25 – Kudi

Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Kudi.

Top 3 Mafi Muhimmanci ayoyi

Mattiyu 6:19-21

‹“Kada ku yi wa kanku ajiyar dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda kuma ɓarayi sukan fasa, su yi sata.› ‹Amma ku yi wa kanku ajiyar dukiya a sama, inda ba tsatsa da asu da za su ɓata su, inda kuma ba ɓarayin da za su fasa, su yi sata.› ‹Gama inda dukiyarka take, a nan ne fa zuciyarka za tă kasance.›

1 Timoti 6:6-10

Amma bin Allah da gamsuwa riba ce mai yawa. Gama ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu fita daga cikinta da kome ba. In dai muna da abinci da sutura, ai, sai mu gamsu da su. Mutanen da suke son yin arziki sukan fāɗi cikin jarraba, su fāɗa a tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka. Gama son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Waɗansu mutane, don tsananin son kuɗi, sun bauɗe daga bangaskiya suka kuma jawo wa kansu da baƙin ciki iri-iri.

Markus 10:23-27

Yesu ya dudduba, sai ya ce wa almajiransa, ‹“Yana da wuya fa masu arziki su shiga mulkin Allah!”› Almajiransa suka yi mamakin kalmominsa. Amma Yesu ya sāke ce musu, ‹“’Ya’yana, yana da wuya fa a shiga mulkin Allah!› ‹Ya fi sauƙi raƙumi yă shiga ta kafar allura, da mai arziki yă shiga mulkin Allah.”› Almajiran suka yi mamaki ƙwarai, suka ce wa juna, “To, wa zai sami ceto ke nan?” Yesu ya kalle su ya ce, ‹“Ga mutum kam, wannan ba mai yiwuwa ba ne, amma ga Allah, wannan mai yiwuwa ne; dukan abubuwa masu yiwuwa ne ga Allah.”›

Kowane Aya A Canonical Order – 384 sassa

Farawa 4:3-5

Ana nan sai Kayinu ya kawo waɗansu amfanin gona a matsayin hadaya ga Ubangiji. Amma Habila ya kawo mafi kyau daga ’ya’yan fari na garkensa. Ubangiji ya yi farin ciki da sadakar da Habila ya kawo, amma bai yi farin ciki da sadakar da Kayinu ya kawo ba. Saboda haka Kayinu ya ji fushi sosai, fuskarsa kuma ta ɓace.

Farawa 13:2

Abram ya azurta ƙwarai da dabbobi, da azurfa, da kuma zinariya.

Farawa 13:6

Wannan ya sa har ƙasar ba tă ishe su yayinda suke zama tare ba, saboda mallakarsu ta yi yawa har ba za su iya zama tare ba.

Farawa 14:20

Kuma albarka ta tabbata ga Allah Mafi Ɗaukaka wanda ya ba da maƙiyanka a hannunka.” Sa’an nan Abram ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na kome.

Farawa 24:35

Ubangiji ya albarkaci maigidana sosai, ya kuma zama mai arziki. Ya ba shi tumaki, shanu, azurfa, zinariya, bayi maza da mata, raƙuma, da kuma jakuna.

Farawa 24:53

Sa’an nan bawan ya fito da kayan ado na zinariya da azurfa da kayayyaki na tufafi ya ba wa Rebeka; ya kuma ba wa ɗan’uwanta da mahaifiyarta kyautai masu tsada.

Farawa 26:12-14

Ishaku ya shuka hatsi a wannan ƙasa, a shekaran nan ya yi girbi ninki ɗari, domin Ubangiji ya albarkace shi. Mutumin ya arzuta, arzikinsa ya yi ta haɓaka har ya zama attajiri. Ya kasance da garkunan tumaki da na shanu da bayi masu yawa, har Filistiyawa suka yi ƙyashinsa.

Farawa 28:22

kuma wannan dutsen da na kafa al’amudi, zai zama gidan Allah, kuma dukan abin da ka ba ni zan ba ka kashi ɗaya bisa goma.”

Farawa 41:49

Sai Yusuf ya tara hatsi da yawan gaske, kamar yashi a bakin teku, har sai da ya kāsa iya auna shi, gama ba a iya aunawa.

Farawa 41:56-57

Sa’ad da yunwa ta bazu a dukan ƙasar, sai Yusuf ya buɗe gidajen ajiya, ya kuma sayar da hatsi ga Masarawa, gama yunwa ta yi tsanani a dukan Masar. Dukan ƙasashe kuwa suka zo Masar don saya hatsi daga Yusuf, gama yunwa ta yi tsanani a dukan duniya.

Farawa 47:12

Yusuf ya kuma tanada wa mahaifinsa da kuma ’yan’uwansa da dukan gidan mahaifinsa, abinci bisa ga yawan ’ya’yansu.

Farawa 47:13-21

A yanzu, a cikin ƙasar duka, ba abinci, gama yunwa ta yi tsanani ƙwarai, har ƙasar Masar da ƙasar Kan’ana suka shiga matsananciyar wahala! Yusuf ya tattara dukan kuɗaɗen da suke a Masar da Kan’ana don biyan hatsin da suke saya, ya kuwa kawo su a fadan Fir’auna. Sa’ad da kuɗin mutanen Masar da Kan’ana suka ƙare, dukan Masar ta zo wurin Yusuf ta ce, “Ka ba mu abinci. Me zai sa mu mutu a idanunka? Kuɗinmu duk sun ƙare.” Yusuf ya ce, “To, ku kawo dabbobinku, zan sayar muku da abinci a madadin dabbobinku, tun da kuɗinku ya ƙare.” Saboda haka suka kawo dabbobinsu wa Yusuf, ya kuma ba su abinci a madadin dawakai, tumaki da awaki, shanu da jakunansu. Ya kuwa ba su abinci a madadin dabbobinsu, a wannan shekara. Sa’ad da wannan shekara ta ƙare, sai suka zo wurinsa a shekara ta biye suka ce, “Ba za mu ɓoye maka ba ranka yă daɗe, kuɗinmu sun ƙare, dabbobinmu kuma sun zama naka. Ranka yă daɗe, in ban da jikunanmu da gonakinmu, ba abin da ya rage mana. Kada ka bar mu mu mutu, ka yi wata dabara! Kada ka bari mu rasa gonakinmu. Ka musaye mu da abinci, mu da gonakinmu. Mu kuwa za mu zama bayin Fir’auna. Ka ba mu iri don mu rayu, kada mu mutu, don kuma kada gonakin ƙasarmu su zama kango.” Ta haka Yusuf ya saya wa Fir’auna ƙasar Masar duka, gama Masarawa duka sun sayar da gonakinsu, saboda yunwa ta tsananta musu. Ƙasar ta zama mallakar Fir’auna. Yusuf kuwa ya mai da mutanen bayi, daga wannan iyakar Masar zuwa wancan.

Fitowa 3:22

Kowace mace ta tambayi maƙwabciyarta, da kuma duk wata macen da take cikin gidanta, kayayyakin azurfa da na zinariya da kuma na riguna, waɗanda za ku sa wa ’ya’yanku maza da mata. Ta haka nan za ku washe Masarawa.”

Fitowa 16:4-5

Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Zan zubo muku burodi kamar ruwa daga sama. Mutanen za su fita kowace rana su tattara abin da zai ishe su na ranan. Ta haka zan gwada su in ga ko za su bi umarnaina. A rana ta shida za su shirya abin da suka kwaso, wannan kuwa zai zama ninki biyu na abin da sukan tattara na sauran ranaku.”

Fitowa 16:19-20

Sa’an nan Musa ya ce musu, “Kada wani yă bar saura har safe.” Duk da haka waɗansu ba su kula da umarnin Musa ba, suka bar saura har safe, kashegari kuwa ta yi tsutsotsi, ta ruɓe, sai Musa ya yi fushi da su.

Fitowa 20:15

Ba za ka yi sata ba.

Fitowa 20:17

Ba za ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba. Ba za ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, ko bawansa, ko baiwarsa, ko sansa, ko jakinsa, ko duk abin da yake na maƙwabcinka ba.”

Fitowa 20:23

Kada ku yi waɗansu alloli in ban da ni, kada ku yi wa kanku allolin azurfa ko na zinariya.

Fitowa 21:16

“Duk wanda ya saci mutum ya sayar da shi, ko kuwa aka iske shi a hannunsa, lalle kashe shi za a yi.

Fitowa 22:7-8

“In mutum ya ba maƙwabcinsa azurfa, ko kaya ajiya, aka kuma sace su daga gidan maƙwabcin, in an kama ɓarawon, sai ɓarawon yă biya abin da ya sata har sau biyu. Amma in ba a sami ɓarawon ba, sai wanda aka yi ajiyar a gidansa, yă bayyana a gaban alƙalai a bincika ko yana da hannu a kan kayan maƙwabcinsa.

Fitowa 22:25

“In kun ba wa jama’ata matalauta da suke tsakaninku bashin kuɗi, kada ku zama kamar masu ba da rance; kada ku sa yă biya da ruwa.

Fitowa 25:2

“Ka faɗa wa Isra’ilawa su kawo mini hadaya. Za ka karɓi hadaya daga hannun kowane mutum wanda zuciyarsa ta yarda yă bayar.

Fitowa 35:5

Daga cikin abin da kuke da shi, ku ɗauki kyauta domin Ubangiji, duk wanda yana niyya, sai yă kawo wa Ubangiji kyauta ta, “zinariya, azurfa da tagulla;

Fitowa 35:22

Duk waɗanda suke da niyya, maza da mata, gaba ɗaya, suka kawo kayan ado na zinariya na kowane iri. ’Yan kunne, da ƙawane, da mundaye, da kayayyakin zinariya iri-iri. Dukansu suka miƙa zinariyarsu a matsayin hadaya ga Ubangiji.

Fitowa 36:5-7

suka ce wa Musa, “Mutane suna kawo fiye da abin da ake bukata domin aikin da Ubangiji ya umarta a yi.” Sai Musa ya ba da umarni, suka aika ko’ina a cikin sansani cewa, “Kada namiji ko ta mace yă sāke kawo kyauta don wuri mai tsarki.” Ta haka mutane suka daina kawowa. Saboda abin da suke da shi ya fi abin da ake bukata domin aikin.

Firistoci 6:2-3

“In wani ya yi zunubi bai kuma yi aminci ga Ubangiji ba, wato, ta wurin yin wa abokin zamansa karya game da ajiyar da abokin ya ba shi amana, ko a kan wani alkawarin da suka yi wa juna, ko kuwa a kan yă cuci abokin, ko kuma idan ya sami abin da ya ɓace amma ya yi ƙarya cewa bai samu ba. Ko ya yi rantsuwar ƙarya a kan duk irin abubuwan da akan aikata na laifi,

Firistoci 19:9-11

“ ‘Sa’ad da kuka yi girbin amfanin gonarku, kada ku girbe har zuwa gefen gonar, ko ku yi kalan girbinku. Kada ku koma gonar inabinku kuna kala, ko ku tattara ’ya’yan inabin da suka fāffāɗi. Ku bar su domin matalauta da kuma baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku. “ ‘Kada ku yi sata. “ ‘Kada ku yi ƙarya. “ ‘Kada ku ruɗe juna.

Firistoci 19:13

“ ‘Kada ku zalunci maƙwabcinku, ko ku yi masa ƙwace. “ ‘Kada ku riƙe albashin ma’aikaci yă kwana.

Firistoci 19:35-36

“ ‘Kada ku yi amfani da mudun ƙarya sa’ad da kuke awon tsawo, nauyi, ko yawan abu. Ku yi amfani da ma’auni na gaskiya da mudu na gaskiya, da kuma magwaji na gaskiya. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar.

Firistoci 23:22

“ ‘Sa’ad da kuka yi girbin gonarku, kada ku girbe har ƙarshen gefen gonar, ko ku yi kalar girbinku. Ku bar su wa matalauta da baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”

Firistoci 25:3-5

Shekara shida, za ku yi shuki, shekara shida kuma za ku aske gonakin inabinku, ku kuma tattara hatsinsu. Amma a shekara ta bakwai, ƙasar za tă sami hutun Asabbaci, Asabbaci ga Ubangiji. Kada ku yi shuki a gonakinku, ko kuwa ku aske gonakinku na inabi. Kada ku girbe abin da ya yi girma ba tare da ku kuka shuka ba, ko ku girbe inabin da ba ku aske ba. Ƙasar za tă kasance da shekarar hutu.

Firistoci 25:8-12

“ ‘Ku ƙirga asabbatai bakwai na shekaru bakwai, sau bakwai. Gama asabbatai bakwai na shekaru bakwai za su yi daidai da shekaru arba’in da tara. Sa’an nan a busa ƙaho a ko’ina, a rana ta goma ga wata na bakwai; a Ranar Kafara, a busa ƙaho a dukan ƙasarku. Ku keɓe shekara ta hamsin ku kuma yi shelar ’yanci a dukan ƙasar ga mazaunanta. Za tă zama shekarar murna gare ku; kowannenku zai koma ga mallakar iyalinsa, kuma kowa ga danginsa. Shekara ta hamsin za tă zama ta murna a gare ku; kada ku yi shuki, kada kuma ku yi girbi abin da ya yi girma da kansa, ko ku girbe inabin da ba ku lura da shi ba. Gama shekara ce ta murna, za tă kuma zama mai tsarki a gare ku, ku dai ci abin da aka ɗauka kai tsaye daga gonaki.

Firistoci 25:35

“ ‘In ɗaya daga ciki mutanen ƙasarku ya talauta, ba ya kuma iya tallafa wa kansa a cikinku, sai ku taimake shi kamar yadda za ku yi da baƙo a cikinku.

Firistoci 25:36-37

Kada ku karɓi riba ta kowace iri daga gare shi, amma ku ji tsoron Allahnku, saboda mutumin ƙasarku yă ci gaba da zama a cikinku. Kada ku ba shi rancen kuɗi da ruwa, ko ku sayar masa abinci don samun riba.

Firistoci 27:30

“ ‘Ushirin kome daga gona, ko hatsi daga ƙasa, ko ’ya’yan itatuwa daga itatuwa, na Ubangiji ne, mai tsarki ne ga Ubangiji.

Ƙidaya 18:20-21

Ubangiji ya ce wa Haruna, “Ba ka da gādo a ƙasarsu, ba kuwa za ka sami rabo daga cikinsu ba; ni ne rabonka da gādonka a cikin Isra’ilawa. “Na ba wa Lawiyawa dukan zakka na Isra’ilawa a matsayin gādonsu, saboda aikin da suke yi yayinda suke hidima a Tentin Sujada.

Ƙidaya 18:25-29

Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka yi wa Lawiyawa magana, ka ce musu, ‘Sa’ad da kuka karɓi zakka daga Isra’ila da na ba ku gādo, dole ku miƙa kashi ɗaya bisa goma na wannan zakka a matsayin hadaya ga Ubangiji. Za a lissafta hadayarku kamar hatsin da aka sussuka daga masussuka, ko ruwan inabi daga wurin matsewar inabi. Ta haka za ku miƙa hadaya ga Ubangiji daga cikin dukan zakkar da kuka karɓa daga wurin Isra’ilawa. Daga waɗannan zakka kuwa dole ku ba Haruna firist rabon Ubangiji. Dole ku miƙa wa Ubangiji rabo mafi kyau da kuma sashi mafi tsarki na kowane abin da aka ba ku.’

Ƙidaya 27:4-11

Me ya sa sunan mahaifinmu zai ɓace a kabilarsa don kawai ba shi da ɗa? Ka ba mu gādo cikin ’yan’uwan mahaifinmu.” Saboda haka Musa ya kawo maganarsu a gaban Ubangiji. Ubangiji kuwa ya ce wa masa, “Abin da ’ya’yan nan mata na Zelofehad suke faɗi gaskiya ne. Dole ka ba su mallaka a matsayin gādo cikin ’yan’uwan mahaifinsu, ka kuma mayar musu da gādon mahaifinsu. “Ka faɗa wa Isra’ilawa cewa, ‘In wani ya mutu ba shi da ɗa, a ba da gādonsa ga ’yarsa. In ba shi da diya, sai a ba wa ’yan’uwansa gādonsa. In ba shi da ’yan’uwa, a ba da gādonsa ga ’yan’uwan mahaifinsa. In mahaifinsa ba shi da ’yan’uwa, a ba da gādonsa ga danginsa na kusa, a kabilarsa don yă mallaka. Wannan ya zama ƙa’ida wa Isra’ilawa, yadda Ubangiji ya umarci Musa.’ ”

Ƙidaya 31:50

Saboda haka mun kawo wa Ubangiji hadaya na kayan zinariya da kowannenmu ya samu, mundaye, ƙawane, ’yan kunne da duwatsun wuya, don yin wa kanmu kafara a gaban Ubangiji.”

Ƙidaya 36:9

Ba gādon da za a ba wa wata kabila daga wata kabila, gama kowace kabilar Isra’ilawa za tă riƙe mallaka da ta gāda.”

Maimaitawar Shari’a 5:19

Kada ka yi sata.

Maimaitawar Shari’a 5:21

Kada ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka. Kada kuma ka yi sha’awar gidan maƙwabcinka, ko gonarsa, ko bayinsa maza da mata, ko saniyarka, ko jakinsa, ko dai wani abin da yake na maƙwabtanka.”

Maimaitawar Shari’a 8:9

ƙasa inda abinci ba zai yi ƙaranci ba, ba kuma za ku rasa kome ba; ƙasa ce inda ƙarfe ne duwatsunta, ana kuma haƙar tagulla a tuddanta.

Maimaitawar Shari’a 8:12-18

To, sa’ad da kuka ci, kuka ƙoshi, sa’ad da kuka gina gidaje masu kyau, kuka zauna, sa’ad da kuma garkunanku na shanu da na tumaki suka ƙaru, azurfanku da zinariyarku kuma suka ƙaru, sa’an nan dukan abin da kuke da shi ya haɓaka, to, sai ku lura, kada ku ɗaukaka kanku, har ku manta da Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta kuma. Ya bishe ku cikin hamada mai fāɗi, mai bantsoro, wannan busasshiyar ƙasa wadda ba ta da ruwa, ga macizai masu dafi da kuma kunamai. Ya ba ku ruwa daga dutsen ƙanƙara. Ya ba ku Manna don ku ci a cikin hamada, wani abin da kakanninku ba su taɓa sani ba, don yă ƙasƙantar yă kuma gwada ku, saboda yă yi muku alheri daga baya. Wataƙila ku ce wa kanku, “Ikona da ƙarfin hannuwana ne suka ba ni da wannan arziki.” Amma ku tuna da Ubangiji Allahnku, gama shi ne wanda yake ba ku azanci na yin arziki, ta haka kuwa ya tabbatar da alkawarinsa, wanda ya rantse wa kakanninku, kamar yadda yake a yau.

Maimaitawar Shari’a 10:17-18

Gama Ubangiji Allahnku ne Allahn alloli da Ubangijin iyayengiji, Allah mai girma, mai ƙarfi da kuma mai banrazana, wanda ba ya sonkai, ba ya cin hanci. Yakan tsare marayu da gwauraye, yana ƙaunar baƙon da yake zama a cikinku, yana ba su abinci da tufafi.

Maimaitawar Shari’a 12:6

a can ne kuma za ku kawo hadayun ƙonawa da sadakoki, zakkarku da kyautai na musamman, da abin da kuka yi alkawari za ku bayar, da hadayunku na yardar rai, da kuma ’ya’yan farin garkunanku na shanu da na tumaki.

Maimaitawar Shari’a 12:11

sai ku kai dukan abin da na umarce ku ku kai, wato, hadayu na ƙonawa, da sadakokinku, da zakkarku, da hadayunku na ɗagawa, da hadayunku na alkawarin da kuka yi wa Ubangiji a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa yă sa sunansa.

Maimaitawar Shari’a 12:17

Kada ku ci zakkar hatsi, da na sabon inabi, da kuma na mai a biranenku, ko kuwa na ’ya’yan fari na garkunanku na shanu da na tumaki, ko kuwa duk wani abin da kuka yi alkawari za ku bayar, ko hadayunku na yardar rai, ko kyautai na musamman.

