sunan waɗansu alloli, dole a kashe shi.”

Maimaitawar Shari’a 18:21-22

Mai yiwuwa ku ce wa kanku, “Yaya za mu san cewa wannan saƙo ba Ubangiji ne ya faɗa ba?” In abin da annabin ya furta da sunan Ubangiji bai faru ba, ko bai zama gaskiya ba, saƙo ne da Ubangiji bai faɗa ba ke nan. Wannan annabi ya yi rashin hankali ne kawai. Kada ku ji tsoronsa.

1 Sama’ila 15:23

Gama tawaye yana kama da zunubi na duba, girman kai kuma yana kama da bautar gumaka. Saboda ka ƙi maganar Ubangiji, shi ma ya ƙi ka da zaman sarki.”

1 Sarakuna 22:21-23

A ƙarshe, wani ruhu ya zo gaba, ya tsaya a gaban Ubangiji ya ce, ‘Zan ruɗe shi.’ “Ubangiji ya yi tambaya ‘Ta wace hanya?’ Ya ce, “ ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawansa.’ “Ubangiji ya ce, ‘Za ka yi nasara a ruɗinsa. Ka tafi, ka yi haka.’ “Saboda haka yanzu Ubangiji ya sa ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawanka. Ubangiji ya zartar maka da masifa.”

2 Tarihi 18:20-22

A ƙarshe, wani ruhu ya zo gaba, ya tsaya a gaban Ubangiji ya ce, ‘Zan ruɗe shi.’ “ Ubangiji ya yi tambaya, ‘Ta wace hanya?’ “Ya ce, ‘Zan tafi in zama ruhun ƙarya a bakunan dukan annabawansa.’ “ Ubangiji ya ce, ‘Za ka yi nasara a ruɗinsa. Ka tafi, ka yi haka.’ “To yanzu, Ubangiji ya sa ruhun ruɗu a bakunan waɗannan annabawanka. Ubangiji ya ƙayyade masifa dominka.”

2 Tarihi 36:15-16

Sai Ubangiji Allah na kakanninsu, ya yi ta aika da magana gare su ta wurin ’yan saƙonsa sau da sau, domin ya ji tausayi mutanensa da mazauninsa. Amma suka yi wa ’yan saƙon Allah ba’a, suka rena maganarsa, suka yi wa annabawansa dariyar reni, har sai da fushin Ubangiji ya tasar a kan mutanensa babu makawa.

Ayuba 13:4

Ku kuma kun ishe ni da ƙarairayi; ku likitocin wofi ne, dukanku!

Zabura 2:1-4

Me ya sa ƙasashe suke haɗa baki mutane kuma suke ƙulla shawarwarin banza? Sarakunan duniya sun ɗauki matsayi masu mulki sun taru gaba ɗaya suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa. Suna cewa, “Bari mu tsittsinke sarƙoƙinsu, mu kuma ’yantar da kamammu daga kangin bautar Allah.” Mai zama a kursiyi a sama yana dariya; Ubangiji yana musu ba’a.

Zabura 5:6

Kakan hallaka masu yin ƙarya. Masu kisankai da mutane masu ruɗu Ubangiji yana ƙyama.

Zabura 5:9

Babu ko kalma guda daga bakinsu da za a dogara da ita; marmarinsu kawai shi ne su hallakar da waɗansu. Maƙogwaronsu buɗaɗɗen kabari ne; da harshensu suna faɗin ƙarya.

Zabura 14:1-3

Wawaye sukan ce a ransu, “Ba Allah.” Sun lalace, ayyukansu kuwa mugaye ne; babu wani da yake yi abu mai kyau. Ubangiji ya duba daga sama a kan ’yan adam don yă ga ko akwai wani da ya gane, wani wanda yake neman Allah. Duka sun kauce, duka gaba ɗaya sun zama lalatattu; babu ɗaya wanda yake yin abu mai kyau, ba ko ɗaya.

Zabura 31:18

Bari a rufe leɓunan ƙarairayinsu, gama da fariya da reni suna magana da girman kai a kan adalai.

Zabura 34:13

ka kiyaye harshenka daga mugunta da kuma leɓunanku daga faɗar ƙarairayi.

Zabura 50:16-17

Amma ga mugaye, Allah ya ce, “Wace dama ce kuke da ita na haddace dokokina ko na yin maganar alkawarina a leɓunanku? Kun ƙi umarnina kuka kuma zubar da kalmomina a bayanku

Zabura 52:2-5

Harshenka kan shirya hallaka; yana nan kamar reza mai ci, kana ta ruɗu. Kana ƙaunar mugunta fiye da alheri, ƙarya a maimakon faɗin gaskiya. Sela Kana ƙaunar kowace kalmar cutarwa, Ya kai harshe mai ruɗu! Tabbatacce Allah zai kai ka ga madawwamiyar hallaka. Zai fizge ka yă yayyage ka daga tentinka; zai tumɓuke ka daga ƙasar masu rai. Sela

Zabura 55:21

Maganarsa tana da laushi kamar man zaitun, duk da haka yaƙi yana a cikin zuciyarsa; kalmominsa sun fi mai sulɓi, duk da haka takuba ne zārarru.

Zabura 59:12

Saboda zunuban bakunansu, saboda maganganun leɓunansu, bari a kama su cikin fariyarsu. Saboda zage-zage da ƙarairayin da suke yi,

Zabura 101:7

Babu mai ruɗun da zai zauna a gidana; babu mai ƙaryan da zai tsaya a gabana.

Zabura 119:118

Ka ki dukan waɗanda suka kauce daga ƙa’idodinka, gama yaudararsu banza ne.

Zabura 119:163

Na ƙi ina kuma ƙyamar ƙarya amma ina ƙaunar dokarka.

Karin Magana 1:7

Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi, amma wawaye sun rena hikima da horo.

Karin Magana 1:22-23

“Har yaushe ku da kuke marasa azanci za ku ci gaba a hanyoyinku marasa azanci? Har yaushe ku masu ba’a za ku yi ta murna cikin ba’arku wawaye kuma ku ƙi ilimi? Da a ce kun saurari tsawatata, da na faɗa muku dukan abin da yake zuciyata in kuma sanar da ku tunanina.

Karin Magana 3:5-7

Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka kada kuma ka dangana ga ganewarka; cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi, zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe. Kada ka zama mai hikima a ganinka; ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta.

Karin Magana 4:24

Ka kau da muguwar magana daga bakinka; ka yi nesa da magana marar kyau daga leɓunanka.

Karin Magana 4:25-27

Bari idanunka su dubi gaba sosai, ka kafa idanunka kai tsaye a gabanka. Ka san inda ƙafafunka suke takawa ka bi hanyoyin da suke daram kawai. Kada ka kauce dama ko hagu; ka kiyaye ƙafarka daga mugunta.

Karin Magana 6:16-19

Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi, abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi, duban reni, harshe mai ƙarya, hannuwa masu zub da jinin marar laifi, zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru, ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta, mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi, da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.

Karin Magana 9:7-9

“Duk wanda ya yi wa mai ba’a gyara yana gayyatar zagi duk wanda ya tsawata wa mugu yakan gamu da cin mutunci. Kada ka tsawata wa masu ba’a gama za su ƙi ka; ka tsawata wa mai hikima zai kuwa ƙaunace ka. Ka koya wa mai hikima zai kuwa ƙara hikima; ka koya wa mai adalci zai kuwa ƙara koyonsa.

Karin Magana 9:10

“Tsoron Ubangiji shi ne mafarin hikima, sanin Mai Tsarki kuwa fahimi ne.

Karin Magana 12:19

Leɓunan gaskiya kan dawwama har abada, amma harshen ƙarya yakan dawwama na ɗan lokaci ne kawai.

Karin Magana 12:22

Ubangiji yana ƙyamar leɓunan masu ƙarya, amma yana jin daɗin mutanen da suke masu gaskiya.

Karin Magana 14:5-7

Mashaidi na gaskiya ba ya ruɗu, amma mashaidin ƙarya kan baza ƙarairayi. Mai ba’a kan nemi hikima amma ba ya samun kome, amma sani kan zo a sawwaƙe ga mai basira. Ka guji wawa, gama ba za ka sami sani a leɓunansa ba.

Karin Magana 14:25

Mashaidin gaskiya kan ceci rayuka, amma mashaidin ƙarya mai ruɗu ne.

Karin Magana 15:12

Mai yin ba’a yakan ƙi gyara; ba zai nemi shawara mai hikima ba.

Karin Magana 17:4

Mugun mutum kan mai da hankali ga mugayen leɓuna; maƙaryaci yakan kasa kunne ga harshen ƙarairayi.

Karin Magana 19:5

Mai ba da shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba, kuma duk wanda ya baza ƙarairayi ba zai kuɓuta ba.

Karin Magana 19:9

Mai shaidar ƙarya ba zai tafi babu hukunci ba, kuma duk mai baza ƙarairayi zai hallaka.

Karin Magana 22:10

Ka hori mai ba’a, hatsaniya kuwa za tă yi waje; fitina da zargi kuma za su ƙare.

Karin Magana 24:28

Kada ka ba da shaida a kan maƙwabcinka ba tare da isashen dalili ba, ko ka yi amfani da leɓunanka ka yi ruɗu.

Karin Magana 27:5-6

Gara tsawatawar da ake yi a fili da ƙaunar da ake yi a ɓoye. Za a iya amince da rauni daga aboki, amma abokin gāba ko da ya sumbace ka kada ka sake da shi!

Karin Magana 29:12

In mai mulki yana sauraran ƙarairayi, dukan ma’aikatansa za su zama mugaye.

Karin Magana 30:5-6

“Kowace maganar Allah ba ta da kuskure; shi ne garkuwa ga waɗanda suke neman mafaka daga gare shi. Kada ka ƙara ga maganarsa, in ba haka ba zai tsawata maka ya kuma nuna kai maƙaryaci ne.

Mai Hadishi 7:1

Suna mai kyau ya fi turare mai ƙanshi, kuma ranar mutuwa ta fi ranar haihuwa.

Ishaya 1:2-5

Ku kasa kunne, ya sammai! Ki saurara, ya duniya! Gama Ubangiji ya yi magana, “Na yi renon ’ya’ya, na kuma raya su, amma sun tayar mini. Saniya ta san maigidanta, jaki ya san wurin sa wa dabbobi abinci maigidansa, amma Isra’ila ba su sani, mutanena ba su gane ba.” Kash, ya ke al’umma mai zunubi, mutane cike da laifi, tarin masu aikata mugunta, ’ya’yan da aka miƙa wa lalaci! Sun yashe Ubangiji; sun rena Mai Tsarkin nan na Isra’ila suka juya masa baya. Me ya sa za a ƙara yin muku dūka? Me ya sa kuka nace ga yin tayarwa? An yi wa dukan kanku rauni, zuciyarku duk tana ciwo.

Ishaya 1:28

Amma za a karye ’yan tawaye da masu zunubi, waɗanda suka rabu da Ubangiji kuma za su hallaka.

Ishaya 5:20-21

Kaiton waɗanda suke ce da mugunta nagarta nagarta kuma mugunta, waɗanda suke mai da duhu haske haske kuma duhu, waɗanda suke mai da ɗaci zaƙi zaƙi kuma ɗaci. Kaiton waɗanda suke tsammani suna da hikima da kuma wayo a idonsu.

Ishaya 8:13-14

Ubangiji Maɗaukaki shi ne za ka ɗauka a matsayi mai tsarki, shi ne wanda za ka ji tsoro, shi ne za ka yi rawar jiki a gabansa, zai kuwa kasance a wuri mai tsarki; amma ga dukan gidajen Isra’ila zai zama dutsen da zai sa mutane su yi tuntuɓe dutse kuma da zai sa su fāɗi. Ga dukan mutanen Urushalima kuma zai zama tarko da raga.

Ishaya 8:20

Nemi umarnin Allah da kuma shaidar jan kunne. Duk wanda bai yi magana bisa ga wannan kalma ba, ba su da amfani.

Ishaya 14:12-16

Yaya aka yi ka fāɗo daga sama Ya tauraron safiya, ɗan hasken asuba! An fyaɗa ka da ƙasa, kai da ka taɓa ƙasƙantar da al’ummai! Ka yi tunani a ranka ka ce, “Zan hau zuwa sama; zan ɗaga kursiyina sama da taurarin Allah; zan zauna a kursiyi a kan dutsen taro, a can ƙurewar saman dutse mai tsarki. Zan haura can bisa gizagizai; zan mai da kaina kamar Mafi Ɗaukaka.” Amma ga shi an gangara da kai zuwa kabari, zuwa zurfafan rami. Waɗanda suka gan ka sun zura maka ido, suna tunani abin da zai same ka. “Wannan mutumin ne ya girgiza duniya ya kuma sa mulkoki suka razana,

Ishaya 19:3

Masarawa za su karai, zan kuma sa shirye-shiryensu su zama banza; za su nemi shawarar gumaka da kuma ruhohin matattu, za su nemi shawarar mabiya da na masu duba.

Ishaya 28:7

Da waɗannan kuma masu tangaɗi saboda sun sha ruwan inabi suke jiri don sun sha barasa Firistoci da annabawa suna tangaɗi saboda sun sha barasa sun kuma yi tatur da ruwan inabi; suna jiri saboda sun sha barasa, suna tangaɗi sa’ad da suke ganin wahayi, suna tuntuɓe sa’ad da suke ba da shawara.

Ishaya 29:13

Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane sun zo kusa da ni da bakinsu suka kuma girmama ni da leɓunansu, amma zukatansu suna nesa daga gare ni. Sujadar da suke mini cike take da dokokin da mutane suka koyar.

Ishaya 29:16

Kuna birkitar abubuwa, sai ka ce an mayar da mai ginin tukwane ya zama yumɓu! Abin da aka yi zai ce wa wanda ya yi shi, “Ba shi ne ya yi ni ba”? Tukunya za tă iya ce wa mai ginin tukwane, “Ba ka san kome ba”?

Ishaya 29:24

Su da suke marasa azanci a ruhu za su sami fahimtar; waɗanda suke gunaguni za su yarda da koyarwa.”

Ishaya 30:9

Waɗannan mutane masu tawaye, ’ya’ya masu ruɗu, ’ya’yan da ba sa niyya su saurara ga umarnan Ubangiji.

Ishaya 30:10-13

Sukan ce wa masu gani, “Kada ku ƙara ganin wahayi!” Ga annabawa kuwa sukan ce, “Kada ku ƙara ba mu wahayin abin da yake daidai! Faɗa mana abubuwan da muke so mu ji ne kawai, ku yi annabcin abin da zai ruɗe mu. Ku bar wannan hanya, ku tashi daga wannan hanya, ku kuma daina kalubalantarmu da Mai Tsarkin nan na Isra’ila!” Saboda haka, ga abin da Mai Tsarkin nan na Isra’ila yake cewa, “Saboda haka kun ƙi wannan saƙo, kuka dogara ga aikin kama-karya kuka kuma dogara ga yin ruɗu, wannan zunubi zai zama muku kamar bango mai tsayi, tsagagge da yake kuma fāɗuwa, da zai rushe nan da nan, ba tsammani.

