27 – Wahalhalu
Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Wahalhalu.
Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Wahalhalu.
Matarsa ta ce masa, “Har yanzu kana nan da amincinka? Ka la’anta Allah ka mutu!” Ya amsa ya ce, “Kina magana kamar wawiya. Alheri kaɗai za mu dinga samu daga Allah ban da wahala?” A cikin wannan duka Ayuba bai yi zunubi ba cikin maganarsa.
”A matse muke a kowane gefe, sai dai ba a gurgunta mu ba. An rikitar da mu, amma ba mu fid da zuciya ba. An tsananta mana, amma ba a yashe mu ba, an fyaɗe mu da ƙasa, amma ba a hallaka mu ba. Kullum muna ɗauke da mutuwar Yesu a jikinmu, domin ran Yesu yă bayyana a jikinmu. Muddin muna a raye, kullum zaman mutuwa muke yi saboda Yesu, don a bayyana ran Yesu ta wurin jikin nan namu mai mutuwa. Ta haka, mutuwa tana aiki a cikinmu, ku kuwa rai a cikinku.
”Saboda haka, ba mu fid da zuciya ba. Ko da yake a waje, jikinmu mai mutuwa yana lalacewa, amma can ciki, ana sabunta mu kowace rana. Don wannan ’yar wahalar tamu mai saurin wucewa, ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci. Domin ba abubuwan da ido yake gani ne muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa. Gama abubuwan da ake gani masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne.
”amma kada ka ci daga itacen sanin abin da yake mai kyau da abin da yake mugu, gama a ranar da ka ci shi, lalle za ka mutu.”
”Sa’an nan ya ce wa macen, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba kuma za ki haifi ’ya’ya. Za ki riƙa yin marmarin mijinki zai kuwa yi mulki a kanki.” Ga Adamu kuwa ya ce, “Saboda ka saurari matarka, ka kuma ci daga itacen da na ce, ‘Kada ka ci,’ “Za a la’anta ƙasa saboda kai. Da wahala za ka ci daga cikinta dukan kwanakin rayuwarka. Za tă ba ka ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya za ka kuwa ci ganyayen gona. Da zuffan goshinka za ka ci abincinka har ka koma ga ƙasa, da yake daga cikinta aka yi ka. Gama kai turɓaya ne, kuma ga turɓaya za ka koma.”
”Ubangiji ya ce, “Tabbatacce na ga azabar mutanena a Masar. Na ji su suna kuka saboda matsin da shugabannin gandunsu suke musu, na kuma damu da wahalarsu. Saboda haka na sauko domin in cece su daga hannun Masarawa, in kuma fitar da su daga ƙasar Masar, in kai su ƙasa mai kyau mai fāɗi, ƙasa mai zub da madara da zuma, inda Kan’aniyawa, Hittiyawa, Amoriyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa da Yebusiyawa suke. Yanzu kukan Isra’ilawa ya kai gare ni, na kuma ga yadda Masarawa suke wulaƙanta su
”Ubangiji zai yi yaƙi dominku, ku dai tsaya kurum.”
”Ya ce, “In kun kasa kunne ga muryar Ubangiji Allahnku kuka yi abin da yake daidai a idanunsa, in kun mai da hankali ga umarnansa, kuka kiyaye dukan farillansa, ba zan kawo muku wani ciwon da na kawo a kan Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku.”
”In kuka yi haka, idan kuma suka yi kuka gare ni, zan ji kukansu.
”Ku bauta wa Ubangiji Allahnku, albarkansa kuwa za tă kasance a kan abincinku da ruwan shanku. Zan ɗauke cuta daga cikinku.
”“ ‘In ɗaya daga ciki mutanen ƙasarku ya talauta, ba ya kuma iya tallafa wa kansa a cikinku, sai ku taimake shi kamar yadda za ku yi da baƙo a cikinku.
”“ ‘Zan ba ku salama a ƙasar, za ku kuwa kwanta, kuma babu wani da zai tsorata ku. Zan kori mugayen namun jeji daga ƙasar, takobi kuma ba zai ratsa cikin ƙasarku ba.
”in kuka kuma ƙi farillaina, kuka yi ƙyamar dokokina, kuka kuma kāsa kiyaye umarnaina, har kuka karya alkawarina, to, zan yi muku wannan. Zan kawo muku abin bantsoro, cututtuka da zazzaɓin da zai lalatar da idonku, yă kuma sa ranku a wahala. Za ku shuka iri a banza, domin abokan gābanku ne za su ci. Zan yi gāba da ku har abokan gābanku su ci ku a yaƙi, su waɗanda suke ƙinku za su yi mulki a kanku, za ku gudu ba tare da wani yana korinku ba.
”Sa’ad da kuke cikin wahala saboda waɗannan abubuwan da suka same ku nan gaba, to, sai ku juyo ga Ubangiji Allahnku, ku kuma yi masa biyayya. Gama Ubangiji Allahnku, Allah ne mai jinƙai; ba zai yashe ku ko yă hallaka, ko kuma yă manta da alkawarin da ya yi da kakanninku, wanda ya tabbatar da su da rantsuwa ba.
”Ubangiji zai kiyaye ku daga kowace cuta. Ba zai wahalshe ku da mugayen cututtukan da kuka sani a Masar ba, amma zai aukar wa dukan maƙiyanku.
”Tufafinku ba su yayyage ba, ƙafafunku kuma ba su kumbura ba a waɗannan shekaru arba’in. Sai ku sani fa a cikin zuciyarku cewa kamar yadda mutum kan horar da ɗansa, haka Ubangiji Allahnku ke horar da ku. Ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, kuna tafiya cikin hanyoyinsa, kuna kuma girmama shi.
”Yakan tsare marayu da gwauraye, yana ƙaunar baƙon da yake zama a cikinku, yana ba su abinci da tufafi.
”Ga shi, a yau, ina sa a gabanku albarka da kuma la’ana, albarka in kun yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku, da nake ba ku; la’ana in ba ku yi biyayya da umarnan Ubangiji Allahnku, kuka kuma juya daga hanyar da na umarce ku, ta wurin bin waɗansu alloli, waɗanda ba ku sani ba.
”Sa’ad da kuka tafi yaƙi da abokan gābanku, kuka ga dawakai da kekunan yaƙi da kuma mayaƙan da suka fi ku yawa, kada ku ji tsoronsu, domin Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar zai kasance tare da ku.
”In kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, kuka kuma lura, kuka bi dukan umarnan da na ba ku a yau, Ubangiji Allahnku zai sa ku bisa dukan al’ummai a duniya.
”A wannan rana na kira bisa sama da ƙasa a matsayin shaidu a kanku, cewa na sa a gabanku rai da mutuwa, albarku da la’anoni. Yanzu sai ku zaɓi rai, saboda ku da ’ya’yanku ku rayu don kuma ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku saurari muryarsa, ku kuma manne masa. Gama Ubangiji shi ranku, zai kuwa ba ku shekaru masu yawa a ƙasar da ya rantse zai ba wa kakanninku, Ibrahim, Ishaku da Yaƙub.
”Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tafe tare da ku, ba zai taɓa barinku ko yă yashe ku ba.”
”Ubangiji kansa yana tafe a gabanka, zai kuma kasance tare da kai, ba zai taɓa barinka ko yă yashe ka ba. Kada ka ji tsoro; kada kuma ka karai.”
”“Ku duba yanzu cewa ni ne Shi! Ba wani allah in ban da ni. Nakan kashe in kuma rayar, nakan sa rauni in kuma warkar, ba wanda yake da iko yă cece wani daga hannuna.
”Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je.”
”Yoshuwa ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ko kuwa ku razana, amma ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Haka Ubangiji zai yi da duk abokan gāban da za ku yi yaƙi da su.”
”“Ubangiji ne ke kawo mutuwa, yă kuma rayar yana kai ga kabari, yă kuma tā da. Ubangiji ne yakan aika da talauci da kuma dukiya; yakan ƙasƙantar yă kuma ɗaukaka. Yakan tā da matalauci daga ƙura, yă kuma ɗaga mai bukata daga tarin toka; yă zaunar da su tare da ’ya’yan sarki; yă kuma sa su gāji mulki na ɗaukaka. “Harsashin duniya na Ubangiji ne; a bisansu ne ya kafa duniya.
”Dawuda ya gina wa Ubangiji bagade a wurin, ya kuma miƙa masa hadaya ta ƙonawa, da hadaya ta salama. Sa’an nan Ubangiji ya amsa addu’o’in a madadin ƙasar, aka kuma kawar wa Isra’ila annoban.
”A kwanakin nan sai Hezekiya ya kamu da rashin lafiya har ya kusa mutuwa. Sai annabi Ishaya ɗan Amoz ya zo wurinsa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ka kintsa gidanka domin za ka mutu, ba za ka warke ba.” Hezekiya ya juya fuskarsa wajen bango ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, ka tuna yadda na yi tafiya a gabanka da aminci da zuciya ɗaya, na kuma aikata abin da yake daidai a gabanka.” Sai Hezekiya ya yi kuka mai zafi. Kafin Ishaya yă bar tsakiyar filin gida, sai maganar Ubangiji ta zo masa cewa, “Ka koma ka ce wa Hezekiya, shugaban mutanena, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na mahaifinka Dawuda ya ce, na ji addu’arka na kuma ga hawayenka; zan warkar da kai. A rana ta uku daga yau za ka haura zuwa haikalin Ubangiji. Zan ƙara maka shekara goma sha biyar. Zan kuma cece ka daga hannun sarkin Assuriya. Zan kāre birnin nan saboda kaina da kuma bawana Dawuda.’ ”
”Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki. Ku dogara ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa; ku nemi fuskarsa kullum. Ku tuna ayyukan banmamakin da ya aikata, mu’ujizansa da kuma hukuntai da ya yanke,
”in mutanena, waɗanda ake kira da sunana, sun ƙasƙantar da kansu, suka kuma yi addu’a, suka nemi fuskata, suka kuma juye daga mugayen hanyoyinsu, zan ji daga sama in kuma gafarta zunubinsu in kuwa warkar da ƙasarsu. Yanzu, idanuna za su buɗu, kunnuwata kuma za su saurara ga addu’o’in da aka miƙa a wannan wuri.
”Mayaƙa na jiki ne kawai suke tare da shi, amma Ubangiji Allahnmu ne yake tare da mu, zai kuwa taimake mu yă kuma yi yaƙinmu.” Mutane kuwa suka amince da maganar Hezekiya, Sarkin Yahuda.
”sai ɗan aika ya zo wurin Ayuba ya ce masa, “Shanu suna huɗa, jakuna kuma suna kiwo nan kusa, sai Sabenawa suka auka musu suka kwashe su suka tafi, suka karkashe masu yi maka aiki duka, ni kaɗai na tsira na zo in gaya maka!” Yana cikin magana sai ga wani ɗan aika ya zo ya ce, “Wutar Allah ta sauko daga sama ta ƙona dukan tumaki da masu lura da su, wato, bayinka, ni kaɗai na tsira na zo in gaya maka!” Yana cikin magana sai ga wani ɗan aika ya zo ya ce, “Ƙungiyoyin mahara uku na Kaldiyawa sun auka wa raƙumanka sun kwashe su duka, suka kuma karkashe masu yi maka aiki, ni kaɗai ne na tsira na zo in gaya maka!” Yana cikin magana, sai ga wani ɗan aika ya zo ya ce, “’Ya’yanka maza da mata suna biki, suna ci suna sha a gidan babban ɗanka, sai wata iska mai ƙarfi daga hamada ta auka ta rushe gidan, gidan kuwa ya fāɗi a kan ’ya’yanka ya kashe su, ni kaɗai na tsira na zo in gaya maka!” Da jin haka sai Ayuba ya tashi ya yayyaga tufafin jikinsa, ya aske kansa. Ya fāɗi a ƙasa ya yi sujada
”ya ce, “Tsirara na fito daga cikin mahaifiyata, tsirara kuma zan koma. Ubangiji ya bayar, Ubangiji kuma ya karɓa; yabo ya tabbata ga Ubangiji.”
”Shaiɗan ya amsa ya ce, “Fata don fata! Mutum zai iya rabuwa da duk abin da yake da shi domin ransa. Ka ɗan taɓa lafiyar jikinsa ka gani ba shakka zai la’anta ka kana ji kana gani.” Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “To, shi ke nan, duk abin da yake da shi yana hannunka, amma kada ka taɓa shi, shi kansa.” Sai Shaiɗan ya bar Ubangiji, ya je ya sa wa Ayuba ƙuraje masu zafi a jikinsa daga tafin ƙafafunsa har zuwa kansa. Sai Ayuba ya ɗauki kaskon tukunya yana ta sosa ƙurajen da shi, yayinda yake zaune cikin toka.
”Matarsa ta ce masa, “Har yanzu kana nan da amincinka? Ka la’anta Allah ka mutu!” Ya amsa ya ce, “Kina magana kamar wawiya. Alheri kaɗai za mu dinga samu daga Allah ban da wahala?” A cikin wannan duka Ayuba bai yi zunubi ba cikin maganarsa.
”Lokacin da abokan Ayuba su uku wato, Elifaz mutumin Teman, Bildad mutumin Shuwa, da Zofar mutumin Na’ama suka ji wahalar da ta auka wa Ayuba, sai suka shirya suka bar gidajensu suka je don su ta’azantar da shi. Sa’ad da suka gan shi daga nesa, da ƙyar suka gane shi; sai suka fara kuka da ƙarfi, suka yayyaga tufafinsu suka zuba toka a kawunansu, sai suka zauna da shi a ƙasa har kwana bakwai. Ba wanda ya ce masa kome, don sun ga tsananin wahalar da yake ciki.
”“Mai albarka ne wanda Allah yake yi masa gyara in mutumin ya yi kuskure; saboda haka kada ka guje wa horon Maɗaukaki. Ko da yake yana sa ciwo, shi ne kuma yake warkar da ciwon; ciwon da ya ji maka, shi da kansa zai warkar da shi.
”Da sai in ji daɗi duk zafin da nake sha ban hana maganar Mai Tsarkin nan cika ba. “Wane ƙarfi nake da shi, har da zan ci gaba da sa zuciya? Wane sa zuciya ne zai sa in yi haƙuri?
”“Duk wanda ya ƙi yă yi alheri ga aboki ya rabu ta tsoron Maɗaukaki.
”Jikina duk tsutsotsi da ƙuraje sun rufe shi, fatar jikina ta ruɓe tana fitar da ruwan miki.
”Sai dai yă cika bakinka da dariya, yă sa ka yi sowa ta murna.
”“Na gaji da rayuwa; saboda haka bari in faɗi zuciyata gabagadi yadda raina yake jin ba daɗi.
”Ba shakka za ka manta da wahalolinka, za ka tuna da su kamar yadda ruwa yake wucewa. Rayuwarka za tă fi hasken rana haske, duhu kuma zai zama kamar safiya. Za ka zauna lafiya, domin akwai bege; za ka duba kewaye da kai ka huta cikin kwanciyar rai. Za ka kwanta, ba wanda zai sa ka ji tsoro, da yawa za su zo neman taimako a wurinka.
”Ku kuma kun ishe ni da ƙarairayi; ku likitocin wofi ne, dukanku!
”Ko da zai kashe ni ne, begena a cikinsa zai kasance; ba shakka zan kāre kaina a gabansa
”“Haka mutum yake lalacewa kamar ruɓaɓɓen abu, kamar rigar da asu ya cinye.
”Zafin jikinsa kaɗai yake ji yana kuka wa kansa ne kaɗai.”
”Ni ba kome ba ne sai dai fata da ƙashi, da ƙyar na tsira.
”Na san wanda zai fanshe ni yana nan da rai, kuma a ƙarshe zai tsaya a kan duniya. Kuma bayan an hallaka fatata, duk da haka a cikin jiki zan ga Allah.
”“Yanzu raina yana ƙarewa; kwanakin wahala sun kama ni. Dare ya huda ƙasusuwana; ina ta shan azaba ba hutawa.
”Zuciyata ba tă daina ƙuna ba; ina fuskantar kwanakin wahala. Na yi baƙi ƙirin, amma ba rana ce ta ƙona ni ba. Na tsaya a cikin mutane, na kuma yi kuka don taimako. Na zama ɗan’uwan diloli, na zama abokan mujiyoyi. Fatar jikina ta yi baƙi tana ɓarewa; jikina yana ƙuna da zazzaɓi.
”“Ko kuma mutum yă sha horo ta wurin kwanciya da ciwo da rashin jin daɗi cikin ƙasusuwansa, yadda zai ji ƙyamar abinci, har yă ƙi son abinci mafi daɗi. Naman jikinsa ya lalace ba wani abu mai kyau a ciki kuma ƙasusuwansa da suke a rufe da tsoka yanzu duk sun fito. Ransa yana matsawa kusa da rami, ransa kuma kusa da ’yan aikan mutuwa.
”“A ce mutum ya ce wa Allah, ‘Na yi laifi, amma ba zan sāke saɓa wa wani ba. Ka koya mini abin da ba zan iya gani ba; in na yi ba daidai ba, ba zan sāke yi ba.’
”Bayan Ayuba ya yi wa abokansa addu’a, Ubangiji ya sa shi ya sāke zama mai arziki ya ninka abin da yake da shi a dā sau biyu. Dukan ’yan’uwansa maza da mata da duk waɗanda suka san shi a dā suka zo suka ci abinci tare da shi a cikin gidansa. Suka ta’azantar da shi suka ƙarfafa shi game da duk wahalar da Ubangiji ya auka masa, kowannensu kuma ya ba shi azurfa da zobe na zinariya.
”Sarakunan duniya sun ɗauki matsayi masu mulki sun taru gaba ɗaya suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa. Suna cewa, “Bari mu tsittsinke sarƙoƙinsu, mu kuma ’yantar da kamammu daga kangin bautar Allah.” Mai zama a kursiyi a sama yana dariya; Ubangiji yana musu ba’a.
”Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji; ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina. Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi, ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela Na kwanta na yi barci; na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni. Ba zan ji tsoro ko dubu goma suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba.
”Zan kwanta in kuma yi barci lafiya, gama kai kaɗai, ya Ubangiji, kake sa mazaunina yă kasance lafiya lau.
”Ka yi mini jinƙai, Ubangiji, gama na suma; Ya Ubangiji, ka warkar da ni, gama ƙasusuwana suna zafin ciwo. Raina yana cikin wahala. Har yaushe, ya Ubangiji, har yaushe? Ka juyo, ya Ubangiji, ka cece ni; ka cece ni saboda madawwamiyar ƙaunarka.
”Ubangiji shi ne mafakan waɗanda ake danniya, mafaka a lokutan wahala. Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai, gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.
”Ya Ubangiji, dubi yadda abokan gābana suna tsananta mini! Ka yi jinƙai ka kuma ɗaga ni daga ƙofofin mutuwa,
”Amma kai, ya Allah, kana gani wahala da baƙin ciki; kana lura da yadda suke ɗaukansu a hannu. Marar taimako kan danƙa kansa gare ka; kai ne mai taimakon marayu
”Har yaushe zan yi kokawa da tunanina kuma kowace rana in kasance da damuwa a zuciyata? Har yaushe abokin gābana zai yi nasara a kaina? Ka dube ni ka amsa mini, ya Ubangiji Allahna. Ka ba da haske ga fuskata, ko in yi barci cikin mutuwa;
”Kullum nakan sa Ubangiji a gabana. Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba. Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki; jikina kuma zai zauna lafiya, domin ba za ka yashe ni a kabari ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba. Ka sanar da ni hanyar rai; za ka cika ni da farin ciki a gabanka, da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.
”Ka kiyaye ni yadda ake kiyaye ido; ka ɓoye ni cikin inuwar fikafikanka daga mugaye waɗanda suke kai mini hari, daga abokan gāba masu mutuwa waɗanda suka kewaye ni.
”Ina ƙaunarka, ya Ubangiji, ƙarfina. Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona; Allahna shi ne dutsena, a gare shi nake neman mafaka. Shi ne garkuwata da ƙahon cetona, mafakata. Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo, na kuwa kuɓuta daga abokan gābana. Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni; rigyawan hallaka sun sha kaina. Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe kewaye da ni; tarkon mutuwa ya yi mini arangama. Cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji; Na yi kuka ga Allahna don taimako. A Haikalinsa ya ji muryata, Kukana na neman taimako ya kai kunnensa.
”Gama bai rena ko yă ƙyale wahalar masu shan wuya ba; bai ɓoye fuskarsa daga gare shi ba amma ya saurari kukansa na neman taimako.
”Ubangiji ne yake kiwona, ba zan rasa kome ba, Yakan sa in kwanta a makiyaya mai ɗanyar ciyawa, yakan bi da ni kusa da ruwaye marar hayaniya, yakan maido da raina. Yakan bi da ni a hanyoyin adalci saboda sunansa. Ko da na yi tafiya ta kwari na inuwar mutuwa, ba zan ji tsoron mugu ba, gama kana tare da ni; bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya, za su yi mini ta’aziyya. Ka shirya mini tebur a gaban abokan gābana. Ka shafe kaina da mai; kwaf nawa ya cika har yana zuba. Tabbatacce alheri da ƙauna za su bi dukan kwanakin raina, zan kuwa zauna a gidan Ubangiji har abada.
”Ka juye wurina ka kuma yi mini jinƙai, gama na kaɗaice ina kuma wahala. Damuwoyin zuciyata sun ninka; ka ’yantar da ni daga wahalata. Ka dubi wahalata da kuma azabata ka ɗauke mini dukan zunubaina.
”Ubangiji ne haskena da cetona, wa zan ji tsoro? Ubangiji ne mafakar raina, wane ne zan ji tsoro? Sa’ad da mugaye suka tasar mini don su cinye ni, sa’ad da abokan gābana da maƙiyina suka kawo mini hari, sun yi tuntuɓe suka fāɗi. Ko da yake mayaƙa sun kewaye ni, zuciyata ba za tă ji tsoro ba; ko da yake ya ɓarke a kaina, duk da haka zan ƙarfafa. Abu guda na roƙi Ubangiji, wannan shi ne na nema, cewa in zauna a gidan Ubangiji dukan kwanakin raina, in dubi kyan Ubangiji in kuma neme shi a cikin haikalinsa. Gama a lokacin wahala, zai kiyaye ni lafiya a wurin zamansa; zai ɓoye ni cikin inuwar tabanakul nasa ya kuma sa ni can a bisa dutse.
”Ko da mahaifina da mahaifiyata sun yashe ni, Ubangiji zai karɓe ni.
”Ubangiji shi ne ƙarfina da garkuwata; zuciyata ta amince da shi, kuma na sami taimako. Zuciyata ta yi tsalle don farin ciki zan kuwa yi godiya gare shi cikin waƙa.
”Ya Ubangiji Allahna, na yi kira gare ka don taimako ka kuwa warkar da ni. Ya Ubangiji, ka dawo da ni daga kabari; ka kiyaye ni daga gangarawa zuwa cikin rami. Ku rera ga Ubangiji, ku tsarkakansa; ku yabi sunansa mai tsarki. Gama fushinsa na ɗan lokaci ne amma alherinsa har matuƙa ne; mai yiwuwa a yi kuka da dare amma farin ciki kan zo da safe.
”“Wace riba ce a hallakata, a kuma gangarawa ta zuwa cikin rami? Ƙura za tă yabe ka ne? Za tă iya yin shelar amincinka? Ka ji, ya Ubangiji, ka kuwa yi mini jinƙai; Ya Ubangiji, ka zama taimakona.” Ka mai da kukata ta zama rawa; ka tuɓe rigar makokina ka sa mini na farin ciki, don zuciyata za tă iya rera gare ka ba kuwa za tă yi shiru ba. Ya Ubangiji Allahna, zan yi maka godiya har abada.
”Ka juye kunnenka gare ni, ka zo da sauri ka cece ni; ka zama dutsen mafakata, mafaka mai ƙarfi na cetona. Da yake kai ne dutsena da kuma kagarata, saboda sunanka ka bi da ni ka kuma jagorance ni.
”Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, gama ina cikin damuwa; idanuna sun gaji da baƙin ciki, raina da jikina sun tafke tilis. Baƙin ciki ya rufe raina shekaruna sun cika da nishi; ƙarfina ya karai saboda azaba, ƙasusuwana kuma sun gaji tiƙis. Saboda dukan abokan gābana, Na zama tamƙar abin reni na maƙwabtana; na zama abin tsoro ga abokaina, waɗanda suka gan ni a titi sukan gudu daga gare ni. An manta da ni sai ka ce na mutu; na zama kamar fasasshen kasko.
”Lokutana suna a hannuwanka; ka cece ni daga abokan gābana da kuma daga waɗanda suke fafara ta.