Maimaitawar Shari’a 14:22-23

Ku tabbata kun keɓe kashi ɗaya bisa goma na amfanin gonakinku kowace shekara. Ku ci zakkar hatsinku, da na sabon ruwan inabinku, da na manku, da kuma na ’ya’yan fari na garkunanku na shanu da na tumaki a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da ya zaɓa a matsayin mazauni don Sunansa, don ku koyi girmama Ubangiji Allahnku kullum.

Maimaitawar Shari’a 15:1-3

A ƙarshen kowace shekara ta bakwai, dole ku yafe basusuwan da kuke bi. Ga yadda za ku yafe basusuwan, kowane mai bin bashi, yă yafe bashin da yake bin ɗan’uwansa mutumin Isra’ila. Ba zai bukaci mutumin Isra’ila wanda yake ɗan’uwa yă biya shi bashi ba, gama an yi shelar lokacin da Ubangiji ya ajiye na yafe bashi. Za ku iya nemi baƙo yă biya ku bashin da kuke binsa, amma dole ku yafe duk wani bashin da kuke bin ɗan’uwa.

Maimaitawar Shari’a 15:6

Gama Ubangiji Allahnku zai albarkace ku kamar yadda ya yi alkawari, za ku kuma ba al’ummai masu yawa bashi, amma ba za ku karɓa bashi daga wurin wani ba. Za ku yi mulkin al’ummai masu yawa, babu wata kuwa da za tă yi mulkinku.

Maimaitawar Shari’a 15:7-8

In akwai matalauci a cikin ’yan’uwanku, a duk wani daga cikin biranen da Ubangiji Allahnku yake ba ku, kada ku taurara zuciya, ko ku ƙi saki hannu ga ɗan’uwanku matalauci. A maimakon haka ku bayar hannu sake, ku kuma ba shi bashi gwargwadon abin da yake bukata a sauƙaƙe.

Maimaitawar Shari’a 15:9-11

Ku yi hankali kada ku riƙe wannan mugun tunani cewa, “Shekara ta bakwai, shekarar yafewar basusuwa, ta yi kusa,” har ku nuna mugun nufi ga ɗan’uwa mabukaci, ku ƙi ba shi wani abu. Zai yi kuka ga Ubangiji a kanku, abin kuwa zai zama laifi a kanku. Ku bayar hannu sake gare shi, ku kuma yi haka ba tare da gunaguni ba; saboda wannan fa Ubangiji Allahnku zai albarkace ku a cikin dukan aikinku, da kuma kome da kuka sa hannunku a kai. Kullum za ku kasance da matalauta a ƙasar. Saboda haka na umarce ku ku bayar hannu sake ga ’yan’uwa da kuma matalauta, da masu bukata a ƙasarku.

Maimaitawar Shari’a 16:10

Sa’an nan ku yi shagalin Bikin Makoni ga Ubangiji Allahnku, ta wurin ba da hadaya ta yardar rai daidai da albarkun da Ubangiji Allahnku ya yi muku.

Maimaitawar Shari’a 16:17

Dole kowannenku yă kawo kyauta daidai yadda Ubangiji Allahnku ya albarkace shi.

Maimaitawar Shari’a 17:17

Sarkin ba zai auri mata masu yawa ba, in ba haka ba zuciyarsa za tă karkata. Ba zai tara azurfa da zinariya da yawa ba.

Maimaitawar Shari’a 18:2

Ba za su sami gādo a cikin ’yan’uwansu ba; Ubangiji ne gādonsu, kamar yadda ya yi musu alkawari.

Maimaitawar Shari’a 19:14

Kada ka gusar da dutsen nuna shaidar iyakar maƙwabcinka wanda kakanni suka sa, a gādon da ka samu a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka mallaka.

Maimaitawar Shari’a 23:19-20

Kada ku nemi ɗan’uwanku yă biya bashin da kuka ba shi da ruwa, ko kuɗi, ko abinci, ko kowane irin abin da yana iya ba da ruwa. Za ku iya nemi ruwa a bashin da kuka ba baƙo, amma ba ɗan’uwanku mutumin Isra’ila ba, domin Ubangiji Allahnku yă sa muku albarka a kowane abin da kuka sa hannunku a kai, a ƙasar da kuke shiga ku ci gādonta.

Maimaitawar Shari’a 24:7

Idan aka kama wani yana satar ɗan’uwansa mutumin Isra’ila domin yă sa ya zama bawansa, ko yă sayar da shi, sai a kashe ɓarawon nan. Haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.

Maimaitawar Shari’a 24:21

Sa’ad da kuka yi girbin inabi a gonar inabinku, kada ku yi kalan abin da ya rage. Ku bar shi don baƙo, maraya da kuma gwauruwa.

Maimaitawar Shari’a 26:9-11

Ya kawo mu wannan wuri, ya kuma ba mu wannan ƙasa, ƙasa mai zub da madara da kuma zuma; yanzu kuwa na kawo ’ya’yan fari na gonar da kai, ya Ubangiji ka ba ni.” Sai ku sa kwandon a gaban Ubangiji Allahnku, sa’an nan ku rusuna a gabansa. Ku da Lawiyawa da baƙin da suke a cikinku, za ku yi murna cikin dukan abubuwa masu kyau da Ubangiji Allahnku ya ba ku tare da gidanku.

Maimaitawar Shari’a 26:12-13

Sa’ad da kuka gama fitar da kashi ɗaya bisa goma na dukan amfanin gona a shekara ta uku, shekarar zakka, za ku ba da su ga Balawe, baƙo, maraya da kuma gwauruwa, don su ci a cikin garuruwanku su ƙoshi. Sa’an nan ku faɗa wa Ubangiji Allahnku, “Na cire tsattsarkan rabo daga gidana na kuma ba wa Balawe, baƙo, maraya da gwauruwa, bisa ga dukan abin da ka umarta. Ban ja gefe daga umarnanka ko in manta da wani a cikinsu ba.

Maimaitawar Shari’a 28:11-12

Ubangiji zai azurta ku sosai, a ’ya’yan cikinku, a ’ya’yan dabbobinku da kuma a hatsin gonarku, a cikin ƙasar da ya rantse wa kakanninku zai ba ku. Ubangiji zai buɗe sammai, wurin ajiyarsa mai yalwa, don yă aika da ruwan sama a gonarku a lokacinsa, yă kuma albarkaci dukan aikin hannuwanku. Za ku ba wa al’ummai masu yawa rance, amma ba za ku karɓa bashi daga wurin wani ba.

Yoshuwa 6:19

Dukan azurfa da zinariya, da kwanonin tagulla da na ƙarfe, keɓaɓɓu ne ga Ubangiji, dole a sa su cikin ma’ajin Ubangiji.”

Yoshuwa 13:33

Amma Musa bai ba kabilar Lawiyawa gādo ba; Ubangiji, Allah na Isra’ila, shi ne gādonsu kamar yadda ya yi musu alkawari.

1 Sama’ila 2:7-8

Ubangiji ne yakan aika da talauci da kuma dukiya; yakan ƙasƙantar yă kuma ɗaukaka. Yakan tā da matalauci daga ƙura, yă kuma ɗaga mai bukata daga tarin toka; yă zaunar da su tare da ’ya’yan sarki; yă kuma sa su gāji mulki na ɗaukaka. “Harsashin duniya na Ubangiji ne; a bisansu ne ya kafa duniya.

2 Sama’ila 12:1-6

Ubangiji ya aiki Natan wurin Dawuda. Da ya tafi wajensa, sai ya ce, “An yi waɗansu mutum biyu a wani gari, ɗaya mai arziki, ɗayan kuma matalauci. Mai arzikin yana da babban garken tumaki, da kuma shanu, amma matalauci ba shi da kome sai ’yar tunkiyar da ya sayo. Ya yi kiwonta, ta kuwa yi girma tare shi da yaransa. Takan ci tare da shi ta sha ruwa a kwaf nasa, har ma ta kwanta a ƙirjinsa. Ta ma zama kamar ’ya a gare shi. “To, sai ga wani baƙo ya zo wurin mai arzikin nan, amma mai arzikin ya ƙi yă kama tunkiyarsa, ko saniyarsa yă yanka don yă shirya wa baƙon da ya zo abinci. A maimako, sai ya je ya kama ’yar tunkiyan nan ta matalaucin ya yanka ya shirya wa mutumin da ya zo masa.” Dawuda ya husata ƙwarai da mutumin, ya ce wa Natan, “Muddin Ubangiji yana a raye, mutumin da ya yi wannan ya cancanci yă mutu! Dole yă biya diyyar tunkiyan nan sau huɗu, domin ya aikata haka ba tausayi.”

2 Sama’ila 24:24-25

Amma sarki ya ce wa Arauna, “A’a, dole in biya ka saboda waɗannan. Ba yadda zan miƙa wa Ubangiji Allahna hadayun ƙonawa da bai ci mini kome ba.” Sai Dawuda ya saya, ya kuma biya masussukar, da shanun a bakin shekel hamsin na azurfa. Dawuda ya gina wa Ubangiji bagade a wurin, ya kuma miƙa masa hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta salama. Sa’an nan Ubangiji ya amsa addu’o’in a madadin ƙasar, aka kuma kawar wa Isra’ila annoban.

1 Sarakuna 6:21-22

Solomon ya rufe cikin haikalin da zinariya zalla, ya kuma gifta sarƙoƙin zinariya a gaban wuri mai tsarki na ciki, wanda aka dalaye da zinariya. Haka ya dalaye dukan cikin da zinariya. Ya kuma dalaye bagade na cikin wuri mai tsarki da zinariya.

1 Sarakuna 6:30

Ya kuma rufe ƙasan ɗakuna ciki da wajen haikali da zinariya.

1 Sarakuna 7:48-50

Solomon ya kuma yi dukan kayayyakin da suke cikin haikalin Ubangiji. Ya yi bagaden zinariya; teburin zinariya, inda ake ajiye burodin Kasancewa; ya yi alkukai na zinariya zalla (Biyar a dama, biyar kuma a hagu, a gaban wuri mai tsarki na can cikin); ya yi zāne-zānen furannin zinariya da fitilu da kuma arautaki; ya yi kwanonin zinariya zalla, hantsuka, kwanonin yayyafawa, kwanoni, da kuma farantan wuta; ya yi wurin ajiye fitila na zinariya domin ƙofofi na ɗakin can ciki-ciki, da na ƙofofin Wuri Mafi Tsarki, da kuma domin ƙofofin babban zauren haikali.

1 Sarakuna 10:14

Nauyin zinariya da Solomon yake samun kowace shekara, talenti 666 ne.

1 Sarakuna 10:21-23

Dukan kwaf Solomon zinariya ne, kuma dukan kayayyakin gida a Fadan da ake kira Kurmin Lebanon, zinariya ce zalla. Babu wani abin da aka yi da azurfa, domin ba a ɗauki azurfa a bakin kome ba a zamanin Solomon. Sarki yana da jerin jiragen ruwan kasuwanci a teku, tare da jiragen ruwan Hiram. Sau ɗaya kowace shekara uku jerin jiragen yakan dawo ɗauke da zinariya, da azurfa, da hauren giwa, da birai marasa wutsiya, da kuma gogon biri. Sarki Solomon ya yi suna a wadata fiye da dukan sarakunan duniya.

1 Sarakuna 17:11-16

Da ta kama hanya za tă tafi tă kawo, sai ya sāke kiranta ya ce, “Ina roƙonki, ki kuma kawo mini ɗan abinci.” Sai ta ce masa, “Na rantse da Ubangiji Allahnka, ba ni da wani abinci, sai dai ɗan gari hannu guda a tulu, da kuma ɗan mai a kwalaba. Ina tattara ’yan itacen nan ne don in kai gida in yi abinci wa kaina da ɗana, don mu ci, mu mutu.” Iliya ya ce mata, “Kada ki ji tsoro. Ki tafi gida, ki yi yadda kika ce. Amma da farko ki yi mini ’yar wainar burodi daga abin da kike da shi ki kawo mini, sa’an nan ki yi wani abu wa kanki da kuma ɗanki. Gama abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Tulun garin ba zai ƙare ba, kwalabar man kuma ba zai bushe ba sai ranar da Ubangiji ya bayar da ruwan sama a ƙasar.’ ” Sai ta tafi, ta yi yadda Iliya ya faɗa mata. Saboda haka aka kasance da abinci kowace rana wa Iliya da kuma don macen da iyalinta. Gama tulun garin bai ƙare ba, kwalabar man kuma bai bushe ba, kamar yadda Ubangiji ya faɗa wa Iliya.

2 Sarakuna 4:2-7

Elisha ya amsa mata ya ce, “Me kike so in yi miki? Ki faɗa mini, me kike da shi a gidanki?” Sai ta ce, “Baiwarka ba ta da kome a can, sai ɗan tulun man zaitun.” Elisha ya ce, “Ki je wurin dukan maƙwabtanki, ki nemi tulunan da babu kome a ciki. Kada ki nemo kaɗan kawai. Sa’an nan ki shiga ciki, ki kulle ƙofar da ke da ’ya’yanki kuke ciki. Ku ɗuɗɗura man a dukan tulunan, sa’ad da kowanne ya cika, sai ki ajiye a gefe.” Ta tashi ta shiga tare da ’ya’yanta maza, suka kulle ƙofa. ’Ya’yanta suka kawo mata tuluna, ita kuma tana ɗurawa. Da dukan tulunan suka cika, sai ta ce wa ɗanta, “Kawo mini wani tulu.” Amma ya amsa ya ce, “Ai, ba saura.” Sa’an nan man ya daina zuba. Sai ta tafi ta faɗa wa mutumin Allah. Shi kuwa ya ce mata, “Tafi, ki sayar da man, ki biya bashinki. Ki biya bukatanki da na ’ya’yanki da sauran da ya rage.”

2 Sarakuna 18:15-16

Ya zama kuwa cewa, Hezekiya ya bayar da dukan azurfan da suke a haikalin Ubangiji da kuma a ma’ajin fadan sarki. A wannan lokaci ne Hezekiya sarkin Yahuda ya ɓaɓɓalle zinariyan da aka dalaye ƙofofi da madogaran ƙofofin haikalin Ubangiji, ya ba sarkin Assuriya.

2 Sarakuna 24:13-14

Yadda Ubangiji ya faɗa, Nebukadnezzar ya kwashe dukan dukiyar haikalin Ubangiji, da ta fadan sarki, ya kuma kwashe dukan kayan zinariyar da Solomon sarkin Isra’ila ya ƙera domin haikalin Ubangiji. Ya kwashi dukan mutanen Urushalima zuwa bauta, ya kwashi dukan fadawa, da mayaƙa, da masu sana’a, da maƙera, yawansu ya kai dubu goma. Ba wanda ya ragu, sai matalautan ƙasar.

1 Tarihi 4:10

Yabez ya yi kuka ga Allah na Isra’ila ya ce, “Ka yi mini albarka ka fadada yankina! Bari hannunka yă kasance tare da ni, yă kuma kiyaye ni daga abin da zai cuce ni, don kada in shiga wahala.” Sai Allah ya ji roƙonsa.

1 Tarihi 12:40

Haka ma, maƙwabtansu daga nesa har Issakar, Zebulun da Naftali suka zo suka kawo abinci a kan jakuna, raƙuma, alfadarai da shanu. Akwai tanadin mai yawa na gari, kauɗar ɓaure, nonnan busassun ’ya’yan inabi, ruwan inabi, mai, shanu da tumaki. Duk an yi haka don a nuna farin ciki ƙwarai a cikin dukan ƙasar Isra’ila.

1 Tarihi 22:14

“Na sha wahala da yawa don in yi tanadi talentin dubu ɗari na zinariya, talenti miliyon na azurfa, ɗumbun tagulla da ƙarfe da suka wuce ƙirge da katako da dutse saboda haikalin Ubangiji. Za ka iya ƙara su.

1 Tarihi 29:2-3

Na riga na tara dukan kayayyakin da na tanada saboda haikalin Allahna, zinariya saboda dukan ayyukan zinariya, azurfa saboda ayyukan azurfa, tagulla saboda ayyukan tagulla, ƙarfe saboda ayyukan ƙarfe da kuma katako saboda ayyukan katako, da onis don ado, turkuwoyis, duwatsu masu launi dabam-dabam, da kuma dukan duwatsu masu kyau da mabul, dukan waɗannan suna nan jingim. Ban da haka ma, cikin sa zuciyata ga haikalin Allahna, yanzu na ba da ma’ajina na zinariya da azurfa saboda haikalin Allahna, fiye da kome na tanada saboda wannan haikali,

1 Tarihi 29:7-9

Suka bayar talenti dubu biyar na zinariya, talenti dubu goma na azurfa, talenti dubu goma sha takwas na tagulla da talenti dubu ɗari na ƙarfe don aiki a haikalin Allah. Duk waɗanda suke da duwatsu masu daraja suka ba da su ga Yehiyel mutumin Gershon ma’ajin haikalin Ubangiji. Mutane suka yi farin ciki ganin yadda shugabanninsu suke bayarwa da yardar rai, gama sun bayar hannu sake da kuma dukan zuciya ga Ubangiji. Dawuda sarki shi ma ya yi farin ciki ƙwarai.

1 Tarihi 29:12

Wadata da girma daga gare ka suke; kai ne mai mulkin dukan abubuwa. A hannuwanka ne ƙarfi da iko suke don ka ɗaukaka da kuma ba da ƙarfi ga duka.

1 Tarihi 29:14

“Amma wane ni, kuma wace ce jama’ata da za mu iya ba ka a yalwace kamar haka? Kome daga gare ka suka fito, kuma mun ba ka abin da kawai ya fito daga hannunka ne.

1 Tarihi 29:16

Ya Ubangiji Allahnmu, game da dukan wannan yalwar da ka tanada saboda ginin haikali saboda Sunanka Mai Tsarki, sun fito daga hannunka ne, kuma dukan naka ne.

2 Tarihi 1:11-12

Allah ya ce wa Solomon, “Da yake wannan ne sha’awar zuciyarka, ba ka kuwa nemi wadata, arziki ko girma ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, da yake kuma ba ka nemi tsawon rai ba, amma ka nemi hikima da sani don ka shugabanci jama’ata wadda na naɗa ka sarki, saboda haka za a ba ka hikima da sani. Zan kuma ba ka wadata, arziki da girma, waɗanda babu wani sarki kafin kai da ya taɓa kasance da su kuma babu wani a bayanka da zai kasance da su.”

2 Tarihi 1:15

Sarki ya sa azurfa da zinariya suka zama barkatai a Urushalima kamar duwatsu, al’ul kuma kamar itatuwan fir a gindin tsaunuka.

2 Tarihi 31:4-5

Ya umarci mutanen da suke zama a Urushalima su ba da rabon da yake na firistoci da Lawiyawa, don su ƙwallafa ransu ga Dokar Ubangiji. Nan da nan aka baza umarnin, sai Isra’ilawa suka bayar ’ya’yan farin hatsinsu, sabon ruwan inabi, mai da kuma zuma da dukan abin da gona ta bayar, hannu sake. Suka kawo zakan kowane abu da yawa.