Ishaya 44:25

wanda ya sassāke alamun annabawan ƙarya ya masu duba suka zama wawaye, wanda ya tumɓuke koyon masu hikima ya mai da shi banza,

Ishaya 56:10-11

Matsaran Isra’ila makafi ne, dukansu jahilai ne; dukansu bebayen karnuka ne ba za su iya haushi ba; suna kwance ne kawai suna mafarki, suna son barci ba dama. Su karnuka ne masu kwaɗayi; ba su taɓa ƙoshi. Su makiyaya ne marasa ganewa; duk sun nufi inda suka ga dama, kowa yana nemar wa kansa riba.

Ishaya 57:4

Wane ne kuke yi wa ba’a? Ga wa kuke masa gwalo kuna kuma fitar da harshe? Ashe, ku ba tarin ’yan tawaye ba ne, zuriyar maƙaryata?

Irmiya 5:11-13

Gidan Isra’ila da gidan Yahuda sun zama marasa aminci gaba ɗaya gare ni” in ji Ubangiji. Sun yi ƙarya a kan Ubangiji; sun ce, “Ba zai yi kome ba! Ba wata masifar da za tă same mu; ba za mu taɓa ganin takobi ko yunwa ba. Annabawa holoƙo ne kawai maganar kuwa ba ta cikinsu; saboda haka bari abin da suke faɗi ya koma kansu.”

Irmiya 5:30-31

“Abin banmamaki da bantsoro ya faru a ƙasar. Annabawa suna annabcin ƙarya, firistoci suna mulki da ikon kansu, mutanena kuma suna son haka. Amma me za ku yi a ƙarshe?

Irmiya 6:13-14

“Daga ƙarami zuwa babba, dukansu masu haɗama ne don riba; har da annabawa da firistoci, dukansu suna aikata rashin gaskiya. Sukan ɗaura mikin mutanena sai ka ce mikin ba shi da matsala. Suna cewa, ‘Lafiya, Lafiya,’ alhali kuwa ba lafiya.

Irmiya 9:5-6

Aboki kan ruɗi aboki, ba mai faɗar gaskiya. Sun koya wa harshensu faɗar ƙarya; sun gajiyar da kansu da yin zunubi. Kai kana zama a tsakiyar ruɗu; cikin ruɗunsu sun ƙi su san ni,” in ji Ubangiji.

Irmiya 9:8

Harshensu kibiya ce mai dafi; yana magana da ruɗu. Da bakinsa kowa yana maganar alheri da maƙwabcinsa, amma a zuciyarsa ya sa masa tarko.

Irmiya 14:14-15

Sai Ubangiji ya ce mini, “Annabawa suna ta annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba, ban kuma naɗa su ba, ban yi musu magana ba. Suna muku annabci wahayin ƙarya, suna muku duba marar amfani, suna bautar gumaka suna kuma bayyana tunanin kansu ne. Saboda haka, ga abin da Ubangiji ya ce game da annabawan da suke annabci da sunana. Ban aike su ba, duk da haka suna cewa, ‘Babu takobi ko yunwar da zai taɓa wannan ƙasa.’ Waɗannan annabawa takobi da yunwa za su hallaka su.

Irmiya 17:5

Ga abin da Ubangiji yana cewa, “La’ananne ne mutumin da yake dogara ga mutum, wanda ya dogara ga jiki don ƙarfi wanda kuma zuciyarsa ta juya wa Ubangiji baya.

Irmiya 17:9-10

Zuciya ta fi kome ruɗu ta fi ƙarfin warkewa. Wa zai iya gane ta? “Ni Ubangiji nakan bincike zuciya in gwada tunani, don in sāka wa kowane mutum bisa ga halinsa, bisa ga ayyukansa.”

Irmiya 23:9

Game da annabawa kuwa, Zuciyata ta karai; dukan ƙasusuwana suna kaɗuwa. Na zama kamar wanda ya bugu, kamar mutumin da ruwan inabi ya sha kansa, saboda Ubangiji da kuma maganarsa mai tsarki.

Irmiya 23:11-12

“Annabi da firist dukansu biyu marasa sanin Allah ne; har ma a cikin haikalina na tarar da muguntarsu,” in ji Ubangiji. “Saboda haka hanyarsu za tă yi santsi; za a jefar da su cikin duhu a can kuwa za su fāɗi. Zan kawo musu masifa a shekarar da za a hukunta su,” in ji Ubangiji.

Irmiya 23:14-15

A cikin annabawan Urushalima kuma na ga wani abin bantsoro. Suna zina suna kuma rayuwar ƙarya. Sun ƙarfafa hannuwa masu aikata mugunta, domin kada wani ya juya daga muguntarsa. Dukansu sun yi kama da Sodom a gare ni; mutanen Urushalima sun yi kama da Gomorra.” Saboda haka, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa game da annabawa, “Zan sa su ci abinci mai ɗaci su kuma sha ruwa mai dafi, domin daga annabawan Urushalima rashin sani Allah ya bazu ko’ina a ƙasar.”

Irmiya 23:16-17

Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Kada ku saurari abin da annabawan suke muku annabci; suna cika ku da sa zuciyar ƙarya. Suna maganar wahayi daga tunaninsu, ba daga bakin Ubangiji ba. Suna cin gaba da ce wa waɗanda suka rena ni, ‘ Ubangiji ya ce za ku zauna lafiya.’ Ga duka waɗanda suke bin taurin zukatansu kuwa sukan ce, ‘Babu lahanin da zai same ku.’

Irmiya 23:20-21

Fushin Ubangiji ba zai kau ba sai ya aikata nufin zuciyarsa. A kwanakin masu zuwa za ku gane sarai. Ban aiki waɗannan annabawa ba, duk da haka sun tafi da saƙonsu; ban yi musu magana ba, duk da haka sun yi annabci.

Irmiya 23:25-29

“Na ji abin da annabawa suna cewa su da suke annabcin ƙarya a sunana. Suna cewa, ‘Na yi mafarki! Na yi mafarki!’ Har yaushe wannan zai ci gaba a cikin zukata annabawa masu ƙarya, waɗanda suke annabcin ruɗun tunaninsu? Suna tsammanin mafarkan da suke faɗa wa juna za su sa mutane su manta da sunana, kamar yadda kakanninsu suka manta da sunana ta wurin yin wa Ba’al sujada. Bari annabin da ya yi mafarki ya faɗa mafarkinsa, amma bari wanda yake da maganata ya yi ta da aminci. Gama me ya haɗa ciyawa da alkama?” In ji Ubangiji. “Maganata ba wuta ba ce,” in ji Ubangiji, “kuma kamar gudumar da kan ragargaza dutse?

Irmiya 23:31-32

I,” in ji Ubangiji, “Ina gāba da annabawan da suke kaɗa harsunansu sa’an nan su ce, ‘ Ubangiji ne ya furta.’ Tabbatacce, ina gāba da waɗannan da suke annabci mafarkan karya,” in ji Ubangiji. “Suna faɗarsu suna ɓad da mutanena da ƙarairayinsu na rashin hankali, duk da haka ban aike su ba, ban kuwa umarce su ba. Ba su amfani wannan mutane ba ko kaɗan,” in ji Ubangiji.

Irmiya 23:34-36

In annabi ko firist ko da wani dabam ya ce, ‘Wannan ne abin da Ubangiji yake cewa,’ zan hukunta wannan mutum da kuma gidansa. Ga abin da kowannenku yana cin gaba da ce wa abokinsa ko danginsa, ‘Mece ce amsar Ubangiji?’ Ko kuwa ‘mene ne Ubangiji ya faɗa?’ Amma kada ku ƙara ambatar ‘maganar Ubangiji’ domin kowace maganar mutum kan zama maganarsa. Ta haka kukan lalace maganar Allah mai rai, Ubangiji Maɗaukaki, Allahnmu.

Irmiya 23:38-40

Ko da yake kuna cewa, ‘Wannan ce maganar Ubangiji,’ ga abin da Ubangiji yana cewa kuna amfani da kalmomi, ‘Wannan ce maganar Ubangiji,’ ko da yake na ce muku kada ku ce, ‘Wannan ce maganar Ubangiji.’ Saboda haka, tabbatacce zan manta da ku in kuma jefar da ku daga gabana tare da birnin da na ba ku da kuma kakanninku. Zan kawo muku madawwamiyar kunya, kunya ta har abada wadda ba za a taɓa manta ba.”

Irmiya 27:9-10

Saboda haka kada ku saurari annabawanku, masu dubanku, masu fassarar mafarkanku, bokayenku ko masu maitancinku waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba.’ Suna muku annabcin ƙaryar ne kawai da za tă kau da ku daga ƙasarku; zan kore ku za ku kuwa hallaka.

Irmiya 27:14-16

Kada ku saurari maganganun annabawa waɗanda suke ce muku, ‘Ba za ku bauta wa sarkin Babilon ba,’ gama annabcin ƙarya suke muku. ‘Ban aike su ba,’ in ji Ubangiji. ‘Suna annabcin ƙarya ne da sunana. Saboda haka, zan kore ku za ku kuwa hallaka, da ku da kuma annabawan da suke muku annabci.’ ” Sai na ce wa firistoci da dukan waɗannan mutane, “Ga abin da Ubangiji yana cewa, kada ku saurari annabawan da suke cewa, ‘Ba daɗewa ba za a komo da kayan gidan Ubangiji daga Babilon.’ Suna muku annabcin ƙarya ne.

Irmiya 29:8-9

I, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa, “Kada ku bar annabawa da masu sihiri a cikinku su ruɗe ku. Kada ku saurari mafarkan da dā kuke ƙarfafa su su yi. Suna muku annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba,” in ji Ubangiji.

Irmiya 50:6

“Mutanena sun zama ɓatattun tumaki; makiyayansu sun bauɗar da su suka sa suna ta yawo a cikin duwatsu. Sun yi ta yawo a bisa dutse da tudu suka manta wurin hutunsu.

Ezekiyel 3:18-21

In na ce wa mugu, ‘Lalle za ka mutu,’ ba ka kuwa yi masa kashedi ko ka tsawata masa a kan mugayen hanyoyinsa don yă ceci ransa ba, wannan mugun zai mutu saboda zunubinsa, zan kuwa nemi hakkin jininsa a hannunka. Amma in ka yi wa mugun kashedi bai kuwa juya daga mugayen hanyoyinsa ba, zai mutu saboda zunubinsa; amma kai kam za ka kuɓuta. “Har yanzu, in mai adalci ya juya daga adalcinsa ya aikata mugunta, na kuma sa abin tuntuɓe a gabansa, zai mutu. Da yake ba ka yi masa kashedi ba, zai mutu saboda zunubinsa. Ba za a tuna da abin adalcin da ya yi ba, zan kuwa nemi hakkin jininsa a hannunka. Amma in ka yi wa mai adalcin kashedi kada yă yi zunubi bai kuwa yi zunubi ba, tabbatacce zai rayu saboda ya ji kashedin, kuma kai kam za ka kuɓuta.”

Ezekiyel 12:24

Gama ba za a ƙara ganin wahayin ƙarya ko a yi duba na daɗin baki a cikin mutanen Isra’ila ba.

Ezekiyel 13:1-3

Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Ɗan mutum, yi annabci a kan annabawan Isra’ila waɗanda suke annabci yanzu. Ka faɗa wa waɗanda suke annabci bisa ga ra’ayinsu cewa, ‘Ku ji maganar Ubangiji! Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yake faɗa, Kaiton wawaye annabawan da suke bin ruhunsu kuma ba su ga kome ba!

Ezekiyel 13:4-7

Annabawanki, ya Isra’ila, suna kama da diloli a kufai. Ba ku haura don ku rushe katanga don ku gyara gidan Isra’ila saboda ya tsaya daram a yaƙi a ranar Ubangiji ba. Wahayoyinsu ƙarya ne suna yin dubansu na ƙarya ne. Sukan ce, Ubangiji ya furta, alhali kuwa Ubangiji bai aike su ba; duk da haka sukan sa zuciya ga cikawar maganarsu. Ba ku ga wahayin ƙarya kuka kuma faɗa yin duban ƙarya sa’ad da kuka ce, “ Ubangiji ya furta,” ko da yake bai yi magana ba?

Ezekiyel 13:8

“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa saboda maganganunku na ƙarya da wahayinku na ƙarya, ina gāba da ku, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

Ezekiyel 13:9-16

Hannuna zai yi gāba da annabawan da suke ganin wahayin ƙarya suna kuma yin duban ƙarya. Ba za su kasance cikin taron mutanena ba, ba kuwa za a rubuta su a littafin gidan Isra’ila ba, ba za su shiga ƙasar Isra’ila ba. Ta haka za ku san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka. “ ‘Domin sun ɓad da mutanena, suna cewa, “Salama,” sa’ad da ba salama, kuma saboda, sa’ad da ana gina katanga marar ƙarfi, sukan shafe ta da farar ƙasa, saboda haka ka faɗa wa waɗanda suka shafe da farar ƙasa cewa za tă fāɗi. Ruwan sama zai sauko da rigyawa, zan kuma aika da ƙanƙara, kuma babbar iska za tă ɓarke. Sa’ad da katangar ta fāɗi, mutane ba za su tambaye ku ba cewa, “Ina shafen farar ƙasar da kuka yi mata?” “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa a cikin hasalata zan saki babbar iska, kuma cikin fushina zan tura ƙanƙara kuma rigyawan ruwan sama zai sauko da fushin hallaka. Zan rushe katangar da kuka shafe da farar ƙasa zan baje ta har ƙasa saboda tushenta zai tsaya tsirara. Sa’ad da ta fāɗi, za a hallaka ku a cikinta; kuma za ku san cewa ni ne Ubangiji Mai Iko Duka. Ta haka zan aukar wa katangar da hasalata da kuma a kan waɗanda suka yi shafenta da farar ƙasa. Zan ce muku, “Katangar ta fāɗi haka kuma mutanen da suka shafe ta da farar ƙasa, waɗannan annabawan Isra’ila waɗanda suka yi annabci wa Urushalima suka kuma ga mata wahayin salama sa’ad da ba salama, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.” ’

Ezekiyel 13:17

“To, ɗan mutum, ka kafa idonka a kan ’yan matan mutanenka waɗanda suke annabci bisa ga ra’ayinsu. Yi annabci a kansu

Ezekiyel 13:22-23

Domin kun karya zuciyar masu adalci da ƙarairayinku, sa’ad da na fitar da su babu damuwa, kuma domin kun ƙarfafa mugaye kada su juye daga mugayen hanyoyinsu su ceci rayukansu, saboda haka ba za ku ƙara ganin wahayin ƙarya ba, ko ku yi duba. Zan ceci mutanena daga hannuwanku. A sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.’ ”

Ezekiyel 22:28

Annabawanki sun yi wa waɗannan ayyuka shafe da farar ƙasa ta wurin wahayin ƙarya da duban ƙarya. Suna cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa’ alhali kuwa Ubangiji bai faɗa ba.

