30 – Fyaucewa
Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Fyaucewa.
Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Fyaucewa.
‹“Nan da nan bayan tsabar wahalan nan› ‹“ ‘sai a duhunta rana,› ‹wata kuma ba zai ba da haskensa ba;› ‹taurari kuma za su fāffāɗi daga sararin sama,› ‹za a kuma girgiza abubuwan sararin sama.’› ‹“A sa’an nan ne alamar dawowar Ɗan Mutum zai bayyana a sararin sama, dukan al’umman duniya kuwa za su yi kuka. Za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gizagizan sararin sama, da iko da kuma ɗaukaka mai girma.› ‹Zai kuwa aiki mala’ikunsa su busa ƙaho mai ƙara sosai, za su kuwa tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga wannan bangon duniya zuwa wancan.›
”Gama Ubangiji kansa zai sauko daga sama, da umarni mai ƙarfi, da muryar babban mala’ika da kuma busar ƙahon Allah, waɗanda suka mutu kuwa cikin Kiristi za su tashi da farko. Bayan haka, mu da muke da rai da aka bari, za a ɗauke mu tare da su a cikin gizagizai don mu sadu da Ubangiji a sararin sama. Ta haka za mu kasance tare da Ubangiji har abada.
”Game da dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi da game da tattara mu gare shi, muna roƙonku, ’yan’uwa, kada ku yi saurin jijjiguwa ko kuwa hankalinku yă tashi ta wurin wani annabci, rahoto ko wasiƙar da an ce daga wurinmu ne, cewa ranar Ubangiji ta riga ta zo. Kada ku bar wani yă ruɗe ku ko ta yaya, gama wannan rana ba za tă zo ba sai an yi tawayen nan an kuma bayyana mutumin tawayen nan, mutumin da aka ƙaddara ga hallaka. Zai yi gāba yă kuma ɗaukaka kansa a bisa kome da ya shafe sunan Allah, ko kuma ake yi wa sujada, domin yă kafa kansa a haikalin Allah, yana shelar kansa a kan shi Allah ne.
”Zan kuma sa ƙiyayya tsakaninka da macen, tsakanin zuriyarka da zuriyarta. Zai ragargaje kanka, kai kuma za ka sari ɗiɗɗigensa.”
”Na san wanda zai fanshe ni yana nan da rai, kuma a ƙarshe zai tsaya a kan duniya. Kuma bayan an hallaka fatata, duk da haka a cikin jiki zan ga Allah. Zan gan shi da kaina da idanuna, Ni, ba wani ba ne. Zuciyata ta cika da wannan tunani!
”A kwanaki masu zuwa za a kafa dutsen haikalin Ubangiji a matsayin babba cikin duwatsu; za a daga shi bisa tuddai, kuma dukan al’ummai za su bumbunto zuwa gare shi. Mutane da yawa za su zo su ce, “Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji, zuwa gidan Allah na Yaƙub. Zai koya mana hanyoyinsa, domin mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.” Dokar za tă fito daga Sihiyona, maganar Ubangiji daga Urushalima. Zai shari’anta tsakanin al’ummai zai kuma sulhunta faɗar mutane masu yawa. Za su mai da takubansu su zama garemani māsunsu su zama wuƙaƙen askin itatuwa. Al’umma ba za tă ƙara ɗauki takobi a kan al’umma ba, ba kuwa za su ƙara yin horarwar yaƙi.
”Ku tafi cikin duwatsu, ku ɓuya cikin ƙasa daga razanar Ubangiji da kuma darajar ɗaukakarsa! Za a ƙasƙantar da mai girman kai za a kuma lalatar da fariyar masu ɗaga kai; Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana. Ubangiji Maɗaukaki yana da rana ajiye domin dukan masu girman kai da masu fariya domin dukan waɗanda aka ɗaukaka (zai kuwa ƙasƙantar da su), domin dukan al’ul na Lebanon, masu tsayi da masu fariya, da kuma dukan itatuwan oak na Bashan, domin dukan dogayen duwatsu da kuma tuddai masu tsayi, domin kowace doguwar hasumiya da kowace katanga mai ƙarfi, domin kowane jirgin ruwan kasuwanci da kuma jirgi mafi girma mafi kyau. Za a jawo mai girman kai ƙasa a kuma ƙasƙantar da mai ɗaga kai; Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana, za a kuma kawar da gumaka ƙaƙaf. Mutane za su gudu zuwa kogwannin duwatsu da kuma ramummuka a ƙasa daga razanar Ubangiji da kuma darajar ɗaukakarsa, sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya. A wannan rana mutane za su zubar wa jaba da jamage gumakansu na azurfa da gumakansu na zinariya da suka yi don su bauta musu. Za su gudu zuwa kogwannin duwatsu da kuma zuwa tsagaggun duwatsu daga razanar Ubangiji da kuma darajar ɗaukakarsa, sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya.