Nehemiya 5:1-13

To, sai maza da matansu suka tā da fara gunaguni mai tsanani a kan ’yan’uwansu Yahudawa. Waɗansu suka ce, “Mu da ’ya’yanmu maza da mata muna da yawa, muna bukatar hatsi domin mu ci mu rayu.” Waɗansu kuwa suka ce, “Saboda yunwa mun jinginar da gonakinmu, da gonakin inabinmu, da gidajenmu don mu sami hatsi.” Har illa yau waɗansu suka ce, “Mun ci bashin kuɗi don mu biya haraji a kan gonakinmu, da gonakin inabinmu. Ga shi kuwa, mu da su dangin juna ne, ’ya’yanmu da nasu kuma ɗaya ne, duk da haka an tilasta mu mu sa ’ya’yanmu mata da maza su zama bayi. Har ma an riga an bautar waɗansu daga cikin ’ya’yanmu mata, amma ba mu da iko mu ce kome, domin gonakinmu da gonakin inabinmu suna a hannun waɗansu mutane.” Sa’ad da na ji kukansu da waɗannan koke-koke, na husata ƙwarai. Na yi tunaninsu a zuciyata sa’an nan na zargi manyan gari da shugabanni. Na ce musu, “Kuna musguna wa ’yan’uwanku ta wurin ba su rance da ruwa!” Saboda haka na kira babban taro gaba ɗaya don a magance wannan. Na ce, “Da dukan iyakar ƙoƙarinmu, mun fanshi ’yan’uwanmu Yahudawan da aka sayar wa Al’ummai. Amma ga shi kuna sayar da ’yan’uwanku ga Al’ummai, don kawai a sāke sayar mana da su!” Saboda haka na ci gaba na ce, “Abin da kuke yi a yanzu ba daidai ba ne. Bai kamata ku yi tafiya cikin tsoron Allahnmu don mu guji ba’ar Al’ummai abokan gābanmu ba? Ni ma da ’yan’uwana da kuma mutanena muna ba wa mutane bashin kuɗi da kuma hatsi. Sai mu daina sha’anin ba da rance da ruwa! Yau sai ku mayar musu da gonakinsu, da gonakin inabinsu, da na zaitunsu, da gidajensu, da kashi ɗaya bisa ɗari na kuɗi, da na hatsi, da na ruwan inabi, da na mai, waɗanda kuka karɓa a wurinsu.” Suka ce, “Za mu mayar musu, kuma ba za mu bukaci wani abu daga gare su ba. Za mu yi yadda ka faɗa.” Sai na tattara firistoci na kuma sa manyan gari da shugabanni su yi rantsuwa don su yi abin da suka yi alkawari. Na kuma kakkaɓe hannuna, na ce, “Duk wanda ya karya wannan alkawari, haka Allah zai kakkaɓe shi daga gidansa da aikinsa. Allah zai kakkaɓe shi, yă wofintar da shi!” Da jin wannan, sai dukan taron suka ce, “Amin,” suka kuma yabi Ubangiji. Mutane kuwa suka yi kamar yadda suka yi alkawari.

Nehemiya 10:34-39

“Mu, firistoci, da Lawiyawa da kuma mutane, mun jefa ƙuri’a don a san lokacin da kowane iyalinmu zai kawo sadakar itace don ƙonewa a gidan Allahnmu a ƙayyadaddun lokuta a bagaden Ubangiji Allahnmu, kamar yadda yake a rubuce a cikin Doka. “Mun kuma ɗauka hakkin kawo nunan fari na hatsinmu da kuma na kowane itace mai ba da ’ya’ya a gidan Ubangiji kowace shekara. “Kamar yadda yake a rubuce a cikin Doka, za mu kawo ɗan fari na ’ya’yanmu maza da na garken shanunmu, da na tumakinmu, da kuma na awakinmu a gidan Allahnmu, don firistocin da suke aikin a can. “Ban da haka ma, za mu kawo wa ɗakunan ajiyar gidan Allahnmu, abincinmu na farko daga ƙasa, na hadayun hatsinmu, na ’ya’yan dukan itatuwanmu da kuma na sabon ruwan inabinmu da mai namu wa firistoci. Za mu kuma kawo zakkar hatsinmu wa Lawiyawa, gama Lawiyawa ne ke karɓan Zakka cikin dukan garuruwan da muke noma. Firist wanda yake daga zuriyar Haruna zai raka Lawiyawa sa’ad da suke karɓan zakka, Lawiyawan kuma za su kawo kashi ɗaya bisa goma na zakka zuwa gidan Allahnmu, su kawo a ɗakunan ajiya na baitulmali. Mutanen Isra’ila haɗe da Lawiyawa, za su kawo sadakokinsu na hatsi, sabon ruwan inabi da mai a ɗakunan ajiya inda ake ajiyar kayayyakin wuri mai tsarki da kuma inda firistoci, matsaran ƙofofi da kuma mawaƙa suke zama. “Ba za mu ƙyale gidan Allahnmu ba.”

Nehemiya 13:5

ya kuma tanada masa babban ɗakin da dā ake ajiyar hadayun hatsi da turare da kayayyaki haikali, da kuma zakan hatsi, sabon ruwan inabi da kuma mai da aka umarta don Lawiyawa, mawaƙa da kuma matsaran ƙofofi, da kuma sadakoki domin firistoci.

Nehemiya 13:12

Dukan Yahuda suka kawo zakan hatsi, sabon ruwan inabi da mai cikin ɗakunan ajiya.

Ayuba 1:3-4

yana da tumaki dubu bakwai, raƙuma dubu uku, shanu ɗari biyar, da jakuna ɗari biyar, yana kuma da masu yi masa aiki da yawa. A ƙasar Gabas ba wani kamar sa. ’Ya’yansa maza sukan yi biki a gidajensu, wannan yă yi yă ba wancan, sai su kira ’yan’uwansu mata ukun su ci, su sha tare.

Ayuba 1:21

ya ce, “Tsirara na fito daga cikin mahaifiyata, tsirara kuma zan koma. Ubangiji ya bayar, Ubangiji kuma ya karɓa; yabo ya tabbata ga Ubangiji.”

Ayuba 20:15

Zai haras da dukiyar da ya haɗiye; Allah zai sa cikinsa yă haras da su.

Ayuba 20:19

Gama ya ci zalin talakawa ya bar su cikin wahala; ya ƙwace gidajen da ba shi ya gina ba.

Ayuba 21:13

Suna yin rayuwarsu cikin arziki kuma su mutu cikin salama.

Ayuba 22:6-7

Ka sa ɗan’uwanka yă biya ka bashin da kake binsa ba dalili; ka ƙwace wa mutanen rigunansu ka bar su tsirara. Ba ka ba masu jin ƙishirwa su sha ba kuma ka hana wa masu jin yunwa abinci su ci.

Ayuba 22:25

sa’an nan ne Maɗaukaki zai zama zinariyarka, zai zama azurfa mafi kyau a wurinka.

Ayuba 24:2-10

Mugaye suna satar fili ta wurin matsar da duwatsun da aka yi iyaka da su; suna satar dabbobi su kuma yi kiwon su. Suna ƙwace wa marayu jakunansu suna kuma ƙwace wa gwauruwa sa don suna binta bashi. Suna ture matalauta daga hanya suna kuma sa dole matalautan ƙasar su ɓoye. Kamar jakunan jeji a hamada, matalauta suna aikin neman abinci gonaki marasa amfani suna tanada abinci wa ’ya’yansu. Suna girbi a gonakin da ba nasu ba, suna yin kala a gonar inabi ta mugaye. Don ba su da tufafi, sukan kwana tsirara; ba su da wani abin da zai rufe su cikin sanyi. Sun jiƙe sharkaf da ruwan da yake kwararowa daga duwatsu, sun rungume duwatsu don rashin wurin fakewa. Ana ƙwace jinjiri mai shan mama; ana ƙwace ɗan yaron matalauci don biyan bashi. Don ba su da tufafi suna yawo tsirara; suna dakon dammunan hatsi amma duk da haka suna cikin shan yunwa.

Ayuba 31:23-25

Gama ina jin tsoron hallaka daga Allah, kuma domin tsoron ɗaukakarsa ba zan iya yin waɗannan abubuwa ba. “In na dogara ga zinariya ko kuma na ce wa zallan zinariya, ‘Gare ki nake dogara,’ in na yi fahariya don yawan dukiyata, arzikin da hannuwana suka samu.

Ayuba 34:19

wanda ba ya nuna sonkai ga ’ya’yan sarki kuma ba ya goyon bayan masu arziki a kan matalauta, gama dukansu shi ya yi su da hannuwansa.

Ayuba 42:10

Bayan Ayuba ya yi wa abokansa addu’a, Ubangiji ya sa shi ya sāke zama mai arziki ya ninka abin da yake da shi a dā sau biyu.

Ayuba 42:15

Duk a cikin ƙasar ba a samu kyawawan mata kamar ’ya’yan Ayuba ba, kuma babansu ya ba su gādo tare ta ’yan’uwansu maza.

Zabura 2:8

Ka tambaye ni zan kuwa sa al’ummai su zama gādonka, iyakokin duniya su zama mallakarka.

Zabura 9:18

Amma har abada ba za a manta da mai bukata ba, ba kuwa sa zuciyar mai wahala zai taɓa hallaka.

Zabura 10:3

Yakan yi taƙama da ƙulle-ƙullen zuciyarsa; yana albarkaci mai haɗama yana kuma ƙin Ubangiji.

Zabura 15:5

wanda yake ba da rance ba tare da ruwa ba kuma ba ya karɓan cin hanci don yă kā da marar laifi. Shi wanda yake yin waɗannan abubuwa ba zai taɓa jijjiguwa ba.

Zabura 16:5-6

Ubangiji, ka ba ni rabona da kwaf ɗin na; ka kiyaye rabona, Iyakoki sun fāɗo mini a wurare masu daɗi; tabbatacce ina da gādo mai bansha’awa.

Zabura 23:1

Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba,

Zabura 34:9

Ku ji tsoron Ubangiji, ku tsarkakansa, gama masu tsoronsa ba sa rasa kome.

Zabura 35:10

Dukan raina zai ce, “Wane ne kamar ka, ya Ubangiji? Ka kuɓutar da matalauta daga waɗanda suka fi ƙarfinsu, matalauta da masu bukata daga waɗanda suke musu fashi.”

Zabura 37:3-4

Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri; yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya. Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji zai kuwa biya bukatun zuciyarka.

Zabura 37:25-26

Dā ni yaro ne amma yanzu na tsufa, duk da haka ban taɓa ganin an yashe masu adalci ba ko a ce ’ya’yansu suna roƙon burodi. Kullum suna bayar hannu sake suna kuma ba da bashi ba da wahala ba, za a yi wa ’ya’yansu albarka.

Zabura 37:29

Masu adalci za su gāji ƙasar su kuma zauna a cikinta har abada.

Zabura 40:17

Ni dai matalauci ne da mai bukata; bari Ubangiji yă tuna da ni. Kai ne taimakona da mai cetona; Ya Allahna, kada ka jinkirta.

Zabura 41:1-2

Mai albarka ne wanda yake jin tausayin marasa ƙarfi; Ubangiji yakan kuɓutar da shi a lokutan wahala. Ubangiji zai kāre shi yă kuma kiyaye ransa; zai albarkace shi a cikin ƙasar ba kuwa zai miƙa shi ga hannun maƙiyansa ba.

Zabura 49:6-8

waɗanda suka dogara ga arzikinsu suna kuma fariya a kan yawan arzikinsu? Ba wani da zai iya ceton ran wani ko yă ba wa Allah kuɗin fansa saboda shi, kuɗin fansa domin rai yana da tsada, babu abin da za a biya da ya taɓa isa,

Zabura 52:7

“Yanzu, ga mutumin da bai mai da Allah mafakarsa ba amma ya dogara a yawan arzikinsa ya kuma yi ƙarfi ta wurin hallaka waɗansu!”

Zabura 62:10

Kada ku dogara a kan ƙwace ko yin fariya a kayan sata; ko arzikinku ya ƙaru, kada ku sa zuciyarku a kansu.

Zabura 72:12-13

Gama zai ceci masu bukatan da suka yi kuka, marasa ƙarfin da ba su da mai taimako. Zai ji tausayin gajiyayyu da masu bukata yă ceci masu bukata daga mutuwa.

Zabura 82:3-4

Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu; ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya. Ku ceci marasa ƙarfi da masu bukata; ku kuɓutar da su daga hannun mugaye.

Zabura 84:11

Gama Ubangiji Allah rana ne da kuma garkuwa; Ubangiji yakan yi alheri da kuma daraja; ba ya hana kowane abu mai kyau wa waɗanda suke aikata abin da yake daidai.

Zabura 102:17

Zai amsa addu’ar marasa ƙarfi; ba zai ƙyale roƙonsu ba.

Zabura 112:3

Wadata da arziki suna a cikin gidansa, adalcinsa zai dawwama har abada.

Zabura 112:5

Abu mai kyau zai zo masa shi da yake kyauta yake kuma ba da bashi hannu sake, shi da yake yin al’amuransa cikin gaskiya.

Zabura 113:7-8

Yakan tā da matalauta daga ƙura yakan ɗaga mabukata daga tarin toka; ya zaunar da su tare da sarakuna, tare da sarakunan mutanensu.

Zabura 115:4

Amma gumakansu azurfa da zinariya ne, da hannuwan mutane suka yi.

Zabura 115:14-15

Bari Ubangiji yă sa ku ƙaru, da ku da ’ya’yanku. Bari Ubangiji yă albarkace ku, shi Mahalicci sama da ƙasa.

Zabura 116:12

Yaya zan sāka wa Ubangiji saboda dukan alherinsa gare ni?

Zabura 145:15-16

Idanun kowa yana dogara gare ka, kana kuma ba su abincinsu a lokacin da ya dace. Ka buɗe hannunka ka kuma ƙosar da sha’awar kowane abu mai rai.

Karin Magana 1:19

Dukan waɗanda suke neman ribar da ba a samu a hanya mai kyau; ƙarshen wannan yakan ɗauke rayukansu.

Karin Magana 2:4-5

in ka neme shi yadda ake neman azurfa ka kuma neme shi kamar yadda ake neman ɓoyayyiyar dukiya, to, za ka gane tsoron Ubangiji ka kuma sami sanin Allah.

Karin Magana 3:9-10

Ka girmama Ubangiji da dukan dukiyarka, ta wurin miƙa masa nunan fari na dukan amfanin gonarka; ta haka rumbunanka za su cika har su zuba, randunanka kuma su cika har baki da sabon ruwan inabi.

Karin Magana 3:13-15

Mai albarka ne mutumin da ya sami hikima, mutumin da ya sami fahimi, gama ta fi azurfa riba tana kuma da amfani fiye da zinariya. Ta fi lu’ulu’u daraja; ba a kwatanta abin da ka fi sha’awa da ita.

Karin Magana 3:27-28

Kada ka ƙi yin alheri ga duk wanda ya dace, sa’ad da kana iya yin haka. Kada ka ce wa maƙwabcinka “Ka yă dakata sai gobe,” idan kana iya taimakonsa yanzu.

Karin Magana 6:1-5

Ɗana, in ka shirya tsaya wa maƙwabcinka don yă karɓi bashi, in ka sa hannunka don ɗaukar lamunin wani, in maganarka ta taɓa kama ka, ko kalmomin bakinka sun zama maka tarko, to, sai ka yi haka, ɗana don ka ’yantar da kanka; da yake ka shiga hannuwan maƙwabcinka, ka tafi ka ƙasƙantar da kanka; ka roƙi maƙwabcinka! Ka hana kanka barci, ko gyangyaɗi a idanunka ma. Ka ’yantar da kanka, kamar barewa daga hannun mai farauta, kamar tsuntsu daga tarkon mai kafa tarko.

Karin Magana 6:30-31

Mutane ba sa ƙyale ɓarawo in ya yi sata don yă ƙosar da yunwarsa sa’ad da yake jin yunwa. Duk da haka in aka kama shi, dole yă biya sau bakwai ko da yake abin zai ci dukan arzikin gidansa.

Karin Magana 8:18-21

Tare da ni akwai wadata da girmamawa, dukiya da wadata masu dawwama. ’Ya’yan itacena sun fi zinariya zalla; amfanin gonar da nake bayar ya fi azurfa mafi kyau. Ina tafiya a hanyar adalci, a kan hanyoyin gaskiya, ina ba da wadata ga waɗanda suke ƙaunata ina sa wuraren ajiyarsu su cika.

Karin Magana 10:2-5

Dukiyar da aka samu a hanyar da ba tă dace ba, ba ta da albarka, amma adalci kan ceci mutum daga mutuwa. Ubangiji ba ya barin mai adalci da yunwa amma yakan lalace burin mugu. Ragwanci kan sa mutum yă zama matalauci, amma aiki tuƙuru kan ba da dukiya. Shi da ya tattara hatsi da rani ɗa ne mai hikima, amma shi da yakan yi barci a lokacin girbi ɗa ne wanda ya zama abin kunya.

Karin Magana 10:15

Dukiyar masu arziki yakan zama mafakar birninsu, amma talauci shi ne lalacin matalauci.

Karin Magana 10:20-22

Harshen adali azurfa ce zalla, amma zuciyar mugu ba ta da wani amfani. Leɓunan adalai kan amfane yawanci, amma wawa kan mutu saboda rashin azanci. Albarkar Ubangiji kan kawo wadata, ba ya kuma ƙara wahala a kai.

Karin Magana 11:1

Ubangiji yana ƙyamar ma’aunan zamba, amma ma’aunin da suke daidai ne abin farin cikinsa.

Karin Magana 11:15-16

Duk wanda ya ɗauki lamunin wani tabbatacce zai sha wahala, amma duk wanda ya ƙi ya sa hannu a ɗaukar lamuni ba ruwansa. Mace mai hankali na samu bangirma, amma azzalumai za su sami dukiya.

Karin Magana 11:24-28

Wani mutum kan bayar hannu sake, duk da haka yakan sami fiye; wani yakan riƙe abin da ba nasa ba, amma sai ya ƙarasa cikin talauci. Mutum mai kyauta zai azurta; shi da yakan taimake waɗansu, za a taimake shi. Mutane kan la’anci mai ɓoye hatsi yana jira ya yi tsada, amma albarka kan zauna a kan wanda yake niyya ya sayar. Duk mai nema alheri kan sami alheri, amma mugu kan zo wa wanda yake nemansa. Duk wanda ya dogara ga arzikinsa zai fāɗi, amma adali zai yi nasara kamar koren ganye.

Karin Magana 13:4

Rago ya ƙosa ya sami wani abu ainun amma ba ya samun kome, amma sha’awar mai aiki tuƙuru yakan ƙoshi sosai.

Karin Magana 13:7-8

Wani mutum yakan ɗauki kansa mai arziki ne, alhali ba shi da kome, wani ya ɗauki kansa shi matalauci ne, alhali shi mawadaci ne ƙwarai. Arzikin mutum zai iya kuɓutar da ransa, amma matalauci ba ya jin barazana.

Karin Magana 13:11

Kuɗin da aka same su a rashin gaskiya yakan ɓace da sauri, amma duk wanda ya tara kuɗi kaɗan-kaɗan za su yi ta ƙaruwa.

Karin Magana 13:22

Mutumin kirki kan bar gādo wa ’ya’ya ’ya’yansa, amma arzikin mai zunubi ajiye ne da aka yi wa mai adalci.

Karin Magana 14:20-23

Maƙwabta sukan gudu daga matalauta, amma masu arziki suna da abokai da yawa. Duk wanda ya rena maƙwabci ya yi zunubi, amma mai albarka ne wanda yake alheri ga mabukata. Ba waɗanda suke ƙulla mugunta sukan kauce ba? Amma waɗanda suke ƙulla abin da yake mai kyau sukan sami ƙauna da aminci. Duk aiki tuƙuru yakan kawo riba, amma zama kana surutu kan kai ga talauci kawai.

Karin Magana 14:31

Duk wanda ya zalunci matalauci ya zagi Mahaliccinsu ke nan, amma duk wanda ya yi alheri ga mabukata yana girmama Allah ne.

Karin Magana 15:6

Gidan adali yana da dukiya mai yawa, amma albashin mugaye kan kawo musu wahala.

Karin Magana 15:16-17

Gara a kasance da kaɗan da tsoron Ubangiji da a kasance da arziki mai yawa game da wahala. Gara a ci abincin kayan ganye inda akwai ƙauna da a ci kiwotaccen saniya inda ƙiyayya take.

Karin Magana 15:27

Mutum mai haɗama kan kawo wahala ga iyalinsa, amma wanda yake ƙin cin hanci zai rayu.

Karin Magana 16:8

Gara ka sami kaɗan ta hanyar adalci da sami riba mai yawa ta hanyar rashin gaskiya.

Karin Magana 16:16

Ya ma fi kyau ka sami hikima fiye da zinariya, ka zaɓi fahimi a maimakon azurfa!