Ezekiyel 28:6-7

“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Domin ka ɗauka kai mai hikima ne, mai hikima kamar allah, zan kawo baƙi a kanka, waɗanda suka fi mugunta cikin sauran al’ummai; za su zāre takubansu a kan kyakkyawar hikimarka su kuma ɓarke darajarka mai walƙiya.

Ezekiyel 33:3-6

ya kuma ga takobi yana zuwa a kan ƙasar ya kuwa busa ƙaho don yă faɗakar da mutane, in wani ya ji busar amma bai kula ba, takobin zai zo ya ɗauki ransa, jininsa kuwa zai zauna a kansa. Da yake ya ji ƙarar busar amma bai kula ba, jininsa zai zauna a kansa. Da a ce ya kula, da ya ceci kansa. Amma a ce mai tsaron ya ga takobi yana zuwa bai kuwa busa ƙaho don yă faɗakar da mutane ba sai takobi ya zo ya ɗauki ran waninsu, za a kawar da wannan mutum saboda zunubinsa, amma zan nemi hakkin jinin mutumin a kan mai tsaron.’

Ezekiyel 33:7-9

“Ɗan mutum, na mai da kai mai tsaro bisa gidan Isra’ila; saboda haka ka ji abin da zan faɗa ka kuma gargaɗe su. Sa’ad da na ce wa mugu, ‘Ya mugun mutum, tabbatacce za ka mutu,’ kai kuma ba ka yi magana don ka juyar da shi daga hanyoyinsa ba, wannan mugun mutum zai mutu domin zunubinsa, zan kuma nemi hakkin jininsa a kanka. Amma in ka faɗakar da mugun mutumin don yă juye daga hanyoyinsa bai kuwa yi haka ba, zai mutu saboda zunubinsa, amma kai za ka kuɓutar da kanka.

Ezekiyel 33:14-15

Kuma in na ce wa mugu, ‘Tabbatacce za ka mutu,’ amma sai ya juye daga zunubinsa ya kuma yi abin da yake gaskiya da kuma daidai, in ya mayar da jingina, ya mayar da abin da ya sata, ya kiyaye ƙa’idodin da suke ba da rai, ya daina yin mugunta, tabbatacce zai rayu; ba zai mutu ba.

Ezekiyel 33:17-20

“Duk da haka mutanen ƙasarka sun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Alhali kuwa tasu ce ba daidai ba. In adali ya juye daga adalcinsa ya yi mugunta, zai mutu saboda haka. Kuma in mugu ya juye daga muguntarsa ya aikata abin da yake gaskiya da kuma daidai, zai rayu ta yin haka. Duk da haka, ya gidan Isra’ila kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Amma zan hukunta kowane ɗayanku gwargwadon ayyukansa.”

Ezekiyel 34:2-6

“Ɗan mutum, ka yi annabci a kan makiyayan Isra’ila; ka yi annabci ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa kaiton makiyayan Isra’ila waɗanda suke kula da kansu ne kawai! Ashe, bai kamata makiyaya ne su lura da tumaki ba? Kuna cin kitsensu, kuna yi wa kanku tufafi da gashinsu, kukan yanka turkakkun, amma ba ku yi kiwon tumakin ba. Ba ku ƙarfafa marasa ƙarfi ba, ko ku warkar da marasa lafiya ko ku ɗaura waɗanda suka ji rauni. Ba ku dawo da waɗanda suka yi makuwa ko ku nemi waɗanda suka ɓace ba. Amma sai kuka mallake su ƙarfi da yaji. Saboda haka suka warwatse domin babu makiyayi, kuma da suka warwatsu sai suka zama abincin namun jeji. Tumakina suna ta yawo a kan dukan duwatsu da kuma kowane tudu. Sun watsu a dukan duniya, kuma ba wanda ya neme su.

Ezekiyel 34:8-10

Muddin ina raye, in ji Ubangiji Mai Iko Duka, domin tumaki sun rasa makiyayi ta haka aka washe su suka kuma zama abincin dukan namun jeji, kuma domin makiyayana ba su nemi tumakina ba amma suka kula da kansu a maimakon tumakina, saboda haka, ya ku makiyaya, ku ji maganar Ubangiji, Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da makiyaya kuma zan nemi hakkin tumakina daga gare su. Zan hana su yin kiwon tumakin don kada makiyayan su ƙara yin kiwon kansu. Zan ƙwace tumakina daga bakunansu, ba kuwa za su ƙara zama abincinsu.

Ezekiyel 34:17

“ ‘Game da ku, tumakina, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan hukunta tsakanin tunkiya da tunkiya, da tsakanin raguna da awaki.

Ezekiyel 34:20-22

“ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce musu, duba, ni kaina zan hukunta tsakanin turkakkun tumaki da ramammun tumaki. Domin kun tunkuɗe marasa ƙarfi da kafaɗunku, kun kuma tunkuye su da ƙahoninku sai da suka gudu, zan cece tumakina ba za su ƙara zama ganima ba. Zan hukunta tsakanin tunkiya da tunkiya.

Ezekiyel 35:13

Ka yi fariya a kaina, ka kuma yi magana a kaina ba gaggautawa, na ji shi sarai.

Hosiya 4:6

mutanena suna hallaka saboda jahilci. “Domin kun ƙi neman sani, ni ma na ƙi ku a matsayin firistocina; domin kun ƙyale dokar Allahnku, ni ma zan ƙyale ’ya’yanku.

Hosiya 4:12

Sun nemi shawarar gunkin da aka yi da itace suka kuwa sami amsa daga sanda. Halin karuwanci yakan ɓad da su; sun yi rashin aminci ga Allahnsu.

Mika 3:5-7

Ga abin da Ubangiji ya faɗa, “Game da annabawa masu ɓad da mutanena, in wani ya ciyar da su, sai su ce akwai ‘salama’ amma in bai ciyar da su ba, a shirye suke su kai masa hari. Saboda haka dare yana zuwa a bisanku, ba tare da wahayi ba, kuma duhu, ba tare da duba ba. Rana za tă fāɗi wa annabawa, yini kuma zai zama musu duhu. Masu gani za su ji kunya, masu duba kuma za su ji taƙaici. Dukansu za su rufe fuskokinsu gama ba amsa daga Allah.”

Mika 3:11

Hukunce-hukuncen shugabannin ƙasar na cin hanci ne, firistocinta kuma suna koyarwa don a biya su, annabawanta kuwa suna yin annabci don neman kuɗi. Duk da haka suna jingina a kan Ubangiji suna cewa, “Ba Ubangiji yana tare da mu ba? Ba bala’in da zai zo mana.”

Zakariya 8:16-17

Abubuwan da za ku yi ke nan. Ku gaya wa juna gaskiya, ku kuma dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunanku na shari’arku; kada ku ƙulla wa maƙwabtanku mugunta, kuma kada ku so yin rantsuwa ta ƙarya. Ina ƙyamar waɗannan duka,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

Zakariya 10:2

Gumaka suna maganganun ruɗu, masu duba suna ganin wahayoyin ƙarya, suna faɗa mafarkan ƙarya suna ba da ta’aziyyar banza. Saboda haka mutane suna yawo kamar tumaki waɗanda suke shan wahala saboda rashin makiyayi.

Zakariya 11:17

“Kaito ga banzan makiyayin nan, wanda ya bar garken! Bari takobi yă sare hannunsa da idonsa na dama! Bari hannunsa yă shanye gaba ƙaf, idonsa na dama kuma yă makance sarai!”

Zakariya 13:2-5

“A ranan nan, zan kawar da sunayen gumaka daga ƙasar, ba kuwa za a ƙara tunawa da su ba,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan kawar da annabawa da kuma ruhu marar tsabta daga ƙasar. In kuma wani ya yi annabci, sai mahaifinsa da mahaifiyarsa su ce masa, ‘Ba za ka rayu ba, gama kana faɗar ƙarya da sunan Ubangiji.’ Sa’ad da yake yin annabci, iyayensa za su soke shi da takobi. “A ranan nan kowane annabi zai ji kunyar annabcin wahayinsa. Ba zai sa rigar annabci mai gashi ba don yă yi ruɗu. Zai ce, ‘Ni ba annabi ba ne. Ni manomi ne; ƙasa ce nake samun abin zaman gari tun ina matashi.’

Malaki 2:7-9

“Gama ya kamata leɓunan firist su kiyaye ilimi, ya kamata kuma mutane su nemi umarni daga bakinsa, domin shi ne manzon Ubangiji Maɗaukaki. Amma sai kuka kauce hanya, ta wurin koyarwarku kuma kuka sa mutane da yawa suka yi tuntuɓe; kun keta alkawarin da na yi da Lawi,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Saboda haka na sa a rena ku, a kuma wulaƙanta ku a gaban dukan mutane, domin ba ku bi hanyoyina ba amma kuka nuna sonkai a al’amuran shari’a.”

Mattiyu 5:10-12

‹Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu don gani an yi adalci,› ‹gama mulkin sama nasu ne.› ‹“Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni.› ‹Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.›

Mattiyu 5:17-19

‹“Kada ku yi tsammani na zo ne domin in kawar da Doka ko kuma Annabawa; ban zo domin in kawar da su ba ne, sai dai domin in ciccika su.› ‹Gaskiya nake gaya muku, kafin sama da ƙasa sun shuɗe, babu ko ɗan wasali, babu wani ɗigo ta kowace hanya da zai ɓace daga Dokar, sai an cika kome.› ‹Duk wanda ya karya ɗaya daga cikin mafi ƙanƙanta na umarnan nan, ya kuma koya wa waɗansu su yi haka, za a ce da shi mafi ƙanƙanta a mulkin sama. Amma duk wanda ya aikata, ya kuma koyar da waɗannan umarnai, za a kira shi mai girma a cikin mulkin sama.›

Mattiyu 7:3-6

‹“Don me kake duban ɗan tsinken da yake idon ɗan’uwanka, alhali kuwa ga gungume a naka ido?› ‹Yaya za ka ce wa ɗan’uwanka, ‘Bari in cire maka ɗan tsinken nan daga idonka,’ alhali kuwa a kowane lokaci akwai gungume a naka ido?› ‹Kai munafuki, fara cire gungumen da yake idonka, a sa’an nan ne za ka iya gani sosai yadda za ka cire ɗan tsinken da yake a idon ɗan’uwanka.› ‹“Kada ku ba karnuka abin da yake mai tsarki; kada kuma ku jefa wa aladu lu’ulu’anku. In kuka yi haka za su tattake su, sa’an nan su juyo su jijji muku ciwo.›

Mattiyu 7:13-14

‹“Ku shiga ta matsattsiyar ƙofa. Gama ƙofar zuwa hallaka faɗaɗɗiya ce mai sauƙin bi kuma, masu shiga ta cikinta kuwa suna da yawa.› ‹Amma ƙofar zuwa rai, ƙarama ce matsattsiya kuma, masu samunta kuwa kaɗan ne.›

Mattiyu 7:15

‹“Ku yi hankali da annabawan ƙarya. Sukan zo muku da kamannin tumaki, amma daga ciki mugayen kyarketai ne.›

Mattiyu 7:19-20

‹Duk itacen da ba ya ba da ’ya’ya masu kyau sai a sare shi a jefa cikin wuta.› ‹Ta haka, ta wurin aikinsu za ku gane su.”›

Mattiyu 7:21-23

‹“Ba duk mai ce mini, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ne zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda yake aikata nufin Ubana da yake sama.› ‹Da yawa za su ce mini a wannan rana, ‘Ubangiji, Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, ba kuma a cikin sunanka ne muka fitar da aljanu, muka yi abubuwan banmamaki da yawa ba?’› ‹Sa’an nan zan ce musu a fili, ‘Ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!’›

Mattiyu 12:32

‹Duk wanda ya zargi Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya zargi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, ko a wannan zamani ko a zamani mai zuwa.›

Mattiyu 13:13-14

‹Abin da ya sa nake musu magana da misalai ke nan.› ‹“Ko da yake suna kallo, ba sa gani;› ‹ko da yake suna saurara, ba sa ji ko su gane.› ‹A kansu ne aka cika annabcin Ishaya cewa,› ‹“ ‘Za ku yi ta ji amma ba za ku taɓa ganewa ba;› ‹za ku yi ta kallo amma ba za ku taɓa gani ba.›

Mattiyu 13:18-23

‹“To, ku saurari ma’anar misali na mai shukan nan.› ‹Duk sa’ad da wani ya ji saƙo game da mulkin bai kuwa fahimce shi ba, mugun nan yakan zo yă ƙwace abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da ya fāɗi a kan hanya.› ‹Wanda ya karɓi irin da ya fāɗi a wuraren duwatsu kuwa, shi ne mutumin da yakan ji maganar, nan da nan kuwa yă karɓe ta da murna.› ‹Sai dai da yake ba shi da saiwa, yakan ɗan jima kaɗan kawai. Da wata wahala ko tsanani ya auko masa saboda maganar, nan da nan sai yă ja da baya.› ‹Wanda ya karɓi irin da ya fāɗi cikin ƙaya kuwa, shi ne mutumin da yakan ji maganar, sai dai damuwoyin rayuwan nan da jarrabar arzikin duniya sukan shaƙe shi, yă sa maganar ta kāsa amfani.› ‹Amma wanda ya karɓi irin da ya fāɗi a ƙasa mai kyau, shi ne mutumin da yakan ji maganar yă kuwa fahimce ta. Yakan ba da amfani wani riɓi ɗari, sittin, ko talatin na abin da aka shuka.”›

Mattiyu 15:3

Yesu ya amsa ya ce, ‹“Ku ma me ya sa kuke karya dokar Allah saboda al’adarku?›

Mattiyu 15:8-9

‹“ ‘Waɗannan mutane da baki kawai suke girmama ni,› ‹amma zukatansu suna nesa da ni.› ‹A banza suke mini sujada,› ‹koyarwarsu, dokoki ne kawai da mutane suke koyarwa.’ ”›

Mattiyu 15:13-14

Ya amsa ya ce, ‹“Duk tsiron da Ubana na sama bai shuka ba, za a tumɓuke shi daga saiwoyi.› ‹Ku ƙyale su, ai, makafin jagorai ne.›‹In makaho ya yi wa makaho jagora, dukansu za su fāɗa a rami.”›

Mattiyu 16:11-12

‹Yaya kuka kāsa gane cewa ba zancen burodi nake yi ba? Sai dai ku yi hankali da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.”› Sa’an nan suka gane ba cewa yake musu su yi hankali da yistin da ake amfani da shi a burodi ba ne, sai dai su yi hankali da koyarwar Farisiyawa da Sadukiyawa ne.