”Sa’ad da na yi shiru, ƙasusuwana sun yi ta mutuwa cikin nishina dukan yini. Gama dare da rana hannunka yana da nauyi a kaina; an shanye ƙarfina ƙaf sai ka ce a zafin bazara. Sela
”Amma idanun Ubangiji suna a kan wanda yake tsoronsa, a kan waɗanda suke sa zuciya cikin ƙaunarsa marar ƙarewa, don yă cece su daga mutuwa ya bar su da rai a lokacin yunwa.
”Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa, ya kuwa cece su.
”Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu; fuskar Ubangiji yana gāba da waɗanda suke aikata mugunta, don yă sa a manta da su a duniya. Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su; yakan cece su daga dukan wahalarsu. Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu. Adali zai iya kasance da wahala da yawa, amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu; yakan tsare dukan ƙasusuwansa, ba ko ɗayansu da zai karye.
”Duk da haka sa’ad da suke ciwo, na sanya rigar makoki na ƙasƙantar da kaina da azumi. Sa’ad da aka mayar mini da addu’o’i babu amsa, nakan yi ta yawo ina makoki sai ka ce yadda nake yi wa abokina ko ɗan’uwana. Nakan sunkuyar da kaina cikin baƙin ciki sai ka ce ina kuka domin mahaifiyata.
”Ina misalin ƙaunarka marar ƙarewa! Mutane manya da ƙanana kan sami mafaka cikin inuwar fikafikanka. Suna biki a yalwar gidanka; kakan ba su sha daga rafin farin cikinka. Gama a gare ka akwai maɓulɓular rai cikin haskenka mukan ga haske.
”amma Ubangiji yakan yi dariyar mugaye, gama ya sani ranarsu tana zuwa. Mugaye sukan zare takobi su ja baka don su kashe matalauta da masu bukata, don su kashe waɗanda hanyoyinsu daidai suke. Amma takubansu za su soki zukatansu, kuma bakkunansu za su kakkarye.
”Ka dubi marasa zargi, ka lura da adali; akwai sa zuciya domin mutum mai salama.
”Saboda hasalarka babu lafiya a jikina; ƙasusuwana ba lafiya saboda zunubina. Laifofina sun mamaye ni kamar nauyin da ya sha ƙarfin ɗauka. Miyakuna sun ruɓe suna kuma wari saboda wawancina na zunubi. An tanƙware ni aka kuma ƙasƙantar da ni; dukan yini ina ta kuka. Bayana yana fama da zazzaɓi; babu lafiya a jikina. Na gaji sharkaf an kuma ragargaza ni; ina nishi da wahala a cikin zuciyata. Dukan bukatata tana a shimfiɗe a gabanka, ya Ubangiji; ajiyar zuciyata ba ta ɓoyuwa daga gare ka. Zuciyata na bugu, ƙarfina kuma ya ƙare, har ma haske ya rabu da idanuna.
”Ka ɗauke bulalarka daga gare ni; na ji jiki ta wurin bugun da hannunka ya yi mini. Kakan tsawata ka kuma hore mutane saboda zunubinsu; kakan cinye wadatarsu kamar yadda asu ke yi, kowane mutum dai shaƙar iska ne. Sela “Ka ji addu’ata, ya Ubangiji, ka saurari kukata ta neman taimako; kada ka kurmance ga kukata. Gama ina zama tare da kai kamar baƙo, baƙo, kamar yadda dukan kakannina sun kasance.
”Ya ɗaga ni daga rami marar fāɗi, daga laka da taɓo; ya sa ƙafafuna a kan dutse ya kuma ba ni tsayayyen wuri don in tsaya. Ya sa sabuwar waƙa a bakina, waƙar yabo ga Allahna. Da yawa za su gani su tsorata su kuma dogara ga Ubangiji.
”Kada ka hana mini jinƙanka, ya Ubangiji; bari ƙaunarka da gaskiyarka kullum su kāre ni.
”Ubangiji zai ba shi ƙarfi a gadon rashin lafiyarsa ya mayar masa da lafiya daga ciwon da ya kwantar da shi. Na ce, “Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai; ka warkar da ni, gama na yi maka zunubi.”
”Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina? Me ya sa ka damu a cikina? Ka dogara ga Allah, gama zai sāke yabe shi, Mai Cetona da kuma Allahna. Raina yana baƙin ciki a cikina; saboda haka zan tuna da kai daga ƙasar Urdun, a ƙwanƙolin Hermon, daga Dutsen Mizar.
”Sa’an nan zan tafi bagaden Allah, ga Allah, farin cikina da murnata. Zan yabe ka da garaya, Ya Allah, Allahna. Me ya sa kake baƙin ciki, ya raina? Me ya sa ka damu a cikina? Ka dogara ga Allah, gama zai sāke yabe shi, Mai Cetona da Allahna.
”Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala. Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku,
”“Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah; za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai, za a ɗaukaka ni cikin duniya.” Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela
”Gama wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin; zai zama jagorarmu har zuwa ƙarshe.
”ku kira gare ni a ranar wahala; zan cece ku, za ku kuwa girmama ni.”
”Bari in ji farin ciki da murna; bari ƙasusuwan da ka ragargaza su yi farin ciki.
”Hadayun Allah su ne karyayyen ruhu; karyayyiya da kuma zuciya mai tuba, Ya Allah, ba za ka ƙi ba.
”Masu adalci za su ga su ji tsoro; za su yi masa dariya, suna cewa, “Yanzu, ga mutumin da bai mai da Allah mafakarsa ba amma ya dogara a yawan arzikinsa ya kuma yi ƙarfi ta wurin hallaka waɗansu!”
”Yakan fisshe ni lafiya daga yaƙin da ake yi da ni, ko da yake da yawa suna gāba da ni.
”Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji zai kuwa riƙe ku; ba zai taɓa barin mai adalci yă fāɗi ba.
”Sa’ad da nake tsoro, zan dogara gare ka. Ga Allah wanda maganarsa nake yabo ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba. Me mutum mai mutuwa zai yi mini? Dukan yini sun yi ta juya maganata; kullum suna ƙulle-ƙulle su cuce ni. Sun haɗa baki, sun ɓoye, suna kallon takawata suna a shirye su ɗauki raina.
”Ka lissafta makokina; ka jera hawayena a littafinka, ba a rubuce suke a cikin littafinka ba?
”ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini? Ina ƙarƙashin alkawari gare ka, ya Allah; zan miƙa hadayuna na godiya gare ka. Gama ka cece ni daga mutuwa da kuma ƙafafun daga tuntuɓe, don in yi tafiya a gaban Allah cikin hasken rai.
”Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi mini jinƙai, gama a gare ka raina yake samun mafaka. Zan sami mafaka a inuwar fikafikanka sai masifar ta wuce.
”Amma kai, ya Ubangiji, kakan yi musu dariya; kana yi wa dukan waɗannan al’ummai ba’a. Ya ƙarfina, na dogara gare ka; kai, ya Allah, kai ne kagarata,
”Amma zan rera game da ƙarfinka, da safe zan rera game da ƙaunarka; gama kai ne mafakata, kagarata a lokacin wahala. Ya ƙarfina, na rera yabo gare ka; kai, ya Allah, kai ne kagarata, Allah mai ƙaunata.
”Ka ji kukata, ya Allah; ka saurari addu’ata. Daga iyakar duniya na yi kira gare ka, na yi kira yayinda zuciyata ta karai; ka bishe ni zuwa dutsen da ya fi ni tsayi. Gama kai ne mafakata, hasumiya mai ƙarfi gāba da maƙiyi. Ina marmari in zauna a tentinka har abada in sami mafaka a cikin inuwar fikafikanka. Sela
”Raina na samun hutu a wurin Allah ne kaɗai; cetona na zuwa daga gare shi. Shi kaɗai ne dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba.
”Ka nemi hutu, ya raina, a wurin Allah kaɗai; dogarata kan zo daga gare shi ne. Shi ne kaɗai dutsena da cetona; shi ne kagarata, ba zan jijjigu ba. Cetona da girmata sun dangana ga Allah ne, shi ne dutsena mai ƙarfi, mafakata. Ku dogara a gare shi a duk lokuta, ya mutane; ku faɗi albarkaci bakin zukatanku a gare shi, gama Allah ne mafakarmu. Sela
”Ya Allah, kai ne Allahna, da nacewa na neme ka; raina yana ƙishinka, jikina yana marmarinka, cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye inda babu ruwa. Na gan ka a wuri mai tsarki na kuma dubi ikonka da ɗaukakarka. Domin ƙaunarka ta fi rai kyau, leɓunana za su ɗaukaka ka. Zan yabe ka muddin raina, kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana. Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau; da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka. A gadona na tuna da kai; ina tunaninka dukan dare. Domin kai ne mai taimakona, ina rera a cikin inuwar fikafikanka. Raina ya manne maka; hannunka na dama yana riƙe da ni.
”Uba ga marayu, mai kāre gwauraye, shi ne Allah a mazauninsa mai tsarki. Allah ya shirya masu kaɗaici a cikin iyalai, ya jagorance ’yan kurkuku da waƙoƙi; amma ’yan tawaye suna zama a ƙasa mai zafin rana.
”Ko sa’ad da na tsufa da furfura, kada ka yashe ni, ya Allah, sai na furta ikonka ga tsara mai zuwa, ƙarfinka ga dukan waɗanda suke zuwa. Adalcinka ya kai sararin sama, ya Allah, kai da ka yi manyan abubuwa. Wane ne kamar ka, ya Allah? Ko da yake ka sa na ga wahaloli, masu yawa da kuma masu ɗaci, za ka sāke mayar mini da rai; daga zurfafan duniya za ka sāke tā da ni. Za ka ƙara girmana ka sāke ta’azantar da ni. Zan yabe ka da garaya saboda amincinka, ya Allah; zan rera yabo gare ka da molo, Ya Mai Tsarki na Isra’ila. Leɓunana za su yi sowa don farin ciki sa’ad da na rera yabo gare ka, ni, wanda ka fansa.
”Duk da haka kullum ina tare da kai; ka riƙe ni a hannun damana. Ka bishe ni da shawararka, bayan haka kuma za ka kai ni cikin ɗaukaka. Wa nake da shi a sama in ba kai ba? Ba na kuma sha’awar kome a duniya in ban da kai. Jikina da zuciyata za su iya raunana, amma Allah ne ƙarfin zuciyata da kuma rabona har abada.
”Ku tsare mutuncin marasa ƙarfi da marayu; ku kāre hakkin matalauta da waɗanda ake danniya.
”Raina yana marmari, har yana suma, don filayen gidan Ubangiji; zuciyata da namana na tā da murya domin Allah mai rai. Har tsada ma ta sami gida, tsatsewa kuma ta yi wa kanta sheƙa, inda za tă ƙyanƙyashe ’ya’yanta, wuri kusa da bagadenka, Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina da kuma Allahna. Masu albarka ne waɗanda suke zama a gidanka; kullum suna ta yabonka. Sela
”A lokacin wahala zan yi kira gare ka, gama za ka amsa mini.
”Gama ƙaunarka da girma take gare ni; kai ka cece ni daga zurfafa, daga mazaunin matattu.
”Ka tuna yadda raina mai wucewa ne. Gama ka halicce dukan mutane ba amfani! Wanda mutum ne zai rayu da ba zai ga mutuwa ba, ko yă cece kansa daga ikon kabari? Sela
”Ubangiji kai ne mazauninmu cikin dukan zamanai.
”Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki. Zan ce game da Ubangiji, “Shi ne mafakata da kagarata, Allahna, wanda nake dogara.” Tabbatacce zai cece ka daga tarkon mai farauta da kuma daga cututtuka masu kisa. Zai rufe ka da fikafikansa, a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka; amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga. Ba za ka ji tsoron razanar dare, ko kibiyoyi da suke firiya da rana ba, ko bala’in da yake aukowa cikin duhu, ko annobar da take hallakarwa da tsakar rana. Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka, dubu goma a hannun damanka, amma ba abin da zai zo kusa da kai.
”In ka mai da Mafi Ɗaukaka wurin zamanka, har ma Ubangiji wanda yake mafakata, to, babu wani mugun abin da zai same ka, ba masifar da za tă zo kusa da tentinka. Gama zai umarci mala’ikunsa game da kai don su tsare ka a dukan hanyoyinka; za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse. Za ka taka zaki da gamsheƙa; za ka tattake babban zaki da maciji. Ubangiji ya ce, “Domin ya ƙaunace ni, zan kuɓutar da shi; zan kiyaye shi, gama ya yarda da sunana. Zai kira bisa sunana, zan kuma amsa masa; zan kasance tare da shi a lokacin wahala, zan kuɓutar da shi in kuma girmama shi. Da tsawon rai zan ƙosar da shi in kuma nuna masa cetona.”
”Sa’ad da alhini ya yi yawa a cikina, ta’aziyyarka ta kawo farin ciki wa raina.
”Amma Ubangiji ya zama kagarata, Allahna kuma dutsen da nake samun mafaka.
”Ku yi sowa don farin ciki ga Ubangiji, dukan duniya. Yi wa Ubangiji sujada da murna; ku zo gabansa da waƙoƙin farin ciki. Ku san cewa Ubangiji shi ne Allah. Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne; mu mutanensa ne, tumakin makiyayarsa. Ku shiga ƙofofinsa da godiya filayen gidansa kuma da yabo; ku gode masa ku kuma yabi sunansa. Gama Ubangiji yana da kyau kuma ƙaunarsa madawwamiya ce har abada; amincinsa na cin gaba a dukan zamanai.
”Ka ji addu’ata, ya Ubangiji; bari kukata ta neman taimako ta zo gare ka. Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni sa’ad da nake cikin damuwa. Ka juye kunnenka gare ni; sa’ad da na yi kira, ka amsa mini da sauri. Gama kwanakina sun ɓace kamar hayaƙi; ƙasusuwana suna ƙuna kamar jan wuta. Zuciyata ta kamu da ciwo ta kuma bushe kamar ciyawa; na manta in ci abinci. Saboda nishina mai ƙarfi na rame na bar ƙasusuwa kawai.
”Kwanakina suna kamar inuwar yamma; na bushe kamar ciyawa. Amma kai, ya Ubangiji, kana zaune a kursiyinka har abada; sunan da ka yi zai dawwama a dukan zamanai.
”Yabi Ubangiji, ya raina; dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki. Yabi Ubangiji, ya raina, kada kuma ka manta dukan alheransa, wanda yake gafarta dukan zunubai yake kuma warkar da dukan cututtuka, wanda ya fanshi ranka daga rami ya naɗa maka rawani da ƙauna da kuma tausayi,
”gama ya san yadda aka yi mu, ya tuna cewa mu ƙura ne. Game da mutum dai, kwanakinsa suna kamar ciyawa da suke haɓaka kamar fure a gona; iska kan hura a kansa sai ya ɓace ba a kuwa sāke tuna da inda dā yake. Amma daga madawwami zuwa madawwami ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa, adalcinsa kuma tare da ’ya’yansu,
”Sau da yawa ya cece su, amma sun nace su yi tawaye suka kuma lalace cikin zunubinsu. Amma ya lura da wahalarsu sa’ad da ya ji kukansu; saboda su ya tuna da alkawarinsa kuma daga yawan ƙaunarsa ya ji tausayi. Ya sa aka ji tausayinsu a wurin dukan waɗanda suka kame su.
”Sun ji yunwa da ƙishirwa, suka kuma fid da zuciya. Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuma cece su daga damuwarsu.
”gama yana shayar da masu ƙishirwa yana kuma ƙosar da mayunwata da abubuwa masu kyau. Waɗansu sun zauna a cikin duhu da kuma zurfin ɓacin rai, ’yan kurkuku suna wahala cikin sarƙoƙin ƙarfe, gama sun yi tayarwa a kan maganar Allah suka ƙi shawarar Mafi Ɗaukaka. Saboda haka ya ba da su ga aiki mai wuya; suka yi tuntuɓe, kuma ba mai taimako. Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa cece su daga damuwarsu. Ya fitar da su daga duhu da zurfin ɓaci rai ya tsintsinke sarƙoƙinsu.
”Waɗansu suka zama wawaye ta wurin hanyoyinsu na tayarwa suka kuwa sha wahala saboda laifofinsu. Ba su so su ga abinci ba suka kuwa kai bakin mutuwa. Sa’an nan suka yi kuka ga Ubangiji cikin wahalarsu, ya kuwa cece su daga damuwarsu. Ya ba da umarninsa ya kuma warkar da su ya kuɓutar da su daga kabari.
”Ka kwantar da hankali, ya raina, gama Ubangiji mai alheri ne a gare ka. Gama kai, ya Ubangiji, ka ceci raina daga mutuwa, idanuna daga hawaye, ƙafafuna daga tuntuɓe, don in iya tafiya a gaban Ubangiji a ƙasar masu rai.
”Abu mai daraja a gaban Ubangiji shi ne mutuwar tsarkakansa.
”Cikin azabata na yi kuka ga Ubangiji, ya kuwa amsa ta wurin ’yantar da ni. Ubangiji yana tare da ni; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai yi mini?
”Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji da in dogara ga mutum. Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji da in dogara ga sarakuna.
”Ba zan mutu ba amma zan rayu, zan kuwa yi shelar abin da Ubangiji ya yi.
”Ubangiji ya hore ni sosai, amma bai ba da ni ga mutuwa ba.
”An kwantar da ni ƙasa cikin ƙura; ka kiyaye raina bisa ga maganarka.
”Raina ya gaji da baƙin ciki; ka ƙarfafa ni bisa ga maganarka.
”Ta’aziyyata cikin wahalata ita ce alkawarinka yana kiyaye raina.
”Kafin in sha wahala na kauce, amma yanzu ina biyayya da maganarka.
”Ya yi kyau da na sha wahala don in koyi ƙa’idodinka.
”Ya Ubangiji na sani, cewa dokokinka masu adalci ne, kuma cikin aminci ka hore ni. Bari ƙaunarka marar ƙarewa tă yi mini ta’aziyya, bisa ga alkawarinka ga bawanka. Bari tausayinka yă zo mini don in rayu, gama dokarka ce farin cikina.
”Da ba don dokarka ce farin cikina ba, da na hallaka a cikin azabana. Ba zan taɓa manta da farillanka ba, gama ta wurinsu ne ka kiyaye raina.
”Na sha wahala sosai; ka kiyaye raina, ya Ubangiji, bisa ga maganarka.
”Wahala da damuwa suna a kaina, amma umarnanka su ne farin cikina.
”Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, wanda ya kafa sama da ƙasa.
”Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan masifa, zai tsare ranka; Ubangiji zai kiyaye shigarka da fitarka yanzu da har abada kuma.
”Waɗanda suka yi shuka da hawaye za su yi girbi da waƙoƙin farin ciki. Shi da ya fita yana kuka, riƙe da iri don shuki, zai dawo da waƙoƙin farin ciki, ɗauke da dammuna.
”Zan jira Ubangiji, raina zai jira, kuma a cikin maganarsa na sa zuciyata. Raina na jiran Ubangiji fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya, fiye da yadda mai tsaro yakan jira safiya.
”Ka cece ni, ya Ubangiji, daga mugaye; ka tsare ni daga mutane masu rikici, masu shirya maƙarƙashiya a zukatansu suna kuma kawo yaƙi kullum. Suna sa harsunansu su yi kaifi kamar na maciji; dafin gamsheƙa yana a leɓunansu. Sela
”Na san cewa Ubangiji ya shirya wa matalauta adalci yana kuma yi wa mabukata adalci.
”Na yi kuka mai ƙarfi ga Ubangiji; na tā da muryata ga Ubangiji neman jinƙai. Na kawo gunagunina a gabansa; a gabansa na faɗa wahalata. Sa’ad da ƙarfina ya kāre a cikina, kai ne wanda ya san hanyata. A hanyar da nake tafiya mutane sun kafa mini tarko. Duba ta damata ka gani; babu wanda ya kula da ni. Ba ni da mafaka; babu wanda ya kula da raina. Na yi kuka gare ka, ya Ubangiji; Na ce, “Kai ne mafakata, rabona a ƙasar masu rai.” Ka saurari kukata, gama ina cikin matsananciyar bukata; ka cece ni daga waɗanda suke fafarata, gama sun fi ni ƙarfi sosai. Ka ’yantar da ni daga kurkuku, don in yabi sunanka. Ta haka masu adalci za su taru kewaye da ni saboda alherinka gare ni.
”Na buɗe hannuwana gare ka; raina yana jin ƙishinka kamar busasshiyar ƙasa. Sela Ka amsa mini da sauri, ya Ubangiji; ƙarfina ya ƙare. Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni in ba haka ba zan zama kamar waɗanda suka gangara zuwa rami.
”Ubangiji yana kusa da kowa da ya kira gare shi, ga duk wanda ya kira gare shi cikin gaskiya. Yakan cika sha’awar waɗanda suke tsoronsa; yakan ji kukansu yă kuma cece su. Ubangiji yakan lura da dukan waɗanda suke ƙaunarsa, amma dukan mugaye zai hallaka su. Bakina zai yi magana cikin yabon Ubangiji. Bari kowace halitta ta yabi sunansa mai tsarki har abada abadin.
”Yakan biya bukatun mutanen da aka danne ya kuma ba da abinci ga mayunwata. Ubangiji yakan ’yantar da ’yan kurkuku, Ubangiji yakan ba wa makafi ido, Ubangiji yakan ɗaga waɗanda aka rusunar da su ƙasa, Ubangiji yana ƙaunar masu adalci. Ubangiji yana tsaron baƙi yana kuma lura da marayu da kuma gwauruwa, amma yakan lalatar da hanyoyin mugaye.
”Ya warkar da masu raunanar zuciya ya ɗaɗɗaura miyakunsu.
”Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka kada kuma ka dangana ga ganewarka; cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi, zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe. Kada ka zama mai hikima a ganinka; ka ji tsoron Ubangiji ka kuma guji mugunta. Wannan zai ba wa jikinka lafiya yă kuma adana ƙasusuwanka.
”Zuciya mai damuwa takan naƙasar da mutum, amma maganar alheri kan faranta masa rai.
”Zuciya mai farin ciki kan sa fuska tă yi haske, amma ciwon zuciya kan ragargaza rai.
”Zuciya mai farin ciki magani ne mai kyau, amma bakin rai kan busar da ƙasusuwa.
”Sunan Ubangiji hasumiya ce mai ƙarfi; masu adalci kan gudu zuwa wurinta don su zauna lafiya.
”Sa rai da mutum ke yi kan taimake shi sa’ad da yake ciwo, amma in ya karai, to, tasa ta ƙare.
”Harshe yana da ikon rai da mutuwa, kuma waɗanda suke ƙaunarsa za su ci amfaninsa.
”In ba ka da ƙarfi a lokacin wahala, ka tabbatar kai marar ƙarfi ne sosai! Ka kuɓutar da waɗanda ake ja zuwa inda za a kashe su; ka riƙe waɗanda suke tangaɗi zuwa wajen yanka.
”A ba da barasa ga waɗanda suke cikin halin ƙaƙa naka yi, ruwan inabi ga waɗanda suke cikin wahala; bari su sha su manta da talaucinsu kada kuma su ƙara tunawa da ɓacin ransu. “Yi magana domin bebaye, domin hakkin dukan waɗanda suke naƙasassu.
”Akwai lokaci domin kowane abu, da kuma lokaci domin kowane aiki a duniya. Lokacin haihuwa da lokacin mutuwa, lokacin shuki da lokacin tumɓukewa. Lokacin kisa da lokacin warkarwa, lokacin rushewa da lokacin ginawa. Lokacin kuka da lokacin dariya, lokacin makoki da lokacin rawa.
”Suna mai kyau ya fi turare mai ƙanshi, kuma ranar mutuwa ta fi ranar haihuwa. Gara a tafi gidan makoki da a je gidan biki, gama mutuwa ce ƙaddarar kowane mutum; ya kamata masu rai su lura da haka. Baƙin ciki ya fi dariya, gama baƙin ciki yakan kawo gyara. Zuciyar masu hikima tana a gidan makoki, amma zuciya wawaye tana a gidan shagali.
”Sa’ad da al’amura suke tafiya daidai, ka yi farin ciki, amma sa’ad da suka lalace, ka tuna, Allah ne ya yi wancan shi ne kuma ya yi wannan. Saboda haka, mutum ba zai san wani abu game da nan gabansa ba.
”Me ya sa za a ƙara yin muku dūka? Me ya sa kuka nace ga yin tayarwa? An yi wa dukan kanku rauni, zuciyarku duk tana ciwo. Daga tafin ƙafarku zuwa saman kanku ba lafiya, sai miyaku da ƙujewa da manyan gyambuna, ba a tsabtacce su ba ko a daure ko shafa musu magani.