Karin Magana 17:1-3

Gara ka ci busasshen burodi da kwanciyar rai kuma shiru da ka je cin abinci a gidan da ke cike da biki amma da ɓacin rai. Bawa mai hikima zai yi mulki a kan da mai rashin kunya, kuma zai raba gādo kamar ɗaya daga cikin ’yan’uwansa. Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta, amma Ubangiji ne mai gwajin zuciya.

Karin Magana 17:18

Mutumin da ba shi da azanci yakan ɗauki lamunin wani ya kuma ɗauki nauyin biyan basusuwan maƙwabci.

Karin Magana 18:23

Matalauci kan yi roƙo da taushi, amma mawadaci kan amsa da kakkausar murya.

Karin Magana 19:17

Duk wanda yake kirki ga matalauta yana ba wa Ubangiji bashi ne, zai kuwa sami lada game da abin da ya yi.

Karin Magana 20:4

Rago ba ya noma a lokacin noma; saboda haka a lokacin girbi ba ya bukata samun kome.

Karin Magana 20:10

Ma’auni marar gaskiya da magwajin da ba daidai ba, Ubangiji ya ƙi su duka.

Karin Magana 20:17

Abincin da aka samu ta hanyar zamba yakan zama da daɗi, amma mutum zai ƙarasa da baki cike da yashi.

Karin Magana 20:21

Gādon da aka samu da sauri a farkon farawa ba zai zama mai albarka a ƙarshe ba.

Karin Magana 21:5-6

Shirye-shiryen mai aiki tuƙuru kan kai ga riba in kuwa ka cika gaggawa zai kai ga talauci. Dukiyar da aka samu ta wurin harshe mai yin ƙarya tarin tururi ne da kuma mugun tarko.

Karin Magana 21:13

In mutum ya toshe kunnuwansa ga kukan matalauci, shi ma zai yi kukan neman taimako ba kuwa zai sami amsa ba.

Karin Magana 21:17-20

Duk mai son jin daɗi zai zama matalauci; duk mai son ruwan inabi da mai ba zai taɓa zama mai arziki ba. Mugu kan zama abin fansa don adali, marar aminci kuma don mai aikata gaskiya. Gara a zauna a hamada da a zauna da mace mai fitina da kuma mugun hali. A gidan mai hikima akwai wuraren ajiya na abinci da mai masu kyau, amma wawa kan cinye duk abin da yake da shi.

Karin Magana 21:25-26

Marmarin rago zai zama mutuwarsa, domin hannuwansa sun ƙi su yi aiki. Dukan yini yana marmari ya sami ƙari, amma mai adalci yakan bayar hannu sake.

Karin Magana 22:1-2

An fi son suna mai kyau fiye da wadata mai yawa; tagomashi kuma ya fi azurfa ko zinariya. Mawadaci da matalauci suna da abu guda. Ubangiji ne Mahaliccinsu duka.

Karin Magana 22:7-9

Mawadaci yakan yi mulki a kan matalauci, mai cin bashi kuwa bawan mai ba da bashi ne. Duk wanda ya shuka mugunta yakan girbe wahala, za a kuma hallaka sandar fushinsa. Mai bayarwa hannu sake shi kansa zai sami albarka, gama yakan raba abincinsa da matalauta.

Karin Magana 22:16

Duk wanda yake danne matalauta don yă azurta kuma duk wanda yake kyauta ga mawadata, dukansu kan talauta.

Karin Magana 22:22-23

Kada ka zalunci matalauta a kan suna matalauta kada kuma ka ƙwari wanda ba shi da mai taimako a gaban shari’a, gama Ubangiji zai yi magana dominsu zai kuwa washe waɗanda suka washe su.

Karin Magana 22:26-27

Kada ka zama mai ɗaukar lamuni ko ka ba da jingina saboda bashi; gama in ka kāsa biya za a ƙwace gadon da kake kwanciya a kai ma.

Karin Magana 23:4-5

Kada ka gajiyar da kanka don ka yi arziki; ka kasance da hikimar dainawa. Da ƙyiftawar ido a kan wadata ta ɓace, gama tabbatacce sukan yi fikafikai sukan tashi sama kamar gaggafa.

Karin Magana 23:21

gama bugaggu da ruwan inabi da masu yawan ci sukan zama matalauta, gama jiri yakan yi musu sutura da tsummoki.

Karin Magana 24:3-4

Ta wurin hikima ce ake gina gida, kuma ta wurin fahimi ake kafa ta; ta wurin sani ɗakunanta sukan cika da kyawawan kayayyaki masu daraja.

Karin Magana 24:33-34

Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi, ɗan naɗin hannuwa don a huta, sai talauci ya shigo maka kamar ’yan fashi rashi kuma ya zo maka kamar mai hari.

Karin Magana 25:11

Kalmar da aka faɗa daidai tana kamar zubin zinariyar da aka yi a mazubin azurfa.

Karin Magana 25:21-22

In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ba shi abinci ya ci; in yana jin ƙishi, ka ba shi ruwa ya sha. Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta mai ci a kansa, Ubangiji kuma zai sāka maka.

Karin Magana 27:24

domin dukiya ba ta dawwama har abada, ba a kuma kasance da rawani daga tsara zuwa tsara.

Karin Magana 28:6-8

Gara matalauci wanda yake tafiya babu abin zargi da mai arziki wanda hanyoyinsa mugaye ne. Duk wanda ya kiyaye doka ɗa ne mai la’akari, amma wanda yake abokantaka da masu zari yakan jawo wa mahaifinsa kunya. Duk wanda ya tara dukiyarsa ta wurin ba da bashi da ruwan da ya wuce misali yana tara wa wani ne wanda zai yi wa talakawa alheri.

Karin Magana 28:11

Mai arziki zai yi zato shi mai hikima ne a ganinsa, amma matalauci mai basira ya fi shi sanin abin da yake daidai.

Karin Magana 28:19-24

Duk wanda ya nome gonarsa zai sami amfani a yalwace, amma duk wanda yake zaman banza zai zama matalauci a koyaushe. Mutum mai aminci zai cika da albarka, amma duk mai son yin arziki dare ɗaya zai sha hukunci. Nuna sonkai ba shi da kyau, duk da haka mutum zai aikata abin da ba daidai ba saboda ’yar ƙaramar rashawa. Mai rowa yana alla-alla ya yi arziki bai san cewa talauci ne ke jiransa ba. Duk wanda ya tsawata wa wani mutum zai sami yabo a ƙarshe fiye da wanda yake mai daɗin baki. Duk wanda ya yi wa mahaifin ko mahaifiyarsa sata ya kuma ce, “Ai, ba laifi ba ne” abokin mai hallakarwa ne shi.

Karin Magana 28:27

Duk wanda yake bayarwa ga matalauta ba zai rasa kome ba, amma duk wanda bai kula da su ba yana samu la’ana masu yawa.

Karin Magana 29:7

Masu adalci sun damu game da adalci don talakawa, amma mugaye ba su da wannan damuwa.

Karin Magana 29:24

Duk wanda yake abokin ɓarawo abokin gāban kansa ne; yana jin sa yana ta rantsuwa, amma bai isa ya ce kome ba.

Karin Magana 30:8-9

Ka kawar da ƙarya da kuma ƙarairayi nesa da ni; kada ka ba ni talauci ko arziki, amma ka ba ni abincina na yini kaɗai. In ba haka ba, zan wadace in ƙi ka har in ce, ‘Wane ne Ubangiji?’ Ko kuwa in zama matalauci in yi sata ta haka in kunyata sunan Allahna.

Karin Magana 31:9-10

Yi magana a kuma yi shari’ar adalci; a tsare hakkin talakawa da masu bukata.” Wa yake iya samun mace mai halin kirki? Darajarta ta fi ta lu’ulu’ai.

Karin Magana 31:20

Takan marabci talakawa takan kuma taimaki masu bukata.

Mai Hadishi 2:4-11

Na yi ayyuka masu girma. Na gina gidaje wa kaina na kuma shuka gonakin inabi. Na yi lambuna da wuraren shaƙatawa, na shuka itatuwa masu ’ya’ya iri-iri a cikinsu. Na yi tankuna don in yi banruwan kurmin itatuwa. Na sayi bayi mata da maza, ina kuma da waɗansu bayin da aka haifa a gidana. Ina da garkunan shanu da na tumaki da na awaki fiye da duk wanda ya taɓa zama a Urushalima kafin ni. Na tara wa kaina azurfa da zinariya, ina da ma’ajin sarakuna da yankuna. Na samo wa kaina mawaƙa mata da maza, da dukan irin matan da kowane namiji zai so. Na ƙasaita fiye da kowane mutumin da ya riga ni zama a Urushalima. Cikin dukan wannan, hikimata ba tă rabu da ni ba. Ban hana kaina duk wani abin da idona ya yi sha’awarsa ba; ban hana zuciyata wani jin daɗi ba. Zuciyata ta yi murna da dukan aikina, wannan kuwa shi ne ladan dukan famata. Duk da haka sa’ad da na duba dukan aikin hannuwana, da abin da na yi fama don in samu, sai kome ya zama ba shi da amfani, naushin iska ne kawai; babu wata riba a duniya.

Mai Hadishi 5:10

Duk mai ƙaunar kuɗi ba ya samun isashe; duk ma ƙaunar dukiya ba ya ƙoshi da abin da yake samu. Wannan ma ba shi da amfani.

Mai Hadishi 5:15

Tsirara mutum yakan fito daga cikin mahaifiyarsa, kuma kamar yadda ya fito, haka zai koma. Ba ya ɗaukan kome daga wahalarsa da zai riƙe a hannunsa.

Mai Hadishi 5:19

Ban da haka ma, sa’ad da Allah ya ba wa mutum dukiya da wadata, ya kuma ba shi zarafi yă ji daɗinsu, ya kuma amince da rabonsa, sai yă ji daɗin aikinsa, wannan kyauta ce ta Allah.

Mai Hadishi 6:2

Allah yakan ba mutum dukiya, da wadata da kuma girma, don kada yă rasa abin da ransa yake so, amma Allah bai ba shi zarafin more su ba, a maimakon haka ma sai baƙo ne yă more su. Wannan ba shi da amfani, mugun abu ne ƙwarai.

Mai Hadishi 10:19

Akan shirya abinci don jin daɗi, ruwan inabi kuwa don faranta zuciya, amma kuɗi ne amsar kome.

Mai Hadishi 11:6

Ka shuka irinka da safe, da yamma kuma kada ka janye hannunka, gama ba ka san wanda zai yi albarka ba, ko wannan ko wancan, ko kuma duka biyunsu su yi albarka.

Ishaya 2:7-8

Ƙasarsu ta cika da azurfa da zinariya; dukiyarsu kuma ba iyaka. Ƙasarsu ta cika da dawakai; kekunan yaƙinsu kuma ba iyaka. Ƙasarsu ta cika da gumaka; sukan rusuna ga aikin hannuwansu, ga abin da yatsotsinsu suka yi.

Ishaya 10:2

don su hana matalauta hakkinsu su kuma ƙi yin shari’ar gaskiya a kan waɗanda suke zaluntar mutanena, suna ƙwace wa gwauraye dukiyarsu suna kuma yi wa marayu ƙwace.

Ishaya 32:8

Amma mutumin kirki kan yi shirye-shirye masu kirki, kuma yakan tsaya a kan ayyukan kirki.

Ishaya 55:1-2

“Ku zo, dukanku masu jin ƙishi, ku zo wurin ruwaye; ku kuma da ba ku da kuɗi, ku zo, ku saya ku kuma ci! Ku zo, ku saya ruwan inabi da madara ba tare da kuɗi ba ba za ku kuma biya kome ba. Don me za ku kashe kuɗi a kan abin da ba abinci ba, ku kuma yi wahala a kan abin da ba za ku ƙoshi ba? Ku saurara, ku saurare ni, ku kuma ci abin da yake da kyau, ranku kuma zai ji daɗin abinci mafi kyau.

Ishaya 58:7

Ba shi ne ku rarraba abincinku da mayunwata ku kuma tanada wa matalauta masu yawo mahalli, sa’ad da kuka ga wanda yake tsirara, ku yi masa sutura, kada kuma ku ba wa namanku da jininku baya?

Ishaya 58:10

in kuma kuka ɗauki lokaci kuka ƙosar da mayunwata kuka kuma biya bukatun waɗanda suke shan tsanani, sa’an nan ne haskenku zai haskaka cikin duhu darenku kuma zai zama kamar tsakar rana.

Ishaya 60:5-6

Sa’an nan za ki duba ki kuma haskaka zuciyarki zai motsa ya kuma cika da farin ciki; za a kawo miki wadata daga tekuna, za a kawo miki arzikin al’ummai. Manyan ayarin raƙuma za su cika ƙasar, ƙananan raƙuma ke nan daga Midiyan da Efa. Daga Sheba kuma duka za su zo, suna ɗauke da zinariya da turare suna shelar yabon Ubangiji.

Ishaya 60:17

A maimakon tagulla zan kawo zinariya, azurfa kuma a maimakon baƙin ƙarfe. A maimakon katako zan kawo tagulla, baƙin ƙarfe kuma a maimakon duwatsu. Zan sa salama ta zama gwamnarki adalci kuma mai mulkinki.

Irmiya 4:30

Me kike yi, ya wadda aka ragargaza? Me ya sa kika sanya mulufi kika sa kayan adon zinariya? Me ya sa kika sa wa idanunki tozali? Kin yi kwalliyarki a banza. Masoyanki sun bar ki; suna neman ranki.

Irmiya 15:13

“Dukiyarku da arzikinku zan ba da su ganima, babu tara, saboda duka zunubanku ko’ina a ƙasar.

Irmiya 51:13

Ke da kike zama kusa da ruwaye da kike kuma wadatar dukiya, ƙarshenki ya zo, lokaci ya yi da za a kau da ke.

Makoki 1:11

Dukan mutanenta suna nishi da ƙyar suna neman burodi; sun sayar da dukiyarsu don su samu abinci don kada su mutu da yunwa. “ Ubangiji, ka duba ka gani, gama an yashe ni.”

Ezekiyel 7:19

“ ‘Za su zubar da azurfarsu a tituna, zinariyarsu kuma za tă zama ƙazantacciyar aba. Azurfarsu da zinariyarsu ba za su iya cetonsu a ranar hasalar Ubangiji ba. Ba za su ƙosar da yunwansu ko su cika cikinsu da shi ba, gama su ne sanadin tuntuɓensu cikin zunubi.

Ezekiyel 16:49-50

“ ‘To, fa, ga zunubin ’yar’uwarki Sodom. Ita da ’ya’yanta mata sun yi girman kai, sun ƙoshi fiye da kima kuma ba su kula da wani abu ba; ba su taimaki matalauta da kuma masu bukata ba. Su masu girman kai ne kuma suka aikata abubuwa masu banƙyama a gabana. Saboda haka na kau da su kamar yadda ka gani.

Ezekiyel 18:7-9

Ba ya cin zalin wani, amma yakan mayar wa wanda ya ba shi jingina abin da ya jinginar masa. Ba ya yi fashi amma yakan ba wa mayunwata abinci ya kuma tanada wa marasa tufafi riga. Ba ya ba da bashi da ruwa ko ya karɓa ƙarin riba. Yakan janye hannunsa daga aikata mugunta yakan kuma yi shari’a cikin gaskiya tsakanin mutum da mutum. Yana bin ƙa’idodina yana kuma kiyaye dokokina da aminci. Wannan mutumin adali ne; tabbatacce zai rayu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

Ezekiyel 18:12-13

Yakan ci zalin matalauta da mabukata. Yakan yi fashi. Ba ya mayar da abin da aka jinginar masa. Ya dogara ga gumaka. Yana aikata ayyukan banƙyama. Yakan ba da bashi da ruwa ya kuma karɓi riba mai yawa. Irin wannan mutum zai rayu? Ba zai rayu ba! Domin ya aikata dukan waɗannan abubuwa masu banƙyama, tabbatacce za a kashe shi, kuma hakkin jininsa zai zauna a kansa.

Ezekiyel 22:12

A cikinki mutane suna karɓan cin hanci don su yi kisankai; kina ba da rance da ruwa da ƙari, kina kuma cin riba a kan maƙwabcinki ta wurin ƙwace. Kina kuma manta da ni, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

Ezekiyel 22:29-30

Mutanen ƙasar na yin ƙwace suna yin fashi; suna cin zalin matalauta da mabukata suna wulaƙanta baƙo suna hana musu adalci. “Na nemi mutum guda a cikinsu wanda zai gina katanga ya tsaya a gabana a tsakani a madadin ƙasar don kada in hallaka ta, amma ban sami ko ɗaya ba.

Ezekiyel 28:4-7

Ta wurin hikimarka da ganewarka ka sami dukiya wa kanka ka kuma tara zinariya da azurfa cikin wuraren ajiyarka. Ta wurin dabararka mai girma cikin kasuwanci ka ƙara dukiyarka, kuma saboda dukiyarka zuciyarka ta cika da alfarma. “ ‘Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Domin ka ɗauka kai mai hikima ne, mai hikima kamar allah, zan kawo baƙi a kanka, waɗanda suka fi mugunta cikin sauran al’ummai; za su zāre takubansu a kan kyakkyawar hikimarka su kuma ɓarke darajarka mai walƙiya.

Ezekiyel 38:11-13

Za ka ce, “Zan kai hari wa ƙasar da ƙauyukanta ba su da katanga; zan fāɗa wa mutanen da suke zamansu kurum cikin salama, dukansu suna zama babu katanga babu ƙofofi ko ƙyamare. Zan washe in kwashe ganima in kuma juye hannuna gāba da kufai da aka sāke zaunar da mutanen da aka tattara daga al’ummai, masu yawan shanu da kayayyaki, masu zama a tsakiyar ƙasa.” Sheba da Dedan da ’yan kasuwar Tarshish da dukan ƙauyukanta za su ce maka, “Ka zo ka kwashe ganima ne? Ka tattara jama’arka don ka yi waso, ka kuma kwashe azurfa da zinariya, ka kwashe shanu da kayayyaki ka kuma ƙwace ganima mai yawa?” ’

Daniyel 5:2-4

Yayinda Belshazar yake shan ruwan inabi, sai ya umarta a kawo zinariya da azurfan da Nebukadnezzar mahaifinsa ya kwaso daga haikali a Urushalima, saboda sarki da hakimansa, da matansa da ƙwarƙwaransa su sha da su. Sai suka kawo kayan zinariyan nan da aka kwaso daga haikalin Allah a Urushalima, sarki kuwa da hakimansa, da matansa, da ƙwarƙwaransa suka yi ta sha da su. Yayinda suke shan ruwan inabin, sai suka yabi allolin zinariya da azurfa, da na tagulla, da na ƙarfe, da na itace da kuma na dutse.

Hosiya 4:7

Yawan ƙaruwar firistoci, haka suke yawan zunubi a kaina; sun yi musaya Ɗaukakarsu da wani abin kunya.

Hosiya 12:7-8

Ɗan kasuwa yana amfani da mudu marar gaskiya; yana jin daɗin cuta. Efraim yana fariya yana cewa, “Ni mai arziki ne ƙwarai; na azurta. Da dukan wadatata ba za a sami wani laifi ko zunubi a gare ni ba.”

Yowel 2:25-26

“Zan mayar muku da abin da fāra suka ci a waɗannan shekaru waɗanda ɗango da fāra masu gaigayewa, da kuma sauran fāra da tarin fāra babban mayaƙan da na aika don su fāɗa muku. Za ku sami a wadace ku ci, har sai kun ƙoshi, za ku kuma yabi sunan Ubangiji Allahnku, wanda ya yi muku ayyukan banmamaki; mutanena ba za su ƙara shan kunya ba.

Amos 5:11-12

Kuna matsa wa matalauta kuna sa su dole su ba ku hatsi. Saboda haka, ko da yake kun gina gidajen duwatsu, ba za ku zauna a cikinsu ba; ko da yake kun nome gonaki masu kyau, ba za ku sha ruwan inabinsu ba. Gama na san yawan laifofinku da kuma girman zunubanku. Kuna danne masu adalci kuna kuma cin hanci kuna kuma hana a yi wa matalauta shari’ar adalci a majalisa.