Mattiyu 16:23

Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, ‹“Rabu da ni, Shaiɗan! Kai abin sa tuntuɓe ne a gare ni; ba ka tunanin al’amuran Allah, sai dai al’amuran mutane.”›

Mattiyu 18:15-17

‹“In ɗan’uwanka ya yi maka laifi, ka je ka nuna masa laifinsa, tsakaninku biyu kaɗai. In ya saurare ka, ka maido da ɗan’uwanka ke nan.› ‹Amma in bai saurare ka ba, ka je tare da mutum ɗaya ko biyu, domin ‘a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.’› ‹In kuwa ya ƙi yă saurare su, sai ka gaya wa ikkilisiya; in kuma ya ƙi yă saurari ikkilisiya ma, ka yi da shi kamar marar sanin Allah ko mai karɓar haraji.›

Mattiyu 22:18

Amma Yesu da yake ya san mugun nufinsu, sai ya ce, ‹“Ku munafukai, don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko?›

Mattiyu 23:1-5

Sa’an nan Yesu ya ce wa taron mutane da kuma almajiransa, ‹“Malaman dokoki da Farisiyawa suke zama a kujerar Musa.› ‹Saboda haka dole ku yi musu biyayya, ku kuma yi duk abin da suka faɗa muku. Sai dai kada ku yi abin da suke yi, gama ba sa yin abin da suke wa’azi.› ‹Sukan ɗaura kaya masu nauyi, su sa wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu, ba sa ko sa yatsa su taimaka.› ‹“Kome suke yi, suna yi ne don mutane su gani. Sukan yi layunsu›‹fantam-fantam bakin rigunarsu kuma sukan kai har ƙasa;›

Mattiyu 23:6-12

‹suna son wurin zaman manya a wurin biki, da kuma wuraren zama gaba-gaba a majami’u;› ‹suna so a yi ta gaisuwarsu a kasuwa, ana kuma riƙa ce musu, ‘Rabbi.’› ‹“Amma kada a kira ku ‘Rabbi,’ gama kuna da Maigida ɗaya ne, ku duka kuwa, ’yan’uwa ne.› ‹Kada kuma ku kira wani a duniya ‘uba,’ gama kuna da Uba ɗaya ne, yana kuwa a sama.› ‹Ba kuwa za a kira ku ‘malam’ ba, gama kuna da Malami ɗaya ne, Kiristi.› ‹Mafi girma a cikinku, zai zama bawanku.› ‹Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi, duk kuma wanda ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.›

Mattiyu 23:13-15

‹“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, ku munafukai! Kun rufe ƙofar mulkin sama a gaban mutane. Ku kanku ba ku shiga ba, ba kuwa bar waɗanda suke ƙoƙarin shiga su shiga ba.› ‹“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan yi tafiye-tafiye zuwa ƙasashe, ku ƙetare teku don ku sami mai tuba ɗaya, sa’ad da ya tuba kuwa, sai ku mai da shi ɗan wuta fiye da ku, har sau biyu.›

Mattiyu 23:23-28

‹“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan ba da kashi ɗaya bisa goma na kayan yajinku, na’ana’a, anise, da lafsur. Amma kun ƙyale abubuwan da suka fi girma na dokoki, adalci, jinƙai da aminci. Waɗannan ne ya kamata da kun kiyaye ba tare da kun ƙyale sauran ba.› ‹Makafi jagora! Kukan tace ƙwaro ɗan mitsil amma sai ku haɗiye raƙumi.› ‹“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan wanke bayan kwaf da kwano, amma a ciki, cike suke da zalunci da sonkai.› ‹Kai makaho Bafarisiye! Ka fara wanke cikin kwaf da kwano, sa’an nan bayan ma zai zama da tsabta.› ‹“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kuna kama da kaburburan da aka shafa musu farin fenti, waɗanda suna da kyan gani a waje, amma a ciki, cike suke da ƙasusuwan matattu da kuma kowane irin abu mai ƙazanta.› ‹Haka ku ma, a waje, a idon mutane, ku masu adalci ne, amma a ciki, cike kuke da munafunci da mugunta.›

Mattiyu 23:29-35

‹“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan gina kaburbura don annabawa, ku kuma yi wa kaburburan mutane masu adalci ado.› ‹Kuna cewa, ‘Da mun kasance a zamanin kakanninmu, ai, da ba mu haɗa hannu da su muka karkashe annabawa ba.’› ‹Ta haka kuna ba da shaida a kanku cewa ku zuriyar waɗanda suka karkashe annabawa ne.› ‹To, sai ku ci gaba ku cikasa ayyukan da kakanninku suka fara!› ‹“Ku macizai! ’Ya’yan macizai! Ta yaya za ku tsere wa hukuncin jahannama ta wuta?› ‹Saboda haka ina aika muku da annabawa, da masu hikima da malamai. Waɗansunsu za ku kashe ku kuma gicciye; waɗansu kuma za ku yi musu bulala a majami’unku kuna kuma binsu gari-gari.› ‹Ta haka alhakin jinin masu adalcin da aka zubar a duniya, tun daga jinin Habila mai adalci, zuwa jinin Zakariya ɗan Berekiya, wanda kuka kashe tsakanin haikali da bagade zai koma kanku.›

Mattiyu 24:4-5

Yesu ya amsa, ‹“Ku lura fa, kada wani yă ruɗe ku.› ‹Gama mutane da yawa za su zo cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne Kiristi,’ za su kuwa ruɗi mutane da yawa.›

Mattiyu 24:10-12

‹A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna,› ‹annabawan ƙarya da yawa za su firfito su kuma ruɗi mutane da yawa.› ‹Saboda ƙaruwar mugunta, ƙaunar yawanci za tă yi sanyi,›

Mattiyu 24:24-25

‹Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu.› ‹Ga shi, na faɗa muku tun da wuri.›

Mattiyu 24:35

‹Sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za tă taɓa shuɗe ba.›

Mattiyu 28:18-20

Sai Yesu ya zo wurinsu ya ce, ‹“An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa.› ‹Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikin›‹sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki,› ‹kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani.”›

Markus 4:14-20

‹Manomi yakan shuka maganar Allah.› ‹Waɗansu mutane suna kama da irin da ya fāɗi a kan hanya, inda akan shuka maganar Allah. Da jin maganar, nan da nan sai Shaiɗan yă zo yă ɗauke maganar da aka shuka a zuciyarsu.› ‹Waɗansu suna kama da irin da aka shuka a wurare masu duwatsu, sukan ji maganar Allah, sukan kuma karɓe ta nan da nan da farin ciki.› ‹Amma da yake ba su da saiwa, ba sa daɗewa. Da wahala ko tsanani ya tashi saboda maganar, nan da nan, sai su ja da baya.› ‹Har yanzu, waɗansu kamar irin da aka shuka cikin ƙaya, sukan ji maganar,› ‹amma damuwar wannan duniya, da son dukiya, da kuma kwaɗayin waɗansu abubuwa, sukan shiga, su shaƙe maganar, har su mai da ita marar amfani.› ‹Waɗansu mutane kuwa suna kama da irin da aka shuka a ƙasa mai kyau, sukan ji maganar Allah, su kuma karɓa, sa’an nan kuma su fid da amfani riɓi talatin-talatin, ko sittin-sittin, ko ɗari-ɗari.”›

Markus 7:6-7

Ya amsa ya ce, ‹“Daidai ne Ishaya ya yi annabci game da ku munafukai; kamar yadda yake a rubuce cewa,› ‹“ ‘Waɗannan mutane da baki suke girmama ni,› ‹amma zukatansu sun yi nesa da ni.› ‹A banza suke mini sujada,› ‹koyarwarsu, dokokin mutane ne kawai.’›

Markus 7:8-9

‹Kun yar da umarnan Allah, kuna bin al’adun mutane.”› Ya kuma ce musu, ‹“Kuna da hanya mai sauƙi na ajiye umarnan Allah a gefe ɗaya, don ku kiyaye al’adunku!›

Markus 13:22-23

‹Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu.› ‹Amma ku kula! Na dai gaya muku kome tun da wuri.›

Markus 13:31

‹Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.›

Luka 4:4

Yesu ya amsa ya ce, ‹“A rubuce yake, ‘Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba.’›‹”›

Luka 6:26

‹Kaitonku sa’ad da dukan mutane suna magana mai kyau a kanku,› ‹gama haka kakanninsu suka yi da annabawan ƙarya.›

Luka 6:39-40

Ya kuma faɗa musu wannan misali cewa, ‹“Makaho yana iya jagoran makaho ne? Ba sai dukansu biyu su fāɗa a rami ba?› ‹Ɗalibi bai fi malaminsa ba, sai dai kowane ɗalibi wanda ya sami cikakkiyar koyarwa, zai zama kamar malaminsa.›

Luka 8:11-15

‹“Ga ma’anar misalin, irin, shi ne maganar Allah.› ‹Waɗanda suka fāɗi a kan hanya su ne mutanen da suka ji, amma Iblis, yakan zo ya ɗauke maganar daga zuciyarsu, don kada su gaskata, su sami ceto.› ‹Na kan dutse kuwa, su ne da jin maganar, sukan karɓa da murna, amma ba su da saiwa. Sukan gaskata na ɗan lokaci, amma lokacin gwaji, sai su ja da baya.› ‹Irin da suka fāɗi a cikin ƙaya kuwa, su ne mutanen da suka ji, amma a kwana a tashi, tunanin kayan duniya, da neman arziki, da son jin daɗi, sukan hana su ba da ’ya’ya.› ‹Amma irin da suka fāɗi a ƙasa mai kyau kuwa, su ne mutane masu kyakkyawar zuciya, mai kyau, da suka ji, suka riƙe, suka kuma jimre har suka ba da ’ya’ya.”›

Luka 8:17-18

‹Ba abin da yake ɓoye da ba za a fallasa ba. Kuma ba abin da yake rufe, da ba za a sani ba, ko a fitar da shi a fili ba.› ‹Saboda haka, ku yi tunani da kyau yadda kuke saurara. Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, duk wanda ba shi da shi kuma, abin da yake tsammani yana da shi ma, za a karɓe daga gare shi.”›

Luka 16:17

‹Gama ta fi sauƙi sama da ƙasa su shuɗe, da a ce ɗigo guda ɗaya na rubutun, ya fita ya fāɗi daga cikin Doka.›

Luka 21:8

Ya amsa ya ce, ‹“Ku lura, kada ku kuma a ruɗe ku. Gama da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ai, ni ne shi,’ da kuma, ‘Lokaci ya yi kusa.’ Kada ku bi su.›

Luka 21:33

‹Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.›

Yohanna 2:24-25

Sai dai Yesu bai amince da su ba, don ya san dukan mutane. Ba ya bukatar shaidar mutum game da mutum, don yă san abin da yake cikin zuciyar mutum.

Yohanna 3:18-20

Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba. Hukuncin shi ne, Haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka so duhu a maimakon haske domin ayyukansu mugaye ne. Duk mai aikata mugunta yana ƙin haske, ba zai kuwa zo cikin haske ba don yana tsoro kada ayyukansa su tonu.

Yohanna 4:23-24

‹Duk da haka, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a Ruhu da kuma gaskiya, gama irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema.› ‹Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.”›

Yohanna 7:16-17

Yesu ya amsa ya ce, ‹“Koyarwata ba tawa ba ce, ta fito ne daga wurin wanda ya aiko ni.› ‹Duk wanda ya zaɓi yin nufin Allah, zai gane ko koyarwata daga Allah ce, ko kuwa don kaina ne nake magana.›

Yohanna 7:19-20

‹Ashe, ba Musa ba ne ya ba ku Doka? Duk da haka ba ko ɗayanku da yake kiyaye Dokar. Me ya sa kuke nema ku kashe ni?”› Taron suka amsa suka ce, “Kana da aljani, wane ne yake so yă kashe ka?”

Yohanna 7:24

‹Ku daina yin shari’a bisa ga ganin ido, sai dai ku yi shari’a bisa ga adalci.”›

Yohanna 8:12

Sa’ad da Yesu ya sāke magana da mutanen, sai ya ce, ‹“Ni ne hasken duniya. Duk wanda ya bi ni ba zai yi tafiya cikin duhu ba, sai dai yă sami hasken rayuwa.”›

Yohanna 8:31-32

Sai Yesu ya ce wa Yahudawan da suka gaskata da shi, ‹“In dai kun riƙe koyarwata, ku almajiraina ne da gaske.› ‹Sa’an nan za ku san gaskiya, gaskiyar kuwa za tă ’yantar da ku.”›

Yohanna 8:43-44

‹Me ya sa ba kwa gane da maganata? Don ba kwa iya jin abin da nake faɗi.› ‹Ku na ubanku ne, Iblis, kuna kuwa so ku aikata abin da ubanku yake so. Shi mai kisankai ne tun farko. Ba ruwansa da gaskiya, gama gaskiya ba ta cikinsa. Yayinda yake ƙarya, yana yin halinsa ne, gama shi maƙaryaci ne, uban ƙarairayi kuma.›

Yohanna 8:47

‹Wanda yake na Allah, yakan ji abin da Allah yake faɗi. Abin da ya sa ba kwa jin sa kuwa shi ne don ku ba na Allah ba ne.”›

Yohanna 9:39-41

Yesu ya ce, ‹“Saboda shari’a ce na zo duniya nan, saboda makafi su sami ganin gari, waɗanda suke gani kuma su makance.”› Da Farisiyawan da suke tare da shi suka ji ya faɗi haka sai suka yi tambaya suka ce, “Mene? Mu ma makafi ne?” Yesu ya ce, ‹“Ai, da ku makafi ne ma, da ba ku da zunubi, amma da yake kun ce, kuna gani, zunubanku suna nan daram.›

Yohanna 10:1-5

‹“Gaskiya nake gaya muku, mutumin da bai shiga inda ake ajiye garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya hau ta katanga, ɓarawo ne, ɗan fashi kuma.› ‹Mutumin da ya shiga ta ƙofa makiyayin tumakinsa ne.› ‹Mai gadin yakan buɗe wa makiyayin ƙofa, tumakin kuma sukan saurari muryarsa. Yakan kira tumakinsa da suna, yă kuma fid da su waje.› ‹Sa’ad da ya fitar da dukan nasa waje, sai ya ja gabansu, tumakinsa kuma sukan bi shi domin sun san muryarsa.› ‹Amma ba za su taɓa bin baƙo ba; sai dai ma su guje masa don ba su san muryar baƙo ba.”›

Yohanna 10:12-13

‹Wanda aka ɗauko haya ba shi ne makiyayi mai tumakin ba. Saboda haka sa’ad da ya ga kyarkeci yana zuwa, sai yă sheƙa da gudu yă bar tumakin. Sai kyarkecin yă kai wa garken hari, yă kuma watsar da su.› ‹Mutumin yakan gudu don shi ɗan haya ne kawai, bai kuwa damu da tumakin ba.›

Yohanna 12:37-40

Ko bayan Yesu ya yi dukan waɗannan abubuwan banmamaki a gabansu, duk da haka ba su gaskata da shi ba. Wannan ya faru ne, don a cika maganar annabi Ishaya cewa, “Ubangiji, wa ya gaskata saƙonmu, ga wa kuma aka bayyana hannun ikon Ubangiji?” Saboda haka ba su iya gaskatawa ba, domin, kamar yadda Ishaya ya faɗa a wani wuri cewa, “Ya makantar da idanunsu ya kuma taurare zukatansu, don kada su gani da idanunsu, ko su fahimta a zukatansu, ko kuwa su juyo, har in warkar da su.”