”Dukan ƙasashe suna hutawa suna kuma cikin salama; sun ɓarke da waƙa.
”Ubangiji zai bugi Masar da annoba; zai buge su ya kuma warkar da su. Za su juyo wurin Ubangiji, zai amsa roƙonsu ya kuma warkar da su.
”Game da wannan jikina yana ciwo, zafi ya kama ni, kamar na mace mai naƙuda; na razana game da abin da na ji, na yi mamakin abin da na gani.
”Duniya ta bushe ta kuma yanƙwane, duniya tana shan azaba ta kuma raunana, masu daraja na duniya suna shan azaba. Duniya ta ƙazantu ta wurin mutanenta sun ƙi yin biyayya da dokoki, sun keta farillai suka kuma karya madawwamin alkawari. Saboda haka la’ana za tă auko wa duniya; dole mutanenta su ɗauki hakkin laifinsu. Saboda haka aka ƙone mazaunan duniya, kuma kaɗan ne kurum suka rage.
”Kai ka zama mafakar matalauta, mafaka don mabukata cikin damuwa, wurin ɓuya daga hadari, inuwa kuma daga zafin rana. Gama numfashin mugaye yana kamar da hadari mai bugun bango
”zai haɗiye mutuwa har abada. Ubangiji Mai Iko Duka zai share hawaye daga dukan fuskoki; zai kawar da kunyar mutanensa daga dukan duniya. Ubangiji ne ya faɗa.
”Za ka kiyaye shi da cikakken salama shi wanda ya kafa zuciyarsa gare ka, domin ya dogara a gare ka. Ku dogara ga Ubangiji, gama shi Ubangiji, ne madawwamin Dutse.
”Ubangiji ka kafa salama dominmu; duk abin da muka iya yi kai ne ka yi mana.
”Duk da haka Ubangiji yana marmari ya yi muku alheri; ya tashi don yă nuna muku jinƙai. Gama Ubangiji Allah ne mai aikata gaskiya. Masu albarka ne dukanku waɗanda suke dogara gare shi! Ya mutanen Sihiyona, waɗanda suke zama a Urushalima, ba za ku ƙara kuka ba. Zai zama mai alheri sa’ad da kuka yi kukan neman taimako! Da zarar ya ji, zai amsa muku. Ko da yake Ubangiji yakan ba da abincin azaba da ruwan wahala, ba za a ƙara ɓoye malamanku ba; da idanunku za ku gan su. Ko kun juye dama ko hagu, kunnuwanku za su ji murya a bayanku tana cewa, “Ga hanya; ku yi tafiya a kai.”
”Ku ƙarfafa hannuwa marasa ƙarfi, ku ƙarfafa gwiwoyin da suka gaji; ku faɗa wa waɗanda suka karai a zukata, “Ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro; Allahnku zai zo, zai zo domin ya ɗau fansa; da ramuwar Allah zai zo don yă cece ku.” Sa’an nan idanun makafi za su buɗe kunnuwan kurame kuma su ji. Sa’an nan guragu za su yi tsalle kamar barewa, bebaye kuma su yi sowa don farin ciki. Ruwa zai kwararo daga jeji rafuffuka kuma a cikin hamada.
”Kuma babbar hanya za tă kasance a can; za a ce ta ita Hanyar Mai Tsarki. Marasa tsarki ba za su yi tafiya a kanta ba; za tă zama domin waɗanda suka yi tafiya a wannan Hanya ce; mugaye da wawaye ba za su yi ta yawo a kanta ba. Zaki ba zai kasance a can ba, balle wani naman jeji mai faɗa ya haura kanta; ba za a same su a can ba. Amma fansassu ne kaɗai za su yi tafiya a can, kuma fansassu na Ubangiji za su komo. Za su shiga Sihiyona da rerawa; matuƙar farin ciki zai mamaye su. Murna da farin ciki za su sha kansu, baƙin ciki kuma da nishi za su gudu.
”Ta’aziyya, ku ta’azantu mutanena, in ji Allahnku. Yi magana mai kwantar da rai ga Urushalima, ku kuma furta mata cewa aiki mai zafinta ya isa, cewa an fanshi zunubinta, cewa ta karɓi daga hannun Ubangiji ninki biyu saboda dukan zunubanta.
”Yakan lura da garkensa kamar makiyayi. Yakan tattara tumaki wuri ɗaya yă riƙe su kurkusa da ƙirjinsa; a hankali kuma yakan bi da masu ba da mama.
”Ba ku sani ba? Ba ku ji ba? Ubangiji madawwamin Allah ne, Mahaliccin iyakokin duniya. Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba, kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum. Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji yă kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi. Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala, samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi; amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji za su sabunta ƙarfinsu. Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa; za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba, za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.
”Saboda haka kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai; kada ka karai, gama ni ne Allahnka. Zan ƙarfafa ka in kuma taimake ka; zan riƙe ka da hannun damana mai adalci.
”“Matalauta da mabukata suna neman ruwa, amma babu kome; harsunansu sun bushe saboda ƙishi. Amma Ni Ubangiji zan amsa musu; Ni, Allah na Isra’ila, ba zan yashe su ba.
”To, fa, ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya halicce ka, ya Yaƙub, shi da ya siffanta ka, ya Isra’ila, “Kada ka ji tsoro, gama na fanshe ka; na kira ka da suna; kai nawa ne. Sa’ad da kuka bi ta ruwaye, zan kasance tare da ku; sa’ad da kuka bi ta koguna, ba za su kwashe ku ba. Sa’ad da kuke tafiyata cikin wuta, ba za tă ƙone ku ba; harsunan wutar ba za su ƙone ku ba.
”Ni ne na siffanta haske na kuma halicci duhu, ni ne nake ba da nasara in kuma jawo bala’i; ni, Ubangiji ne ke aikata dukan waɗannan abubuwa.
”Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura ni ne shi, ni ne shi wanda zai lura da ku. Na yi ku zan kuma riƙe ku; zan lura da ku in kuma kuɓutar da ku.
”Duba, na tace ku, ko da yake ba kamar azurfa ba; na gwada ku cikin wutar wahala.
”Ba za su taɓa jin yunwa ko ƙishi ba, ba kuwa zafin hamada ko rana ta buge su ba. Shi da ya yi musu jinƙai zai jagorance su ya kuma bishe su kusa da maɓulɓulan ruwa.
”Ku yi sowa don farin ciki, ya ku sammai; ki yi farin ciki, ya ke duniya; ku ɓarke da waƙa, ya ku duwatsu! Gama Ubangiji ya ta’azantar da mutanensa zai kuma ji tausayin mutanensa da suke shan wahala.
”Duba, na zāna ki a tafin hannuwana; katangarki kullum suna a gabana.
”Tabbatacce Ubangiji zai ta’azantar da Sihiyona zai kuma duba da tausayi a kan dukan kufanta; zai sa hamadanta ta zama kamar Eden, ƙeƙasasshiyar ƙasarta kamar lambun Ubangiji. Za a sami farin ciki da murna a cikinta, godiya da ƙarar rerawa.
”Waɗanda Ubangiji ya fansar za su dawo. Za su shiga Sihiyona da waƙoƙi; madawwamin farin ciki zai rufe kansu da rawani. Murna da farin ciki zai cika su, baƙin ciki da nishi zai ɓace. “Ni kaɗai ne na ta’azantar da ku. Wane ne ku da kuke tsoron mutane masu mutuwa, ’ya’yan mutane waɗanda suke ciyawa ne kawai,
”Wa ya gaskata saƙonmu kuma ga wa hannun Ubangiji ya bayyana? Ya yi girma kamar dashe marar ƙarfi, kamar saiwa kuma daga ƙeƙasasshiyar ƙasa. Ba shi da kyan gani ko wani makamin da zai ja hankalinmu, babu wani abin da yake da shi da zai sa mu yi sha’awarsa. Mutane suka rena shi suka ƙi shi, mutum ne cike da baƙin ciki, ya kuma saba da wahala. Kamar wanda mutane suna ɓuya fuskokinsu daga gare shi aka rena shi aka yi banza da shi. Tabbatacce ya ɗauki cututtukanmu ya kuma daure da baƙin cikinmu duk da haka muka ɗauka Allah ya hukunta shi ne, ya buge shi ya kuma sa ya sha azaba. Amma aka yi masa rauni saboda laifofinmu, aka ƙuje shi saboda kurakuranmu; hukuncin da ya kawo mana salama ya kasance a kansa, kuma ta wurin mikinsa ya sa muka warke. Dukanmu, muna kama da tumakin da suka ɓata, kowannenmu ya kama hanyarsa; Ubangiji kuwa ya sa hukunci ya auko a kansa hukuncin da ya wajaba a kanmu. Aka wulaƙanta shi aka kuma yi masa azaba, duk da haka bai buɗe bakinsa ba; aka kai shi kamar ɗan rago zuwa wurin yanka, kuma kamar tunkiya a gaban masu askinta tana shiru, haka bai buɗe bakinsa ba. Da wulaƙanci da kuma hukunci aka ɗauke shi aka tafi. Wa kuwa zai yi maganar zuriyarsa? Gama an kawar da shi daga ƙasar masu rai; saboda laifin mutanena aka kashe shi. Aka yi jana’izarsa tare da mugaye, aka binne shi tare da masu arziki, ko da yake bai taɓa yin wani tashin hankali ba, ko a sami ƙarya a bakinsa. Duk da haka nufin Ubangiji ne a ƙuje shi yă kuma sa yă sha wahala, kuma ko da yake Ubangiji ya sa ransa ya zama hadaya don zunubi, zai ga zuriyarsa zai kuma kawo masa tsawon rai, nufin Ubangiji kuma zai yi nasara a hannunsa. Bayan wahalar ransa, zai ga hasken rai, ya kuma gamsu; ta wurin saninsa bawana mai adalci zai ’yantar da mutane masu yawa, zai kuma ɗauki laifofinsu. Saboda haka zan ba shi rabo tare da manya, zai kuma raba ganima tare da masu ƙarfi, domin ya ba da ransa har mutuwa, aka kuma lissafta shi tare da masu laifofi. Gama ya ɗauki zunubin mutane masu yawa, ya kuma yi roƙo saboda laifofinsu.
”“Kada ki ji tsoro; ba za ki sha kunya ba. Kada ki ji tsoron wulaƙanci, ba za a ƙasƙantar da ke ba. Za ki manta da kunyar ƙuruciyarki ba kuwa za ki tuna da zargin zaman gwauruwarki ba.
”Da adalci za a kafa ke. Zalunci zai yi nesa da ke; ba za ki kasance da wani abin da za ki ji tsoro ba. Za a kawar da duk wani abin banrazana; ba zai yi kusa da ke ba.
”ba makamin da aka ƙera don yă cuce ki da zai yi nasara, za ki kuma mayar da magana ga duk wanda ya zarge ki. Wannan ne gādon bayin Ubangiji, kuma wannan ita ce nasararsu daga gare ni,” in ji Ubangiji.
”Za ku fita da farin ciki a kuma bi da ku da salama; duwatsu da tuddai za su ɓarke da waƙa a gabanku, dukan itatuwan jeji kuma za su tafa hannuwansu.
”Waɗanda suke aikata abin da yake daidai sukan shiga da salama; sukan huta yayinda suka kwanta cikin kabari.
”Gama abin da Maɗaukaki da kuma Mai daraja ya faɗa wanda yake raye har abada, wanda sunansa mai tsarki ne, “Ina zama a bisa da kuma a tsattsarkan wuri, amma kuma tare da shi wanda yake mai halin tuba mai tawali’u a ruhu, don in farfaɗo da ruhu mai tawali’u in kuma farfaɗo da zuciyar mai halin tuba.
”Na ga al’amuransa, amma zan warkar da shi; zan bi da shi in mayar da ta’aziyya a gare shi, ina ƙirƙiro yabo a leɓunan masu makoki a Isra’ila. Salama, salama, ga waɗanda suke nesa da kuma kusa,” in ji Ubangiji. “Zan kuma warkar da su.”
”Irin azumin da na zaɓa ke nan, rana guda kawai don mutum ya ƙasƙantar da kansa? Sunkuyar da kanku kamar iwa kawai kuna kuma kwance a tsummoki da toka? Abin da kuke kira azumi ke nan rana yardajje ga Ubangiji? “Irin azumin da na zaɓa shi ne, a kunce sarƙoƙin rashin adalci a kuma kunce igiyoyin karkiya, a ’yantar da waɗanda ake zalunta a kuma kakkarye kowace karkiya? Ba shi ne ku rarraba abincinku da mayunwata ku kuma tanada wa matalauta masu yawo mahalli, sa’ad da kuka ga wanda yake tsirara, ku yi masa sutura, kada kuma ku ba wa namanku da jininku baya?
”Sa’an nan haskenku zai keto kamar ketowar alfijir, warkarwarku kuma zai bayyana nan da nan; sa’an nan adalcinku zai tafi a gabanku, ɗaukakar Ubangiji kuma zai tsare ku daga baya. Sa’an nan za ku yi kira, Ubangiji kuma zai amsa; za ku yi kuka don neman taimako, zai kuwa ce ga ni nan. “In kuka kawar da karkiyar zalunci, kuka daina nuna wa juna yatsa da kuma faɗar mugayen maganganu, in kuma kuka ɗauki lokaci kuka ƙosar da mayunwata kuka kuma biya bukatun waɗanda suke shan tsanani, sa’an nan ne haskenku zai haskaka cikin duhu darenku kuma zai zama kamar tsakar rana. Ubangiji zai bishe ku kullum; zai biya muku bukatunku a ƙasa mai zafin rana ya kuma ƙarfafa ƙasusuwanku. Za ku zama kamar lambun da aka yi masa banruwa, kamar rafin da ruwansa ba ya ƙafewa.
”Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina, domin Ubangiji ya shafe ni domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta. Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci, don in yi shelar ’yanci don ɗaurarru in kuma kunce ’yan kurkuku daga duhu don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangiji da kuma ranar ɗaukan fansar Allahnmu, don in ta’azantar da dukan waɗanda suke makoki, in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona, in maido musu rawani mai kyau a maimako na toka, man murna a maimako na makoki, da kuma rigar yabo a maimako na ruhun fid da zuciya. Za a ce da su itatuwan oak na adalci, shukin Ubangiji don bayyana darajarsa.
”Cikin dukan damuwarsu shi ma ya damu, mala’ikan da yake gabansa ya cece su. Cikin ƙauna da jinƙai ya fanshe su; ya kuma ɗaga su ya riƙe su dukan kwanakin dā
”“Ga shi, na halicci sabuwar sama da kuma sabuwar duniya. Abubuwa na dā za a manta da su, ba kuwa za a ƙara tuna da su ba. Amma ku yi murna ku kuma yi farin ciki har abada a abin da na halitta, gama zan halicci Urushalima ta zama abin murna mutanenta kuwa abin farin ciki. Zan yi farin ciki a kan Urushalima in kuma yi murna saboda mutanena; a can ba za a ƙara jin karar makoki da na kuka ba.
”Kamar yadda uwa takan ta’azantar da ɗanta haka zan ta’azantar da ku; za ku kuma ta’azantu a Urushalima.”
”“Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji, wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji. Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi. Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo; ganyayensa kullum kore suke. Ba shi da damuwa a shekarar fări ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.”
”Ka warkar da ni, ya Ubangiji, zan kuwa warke; ka cece ni zan kuwa cetu, gama kai ne nake yabo.
”Gama na san shirye-shiryen da na yi muku,” in ji Ubangiji, “shirye-shiryen cin gaba ba na cutarwa ba, shirye-shiryen ba ku sa zuciya da kuma na nan gaba. Sa’an nan za ku kira gare ni ku zo ku kuma yi addu’a gare ni, zan kuwa ji ku. Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku.
”Amma zan mayar muku da lafiya in kuma warkar da mikinku,’ in ji Ubangiji, ‘domin ana ce da ku yasassu, Sihiyona wadda ba wanda ya kula da ita.’
”Zan wartsake waɗanda suka gaji in kuma ƙosar da waɗanda ransu ya yi yaushi.” A kan wannan na farka na duba kewaye. Barcina ya yi mini daɗi.
”“ ‘Duk da haka, zan kawo lafiya da warkarwa gare ta; zan warkar da mutanena in kuma wadata su da salama da zama lafiya.
”Na tuna da azabata da kuma sintiri, da na yi ta yi da ɗacin rai. Na tuna su sosai, sai kuma na ji ba daɗi a raina.
”Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba; gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa. Sababbi ne kowace safiya; amincinka kuwa mai girma ne. Na ce wa kaina, “ Ubangiji shi ne nawa; saboda haka zan jira shi.” Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa, ga kuma wanda yake neman shi; yana da kyau ka jira shiru domin samun ceton Ubangiji.
”Ko da ya kawo ɓacin rai, zai nuna tausayi sosai, ƙaunarsa tana da yawa. Gama ba haka kawai yake kawo wahala ko ɓacin rai ga ’yan adam ba.
”Ka zo kusa lokacin da na kira ka, kuma ka ce mini, “Kada ka ji tsoro.” Ya Ubangiji, ka goyi bayana; ka fanshi raina.
”Fatar jikinmu ta yi zafi kamar murhu, muna jin zazzaɓi domin yunwa.
”Zan kula da su a wurin kiwo mai kyau, kuma ƙwanƙolin duwatsun Isra’ila ne zai zama wurin kiwonsu. Za su kwanta a wurin kiwo mai kyau, a can kuma za su yi kiwo a wurin kiwo mai kyau a kan duwatsun Isra’ila. Ni kaina zan lura da tumakina in kuma sa su kwanta, in ji Ubangiji Mai Iko Duka. Zan nemi ɓatattuna in kuma dawo da waɗanda suka yi makuwa. Zan ɗaura raunin waɗanda suka ji ciwo in kuma ƙarfafa marasa ƙarfi, amma zan hallaka ƙarfafa da kuma masu ƙiba. Zan yi kiwo tumaki da adalci.
”Sa’an nan Nebukadnezzar ya ce, “Yabo ya tabbata ga Allahn Shadrak, Meshak da Abednego wanda ya aiko da mala’ikansa ya ceci bayinsa da suka dogara matuƙa a gare shi, suka ki bin umarnin sarki kuma su na a shirye domin su ba da ransu da suka ƙi bauta ko su yi sujada ga wani allah sai dai Allahnsu.
”Allahna ya aiko da mala’ikansa, ya kuwa rufe bakunan zakoki. Ba su yi mini rauni ba, gama an same ni marar laifi ne a gabansa. Ban kuwa taɓa yin wani abu marar kyau a gabanka ba, ya sarki.” Sai sarki ya cika da murna ƙwarai, ya kuma yi umarni a ciro Daniyel daga ramin zakoki. Kuma da aka fito da Daniyel daga ramin, ba a sami wani rauni a jikinsa ba, domin ya dogara ga Allahnsa.
”Yakan kuɓutar ya kuma ceci; yana yin alamu da al’ajabai a sama da kuma a duniya. Shi ya ceci Daniyel daga ikon zakoki.”
”“Ku zo, mu koma ga Ubangiji. Ya yayyage mu kucu-kucu amma zai warkar da mu; ya ji mana ciwo amma zai daure mana miyakunmu. Bayan kwana biyu zai rayar da mu, a rana ta uku zai tashe mu, don mu rayu a gabansa.
”“Zan fanshe su daga ikon kabari; zan cece su daga mutuwa. Ina annobanki, ya mutuwa? Ina hallakarka, ya kabari? “Ba zan ji tausayi ba,
”“Zan mayar muku da abin da fāra suka ci a waɗannan shekaru waɗanda ɗango da fāra masu gaigayewa, da kuma sauran fāra da tarin fāra babban mayaƙan da na aika don su fāɗa muku. Za ku sami a wadace ku ci, har sai kun ƙoshi, za ku kuma yabi sunan Ubangiji Allahnku, wanda ya yi muku ayyukan banmamaki; mutanena ba za su ƙara shan kunya ba.
”Ya ce, “A cikin damuwata na yi kira ga Ubangiji, ya kuwa amsa mini. Daga cikin zurfi kabari na yi kiran neman taimako, ka kuwa saurari kukata.
”Ubangiji Allahnki yana tare da ke, mai iko ne don ceto. Zai yi matuƙar farin ciki da ke, zai rufe ki da ƙaunarsa, zai yi farin ciki da ke ta wurin rerawa.”
”Amma ku da kuke girmama sunana, ranar adalci za tă fito tare da warkarwa a fikafikanta. Za ku kuwa fita kuna tsalle kamar ’yan maruƙan da aka sake daga garke.
”Da Hiridus ya gane cewa Masanan nan sun yi masa wayo, sai ya husata ƙwarai, ya yi umarni cewa a karkashe dukan ’yan yara maza da suke a Betlehem da kewayenta, daga masu shekara biyu zuwa ƙasa, bisa ga lokacin da ya sami labarin daga Masanan nan. Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika, cewa, “An ji murya a Rama, tana kuka da makoki mai tsanani, Rahila ce take kuka domin ’ya’yanta, an kāsa ta’azantar da ita, don ba su.”
”Yesu ya zazzaga dukan Galili, yana koyarwa a cikin majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin sama, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiyar mutane. Labarinsa ya bazu ko’ina a Suriya, mutane kuwa suka kawo masa dukan waɗanda suke fama da cututtuka iri-iri, da waɗanda suke da zafin ciwo, da masu aljanu, da waɗanda suke masu farfaɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.
”‹“Masu albarka ne waɗanda suke matalauta a ruhu,› ‹gama mulkin sama nasu ne.› ‹Masu albarka ne waɗanda suke makoki,› ‹gama za a yi musu ta’aziyya.›
”‹Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu don gani an yi adalci,› ‹gama mulkin sama nasu ne.› ‹“Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni.› ‹Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.›
”‹Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku›‹kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a,›
”‹“Saboda haka, ina gaya muku, kada ku damu game da rayuwarku, game da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha; ko kuma game da jikinku, game da abin da za ku sa. Ashe, rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba?› ‹Ku dubi tsuntsayen sararin sama mana; ba sa shuki ko girbi ko ajiya a rumbuna, duk da haka, Ubanku na sama yana ciyar da su. Ashe, ba ku fi su daraja nesa ba?› ‹Wane ne a cikinku ta wurin damuwa zai iya ƙara wa rayuwarsa ko sa’a ɗaya›‹?› ‹“Me ya sa kuke damuwa a kan riguna? Ku dubi yadda furannin jeji suke girma mana. Ba sa aiki ko saƙa.› ‹Duk da haka ina gaya muku ko Solomon cikin dukan darajarsa bai sa kayan adon da ya kai na ko ɗaya a cikinsu ba.› ‹In haka Allah yake yi wa ciyawar jeji sutura, wadda yau tana nan, gobe kuwa a jefa a cikin wuta, ba zai ma fi yi muku sutura ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya?› ‹Don haka, kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci?’ Ko, ‘Me za mu sha?’ Ko kuma, ‘Me za mu sa?’› ‹Gama marasa sanin Allah suna fama neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu.› ‹Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa.› ‹Saboda haka kada ku damu game da gobe, gama gobe zai damu da kansa. Damuwar yau ma ta isa wahala.›
”‹“Ku roƙa za a ba ku; ku nema za ku samu; ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa.› ‹Gama duk wanda ya roƙa, akan ba shi; wanda ya nema kuwa, yakan samu, wanda kuma ya ƙwanƙwasa, za a buɗe masa ƙofa.›
”Wani mutum mai kuturta ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “Ubangiji, in kana so, kana iya tsabtacce ni.” Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin. Ya ce, ‹“Ina so, ka tsabtacce!”› Nan da nan aka warkar da shi daga kuturtarsa.
”Da Yesu ya shiga Kafarnahum, sai wani jarumi ya zo wurinsa, yana neman taimako. Ya ce, “Ubangiji, bawana yana kwance a gida shanyayye, yana kuma shan azaba ƙwarai.” Yesu ya ce masa, ‹“Zan je in warkar da shi.”› Jarumin ya amsa, “Ubangiji, ban cancanci in sa ka zo gidana ba, ka dai yi magana kawai, bawana zai warke. Gama ni kaina mutum ne a ƙarƙashin iko, da kuma sojoji a ƙarƙashina. Nakan ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai yă tafi; wancan kuma, ‘Zo nan,’ sai yă zo. Nakan ce wa bawana, ‘Yi wannan,’ sai kuwa yă yi.” Da Yesu ya ji wannan, sai ya yi mamaki ya kuma ce wa waɗanda suke binsa, ‹“Gaskiya nake gaya muku, ban taɓa samun wani a Isra’ila da bangaskiya mai girma haka ba.› ‹Ina kuma gaya muku da yawa za su zo daga gabas da kuma yamma, su ɗauki wuraren zamansu a biki tare da Ibrahim, Ishaku, da Yaƙub a cikin mulkin sama.› ‹Amma za a jefar da ’ya’yan mulki waje, zuwa cikin baƙin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.”› Sa’an nan Yesu ya ce wa jarumin, ‹“Je ka! Za a yi bisa ga bangaskiyarka.”› A daidai wannan lokaci bawansa kuwa ya warke.