Amos 8:4-6

Ku ji wannan, ku da kuke tattake masu bukata kuka kori matalautan ƙasar. Kuna cewa, “Yaushe Sabon Wata zai wuce don mu sayar da hatsi, Asabbaci ta wuce, don mu sayar da alkama?” Mu yi awo da ma’aunin zalunci mu ƙara kuɗin kaya mu kuma cutar da mai saya, mu sayi matalauta da azurfa masu bukata kuma da takalmi, mu sayar da alkamar haɗe da yayi.

Mika 2:2

Kukan yi ƙyashin gonaki ku kuma ƙwace su, ku yi ƙyashin gidaje ku kuma ƙwace. Kukan zalunci mutum, ku ƙwace masa gidansa, har ku ƙwace masa gādonsa.

Habakkuk 2:6-7

“Dukansu ba za su yi masa tsiya, suna yin masa ba’a da dariya ba, suna cewa, “ ‘Kaito ga wannan wanda ya tara wa kansa kayan sata ya kuma wadatar da kansa da kayan ƙwace! Har yaushe wannan abu zai ci gaba?’ Masu binka bashi ba za su taso maka nan da nan ba? Ba za su farka su sa ka fargaba ba? Ta haka ka zama ganima a gare su.

Zefaniya 1:13

Za a washe dukiyarsu, a rurrushe gidajensu. Za su gina gidaje amma ba za su zauna a ciki ba; za su shuka inabi amma ba za su sha ruwansa ba.”

Zefaniya 1:18

Azurfarsu ko zinariyarsu ba za su iya cetonsu ba a ranar fushin Ubangiji.” A cikin zafin kishinsa za a hallaka dukan duniya gama zai kawo ƙarshen dukan mazaunan duniya nan da nan.

Haggai 2:8

‘Da zinariya da azurfa duka nawa ne,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.

Zakariya 11:12-13

Na faɗa musu cewa, “In kun ga ya fi kyau, ku biya ni; in kuwa ba haka ba, ku riƙe.” Saboda haka suka biya ni azurfa talatin. Sai Ubangiji ya ce mini, “Jefar da shi cikin ma’aji,” Lada mai kyau da aka yi cinikina ne! Saboda haka sai na ɗauki azurfa talatin ɗin na jefa su cikin gidan Ubangiji don a sa cikin ma’aji.

Malaki 3:8-10

“Mutum zai iya yi wa Allah fashi ne? Duk da haka kun yi mini fashi. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya muka yi maka fashi?’ “A wajen zakka da hadayu. Kuna ƙarƙashin la’ana, dukan al’ummarku, domin kuna yin mini fashi. Ku kawo dukan zakka cikin gidan ajiya, don a kasance da abinci a gidana. Ku gwada ni a wannan ku ga, ko ba zan buɗe taskokin sama in zubo muku albarka mai yawa, wadda har ba za ku rasa wurin sa ta ba, in ji Ubangiji Maɗaukaki.

Mattiyu 2:11

Suka shiga gidan, suka kuwa ga yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka durƙusa har ƙasa, suka yi masa sujada. Sa’an nan suka kunce dukiyarsu, suka miƙa masa kyautai na zinariya da na turare da na mur.

Mattiyu 5:3

‹“Masu albarka ne waɗanda suke matalauta a ruhu,› ‹gama mulkin sama nasu ne.›

Mattiyu 5:6

‹Masu albarka ne waɗanda suke jin yunwa da ƙishirwa don gani an yi adalci,› ‹gama za a ƙosar da su.›

Mattiyu 5:40-42

‹In kuma wani yana so yă yi ƙararka yă ƙwace rigarka, to, ba shi mayafinka ma.› ‹In wani ya tilasta ka yin tafiya mil ɗaya, to, tafi tare da shi mil biyu.› ‹Ka ba wa duk wanda ya roƙe ka abu, kada kuma ka hana wa wanda yake neman bashi daga gare ka.›

Mattiyu 6:1-4

‹“Ku yi hankali kada ku nuna ‘ayyukanku na adalci’ a gaban mutane, don su gani. In kuka yi haka, ba za ku sami lada daga wurin Ubanku da yake cikin sama ba.› ‹“Saboda haka sa’ad da kake ba wa masu bukata taimako, kada ka yi shelarsa, yadda munafukai suke yi a majami’u da kuma kan tituna, don mutane su yabe su. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke.› ‹Amma sa’ad da kake ba wa masu bukata taimako, kada ka yarda hannun hagunka yă ma san abin da hannun damarka yake yi,› ‹don bayarwarka ta zama a ɓoye. Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.›

Mattiyu 6:11-12

‹Ka ba mu yau abincin yininmu.› ‹Ka gafarta mana laifofinmu,› ‹kamar yadda mu ma muke gafarta wa masu yin mana laifi.›

Mattiyu 6:19-21

‹“Kada ku yi wa kanku ajiyar dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda kuma ɓarayi sukan fasa, su yi sata.› ‹Amma ku yi wa kanku ajiyar dukiya a sama, inda ba tsatsa da asu da za su ɓata su, inda kuma ba ɓarayin da za su fasa, su yi sata.› ‹Gama inda dukiyarka take, a nan ne fa zuciyarka za tă kasance.›

Mattiyu 6:24

‹“Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu. Ko dai yă ƙi ɗaya, yă ƙaunaci ɗaya, ko kuwa yă yi aminci ga ɗaya, sa’an nan yă rena ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah, ku kuma bauta wa kuɗi gaba ɗaya.”›

Mattiyu 6:25-34

‹“Saboda haka, ina gaya muku, kada ku damu game da rayuwarku, game da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha; ko kuma game da jikinku, game da abin da za ku sa. Ashe, rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba?› ‹Ku dubi tsuntsayen sararin sama mana; ba sa shuki ko girbi ko ajiya a rumbuna, duk da haka, Ubanku na sama yana ciyar da su. Ashe, ba ku fi su daraja nesa ba?› ‹Wane ne a cikinku ta wurin damuwa zai iya ƙara wa rayuwarsa ko sa’a ɗaya›‹?› ‹“Me ya sa kuke damuwa a kan riguna? Ku dubi yadda furannin jeji suke girma mana. Ba sa aiki ko saƙa.› ‹Duk da haka ina gaya muku ko Solomon cikin dukan darajarsa bai sa kayan adon da ya kai na ko ɗaya a cikinsu ba.› ‹In haka Allah yake yi wa ciyawar jeji sutura, wadda yau tana nan, gobe kuwa a jefa a cikin wuta, ba zai ma fi yi muku sutura ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya?› ‹Don haka, kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci?’ Ko, ‘Me za mu sha?’ Ko kuma, ‘Me za mu sa?’› ‹Gama marasa sanin Allah suna fama neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu.› ‹Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa.› ‹Saboda haka kada ku damu game da gobe, gama gobe zai damu da kansa. Damuwar yau ma ta isa wahala.›

Mattiyu 7:7-8

‹“Ku roƙa za a ba ku; ku nema za ku samu; ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa.› ‹Gama duk wanda ya roƙa, akan ba shi; wanda ya nema kuwa, yakan samu, wanda kuma ya ƙwanƙwasa, za a buɗe masa ƙofa.›

Mattiyu 7:11

‹In ku da kuke mugaye kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga ’ya’yanku, balle Ubanku na sama, ba zai fi ku iya ba da abubuwa masu kyau, ga su waɗanda suka roƙe shi ba!›

Mattiyu 8:20

Sai Yesu ya amsa ya ce, ‹“Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.”›

Mattiyu 10:9-10

‹“Kada ku riƙe wata zinariya ko azurfa ko jan ƙarfe a aljihunanku,› ‹kada ku ɗauki jaka don tafiya, ko ƙarin riga, ko takalma ko sanda; domin ma’aikaci ya cancanci hakkinsa.›

Mattiyu 10:42

‹In kuma wani ya ba wa ɗaya daga cikin ƙananan nan ko da kwaf ruwan sanyi ne kan shi almajirina ne, gaskiya nake gaya muku, ba shakka ba zai rasa ladarsa ba.”›

Mattiyu 13:8

‹Har yanzu, waɗansu irin suka fāffāɗi a ƙasa mai kyau, inda suka ba da amfani riɓi ɗari, sittin ko kuma talatin na abin da aka shuka.›

Mattiyu 13:22-23

‹Wanda ya karɓi irin da ya fāɗi cikin ƙaya kuwa, shi ne mutumin da yakan ji maganar, sai dai damuwoyin rayuwan nan da jarrabar arzikin duniya sukan shaƙe shi, yă sa maganar ta kāsa amfani.› ‹Amma wanda ya karɓi irin da ya fāɗi a ƙasa mai kyau, shi ne mutumin da yakan ji maganar yă kuwa fahimce ta. Yakan ba da amfani wani riɓi ɗari, sittin, ko talatin na abin da aka shuka.”›

Mattiyu 13:44-46

‹“Mulkin sama yana kama da dukiyar da aka ɓoye a gona. Da wani ya same ta, sai yă sāke ɓoye ta, sa’an nan cikin farin cikinsa yă je yă sayar da duk abin da yake da shi yă sayi gonar.› ‹“Har wa yau dai, mulkin sama yana kama da ɗan kasuwa mai neman lu’ulu’ai masu kyau.› ‹Da ya sami dutse guda mai daraja sosai, sai ya tafi ya sayar da dukan abin da yake da shi ya saye shi.›

Mattiyu 16:26

‹Me mutum zai amfana in ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa? Ko kuwa me mutum zai bayar a bakin ransa?›

Mattiyu 17:24-27

Bayan Yesu da almajiransa suka isa Kafarnahum, sai masu karɓan harajin rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, “Malaminku ba ya biyan harajin haikali ne?” Ya amsa ya ce “I, yana biya.” Da Bitrus ya shiga gida, Yesu ne ya fara magana. Ya ce masa, ‹“Me ka gani, Siman? Daga wurin wane ne sarakunan duniya suke karɓar kuɗin shiga da kuma haraji, daga wurin ’ya’yansu ne ko kuwa daga wurin waɗansu?”› Bitrus ya amsa ya ce, “Daga wurin waɗansu.” Yesu ya ce masa, ‹“Wato, an ɗauke wa ’ya’yan ke nan.› ‹Amma don kada mu ɓata musu rai, ka je tafki ka jefa ƙugiyarka. Ka ɗauki kifin da ka fara kama; ka buɗe bakinsa, za ka sami shekel guda. Ka kawo ka ba su, harajina da naka ke nan.”›

Mattiyu 18:23-35

‹“Saboda haka, mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya so yă yi ƙididdigar dukiyarsa da take a hannun bayinsa.› ‹Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wani wanda yake bin bashin talenti dubu goma.› ‹Da yake bai iya biya ba, sai maigida ya umarta a sayar da shi da matarsa da yaransa da kuma duk abin da yake da shi, a biya bashin.› ‹“Bawan ya durƙusa a gabansa. Ya yi roƙo ya ce, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka ƙaf.’› ‹Maigidan bawan ya ji tausayinsa, ya yafe masa bashin, ya kuma sake shi.› ‹“Amma da wannan bawa ya fita, sai ya gamu da wani abokin bautarsa wanda yake binsa bashin dinari ɗari. Sai ya cafke shi, ya shaƙe shi a wuya yana cewa, ‘Biya ni abin da nake binka!’› ‹“Wannan abokin bautarsa ya durƙusa ya roƙe shi, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka.’› ‹“Amma ya ƙi. A maimako, sai ya je ya sa aka jefa shi a kurkuku, har yă biya bashin.› ‹Sa’ad da sauran bayin suka ga abin da ya faru, abin ya ɓata musu rai ƙwarai, sai suka tafi suka faɗa wa maigidansu dukan abin da ya faru.› ‹“Sai maigidan ya kira wannan bawa. Ya ce, ‘Kai mugun bawa, na yafe duk bashin da nake binka domin ka roƙe ni.› ‹Ashe, bai kamata kai ma ka ji tausayin abokin bautarka yadda na yi maka ba?’› ‹Cikin fushi, maigidan ya miƙa shi ga ma’aikatan kurkuku su gwada masa azaba, har yă biya dukan bashin da ake binsa.› ‹“Haka Ubana da yake cikin sama zai yi da kowannenku, in ba ku yafe wa ’yan’uwanku daga zuciyarku ba.”›

Mattiyu 19:21-22

Yesu ya amsa ya ce, ‹“In kana so ka zama cikakke, ka je, ka sayar da dukan dukiyarka ka kuma ba matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo, ka bi ni.”› Da saurayin ya ji haka, sai ya tafi rai a ɓace, don yana da arziki sosai.

Mattiyu 19:23-26

Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, ‹“Gaskiya nake gaya muku, yana da wuya mai arziki yă shiga mulkin sama.› ‹Har wa yau ina gaya muku, zai fi sauƙi raƙumi yă shiga ta kafar allura, da mai arziki yă shiga mulkin Allah.”› Sa’ad da almajiran suka ji wannan, sai suka yi mamaki ƙwarai. Suka yi tambaya suka ce, “To, wa zai sami ceto ke nan?” Yesu ya kalle su ya ce, ‹“Ga mutum kam, wannan ba ya yiwuwa, amma ga Allah kuwa, dukan abubuwa masu yiwuwa ne.”›

Mattiyu 19:27-29

Sai Bitrus ya amsa masa, “Ga shi mun bar kome don mu bi ka! Me za mu samu ke nan?” Yesu ya ce musu, ‹“Gaskiya nake gaya muku, a lokacin sabunta dukan kome, sa’ad da Ɗan Mutum ya zauna a kan kursiyinsa mai daraja, ku da kuka bi ni, ku ma za ku zauna a kan kursiyoyi goma sha biyu, kuna yi wa kabilu goma sha biyu na Isra’ila shari’a.› ‹Duk kuma wanda ya bar gidaje ko ’yan’uwa maza ko ’yan’uwa mata ko mahaifi ko mahaifiya ko yara ko gonaki, saboda ni, zai sami abin da ya fi haka riɓi ɗari, yă kuma gāji rai madawwami.›

Mattiyu 20:1-16

‹“Mulkin sama yana kama da wani mai gona, wanda ya fita da sassafe don yă yi hayar mutane su yi aiki a gonar inabinsa.› ‹Ya yarda yă biya su dinari guda a yini, sai ya tura su gonar inabinsa.› ‹“Wajen sa’a ta uku, ya fita sai ya ga waɗansu suna tsattsaye a bakin kasuwa ba sa kome.› ‹Ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi gonar inabina ku yi aiki, zan kuwa biya ku abin da ya dace.’› ‹Saboda haka suka tafi.› ‹“Ya sāke fita a sa’a ta shida da kuma sa’a ta tara, ya sāke yin haka.› ‹Wajen sa’a ta goma sha ɗaya, ya sāke fita, ya tarar da waɗansu har yanzu suna tsattsaye. Ya tambaye su, ‘Don me kuke yini tsattsaye a nan ba kwa kome?’› ‹“Suka amsa, ‘Don ba wanda ya ɗauke mu aiki.’› ‹“Ya ce musu, ‘Ku ma ku je ku yi aiki a gonar inabina.’› ‹“Sa’ad da yamma ta yi, sai mai gonar inabin ya ce wa wakilinsa, ‘Kira ma’aikatan, ka biya su hakkin aikinsu, fara daga waɗanda aka ɗauke su a ƙarshe har zuwa na farko.’› ‹“Ma’aikatan da ka ɗauka wajen sa’a ta goma sha ɗaya suka zo, kowannensu kuwa ya karɓi dinari guda.› ‹Saboda haka da waɗanda aka ɗauka da fari suka zo, sun zaci za su sami fiye da haka. Amma kowannensu ma ya karɓi dinari guda.› ‹Sa’ad da suka karɓa, sai suka fara yin gunaguni a kan mai gonar.› ‹Suna cewa, ‘Waɗannan mutanen da aka ɗauka a ƙarshe sun yi aikin sa’a ɗaya ne kawai, ka kuma mai da su daidai da mu da muka yini muna faman aiki, muka kuma sha zafin rana.’› ‹“Amma ya amsa wa ɗayansu ya ce, ‘Aboki, ban cuce ka ba. Ba ka yarda ka yi aiki a kan dinari guda ba?› ‹Ka karɓi hakkinka ka tafi. Ni na ga damar ba waɗannan na ƙarshe daidai da yadda na ba ka.› ‹Ba ni da ikon yin abin da na ga dama da kuɗina ne? Ko kana kishi saboda ni mai kyauta ne?’› ‹“Saboda haka fa, na ƙarshe za su zama na farko, na farko kuma su zama na ƙarshe.”›

Mattiyu 21:12-13

Yesu ya shiga filin haikali, ya kuma kori duk masu saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur masu canjin kuɗi da kuma kujerun masu sayar da tattabarai. Ya ce musu, ‹“A rubuce yake, ‘Za a ce da gidana, gidan addu’a,’›‹amma kuna mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ”›

Mattiyu 22:17-21

To, ka gaya mana, a ra’ayinka? Ya dace a biya Kaisar haraji ko a’a?” Amma Yesu da yake ya san mugun nufinsu, sai ya ce, ‹“Ku munafukai, don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko?› ‹Ku nuna mini kuɗin da ake biyan haraji da shi.”› Sai suka kawo masa dinari, sai ya tambaye su ya ce, ‹“Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne?”› Suka amsa, “Na Kaisar ne.” Sai ya ce musu, ‹“Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”›

Mattiyu 23:23

‹“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan ba da kashi ɗaya bisa goma na kayan yajinku, na’ana’a, anise, da lafsur. Amma kun ƙyale abubuwan da suka fi girma na dokoki, adalci, jinƙai da aminci. Waɗannan ne ya kamata da kun kiyaye ba tare da kun ƙyale sauran ba.›

Mattiyu 25:14-30

‹“Har wa yau, za a kwatanta shi da mutumin da zai yi tafiya, wanda ya kira bayinsa ya kuma danƙa musu mallakarsa.› ‹Ga guda, ya ba shi talenti biyar na kuɗi, ga wani talenti biyu, ga wani kuma talenti ɗaya, kowa bisa ga azancinsa. Sa’an nan ya yi tafiyarsa.› ‹Mutumin da ya karɓi talenti biyar, nan da nan ya tafi ya yi kasuwanci da su har ya sami ribar talenti biyar.› ‹Haka ma, wannan mai talenti biyu, shi ma ya yi riba biyu.› ‹Amma mutumin da ya karɓi talenti ɗaya ɗin, ya tafi, ya tona rami, ya ɓoye kuɗin maigidansa.› ‹“Bayan an daɗe, sai maigidan bayin nan ya dawo, ya kuma daidaita lissafi da su.› ‹Mutumin da ya karɓi talenti biyar, ya kawo ƙarin talenti biyar. Ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talenti biyar. Ga shi, na yi ribar biyar.’› ‹“Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’› ‹“Mutumin da yake da talenti biyu, shi ma ya zo ya ce, ‘Maigida, ka danƙa mini talenti biyu; ga shi, na yi ribar biyu.’› ‹“Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!’› ‹“Sa’an nan mutumin da ya karɓi talenti ɗaya ya zo. Ya ce, ‘Maigida, na san cewa kai mutum ne mai wuyan sha’ani, kana girbi inda ba ka shuka ba, kana kuma tara inda ba ka yafa iri ba.› ‹Saboda haka na ji tsoro, na je na ɓoye talentinka a ƙasa. Ga abinka.’› ‹“Maigidansa ya amsa ya ce, ‘Kai mugun bawa, mai ƙyuya! Ashe, ka san cewa ina girbi inda ban yi shuka ba, ina kuma tarawa inda ban yafa iri ba?› ‹To, in haka ne, ai, da ka sa kuɗina a banki, don sa’ad da na dawo da na karɓi abina da riba.› ‹“ ‘Karɓi talentin daga hannunsa ku ba wanda yake da talenti goma.› ‹Gama duk mai abu za a ƙara masa, zai kuma same shi a yawalce. Duk wanda ba shi da shi kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.› ‹Ku jefar da banzan bawan nan waje, cikin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.’›

Mattiyu 25:34-40

‹“Sa’an nan Sarki zai ce wa waɗanda suke damansa, ‘Ku zo, ku da Ubana ya yi wa albarka; ku karɓi gādonku, mulkin da aka shirya muku tun halittar duniya.› ‹Gama da nake jin yunwa, kun ciyar da ni, da nake jin ƙishirwa, kun ba ni abin sha, da nake baƙunci, kun karɓe ni,› ‹da nake bukatar tufafi, kun yi mini sutura, da na yi rashin lafiya, kun lura da ni, da nake kurkuku, kun ziyarce ni.’› ‹“Sa’an nan masu adalci za su amsa masa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka da yunwa muka ciyar da kai, ko da ƙishirwa muka ba ka abin sha?› ‹Yaushe kuma muka gan ka baƙo muka karɓe ka, ko cikin bukatar tufafi muka yi maka sutura?› ‹Yaushe kuma muka gan ka cikin rashin lafiya ko a kurkuku muka ziyarce ka?’› ‹“Sarkin zai amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan’uwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.’›

Mattiyu 25:41-45

‹“Sa’an nan zai ce wa waɗanda suke a hagunsa, ‘Ku rabu da ni, la’anannu, zuwa cikin madawwamiyar wutar da aka shirya don Iblis da mala’ikunsa.› ‹Gama da nake jin yunwa, ba ku ba ni abinci ba, da nake jin ƙishirwa, ba ku ba ni abin sha ba,› ‹da na yi baƙunci, ba ku karɓe ni ba, da nake bukatar tufafi, ba ku yi mini sutura ba, da na yi rashin lafiya kuma ina a kurkuku, ba ku lura da ni ba.’› ‹“Su ma za su amsa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka cikin yunwa ko ƙishirwa ko baƙo ko cikin bukatar tufafi ko cikin rashin lafiya ko cikin kurkuku, ba mu taimake ka ba?’› ‹“Zai amsa, yă ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ba ku yi mini ba ke nan.’›

Mattiyu 26:7-11

wata mace ta zo wurinsa da wani ɗan tulun alabasta na turaren mai tsada sosai, wanda ta zuba a kansa a lokacin da yake cin abinci. Sa’ad da almajiransa suka ga wannan, sai suka yi fushi. Suka ce, “Wannan almubazzaranci fa! Wannan turare ai, da an sayar da shi da kuɗi mai yawa a ba matalauta kuɗin.” Sane da wannan, Yesu ya ce musu, ‹“Me ya sa kuke damun macen nan? Ta yi mini abu mai kyau ne.› ‹Matalauta za su kasance tare da ku kullum, amma ni ba zan kasance tare da ku kullum ba.›

Mattiyu 26:15-16

ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi gare ku?” Sai suka ƙirga masa kuɗi azurfa talatin. Daga wannan lokaci, Yahuda ya yi ta neman zarafin da zai miƙa shi.