Yohanna 12:48

‹Akwai mai hukunci saboda wanda ya ƙi ni, bai kuma karɓi kalmomina ba; wannan maganar da na faɗa ita ce za tă hukunta shi a rana ta ƙarshe.›

Yohanna 14:6

Yesu ya amsa ya ce, ‹“Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai dai ta wurina.›

Yohanna 14:15

‹“In kuna ƙaunata za ku yi biyayya da umarnina.›

Yohanna 14:17

‹Ruhun gaskiya. Duniya ba ta iya karɓarsa, don ba ta ganinsa ba ta kuma san shi ba. Amma kun san shi, saboda yana zama tare da ku zai kuma kasance a cikinku.›

Yohanna 14:26

‹Amma Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko cikin sunana, zai koya muku kome, zai kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku.›

Yohanna 15:26

‹“Sa’ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, Ruhun gaskiya wanda yake fitowa daga wurin Uba, zai ba da shaida game da ni.›

Yohanna 16:13

‹Amma sa’ad da shi, Ruhun gaskiya ya zo, zai bi da ku zuwa ga dukan gaskiya. Ba zai yi magana don kansa ba; zai faɗi abin da ya ji ne kaɗai, zai kuma faɗa muku abin da bai faru ba tukuna.›

Yohanna 17:17

‹Ka tsarkake su ta wurin gaskiya; maganarka ce gaskiya.›

Ayyukan Manzanni 5:3-4

Sai Bitrus ya ce, “Ananiyas, ta yaya Shaiɗan ya cika zuciyarka haka da ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya ka kuma ajiye wa kanka sauran kuɗin da ka karɓa na filin? Ba naka ba ne kafin ka sayar da shi? Bayan da ka sayar da shi kuma, kuɗin ba naka ba ne? Me ya sa ka yi tunanin yin irin wannan abu? Ba mutum ne ka yi wa ƙarya ba, Allah ne ka yi masa.”

Ayyukan Manzanni 7:51

“Ku mutane masu taurinkai, da zukata da kuma kunnuwa marasa kaciya! Kuna kama da kakanninku. Kullum kuna tsayayya da Ruhu Mai Tsarki!

Ayyukan Manzanni 20:28

Ku lura da kanku da dukan garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi. Ku zama masu kiwon ikkilisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa.

Ayyukan Manzanni 20:29-31

Na san cewa bayan na tafi, mugayen kyarketai za su shigo cikinku ba za su kuwa ƙyale garken ba. Ko cikinku ma mutane za su taso su karkatar da gaskiya don su jawo wa kansu almajirai. Saboda haka ku zauna a faɗake! Ku tuna cewa shekara uku, dare da rana ban taɓa fasa yin wa kowannenku gargaɗi ba, har da hawaye.

Ayyukan Manzanni 26:18

‹ka buɗe idanunsu su kuwa juyo daga duhu zuwa haske, daga mulkin Shaiɗan kuma zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai da kuma matsayi a cikin waɗanda aka tsarkake ta wurin bangaskiya a cikina.’›

Romawa 1:18

Ana bayyana fushin Allah daga sama a kan dukan rashin sanin Allah da kuma muguntar mutanen da suke danne gaskiya ta wurin muguntarsu,

Romawa 1:20-21

Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja. Gama ko da yake sun san Allah, ba su ɗaukaka shi a matsayin Allah ko su gode masa ba, sai dai tunaninsu ya zama banza, zukatansu masu wauta kuma suka duhunta.

Romawa 1:22

Ko da yake sun ɗauka su masu hikima ne, sai suka zama wawaye,

Romawa 1:25

Sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, suka kuma yi wa abubuwan da aka halitta sujada suna bauta musu a maimakon Mahalicci, wanda ake yabo har abada. Amin.

Romawa 2:13

Gama ba masu jin dokar ne suke da adalci a gaban Allah ba, amma waɗanda suke yin biyayya da dokar, su za a ce da su masu adalci.

Romawa 3:4

Ko kaɗan! Bari Allah yă zama mai gaskiya, kowane mutum kuma yă zama maƙaryaci. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Gama a tabbatar kana da gaskiya, sa’ad da ka yi magana, ka kuma yi nasara sa’ad da ka yi shari’a.”

Romawa 3:11-13

babu wani mai fahimta, babu wani mai neman Allah. Duk sun kauce gaba ɗaya, sun zama marasa amfani; babu wani mai aikata nagarta, babu ko ɗaya.” “Maƙogwaronsu kamar buɗaɗɗun kaburbura ne, harsunansu suna yin ƙarya.” “Dafin mugun maciji yana a leɓunansu.”

Romawa 7:12

Saboda haka fa, dokar tana da tsarki, umarnin kuma yana da tsarki, su duka suna da adalci da kuma kyau.

Romawa 9:1

Ina faɗin gaskiya a cikin Kiristi ba ƙarya nake yi ba, lamirina ya tabbatar da wannan a cikin Ruhu Mai Tsarki.

Romawa 10:2-4

Gama na shaida su a kan suna da kishi bin Allah, sai dai kishinsu ba a bisa sani ba. Da yake ba su san adalcin da yake fitowa daga Allah ba suka kuma nemi su kafa nasu, sai suka ƙi miƙa kai ga adalcin Allah. Kiristi shi ne ƙarshen doka domin a sami adalci wa kowane mai bangaskiya.

Romawa 10:17

Saboda haka, bangaskiya takan zo ne ta wurin jin saƙo, akan ji saƙon kuma ta wurin maganar Kiristi.

Romawa 11:8

kamar yadda yake a rubuce cewa, “Allah ya ba su ruhun ruɗewa, idanu don su kāsa gani, da kuma kunnuwa don su kāsa ji, har yă zuwa yau.”

Romawa 14:1

Ku karɓi wanda bangaskiyarsa ba tă yi ƙarfi ba, amma fa kada ku hukunta shi a kan abubuwan da ake da shakka a kai ba.

Romawa 16:17-18

Ina roƙonku, ’yan’uwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su. Gama irin waɗannan mutane ba sa bautar Ubangijinmu Kiristi, sai dai cikinsu. Ta wurin yaudara da kuma daɗin baki, suna ruɗin marasa wayo.

1 Korintiyawa 1:21-25

Gama tun da a cikin hikimar Allah, duniya a cikin hikimarta ba tă san shi ba, Allah ya ji daɗin ceton waɗanda suka ba da gaskiya ta wurin wautar wa’azin bishara. Yahudawa suna so su ga alama, Hellenawa kuma suna neman hikima, amma mu, muna wa’azin Kiristi wanda aka gicciye ne, wanda ya zama dutsen tuntuɓe ga Yahudawa, wauta kuma ga Al’ummai, amma ga su waɗanda Allah ya kira, Yahudawa da Hellenawa, Kiristi ikon Allah ne, da kuma hikimar Allah. Gama wautar Allah ta fi hikimar mutum, kuma rashin ƙarfin Allah ya fi ƙarfin mutum.

1 Korintiyawa 2:1-5

Da na zo wurinku ’yan’uwa, ban zo da iya magana ko wani mafificin hikima yayinda na yi muku shelar shaida game da Allah ba. Don na ƙudura a raina sa’ad da nake tare da ku cewa ba zan mai da hankali ga kome ba sai dai Yesu Kiristi wanda aka gicciye. Na zo wurinku cikin rashin ƙarfi da tsoro, da rawan jiki ƙwarai. Saƙona da wa’azina ba su zo cikin hikima da kalmomin lallashi ba, sai dai da nuna ikon Ruhu, domin kada bangaskiyarku ta dogara a kan hikimar mutane, sai dai a kan ikon Allah.

1 Korintiyawa 2:6-8

Duk da haka, muna sanar da saƙon hikima cikin waɗanda suka balaga, amma ba hikima irin ta wannan zamani ba ne, ko kuwa irin ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda za su shuɗe ba. A’a, muna magana ne a kan asirin hikimar Allah, hikimar da tun dā, take a ɓoye, wadda Allah ya ƙaddara domin ɗaukakarmu, tun kafin farkon zamanai. Ba ko ɗaya daga cikin masu mulkin wannan zamani da ya fahimce ta, gama da a ce sun fahimce ta, da ba su gicciye Ubangiji mai ɗaukaka ba.

1 Korintiyawa 2:11-13

Wane ne a cikin mutane ya san tunanin mutum, in ba ruhun mutumin da yake cikinsa ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah. Ba mu karɓi ruhun duniya ba, sai dai Ruhun da yake daga Allah, domin mu fahimci abin da Allah ya ba mu hannu sake. Wannan shi ne abin da muke sanarwa, ba da kalmomin da muka koya ta wurin hikimar mutum ba, amma da kalmomin da Ruhu yake koyarwa, muna faɗin gaskiya ta ruhaniya da kalmomin ruhaniya.

1 Korintiyawa 2:14-16

Mutumin da ba shi da Ruhu, ba ya yarda da abubuwan da suka fita daga Ruhun Allah, domin wauta ce a gare shi. Ba kuwa zai fahimce su ba, domin ta Ruhu ne ake fahimtarsu. Mutumin ruhaniya yakan gwada dukan abubuwa, amma shi kansa ba ya ƙarƙashin shari’ar mutum. “Wa ya taɓa sanin hankalin Ubangiji, har da zai koya masa?” Amma muna da tunani iri na Kiristi ne.

1 Korintiyawa 3:11

Gama babu wanda zai iya kafa wani tushen gini dabam da wanda aka riga aka kafa, wanda yake Yesu Kiristi.

1 Korintiyawa 3:18-20

Kada ku ruɗi kanku. In waninku yana tsammani cewa yana da hikima, yadda duniya ta ɗauki hikima, to, sai ya mai da kansa “wawa” don yă zama mai hikima. Gama hikimar duniyan nan, wauta ce a gaban Allah, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yakan kama masu hikima a cikin makircinsu”; kuma a rubuce yake cewa, “Ubangiji ya san dukan tunanin masu hikima banza ne.”

1 Korintiyawa 9:18

To, mene ne ladana? Ladana kaɗai shi ne, in yi wa’azin bishara, in kuma yi shi a kyauta, yadda ba zan yi amfani da ’yancina cikin wa’azin ba.

1 Korintiyawa 10:9

Kada mu gwada Kiristi yadda waɗansunsu suka yi, har macizai suka kakkashe su.

1 Korintiyawa 11:16

In akwai mai gardama da wannan, to, mu dai ba mu da wata al’ada, haka ma ikkilisiyoyin Allah.

1 Korintiyawa 11:18-19

Da farko dai, na ji cewa sa’ad da kuka taru a matsayin ikkilisiya, akwai tsattsaguwa a tsakaninku, har na fara yarda da zancen. Ba shakka dole a sami bambanci a tsakaninku don a nuna wa Allah ya amince da shi a cikinku.

1 Korintiyawa 11:27-32

Saboda haka, duk wanda ya ci burodin ko ya sha daga kwaf na Ubangiji da rashin cancanta, ya yi laifin wulaƙanta jiki da jinin Ubangiji ke nan. Dole kowa yă bincike kansa kafin yă ci burodin yă kuma sha daga kwaf ɗin. Gama duk wanda ya ci ya kuma sha ba tare da fahimtar jikin Ubangiji ba, ya ci ya kuma sha wa kansa hukunci ne. Shi ya sa da yawa a cikinku ba su da ƙarfi, suna kuma da rashin lafiya, waɗansunku kuma sun riga sun yi barci. Amma in da za mu auna kanmu sosai, da ba za mu shiga irin hukuncin nan ba. Duk da haka sa’ad da Ubangiji ya hukunta mu, ana yin mana horo ne don kada a ƙarshe a hallaka mu tare da duniya.

1 Korintiyawa 14:19-21

Amma a cikin ikkilisiya zan gwammace in yi magana da kalmomi biyar da za a fahimta don in koyar da waɗansu da a ce in yi magana da kalmomi guda dubu goma a wani harshe. ’Yan’uwa, ku daina tunani kamar yara. Wajen mugunta ku zama jarirai, sai dai wajen tunaninku, ku zama manya. A cikin Doka yana a rubuce cewa, “Ta wurin mutane masu baƙin harsuna da kuma ta leɓunan baƙi zan yi magana da waɗannan mutane, amma duk da haka, ba za su saurare ni ba,” in ji Ubangiji.

1 Korintiyawa 14:33-38

Gama Allah, ba Allah mai sa rikicewa ba ne, sai dai mai salama. Kamar yadda yake a dukan ikkilisiyoyi na tsarkaka. Ya kamata mata su zauna shiru a cikin ikkilisiyoyi. Ba su da izinin yin magana, sai dai su yi biyayya yadda Doka ta faɗi. In suna so su yi tambaya game da wani abu, ya kamata su tambayi mazansu a gida, domin abin kunya ne mace tă yi magana a cikin ikkilisiya. Shin, a kanku ne maganar Allah ta fara? Ko kuma a gare ku ne kaɗai ta iso? In wani yana tsammani shi annabi ne, ko yana da baiwar ruhaniya, bari yă gane cewa abin da nake rubuta muku umarnin Ubangiji ne. In ya ƙi kula da wannan, shi ma sai a ƙi kula da shi.

1 Korintiyawa 15:1-2

To, ’yan’uwa, ina so in tuna muku da bisharar da na yi muku wa’azinta, wadda kuka karɓa, wadda kuma kuka yanke shawara ku tsaya a kai. Ta wurin wannan bisharar ce kuka sami ceto, muddin kuna riƙe da wa’azin da na yi muku kam-kam. In ba haka ba, kun gaskata a banza ke nan.

1 Korintiyawa 15:33-34

Kada fa a ruɗe ku, “Ajiyar mugayen abokai yana ɓata hali mai kyau.” Ku koma cikin hankalinku yadda ya kamata, ku kuma daina yin zunubi, gama akwai waɗansu da ba su san Allah ba, na faɗi wannan ne don ku kunyata.

2 Korintiyawa 2:11

don kada Shaiɗan yă rinjaye mu. Da yake muna sane da dabarunsa.

2 Korintiyawa 2:14-17

Amma godiya ga Allah, wanda kullum yake bi da mu da nasara cikin Kiristi, kuma ta wurinmu, yana baza ƙanshin nan na sanin Kiristi a ko’ina. Don kuwa, a wurin Allah mu ƙanshin Kiristi ne cikin waɗanda ake ceto, da kuma waɗanda suke hanyar hallaka. Ga wani, mu warin mutuwa ne, amma ga wani kuwa, mu ƙanshin rai ne. Wa ya isa yă yi irin wannan aikin? Ba ma tallar maganar Allah don riba yadda waɗansu mutane da yawa suke yi. A maimakon haka, muna magana cikin Kiristi a gaban Allah da gaskiya, kamar mutanen da aka aika daga Allah.

2 Korintiyawa 3:6

Shi ya sa muka gwaninta a matsayinmu na masu hidimar sabon alkawari ba ta rubutacciyar Dokar ba, amma ta Ruhu; don Dokar, kisa take yi, Ruhu kuwa yana ba da rai.