”Da Yesu ya zo cikin gidan Bitrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance a gado tana da zazzaɓi. Ya taɓa hannunta sai zazzaɓin ya sake ta, ta kuwa tashi ta fara yin masa hidima.
”Da yamma ta yi, aka kawo masa masu aljanu da yawa, ya kuwa fitar da ruhohin ta wurin magana, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya. Wannan ya faru ne domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa, “Ya ɗebi rashin lafiyarmu, ya kuma ɗauki cututtukanmu.”
”Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci. Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, “Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!” Ya amsa ya ce, ‹“Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?”› Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya.
”Da ya isa ɗayan gefen a yankin Gadarenawa (ko kuwa Gerasenawa), sai ga mutum biyu masu aljanu suna fitowa daga kaburbura suka tarye shi. Su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bin wannan hanya. Suka yi ihu suka ce, “Me ya haɗa ka da mu, Ɗan Allah?” Ka zo ne nan don ka ji mana kafin lokaci yă yi? Nesa kaɗan da su kuwa akwai babban garken aladu da yake kiwo. Aljanun suka roƙi Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.” Ya ce musu, ‹“Ku tafi!”› Sai suka fita suka shiga cikin aladun, dukan garken kuwa ya gangara a guje daga kan tudun zuwa cikin tafkin aladun kuma suka mutu a cikin ruwa.
”Waɗansu mutane suka kawo masa wani shanyayye, kwance a tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, ‹“Kada ka damu saurayi, an gafarta maka zunubanka.”› Da jin wannan, waɗansu malaman dokoki suka ce wa juna, “Wannan mutum yana yin saɓo!” Sane da tunaninsu, Yesu ya ce, ‹“Me ya sa kuke da mugun tunani a zuciyarku?› ‹Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya?’› ‹Amma don ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.”› Sai ya ce wa shanyayyen, ‹“Tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.”› Mutumin kuwa ya tashi ya tafi gida.
”Da jin wannan, Yesu ya ce, ‹“Ai, ba masu lafiya ba ne su bukatar likita, sai dai marasa lafiya.›
”A daidai wannan lokaci sai ga wata mace wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini ta raɓo ta bayansa ta taɓa gefen rigarsa. Ta ce a ranta, “Ko da rigarsa ce kawai na taɓo, zan warke.” Yesu ya juya ya gan ta. Sai ya ce, ‹“Kada ki damu diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke.”› Nan take macen ta warke.
”Da Yesu ya shiga gidan mai mulkin ya ga masu busan sarewa da taro mai hayaniya, sai ya ce, ‹“Ku ba da wuri. Ai, yarinyar ba tă mutu ba, tana barci ne.”› Amma suka yi masa dariya. Bayan an fitar da taron waje, sai ya shiga ciki ya kama yarinyar a hannu, ta kuwa tashi.
”Da Yesu ya fita daga can, sai waɗansu makafi biyu suka bi shi, suna kira, suna cewa, “Ka yi mana jinƙai, Ɗan Dawuda!” Da ya shiga cikin gida, sai makafin nan suka zo wurinsa, ya kuma tambaye su, ‹“Kun gaskata cewa ina iya yin wannan?”› Suka amsa suka ce, “I, Ubangiji.” Sa’an nan ya taɓa idanunsu ya ce, ‹“Bisa ga bangaskiyarku a yi muku haka”;› sai idanunsu suka buɗe. Yesu ya gargaɗe su sosai ya ce, ‹“Ku lura kada wani yă san wani abu game da wannan.”›
”Yayinda suke fitowa, sai aka kawo wa Yesu wani mutum mai aljani, da ba ya iya magana. Sa’ad da aka fitar da aljanin kuwa, sai beben ya yi magana. Taron suka yi mamaki suka ce, “Ba a taɓa ganin irin wannan abu a Isra’ila ba.”
”Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.
”Sai ya kira almajiransa goma sha biyu wurinsa ya kuma ba su iko su fitar aljanu, su kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.
”‹Ku warkar da marasa lafiya, ku tā da matattu, ku tsabtacce kutare, ku kuma fitar da aljanu. A kyauta kuka samu, ku kuma bayar a kyauta.›
”‹Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta.› ‹Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa ba da yardar Ubanku.› ‹Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su.› ‹Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.›
”‹Duk mai son adana ransa zai rasa shi, duk wanda kuwa ya rasa ransa saboda ni zai same shi.›
”‹Makafi suna gani, guragu suna tafiya, ana warkar da waɗanda suke da kuturta, kurame suna ji, ana tā da matattu, ana kuma yi wa matalauta wa’azin labari mai daɗi.›
”‹“Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu.› ‹Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku.› ‹Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”›
”a nan kuwa akwai wani mutum mai shanyayyen hannu. Don neman dalili su zargi Yesu, sai suka tambaye shi suka ce, “Ya dace a warkar a ranar Asabbaci?” Ya ce musu, ‹“In waninku yana da tunkiya, ta kuma fāɗa a rami ran Asabbaci, ba zai cire ta daga ramin ba?› ‹Sau nawa mutum ya fi tunkiya daraja! Saboda haka ya dace a aikata alheri ran Asabbaci.”› Sa’an nan ya ce wa mutumin, ‹“Miƙa hannunka.”› Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye, kamar dai ɗayan.
”Da ya gane wannan, sai Yesu ya janye daga wurin. Da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da dukan masu ciwonsu,
”Sai aka kawo masa wani bebe kuma makaho mai aljani, Yesu kuwa ya warkar da shi, har ya iya magana ya kuma sami ganin gari.
”‹Wanda ya karɓi irin da ya fāɗi a wuraren duwatsu kuwa, shi ne mutumin da yakan ji maganar, nan da nan kuwa yă karɓe ta da murna.› ‹Sai dai da yake ba shi da saiwa, yakan ɗan jima kaɗan kawai. Da wata wahala ko tsanani ya auko masa saboda maganar, nan da nan sai yă ja da baya.›
”Da Yesu ya sauka ya kuma ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu ya kuma warkar da marasa lafiyarsu.
”Da mutanen wurin suka gane da Yesu, sai suka kai labari a ko’ina a ƙauyukan da suke kewaye. Mutane suka kawo masa dukan marasa lafiyarsu suka kuwa roƙe shi yă bar marasa lafiya su taɓa ko da gefen rigarsa kawai, duk waɗanda suka taɓa shi kuwa suka warke.
”Wata mutuniyar Kan’ana daga wajajen ta zo wurinsa, tana ihu tana cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai! ’Yata tana shan wahala ƙwarai daga aljanin da yake cikinta.” Yesu bai ce mata uffam ba. Saboda haka almajiransa suka zo wurinsa suka roƙe shi suka ce, “Ka kore ta tă tafi, tana ta binmu tana damunmu da ihu.” Ya amsa ya ce, ‹“An aiko ni wurin ɓatattun tumakin Isra’ila ne kaɗai.”› Sai macen ta zo ta durƙusa a gabansa ta ce, “Ubangiji, ka taimake ni!” Ya amsa ya ce, ‹“Ba daidai ba ne a ɗauki abincin yara a jefa wa karnukansu.”› Ta amsa, ta ce, “I, Ubangiji, amma karnuka ma sukan ci gutsattsarin da sukan fāɗi daga teburin maigidansu.” Sa’an nan Yesu ya amsa ya ce, ‹“Mace, kina da bangaskiya mai yawa! An biya miki bukatarki.”› ’Yarta kuwa ta warke nan take.
”Taron mutane mai girma kuwa suka zo wurinsa, suna kawo masa guragu, makafi, shanyayyu, kurame da dai waɗansu da yawa, suka kuwa kwantar da su a gabansa; ya kuma warkar da su. Mutanen kuwa suka yi mamaki sa’ad da suka ga kurame suna magana, shanyayyu suna samun lafiya, guragu suna takawa, makafi kuma suna ganin gari. Sai suka yabi Allah na Isra’ila.
”Da suka isa wajen taron, sai wani mutum ya zo ya durƙusa a gabansa. Ya ce, “Ubangiji, ka yi wa ɗana jinƙai. Yana da farfaɗiya yana kuma shan wahala ƙwarai. Ya sha fāɗuwa cikin wuta ko ruwa. Na kuma kawo shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba.” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Ya ku zamani marasa bangaskiya da kuma masu taurinkai, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe kuma zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron a nan.”› Yesu ya tsawata wa aljanin, ya kuwa rabu da yaron, nan take yaron ya warke.
”Ya amsa ya ce, ‹“Saboda kuna da ƙarancin bangaskiya sosai. Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiyar da take ƙanƙanuwa kamar ƙwayar mustad, za ku iya ce wa wannan dutse, ‘Matsa daga nan zuwa can,’ zai kuwa matsa. Babu abin da zai gagare ku.”›
”‹In hannunka ko ƙafarka yana sa ka zunubi, yanke shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da hannu ko ƙafa ɗaya da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu da a jefar da kai cikin madawwamiyar wuta da hannuwa biyu ko ƙafafu biyu.› ‹In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da ido ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta da idanunka biyu.›
”‹Haka ma Ubanku da yake cikin sama ba ya so ko ɗaya daga cikin ƙananan nan yă ɓace.›
”Makafi biyu kuwa suna zaune a bakin hanya, da suka ji cewa Yesu yana wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!” Mutane suka tsawata musu, suka ce musu su yi shiru. Sai suka ƙara ɗaga murya suna cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!” Yesu ya tsaya ya kira su. Ya tambaye su, ‹“Me kuke so in yi muku?”› Suka amsa suka ce, “Ubangiji, muna so mu sami ganin gari.” Sai Yesu ya ji tausayinsu, ya taɓa idanunsu. Nan da nan kuwa suka sami ganin gari, suka kuma bi shi.
”Makafi da guragu suka zo wurinsa a haikali, ya kuwa warkar da su.
”Yesu ya amsa ya ce, ‹“Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiya, ba kuwa da wata shakka ba, ba kawai za ku iya yin abin da aka yi wa itacen ɓauren nan ba, amma za ku ma iya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka jefa kanka cikin teku,’ sai yă faru.› ‹In kun gaskata, za ku karɓi duk abin da kuka roƙa a cikin addu’a.”›
”‹“Sa’an nan za a bashe ku don a tsananta muku a kuma kashe ku, dukan al’ummai za su ƙi ku saboda ni.› ‹A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna,› ‹annabawan ƙarya da yawa za su firfito su kuma ruɗi mutane da yawa.› ‹Saboda ƙaruwar mugunta, ƙaunar yawanci za tă yi sanyi,› ‹amma duk wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.›
”‹Gama a lokacin za a yi wata matsananciyar wahala, wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu ba kuwa za a ƙara yi ba.› ‹“Da ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da babu wani da zai tsira, amma saboda zaɓaɓɓun nan, za a taƙaita kwanakin.›
”‹da nake bukatar tufafi, kun yi mini sutura, da na yi rashin lafiya, kun lura da ni, da nake kurkuku, kun ziyarce ni.’›
”Bitrus ya furta, “Ko da ma zan mutu ne tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Dukan sauran almajiran ma suka faɗa haka.
”Ya ɗauki Bitrus da ’ya’ya biyun nan na Zebedi tare da shi, sai ya fara baƙin ciki, ya kuma damu. Sai ya ce musu, ‹“Raina yana cike da baƙin ciki har kamar zan mutu. Ku dakata a nan, ku kuma yi tsaro tare da ni.”› Da ya yi gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a ya ce, ‹“Ubana, in mai yiwuwa ne, a ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba nufina ba, sai naka.”›
”Sai ya sakar musu Barabbas. Amma ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.
”Bayan da suka gicciye shi, sai suka raba tufafinsa a tsakaninsu ta wurin jefa ƙuri’a.
”Wajen sa’a ta tara, Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, ‹“Eloi, Eloi,› ‹lama sabaktani?”› (Wato, ‹“Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”›).
”Nan take, sai wani mutum mai mugun ruhu a majami’arsu, ya ɗaga murya ya ce, “Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki nan na Allah!” Yesu ya tsawata masa ya ce, ‹“Yi shiru! Fita daga cikinsa!”› Sai mugun ruhun ya jijjiga mutumin da ƙarfi, ya fita daga jikinsa da ihu.
”Surukar Siman tana kwance da zazzaɓi, sai suka gaya wa Yesu game da ita. Sai ya je wajenta, ya kama hannunta, ya ɗaga ta. Zazzaɓin kuwa ya sāke ta, ta kuma yi musu hidima.
”A wannan yamma, bayan fāɗuwar rana, mutane suka kawo wa Yesu dukan marasa lafiya, da masu aljanu. Duk garin ya taru a ƙofar gidan. Yesu kuwa ya warkar da marasa lafiya da yawa da suke da cututtuka iri-iri. Ya kuma fitar da aljanu da yawa, amma bai yarda aljanun suka yi magana ba, don sun san wane ne shi.
”Sai ya tafi ko’ina a Galili, yana wa’azi a majami’unsu, yana kuma fitar da aljanu. Wani mutum mai kuturta ya zo wurinsa, ya durƙusa ya roƙe shi ya ce, “In kana so, za ka iya tsabtacce ni.” Cike da tausayi, sai Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin ya ce, ‹“Na yarda, ka tsabtacce!”› Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi, ya kuma warke.
”Waɗansu mutum huɗu suka zo wajensa ɗauke da wani shanyayye. Da ba su iya kai shi wurin Yesu ba, saboda taron, sai suka buɗe rufin gidan saman, bisa daidai inda Yesu yake. Bayan da suka huda rami, sai suka saukar da shanyayyen, kwance a kan tabarmarsa. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, ‹“Saurayi, an gafarta zunubanka.”› To, waɗansu malaman dokoki da suke zaune a wurin, suka yi tunani a zuciyarsu, suna cewa, “Me ya sa mutumin nan yake magana haka? Yana saɓo! Wane ne zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?” Nan da nan, Yesu ya gane a ruhunsa abin da suke tunani a zuciyarsu, sai ya ce musu, ‹“Me ya sa kuke tunanin waɗannan abubuwa?› ‹Wanne ya fi sauƙi, a ce wa shanyayyen, ‘An gafarta zunubanka,’ ko a ce, ‘Tashi, ɗauki tabarmarka ka yi tafiya’?› ‹Amma don ku san cewa, Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.”› Sai ya ce wa shanyayyen, ‹“Ina ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka, ka tafi gida.”› Sai ya tashi, ya ɗauki tabarmarsa, ya yi tafiyarsa a gabansu duka. Wannan ya ba wa kowa mamaki, suka kuma ɗaukaka Allah suna cewa, “Ba mu taɓa ganin abu haka ba!”
”Da jin wannan, Yesu ya ce musu, ‹“Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya. Ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.”›
”Wani lokaci, da ya sāke shiga majami’a, sai ga wani mutum mai shanyayyen hannu. Waɗansu daga cikin mutane suna neman dalilin zargin Yesu, sai suka zuba masa ido, su ga ko zai warkar da shi a ranar Asabbaci. Yesu ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, ‹“Tashi ka tsaya a gaban kowa.”› Sai Yesu ya tambaye su ya ce, ‹“Me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci, a aikata alheri, ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a yi kisa?”› Amma suka yi shiru. Sai ya kalle su da fushi, don taurin zuciyarsu ya ɓata masa rai sosai. Sai ya ce wa mutumin, ‹“Miƙo hannunka.”› Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.
”Gama ya warkar da mutane da yawa, masu cututtuka suka yi ta ƙoƙarin zuwa gaba, don su taɓa shi. Duk sa’ad da mugayen ruhohi suka gan shi, sai fāɗi a gabansa, su ɗaga murya, su ce, “Kai Ɗan Allah ne.”
”Ya naɗa sha biyu, ya kira su manzanni don su kasance tare da shi, domin kuma yă aike su yin wa’azi, don kuma su sami ikon fitar da aljanu.
”‹Waɗansu suna kama da irin da aka shuka a wurare masu duwatsu, sukan ji maganar Allah, sukan kuma karɓe ta nan da nan da farin ciki.› ‹Amma da yake ba su da saiwa, ba sa daɗewa. Da wahala ko tsanani ya tashi saboda maganar, nan da nan, sai su ja da baya.›
”Sai babban hadari mai iska ya tashi, raƙuman ruwa suna ta bugun jirgin ruwan, har jirgin ruwan ya kusa yă cika da ruwa. Yesu kuwa yana can baya, yana barci a kan katifa. Sai almajiran suka tashe shi suka ce masa, “Malam, ba ka kula ba ko mu nutse?” Sai ya farka ya tsawata wa iskar, ya ce wa raƙuman ruwan, ‹“Shiru! Ku natsu!”› Sai iskar ta kwanta, kome kuma ya yi tsit. Sai ya ce wa almajiransa, ‹“Don me kuke tsoro haka? Har yanzu ba ku da bangaskiya ne?”›
”Da Yesu ya sauka daga jirgin ruwa, sai wani mutum mai mugun ruhu ya fito daga kaburbura, ya tarye shi. Wannan mutumin ya mai da kaburbura gidansa. Kuma ba wanda ya iya daure shi, ko da sarƙa ma. Gama an sha daure shi hannu da ƙafa da sarƙa, amma yakan tsintsinke sarƙar, yă kuma karye ƙarafan da suke ƙafafunsa. Ba wanda yake da ƙarfin da zai iya yă riƙe shi. Dare da rana, sai yă dinga kuka yana ƙuƙƙuje jikinsa da duwatsu a cikin kaburbura da kan tuddai. Da ya hangi Yesu daga nesa, sai ya ruga da gudu, ya zo ya durƙusa a gabansa. Ya yi ihu da babbar murya ya ce, “Ina ruwanka da ni Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ka rantse da Allah cewa ba za ka ba ni azaba ba!” Gama Yesu ya riga ya ce masa, ‹“Ka fita daga jikin mutumin nan, kai mugun ruhu!”› Sai Yesu ya tambaye shi ya ce, ‹“Mene ne sunanka?”› Sai ya amsa ya ce, “Sunana Lejiyon, wato, ‘Tuli,’ domin muna da yawa.” Sai ya yi ta roƙon Yesu, kada yă kore su daga wurin. A kan tudun da yake nan kusa kuwa, akwai wani babban garken aladu, suna kiwo. Sai aljanun suka roƙi Yesu, suka ce, “Tura mu cikin aladun nan, ka bari mu shiga cikinsu.” Ya kuwa yarda musu, sai mugayen ruhohin suka fita suka shiga cikin aladun. Garken kuwa, yana da kusan aladu dubu biyu, suka gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, suka nutse.
”A can kuwa akwai wata mace, wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini. Ta kuma sha wahala ƙwarai a hannun likitoci da yawa, har ta kashe duk abin da take da shi, amma maimakon samun sauƙi, sai ciwon ya ƙara muni. Da ta ji labarin Yesu, sai ta zo ta bayansa, a cikin taron, ta taɓa rigarsa, domin ta yi tunani cewa, “Ko da rigunarsa ma na taɓa, zan warke.” Nan da take, zub da jininta ya tsaya, sai ta ji a jikinta ta rabu da shan wahalarta.
”Yayinda Yesu yana cikin magana, sai waɗansu mutane daga gidan Yayirus, mai mulkin majami’a, suka zo suka ce, “Diyarka ta rasu. Kada ma ka wahal da Malam.” Yesu bai kula da abin da suka faɗa ba, sai ya ce wa mai mulkin majami’ar, ‹“Kada ka ji tsoro, ka gaskata kawai.”› Bai bar kowa ya bi shi ba, sai Bitrus, Yaƙub da Yohanna ɗan’uwan Yaƙub. Da suka iso gidan mai mulkin majami’ar, sai Yesu ya ga ana hayaniya, mutane suna kuka da kururuwa. Sai ya shiga ciki, ya ce musu, ‹“Mene ne dalilin wannan hayaniya da kuka? Yarinyar ba mutuwa ne ta yi ba, barci take yi.”› Sai suka yi masa dariya. Bayan ya fitar da su duk waje, sai ya ɗauki mahaifin da mahaifiyar yarinyar tare da almajiran da suke tare da shi, suka shiga inda yarinyar take. Sai ya kama hannunta ya ce mata, ‹“Talita kum!”› (Wato, ‹“Ƙaramar yarinya, na ce miki, tashi!”›). Nan da nan, sai yarinyar ta tashi ta yi tafiya (shekarunta goma sha biyu ne). Saboda wannan, suka yi mamaki ƙwarai.
”Bai iya yin ayyukan banmamaki a wurin ba, sai dai ɗibiya hannuwansa da ya yi a kan mutane kima da suke da cututtuka, ya kuwa warkar da su.
”Suka fitar da aljanu da yawa, suka shafa wa marasa lafiya da yawa mai, suka kuwa warkar da su.
”Suka gama yankin da gudu, suna ɗaukan marasa lafiya a kan tabarmai zuwa duk inda suka ji yake. Duk inda ya shiga, cikin ƙauyuka, birane ko karkara, sai su kwantar da marasa lafiya a bakin kasuwa. Suka roƙe shi yă bari su taɓa gefen rigarsa kawai, kuma duk waɗanda suka taɓa shi kuwa, suka warke.
”Da jin labarinsa, sai wata mace wadda ƙaramar diyarta tana da mugun ruhu, ta zo ta durƙusa a gabansa. Macen kuwa mutuniyar Hellenawa ce, an haife ta a Funisiya a Suriya. Ta roƙi Yesu yă fitar da aljani da yake jikin diyarta. Yesu ya ce mata, ‹“Da farko, bari ’ya’ya su ci su ƙoshi tukuna, gama ba daidai ba ne, a ɗauki burodin yara a jefa wa karnukansu.”› Ta amsa, ta ce, “I, Ubangiji, ko karnuka ma da suke ƙarƙashin tebur, sukan ci burbuɗin da suke fāɗuwa daga abincin yara.” Sai ya ce mata, ‹“Saboda irin wannan amsa, ki tafi, aljanin ya rabu da diyarki.”› Ta tafi gida, ta tarar da diyarta kwance a gado, aljanin kuwa ya fita.
”A can ne waɗansu mutane suka kawo masa wani kurma, wanda da ƙyar yake magana. Sai suka roƙe shi yă ɗibiya hannunsa a kan mutumin. Bayan da ya jawo shi gefe, sai Yesu ya sa yatsotsinsa a kunnuwan mutumin, ya tofa miyau ya kuma taɓa harshen mutumin. Ya ɗaga kai sama, ya ja numfashi mai zurfi, sa’an nan ya ce masa, ‹“Effata!”› (Wato, ‹“Buɗe!”›). Bayan ya faɗa haka, sai kunnuwan mutumin suka buɗe, harshensa kuma ya kunce, sai ya fara magana sarai. Yesu ya umarce su, kada su gaya wa kowa. Amma ƙara yawan kwaɓarsu ƙara yawan yaɗa labarin suke ta yi. Mutane suka cika da mamaki, suka ce, “Kai, ya yi kome daidai. Har ma yana sa kurame su ji, bebaye kuma su yi magana.”
”Suka iso Betsaida, sai waɗansu mutane suka kawo wani makaho, suka roƙi Yesu yă taɓa shi. Yesu ya kama hannun makahon ya kai shi bayan ƙauyen. Bayan ya tofa miyau a idanun mutumin, ya kuma ɗibiya masa hannuwansa, sai ya tambaye shi ya ce, ‹“Kana iya ganin wani abu?”› Sai ya ɗaga kai ya ce, “Ina ganin mutane, suna kama da itatuwa da suke tafiya.” Yesu ya sāke ɗibiya hannuwansa a idanun mutumin, sai idanunsa suka buɗe, ya sami gani, ya kuma ga kome sarai.