Mattiyu 27:3-10

Sa’ad da Yahuda, wanda ya bashe Yesu, ya ga an yanke wa Yesu hukuncin kisa, sai ya yi “da na sani.” Ya je mayar wa manyan firistoci da dattawan kuɗin azurfa talatin ɗin. Ya ce, “Na yi zunubi da na ci amanar marar laifi.” Suka ce masa, “Ina ruwanmu da wannan? Wannan dai ruwanka ne.” Sai Yahuda ya zubar da kuɗin a cikin haikalin ya tafi. Sa’an nan ya je ya rataye kansa. Manyan firistoci suka ɗauki kuɗin, suka ce, “Doka ta hana a sa kuɗin a cikin ma’aji, da yake kuɗin jini ne.” Saboda haka, sai suka yanke shawara su yi amfani da kuɗin suka sayi filin mai yin tukwane, saboda binne baƙi. Shi ya sa ake kiran filin, Filin Jini har yă zuwa yau. Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika cewa, “Suka ɗauki azurfa talatin, kuɗin da mutanen Isra’ila suka sa a kansa, suka kuma yi amfani da su, suka sayi filin mai yin tukwane, kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.”

Markus 4:8

‹Har yanzu, waɗansu irin suka fāɗi a ƙasa mai kyau. Suka tsira, suka yi girma, suka ba da amfani, suka yi riɓi talatin-talatin, waɗansu sittin-sittin, waɗansu kuma ɗari-ɗari.”›

Markus 4:18-20

‹Har yanzu, waɗansu kamar irin da aka shuka cikin ƙaya, sukan ji maganar,› ‹amma damuwar wannan duniya, da son dukiya, da kuma kwaɗayin waɗansu abubuwa, sukan shiga, su shaƙe maganar, har su mai da ita marar amfani.› ‹Waɗansu mutane kuwa suna kama da irin da aka shuka a ƙasa mai kyau, sukan ji maganar Allah, su kuma karɓa, sa’an nan kuma su fid da amfani riɓi talatin-talatin, ko sittin-sittin, ko ɗari-ɗari.”›

Markus 6:37-44

Sai ya amsa ya ce, ‹“Ku, ku ba su wani abu su ci.”› Suka ce masa, “Ai, wannan zai ɗauki albashin wata takwas na mutum! Mu je mu kashe yawan kuɗin nan a burodi mu ba su su ci?” Sai ya yi tambaya ya ce, ‹“Burodi nawa kuke da su? Je ku duba.”› Da suka duba, sai suka ce, “Biyar da kifi biyu.” Sa’an nan Yesu ya umarce su su sa dukan mutanen su zazzauna ƙungiya-ƙungiya a kan ɗanyar ciyawa. Haka suka zazzauna a ƙungiyar ɗari-ɗari, da kuma hamsin-hamsin. Ya ɗauki burodi guda biyar da kifin nan biyu, ya ɗaga kai sama, ya yi godiya, ya kakkarya burodin. Sai ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutane. Ya kuma rarraba kifi biyun a tsakaninsu duka. Kowa ya ci, ya ƙoshi, almajiran suka kwashe gutsattsarin burodin da na kifin cike da kwanduna goma sha biyu. Yawan mutanen da suka ci kuwa maza dubu biyar ne.

Markus 7:22-23

‹kwaɗayi, ƙeta, ruɗu, ƙazantaccen sha’awa, kishi, ɓata suna, girman kai da kuma wauta.› ‹Duk waɗannan mugayen abubuwa daga cikin suke fitowa, suna kuma ƙazantar da mutum.”›

Markus 8:35-37

‹Domin duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, da kuma bishara, zai same shi.› ‹Me mutum zai amfana, in ya ribato duniya duka a bakin ransa?› ‹Ko kuma, me mutum zai bayar a musayar ransa?›

Markus 10:21-22

Yesu ya kalle shi da ƙauna ya ce, ‹“Abu ɗaya ka rasa, ka tafi ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo ka bi ni.”› Da jin wannan, sai mutumin ya ɓata fuskarsa, ya tafi da baƙin ciki, gama yana da arziki sosai.

Markus 10:23-27

Yesu ya dudduba, sai ya ce wa almajiransa, ‹“Yana da wuya fa masu arziki su shiga mulkin Allah!”› Almajiransa suka yi mamakin kalmominsa. Amma Yesu ya sāke ce musu, ‹“’Ya’yana, yana da wuya fa a shiga mulkin Allah!› ‹Ya fi sauƙi raƙumi yă shiga ta kafar allura, da mai arziki yă shiga mulkin Allah.”› Almajiran suka yi mamaki ƙwarai, suka ce wa juna, “To, wa zai sami ceto ke nan?” Yesu ya kalle su ya ce, ‹“Ga mutum kam, wannan ba mai yiwuwa ba ne, amma ga Allah, wannan mai yiwuwa ne; dukan abubuwa masu yiwuwa ne ga Allah.”›

Markus 10:28-30

Bitrus ya ce, “Mun bar kome domin mu bi ka!” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Gaskiya nake gaya muku, babu wanda zai bar gida, ko ’yan’uwa maza da mata, ko mahaifiya, ko mahaifi, ko ’ya’ya, ko gonaki saboda ni, da kuma bishara,› ‹sa’an nan yă kāsa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu (na gidaje, da ’yan’uwa mata, da ’yan’uwa maza, da uwaye, da ’ya’ya, da gonaki amma tare da tsanani) a lahira kuma yă sami rai madawwami.›

Markus 11:15-17

Da suka kai Urushalima, sai Yesu ya shiga filin haikalin, ya fara korar waɗanda suke saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur na masu musayar kuɗi, da kujerun masu sayar da tattabaru, ya kuma hana kowa yă ratsa da a filin haikali ɗauke da kayan ciniki. Da yake koya musu, sai ya ce, ‹“Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira gidana, gidan addu’a na dukan al’ummai ba’?›‹Amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’›‹”›

Markus 12:14-17

Suka zo wurinsa suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci. Ba ka bin ra’ayin mutane, don ba ka nuna bambanci. Amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya. Daidai ne a biya wa Kaisar haraji, ko babu? Mu biya ko kada mu biya?” Amma Yesu ya san munafuncinsu, sai ya yi tambaya ya ce, ‹“Don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko? Ku kawo mini dinari in ga.”› Suka kawo masa kuɗin, sai ya tambaye, su ya ce, ‹“Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne wannan?”› Suka ce, “Na Kaisar.” Sai Yesu ya ce musu, ‹“Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku ba wa Allah kuma abin da yake na Allah.”› Suka yi mamakinsa ƙwarai.

Markus 12:41-44

Yesu ya zauna ɗaura da inda ake bayarwa, ya kuma dubi yadda taron suke sa kuɗinsu a cikin ɗakunan ajiya haikali. Masu arziki da yawa suka zuba kuɗaɗe masu yawa. Amma wata matalauciya gwauruwa, ta zo ta saka anini biyu, da suka yi daidai da rabin kobo. Yesu ya kira almajiransa wurinsa ya ce, ‹“Gaskiya nake gaya muku, abin da matalauciya gwauruwan nan ta zuba cikin ɗakunan ajiya nan ya fi na sauran dukan.› ‹Dukansu sun bayar ne daga cikin arzikinsu; ita kuwa, daga cikin talaucinta, ta ba da kome, duk abin da take da shi na rayuwa.”›

Markus 14:3-7

Yayinda yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu, yana cin abinci, sai wata mace ta zo da wani ɗan tulu na turaren alabasta da aka yi da nardi zalla, mai tsadan gaske. Ta fasa tulun, ta kuma zuba turaren a kansa. Waɗansu daga cikin waɗanda suke wurin, suka ji haushi, suka ce wa juna, “Me ya sa za a ɓata turaren nan haka? Da an sayar da shi, ai, da an sami kuɗi fiye da albashi ma’aikaci na shekara guda, a ba wa matalauta. Sai suka tsawata mata da zafi.” Yesu ya ce, ‹“Ku ƙyale ta mana. Don me kuke damunta? Ta yi abu mai kyau a gare ni.› ‹Matalauta dai suna tare da ku kullum, za ku kuma iya taimakonsu a duk lokacin da kuke so. Amma ni ba zan kasance da ku kullum ba.›

Markus 14:11

Suka yi murna da jin haka, suka yi alkawari za su ba shi kuɗi. Don haka, ya fara neman zarafi yă ba da shi.

Luka 3:11

Ya amsa ya ce, “Ya kamata, mutumin da yake da riguna biyu, yă raba da wanda ba shi da riga, mai abinci kuma yă yi haka.”

Luka 3:12-14

Masu karɓar haraji ma suka zo, domin a yi musu baftisma. Suka yi tambaya, suka ce “Malam, me ya kamata mu yi?” Ya ce musu, “Kada ku karɓa fiye da abin da aka ce a karɓa.” Sai waɗansu sojoji suka tambaye shi, “Mu fa? Me ya kamata mu yi?” Sai ya amsa ya ce, “Kada ku ƙwace kuɗin mutane, kada kuma ku yi shaidar ƙarya. Ku yi haƙuri da abin da ake biyanku.”

Luka 6:20-21

Da ya dubi almajiransa, sai ya ce, ‹“Masu albarka ne ku da kuke matalauta,› ‹gama mulkin Allah naku ne.› ‹Masu albarka ne ku da kuke jin yunwa yanzu,› ‹gama za ku ƙoshi.› ‹Masu albarka ne ku da kuke kuka yanzu,› ‹gama za ku yi dariya.›

Luka 6:24-25

‹“Amma kaitonku da kuke da arziki,› ‹gama kun riga kun sami ta’aziyyarku.› ‹Kaitonku da kuke ƙosassu yanzu,› ‹gama za ku zauna da yunwa.› ‹Kaitonku da kuke dariya yanzu,› ‹gama za ku yi makoki da kuka.›

Luka 6:29-30

‹In wani ya mare ka a wannan kumatu, juya masa ɗayan ma, in wani ya ƙwace maka babban riga, kada ma ka hana masa ’yar cikin ma.› ‹Duk wanda ya roƙe ka abu, ka ba shi. In kuma wani ya yi maka ƙwace, kada ka nema yă mayar maka.›

Luka 6:32-33

‹“In kana ƙaunar masu ƙaunarka ne kawai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma suna ƙaunar waɗanda suke ƙaunarsu.› ‹In kuma kana yin alheri ga masu yi maka ne kaɗai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma suna yin haka.›

Luka 6:34-35

‹In kana ba da bashi ga mutanen da za su iya biyan ka ne kawai, ina ribar wannan? Ko masu zunubi ma, suna ba da bashi ga masu zunubi, da fata za a biya su tsab.› ‹Amma, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku kuma yi musu alheri, ku ba su bashi, ba da sa zuciya sai an biya ku ba. Ta yin haka ne kawai, za ku sami lada mai yawa, ku kuma zama ’ya’yan Mafi Ɗaukaka, gama shi mai alheri ne ga marasa godiya da mugaye.›

Luka 6:38

‹Ku bayar, ku ma sai a ba ku mudu a cike, a danƙare, har yă yi tozo, yana zuba, za a juye muku a hannun riga. Mudun da kuka auna da shi, da shi za a auna muku.”›

Luka 10:30

Yesu ya amsa ya ce, ‹“Wani mutum ya tashi daga Urushalima za shi Yeriko, sai ya fāɗi a hannun mafasa, wato, ’yan fashi. Suka ƙwace tufafinsa, suka yi masa dūka, suka bar shi nan bakin rai da mutuwa.›

Luka 10:35

‹Kashegari, sai ya ɗauki dinari biyu, ya ba wa mai masauƙin ya ce, ‘Ka lura da shi, bayan na dawo, zan biya ka duk abin da ka ƙara kashewa a kansa.’›

Luka 11:3

‹Ka ba mu kowace rana abincin yini.›

Luka 11:13

‹In fa haka ne, ko da yake ku mugaye ne, kun san ba ’ya’yanku kyautai masu kyau, balle fa Ubanku na sama, zai yi fiye da haka, ta wurin ba da Ruhu Mai Tsarki, ga masu roƙonsa!”›

Luka 11:41-42

‹Ku ba matalauta abin da yake cikin kwano, kuma kome zai zama muku da tsabta.› ‹“Kaitonku, Farisiyawa, domin kuna ba wa Allah zakka na na’ana’arku, da ƙarƙashinku, da kuma sauran ganyen lambunku iri-iri, amma kun ƙyale adalci da ƙaunar Allah. Ya kamata da kun kiyaye na ƙarshen, ban ba barin na farkon.›

Luka 12:13-15

Sai wani mutum daga cikin taron ya ce masa, “Malam, ka ce wa ɗan’uwana ya raba gādon da ni.” Yesu ya amsa masa ya ce, ‹“Kai, wa ya naɗa ni alƙali, ko mai sulhu a tsakaninku?”› Sai ya ce musu, ‹“Ku lura fa! Ku tsare kanku daga dukan kowane irin kwaɗayi. Ran mutum ba ya danganta a kan yawan dukiyarsa ba.”›

Luka 12:16-21

Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, ‹“Gonar wani mai arziki ta ba da amfani sosai.› ‹Ya yi tunani a ransa ya ce, ‘Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonana. Me zan yi ke nan?’› ‹“Sai ya ce, ‘Ga abin da zan yi. Zan rushe rumbunana, in gina manya, in zuba dukan hatsina da kayana a ciki.› ‹Ni kuma zan ce wa raina, “Kana da kaya da yawa masu kyau, da aka yi ajiyarsu domin shekaru da dama masu zuwa. Yi hutunka, ka ci, ka sha, ka yi annashuwa.” ’› ‹“Amma Allah ya ce masa, ‘Kai wawa! A wannan dare za a nemi ranka. Bayan haka, wa zai gāji abin da ka tara wa kanka?’› ‹“Haka zai zama ga duk wanda ya tara wa kansa dukiya, amma ba shi da arziki a gaban Allah.”›

Luka 12:22-31

Sai Yesu ya ce wa almajiransa, ‹“Saboda haka, ina faɗa muku, kada ku damu game da rayuwarku, abin da za ku ci, ko kuma game da jikinku, abin da za ku yafa.› ‹Rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi.› ‹Ku dubi hankaki. Ba sa shuki ko girbi, kuma ba su da ɗakin ajiya ko rumbu ba, duk da haka, duk da haka, Allah na ciyar da su. Darajarku ta fi na tsuntsaye sau da yawa!› ‹Wane ne a cikinku ta wurin damuwarsa, zai iya ƙara ko sa’a ɗaya ga rayuwarsa?› ‹Tun da ba za ku iya yin wannan ƙanƙanin abu ba, me ya sa kuke damuwa a kan sauran?› ‹“Ku dubi yadda furanni suke girma. Ba sukan yi aiki, ko saƙa ba, duk da haka, ina faɗa muku cewa, ko Solomon cikin kyakkyawan darajarsa duka, bai yafa kayan ado da ya kai kamar na ko ɗaya a cikinsu ba.› ‹In haka ne Allah yake yi wa ciyayin jeji sutura, wadda yau suna nan, sa’an nan gobe kuma a jefa cikin wuta, Allah ba zai yi muku sutura fiye da ciyayin jeji ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya!› ‹Kada ku sa zuciyarku a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada ku damu a kan su.› ‹Gama duniya da ba tă san Allah ba, tana faman neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa, ya san kuna bukatarsu.› ‹Amma ku nemi mulkinsa, za a kuwa ƙara muku waɗannan abubuwa.›

Luka 12:33

‹Ku sayar da dukiyarku, ku ba wa matalauta. Ku yi wa kanku jakar kuɗin da ba za su lalace ba. Ku yi wa kanku ajiyar dukiyar da ba za tă kare ba a sama, inda ɓarawo ba zai yi kusa ba, asu kuma ba za su iya su lalatar ba.›

Luka 12:34

‹Gama inda dukiyarku take, nan ne zuciyarku ma take.›

Luka 14:12-14

Sai Yesu ya ce wa wanda ya gayyace shi, ‹“Lokacin da ka shirya biki ko liyafa, kada ka gayyaci abokanka, ko ’yan’uwanka, ko danginka, ko kuma maƙwabtanka masu arziki, gama in ka yi haka, suna iya gayyatarka, su biya maka alherin da ka yi musu.› ‹Amma lokacin da ka kira biki, ka gayyaci matalauta, da guragu, da shanyayyu, da makafi.› ‹Ta haka, za ka sami albarka. Ko da yake ba za su iya biyan ka ba, za a biya ka a ranar tashin masu adalci daga matattu.”›

Luka 14:33

‹Haka nan fa, kowane ne a cikinku, da ba ya rabu da abin da yake da shi ba, ba zai iya zama almajirina ba.›

Luka 15:8-10

‹“Ko kuwa in wata mace tana da kuɗi na azurfa guda goma, sa’an nan ɗaya ya ɓata, ashe, ba za tă ƙuna fitila, ta share gidan, ta nema a hankali, har sai ta samu ba?› ‹In ta same shi, sai ta kira ƙawayenta da maƙwabtanta wuri ɗaya, ta ce musu, ‘Ku taya ni murna, na sami kuɗina da ya ɓata.’› ‹Haka, ina gaya muku, akwai murna a gaban mala’ikun Allah a kan mai zunubi guda ɗaya, da ya tuba.”›