2 Korintiyawa 3:14-16

Amma aka sa hankulansu suka dushe, gama har yă zuwa yau akwai lulluɓin nan a duk sa’ad da ake karatun tsohon alkawari. Ba a kawar da shi ba, sai a cikin Kiristi ne kaɗai ake kawar da shi. Har yă zuwa yau, duk sa’ad da ake karatun littattafan Musa, lulluɓin nan yakan rufe zukatansu. Amma duk sa’ad da wani ya juyo ga Ubangiji, akan kawar da lulluɓin.

2 Korintiyawa 4:2-4

Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafuncin da suke abubuwan kunya. Ba ruwanmu da ruɗu, ko yin ƙarya da kalmar Allah. Sai dai muna faɗin gaskiya a fili. Ta haka ne kowa zai yi shaidar gaskiyarmu a gaban Allah cikin zuciyarsa. Ko da bishararmu a rufe take, tana a rufe ne ga waɗanda suke hallaka. Allahn zamanin nan ya makanta hankulan marasa ba da gaskiya, yadda har ba za su iya ganin hasken bishara ta ɗaukakar Kiristi ba, wanda yake kamannin Allah.

2 Korintiyawa 10:4-6

Makaman da muke yaƙi da su, ba makamai na duniya ba ne. Sai dai na ikon Allah ne, masu rushe wuraren mafaka masu ƙarfi. Muna ka da masu gardama da kowane tunanin ɗaga kai da yake kafa kansa gāba da sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Kiristi. A shirye muke mu hori kowane rashin biyayya, sa’ad da biyayyarku ta cika.

2 Korintiyawa 11:3-4

Sai dai ina tsoro kada yă zama, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa’u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Kiristi. Gama in wani ya zo wurinku yana wa’azin wani Yesu dabam da wanda muka yi wa’azinsa, ko kuma in kun karɓi wani ruhu dabam da wanda kuka karɓa, ko wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, ya nuna kun yarda da su ke nan cikin sauƙinkai.

2 Korintiyawa 11:13-15

Gama irin waɗannan mutane manzannin ƙarya ne, ma’aikata ne masu ruɗi, sun ɓad da kamanni kamar su manzannin Kiristi ne. Ba abin mamaki ba ne, gama Shaiɗan kansa ma yana ɓad da kamanni kamar shi mala’ikan haske ne. Don haka, ba abin mamaki ba ne, in bayin Shaiɗan sun ɓad da kamanni kamar su bayin adalci ne. A ƙarshe, za a sāka musu gwargwadon ayyukansu.

2 Korintiyawa 13:5

Ku gwada kanku ku gani ko kuna cikin bangaskiya; ku auna kanku. Ashe, ba ku san cewa Kiristi Yesu yana cikinku ba? Sai ko in kun fāɗi gwajin.

Galatiyawa 1:6-7

Ina mamaki yadda kuka yi saurin yashe wanda ya kira ku ta wurin alherin Kiristi, kuna juyewa ga wata bishara dabam wadda a gaskiya ba bishara ba ce ko kaɗan. Tabbatacce waɗansu mutane suna birkitar da ku, suna kuma ƙoƙari su karkatar da bisharar Kiristi.

Galatiyawa 1:8-9

Amma ko mu, ko mala’ika daga sama ya yi wa’azin wata bishara dabam da wadda muka yi muku, bari yă zama la’ananne har abada! Kamar yadda muka riga muka faɗa, haka yanzu ma ina ƙara cewa in wani yana muku wa’azin wata bishara dabam da wadda kuka karɓa, bari yă zama la’ananne har abada!

Galatiyawa 1:10-12

Za a ce, ina ƙoƙarin neman amincewar mutane ne, ko amincewa ta Allah? Ko kuwa ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne? Da a ce har yanzu ina ƙoƙarin faranta wa mutane zuciya ne, ai, da ban zama bawan Kiristi ba. Ina so ku sani ’yan’uwa, cewa bisharar da nake wa’azi, ba mutum ne ya ƙago ta ba. Ban karɓe ta daga wurin wani mutum ba, ba a kuma koya mini ita ba, a maimako, na karɓe ta, ta wurin wahayi daga Yesu Kiristi ne.

Galatiyawa 2:4-5

Wannan zancen kaciya ya taso domin waɗansu ’yan’uwan ƙarya sun shiga cikinmu domin su yi leƙe a kan ’yancin da muke da shi a cikin Kiristi Yesu, su kuma mai da mu bayi. Ba mu kuwa ba su zarafi ba ko kaɗan, don gaskiyar bishara ta ci gaba da kasance tare da ku.

Galatiyawa 2:11-14

Sa’ad da Bitrus ya zo Antiyok, na tsawata masa ido da ido don laifinsa a fili yake. Kafin waɗansu mutane su zo daga wurin Yaƙub, yakan ci abinci tare da Al’ummai. Amma da suka iso, sai ya fara janyewa, ya kuma ware kansa daga wajen Al’ummai domin yana tsoron waɗanda suke ƙungiyar masu kaciya. Sauran Yahudawa suka haɗa kai da shi a munafuncinsa har Barnabas ma ya bauɗe. Da na ga cewa ba sa yin daidai da gaskiyar bishara, sai na ce wa Bitrus a gabansu duka, “Kai mutumin Yahuda ne, duk da haka kana rayuwa kamar Ba’al’umme ba kamar mutumin Yahuda ba. To, yaya aka yi, kana tilasta Al’ummai su bi al’adun Yahudawa?

Galatiyawa 3:1

Ya ku Galatiyawa marasa azanci! Wa ya ruɗe ku? A idanunku aka bayyana Yesu Kiristi gicciyeyye a sarari.

Galatiyawa 6:1-3

’Yan’uwa, in an kama wani yana cikin yin zunubi, ku da kuke masu ruhaniya ya kamata ku komo da shi a kan hanya a hankali. Amma ku lura da kanku, domin kada maimakon dawowa da ɗan’uwanku, ku ma ku fāɗi cikin jarraba. Ku ɗauki nawayar juna, a haka kuwa za ku cika dokar Kiristi. In wani yana tsammani shi wani abu ne alhali kuwa shi ba kome ba, ruɗin kansa yake yi.

Galatiyawa 6:6-8

Duk haka, wanda aka koya wa maganar Kiristi, bari yă raba abubuwan nan na alheri tare da wanda ya koyar da shi. Kada a ruɗe ku. Ba a yi wa Allah ba’a. Mutum yakan girbe abin da ya shuka ne. Wanda ya yi shuki don yă gamshi mutuntakarsa, daga wannan mutuntaka zai girbi hallaka. Wanda ya yi shuki domin yă gamshi Ruhu, daga Ruhu zai girbi rai madawwami.

Afisawa 4:14-15

An yi wannan kuwa don kada mu koma zama kamar yara, muna ta canja zukatanmu game da abin da muka gaskata don kawai wani ya faɗa mana wani abu dabam, ko domin wani ya yi wayo ya ruɗe mu, ya sa ƙarya ta zama kamar gaskiya. Ya kamata kullum ƙauna tă sa mu faɗa gaskiya. Ta haka za mu yi girma a kowace hanya, mu kuma zama kamar Kiristi, wanda yake kan

Afisawa 4:17-18

To, ina dai faɗa muku, ina kuma nace faɗa muku a cikin Ubangiji, cewa kada ku ci gaba da yin rayuwa kamar yadda Al’ummai suke yi, masu banzan tunani. Suna a cikin duhu a fahimtarsu, kuma a rabe suke daga ran Allah saboda jahilcin da yake cikinsu ta dalilin taurarewar zukatansu.

Afisawa 4:25

Saboda haka dole kowannenku yă bar yin ƙarya, yă kuma riƙa faɗa wa maƙwabcinsa gaskiya, gama dukanmu gaɓoɓi jiki ɗaya ne.

Afisawa 4:29

Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za tă zama da amfani ga masu jinta.

Afisawa 5:6

Kada wani yă ruɗe ku da kalmomin wofi, gama saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake zuwa a kan marasa biyayya.

Afisawa 5:8-10

Gama a dā zukatanku sun cika da duhu, amma yanzu ku haske ne a cikin Ubangiji. Ku yi rayuwa kamar ’ya’yan haske (domin amfanin haske ya ƙunshi nagarta, adalci, da kuma gaskiya) ku nemi abin da zai gamshi Ubangiji.

Afisawa 5:11

Ku yi nesa da ayyukan duhun da mutane suke yi, a maimakon haka, ku tona su.

Afisawa 6:12

Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama.

Afisawa 6:14-17

Saboda haka fa ku dāge, ku sa gaskiya tă zama ɗamararku, adalci yă zama sulkenku, shirin kai bisharar salama yă zama kamar takalmi a ƙafafunku. Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kibiyoyin wutar Mugun nan da ita. Ku kuma ɗauki hular kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah.

Filibbiyawa 1:9-10

Addu’ata ita ce ƙaunarku tă yi ta cin gaba da ƙaruwa cikin sani da kuma zurfin ganewa, don ku iya rarrabe abin da yake mafi kyau, ku kuma zama da tsarki, marasa aibi har yă zuwa ranar Kiristi,

Kolossiyawa 2:4

Ina faɗa muku wannan ne don kada wani yă ruɗe ku da daɗin baki.

Kolossiyawa 2:8

Ku lura kada wani yă ruɗe ku da ilimin banza da wofi. Wannan koyarwa ta mutane ce kawai. Ta fito daga ikokin wannan duniya ne ba daga Kiristi ba.

Kolossiyawa 2:18

Kada ku yarda wani yă ɓata ku, cewa shi wani abu ne don yă ga wahayi. Irin mutumin nan yakan nuna ƙasƙancin kai na ƙarya, yă kuma ce yana yi wa mala’iku sujada. Irin mutumin nan yana kumbura kansa ba dalili, sai son zuciya irin na halin mutuntaka.

Kolossiyawa 2:20-23

Kun mutu tare da Kiristi. Yanzu ƙa’idodin wannan duniya ba su da iko a kanku. Don me kuke zama har yanzu kamar ku nasu ne? Kuna biyayya da umarnansu cewa, “Kada ka kama! Kada ka ɗanɗana! Kada ka taɓa”? Irin waɗannan dokoki suna magana a kan abubuwan da ba sa daɗewa. Su ayyukan mutane ne, sun kuma fito daga koyarwar mutane. Yin biyayya da irin waɗannan ƙa’idodi za su yi kamar su ne abu mafi kyau da za a yi. Sukan yi kamar suna sa a ƙaunaci Allah sosai a kuma kasance da sauƙinkai a kuma kasance da kamunkai. Amma ba su da wani iko a kan sha’awace-sha’awacenmu.

Kolossiyawa 3:9-10

Kada ku yi wa juna ƙarya, da yake kun tuɓe tsohon halinku tare da ayyukansa kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa.

1 Tessalonikawa 5:21

amma ku gwada kome, ku riƙe abin da yake mai kyau,

2 Tessalonikawa 2:3

Kada ku bar wani yă ruɗe ku ko ta yaya, gama wannan rana ba za tă zo ba sai an yi tawayen nan an kuma bayyana mutumin tawayen nan, mutumin da aka ƙaddara ga hallaka.

2 Tessalonikawa 2:9-12

Zuwan mai tawayen nan zai zama ta wurin aikin Shaiɗan da aka bayyana cikin kowane irin ayyukan banmamaki, alamu da abubuwan banmamaki na ƙarya, da kuma cikin kowace irin muguntar da take ruɗin waɗanda suke hallaka. Sun hallaka ne domin sun ƙi su ƙaunaci gaskiya don su sami ceto. Saboda haka Allah zai aiko musu da babban ruɗu don su gaskata ƙarya don kuma a hukunta dukan waɗanda ba su gaskata gaskiyar ba sai dai suke jin daɗin mugunta.

2 Tessalonikawa 2:15

Saboda haka fa, ’yan’uwa, sai ku tsaya daram ku riƙe koyarwar da muka miƙa muku, ko ta wurin maganar baki ko kuma ta wurin wasiƙa.

2 Tessalonikawa 3:6

A cikin sunan Ubangiji Yesu Kiristi, muna muku umarni, ’yan’uwa, da ku kiyaye kanku daga kowane ɗan’uwa mai zaman banza da ba ya rayuwa bisa ga koyarwar da kuka karɓa daga wurinmu.

1 Timoti 1:3-7

Kamar yadda na gargaɗe ka sa’ad da zan je Makidoniya, ka zauna can Afisa domin ka umarci waɗansu mutane kada su koyar da ƙa’idodin ƙarya nan gaba ko su ba da kansu ga tatsuniyoyi da ƙididdigar asali marar iyaka. Waɗannan suna kawo faɗa a maimakon aikin Allah wanda yake ta wurin bangaskiya. Maƙasudin wannan umarnin dai ƙauna ce, wadda take zuwa daga zuciya mai tsabta da lamiri mai kyau da kuma sahihiyar bangaskiya. Waɗansu sun bauɗe daga waɗannan al’amura, suka koma ga maganganu marasa ma’ana. So suke su zama malaman doka, ba tare da fahimtar abin da suke faɗa ba, balle abubuwan da suke ta nacewa a kai.

1 Timoti 2:4-7

wanda yake so dukan mutane su sami ceto su kuma zo ga sanin gaskiya. Gama Allah ɗaya ne, matsakanci kuma ɗaya tsakanin Allah da mutane, shi ne kuwa Kiristi Yesu, wanda ya ba da kansa fansa domin dukan mutane, shaidar da aka bayar a daidai lokaci. Don haka ne aka sa ni mai wa’azi, da manzo kuma, gaskiya nake faɗa, ba ƙarya ba, na kuma zama malami mai koya wa al’ummai al’amarin bangaskiya da kuma na gaskiya.

1 Timoti 2:11-14

Ya kamata mace ta riƙa koyo cikin natsuwa da cikakkiyar biyayya. Ban ba mace izini ta koyar ko tă yi mulki a kan namiji ba; sai dai ta zauna shiru. Gama Adamu ne aka fara halitta, sa’an nan Hawwa’u. Ba kuma Adamu ne aka yaudara ba; macen ce aka yaudara ta kuma zama mai zunubi.

1 Timoti 4:1-2

Ruhu a sarari ya faɗa cewa a kwanakin ƙarshe waɗansu za su watsar da bangaskiya su bi ruhohi masu ruɗu da kuma abubuwan da aljanu suke koyarwa. Irin koyarwan nan tana zuwa ne daga waɗansu munafukai maƙaryata, waɗanda aka yi wa lamirinsu kaca-kaca.

1 Timoti 4:6-7

In ka nuna wa ’yan’uwa waɗannan abubuwa, za ka zama mai hidima mai kyau na Kiristi Yesu, wanda aka goya cikin gaskiyar bangaskiya da kuma koyarwa mai kyau wadda ka bi. Ka kiyaye kanka daga tatsuniyoyi na rashin tsoron Allah da labaru banza na tsofaffin mata; a maimako, ka hori kanka ga zama mai tsoron Allah.