”Wani mutum a cikin taron ya amsa ya ce, “Malam, na kawo maka ɗana mai wani ruhun da yake hana shi magana. Duk lokacin da mugun ruhun ya kama shi, yakan jefa shi a ƙasa. Bakinsa yakan yi kumfa, yă cije haƙorarsa, yakan sa jikinsa ya sandare, yă zama da ƙarfi. Na roƙi almajiranka su fitar da ruhun, amma ba su iya ba.” Yesu ya ce, ‹“Ya ku zamani marar bangaskiya, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron.”› Sai suka kawo shi. Da ruhun ya ga Yesu, nan da nan sai ya buge yaron da farfaɗiya. Ya fāɗi a ƙasa, yana birgima, bakinsa yana kumfa. Yesu ya tambayi mahaifin yaron ya ce, ‹“Tun yaushe yake haka?”› Ya ce, “Tun yana ƙarami. Ya sha jefa shi cikin wuta, ko ruwa don yă kashe shi. Amma in za ka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimake mu.” Yesu ya ce, ‹“ ‘In za ka iya’? Ai, kome mai yiwuwa ne ga wanda ya gaskata.”› Nan da nan mahaifin yaron ya faɗa da ƙarfi ya ce, “Na gaskata, ka taimake ni in sha kan rashin bangaskiyata!” Da Yesu ya ga taron suna zuwa can a guje, sai ya tsawata wa mugun ruhun ya ce, ‹“Kai ruhun kurma, da na bebe, na umarce ka, ka fita daga cikinsa, kada kuma ka ƙara shigarsa.”› Sai ruhun ya yi ihu, ya buge shi da ƙarfi da farfaɗiya, ya fita. Yaron ya kwanta kamar matacce, har mutane da yawa suka ce, “Ai, ya mutu.” Amma Yesu ya kama shi a hannu ya ɗaga, ya kuwa tashi tsaye.
”‹In hannunka yana sa ka yin zunubi, yanke shi. Ai, gwamma ka shiga rai da hannu ɗaya, da ka shiga jahannama ta wuta, inda ba a iya kashe wutar ba, da hannuwanka biyu.› ‹In kuma ƙafarka tana sa ka yin zunubi, yanke ta. Ai, gwamma ka shiga rai da ƙafa ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da ƙafafunka biyu.› ‹In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi. Ai, gwamma ka shiga mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da idanu biyu,› ‹inda› ‹“ ‘tsutsotsinsu ba sa mutuwa,› ‹wutar kuma ba a iya kashewa.’›
”Sai suka iso Yeriko. Sa’ad da Yesu da almajiransa tare da taro mai yawa suke barin birnin, wani makaho da ake kira Bartimawus kuwa (wato, “ɗan Timawus”), yana zaune a gefen hanya yana bara. Da ya ji cewa Yesu Banazare ne, sai ya ɗaga murya, yana cewa, “Yesu Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!” Mutane da yawa suka kwaɓe shi, suka ce yă yi shiru, amma ya ƙara ɗaga murya yana cewa, “Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!” Yesu ya tsaya ya ce, ‹“Ku kira shi.”› Sai suka kira makahon suka ce, “Ka yi farin ciki! Tashi tsaye! Yana kiranka.” Ya jefar da mayafinsa waje ɗaya, ya yi wuf, ya zo wurin Yesu. Yesu ya tambaye shi ya ce, ‹“Me kake so in yi maka?”› Makahon ya ce, “Rabbi, ina so in sami ganin gari.” Yesu ya ce, ‹“Je ka, bangaskiyarka ta warkar da kai.”› Nan da nan, ya sami ganin gari, ya kuma bi Yesu suka tafi.
”Yesu ya amsa ya ce, ‹“Ku gaskata da Allah.› ‹Gaskiya nake gaya muku, in wani ya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka fāɗa cikin teku,’ bai kuwa yi shakka a zuciyarsa ba, amma ya gaskata cewa, abin da ya faɗa zai faru, haka kuwa za a yi masa.› ‹Saboda haka, ina faɗa muku, duk abin da kuka roƙa cikin addu’a, ku gaskata kun riga kun karɓa, zai kuwa zama naku.›
”‹“Dole ku yi zaman tsaro. Za a ba da ku ga hukuma, a kuma bulale ku a majami’u. Saboda ni kuma, za ku tsaya a gaban gwamnoni da sarakuna, domin ku ba da shaida a gabansu.› ‹Dole sai an fara yin wa’azin bishara ga dukan al’ummai.› ‹Sa’ad da aka kama ku, aka kuma kai ku don a yi muku shari’a, kada ku damu da abin da za ku faɗa. Sai dai ku faɗi abin da aka ba ku a lokacin. Gama ba ku kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne.› ‹“Ɗan’uwa zai ba da ɗan’uwa a kashe. Mahaifi zai ba da ɗansa. ’Ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su.› ‹Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.›
”Amma Bitrus ya yi ta nanatawa da ƙarfi ya ce, “Ko da zan mutu tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Duk sauran ma suka ce haka.
”Ya tafi tare da Bitrus, Yaƙub da kuma Yohanna. Sai ya fara baƙin ciki da damuwa ƙwarai. Sai ya ce musu, ‹“Raina yana cike da baƙin ciki har ma kamar zan mutu. Ku dakata a nan ku yi tsaro.”› Sai ya yi gaba kaɗan, ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a, ya ce in mai yiwuwa ne, a ɗauke masa wannan sa’a. Ya ce, ‹“Ya Abba,›‹Uba, kome mai yiwuwa ne a gare ka. Ka ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba abin da nake so ba, sai dai abin da kake so.”›
”Don son yă faranta wa taron rai, sai Bilatus ya sakar musu Barabbas. Ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.
”Sai suka gicciye shi. Suka rarraba tufafinsa, suka jefa ƙuri’a a kansu don su ga abin da kowa zai samu. Sa’a ta uku na safe ce kuwa aka gicciye shi.
”A daidai sa’a ta tara na rana, sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, ‹“Eloi, Eloi, lama sabaktani?”› (Wato, ‹“Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”›).
”‹Waɗannan alamu za su kasance tare da waɗanda suka gaskata. A cikin sunana za su fitar da aljanu, za su yi magana da sababbin harsuna.› ‹Za su ɗauki macizai da hannuwansu. In kuwa suka sha mugun dafi, ba zai cuce su ba ko kaɗan. Za su ɗibiya hannuwansu a kan marasa lafiya, su kuwa warke.”›
”‹“Ruhun Ubangiji yana kaina,› ‹domin ya shafe ni,› ‹in yi wa matalauta wa’azin bishara.› ‹Ya aiko ni in yi shelar ’yanci ga ’yan kurkuku,› ‹in kuma buɗe idanun makafi,› ‹in ba da ’yanci ga waɗanda aka danne.›
”A cikin majami’ar, akwai wani mutum mai aljani, wani mugun ruhu. Mutumin ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Wayyo! Ina ruwanka da mu, Yesu Banazare? Ka zo ne don ka hallaka mu? Na san wane ne kai, Mai Tsarki na Allah!” Yesu ya tsawata masa da ƙarfin cewa, ‹“Yi shiru! Ka fita daga cikinsa!”› Sai aljanin ya fyaɗa mutumin da ƙasa a gabansu duka, sa’an nan ya fita, ya bar shi ba wani rauni. Dukan mutanen suka yi mamaki, suka ce wa junansu, “Wace irin koyarwa ce haka? Da ƙarfi da iko, yana ba wa mugayen ruhohin umarni suna kuma fita!”
”Yesu ya fita daga majami’ar, ya tafi gidan Siman. Surukar Siman kuwa tana fama da zazzaɓi mai tsanani, sai suka roƙi Yesu yă taimake ta. Sai ya sunkuya kusa da ita, ya kuma tsawata wa zazzaɓin, sai zazzaɓin ya sāke ta. Nan take ta tashi, ta yi musu hidima.
”Rana tana fāɗuwa, sai mutane suka yi ta kawo wa Yesu dukan waɗanda suke da cuta iri-iri, sai ya ɗibiya wa kowannensu hannuwansa, ya warkar da su.
”Yayinda Yesu yake ɗaya daga cikin garuruwan nan, sai ga wani mutum wanda kuturta ta ci ƙarfinsa. Da ganin Yesu, sai ya fāɗi da fuskarsa a ƙasa, ya roƙe shi ya ce, “Ubangiji, in ka yarda, kana iya ka tsabtacce ni.” Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin ya ce, ‹“Na yarda, ka zama da tsabta!”› Nan da nan, sai kuturtar ta rabu da shi.
”Duk da haka, labarinsa ya ƙara bazuwa sosai, har taron mutane suka dinga zuwa don jinsa, da kuma neman warkarwa daga cututtukansu.
”Wata rana, da yake cikin koyarwa, waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki waɗanda suka zo daga kowane ƙauye a Galili, Yahudiya da Urushalima kuwa suna zaune. Ikon Ubangiji yana nan don yă warkar da masu ciwo. Sai ga waɗansu mutane suka kawo wani shanyayye a kan tabarma. Suka yi ƙoƙari su shigar da shi cikin gidan, domin su kwantar da shi a gaban Yesu. Da suka ga babu hanyar da za su bi saboda taron, sai suka haura rufin, suka saukar da shi a kan tabarmarsa, ta bakin ramin da suka huda a rufin, suka ajiye shi a tsakiyar taron, a gaban Yesu. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce, ‹“Saurayi, an gafarta maka zunubanka.”› Farisiyawa da malaman dokoki suka fara yin tunani a zukatansu, “Wane ne wannan mutum da yake saɓo haka? Wa zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?” Yesu ya san abin da suke tunani, sai ya yi tambaya ya ce, ‹“Don me kuke tunanin waɗannan abubuwa a zukatanku?› ‹Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuma a ce, ‘Tashi, ka yi tafiya’?› ‹Amma domin ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya ya gafarta zunubai.”› Sai ya ce wa shanyayyen, ‹“Na ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.”› Nan da nan, ya tashi tsaye a gabansu, ya ɗauki tabarmar da yake kwance a kai, ya tafi gida, yana yabon Allah.
”Yesu ya amsa musu ya ce, ‹“Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya.› ‹Ban zo don in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi zuwa ga tuba.”›
”A wata ranar Asabbaci kuma, Yesu ya shiga majami’a yana koyarwa. To, a nan kuwa akwai wani mutumin da hannun damansa ya shanye. Farisiyawa da malaman dokoki suka zuba wa Yesu ido, su ga ko zai warkar a ranar Asabbaci, don su sami dalilin zarginsa. Amma Yesu ya san abin da suke tunani. Sai ya ce wa mutumin mai shanyayyen hannun, ‹“Tashi ka tsaya a gaban kowa.”› Sai ya tashi ya tsaya. Yesu ya ce musu, ‹“Ina tambayarku, me ya kamata a yi bisa ga doka, a ranar Asabbaci, a aikata alheri ko a aikata mugunta, a ceci rai, ko a hallaka shi?”› Sai ya kalle su duka, sa’an nan ya ce wa mutumin, ‹“Miƙo hannunka.”› Sai ya miƙe, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.
”Sai ya sauko tare da su, ya tsaya a wani fili. A can, akwai taro mai yawa na almajiransa, da kuma mutane masu yawan gaske daga ko’ina a Yahudiya, Urushalima da kuma Taya da Sidon da suke bakin teku, waɗanda suka zo domin su ji shi, a kuma warkar da cututtukansu. Waɗanda suke fama da mugayen ruhohi kuwa aka warkar da su. Kuma dukan mutane suka yi ƙoƙari su taɓa shi, domin iko yana fitowa daga gare shi, ya kuwa warkar da su duka.
”‹Masu albarka ne ku da kuke jin yunwa yanzu,› ‹gama za ku ƙoshi.› ‹Masu albarka ne ku da kuke kuka yanzu,› ‹gama za ku yi dariya.› ‹Masu albarka ne sa’ad da mutane suka ƙi ku,› ‹suka ware ku, suka zage ku,› ‹suna ce da ku mugaye,› ‹saboda Ɗan Mutum.› ‹“Ku yi farin ciki a wannan rana, ku kuma yi tsalle don murna, saboda ladarku yana da yawa a sama. Gama haka kakanninsu suka yi wa annabawa.›
”A can, akwai wani bawan wani jarumin yana ciwo, yana kuma a bakin mutuwa. Maigidansa kuwa yana sonsa sosai. Jarumin sojan ya ji labarin Yesu, sai ya aiki waɗansu dattawan Yahudawa wajensa, yana roƙonsa yă zo yă warkar da bawansa. Da suka isa wurin Yesu, sai suka roƙe shi sosai, suka ce, “Wannan mutum, ai, ya dace a yi masa haka, gama yana ƙaunar al’ummarmu ta Yahudawa, har ya gina majami’armu.” Sai Yesu ya tafi tare da su. Da ya yi kusa da gidan, sai jarumin nan, ya aiki abokai su ce masa, “Ubangiji, kada ka dami kanka, gama ban isa ka shiga gidana ba. Shi ya sa ban ma ga na isa in zo wurinka ba. Amma ka yi magana kawai, bawana zai warke. Gama ni kaina, mutum ne a ƙarƙashin iko, akwai kuma sojoji a ƙarƙashin ikona. Nakan ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai yă tafi, ga wani kuma in ce, ‘Zo nan,’ sai yă zo. Nakan kuma ce wa bawana, ‘Yi abu kaza,’ sai yă yi.” Da Yesu ya ji haka, sai ya yi mamaki sosai. Ya juya ya wa taron da yake bin sa, ‹“Ina faɗa muku, ban taɓa samun irin bangaskiya mai girma haka ko cikin Isra’ila ba.”› Sai mutanen da aka aika, suka koma gida, suka tarar bawan ya warke.
”Da ya yi kusa da ƙofar garin, sai ga wata gawa ana fitowa da ita. Shi ne ɗa kaɗai ga mahaifiyarsa, ita kuma gwauruwa ce. Taro mai yawa daga garin yana tare da ita. Da Ubangiji ya gan ta, sai ya ji tausayinta ya ce, ‹“Kada ki yi kuka.”› Yesu ya je ya taɓa akwatin gawar, sai masu ɗaukarsa suka tsaya cik. Sai ya ce, ‹“Saurayi, na ce maka, tashi!”› Sai mamacin ya tashi zaune, ya fara magana. Yesu kuma ya ba da shi ga mahaifiyarsa.
”A daidai lokacin nan, Yesu ya warkar da mutane da yawa masu ciwo, masu cututtuka, da kuma masu mugayen ruhohi. Ya kuma ba makafi da yawa ganin gari. Sai ya amsa wa almajiran Yohanna ya ce, ‹“Ku koma ku faɗa wa Yohanna abin da kuka ji, da abin da kuka gani. Makafi suna ganin gari, guragu suna tafiya, ana warkar da waɗanda suke da kuturta, kurame suna ji, ana tā da matattu, ana kuma yi wa matalauta wa’azin bishara.›
”da kuma waɗansu mata waɗanda aka warkar da su daga cututtukansu, da kuma mugayen ruhohi. Cikinsu akwai Maryamu (wadda ake kira Magdalin) wadda aljanu bakwai suka fito daga cikinta.
”Da suna cikin tafiya, sai barci ya kwashe shi. Sai wata babban iska ta taso kan tafkin, har ruwa ya fara shiga cikin jirgin. Suka shiga babban hatsari. Almajiran suka je suka tashe shi daga barci, suka ce, “Ubangiji, Ubangiji, za mu nutse!” Ya tashi ya kwaɓe iskar da kuma haukar ruwan. Sai ruwan da iskar suka natsu. Kome ya yi tsit. Sai ya tambayi almajiransa, ‹“Ina bangaskiyarku?”› A cikin tsoro da mamaki, suka ce wa junansu, “Wane ne wannan? Yana ba da umarni ga iska da ruwa ma, kuma suna biyayya da shi?”
”Suka shiga jirgin ruwa zuwa yankin Gerasenawa da yake a hayin tafkin, daga wajen Galili. Da Yesu ya sauka daga jirgin, sai ga wani mutum mai aljanu daga garin. Mutumin ya daɗe bai sa tufafi ba, kuma ba ya zama a gida. Yana zama a cikin kaburbura. Da ya ga Yesu, sai mutumin ya ɗaga murya da ƙarfi, ya fāɗi a gabansa, yana ihu cewa, “Ina ruwanka da ni, Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ina roƙonka, kada ka ba ni wahala!” Gama Yesu ya riga ya umarci mugun ruhun ya fita daga mutumin. Sau da yawa mugun ruhun ya sha kamunsa. Ko da yake akan daure shi hannu da ƙafa, da sarƙa, a kuma yi gadinsa, amma yakan tsinke sarƙoƙinsa, aljanun kuma su kore shi zuwa wuraren kaɗaici, inda ba kowa. Yesu ya tambaye shi, ‹“Mene ne sunanka?”› Sai ya amsa, “Tuli,” gama aljanu masu ɗumbun yawa ne suna cikinsa. Suka yi ta roƙonsa kada yă umarce su su shiga ramin Abis. A wurin kuwa, akwai babban garken aladu da suke kiwo a gefen tudu. Aljanun suka roƙi Yesu ya bar su, su shiga cikin aladun, ya kuwa yardar musu. Da aljanun suka fita daga cikin mutumin, sai suka shiga cikin aladun. Garken kuma ya gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, kuma suka nutse.
”A wurin kuwa, akwai wata mace wadda tana da ciwon zubar da jini, har na shekara goma sha biyu, amma babu wanda ya iya warkar da ita. Sai ta zo ta bayansa, ta taɓa bakin rigarsa. Nan da nan, zubar da jininta ya tsaya.
”Yayinda Yesu na cikin magana har yanzu, sai ga wani daga gidan Yayirus, mai mulkin majami’ar ya ce, “Kada ka ƙara damun malam, diyarka ta rasu.” Da Yesu ya ji wannan, sai ya ce wa Yayirus, ‹“Kada ka ji tsoro, ka gaskata, za a kuma warkar da ita.”› Da ya iso gidan Yayirus, sai ya hana kowa yă bi shi cikin ɗakin, sai dai Bitrus, da Yohanna, da Yaƙub, da kuma mahaifin da mahaifiyar. Ana cikin haka, dukan mutanen kuma sai kuka da makoki suke ta yi, domin yarinyar. Sai Yesu ya ce, ‹“Ka daina yin kuka, ba tă mutu ba, tana barci ne.”› Sai suka yi masa dariya, da yake sun san cewa, ta mutu. Amma Yesu ya kama ta a hannu ya ce, ‹“Diyata, tashi.”› Ruhunta ya dawo, kuma ta tashi, nan take. Yesu ya ce musu, su ba ta wani abu tă ci.
”Bayan da Yesu ya tara Sha Biyun wuri ɗaya, sai ya ba su iko da izini na fitar da dukan aljanu, da na warkar da cututtuka. Ya kuma aike su, su yi wa’azin mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya.
”Sai suka tashi suka shiga ƙauye zuwa ƙauye suna wa’azin bishara, suna warkar da marasa lafiya a ko’ina.
”Amma taron mutane suka ji labari, sai suka bi shi. Ya marabce su, kuma ya yi musu magana a kan mulkin Allah, ya kuma warkar da masu bukatar warkarwa.
”Sai wani mutum daga cikin taron ya yi kira da ƙarfi ya ce, “Malam, ina roƙonka, ka dubi ɗan nan nawa, gama shi ne kaɗai nake da shi. Wani ruhu yakan kama shi, sai ya yi ihu farar ɗaya. Yakan sa shi farfaɗiya, har bakinsa ya yi kumfa. Da ƙyar yake barinsa, yana kuwa kan hallakar da shi. Na roƙi almajiranka su fitar da shi, amma ba su iya ba.” Yesu ya amsa ya ce, ‹“Ya karkataccen zamani marar bangaskiya, har yaushe ne zan kasance tare da ku, ina kuma haƙuri da ku? Kawo yaronka nan.”› Yaron yana kan zuwa ke nan, sai aljanin ya buga shi ƙasa, cikin farfaɗiya. Amma Yesu ya kwaɓe mugun ruhun, ya warkar da yaron, sai ya miƙa shi ga mahaifinsa.
”‹Ku warkar da marasa lafiya da suke wurin. Ku kuma faɗa musu cewa, ‘Mulkin Allah yana kusa da ku.’›
”‹Na ba ku iko da za ku tattaka macizai, da kunamai, ku kuma shawo kan dukan ikon abokin gāba, kuma ba wani lahani da zai same ku.›
”Yesu ya amsa ya ce, ‹“Wani mutum ya tashi daga Urushalima za shi Yeriko, sai ya fāɗi a hannun mafasa, wato, ’yan fashi. Suka ƙwace tufafinsa, suka yi masa dūka, suka bar shi nan bakin rai da mutuwa.› ‹Ya zamana wani firist ya bi kan wannan hanya. Da ya ga mutumin, sai ya bi gefe ya wuce abinsa.› ‹Haka ma wani daga kabilar Lawi, mai hidima cikin haikali, da ya zo wurin, ya gan shi, sai shi ma ya bi gefe ɗaya, ya wuce abinsa.› ‹Amma wani mutumin Samariya da yake kan tafiya, da ya kai inda mutumin yake, ya gan shi, sai ya ji tausayinsa.› ‹Ya je wurinsa, ya daddaure masa raunukansa, sa’an nan ya zuba mai, da ruwan inabi. Ya ɗauki mutumin ya sa a kan jakinsa, ya kai shi wani masauƙi, ya yi jinyarsa.›
”Sa’ad da Yesu yake fitar da wani beben aljani daga wani mutum, da aljanin ya fita, sai mutumin wanda da bebe ne, ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki.
”‹Ba ana sayar da kanari biyar a kan kobo biyu ba? Duk da haka, Allah bai manta da ko ɗayansu ba.› ‹Tabbatacce, gashin kanku ɗin nan ma, an ƙidaya su duka. Kada ku ji tsoro. Darajarku ta fi na kanari masu yawa girma.›
”Sai Yesu ya ce wa almajiransa, ‹“Saboda haka, ina faɗa muku, kada ku damu game da rayuwarku, abin da za ku ci, ko kuma game da jikinku, abin da za ku yafa.› ‹Rai ya fi abinci, jiki kuma ya fi tufafi.› ‹Ku dubi hankaki. Ba sa shuki ko girbi, kuma ba su da ɗakin ajiya ko rumbu ba, duk da haka, duk da haka, Allah na ciyar da su. Darajarku ta fi na tsuntsaye sau da yawa!› ‹Wane ne a cikinku ta wurin damuwarsa, zai iya ƙara ko sa’a ɗaya ga rayuwarsa?› ‹Tun da ba za ku iya yin wannan ƙanƙanin abu ba, me ya sa kuke damuwa a kan sauran?› ‹“Ku dubi yadda furanni suke girma. Ba sukan yi aiki, ko saƙa ba, duk da haka, ina faɗa muku cewa, ko Solomon cikin kyakkyawan darajarsa duka, bai yafa kayan ado da ya kai kamar na ko ɗaya a cikinsu ba.› ‹In haka ne Allah yake yi wa ciyayin jeji sutura, wadda yau suna nan, sa’an nan gobe kuma a jefa cikin wuta, Allah ba zai yi muku sutura fiye da ciyayin jeji ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya!› ‹Kada ku sa zuciyarku a kan abin da za ku ci, ko abin da za ku sha, kada ku damu a kan su.› ‹Gama duniya da ba tă san Allah ba, tana faman neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa, ya san kuna bukatarsu.› ‹Amma ku nemi mulkinsa, za a kuwa ƙara muku waɗannan abubuwa.› ‹“Ya ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, gama ya gamshi Ubanku ya ba ku mulkin.›
”‹Ku sayar da dukiyarku, ku ba wa matalauta. Ku yi wa kanku jakar kuɗin da ba za su lalace ba. Ku yi wa kanku ajiyar dukiyar da ba za tă kare ba a sama, inda ɓarawo ba zai yi kusa ba, asu kuma ba za su iya su lalatar ba.› ‹Gama inda dukiyarku take, nan ne zuciyarku ma take.›
”a wurin kuwa, akwai wata mace wadda aljani ya gurgunta, har na shekaru goma sha takwas. Duk ta tanƙware, ba ta ma iya miƙewa ko kaɗan. Da Yesu ya gan ta, sai ya kirata gaba, ya ce mata, ‹“Mace, an ’yantar da ke daga rashin lafiyarki.”› Sai ya ɗibiya hannuwansa a kanta, nan da nan sai ta miƙe, ta yabi Allah.
”‹Ashe, bai kamata a ’yantar da macen nan, diyar zuriyar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya daure, har shekara goma sha takwas, a ranar Asabbaci, daga abin da ya daure ta ba?”›
”Ya amsa ya ce, ‹“Ku je ku gaya wa dilan nan, wato, mai makirci cewa, ‘Da yau da kuma gobe, zan fitar da aljanu, in kuma warkar da mutane, sa’an nan a rana ta uku in cika burin aikina.›
”A nan a gabansa kuwa akwai wani mutum mai ciwon kumburin ƙafa da hannu. Sai Yesu ya tambayi masanan dokoki da Farisiyawa ya ce, ‹“Daidai ne bisa ga doka, a yi warkarwa a ranar Asabbaci, ko babu?”› Amma ba su ce kome ba. Sai ya riƙe mutumin, ya warkar da shi, sa’an nan ya sallame shi.