Luka 15:11-24

Yesu ya ci gaba da cewa, ‹“Akwai wani mutum wanda yake da ’ya’ya biyu maza.› ‹Ƙaramin ya ce wa mahaifinsu, ‘Baba, ba ni rabon gādona.’ Sai mahaifin ya raba musu dukiyarsa.› ‹“Bayan ’yan kwanaki, sai ƙaramin ɗan ya tattara kayansa duk, ya tashi ya tafi wata ƙasa mai nisa. A can, ya ɓatar da dukiyarsa duka a rayuwar banza.› ‹Bayan ya ɓatar da kome, sai ga muguwar yunwa a dukan ƙasar, har ya shiga rashi.› ‹Sai ya je ya sami aiki a wurin wani mutumin ƙasar, wanda ya aike shi a gonakinsa, ya yi kiwon aladu.› ‹Ya yi marmarin cin dusan da aladun suke ci, amma ba wanda ya ba shi wani abu.› ‹“Da hankalinsa ya dawo, sai ya ce, ‘Kai, bayin mahaifina guda nawa ne, da suke da abinci fiye da isashe, ni kuma ina nan, zan mutu don yunwa!› ‹Zan tashi in koma wurin mahaifina, in ce masa, “Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi.› ‹Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba. Ka mai da ni kamar ɗaya daga cikin bayinka.” ’› ‹Sai ya tashi ya kama hanya ya koma wurin mahaifinsa.› ‹“Amma tun yana nesa, mahaifinsa ya hange shi. Tausayi kuma ya kama shi, sai ya tashi ya ruga da gudu wurinsa, ya rungume shi, ya yi masa sumba.› ‹“Sai ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba.’› ‹“Amma mahaifin ya ce wa bayinsa, ‘Maza! Ku kawo riga mafi kyau ku sa masa. Ku sa zobe a yatsarsa, da takalma kuma a ƙafafunsa.› ‹Ku kawo ɗan saniya mai ƙiba ku yanka. Bari mu yi biki mu yi shagali.› ‹Gama ɗan nan nawa, da ya mutu, amma yanzu yana da rai kuma. Da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ Sai suka fara shagali.›

Luka 16:1-9

Yesu ya ce wa almajiransa, ‹“An yi wani mai arziki wanda aka yi wa manajansa zargin yin banza da dukiyarsa.› ‹Sai ya kira manajan, ya tambaye shi, ‘Me nake ji haka a kanka? Ka kawo lissafin aikinka, domin ba za ka iya cin gaba da aikinka ba.’› ‹“Sai manajan ya ce cikin tunaninsa, ‘Maigidana zai kore ni daga aiki, me zan yi? Ba ni da ƙarfin noma, kuma ina jin kunyan yin bara.› ‹Na san abin da zan yi, don mutane su karɓe ni a gidajensu, bayan an kore ni daga aiki a nan.’› ‹“Sai ya kira kowane ɗaya da maigidansa yake bin bashi. Ya tambayi na farkon ya ce, ‘Nawa ne maigidana yake bin ka?’› ‹“Ya amsa ya ce, ‘Garwar mai na zaitun guda ɗari tara.’› ‹“Manajan ya ce, ‘Ga takardarka, ka zauna maza ka mai da shi ɗari huɗu.’› ‹“Ya kuma tambayi na biyun, ‘Kai fa, nawa ne ake bin ka?’› ‹“Sai ya amsa ya ce, ‘Buhunan alkama dubu.’› ‹“Ya ce, ‘Ga takardarka, ka mai da shi ɗari takwas.’› ‹“Maigidan kuwa ya yabi manajan nan marar gaskiya saboda wayonsa. Gama ’yan duniyan nan suna da wayon yin hulɗa da junansu fiye da ’yan haske.› ‹Ina gaya muku, ku yi amfani da dukiya na wannan duniya, domin ku sami wa kanku abokai. Saboda bayan dukiyar ta ƙare, za a karɓe ku a wuraren zama da sun dawwama.›

Luka 16:10-12

‹“Duk wanda ana amincewa da shi cikin ƙaramin abu, ana kuma amincewa da shi cikin babba. Kuma duk marar gaskiya cikin ƙaramin abu, zai zama marar gaskiya cikin babba.› ‹In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiya ta wannan duniya ba, wa zai amince muku da dukiya ta gaskiya?› ‹In fa ku ba amintattu ne cikin tafiyar da dukiyar wani ba, wa zai ba ku dukiya naku, na kanku?›

Luka 16:13-14

‹“Babu wani bawa mai iya bauta wa iyayengiji biyu ba. Ko dai ya ƙi ɗaya, ya so ɗayan, ko kuwa ya dāge ga yi wa ɗaya bauta, sa’an nan ya rena ɗayan. Ba za ku iya ku bauta wa Allah tare da bauta wa Mammon (wato, Kuɗi) a lokaci ɗaya ba.”› Da Farisiyawa masu son kuɗi suka ji wannan duka, sai suka yi wa Yesu tsaki.

Luka 16:19-31

‹“An yi wani mutum mai arziki wanda yakan sa tufafi masu ruwan shunayya, da kuma na lallausan lilin, yana kuma cikin rayuwar jin daɗi kullum.› ‹A ƙofar gidansa kuma akan ajiye wani mai bara, mai suna Lazarus, wanda jikinsa duk gyambuna ne.› ‹Shi kuwa yakan yi marmarin cin abin da yakan fāɗi daga tebur na mai arzikin nan. Har karnuka ma sukan zo su lashe gyambunansa.› ‹“Ana nan, sai mai baran ya mutu, kuma mala’iku suka ɗauke shi zuwa gefen Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi.› ‹A cikin jahannama ta wuta, inda yana shan azaba, ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim can nesa, da kuma Lazarus a gefensa.› ‹Sai ya yi masa kira ya ce, ‘Baba, Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiki Lazarus ya sa ɗan yatsarsa a ruwa, ya ɗiga mini a harshe saboda in ji sanyi, domin ina shan azaba cikin wannan wuta.’› ‹“Amma Ibrahim ya ce, ‘Ka tuna fa ɗana, a lokacin da kake duniya, ka sami abubuwa masu kyau naka, Lazarus kuwa ya sami munanan abubuwa. Amma yanzu ya sami ta’aziyya a nan, kai kuwa kana shan azaba.› ‹Ban da wannan duka ma, tsakaninmu da kai, akwai wani babban rami da aka yi, yadda waɗanda suke son ƙetarewa daga nan zuwa wurinku, ba za su iya ba, kuma ba mai iya ƙetarewa daga wurinku zuwa wurinmu.’› ‹“Ya amsa ya ce, ‘To, ina roƙonka, ya uba, ka aiki Lazarus zuwa gidan mahaifina,› ‹gama ina da ’yan’uwana biyar maza. Bari yă ba su gargaɗi, don kada su ma su zo wurin nan mai azaba.’› ‹“Ibrahim ya amsa ya ce, ‘Suna da Musa da Annabawa, ai, sai su saurare su.’› ‹“Sai ya ce, ‘A’a, ya uba, Ibrahim, in dai wani ya tashi daga matattu ya je wurinsu, za su tuba.’› ‹“Amma ya ce masa, ‘In ba su saurari Musa da Annabawa ba, kai, ko da wani ya tashi daga matattu ma, ba za su saurare shi ba.’ ”›

Luka 17:33

‹Duk wanda yake so ya ceci ransa, zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa, zai cece shi.›

Luka 18:12

‹Ina azumi sau biyu a mako, ina ba da zakka daga kowane abin da na samu.’›

Luka 18:22-23

Da Yesu ya ji haka, sai ya ce masa, ‹“Akwai abu ɗaya har yanzu da ya rage maka. Ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, sa’an nan za ka sami dukiya a sama. Bayan haka, ka zo ka bi ni.”› Da jin haka, sai ya ɓata rai, domin shi mai arziki ne sosai.

Luka 18:24-27

Yesu ya kalle shi ya ce, ‹“Yana da wuya fa, masu arziki su shiga mulkin Allah!› ‹Tabbatacce, zai fi sauƙi raƙumi ya shiga ta kafar allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.”› Waɗanda suka ji wannan suka yi tambaya suka ce, “To, wa zai iya samun ceto?” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Abin da ba ya yiwuwa ga mutane, mai yiwuwa ne ga Allah.”›

Luka 18:28-30

Sai Bitrus ya ce, masa, “To, ga shi mun bar kome da muke da shi, don mu bi ka!” Yesu ya ce musu, ‹“Gaskiya nake gaya muku, ba wanda ya bar gida, ko mata, ko ’yan’uwa maza, ko iyaye, ko yara, saboda mulkin Allah,› ‹da zai kāsa samun riɓi mai yawa, a wannan zamani, ya kuma sami rai madawwami a zamani mai zuwa.”›

Luka 19:8

Amma Zakka ya tashi a tsaye, ya ce wa Ubangiji, “Duba, Ubangiji! Nan take, rabin dukiyar da nake da shi, na ba wa matalauta. In kuma na taɓa cutan wani, a kan wani abu, zan mayar da shi ninki huɗu.”

Luka 19:12-26

Ya ce, ‹“Wani mutum mai martaba ya tafi wata ƙasa mai nisa don a naɗa shi sarki sa’an nan ya dawo.› ‹Saboda haka ya kira bayinsa goma ya ba su mina goma. Ya ce, ‘Ku yi kasuwanci da kuɗin nan, sai na dawo.’› ‹“Amma talakawansa suka ƙi shi, sai suka aikar da wakilai bayansa, domin su ce, ‘Ba mu son wannan mutum ya zama sarkinmu.’› ‹“Duk da haka, aka naɗa shi sarki, sa’an nan ya dawo gida. Sai ya aika aka kira bayin da ya ba su kuɗin, don yă san ribar da suka samu.› ‹“Na fari ya zo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, minarka ya sami ribar goma.’› ‹“Maigidan ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawana mai kirki! Tun da ka yi aminci a kan abu ƙanƙani, ka yi riƙon birane goma.’› ‹“Na biyun ya zo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, minarka ya sami ribar biyar.’› ‹“Maigidansa ya ce, ‘Kai ka yi riƙon birane biyar.’› ‹“Sai wani bawan ya zo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, ga minarka. Na ɓoye shi a wani ɗan tsumma.› ‹Na ji tsoronka, don kai mai wuyan sha’ani ne. Kakan ɗauki abin da ba ka ajiye ba, kakan kuma yi girbin abin da ba ka shuka ba.’› ‹“Sai maigidansa, ya amsa ya ce, ‘Zan hukunta ka a kan kalmominka, kai mugun bawa! Ashe, ka san cewa ni mai wuyan sha’ani ne, nakan ɗauka abin da ban ajiye ba, ina kuma girbin abin da ban shuka ba?› ‹Don me ba ka sa kuɗina a wajen ajiya, don in na dawo, in sami riba a kai ba?’› ‹“Sai ya ce wa waɗanda suke tsaye a wajen, ‘Ku karɓi minarsa ku ba wa wanda yake da mina goma.’› ‹“Suka ce, ‘Ranka yă daɗe, ai, yana da guda goma ko!’› ‹“Ya amsa ya ce, ‘Ina gaya muku, duk wanda yake da abu, za a ƙara masa. Amma wanda ba shi da shi kuwa, ko abin da yake da shi ma, za a karɓe.›

Luka 19:45-46

Sai ya shiga filin haikali, ya fara korar masu sayar da kaya. Ya ce musu, ‹“A rubuce, yake cewa, ‘Gidana, zai zama gidan addu’a,’›‹amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ”›

Luka 20:22-25

Daidai ne mu biya haraji ga Kaisar, ko babu?” Ya gane makircinsu, sai ya ce musu, ‹“Nuna mini dinari. Hoton wane ne, kuma rubutun wane ne a kai?”› Suka amsa, “Na Kaisar.” Sai ya ce musu, ‹“Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”›

Luka 21:1-4

Da Yesu ya ɗaga ido, sai ya ga waɗansu masu arziki suna sa baikonsu a ma’ajin haikalin. Ya kuma ga wata gwauruwa matalauciya, ta saka anini biyu. Sai ya ce, ‹“Gaskiya ina faɗa muku, wacce nan gwauruwa matalauciya ta sa fiye da dukan sauran.› ‹Dukan mutanen nan sun ba da baikonsu daga cikin arzikinsu ne, amma ita daga cikin talaucinta, ta saka duk abin da take da shi na rayuwa.”›

Yohanna 2:14-17

A filin haikali ya sami mutane suna sayar da shanu, tumaki da tattabaru, waɗansu kuma zaune a tebur suna canjin kuɗi. Saboda haka ya tuƙa bulala ta igiyoyi, ya kori duka daga filin haikali, har da tumaki da shanu; ya watsar da kuɗin masu canjin, ya birkice teburansu. Ga masu sayar da tattabaru kuwa ya ce, ‹“Ku kwashe waɗannan daga nan! Don me za ku mai da gidan Ubana kasuwa!”› Sai almajiransa suka tuna cewa a rubuce yake, “Himma saboda gidanka zai cinye ni.”

Yohanna 6:27

‹Kada ku yi aiki saboda abincin da yake lalacewa, sai dai saboda abinci mai dawwama har yă zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. A kansa ne Allah Uba ya sa hatimin amincewarsa.”›

Yohanna 6:35

Sa’an nan Yesu ya furta cewa, ‹“Ni ne burodin rai. Wanda ya zo wurina ba zai taɓa jin yunwa ba, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai taɓa jin ƙishirwa ba.›

Yohanna 10:10-11

‹Ɓarawo yakan zo don yă yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace.› ‹“Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yakan ba da ransa domin tumakin.›

Yohanna 12:4-8

Amma ɗaya daga cikin almajiransa, Yahuda Iskariyot, wanda daga baya zai bashe shi, bai amince ba ya ce, “Don me ba a sayar da turaren nan aka kuma ba da kuɗin ga matalauta ba? Ai, kuɗin ya kai albashin shekara guda.” Ya yi wannan magana ba don ya kula da matalauta ba ne, sai dai don shi ɓarawo ne. Da yake shi ne mai ajiya jakar kuɗin, yakan taimaki kansa da abin da aka sa a ciki. Yesu ya ce, ‹“Ku ƙyale ta, an nufa ta ajiye wannan turaren don ranar jana’izata.› ‹Kullum za ku kasance da matalauta, amma ba kullum za ku kasance tare da ni ba.”›

Yohanna 16:23-24

‹A ranan nan, ba za ku sāke tambaya ta kome ba. Gaskiya nake gaya muku, Ubana zai ba ku kome da kuka roƙa cikin sunana.› ‹Har yanzu dai ba ku roƙi kome cikin sunana ba. Ku roƙa za ku kuwa samu, farin cikinku kuwa zai zama cikakke.›

Ayyukan Manzanni 2:44-46

Dukan masu bi suna tare, suna kuma mallakar kome tare. Suka dinga sayar da ƙaddarorinsu da kayayyakinsu, suka ba wa kowa gwargwadon bukatarsa. Kowace rana suka ci gaba da taruwa a filin haikali. Suka gutsuttsura burodi a gidajensu suna cin abinci tare da farin ciki da zuciya ɗaya,

Ayyukan Manzanni 3:6

Sai Bitrus ya ce, “Azurfa ko zinariya ba ni da su, amma abin da nake da shi, shi zan ba ka. A cikin sunan Yesu Kiristi Banazare, ka yi tafiya.”

Ayyukan Manzanni 4:32-35

Dukan masu bi kuwa zuciyarsu ɗaya ne, nufinsu kuwa ɗaya. Babu wani da ya ce abin da ya mallaka nasa ne, amma sun raba kome da suke da shi. Da iko mai ƙarfi manzanni suka ci gaba da shaidar tashin matattu na Ubangiji Yesu, alheri mai yawa kuwa yana bisansu duka. Babu mabukata a cikinsu. Lokaci-lokaci waɗanda suke da gonaki ko gidaje sukan sayar da su, su kawo kuɗi daga abin da suka sayar, su ajiye a sawun manzannin, a kuma raba wa kowa gwargwadon bukatarsa.

Ayyukan Manzanni 4:36-37

Yusuf, wani Balawe daga Saifurus, wanda manzanni suke kira Barnabas (wanda yake nufin Ɗan Ƙarfafawa) ya sayar da wata gonar da ya mallaki ya kuma kawo kuɗin ya ajiye a sawun manzanni.

Ayyukan Manzanni 5:1-4

To wani mutum mai suna Ananiyas tare da matarsa Saffiratu, shi ma ya sayar da wata mallakarsa. Da cikakken sanin matarsa ya ajiye sashi daga cikin kuɗin don kansa, ya kuma kawo sauran ya ajiye a sawun manzanni. Sai Bitrus ya ce, “Ananiyas, ta yaya Shaiɗan ya cika zuciyarka haka da ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya ka kuma ajiye wa kanka sauran kuɗin da ka karɓa na filin? Ba naka ba ne kafin ka sayar da shi? Bayan da ka sayar da shi kuma, kuɗin ba naka ba ne? Me ya sa ka yi tunanin yin irin wannan abu? Ba mutum ne ka yi wa ƙarya ba, Allah ne ka yi masa.”

Ayyukan Manzanni 8:18-20

Sa’ad da Siman ya ga cewa ana ba da Ruhu ta wurin ɗibiya hannuwan manzannin, sai ya miƙa musu kuɗi, ya ce, “Ni ma ku ba ni wannan iyawa don kowa na ɗibiya wa hannuwana yă karɓi Ruhu Mai Tsarki.” Bitrus ya amsa ya ce, “Bari kuɗinka ya hallaka tare da kai, domin ka yi tsammani za ka iya saya kyautar Allah da kuɗi!

Ayyukan Manzanni 11:29

Kowanne a cikin almajiran, gwargwadon azancinsa, ya yanke shawara ya ba da gudummawa ga ’yan’uwan da suke zama a Yahudiya.

Ayyukan Manzanni 20:33-35

Ban yi ƙyashin azurfa ko zinariya ko tufafin kowa ba. Ku kanku kun san cewa hannuwan nan nawa sun biya mini bukatuna da kuma na abokan aikina. Cikin kowane abin da na yi, na nuna muku cewa da irin wannan aiki tuƙuru don mu taimaki marasa ƙarfi, muna tunawa da kalmomin da Ubangiji Yesu kansa ya ce, ‹‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’› ”

Romawa 2:21

to, kai mai koya wa waɗansu, ba kanka kake koya wa ba? Kai da kake wa’azi kada a yi sata, kana sata?

Romawa 12:20

A maimakon haka, “In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ciyar da shi; in yana jin ƙishirwa, ka ba shi ruwan sha. Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta a kansa.”

Romawa 13:6-9

Shi ne ma ya sa kuke biyan haraji, gama hukumomin nan bayin Allah ne, waɗanda suke ba da dukan lokacinsu don aikin shugabanci. Ku ba wa kowa hakkinsa. In kuna da bashin haraji, sai ku biya; in kuɗin shiga ne, ku biya kuɗin shiga; in ladabi ne, ku yi ladabi; in kuma girmamawa ne, ku ba da girma. Kada hakkin kowa yă zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan. Umarnan nan, “Kada ka yi zina.” “Kada ka yi kisankai.” “Kada ka yi sata.” “Kada kuma ka yi ƙyashi.” Da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”

1 Korintiyawa 6:9-10

Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko ’yan daudu, ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah.

1 Korintiyawa 13:3

In na ba wa matalauta dukan abin da nake da shi, na kuma miƙa jikina a ƙone, amma ba ni da ƙauna, ban yi riban kome ba.

1 Korintiyawa 16:1-2

To, game da tara kuɗi domin taimakon mutanen Allah, ku yi abin da na gaya wa ikkilisiyoyin Galatiyawa. A ranar farko ta kowace mako, ya kamata kowannenku yă keɓe ’yan kuɗi bisa ga abin da yake samu, yă ajiye, ba sai na zo kafin a tara taimakon ba.