1 Timoti 4:11-16

Ka umarta ka kuma koyar da waɗannan abubuwa. Kada ka bar wani yă rena ka domin kai matashi ne, sai dai ka zama gurbi ga masu bi cikin magana, cikin rayuwa, cikin ƙauna, cikin bangaskiya da kuma cikin zaman tsarki. Kafin in zo, ka ci gaba da karanta wa mutane Nassi, da yin wa’azi, da kuma koyarwa. Kada ka yi sakaci da baiwarka, wadda aka ba ka ta wurin saƙon annabci sa’ad da ƙungiyar dattawa suka ɗibiya hannuwa a kanka. Ka yi ƙwazo cikin waɗannan batuttuwa; ka ba da kanka gaba ɗaya gare su, don kowa yă ga ci gabanka. Ka kula da rayuwarka da kuma koyarwarka da kyau. Ka daure a cikinsu, domin in ka yi, za ka ceci kanka da kuma masu sauraronka.

1 Timoti 5:17-18

Dattawan da suka bi da al’amuran ikkilisiya da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu, musamman waɗanda aikinsu wa’azi ne da kuma koyarwa. Gama Nassi ya ce, “Kada ka sa wa bijimi takunkumi yayinda yake sussukar hatsi,” da kuma, “Ma’aikaci ya cancanci hakkinsa.”

1 Timoti 5:19-22

Kada ka saurari ƙara game da dattijo sai da shaidu biyu ko uku. Amman waɗannan dattawa waɗanda suke yin zunubi kuwa sai ka kwaɓe su a gaban jama’a, don saura su ji tsoro. Na gama ka da Allah, da Kiristi Yesu, da kuma zaɓaɓɓun mala’iku, ka kiyaye waɗannan abubuwa ƙwarai da gaske, kada ka nuna bambanci. Kada ka yi garajen ɗibiya hannuwa, kada kuma ka yi tarayya a cikin zunuban waɗansu. Ka kiyaye kanka da tsarki.

1 Timoti 6:3-5

In wani yana koyarwar ƙarya bai kuma yarda da sahihiyar koyarwar Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma koyarwa ta tsoron Allah ba, yana cike da girman kai bai kuma san kome ba. Yana da mugun halin son gardama da muhawwara game da kalmomin da suke kawo kishi, rikici, maganar ƙeta, da mugayen zace-zace da yawan tankiya tsakanin mutane masu mugun hali, waɗanda aka raba su da gaskiya, suke kuma tsammani cewa bin Allah wata hanya ce ta samun kuɗi.

1 Timoti 6:20-21

Timoti, ka lura da abin da aka danƙa maka amana. Ka yi nesa da masu maganganun rashin tsoron Allah da kuma yawan mūsu da ake ƙarya, ake ce da shi ilimi, wanda waɗansu suka furta kuma ta yin haka suka bauɗe daga bangaskiya. Alheri yă kasance tare da ku.

2 Timoti 2:14

Ka riƙa tuna masu da haka, ka kuma gama su da Allah, kada su yi jayayya a kan maganganu, don ba ta da wani amfani, sai ɓad da masu ji kawai take yi.

2 Timoti 2:15-16

Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka gabatar da kanka a gaban Allah a matsayin wanda aka amince da shi, ma’aikaci wanda ba shi da dalilin jin kunya wanda kuma yake fassara kalmar gaskiya daidai. Ka yi nesa da maganganun banza na rashin tsoron Allah, gama waɗanda suka mai da hankali ga yin waɗannan za su ƙara zama marasa tsoron Allah.

2 Timoti 2:17-19

Koyarwarsu za tă bazu kamar ruɓaɓɓen gyambo. A cikinsu akwai Himenayus da Filetus, waɗanda suka bauɗe daga gaskiya. Suna cewa tashin matattu ya riga ya faru, suna kuma ɓata bangaskiyar waɗansu. Duk da haka, ƙaƙƙarfan tushen nan na Allah yana nan daram, an hatimce shi da wannan rubutu, “Ubangiji ya san waɗanda suke nasa,” da kuma, “Duk wanda ya bayyana yarda ga sunan Ubangiji, to, dole yă yi nesa da aikata mugunta.”

2 Timoti 2:23-26

Kada wani abu yă haɗa ka da gardandamin banza da wofi, domin ka san yadda suke jawo faɗa. Bai kamata bawan Ubangiji yă zama mai neman faɗa ba; a maimako, dole yă nuna alheri ga kowa, mai iya koyarwa, mai haƙuri kuma. Waɗanda suke gāba da shi kuwa dole yă yi musu gargaɗi cikin hankali, da fata Allah zai sa su tuba su kai ga sanin gaskiya, su kuma dawo cikin hankulansu su kuɓuta daga tarkon Iblis, wanda ya sa suka zama kamammu don su aikata nufinsa.

2 Timoti 3:2-5

Mutane za su zama masu son kansu, masu son kuɗi, masu taƙama, masu girman kai, masu zage-zage, marasa biyayya ga iyayensu, marasa godiya, marasa tsarki, marasa ƙauna, marasa gafartawa, masu ɓata sunayen waɗansu, marasa kamunkai, masu ƙeta, marasa ƙaunar nagarta, masu cin amana, marasa hankali, waɗanda sun cika da ɗaga kai, masu son jin daɗi a maimakon ƙaunar Allah suna riƙe da siffofin ibada, amma suna mūsun ikonta. Kada wani abu yă haɗa ka da su.

2 Timoti 3:6-7

Irin su ne suke saɗaɗawa su shiga gidaje suna rinjayar mata marasa ƙarfin hali, waɗanda zunubai suka sha kansu, mugayen sha’awace-sha’awace kuma sun ɗauke hankulansu, kullum suna koyo amma ba sa taɓa iya yarda da gaskiya.

2 Timoti 3:8-9

Kamar dai yadda Yannes da Yamberes suka tayar wa Musa, haka waɗannan mutane ma suke tayar wa gaskiya, mutane masu ɓataccen hankali, waɗanda, in ana zancen bangaskiya ne, to, fa ba sa ciki. Sai dai ba za su yi nisa ba, don rashin hankalinsu zai bayyana ga kowa, kamar na mutanen nan biyu.

2 Timoti 3:12-13

Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna na Kiristi Yesu, za su sha tsanani. Mugayen mutane da masu ruɗi kuwa, ƙara muni za su riƙa yi, suna yaudara, ana kuma yaudararsu.

2 Timoti 3:14-17

Amma kai kam, ka ci gaba da abin da ka koya ka kuma tabbatar, gama ka san waɗanda ka koye su daga gare su, da kuma yadda tun kana ɗan jinjiri ka san Nassosi masu tsarki, waɗanda suke iya sa ka zama mai hikima zuwa ceto ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsawatarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci, domin mutumin Allah yă zama shiryayye sosai saboda kowane kyakkyawan aiki.

2 Timoti 4:2-4

Ka yi wa’azin Maganar Allah, ka zama a shirye a kullum, ko da zarafi, ko babu zarafi, ka yi gyara, ka kwaɓe, ka kuma ƙarfafa, da matuƙar haƙuri da koyarwa cikin natsuwa. Gama lokaci yana zuwa da mutane ba za su jure da sahihiyar koyarwa ba. A maimako, don cimma burinsu, za su taro wa kansu malamai masu yawa, domin su faɗi abin da kunnuwansu masu ƙaiƙayi suke so su ji. Za su juye kunnuwansu daga gaskiya zuwa ga jin tatsuniyoyi.

Titus 1:9-16

Dole yă riƙe tabbataccen saƙon nan kam-kam yadda aka koyar, don yă iya ƙarfafa waɗansu da sahihiyar koyarwa yă kuma ƙaryata waɗanda suke gāba da shi. Gama akwai ’yan tawaye da yawa, masu surutun banza da masu ruɗi, musamman ƙungiyar masu kaciya. Dole a hana su yin magana, domin suna kawo rushewar iyalai ta wurin koyar da abubuwan da bai kamata su koyar ba don neman ƙazamar riba. Wani daga cikin annabawansu ma ya ce, “Kiretawa a kullum maƙaryata ne, mugayen dabbobi, ragwaye haɗamammu.” Wannan shaida gaskiya ce. Saboda haka, sai ka tsawata musu sosai, don su zama sahihai a wajen bangaskiya, ba za su kuma mai da hankalinsu ga tatsuniyoyin Yahudawa ko ga umarnan waɗanda suke ƙin gaskiya ba. Ga tsarkaka kuwa, kome mai tsarki ne, amma ga waɗanda suke marasa tsarki da kuma marasa ba da gaskiya, ba abin da yake da tsarki. Gaskiya dai, hankulansu da lamirinsu duk marasa tsarki ne. Sun ɗauka cewa sun san Allah, amma ta wurin ayyukansu suna mūsunsa. Sun zama abin ƙyama, marasa biyayya, ba su ma isa su yi aiki nagari ba.

Titus 2:1-2

Dole ka koyar da abin da yake bisa sahihiyar koyarwa. Ka koya wa tsofaffin maza su kasance masu sauƙinkai, waɗanda suka cancanci girmamawa, masu kamunkai, sahihai wajen bangaskiya, da ƙauna da kuma jimiri.

Titus 2:3-5

Haka ma, ka koya wa tsofaffin mata su zama masu bangirma cikin rayuwarsu, ba masu ɓata suna ko masu jarrabar shan giya ba, sai dai su zama masu koyar da abin da yake nagari. Sa’an nan za su iya su koya wa mata masu ƙuruciya su ƙaunaci mazansu da ’ya’yansu, su kasance da kamunkai da kuma tsarki, masu aiki a gida, masu kirki da kuma masu biyayya ga mazansu, don kada wani yă rena maganar Allah.

Titus 2:6-8

Haka kuma, ka ƙarfafa samari su zama masu kamunkai. Cikin kowane abu ka zama musu misali mai kyau ta wurin aikata abin da yake nagari. A cikin koyarwarka ka nuna mutunci da ƙwazo da kuma sahihanci cikin maganar da ba za a iya kushewa ba, domin masu gāba da kai su ji kunya, su kuma rasa wani mugun abin da za su faɗa game da mu.

Titus 2:9-10

Ka koya wa bayi su yi wa iyayengijinsu biyayya cikin kowane abu, su yi ƙoƙari su gamshe su, kada su mayar musu da magana, kada kuma su yi musu sata, sai dai su nuna za a iya amince da su sosai, don ta kowace hanya su sa koyarwa game da Allah Mai Cetonmu ta zama abin ɗaukan hankali.

Titus 3:9-11

Amma ka guji jayayyar banza da ƙididdigar asali da gardandami da faɗace-faɗace game da Doka, gama ba su da riba kuma aikin banza ne. Ka gargaɗe mutumin da yake kawo tsattsaguwa sau ɗaya, ka kuma gargaɗe shi sau na biyu. Bayan haka, kada wani abu yă haɗa ka da shi. Ka dai san cewa irin mutumin nan ya taurare kuma mai zunubi ne; ya yanke wa kansa hukunci.

Ibraniyawa 2:1-3

Dole mu ƙara mai da hankali sosai ga abubuwan da muka ji, don kada mu kauce. Gama in saƙon da aka faɗi ta bakin mala’iku ya zama tabbatacce, kuma kowane ƙeta umarni da rashin biyayya suka karɓi sakamakonsu da ya dace, yaya za mu tsira in muka ƙyale irin wannan babban ceto? Wannan ceto, wanda Ubangiji ne ya fara sanar, aka kuma tabbatar mana ta bakin waɗanda suka ji shi.

Ibraniyawa 3:12

Ku lura fa, ’yan’uwa, cewa kada waninku yă kasance da zuciya mai zunubi marar bangaskiya da takan juye daga bin Allah mai rai.

Ibraniyawa 3:18-19

Kuma ga su wane ne Allah ya rantse cewa ba za su taɓa shiga hutunsa ba, in ba ga marasa biyayyan nan ba? Saboda haka mun ga cewa ba su iya shiga ba, saboda rashin bangaskiyarsu ne.

Ibraniyawa 4:12-13

Maganar Allah tana da rai, tana kuma da ƙarfin aiki. Ta fi kowane takobi mai baki biyu kaifi. Maganarsa takan ratsa har ciki-ciki, tana raba rai da ruhu, gaɓoɓi da kuma ɓargon ƙashi; har sai ta tone ainihi wane ne muke. Babu wani abu cikin dukan halittar da yake ɓoye daga fuskar Allah. Kowane abu a buɗe yake yana kuma a shimfiɗe a idanun wanda dole mu ba da lissafi a gare shi.

Ibraniyawa 6:4-6

Waɗanda suka taɓa samun haske, waɗanda suka ɗanɗana kyauta ta sama, waɗanda suka sami rabo cikin Ruhu Mai Tsarki, waɗanda suka ɗanɗana daɗin maganar Allah da kuma ikokin zamani mai zuwa, ba ya yiwuwa a sāke kawo su ga tuba in suka kauce, domin suna sāke gicciye Ɗan Allah ke nan suna kuma kunyata shi a gaban jama’a.

Ibraniyawa 10:26-29

Ba wata hadayar da za a yi don mutanen da suka yanke shawara su yi ci gaba da yin zunubi da gangan bayan sun sami sanin gaskiya. A maimakon haka za su kasance da babban fargabar hukunci da kuma ta ƙunar wuta wadda za tă cinye abokan gāban Allah. Duk wanda ya ƙi ya kiyaye dokar Musa akan kashe shi ba tausayi, a kan shaidar mutum biyu ko uku. Wane irin hukunci mai tsanani ne kuke tsammani zai dace da mutumin da ya nuna rashin bangirma ga Ɗan Allah, wanda ya yi banza da jinin nan na alkawarin da ya tsarkake shi, wanda kuma ya zargi Ruhun alheri?

Ibraniyawa 12:15-17

Ku lura fa kada wani yă kāsa samun alherin Allah, kada kuma wani tushen ɗacin rai yă tsira har yă kawo rikici, yă kuma ƙazantar da mutane da yawa. Ku lura kada wani yă zama mai fasikanci, ko marar tsoron Allah kamar Isuwa, wanda saboda ƙwaryar abinci ɗaya tak ya sayar da gādonsa na ɗan fari. Daga baya, kamar yadda kuka sani, sa’ad da ya nemi yă gāji wannan albarka, aka ƙi shi. Bai sami zarafin tuba ba, ko da yake ya nemi albarkan nan da hawaye.

Ibraniyawa 13:9

Kada a ɗauke muku hankali da sababbin koyarwa dabam-dabam. Yana da kyau zukatanmu su ƙarfafa ta wurin alheri, ba ta wurin abinci waɗanda ba su da amfani ga waɗanda suke cinsu.

Yaƙub 1:3-5

domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi daurewa. Dole daurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba. In waninku ya rasa hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi.

Yaƙub 1:22-24

Kada ku zama masu ji kawai, ku ruɗi kanku. A maimakon haka ku zama masu yin abin da ta ce. Duk wanda yake ji magana ne kawai, bai kuwa aikata abin da ta ce ba, yana kama da mutumin da ya kalli fuskarsa a madubi bayan ya kalli kansa, sa’ad da ya tashi daga wurin, nan da nan sai yă manta da kamanninsa.