”‹Amma lokacin da ka kira biki, ka gayyaci matalauta, da guragu, da shanyayyu, da makafi.›
”‹“An yi wani mutum mai arziki wanda yakan sa tufafi masu ruwan shunayya, da kuma na lallausan lilin, yana kuma cikin rayuwar jin daɗi kullum.› ‹A ƙofar gidansa kuma akan ajiye wani mai bara, mai suna Lazarus, wanda jikinsa duk gyambuna ne.› ‹Shi kuwa yakan yi marmarin cin abin da yakan fāɗi daga tebur na mai arzikin nan. Har karnuka ma sukan zo su lashe gyambunansa.› ‹“Ana nan, sai mai baran ya mutu, kuma mala’iku suka ɗauke shi zuwa gefen Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi.› ‹A cikin jahannama ta wuta, inda yana shan azaba, ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim can nesa, da kuma Lazarus a gefensa.› ‹Sai ya yi masa kira ya ce, ‘Baba, Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiki Lazarus ya sa ɗan yatsarsa a ruwa, ya ɗiga mini a harshe saboda in ji sanyi, domin ina shan azaba cikin wannan wuta.’› ‹“Amma Ibrahim ya ce, ‘Ka tuna fa ɗana, a lokacin da kake duniya, ka sami abubuwa masu kyau naka, Lazarus kuwa ya sami munanan abubuwa. Amma yanzu ya sami ta’aziyya a nan, kai kuwa kana shan azaba.› ‹Ban da wannan duka ma, tsakaninmu da kai, akwai wani babban rami da aka yi, yadda waɗanda suke son ƙetarewa daga nan zuwa wurinku, ba za su iya ba, kuma ba mai iya ƙetarewa daga wurinku zuwa wurinmu.’› ‹“Ya amsa ya ce, ‘To, ina roƙonka, ya uba, ka aiki Lazarus zuwa gidan mahaifina,› ‹gama ina da ’yan’uwana biyar maza. Bari yă ba su gargaɗi, don kada su ma su zo wurin nan mai azaba.’› ‹“Ibrahim ya amsa ya ce, ‘Suna da Musa da Annabawa, ai, sai su saurare su.’› ‹“Sai ya ce, ‘A’a, ya uba, Ibrahim, in dai wani ya tashi daga matattu ya je wurinsu, za su tuba.’› ‹“Amma ya ce masa, ‘In ba su saurari Musa da Annabawa ba, kai, ko da wani ya tashi daga matattu ma, ba za su saurare shi ba.’ ”›
”Da zai shiga wani ƙauye, sai maza goma da suke da kuturta suka sadu da shi. Suka tsaya da nesa, suka yi kira da babbar murya, suka ce, “Yesu, Ubangiji, ka ji tausayinmu!” Da ya gan su sai ya ce, ‹“Ku je ku nuna kanku ga firistoci.”› Suna kan hanyar tafiya sai suka tsabtacce. Da ɗayansu ya ga ya warke, sai ya koma, yana yabon Allah da babbar murya.
”‹Duk wanda yake so ya ceci ransa, zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa, zai cece shi.›
”Da Yesu ya yi kusa da Yeriko, akwai wani makaho da yake zaune a gefen hanya, yana bara. Da ya ji taron suna wucewa, sai ya yi tambaya ko mene ne ke faruwa. Suka ce masa, “Ai, Yesu Banazare ne ke wucewa.” Sai ya yi kira ya ce, “Yesu, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!” Mutane da suke gaba suka kwaɓe shi, suka ce masa ya yi shiru. Amma sai ya ƙara ɗaga murya, yana cewa, “Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!” Sai Yesu ya tsaya, ya ba da umarni a kawo mutumin wurinsa. Da ya zo kusa, Yesu ya tambaye shi ya ce, ‹“Me kake so in yi maka?”› Sai ya amsa ya ce, “Ubangiji, ina so in sami ganin gari.” Yesu ya ce masa, ‹“Ka sami ganin garinka; bangaskiyarka ta warkar da kai.”› Nan da nan, ya sami ganin garinsa, kuma ya bi Yesu, yana yabon Allah. Da dukan mutane suka ga wannan, sai su ma suka yabi Allah.
”‹Saboda Ɗan Mutum ya zo ne, domin yă nemi abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.”›
”‹Kuma ba za su sāke mutuwa ba, gama su kamar mala’iku ne. Su ’ya’yan Allah ne, tun da su ’ya’yan tashin matattu ne.›
”‹“Amma kafin duk abubuwa nan, za a kama ku a tsananta muku. Za a kai ku majami’u, da kurkuku. Za a kuma kai ku gaban sarakuna da gwamnoni, kuma dukan waɗannan saboda sunana.› ‹Wannan zai sa ku zama shaidu a gare su.› ‹Amma ku yi ƙuduri, wato, ku shirya zuciyarku, a kan ba za ku damu ba kafin lokacin, game da yadda za ku kāre kanku.› ‹Gama zan ba ku kalmomi, da hikima waɗanda ba ko ɗaya daga cikin maƙiyanku, za su iya tsayayya da ku, ko su ƙaryata.› ‹Har iyayenku, da ’yan’uwanku maza, da danginku, da abokanku ma, duk za su bashe ku, su kuma kashe waɗansunku.› ‹Duk mutane za su ƙi ku saboda ni.› ‹Amma ko gashi ɗaya na kanku, ba zai hallaka ba.›
”‹Ku ne kuka tsaya tare da ni a gwaje-gwajen da na sha.›
”‹“Siman, Siman, Shaiɗan ya nemi izini ya sheƙe ka›‹kamar alkama.› ‹Amma na yi maka addu’a, Siman, domin kada bangaskiyarka ta kāsa. Bayan ka juyo, ka ƙarfafa ’yan’uwanka.”› Amma ya amsa ya ce, “Ubangiji, ina a shirye in tafi tare da kai har kurkuku, ko mutuwa ma.”
”Domin tsananin azaba, sai ya ƙara himma cikin addu’a, zuffansa kuma na ɗigowa ƙasa kamar jini.
”Da suka isa wurin da ake kira “Ƙoƙon Kai,” nan suka gicciye shi, tare da masu laifin nan, ɗaya a hannun damansa, ɗayan kuma a hagunsa. Yesu ya ce, ‹“Ya Uba ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.”› Suka rarraba tufafinsa ta wurin jefa ƙuri’a.
”Yesu ya amsa, ya ce masa, ‹“Gaskiya nake faɗa maka, yau ɗin nan, za ka kasance tare da ni, a mulkina a sama.”›
”Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, ‹“Ya Uba, na danƙa ruhuna a hannunka.”› Da ya faɗi haka, sai ya ja numfashi na ƙarshe.
”Gama Allah ya ƙaunaci duniya sosai har ya ba da wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗansa domin duk wanda ya gaskata da shi kada yă hallaka sai dai yă sami rai madawwami.
”Sai ya sāke ziyarci Kana ta Galili inda ya juya ruwa ya zama ruwan inabi. Akwai wani ma’aikacin hukuma a can wanda ɗansa yake kwance da rashin lafiya a Kafarnahum. Da mutumin nan ya ji cewa Yesu ya isa Galili daga Yahudiya, sai ya je wurinsa ya roƙe shi yă zo yă warkar da ɗansa da yake bakin mutuwa. Yesu ya ce masa, ‹“Ku mutane, in ba kun ga alamu da abubuwan banmamaki ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.”› Ma’aikacin hukuman ya ce, “Ranka yă daɗe, ka zo kafin ɗana yă mutu.” Sai Yesu ya amsa ya ce, ‹“Ka tafi. Ɗanka zai rayu.”› Mutumin kuwa ya amince da maganar da Yesu ya yi ya kuwa tafi. Tun yana kan hanya, bayinsa suka tarye shi da labari cewa yaron yana warkewa. Da ya tambayi lokacin da ɗansa ya sami sauƙi, sai suka ce masa, “Zazzaɓin ya sake shi jiya a sa’a ta bakwai.” Sai mahaifin ya gane a daidai wannan lokaci ne Yesu ya ce masa, ‹“Ɗanka zai rayu.”› Saboda haka shi da dukan iyalinsa suka gaskata.
”A nan naƙasassu da yawa sukan kwanta, makafi, guragu, shanyayyu. Akwai wani da yake nan ba shi da amfani shekara talatin da takwas. Da Yesu ya gan shi kwance a can ya kuma sami labari cewa ya daɗe a wannan hali, sai ya tambaye shi, ‹“Kana so ka warke?”› Marar amfanin nan ya ce, “Ranka yă daɗe, ba ni da wanda zai taimaka yă sa ni a cikin tafkin sa’ad da aka motsa ruwan. Yayinda nake ƙoƙarin shiga, sai wani yă riga ni.” Sai Yesu ya ce masa, ‹“Tashi! Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.”› Nan take mutumin ya warke; ya ɗauki tabarmarsa ya yi tafiya. A ranar da wannan ya faru ranar Asabbaci ce,
”Daga baya Yesu ya same shi a haikali ya ce masa, ‹“Ga shi, ka warke. Ka daina yin zunubi, in ba haka ba wani abin da ya fi wannan muni zai iya samunka.”›
”sai taro mai yawa na mutane suka bi shi domin sun ga abubuwan banmamakin da ya yi ga marasa lafiya.
”Sa’an nan Yesu ya furta cewa, ‹“Ni ne burodin rai. Wanda ya zo wurina ba zai taɓa jin yunwa ba, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai taɓa jin ƙishirwa ba.› ‹Amma kamar yadda na faɗa muku, kun gan ni duk da haka ba ku gaskata ba.› ‹Duk waɗanda Uba ya ba ni za su zo wurina, kuma duk wanda ya zo wurina ba zan kore shi ba ko kaɗan.›
”Sa’ad da Yesu ya sāke magana da mutanen, sai ya ce, ‹“Ni ne hasken duniya. Duk wanda ya bi ni ba zai yi tafiya cikin duhu ba, sai dai yă sami hasken rayuwa.”›
”Da Yesu yana tafiya, sai ya ga wani mutum wanda aka haifa makaho. Sai almajiransa suka tambaye shi suka ce, “Rabbi, wane ne ya yi zunubi, mutumin ne, ko iyayensa, da ya sa aka haife shi makaho?” Sai Yesu ya ce, ‹“Ba don mutumin ko iyayensa sun yi zunubi ne ba, sai dai don a bayyana aikin Allah ne a rayuwarsa.› ‹Muddin da sauran rana, dole mu yi aikin wanda ya aiko ni. Dare yana zuwa, sa’ad da ba wanda zai iya yin aiki.› ‹Yayinda ina a cikin duniya, ni ne hasken duniya.”› Bayan ya faɗi haka, sai ya tofa miyau a ƙasa, ya kwaɓa laka da miyau ɗin, ya kuma shafa a idanun mutumin. Ya ce masa, ‹“Je ka, ka wanke a Tafkin Silowam”› (kalman nan tana nufin “Aikakke”). Saboda haka mutumin ya tafi ya wanke, ya kuma dawo gida yana gani.
”Ba wanda ya taɓa ji cewa an buɗe idanun wanda aka haifa makaho.
”‹Ɓarawo yakan zo don yă yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace.› ‹“Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yakan ba da ransa domin tumakin.›
”‹Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.› ‹Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba mai ƙwace su daga hannun Ubana.›
”Yesu ya ce mata, ‹“Ni ne tashin matattu da kuma rai. Duk wanda ya gaskata da ni zai rayu, ko ya mutu;› ‹kuma duk wanda yake raye ya kuma gaskata da ni ba zai taɓa mutuwa ba. Kin gaskata wannan?”›
”Sa’ad da Maryamu ta kai inda Yesu yake, ta kuma gan shi, sai ta fāɗi a gabansa ta ce, “Ubangiji, da kana nan, da ɗan’uwana bai mutu ba.” Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita ma suna kuka, sai ya yi juyayi ƙwarai a ruhu ya kuma damu. Sai ya yi tambaya ya ce, ‹“Ina kuka sa shi?”› Suka amsa suka ce, “Ubangiji zo ka gani.” Yesu ya yi kuka. Sai Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake ƙaunarsa!”
”Sai Yesu ya ce, ‹“Ku kawar da dutsen.”› Marta, ’yar’uwan mamacin ta ce, “Ubangiji, yanzu, ai, zai yi wari, don yau kwanansa huɗu ke nan a can.” Sai Yesu ya ce, ‹“Ban gaya miki cewa in kin gaskata za ki ga ɗaukakar Allah ba?”› Saboda haka suka kawar da dutsen. Sa’an nan Yesu ya dubi sama ya ce, ‹“Uba, na gode maka da ka saurare ni.› ‹Na san kullum kakan saurare ni, na dai faɗa haka ne saboda amfanin mutanen nan da suke tsaitsaye, don su gaskata cewa kai ka aiko ni.”› Sa’ad da ya faɗa haka, sai Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, ‹“Lazarus, ka fito!”› Sai mamacin ya fito, hannuwansa da ƙafafunsa a daure da ƙyallayen lilin, fuskarsa kuwa an naɗe da mayafi. Yesu ya ce musu, ‹“Ku tuɓe kayan bizo, ku bar shi yă tafi.”›
”‹“Kada zuciyarku ta ɓaci. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni.› ‹A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa; da a ce ba haka ba ne, da na gaya muku. Za ni can don in shirya muku wuri.›
”‹Kuma zan yi duk abin da kuka roƙa cikin sunana, don Ɗan ya kawo ɗaukaka ga Uban.› ‹Za ku iya roƙe ni kome a cikin sunana, zan kuwa yi.›
”‹Salama na bari tare da ku; salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓaci kada kuma ku ji tsoro.›
”‹In kun kasance a cikina kalmomina kuma suka kasance a cikinku, ku roƙi kome da kuke so, za a kuwa ba ku.› ‹Wannan ne yakan kawo ɗaukaka ga Ubana, ku ba da ’ya’ya da yawa, kuna kuma nuna kanku ku almajiraina ne.›
”‹Na gaya muku wannan domin murnata ta kasance a cikinku, murnanku kuma ta zama cikakkiya.›
”‹Haka ku ma, yanzu ne lokacin baƙin cikinku, amma zan sāke ganinku za ku kuma yi farin ciki, ba kuwa wanda zai ɗauke muku farin cikinku.› ‹A ranan nan, ba za ku sāke tambaya ta kome ba. Gaskiya nake gaya muku, Ubana zai ba ku kome da kuka roƙa cikin sunana.› ‹Har yanzu dai ba ku roƙi kome cikin sunana ba. Ku roƙa za ku kuwa samu, farin cikinku kuwa zai zama cikakke.›
”‹“Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”›
”Sa’an nan Bilatus ya tafi da Yesu ya kuma sa aka yi masa bulala.
”A ƙarshe Bilatus ya ba da shi gare su a gicciye shi. Ɗauke da gicciyensa, ya kuwa fita zuwa wurin Ƙoƙon Kai (wanda a harshen Arameya ana ce da shi Golgota). Nan suka gicciye shi tare da waɗansu mutum biyu, ɗaya a kowane gefe da Yesu a tsakiya.
”Da ya tsotsi abin sha ɗin, sai Yesu ya ce, ‹“An gama.”› Da wannan fa, ya sunkuyar da kansa ya saki ruhunsa.
”kuma kamar yadda wani Nassi ya ce, “Za su dubi wanda suka soka.”
”Kuma duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.’
”Saboda haka, zuciyata na farin ciki, harshena kuma na murna, jikina kuma zai kasance da bege, gama ba za ka bar ni cikin kabari ba, ba kuwa za ka yarda Mai Tsarkinka yă ruɓa ba. Ka sanar da ni hanyoyin rai, za ka cika ni da farin ciki a gabanka.’
”Sai Bitrus ya ce, “Azurfa ko zinariya ba ni da su, amma abin da nake da shi, shi zan ba ka. A cikin sunan Yesu Kiristi Banazare, ka yi tafiya.” Ta wurin kama hannunsa na dama, ya taimake shi ya miƙe, nan take ƙafafu da idon sawun mutumin suka yi ƙarfi. Sai ya yi wuf da ƙafafunsa ya fara tafiya. Ya tafi tare da su ya shiga cikin filin haikali yana tafiya yana tsalle, yana kuma yabon Allah. Sa’ad da dukan mutane suka gan shi yana tafiya yana yabon Allah,
”A sakamakon haka, mutane suka kawo marasa lafiya a tituna suka kwantar da su a kan gadaje da tabarmai domin aƙalla inuwar Bitrus za tă bi kan waɗansunsu yayinda yake wucewa. Jama’a ma suka tattaru daga garuruwa kewaye da Urushalima suna kawo marasa lafiyarsu da kuma waɗanda mugayen ruhohi suke damun su, dukansu kuwa suka warke.
”Sai babban firist da dukan abokan aikinsa, waɗanda suke na ƙungiyar Sadukiyawa suka cika da kishi. Suka kama manzannin suka sa su a kurkukun da ake sa kowa da kowa. Amma da dare wani mala’ikan Ubangiji ya buɗe ƙofofin kurkukun ya fitar da su. Ya ce, “Ku je ku tsaya a filin haikali ku sanar wa mutane cikakken saƙon wannan sabon rai.”
”Manzannin suka bar Majalisar, suna farin ciki domin an ga sun cancanta a kunyata su saboda Sunan nan.
”Amma Shawulu ya fara hallaka ikkilisiya. Yana shiga gida-gida, yana jan maza da mata yana jefa su cikin kurkuku. Waɗanda aka wartsar suka yi ta wa’azin maganar a duk inda suka tafi.
”Sa’ad da taron mutane suka ji Filibus suka kuma ga abubuwan banmamakin da ya yi, sai duk suka mai da hankali sosai ga abin da ya faɗa. Mugayen ruhohi suka fiffito suna kururuwa daga cikin mutane da yawa, shanyayyu da guragu masu yawa suka sami warkarwa. Saboda haka aka yi farin ciki ƙwarai a birnin.
”yadda Allah ya shafe Yesu Banazare da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da kuma yadda ya zaga ko’ina yana aikata alheri yana kuma warkar da dukan waɗanda suke ƙarƙashin ikon Iblis, domin Allah yana tare da shi.
”Bayan ya kama shi, sai ya sa shi a kurkuku, ya danƙa shi a hannun soja hurhuɗu kashi huɗu, don su yi gadinsa. Hiridus ya yi niyyar ya yi masa shari’a a gaban mutane bayan Bikin Ƙetarewa. Saboda haka aka tsare Bitrus a kurkuku, amma ikkilisiya ta nace da addu’a ga Allah dominsa. A daren da in gari ya waye da Hiridus yake niyyar kawo shi domin a yi masa shari’a, Bitrus yana barci tsakanin sojoji biyu, daure da sarƙoƙi biyu, masu gadi kuma suna bakin ƙofa. Ba zato ba tsammani sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana haske kuma ya haskaka a ɗakin. Ya bugi Bitrus a gefe ya kuma tashe shi ya ce, “Maza, ka tashi!” Sarƙoƙin kuwa suka zube daga hannuwansa. Sa’an nan mala’ikan ya ce masa, “Ka sa rigunarka da takalmanka.” Bitrus kuwa ya sa. Mala’ikan ya faɗa masa cewa, “Ka yafa mayafinka ka bi ni.” Bitrus ya bi shi suka fita kurkukun, amma bai ma san cewa abin da mala’ikan yake yi tabbatacce ne ba; yana tsammani wahayi yake gani. Suka wuce masu gadi na fari da na biyu, suka kuma isa ƙofar ƙarfe ta shiga birni. Ƙofar kuwa ta buɗe musu da kanta, suka kuma wuce. Sa’ad da suka yi tafiya tsawon wani titi, nan take mala’ikan ya bar shi.
”suna gina almajirai suna kuma ƙarfafa su su tsaya da gaske cikin bangaskiya. Suka ce, “Sai da shan wahaloli masu yawa za mu shiga mulkin Allah.”
”Sai taron suka fāɗa wa Bulus da Sila gaba ɗaya, alƙalan kuwa suka yi umarni a tuɓe su a kuma yi musu dūka. Bayan an yi musu bulala sosai, sai aka jefa su cikin kurkuku, aka umarci mai gadin kurkukun yă tsare su da kyau.
”Da karɓan irin umarnan nan, sai ya sa su can cikin ɗakin kurkuku na ciki-ciki, kuma ya ɗaura ƙafafunsu a turu. Wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu’a suna rera waƙoƙi ga Allah, sauran ’yan kurkuku kuwa suna sauraronsu. Ba zato ba tsammani sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa har tushen ginin kurkukun ya jijjiga. Nan da nan sai duk ƙofofin kurkukun suka bubbuɗe, sarƙoƙin kowa kuma suka ɓaɓɓalle. Mai gadin kurkukun ya farka daga barci, sa’ad da ya ga ƙofofin kurkukun a buɗe, sai ya zāre takobinsa yana shirin kashe kansa domin ya ɗauka ’yan kurkukun sun gudu. Amma Bulus ya yi ihu ya ce, “Kada ka yi wa kanka lahani! Dukanmu muna nan!” Mai gadin kurkukun ya kira a kawo fitilu, ya ruga ciki ya fāɗi yana rawan jiki a gaban Bulus da Sila. Sai ya fito da su waje ya kuma tambaye su ya ce, “Ranku yă daɗe, me zan yi domin in sami ceto?”
”Allah ya yi ayyukan banmamakin da suka wuce misali ta hannu Bulus, har ma ana kai hankicif da adikan da suka taɓa jikinsa wa marasa lafiya, suka kuwa warke daga cututtukansu mugayen ruhohi kuma suka rabu da su.
”Na bauta wa Ubangiji da matuƙar tawali’u har da hawaye, da gwagwarmaya iri-irin da na sha game da makircin Yahudawa.
”“Yanzu kuma Ruhu ya tilasta ni, za ni Urushalima, ba tare da sanin abin da zai faru da ni a can ba. Na dai san cewa a kowace birni Ruhu Mai Tsarki yakan gargaɗe ni cewa kurkuku da shan wuya suna jirana. Amma ni ban ɗauki raina a bakin kome ba, in dai zan iya gama tserena in kuma kammala aikin da Ubangiji Yesu ya ba ni aikin shaida bisharar alherin Allah.
”Cikin kowane abin da na yi, na nuna muku cewa da irin wannan aiki tuƙuru don mu taimaki marasa ƙarfi, muna tunawa da kalmomin da Ubangiji Yesu kansa ya ce, ‹‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’› ”
”Sai Bulus ya amsa ya ce, “Don me kuke kuka kuna kuma ɓata mini zuciya? A shirye nake ba ma a daure ni kawai ba, amma har ma in mutu a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.” Da dai ya ƙi rarrasuwa, muka yi shiru, muka ce, “Bari Ubangiji yă yi nufinsa.”
”Mahaifinsa kuwa yana kwanciya a gado yana fama da zazzaɓi da atuni. Bulus ya shiga ciki don yă gan shi, bayan ya yi masa addu’a, sai ya ɗibiya masa hannuwa ya warkar da shi. Sa’ad da wannan ya faru, sauran marasa lafiya a tsibirin suka zo aka kuma warkar da su.
”Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege. Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.
”Amma Allah ya nuna mana ƙaunarsa a wannan. Tun muna masu zunubi tukuna, Kiristi ya mutu dominmu. Da yake yanzu mun sami zama marasa laifi ta wurin jininsa, ashe kuwa za a cece mu daga fushin Allah ta wurinsa! Gama in kuwa, sa’ad da muke abokan gāban Allah, aka sulhunta mu da shi ta wurin mutuwar Ɗansa, ashe, da yake an sulhunta mu, za mu sami ceto ta wurin ransa! Ba ma haka yake kawai ba, har muna farin ciki da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa yanzu muka sami sulhu.
”Saboda haka, kamar yadda zunubi ya shigo duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuma ta wurin zunubi, ta haka kuwa mutuwa ta shafi dukan mutane, domin dukan mutane sun yi zunubi.
”Ko ba ku sani ba cewa dukanmu da aka yi wa baftisma a cikin Kiristi Yesu an yi mana baftismar ne zuwa cikin mutuwarsa? Saboda haka, an binne mu da shi ke nan, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa, domin kamar yadda aka tā da Kiristi daga matattu ta wurin ɗaukakar Uba, haka mu ma mu yi zaman sabuwar rayuwa. In kuwa mun zama ɗaya tare da shi haka a cikin mutuwarsa, tabbatacce mu ma za mu zama ɗaya tare da shi cikin tashinsa daga matattu. Gama mun san cewa an gicciye halayenmu na dā tare da shi domin a kawar da jikin nan mai zunubi don kada mu ƙara zama bayi ga zunubi domin duk wanda ya mutu an ’yantar da shi daga zunubi ke nan.