2 Korintiyawa 4:7

Amma muna da wannan dukiya a cikin tulunan yumɓu, don a nuna wannan mafificin ikon nan daga Allah ne, ba daga gare mu ba.

2 Korintiyawa 4:18

Domin ba abubuwan da ido yake gani ne muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa. Gama abubuwan da ake gani masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne.

2 Korintiyawa 5:1

Yanzu mun san cewa in an hallaka tentin duniyan nan da muke ciki, muna da wani gini daga Allah, madawwamin gida a sama, wanda ba da hannuwan mutum ne suka gina shi ba.

2 Korintiyawa 8:3-5

Gama ina shaida cewa sun bayar daidai gwargwadon iyawarsu, har ma fiye da ƙarfinsu. Su kansu, sun roƙe mu sosai don su sami damar yin bayarwa a wannan hidima ga tsarkaka. Ba su yi yadda muka za tă ba, sai ma suka fara ba da kansu ga Ubangiji, sa’an nan sai suka ba da kansu gare mu bisa ga nufin Allah.

2 Korintiyawa 8:9

Gama kun san alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi cewa ko da yake shi mawadaci ne, duk da haka, ya zama matalauci saboda ku, domin ta wurin talaucinsa, ku zama mawadata.

2 Korintiyawa 8:12-15

Gama in da niyyar bayarwa, za a karɓi bayarwa bisa ga abin da mutum yake da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba. Ba nufi nake yi a sawwaƙe wa waɗansu, ku kuwa a jibga muku nauyin ba. Amma ya yi kyau dai a raba daidai wa daida, sai ku taimake su a yanzu da yalwarku saboda rashinsu. Wata rana su ma su taimake ku da yalwarsu saboda rashinku, don a daidaita al’amari, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Wanda ya tara da yawa, bai tara fiye da bukatarsa ba, wanda kuma ya tara kaɗan, bai kāsa masa ba.”

2 Korintiyawa 9:5

Saboda haka, na ga ya dace in roƙi ’yan’uwan nan su ziyarce ku kafin lokacin, su kuma gama shirye-shirye saboda bayarwa ta yardar ran da kuka yi alkawari. Ta haka bayarwar za tă zama a shirye, ta yardar rai ba ta dole ba.

2 Korintiyawa 9:6-9

Ku tuna fa, duk wanda ya yi shuki kaɗan zai girbe kaɗan, kuma duk wanda ya yi shuki da yawa, zai girbe a yalwace. Ya kamata kowa yă bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba, gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai. Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ya ba gajiyayyu hannu sake, ayyukansa na alheri madawwama ne.”

2 Korintiyawa 9:10-13

To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, yă riɓanya shi, yă kuma albarkaci ayyukanku na alheri da yawa. Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za tă zama sanadin godiya ga Allah. Wannan hidimar da kuke yi, ba bukatun mutanen Allah kaɗai take biya ba, amma tana cike da hanyoyin nuna godiya masu yawa ga Allah. Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi na’am da bisharar Kiristi, saboda kuma gudummawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake.

Galatiyawa 2:10

Abin da dai suka roƙa shi ne ya kamata mu riƙa tuna da matalauta, abin nan da nake marmarin yi.

Galatiyawa 5:14

Dukan doka an taƙaita a cikin umarni ɗaya ne cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”

Galatiyawa 6:7-10

Kada a ruɗe ku. Ba a yi wa Allah ba’a. Mutum yakan girbe abin da ya shuka ne. Wanda ya yi shuki don yă gamshi mutuntakarsa, daga wannan mutuntaka zai girbi hallaka. Wanda ya yi shuki domin yă gamshi Ruhu, daga Ruhu zai girbi rai madawwami. Kada mu gaji da yin nagarta, gama a daidai lokaci za mu girbe amfani, in ba mu fid da zuciya ba. Saboda haka, in da hali, bari mu aikata nagarta ga dukan mutane, musamman ga waɗanda suke na iyalin masu bi.

Afisawa 3:8

Ko da yake ni ba kome ba ne a cikin dukan mutanen Ubangiji, aka ba ni wannan baiwa mai daraja don in faɗa wa Al’ummai cewa saboda Kiristi akwai albarkun da suka wuce gaban misali.

Afisawa 4:28

Duk wanda yake sata, sai yă daina sata, dole kuma yă yi aiki, yă yi wani abu mai amfani da hannuwansa, don yă sami abin da zai iya raba da masu bukata.

Filibbiyawa 2:4

Bai kamata kowannenku yă kula da sha’anin kansa kawai ba, sai dai yă kula da sha’anin waɗansu ma.

Filibbiyawa 3:7-8

Amma abin da dā ya zama mini riba yanzu, na ɗauka hasara ce saboda Kiristi. Me kuma ya fi, na ɗauki dukan abubuwa hasara ne in aka kwatanta da mafificiyar girman sanin Kiristi Yesu Ubangijina, wanda saboda shi ne na yi hasarar kome. Na mai da su kayan wofi, domin in sami Kiristi

Filibbiyawa 4:11-19

Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali. Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara. Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi. Duk da haka kun kyauta da kuka yi tarayya da ni cikin wahalolina. Ban da haka, kamar yadda ku Filibbiyawa kuka sani, a farkon kwanakin da kuka ji bishara, sa’ad da na tashi daga Makidoniya, babu wata ikkilisiyar da tă yi tarayya da ni a fannin bayarwa da karɓa, sai ku kaɗai; gama ko sa’ad da nake a Tessalonika ma, kun aiko mini da taimako sau da sau sa’ad da nake cikin bukata. Ba cewa ina neman kyauta ba ne, sai dai ina neman abin da za a ƙara a kan ribarku. An biya ni duka, biyan da ya wuce misali. Bukatata ta biya, da yake na karɓi kyautarku da kuka aiko ta hannun Afaforiditus. Baiwa mai ƙanshi, hadaya abar karɓa, mai faranta wa Allah rai. Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.

Kolossiyawa 3:2

Ku sa hankulanku a kan abubuwan sama, ba kan abubuwan duniya ba.

1 Tessalonikawa 5:16-18

Ku riƙa farin ciki kullum; ku ci gaba da yin addu’a; ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.

2 Tessalonikawa 3:10

Ko ma a sa’ad da muke tare da ku, mun ba ku wannan umarni cewa, “In mutum ya ƙi yin aiki, kada a ba shi abinci.”

1 Timoti 2:9

Ina kuma so mata su lura su yi wa kansu adon da ya cancanta, da rigunan da suka dace, ba da adon kitso ko sa kayan zinariya ko lu’ulu’u ko kuma tufafi masu tsada ba,

1 Timoti 5:8

In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.

1 Timoti 6:6-10

Amma bin Allah da gamsuwa riba ce mai yawa. Gama ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu fita daga cikinta da kome ba. In dai muna da abinci da sutura, ai, sai mu gamsu da su. Mutanen da suke son yin arziki sukan fāɗi cikin jarraba, su fāɗa a tarko, suna mugayen sha’awace-sha’awace iri-iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka. Gama son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Waɗansu mutane, don tsananin son kuɗi, sun bauɗe daga bangaskiya suka kuma jawo wa kansu da baƙin ciki iri-iri.

1 Timoti 6:17

Ka umarci waɗanda suke da arziki a wannan duniya kada su ɗaga kai ko su sa begensu a kan dukiyar da ba ta da tabbaci, sai dai su sa begensu ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don jin daɗinmu.

2 Timoti 3:2

Mutane za su zama masu son kansu, masu son kuɗi, masu taƙama, masu girman kai, masu zage-zage, marasa biyayya ga iyayensu, marasa godiya, marasa tsarki,

Titus 1:7

Da yake an danƙa wa mai kula da ikkilisiya riƙon amana saboda Allah, dole yă zama marar aibi ba mai girman kai ba, ba mai saurin fushi ba, ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba, ba kuma mai son ƙazamar riba ba.

Ibraniyawa 7:1-10

Wannan Melkizedek sarkin Salem ne da kuma firist na Allah Mafi Ɗaukaka. Shi ne ya sadu da Ibrahim ya albarkace shi sa’ad da Ibrahim ya dawowa daga cin nasara a bisa sarakuna, Ibrahim kuwa ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na kome. Ma’anar sunan Melkizedek ita ce, “sarkin adalci.” Amma da yake Salem yana nufin “salama,” shi kuma “Sarkin salama” ne. Ba shi da mahaifi ko mahaifiya, ba shi da asali, ba shi da farko ko ƙarshe, shi dai kamar Ɗan Allah ne kuma firist ne har abada. Ku dubi irin girman da Melkizedek mana. Ko kakanmu Ibrahim ma ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na ganima! Yanzu doka ta umarci zuriyar Lawi waɗanda suka zama firistoci su karɓi kashi ɗaya bisa goma daga wurin mutane, wato, ’yan’uwansu, ko da yake ’yan’uwansu zuriyar Ibrahim ne. Ko da yake Melkizedek ba daga zuriyar Lawi ba ne, duk da haka Ibrahim ya ba shi kashi ɗaya bisa goma na abin da yake da shi, Melkizedek kuwa ya sa masa albarka, shi da aka yi wa alkawura. Kowa ya sani cewa na gaba shi yake sa wa na baya albarka. Firistoci ake ba wa kashi ɗaya bisa goma na abin da mutane suke samu. Amma dukan firistoci sukan mutu, sai dai Melkizedek, kuma nassi ya ce yana da rai. Ana ma iya cewa zuriyar Lawi, mai karɓar kashi ɗaya bisa goma daga mutane, ya ba da kashi ɗaya bisa goma ta wurin Ibrahim, wannan ya kasance haka domin an haifi Lawi daga baya a iyalin Ibrahim wanda ya ba wa Melkizedek kashi ɗaya bisa goma.

Ibraniyawa 11:24-26

Ta wurin bangaskiya ne Musa, sa’ad da ya yi girma, ya ƙi a kira shi ɗan diyar Fir’auna. Ya zaɓa yă sha wahala tare da mutanen Allah, maimakon yă ji daɗin sha’awace-sha’awacen zunubi na ɗan lokaci. Ya ɗauki wulaƙancin da yake sha saboda Kiristi ya fi dukiyar Masar daraja, domin ya sa ido ga ladansa.

Ibraniyawa 13:5

Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce, “Ba zan taɓa bar ka ba; ba zan taɓa yashe ka ba.”

Ibraniyawa 13:16

Kada kuma ku manta yin aikin nagari da kuma taimakon waɗansu, gama da irin waɗannan hadayu ne Allah yake jin daɗi.

Yaƙub 1:9-11

Bari ɗan’uwan da yake cikin halin ƙasƙanci yă yi taƙama a matsayinsa na ɗaukaka. Amma wanda yake mai arziki, ya kamata yă yi taƙama a matsayinsa na ƙasƙanci, gama ba zai daɗe ba kamar furen jeji. Gama in rana ta fito ta yi zafi mai tsanani sai ta sa tsiro yă yanƙwane tsiro; furensa yă kakkaɓe, kyansa kuma yă lalace. Haka ma mai arziki zai shuɗe yayinda yake cikin harkarsa.

Yaƙub 1:17

Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.

Yaƙub 2:2-7

A ce wani ya shigo cikin taronku saye da zoben zinariya da riguna masu tsada, wani matalauci kuma saye da tsummoki shi ma ya shigo, in kuka mai da hankali na musamman ga mutumin da yake da riguna masu tsadan nan kuka kuma ce, “Ga wurin zama mai kyau dominka,” amma kuka ce wa matalaucin nan, “Kai tsaya daga can,” ko kuwa, “Ka zauna a ƙasa kusa da ƙafafuna,” ashe, ba ku nuna bambanci a tsakaninku ke nan ba, kuka kuma zama alƙalai masu mugayen tunani? Ku saurara, ’yan’uwana ƙaunatattu. Ashe, Allah bai zaɓi waɗanda suke matalauta a idon duniya don su zama masu wadata cikin bangaskiya, su kuma gāji mulkin da ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari ba? Ga shi kun wulaƙanta matalauta. Ashe, ba masu arziki ne suke cutarku ba? Ba su ba ne suke jan ku zuwa kotu? Ba su ba ne suke ɓata sunan nan mai martaba wanda aka san ku da shi ba?

Yaƙub 2:8

In fa kun kiyaye dokan nan ta mulki wadda take cikin Nassi mai cewa, “Ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka,” kun yi daidai.

Yaƙub 2:14-17

Wanda amfani ne, ’yan’uwana, a ce wani yă ce yana da bangaskiya, amma ba shi da ayyuka? Anya, wannan bangaskiya za tă iya cetonsa kuwa? A ce wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ba shi da riguna ko abincin yini, sai waninku yă ce masa, “Sauka lafiya, Allah ya ba da ci da sha da kuma sutura,” amma bai yi wani abu game da bukatunsa na jiki ba, ina amfani? Haka ma bangaskiya ita kaɗai, in ba tare da ayyuka ba, matacciya ce.

Yaƙub 4:3

Sa’ad da kuka roƙa, ba kwa samu, don kun roƙa da mugun nufi, don ku kashe abin da kuka samu a kan sha’awace-sha’awacenku.

Yaƙub 4:13-15

Yanzu fa sai ku saurara, ku da kuke cewa, “Yau ko gobe za mu je wannan ko wancan birni, mu yi shekara a can, mu yi kasuwanci, mu ci riba.” Alhali kuwa ba ku ma san abin da zai faru gobe ba. Wane iri ne ranku? Ku kamar hazo ne da yake bayyana na ɗan lokaci sa’an nan yă ɓace. A maimakon haka, ya kamata ku ce, “In Ubangiji ya yarda, muna kuma a raye, za mu yi wannan ko wancan.”

Yaƙub 5:1-3

Yanzu fa sai ku saurara, ku masu arziki, ku yi kuka da ihu, saboda azabar da take zuwa a kanku. Arzikinku ya ruɓa, asu kuma sun cinye tufafinku. Zinariyarku da azurfarku sun yi tsatsa. Tsatsarsu kuwa za tă zama shaida a kanku, ta kuma ci namar jikinku kamar wuta. Kun ɓoye dukiya a kwanakin ƙarshe.

Yaƙub 5:4-5

Ga shi! Zaluncin da kuka yi na hakkin ma’aikatan gonakinku yana ta ƙara. Kukan masu girbi ya kai kunnuwan Ubangiji Maɗaukaki. Kun yi rayuwar jin daɗi a duniya kuna ci kuna sha na ganin dama. Kun ciyar da kanku kun yi ƙiba don ranar yanka.

1 Bitrus 1:7

Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan gwada ta da wuta, domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi.

1 Bitrus 1:18

Gama kun san cewa ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa ko zinariya ce aka fanshe ku daga rayuwar banza da kuka karɓa daga kakanni-kakanninku ba,

1 Bitrus 3:3-4

Kyanku bai kamata yă zama na adon jiki ba, kamar kitso da sa kayan ado na zinariya da kuma sa kaya masu tsada. Maimakon haka, kyanku ya kamata yă zama ainihi na halinku na ciki, kyan da ba ya koɗewa na tawali’u da kuma na natsattsen ruhu, wanda yake mai daraja a gaban Allah.

1 Yohanna 2:15-17

Kada ku ƙaunaci duniya, ko wani abin da yake cikinta. In wani yana ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa. Gama duk abin da yake na duniya, kamar sha’awace-sha’awacen mutuntaka, sha’awar idanunsa, da kuma taƙama da abin da yake da shi, yake kuma yi, ba daga wurin Uba suke fitowa ba sai dai daga duniya. Duniya da sha’awace-sha’awacenta suna shuɗewa, amma mutumin da yake aikata nufin Allah, zai rayu har abada.

1 Yohanna 3:17-18

In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa? ’Ya’yana ƙaunatattu, kada mu yi ƙauna da fatar baki kawai, sai dai mu nuna ta ta wurin aikatawa da kuma gaskiya.

Ru’uya ta Yohanna 3:16-18

‹Amma domin kana tsaka-tsaka ba zafi ba, ba kuma sanyi ba, ina dab da tofar da kai daga bakina.› ‹Ka ce, ‘Ina da arziki; na sami dukiya ba na kuma bukatar kome.’ Amma ba ka gane ba cewa kai matsiyaci ne, abin tausayi, matalauci, makaho kana kuma tsirara.› ‹Na shawarce ka ka sayi zinariyar da aka tace cikin wuta daga gare ni, don ka yi arziki; da fararen tufafi ka sa, don ka rufe kunyar tsirancinka; da kuma maganin ido ka sa a idanunka, don ka gani.›

Ru’uya ta Yohanna 6:6

Sai na ji wani abu mai ƙara kamar wata murya a tsakiyar halittu huɗun nan masu rai tana cewa, “Kwatan alkama don albashin aikin yini, da kuma kwata uku na sha’ir don albashin yini guda, kada kuwa ka ɓata man da ruwan inabi!”

Ru’uya ta Yohanna 6:15-16

Sa’an nan sarakunan duniya, hakimai, jarumawa, masu arziki, masu ƙarfi, da kowane bawa da kuma kowane ’yantacce ya ɓoye a cikin koguna da kuma cikin duwatsun tsaunuka. Suka kira duwatsu da tsaunuka suna cewa, “Ku fāɗi a kanmu ku kuma ɓoye mu daga fuskar wannan mai zama a kan kursiyi da kuma daga fushin Ɗan Ragon nan!

Ru’uya ta Yohanna 13:16-17

Ta kuma tilasta wa kowa, manya da yara, mawadata da matalauta, ’yantattu da bayi, don a yi musu alama a hannun dama ko a goshi, don kada kowa yă saya ko yă sayar, sai dai yana da alamar, wadda take sunan dabbar ko kuma lambar sunanta.

Ru’uya ta Yohanna 18:11-14

“Attajiran duniya za su yi kuka su kuma yi makoki a kanta, domin ba wanda yake ƙara sayen kayayyakinsu kayayyakin zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja da lu’ulu’ai; lallausan lilin, tufa masu ruwan shunayya, siliki da jan tufa; da kowane irin katakai masu ƙanshi da kayayyaki na kowane iri da aka yi da hauren giwa, katakai masu tsada, tagulla, baƙin ƙarfe da dutse mai sheƙi; kayayyakin sinnamon da kayan yaji, na turaren wuta, mur da turare, na ruwan inabi da man zaitun, na gari mai laushi da alkama; shanu da tumaki; dawakai da kekunan doki, da jikuna da kuma rayukan mutane. “Za su ce, ‘Amfanin da kike marmari ya kuɓuce. Dukan arzikinki da darajarki sun ɓace, ba kuwa za a ƙara samunsu ba.’

Ru’uya ta Yohanna 18:15-17

Attajiran da suka sayar da waɗannan kayayyaki suka kuma sami arzikinsu daga gare ta za su tsaya daga nesa, cike da tsoron ganin azabarta. Za su yi kuka da makoki su ce, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma, saye da lallausan lilin, shunayya da kuma ja, mai walƙiya da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai! Cikin sa’a guda irin wannan dukiya mai yawa ta hallaka!’ “Duk matuƙan jirgin ruwa, da dukan waɗanda suke tafiya a jirgin ruwa, ma’aikatanta, da duk masu samun abin zama gari daga teku za su tsaya daga nesa.

Ru’uya ta Yohanna 21:6

Ya ce mini, “An gama. Ni ne Alfa da kuma Omega, na Farko da kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi abin sha kyauta daga maɓulɓular ruwan rai.

Ru’uya ta Yohanna 22:17

Ruhu da kuma amarya suna cewa, “Zo!” Duk wanda ya ji kuwa, yă ce, “Zo!” Duk mai jin ƙishirwa, yă zo; duk mai bukata kuma, yă ɗibi ruwan rai kyauta.

Hausa - Hausa - HA

HA'BSS - Budadden Littafi Mai Tsarki Biblica - 2020

This Bible text is from Biblica Open Hausa Contemporary Bible 2020
https://open.bible/bibles/hausa-biblica-text-bible/
provided by: Biblica Inc, available by Creative Commons CC-BY-SA-4.0,
and this new compilation is shared as www.creativecommons.org/licenses/by-sa/4.0.
Languages are made available to you by www.ipedge.net