Yaƙub 3:1-2

Kada yawancinku su so ɗaukan kansu a matsayin malamai, ’yan’uwana, domin kun san cewa mu da muke koyarwa za a yi mana shari’a mafi tsanani. Dukanmu mukan yi tuntuɓe a hanyoyi dabam-dabam. In wani bai taɓa yin kuskure a cikin maganarsa ba, shi cikakke ne, yana kuma iya ƙame dukan jikinsa.

Yaƙub 3:5-6

Haka ma harshe yake, ga shi ɗan ƙanƙanin gaɓar jiki ne, amma sai manyan fariya. Ku dubi yadda ɗan ƙaramin ƙyastu yake ƙuna wa babban jeji wuta mana. Harshe ma wuta ne! A cikin duk gaɓoɓinmu, harshe shi ne tushen kowace irin mugunta, mai ɓata mutum gaba ɗaya, mai zuga zuciyar mutum ta tafasa, shi kuwa jahannama ce take zuga shi.

1 Bitrus 2:7-8

A gare ku da kuka gaskata, wannan dutse mai daraja ne. Amma ga waɗanda ba su gaskata ba, “Dutsen da magina suka ƙi ya zama dutsen kusurwar gini, kuma, “Dutse ne da yake sa mutane tuntuɓe kuma fā ne da yake sa su fāɗi.” Sun yi tuntuɓe domin sun ƙi su yi biyayya da saƙon, wanda kuma yake abin da aka ƙaddara musu.

1 Bitrus 3:10

Gama, “Duk wanda yake so yă ji daɗin rayuwa, yă kuma ga kwanaki masu kyau dole yă ƙame harshensa daga mugunta leɓunansa kuma daga maganar yaudara.

1 Bitrus 3:15-16

Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi, tare da lamiri mai kyau, saboda waɗanda suke maganganun banza a kan kyawawan ayyukanku cikin Kiristi su ji kunya da irin ɓata suna da suke yi.

1 Bitrus 5:8-9

Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye. Ku yi tsayayya da shi, kuna tsayawa daram cikin bangaskiya, domin kun san cewa ’yan’uwanku ko’ina a duniya suna shan irin wahalolin nan.

2 Bitrus 1:20-21

Gaba da kome dai, dole ku gane cewa babu annabcin Nassin da ya fito daga fassarar annabi da kansa. Gama annabci bai taɓa samo tushensa daga nufin mutum ba, sai dai mutane sun yi magana daga Allah yayinda Ruhu Mai Tsarki ya bishe su.

2 Bitrus 2:1-3

Amma a dā akwai annabawan ƙarya a cikin mutane, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku. A ɓoye za su shigar da karkataccen koyarwa mai hallaka, har ma su yi mūsun Ubangiji mai iko duka wanda ya saye su suna kawo wa kansu hallaka farat ɗaya. Da yawa za su bi hanyoyinsu na rashin kunya su kuma sa a rena hanyar gaskiya. Cikin kwaɗayinsu waɗannan malaman ƙarya za su cuce ku da tatsuniyoyin da suka ƙaga. Hukuncinsu yana a rataye a kansu tun da daɗewa, hallakarsu kuma ba ta barci.

2 Bitrus 2:20-21

In har sun kuɓuta daga lalacin duniya ta wurin sanin Ubangijinmu da kuma Mai Cetonmu Yesu Kiristi sai suka sāke koma a cikin lalacin, har ya rinjaye su, za su fi muni a ƙarshe fiye da farko. Zai fi musu kyau da ba su taɓa sanin hanyar adalci ba, fiye da a ce sun sani sa’an nan su juya bayansu ga umarni mai tsarkin nan da aka ba su.

2 Bitrus 3:16

Haka yake rubutu cikin dukan wasiƙunsa, yana magana a cikinsu a kan waɗannan al’amura. Wasiƙunsa sun ƙunshi waɗansu abubuwa masu wuyar fahimta, waɗanda jahilai da kuma waɗanda ba tsayayyu ba ne suke murɗe ma’anarsu, kamar yadda suke yi da sauran Nassosi, ta haka suke jawo wa kansu hallaka.

2 Bitrus 3:17-18

Saboda haka, abokaina ƙaunatattu, da yake kun riga kun san wannan, sai ku zauna a faɗake don kada a ɗauke hankalinku ta wurin kuskuren marasa bin dokan nan har ku fāɗi daga matsayinku. Sai dai ku yi girma cikin alheri da sanin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi. A gare shi ɗaukaka ta tabbata yanzu da har abada! Amin.

1 Yohanna 1:5-6

Wannan shi ne saƙon da muka ji daga wurinsa, muna kuma sanar da ku cewa Allah haske ne; a cikinsa kuwa babu duhu ko kaɗan. In muka ce muna zumunci da shi amma muna tafiya cikin duhu, ƙarya muke yi, kuma ba ma rayuwa bisa ga gaskiya.

1 Yohanna 2:3-6

Ta haka za mu tabbata cewa mun san shi in muna yin biyayya da umarnansa. Mutumin da ya ce, “Na san shi,” amma ba ya yin abin da ya umarta, maƙaryaci ne, gaskiya kuwa ba ta cikinsa. Amma in wani ya yi biyayya da maganarsa, ƙaunar Allah ta zama cikakkiya ke nan a cikinsa. Ta haka muka san cewa muna cikinsa. Duk wanda ya ce yana rayuwa a cikinsa dole yă yi tafiya kamar yadda Yesu ya yi.

1 Yohanna 2:26-27

Ina rubuta muku waɗannan abubuwa ne game da waɗanda suke ƙoƙari su sa ku kauce. Game da ku kuwa, shafan nan da kuka karɓa daga gare shi tana nan a cikinku, ba kwa kuma bukata wani yă koyar da ku. Amma kamar yadda shafan nan tasa tana koya muku kome, ita kuwa gaskiya ce ba ƙarya ba, yadda dai ta koya muku, to, sai ku zauna a cikinsa.

1 Yohanna 4:1-3

Abokaina ƙaunatattu, ba kowane ruhu za ku gaskata ba, sai dai ku gwada ruhohi don ku ga ko daga Allah ne, domin annabawan ƙarya da yawa sun fito duniya. Ga yadda za ku gane Ruhun Allah, duk ruhun da ya yarda cewa Yesu Kiristi ya zo cikin jiki, to, daga Allah yake. Amma duk ruhun da bai yarda da Yesu ba, ba daga Allah ba ne, ruhun magabcin Kiristi ne, wanda kuka ji yana zuwa, har ma ya riga ya shigo duniya.

1 Yohanna 4:5-6

Su daga duniya ne saboda haka suke magana yadda duniya take ganin abubuwa, duniya kuwa tana sauraronsu. Mu daga Allah ne, kuma duk wanda ya san Allah yakan saurare mu. Amma duk wanda ba daga Allah ba, ba ya sauraronmu. Ta haka ne muke gane Ruhun gaskiya, da kuma ruhun ƙarya.

2 Yohanna 1:6

Ƙauna, ita ce mu yi biyayya ga umarnansa. Kamar yadda kuka ji tun da fari, umarninsa shi ne ku yi zaman ƙauna.

2 Yohanna 1:7-8

Masu ruɗi da yawa, waɗanda ba su yarda da zuwan Yesu Kiristi cikin jiki ba, sun riga sun fito a duniya. Duk irin mutumin nan mai ruɗi ne kuma magabcin Kiristi. Ku lura don kada ku yi hasarar aikin da kuka yi, sai dai ku sami cikakken lada.

2 Yohanna 1:9-11

Duk mutumin da bai tsaya a kan koyarwar Kiristi ba, amma ya yi ƙari a kanta, mutumin nan ba shi da Allah. Amma wanda ya tsaya a kan koyarwar Kiristi, yana da Uban da kuma Ɗan. Duk wanda ya zo wurinku bai kuma kawo koyarwan nan ba, kada ku karɓe shi a gidanku ko ku marabce shi. Duk wanda ya karɓe shi yana tarayya da mugun aikinsa ke nan.

3 Yohanna 1:9-10

Na rubuta wa ikkilisiya, amma Diyotirefes, wanda yake son zama na farko, ya ƙi yă yi hulɗa da mu. Saboda haka in na zo, zan tone abin da yake yi, yana surutu game da mu, yana ɓaɓɓata mu. Wannan ma bai ishe shi ba, har yana ƙin marabtar ’yan’uwa. Yana hana waɗanda suke so yin haka, yana ma korinsu daga ikkilisiya.

Yahuda 1:3-4

Abokaina ƙaunatattu, ko da yake na yi marmari ƙwarai in rubuta muku game da ceton nan namu, sai na ga ya dace in rubuta, in gargaɗe ku ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiya wadda aka danƙa wa mutane masu tsarki na Allah sau ɗaya tak. Na faɗa haka ne domin waɗansu mutanen da aka rubuta hukuncinsu tun dā sun shiga cikinku a ɓoye. Su fa marasa tsoron Allah ne. Su ne waɗanda suka mai da alherin Allahnmu ya zama dalilin yin fasikanci, suna kuma mūsun Yesu Kiristi wanda shi ne Makaɗaici Mai Iko Duka da kuma Ubangijinmu.

Ru’uya ta Yohanna 2:2

‹Na san ayyukanka, faman aikinka da daurewarka. Na san cewa ba ka iya haƙuri da mugayen mutane, ka gwada waɗanda suke cewa su manzanni ne, alhali kuwa ba haka ba ne, ka kuwa tarar cewa su na ƙarya ne.›

Ru’uya ta Yohanna 2:9

‹Na san wahalarka da kuma talaucinka, duk da haka kai mai arziki ne! Na san ɓata suna da waɗannan suke yi maka waɗannan da suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, su dai majami’ar Shaiɗan ne.›

Ru’uya ta Yohanna 2:14-16

‹Duk da haka, ina da abubuwa kima game da kai. Kana da mutane a can waɗanda suke riƙe da koyarwar Bala’am, wanda ya koya wa Balak yă ja hankalin Isra’ilawa su yi zunubi ta wurin cin abincin da aka miƙa wa gumaka hadaya, su kuma yi fasikanci.› ‹Haka ma kana da waɗanda suke riƙe da koyarwar Nikolaitawa.› ‹Saboda haka ka tuba! In ba haka ba, zan zo wajenka ba da daɗewa ba in yaƙe su da takobin bakina.›

Ru’uya ta Yohanna 2:20

‹Duk da haka, ina da wannan game da kai. Kana haƙuri da matan nan Yezebel, wadda take kira kanta annabiya. Ta wurin koyarwarta tana ɓad da bayina ga yin fasikanci suka kuma ci abincin da aka miƙa wa gumaka.›

Ru’uya ta Yohanna 3:15-17

‹Na san ayyukanka, ba ka da sanyi ba ka kuma da zafi. Na so da kai ɗaya ne daga ciki, ko sanyi, ko zafi!› ‹Amma domin kana tsaka-tsaka ba zafi ba, ba kuma sanyi ba, ina dab da tofar da kai daga bakina.› ‹Ka ce, ‘Ina da arziki; na sami dukiya ba na kuma bukatar kome.’ Amma ba ka gane ba cewa kai matsiyaci ne, abin tausayi, matalauci, makaho kana kuma tsirara.›

Ru’uya ta Yohanna 3:19

‹Waɗanda nake ƙauna su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka ka yi himma ka tuba.›

Ru’uya ta Yohanna 12:9-11

Aka jefar da ƙaton jan macijin ƙasa, tsohon maciji nan da ake kira Iblis, ko Shaiɗan, wanda ya ɓad da dukan duniya. Aka jefar da shi ƙasa, tare da mala’ikunsa a duniya. Sa’an nan na ji babbar murya daga sama tana cewa, “Yanzu ceto da iko da mulkin Allahnmu, da kuma ikon Kiristinsa. Gama mai zargin ’yan’uwanmu, wanda yake zarginsu a gaban Allahnmu dare da rana, an jefar da shi ƙasa. Sun ci nasara a kansa ta wurin jinin Ɗan Ragon da ta wurin kalmar shaidarsu; ba su ƙaunaci rayukansu sosai har da za su ja da baya daga mutuwa.

Ru’uya ta Yohanna 18:4

Sai na ji wata murya daga sama ta ce, “Ku fita daga cikinta, mutanena, don kada zunubanta su shafe ku, don kada wata annobarta ta same ku;

Ru’uya ta Yohanna 18:23

Hasken fitila ba zai ƙara haskakawa a cikinki ba. Ba za a ƙara jin muryar ango da amarya a cikinki ba. Attajiranki, dā su ne manyan mutanen duniya. Ta wurin sihirinki, dukan ƙasashe sun kauce.

Ru’uya ta Yohanna 19:20

Amma aka kama dabbar tare da annabin ƙaryan nan wanda ya aikata alamu masu banmamaki a madadinta. Da waɗannan alamun ne ya ruɗe waɗanda suka sami alamar dabbar suka kuma bauta wa siffarta. Aka jefa dukansu biyu da rai cikin tafkin wuta ta da farar wuta mai ci.

Ru’uya ta Yohanna 20:2-3

Ya kama macijin, wannan tsohon maciji, wanda yake shi ne Iblis, ko kuwa Shaiɗan, aka kuma ɗaura shi har shekara dubu. Ya jefa shi cikin Abis, ya kuma kulle ya sa hatimi a kansa, don a hana kada yă ƙara ruɗin al’ummai, sai shekarun nan dubu sun cika. Bayan wannan, dole a sake shi na ɗan lokaci.

Ru’uya ta Yohanna 20:10

Aka jefa Iblis da ya ruɗe su cikin tafkin farar wuta, inda aka jefa dabban nan da annabin ƙaryan nan. Za a ba su azaba dare da rana har abada abadin.

Ru’uya ta Yohanna 21:8

Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.”

Ru’uya ta Yohanna 21:27

Babu wani abu marar tsarkin da zai taɓa shiga cikin birnin, babu kuma wani mai aikata abin kunya ko ruɗi da zai shiga, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a cikin littafin rai na Ɗan Ragon.

Ru’uya ta Yohanna 22:15

‹Waɗanda suke waje kuwa karnuka ne, masu sihiri, masu fasikanci, masu kisankai, masu bautar gumaka, da duk wanda yake ƙaunar ƙarya yake kuma aikata ta.›

Ru’uya ta Yohanna 22:18-19

Ina yin wa duk wanda ya ji kalmomin annabcin wannan littafi gargaɗi. Duk wanda ya ƙara wani abu a kansu, Allah zai ƙara masa annoban da aka bayyana a littafin nan. Duk wanda kuma ya yi ragi a kalmomi daga littafin annabcin nan, Allah zai ɗauke rabonsa na itacen rai da kuma na birnin nan mai tsarki, waɗanda aka bayyana a littafin nan.

Hausa - Hausa - HA

HA'BSS - Budadden Littafi Mai Tsarki Biblica - 2020

This Bible text is from Biblica Open Hausa Contemporary Bible 2020
https://open.bible/bibles/hausa-biblica-text-bible/
provided by: Biblica Inc, available by Creative Commons CC-BY-SA-4.0,
and this new compilation is shared as www.creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0.
Languages are made available to you by www.ipedge.net