”To, in mun mutu tare da Kiristi, mun gaskata cewa za mu rayu tare da shi kuma. Gama mun san cewa da yake an tā da Kiristi daga matattu, ba zai sāke mutuwa ba; mutuwa ba ta da sauran iko a kansa. Mutuwar da ya yi, ya mutu ne sau ɗaya tak, saboda yă shafe zunubi, amma rayuwar da yake yi, yana yi ne cikin tarayya da Allah. Haka ku ma, ku ɗauke kanku matattu ne ga ikon zunubi amma rayayyu cikin tarayya da Allah cikin Kiristi Yesu. Saboda haka kada ku bar zunubi yă mallaki jikin nan naku mai mutuwa yă sa ku zama masu biyayya ga mugayen sha’awace-sha’awacensa. Kada ku miƙa gaɓoɓin jikinku ga zunubi a matsayin kayan aikin mugunta, sai dai ku miƙa kanku ga Allah, a matsayin waɗanda aka fitar da su daga mutuwa zuwa rai; ku kuma miƙa gaɓoɓin jikinku gare shi a matsayin kayan aikin adalci.
”Wace riba ce kuka samu a lokacin, daga abubuwan nan da yanzu suka zama muku abin kunya? Ƙarshen irin abubuwan nan dai, mutuwa ne! Amma a yanzu da aka ’yantar da ku daga zunubi kuka kuma zama bayi ga Allah, ribar da kuka samu tana kai ga zaman tsarki, ƙarshenta kuwa rai madawwami ne.
”Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
”Kaitona! Wane ne zai cece ni daga wannan jiki mai mutuwa?
”Saboda haka, yanzu babu hukunci don waɗanda suke cikin Kiristi Yesu, gama ta wurin Kiristi Yesu dokar Ruhu mai ba da rai ta ’yantar da ni daga Dokar Musa. Gama abin da dokar ba tă iya yi saboda kāsawar mutuntaka ba, Allah ya yi shi sa’ad da ya aiko da Ɗansa a kamannin mutum mai zunubi, don yă zama hadaya ta zunubi. Ta haka, ya hukunta zunubi a cikin mutum mai zunubi. Ya yi haka domin yă cika bukatun adalcin doka a cikinmu, mu da ba ma rayuwa bisa ga mutuntaka, sai dai bisa ga Ruhu. Waɗanda suke rayuwa bisa ga mutuntaka sun kafa hankulansu a kan sha’awace-shawa’acen jiki; amma waɗanda suke rayuwa bisa ga Ruhu sun kafa hankulansu a kan abubuwan da Ruhu yake so. Ƙwallafa rai ga al’amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga al’amuran Ruhu kuwa rai ne da salama; hankalin mai zunubi na gāba da Allah. Ba ya biyayya da dokar Allah, ba kuwa zai iya yin haka ba. Waɗanda mutuntaka yake mulkinsu ba za su iya su gamshi Allah ba.
”Ku kam, ana mulkinku ba ta wurin mutuntaka ba, sai dai ta wurin Ruhu, in Ruhun Allah yana zaune a cikinku. In kuma wani ba shi da Ruhun Kiristi, shi ba na Kiristi ba ne. Amma in Kiristi yana a cikinku, jikinku matacce ne saboda zunubi, duk da haka ruhunku yana a raye saboda adalci. In kuwa Ruhu wannan da ya tā da Yesu daga matattu yana zama a cikinku, shi wanda ya tā da Kiristi daga matattu zai ba da rai ga jikunanku masu mutuwa ta wurin Ruhunsa, wanda yake zama a cikinku.
”Saboda haka ’yan’uwa, muna da hakki, amma ba na wanda za mu yi rayuwar mutuntaka da yake so ba. Gama in kuna rayuwa bisa ga mutuntaka, za ku mutu; amma in ta wurin Ruhu kuka kashe ayyukan jikin nan, za ku rayu. Domin waɗanda Ruhun Allah yake bi da su ne ’ya’yan Allah. Gama ba ku karɓi ruhun da ya mai da ku bayi da za ku sāke jin tsoro ba ne, sai dai kun karɓi Ruhun zaman ɗa. Ta wurinsa kuwa muke kira, “ Abba, Uba.” Ruhu kansa yana ba da shaida tare da ruhunmu cewa mu ’ya’yan Allah ne. In kuwa mu ’ya’ya ne, to, mu magāda ne, magādan Allah da kuma abokan gādo tare da Kiristi, in kuwa muna tarayya a cikin shan wuyarsa to, za mu yi tarayya a cikin ɗaukakarsa.
”A ganina, wuyar da muke sha a wannan lokaci ba su isa a kwatanta da ɗaukakar da za a bayyana a cikinmu ba. Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar ’ya’yan Allah. Gama an sa halitta a cikin wulaƙanci, ba da son ta ba, sai dai ta wurin nufin wannan da ya mai da ita haka, da bege cewa za a ’yantar da halitta kanta daga bautarta ga ruɓewa a kuma kawo ta cikin ’yancin ɗaukakar ’ya’yan Allah. Mun san cewa dukan halitta tana nishi sai ka ce mace mai naƙuda har yă zuwa wannan lokaci. Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu ’ya’yan riƙo na Allah, fansar jikunanmu. Gama a wannan begen ne muka sami ceto. Amma begen da ake gani ba bege ba ne sam. Wa yake begen abin da ya riga ya samu? Amma in muna begen abin da ba mu riga mun samu tukuna ba, mukan jira da haƙuri.
”Haka nan ma, Ruhu yana taimakonmu cikin rashin ƙarfinmu. Ba mu san abin da ya kamata mu roƙa cikin addu’a ba, amma Ruhu kansa yana roƙo a madadinmu da nishe-nishen da kalmomi ba sa iya bayyanawa. Shi kuma wanda yake binciken zukatanmu ya san halin Ruhu, domin Ruhu yana roƙo a madadin tsarkaka bisa ga nufin Allah.
”Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa. Gama waɗanda Allah ya rigyasani ya kuma ƙaddara su dace da kamannin Ɗansa, don yă zama ɗan fari cikin ’yan’uwa masu yawa. Waɗanda kuwa ya ƙaddara, su ne ya kira; waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar; waɗanda ya kuɓutar kuwa, su ne ya ɗaukaka.
”Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu? Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai kuma ba mu, tare da shi, dukan abubuwa cikin alherinsa ba? Wa zai kawo wani zargi a kan waɗanda Allah ya zaɓa? Allah ne mai kuɓutarwa. Wa zai yi hukunci? Yesu Kiristi ne, wanda ya mutu, fiye da haka ma, shi da aka tā da zuwa rai, yana zaune a hannun dama na Allah yana kuma yin roƙo a madadinmu.
”Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Saboda kai ne muke fuskantar mutuwa dukan yini; an ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.”
”A’a, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu. Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
”Ina faɗin gaskiya a cikin Kiristi ba ƙarya nake yi ba, lamirina ya tabbatar da wannan a cikin Ruhu Mai Tsarki. Ina da baƙin ciki mai yawa da kuma rashin kwanciyar rai marar ƙarewa a zuciyata. Gama da so na ne, sai a la’anta ni a kuma raba ni da Kiristi saboda ’yan’uwana, waɗannan na kabilata,
”Kamar yadda yake a rubuce, “Ga shi, na sa dutse a Sihiyona da yake sa mutane yin tuntuɓe da kuma dutsen da yake sa su fāɗi wanda kuwa ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.”
”Kamar yadda Nassi ya ce, “Duk wanda ya gaskata da shi ba zai taɓa shan kunya ba.” Gama ba bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa yana kuma ba da albarka a yalwace ga duk masu kira gare shi, gama, “Duk wanda ya kira bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.”
”Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya.
”Ku yi farin ciki cikin bege, haƙuri cikin shan wuya, aminci cikin addu’a. Ku taimaki mutanen Allah masu bukata. Ku zama masu karɓan baƙi. Ku sa wa masu tsananta muku albarka; ku sa albarka kada fa ku la’anta. Ku yi murna da masu murna, ku yi kuka da masu kuka.
”In muna rayuwa, muna rayuwa ne ga Ubangiji; in kuma muna mutuwa, muna mutuwa ne ga Ubangiji. Saboda haka, ko muna a raye ko muna a mace, mu na Ubangiji ne. Saboda wannan ne Kiristi ya mutu, ya kuma sāke rayuwa domin yă zama Ubangiji na matattu da na masu rai.
”Bari Allah na bege yă cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
”Ga waɗanda ba su da ƙarfi, na zama marar ƙarfi, domin in rinjayi waɗanda ba su da ƙarfi. Na zama dukan abu ga dukan mutane, domin ko ta yaya in zai yiwu, in ceci waɗansu.
”Duk da haka sa’ad da Ubangiji ya hukunta mu, ana yin mana horo ne don kada a ƙarshe a hallaka mu tare da duniya.
”don kada rarrabuwa ta kasance a jiki, sai dai gaɓoɓin jiki su kula da juna. In wata gaɓa tana a damuwa, duk sai su damu tare. In kuma an ɗaukaka wata gaɓa, sai duk su yi farin ciki tare.
”Gama Allah, ba Allah mai sa rikicewa ba ne, sai dai mai salama. Kamar yadda yake a dukan ikkilisiyoyi na tsarkaka.
”Kamar yadda duka suka mutu cikin Adamu, haka duka za su rayu cikin Kiristi.
”Abokin gāba na ƙarshen da za a hallaka kuwa, shi ne mutuwa.
”Gama dole mai ruɓa yă maye wa mai ruɓan nan, marar mutuwa kuma yă maye wa mai mutuwan nan. Sa’ad da mai ruɓan nan ya maye marar ruɓan nan, mai mutuwa kuma ya maye marar mutuwan nan, sa’an nan ne karin maganar da yake a rubuce zai zama gaskiya cewa, “An haɗiye mutuwa cikin nasara.” “Ya ke mutuwa, ina nasararki? Ya ke mutuwa, ina dafinki?”
”Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah. Gama kamar yadda wahalar Kiristi ta cika har tana zuba a cikin rayuwarmu, haka nan kuma ta wurin Kiristi ta’aziyyarmu ta cika har tana zuba. In muna shan wahala, ai, muna shanta domin ta’aziyyarku, da cetonku ne, in mun sami ta’aziyya, ai, mun same ta domin ta’aziyyarku ce, wadda take sa ku jure wa irin wahalan nan, da muke sha. Begen da muke da shi dominku kuwa, tabbatacce ne, domin mun san cewa kamar yadda kuke tarayya da mu a cikin wahalolinmu, haka kuma kuke tarayya da mu a cikin ta’aziyyarmu.
”’Yan’uwa, ba ma so ku zama da rashin sani, a kan wahalolin da muka sha a lardin Asiya. Mun sha wahaloli sosai, har abin ya fi ƙarfinmu, ya sa muka fid da tsammanin rayuwa. Ba shakka, a zuciyarmu mun ji kamar hukuncin kisa ne aka yi mana. Wannan kuwa ya faru ne domin kada mu dogara da kanmu, sai dai ga Allah, wanda yake tā da matattu. Shi ya cece mu daga irin wannan hatsari na mutuwa, zai kuwa cece mu. A kansa muka kafa bege cewa zai ci gaba da cetonmu,
”Amma muna da wannan dukiya a cikin tulunan yumɓu, don a nuna wannan mafificin ikon nan daga Allah ne, ba daga gare mu ba. A matse muke a kowane gefe, sai dai ba a gurgunta mu ba. An rikitar da mu, amma ba mu fid da zuciya ba. An tsananta mana, amma ba a yashe mu ba, an fyaɗe mu da ƙasa, amma ba a hallaka mu ba. Kullum muna ɗauke da mutuwar Yesu a jikinmu, domin ran Yesu yă bayyana a jikinmu. Muddin muna a raye, kullum zaman mutuwa muke yi saboda Yesu, don a bayyana ran Yesu ta wurin jikin nan namu mai mutuwa. Ta haka, mutuwa tana aiki a cikinmu, ku kuwa rai a cikinku.
”Saboda haka, ba mu fid da zuciya ba. Ko da yake a waje, jikinmu mai mutuwa yana lalacewa, amma can ciki, ana sabunta mu kowace rana. Don wannan ’yar wahalar tamu mai saurin wucewa, ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci. Domin ba abubuwan da ido yake gani ne muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa. Gama abubuwan da ake gani masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne.
”Yanzu mun san cewa in an hallaka tentin duniyan nan da muke ciki, muna da wani gini daga Allah, madawwamin gida a sama, wanda ba da hannuwan mutum ne suka gina shi ba. Kafin nan muna nishi, da marmari a yi mana sutura da gidanmu na sama,
”Saboda haka, kullum muna da tabbaci mun kuma san cewa, muddin muna a duniya cikin jikin nan, ana raba mu da Ubangiji. Rayuwa bangaskiya muke, ba ta ganin ido ba. Ina cewa muna da tabbaci, za mu fi so mu rabu da jikin nan, mu kuma kasance a sama tare da Ubangiji.
”Ƙaunar Kiristi a gare mu, ita take mallakarmu, saboda haka mun tabbata, da yake wani ya mutu saboda dukan mutane, ashe kuwa, mutuwarsu ce dukansu. Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin kada waɗanda suke rayuwa kada su yi zaman ganin dama a nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su, aka kuma tashe shi saboda su. Saboda haka, daga yanzu zuwa nan gaba, ba mu ƙara ɗaukan wani mutum bisa ga ganin duniya ba. Ko da yake a dā, mun ɗauki Kiristi haka, amma yanzu mun daina yin haka.
”Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon al’amari ya shuɗe, sabon ya zo!
”A maimakon haka, duk abin da muke yi, muna yin shi ne don mu nuna cewa mu masu hidimar Allah ne. Muna yin haka cikin jimrewa, da shan wahala, da shan wuya, har da shan masifu. Da shan dūka, da shan dauri, da yawan hargitsi, da yawan fama, da rashin barci, da kuma yunwa. Da cikin tsarki, da fahimta, da haƙuri, da kirki, da cikin Ruhu Mai Tsarki, da cikin ƙauna mai gaskiya,
”mu sanannu ne, duk da haka an ɗauke mu kamar ba a san mu ba, muna mutuwa, duk da haka a raye muke, an ba mu horo, duk da haka ba a kashe mu ba, cikin baƙin ciki, duk da haka kullum cikin murna muke. Cikin matalauta, duk da haka muna azurtar da mutane da yawa. Ba mu da kome, alhali kuwa kome namu ne.
”Ba na faɗin wannan don in sa muku laifi. Na riga na gaya muku yadda muke ƙaunarku ƙwarai cikin zukatanmu, har babu abin da zai iya raba ku da ƙaunarmu, ko a mutuwa ko a rayuwa. Na amince da ku gaya, ina kuma taƙama da ku ƙwarai. Na ƙarfafa sosai. Duk da wahalce wahalcenmu dai ina farin ciki ƙwarai da gaske.
”Gama sa’ad da muka zo Makidoniya, jikin nan namu bai sami hutu ba, sai ma aka matsa mana a ta kowane gefe, a waje ga rikici, a zukatanmu kuma ga tsoro. Amma Allah, wanda yakan yi wa masu ɓacin rai ta’aziyya ya yi mana ta’aziyya da zuwan Titus,
”Baƙin ciki irin na tsoron Allah yana kai ga tuban da yake kawo ceto, ba ya kuma kawo baƙin ciki, amma baƙin ciki irin na duniya yakan kawo mutuwa. Ku dubi abin da wannan baƙin ciki irin na tsoron Allah ya kawo muku mana, ya sa ku marmarin aikatawa, da nuna cewa kun yi kuskure, ya sa kuka yi fushi, kuka kuma ji tsoro, ya sa kuka sa zuciya, kuka kuma sa aniya, ya sa kuna a shirye ku ga an yi horon da ya dace. Game da wannan sha’ani kam, lalle ta kowace hanya kun nuna cewa ba ku da laifi.
”Gama sun sha wuya sosai saboda tsananin wahalar da suka shiga, har yawan farin cikinsu ya kai su ga yin alheri ta bayarwa ga waɗansu, ko da yake suna cikin tsananin talauci.
”Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ya ba gajiyayyu hannu sake, ayyukansa na alheri madawwama ne.” To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, yă riɓanya shi, yă kuma albarkaci ayyukanku na alheri da yawa. Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za tă zama sanadin godiya ga Allah.
”In su bayin Kiristi ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! Ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan dauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri-iri. Sau biyar Yahudawa suka yi mini bulala arba’in ɗaya babu. Sau uku aka bulale ni da bulalar ƙarfe, sau ɗaya aka jajjefe ni da duwatsu, sau uku jirgin ruwa ya ragargaje ina ciki, na kwana na kuma yini ruwan teku yana tafiya da ni. Na yi tafiye-tafiye da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin ’yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al’ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a teku, na kuma sha hatsarin ’yan’uwa na ƙarya. Na yi fama, na shan wuya, ga kuma rashin barci sau da yawa. Na san abin da ake nufin da jin yunwa da ƙishirwa, sau da yawa kuwa na kasance da rashin abinci, na sha sanyi da zaman tsirara. Ban da waɗannan abubuwa, kowace rana ina ɗauke da nauyin kula da dukan ikkilisiyoyi. Wane ne ya rasa ƙarfi, da ban ji shi a jikina ba? Wane ne ya fāɗi cikin zunubi, da ban ji zafin wannan ba? In ma lalle ne in yi taƙama, to, sai in yi taƙama da abubuwan da suka nuna rashin ƙarfina.
”Zan yi taƙama game da mutum irin wannan, sai dai ni ba zan yi taƙama da kaina ba, sai dai a kan rashin ƙarfina.
”Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni. Sau uku na roƙi Ubangiji yă raba ni da wannan abu. Amma ya ce mini, ‹“Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.”› Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni. Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi.
”Babu bambanci tsakanin mutumin Yahuda da mutumin Al’ummai, bawa da ’yantacce, namiji da ta mace, gama dukanku ɗaya ne cikin Kiristi Yesu. In kuwa ku na Kiristi ne, to, ku zuriyar Ibrahim ne, magāda kuma bisa ga alkawarin nan.
”Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci,
”Ku ɗauki nawayar juna, a haka kuwa za ku cika dokar Kiristi.
”Allah ya tashe mu tare da Kiristi, ya kuma ba mu wurin zama tare da shi a cikin mulkin samaniya.
”Saboda haka, ni Bulus, na zama ɗan kurkuku na Kiristi Yesu saboda ku Al’ummai.
”A matsayina na ɗan kurkuku saboda Ubangiji, ina roƙonku ku yi rayuwar da ta dace da kiran da aka yi muku. Kullum ku kasance masu sauƙinkai da kuma hankali; ku zama masu haƙuri, kuna jimrewa da juna cikin ƙauna.
”Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama. Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge.
”A koyaushe ku kasance kuna addu’a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fasawa. A kan wannan manufa ku zauna a faɗake da matuƙar naci, kuna yin wa dukan mutanen Ubangiji addu’a. Ku kuma yi addu’a domina, don duk sa’ad da na buɗe bakina, in sami kalmomi babu tsoro, don in sanar da asirin bishara, wadda nake jakadanta cikin sarƙoƙi. Ku yi addu’a don in iya yin shelarta babu tsoro, yadda ya kamata in yi.
”Gama a gare ni, rai Kiristi ne, mutuwa kuma riba ce. In zan ci gaba da rayuwa a cikin jiki, wannan zai zama aiki mai amfani a gare ni. Duk da haka me zan zaɓa? Ban sani ba! Na rasa wanda zan zaɓa cikin biyun nan. Ina sha’awa in yi ƙaura in zauna tare da Kiristi, wannan kuwa ya fi kyau nesa ba kusa ba;
”Gama an ba ku zarafi a madadin Kiristi cewa ba gaskatawa da shi kaɗai ba kuka yi ba, har ma ku sha wahala dominsa,
”Ba shakka ya yi rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Amma Allah ya nuna masa jinƙai, ba shi kaɗai ba amma har da ni ma, don yă rage mini baƙin ciki kan baƙin ciki.
”Gama mu ne masu kaciya, mu da muke yi sujada ta wurin Ruhun Allah, mu da muke taƙama a cikin Kiristi Yesu, mu da ba mu dogara da ayyukan da ake gani ba,
”Ina so in san Kiristi da ikon tashinsa daga matattu da kuma zumuncin tarayya cikin shan wahalarsa, in kuma zama kamar sa a cikin mutuwarsa,
”Amma mu ’yan mulkin sama ne. Muna kuma jira zuwan Mai Ceto daga can, Ubangiji Yesu Kiristi, shi ne mai ikon kawo dukan abubuwa ƙarƙashin mulkinsa. Ta wurin ikon nan nasa zai sāke jikin nan namu na ƙasƙanci, yă mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka.
”Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki! Bari kowa yă kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa. Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.
”Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara. Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi. Duk da haka kun kyauta da kuka yi tarayya da ni cikin wahalolina.
”Allahna kuma zai biya dukan bukatunku bisa ga ɗaukakar wadatarsa cikin Kiristi Yesu.
”Allah yă ƙarfafa ku da dukan iko bisa ga ɗaukakar ƙarfinsa domin ku kasance da jimrewa sosai da kuma haƙuri, cikin farin ciki kuna gode wa Uba, wanda ya sa kuka cancanci ku sami rabo a gādon tsarkaka a cikin mulkin haske. Gama ya riga ya cece mu daga mulkin duhu ya kuma kawo mu cikin mulkin Ɗan da yake ƙauna,
”Yanzu, ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, don ta wurin wuyan nan zan cika abin da ya rage na wuyar da Kiristi ya sha saboda jikinsa, wato, ikkilisiya.
”Da yake an tashe ku tare da Kiristi, sai ku sa zukatanku a kan abubuwan da suke sama, inda Kiristi yake zaune a hannun dama na Allah. Ku sa hankulanku a kan abubuwan sama, ba kan abubuwan duniya ba. Gama kun mutu, ranku yanzu kuwa yana ɓoye tare da Kiristi a cikin Allah. Sa’ad da Kiristi, wanda shi ne ranku, ya bayyana, ku ma za ku bayyana tare da shi cikin ɗaukaka.
”Ku bar salamar Kiristi tă yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya.
”Mun riga mun sha wahala, aka kuma zage mu a Filibbi, kamar yadda kuka sani, amma da taimakon Allahnmu muka yi ƙarfin hali muka sanar muku bishararsa duk da matsananciyar gāba.
”don kada kowa yă raunana ta wurin waɗannan gwaje-gwajen. Kun sani sarai cewa an ƙaddara mu don waɗannan. Gaskiyar ita ce, sa’ad da muke tare da ku, mun sha gaya muku cewa za a tsananta mana. Haka kuwa ya faru, kamar dai yadda kuka sani. Saboda wannan, sa’ad da ban iya jimrewa ba, sai na aika domin in sami labarin bangaskiyarku, da fata kada yă zama mai jarraban nan ya riga ya jarrabce ku, ƙoƙarinmu kuma yă zama banza.
”’Yan’uwa, ba ma so ku kasance cikin jahilci game da waɗanda suka yi barci, ko kuwa ku yi baƙin ciki kamar sauran mutanen da ba su da bege. Mun gaskata cewa Yesu ya mutu ya tashi kuma daga matattu, ta haka muka gaskata cewa Allah zai kawo waɗanda suka yi barci a cikinsa tare da Yesu. Bisa ga maganar Ubangiji kansa, muna gaya muku cewa mu da muke raye har yanzu, waɗanda aka bari har dawowar Ubangiji, tabbatacce ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba.
”Ku riƙa farin ciki kullum; ku ci gaba da yin addu’a; ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.
”Bari Allah da kansa, Allah na salama, yă tsarkake ku sarai. Bari dukan ruhunku, ranku, da kuma jikinku su zama marar aibi a dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi. Wannan wanda ya kira ku mai aminci ne zai kuwa aikata.
”Saboda haka, a cikin ikkilisiyoyin Allah muna taƙama game da daurewarku da kuma bangaskiyarku cikin dukan tsanani da gwaje-gwajen da kuke sha. Dukan wannan yana tabbatar cewa hukuncin Allah daidai ne, saboda haka kuma za a lissafta ku a kan kun cancanci mulkin Allah, wanda dominsa ne kuke shan wahala. Allah mai adalci ne, Zai sāka wa masu ba ku wahala da wahala yă kuma sauƙaƙa muku ku da kuke wahala, har ma da mu. Wannan zai faru sa’ad da aka bayyana Ubangiji Yesu daga sama cikin wuta mai ci tare da mala’ikunsa masu iko.
”Ubangijinmu Yesu Kiristi kansa da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu kuma ta wurin alherinsa yă ba mu madawwamiyar ƙarfafawa da kyakkyawar bege, yă ƙarfafa zukatanku yă kuma gina ku cikin kowane aikin nagari da kuma magana.
”Yanzu, bari Ubangiji mai salama kansa yă ba ku salama a kowane lokaci da kuma a ta kowace hanya. Ubangiji yă kasance tare da ku duka.
”Ka daina shan ruwa kaɗai, yi amfani da ruwan inabi kaɗan saboda cikinka da kuma yawan rashin lafiyarka.
”Gama ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu fita daga cikinta da kome ba. In dai muna da abinci da sutura, ai, sai mu gamsu da su.
”Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai.
”Saboda haka kada ka ji kunyar ba da shaida game da Ubangijinmu, ko kuwa ka ji kunyata, ni da nake ɗan sarƙa saboda shi. Sai dai ka haɗa kai tare da ni cikin shan wahala saboda bishara ta wurin ikon Allah, wanda ya cece mu ya kuma kira mu ga rayuwar tsarki ba saboda wani abin da muka yi ba sai dai saboda nufinsa da kuma alherinsa. An ba mu wannan alheri cikin Kiristi Yesu tun fil azal, amma yanzu an bayyana ta ta wurin bayyanuwar Mai Cetonmu, Kiristi Yesu, wanda ya hallaka mutuwa ya kuma kawo rai da rashin mutuwa a sarari ta wurin bishara. A wannan bishara ce, aka naɗa ni mai shela da manzo da kuma malami. Shi ya sa nake shan wahalar da nake sha. Duk da haka ba na jin kunya, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata cewa yana iya kiyaye abin da na danƙa masa amana don wancan rana.
”wadda nake shan wahala har ga daurin sarƙa kamar mai laifi. Amma Maganar Allah ba a daure take ba. Saboda haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton da yake cikin Kiristi Yesu, tare da madawwamiyar ɗaukaka. Ga wata magana tabbatacciya, “In muka mutu tare da shi, za mu rayu tare da shi; in muka jimre, za mu yi mulki tare da shi. In muka yi mūsunsa, shi ma zai yi mūsunmu;
”Kai kam, ka san kome game da koyarwata, da halina, da niyyata, bangaskiya, haƙuri, ƙauna, jimiri, tsanani, shan wahala, irin abubuwan da suka faru da ni a Antiyok, Ikoniyum da kuma Listira, tsananin da na jure. Duk da haka Ubangiji ya cece ni daga dukansu. Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna na Kiristi Yesu, za su sha tsanani.
”Amma kai, ka natsu cikin kowane hali, ka jure shan wahala, ka yi aikin mai bishara, ka cika dukan ayyukan hidimarka.
”Gama an riga an tsiyaye ni kamar hadaya ta sha, kuma lokacin tashina ya yi. Na yi fama mai kyau, na gama tseren, na riƙe bangaskiya. Yanzu kuwa an ajiye mini rawanin adalci, wanda Ubangiji, Alƙali mai adalci zai ba ni a ranan nan ba kuwa ni kaɗai ba, amma ga duk waɗanda suka yi marmarin bayyanuwarsa.
”A lokacin da na kāre kaina da farko, ba wanda ya goyi bayana, sai ma kowa ya yashe ni. Ina fata ba za a lasafta wannan laifi a kansu ba. Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya kuma ba ni ƙarfi, don ta wurina a yi cikakkiyar shelar saƙon har Al’ummai duka su ji. Aka kuma cece ni daga bakin zaki. Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun hari yă kuma kai ni mulkinsa na sama lafiya. A gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin.
”duk wannan kuwa saboda begen nan ne ga rai madawwami da Allah ya yi alkawari tun fil azal, shi wanda ƙarya ba ta a gare shi,
”Bulus, ɗan kurkuku saboda Kiristi Yesu, da kuma Timoti ɗan’uwanmu, Zuwa ga Filemon ƙaunataccen abokinmu da kuma abokin aikinmu,
”duk da haka ina roƙonka saboda ƙauna, na fi so in roƙe ka, ni Bulus tsoho, a yanzu kuma ga ni ɗan sarƙa saboda Kiristi Yesu.
”Da yake ’ya’yan suna da nama da jini, shi ma sai ya ɗauki kamanninsu na mutum domin ta wurin mutuwarsa yă hallaka wanda yake riƙe da ikon mutuwa, wato, Iblis ya kuma ’yantar da waɗanda dukan rayuwarsu tsoron mutuwa ya riƙe su cikin bauta.
”Domin shi kansa ya sha wahala sa’ad da aka gwada shi, yana iya taimakon waɗanda ake yi wa gwaji.
”Saboda haka, da yake alkawarin shiga hutunsa yana nan har yanzu, sai mu yi hankali kada waninku yă kāsa shiga. Gama mu ma mun ji an yi mana wa’azin bishara, kamar yadda su ma suka ji; sai dai saƙon da suka ji ba tă amfane su ba, domin waɗanda suka ji ba su karɓe shi da bangaskiya ba. Mu kam da muka gaskata mu ne muka shiga wannan hutu, kamar yadda Allah ya ce, “Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ” Allah ya faɗa haka ko da yake ya riga ya kammala aikinsa tun halittar duniya. Gama a wani wuri ya yi magana a kan rana ta bakwai cikin waɗannan kalmomi, “A rana ta bakwai kuwa Allah ya huta daga dukan aikinsa.” Haka kuma a nassin nan ya ce, “Ba za su taɓa shiga hutuna ba.” Har yanzu dai da sauran dama domin waɗansu su shiga, su kuwa waɗanda aka fara yi wa albishirin nan sun kāsa shiga saboda rashin biyayya. Saboda haka Allah ya sāke sa wata rana, yana kiranta Yau, bayan wani dogon lokaci Allah ya yi magana ta bakin Dawuda, yadda aka riga aka faɗa, “Yau, in kuka ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku.” Gama da a ce Yoshuwa ya ba su hutu, da Allah bai yi magana daga baya a kan wata rana dabam ba. Har yanzu, akwai wani hutun Asabbacin da ya rage domin mutanen Allah;
”Gama babban firist da muke da shi ba marar juyayin kāsawarmu ba ne, amma muna da wanda aka gwada ta kowace hanya, kamar dai yadda akan yi mana, duk da haka bai yi zunubi ba. Saboda haka sai mu matso kusa da kursiyin alheri da ƙarfi zuciya, don mu sami jinƙai mu kuma sami alherin da zai taimake mu a lokacin bukata.
”A lokacin da Yesu ya yi rayuwa a duniya, ya yi addu’o’i da roƙe-roƙe tare da kuka mai zafi da kuma hawaye ga wannan wanda yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa ji shi saboda tsananin bangirman da ya yi. Ko da yake shi ɗa ne, ya yi biyayya ta wurin shan wahala
”Ku tuna da kwanakin nan da suka wuce bayan kun sami haske, sa’ad da kuka tsaya daram a tsananin shan wahala. Wani lokaci a fili an tsananta muku aka kuma zage ku aka kuma tsananta muku; a wani lokaci kuma kuka tsaya tare da waɗanda aka yi musu haka. Kuka ji tausayin waɗanda suke cikin kurkuku, da farin ciki kuma kuka yarda ku rabu da dukiyar da aka ƙwace muku, domin ku kanku kun san cewa kuna da madawwamiyar dukiya mafi kyau. Saboda haka kada ku yar da tabbacinku; za a sāka muku a yalwace. Kuna bukata ku jimre don sa’ad da kuka aikata nufin Allah, za ku karɓi abin da ya yi alkawari. Gama, “A cikin ɗan lokaci kaɗan, mai zuwan nan zai zo ba kuwa zai yi jinkiri ba. Amma, “Mai adalcina zai rayu ta wurin bangaskiya. In kuwa ya ja da baya, ba zan ji daɗinsa ba.”
”Saboda haka, daga mutum ɗaya, wanda dā shi ma da matacce kusan ɗaya ne, zuriya masu yawa suka fito kamar taurari a sararin sama da kuma kamar yashin da ba a iya ƙirgawa a bakin teku.
”Duk mutanen nan suna cikin bangaskiya sa’ad da suka mutu. Ba su kuwa karɓi abubuwan da aka yi alkawari ba; sun dai hango su suka kuma marabce su daga nesa. Suka kuma amince cewa su baƙi ne, bare kuma a duniya.
”Ta wurin bangaskiya ne Musa, sa’ad da ya yi girma, ya ƙi a kira shi ɗan diyar Fir’auna. Ya zaɓa yă sha wahala tare da mutanen Allah, maimakon yă ji daɗin sha’awace-sha’awacen zunubi na ɗan lokaci. Ya ɗauki wulaƙancin da yake sha saboda Kiristi ya fi dukiyar Masar daraja, domin ya sa ido ga ladansa. Ta wurin bangaskiya ya bar Masar, ba tare da jin tsoron fushin sarki ba; ya kuwa jure domin ya ga wannan wanda ba a iya gani.
”Me kuma zan faɗa? Ba ni da lokacin da zan ba da labari a kan Gideyon, Barak, Samson, Yefta, Dawuda, Sama’ila, da kuma annabawa, waɗanda ta wurin bangaskiya ne suka ci nasara a kan mulkoki, suka aikata adalci, suka kuma sami abin da aka yi alkawari; waɗanda suka rurrufe bakunan zakoki, suka kashe harshen wuta, suka kuma tsere wa kaifin takobi; waɗanda aka mai da rashin ƙarfinsu ya zama ƙarfi; waɗanda suka yi jaruntaka wajen yaƙi suka kuma fatattaki mayaƙan waɗansu ƙasashe. Mata suka karɓi ƙaunatattunsu da aka sāke tasar daga matattu. Aka azabtar da yawancin mutanen nan, amma suka ƙi a sake su, domin sun tabbata za su sami lada mafi kyau sa’ad da aka tā da matattu. Waɗansu suka sha ba’a da bulala, har da dauri da sarƙa, da kuma jefa su cikin kurkuku. Aka jajjefe su da duwatsu; aka raba su biyu da zarto; aka kashe su da takobi. Suka yi ta yawo saye da fatun tumaki da na awaki, suka yi zaman rashi, suka sha tsanani da kuma wulaƙanci duniya ba tă ma cancanci su zauna a cikinta ba. Suka yi ta yawo a cikin hamada da a kan duwatsu, da cikin kogwanni da kuma cikin ramummuka. Waɗannan duka an yabe su saboda bangaskiyarsu, duk da haka babu waninsu da ya sami abin da aka yi alkawari. Allah ya shirya mana wani abu mafi kyau. Kuma bai so su kai ga maƙasudin bangaskiyarsu ba sai tare da mu.
”Saboda haka, da yake muna kewaye da irin wannan taron shaidu mai girma, sai mu yar da duk abin da yake hana mu da kuma zunubin da yake saurin daure mu, mu kuma yi tseren da aka sa a gabanmu da nacewa. Bari mu kafa idanunmu a kan Yesu, tushe da kuma kammalar bangaskiyarmu, wanda ya jure kunyar gicciye da aka yi masa, domin ya san cewa daga baya zai yi farin ciki ya yi haka. Yanzu kuma yana zaune a hannun dama na kursiyin Allah. Ku lura da wannan wanda ya jure da irin hamayyan nan daga masu zunubi, don kada ku gaji, har ku fid da zuciya.
”Cikin famanku da zunubi, ba ku yi tsayayya har ga zub da jininku ba tukuna. Kun kuma manta da kalmar ƙarfafawan nan da tana ce da ku ’ya’ya, “Ɗana kada ka rena horon Ubangiji, kada kuma ka fid da zuciya sa’ad da ya kwaɓe ka, domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna, yakan kuma hori duk wanda yakan karɓa a matsayin ɗa.” Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ’ya’ya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa? In ba a hore ku ba (kowa kuwa yakan sami horo), to, ku shegu ne ba ’ya’yan gida ba. Ban da haka ma, dukanmu mun kasance da ubannin jiki waɗanda suka hore mu muka kuma yi musu ladabi. Ashe, bai kamata mu yi wa Uban ruhohinmu biyayya mu kuwa rayu ba! Ubanninmu sun hore mu na ɗan lokaci yadda suka ga ya fi kyau; amma Allah yakan hore mu don amfaninmu, domin mu sami rabo cikin tsarkinsa. Babu horon da yake da daɗi a lokacin da ake yinsa, sai dai zafi. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.
”Saboda haka, sai ku ƙarfafa raunanan hannuwanku da gwiwoyinku marasa ƙarfi! “Ku shirya hanyoyi marasa gargaɗa saboda ƙafafunku,” don kada guragu su daɗa gurguntawa, sai dai su warke.
”Ku riƙa tunawa da waɗanda suke a kurkuku kamar tare kuke a kurkuku, da kuma waɗanda ake gwada musu azaba, kamar ku ake yi wa.
”Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce, “Ba zan taɓa bar ka ba; ba zan taɓa yashe ka ba.” Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce, “Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini?”
”Haka ma Yesu ya sha wahala a bayan gari don yă tsarkake mutane ta wurin jininsa. Saboda haka, sai mu fita mu je wajensa a bayan sansani, muna ɗaukar kunyar da ya sha. Gama a nan ba mu da dawwammamen birni, sai dai muna zuba ido a kan birnin nan mai zuwa.
”Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah, yabon leɓuna da yake shaidar sunansa. Kada kuma ku manta yin aikin nagari da kuma taimakon waɗansu, gama da irin waɗannan hadayu ne Allah yake jin daɗi.
”Ku ɗauki wannan da farin ciki mai tsabta, ’yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje na kowane iri suka zo muku, domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi daurewa. Dole daurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba.
”Mai albarka ne mutumin da yake daurewa cikin gwaji, gama bayan ya yi nasara da gwajin, zai sami rawanin rai wanda Allah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa.
”’Yan’uwa, ku ɗauki annabawa da suka yi magana a cikin sunan Ubangiji, a matsayin gurbi na haƙuri a cikin shan wahala. Kamar yadda kuka sani, mukan ce da waɗanda suka jure, masu albarka ne. Kun ji daurewar Ayuba, kuka kuma ga abin da Ubangiji ya yi a ƙarshe. Ubangiji yana cike da tausayi da jinƙai.
”Akwai waninku da yake shan wahala? Ya kamata yă yi addu’a. Akwai wani mai murna? Sai yă rera waƙoƙin yabo. Akwai waninku da yake ciwo? Ya kamata yă kira dattawan ikkilisiya su yi masa addu’a, su kuma shafa masa mai cikin sunan Ubangiji. Addu’ar da aka yi cikin bangaskiya, za tă warkar da marar lafiya, Ubangiji zai tashe shi. In ya yi zunubi kuwa za a gafarta masa. Saboda haka, ku furta wa juna zunubanku, ku yi addu’a saboda juna, domin ku sami warkarwa. Addu’ar mai adalci tana da iko da kuma amfani.
”A kan wannan kuke cike da farin ciki ƙwarai, ko da yake yanzu na ɗan lokaci kuna fuskantar baƙin ciki daga gwaje-gwaje iri-iri. Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan gwada ta da wuta, domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi.
”Gama abin yabo ne in mutum ya yi haƙuri cikin zafin wahalar rashin adalci saboda yana sane da Allah. Amma ina abin taƙama in kuka sha duka saboda kun yi laifi kuka kuma jimre? Sai dai in kuka sha wahala saboda yin nagari kuka kuma jimre, abin yabo ne a gaban Allah. Ga wannan ne aka kira ku, domin Kiristi ya sha wahala dominku, ya bar muku gurbin da ya kamata ku bi. “Bai taɓa yin laifi ba sam, ba a kuma sami ƙarya a bakinsa ba.” Sa’ad da suka zazzage shi, bai rama ba; sa’ad da ya sha wahala, bai yi barazana ba. A maimakon haka, ya miƙa kansa ga wanda yake shari’ar adalci. Shi kansa ya ɗauki zunubanmu a jikinsa a kan itace, domin mu mutu ga zunubai mu kuma rayu ga adalci; ta wurin raunukansa ne kuka sami warkarwa.
”Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.”
”Ya fi kyau, in nufin Allah ne, a sha wahala don yin nagarta fiye da yin mugunta. Gama Kiristi ya mutu domin zunubi sau ɗaya tak, mai adalci saboda marasa adalci, don yă kawo ku ga Allah. An kashe shi a cikin jiki, amma an rayar da shi a Ruhu,
”Saboda haka, da yake Kiristi ya sha wahala a jikinsa, sai ku ma ku yi wa kanku ɗamara da irin wannan hali, gama wanda ya sha wahala a jikinsa ya gama da zunubi ke nan.
”Abokaina ƙaunatattu, kada ku yi mamakin gwaji mai tsananin da kuke sha, sai ka ce wani baƙon abu ne yake faruwa da ku. Sai dai ku yi murna cewa kuna tarayya cikin shan wahalolin Kiristi, domin ku kai ga farin ciki mai yawa sa’ad da aka bayyana ɗaukakarsa. In an zage ku saboda sunan Kiristi, ku masu albarka ne, gama Ruhun ɗaukaka da kuma na Allah yana bisanku. In kuna shan wahala, kada yă zama don ku masu kisankai ne ko ɓarayi ko masu wani irin laifi ko kuma masu shisshigi. Amma fa, in kuka sha wahala a matsayin ku Kirista ne, kada ku ji kunya, sai dai ku yabi Allah cewa kuna amsa wannan suna.
”Saboda haka, waɗanda suke shan wahala bisa ga nufin Allah ya kamata su danƙa kansu ga Mahaliccinsu mai aminci, su kuma ci gaba da aikata abin da yake daidai.
”Zuwa ga dattawan da suke cikinku, ina roƙo a matsayin ɗan’uwanku dattijo, mashaidin shan wahalar Kiristi wanda kuma shi ma zai sami rabo cikin ɗaukakar da za a bayyana.
”Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yă ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama. Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku. Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye. Ku yi tsayayya da shi, kuna tsayawa daram cikin bangaskiya, domin kun san cewa ’yan’uwanku ko’ina a duniya suna shan irin wahalolin nan. Allah mai dukan alheri, wanda ya kira ku ga madawwamiyar ɗaukaka cikin Kiristi, bayan kun sha wahala na ɗan lokaci, shi da kansa zai raya ku, yă kuma sa ku yi ƙarfi, ku kahu, ku kuma tsaya daram.
”Ikonsa na Allahntaka ya ba mu kome da muke bukata don rayuwa da kuma tsoron Allah ta wurin sanin wanda ya kira mu ta wurin ɗaukakarsa da nagartarsa.
”in haka ne, to, Ubangiji ya san yadda zai ceci mutane masu tsoron Allah daga gwaje-gwaje, yă kuma tsare marasa adalci don ranar hukunci, har yă zuwa ranar shari’a.
”Amma kada ku manta da wannan abu guda ɗaya, abokaina ƙaunatattu. Ga Ubangiji kwana ɗaya kamar shekaru dubu ne, shekaru dubu kuma kamar kwana ɗaya ne. Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani yă hallaka, sai dai kowa yă kai ga tuba.
”Ku, ’ya’yana ƙaunatattu, ku daga Allah ne, kun kuma yi nasara a kan magabtan Kiristi, domin wanda yake a cikinku ya fi wanda yake a duniya girma.
”Ta haka muka sani, muke kuma dogara ga ƙaunar da Allah yake mana. Allah ƙauna ne. Duk wanda yake rayuwa cikin ƙauna, yana rayuwa a cikin Allah ne, Allah kuma a cikinsa. Ta haka, ƙauna ta zama cikakkiya a cikinmu domin mu kasance masu ƙarfin hali a ranar shari’a, domin a wannan duniya muna kama da shi. Babu tsoro cikin ƙauna. Cikakkiyar ƙauna dai takan kawar da tsoro, domin hukunci ne yake kawo tsoro. Mai jin tsoro ba cikakke ba ne a cikin ƙauna.
”domin duk haifaffe na Allah yana cin nasara a kan duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta ba mu wannan nasara a kan duniya. Wa ya cin nasara a kan duniya? Sai wanda ya gaskata cewa Yesu Ɗan Allah ne.
”Wannan shi ne ƙarfin halin da muke da shi sa’ad da muke zuwa a gaban Allah, gama mun san cewa kome muka roƙa bisa ga nufinsa, yakan saurare mu. In kuwa muka san cewa yana sauraranmu, ko mene ne muka roƙa, mun sani, mun riga mun sami abin da muka roƙa daga gare shi ke nan.
”Abokina ƙaunatacce, ina addu’a ka sami zaman lafiya don kome yă yi maka daidai, kamar yadda ruhunka yake zaune lafiya.
”‹Ni ne Rayayye, dā na mutu, ga shi kuwa ina a raye har abada abadin! Ina kuma riƙe da mabuɗan mutuwa da na Hades.›
”‹Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon ci daga itacen rai, da yake cikin aljannar Allah.›
”‹“Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Simirna, ka rubuta,› ‹Waɗannan su ne kalmomin wannan da yake na Farko da na Ƙarshe, wanda ya mutu ya kuma sāke tashi da rai.› ‹Na san wahalarka da kuma talaucinka, duk da haka kai mai arziki ne! Na san ɓata suna da waɗannan suke yi maka waɗannan da suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, su dai majami’ar Shaiɗan ne.› ‹Kada ka ji tsoron wahalar da kake gab da sha. Ina gaya maka, Iblis zai sa waɗansunku a kurkuku don yă gwada ku. Za ku sha tsanani na kwana goma. Ka yi aminci ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka rawanin rai.›
”‹Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara mutuwa ta biyu ba za tă cuce shi ba ko kaɗan.›
”‹Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara zan ba shi kaɗan daga cikin ɓoyayyiyar Manna. Zan kuma ba shi farin dutse tare da sabon suna a rubuce a bisansa, sananne kawai ga mai karɓan dutsen.›
”‹Gare shi wanda ya ci nasara ya kuma aikata nufina har ƙarshe, zan ba shi iko a kan al’ummai.› ‹‘Zai yi mulki a kansu da sandar sarauta ta ƙarfe, zai farfashe su, kamar tukwanen yumɓu’›‹kamar yadda na karɓi iko daga Ubana.› ‹Zan kuma ba shi tauraron asubahi.› ‹Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.›
”‹Wanda ya ci nasara, kamar su, za a sanya masa fararen tufafi. Ba zan taɓa share sunansa daga cikin littafin rai ba, sai dai zan shaida sunansa a gaban Ubana da mala’ikunsa.› ‹Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.›
”‹Duk wanda ya ci nasara zan mai da shi ginshiƙi a haikalin Allahna. Ba kuwa zai sāke barin wurin ba. Zan rubuta a kansa sunan Allahna da kuma sunan birnin Allahna, sabuwar Urushalima, wadda take saukowa daga sama daga Allahna; ni kuma zan rubuta a kansa sabon sunana.› ‹Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.›
”‹Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon zama tare da ni a kursiyina, kamar yadda na ci nasara, kuma ina zaune tare da Ubana a kursiyinsa.› ‹Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.”›
”Na amsa na ce, “Ranka yă daɗe, kai ka sani.” Sai ya ce, “Waɗannan su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala; sun wanke tufafinsu suka kuma mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan. Saboda haka, “suna a gaban kursiyin Allah suna masa hidima dare da rana a cikin haikalinsa; kuma wannan mai zaune a kursiyin zai shimfiɗa tentinsa a bisansu. ‘Ba za su sāke jin yunwa ba; ba za su kuma sāke jin ƙishirwa ba. Rana ba za tă buga su ba,’ ko kuma kowane irin zafin ƙuna. Gama Ɗan Ragon da yake a tsakiyar kursiyin zai zama makiyayinsu; ‘zai bi da su zuwa ga maɓulɓular ruwan rai.’ ‘Allah kuwa zai share dukan hawaye daga idanunsu.’ ”
”Sun ci nasara a kansa ta wurin jinin Ɗan Ragon da ta wurin kalmar shaidarsu; ba su ƙaunaci rayukansu sosai har da za su ja da baya daga mutuwa.
”Wannan yana bukata haƙuri, a gefen tsarkakan da suke biyayya da umarnan Allah suka kuma kasance da aminci ga Yesu. Sai na ji murya daga sama ta ce, “Rubuta, Masu albarka ne matattun da suka mutu cikin Ubangiji daga yanzu zuwa gaba.” “I, za su huta daga faman aikinsu, gama ayyukansu za su bi su,” in ji Ruhu.
”A cikinta aka sami jinin annabawa, da na tsarkaka, da kuma na dukan waɗanda aka kashe a duniya.”
”Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu.
”Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe.” Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. “Ina yin kome sabo!” Sai ya ce, “Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma.” Ya ce mini, “An gama. Ni ne Alfa da kuma Omega, na Farko da kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi abin sha kyauta daga maɓulɓular ruwan rai. Duk wanda ya ci nasara zai gāji dukan wannan, zan kuma zama Allahnsa, shi kuma zai zama ɗana.
”