”Ubangiji zai wanke duk wani ƙazantar matan Sihiyona; ya tsabtacce jinin da aka zubar daga Urushalima ta wurin ruhun hukunci da yake ƙuna kamar wuta. Sa’an nan Ubangiji zai sa girgijen hayaƙi da rana da harshen wuta da dare a bisa dukan Dutsen Sihiyona da kuma bisa waɗanda suka tattaru a can; a bisa duka kuwa ɗaukakar za tă zama rumfa.
”Gama a gare mu an haifa mana yaro, a gare mu an ba da ɗa, gwamnati za tă kasance a kafaɗarsa. Za a ce da shi Mashawarci Mai Banmamaki, Allah Maɗaukaki Uban Madawwami, Sarkin Salama. Game da girmar gwamnatinsa da salama babu iyaka. Zai gāji sarki Dawuda, yă yi mulki a matsayinsa, zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Maɗaukaki ne ya yi niyyar aikata wannan duka.
”Ku yi ihu, gama ranar Ubangiji ta yi kusa za tă zo kamar hallaka daga Maɗaukaki. Saboda wannan, hannun kowane mutum zai yi rauni, ƙarfin halin kowane mutum zai kāsa. Tsoro zai kama su, zafi da azaba za su ci ƙarfinsu; za su yi ta murɗewa kamar mace mai naƙuda. Za su dubi juna a tsorace, fuskokinsu a ɓace. Duba, ranar Ubangiji tana zuwa, muguwar rana, mai hasala da zafin fushi, don ta mai da ƙasar kango ta kuma hallakar da masu zunubi da suke cikinta. Taurarin sama da ƙungiyoyinsu ba za su ba da haskensu ba. Rana za tă yi duhu wata kuma ba zai ba da haskensa ba. Zan hukunta duniya saboda muguntarta, mugaye saboda zunubansu. Zan kawo ƙarshe ga girman kan masu taƙama in kuma ƙasƙantar da ɗaga kan marasa tausayi. Zan sa mutum yă fi zinariya zalla wuyar samuwa, fiye da zinariyar Ofir wuyan gani. Saboda haka zan sa sammai su yi rawar jiki; duniya kuma za tă girgiza daga inda take a fushin Ubangiji Maɗaukaki, a ranar fushinsa mai ƙuna.
”zai haɗiye mutuwa har abada. Ubangiji Mai Iko Duka zai share hawaye daga dukan fuskoki; zai kawar da kunyar mutanensa daga dukan duniya. Ubangiji ne ya faɗa.
”Ubangiji yana fushi da dukan al’ummai; hasalarsa tana a kan mayaƙansu. Zai hallaka su tas, zai ba da su a karkashe. Za a jefar da waɗanda aka kashe gawawwakinsu za su yi wari; duwatsu za su jiƙu da jininsu. Za a tumɓuke dukan taurarin sammai za a kuma nannaɗe sararin sama kamar littafi; dukan rundunar sama za su fāffāɗi kamar ganyayen da suka yanƙwane daga kuringa, kamar ’ya’yan ɓauren da suka bushe daga itacen ɓaure. Takobina ya sha zararsa a cikin sammai; duba, ya sauko cikin hukunci a kan Edom, mutanen da zan hallaka tas. Takobin Ubangiji ya jiƙu da jini, ya rufu da kitse, jinin raguna da na awaki, kitse daga ƙodar raguna. Gama Ubangiji ya yi hadayar Bozra da kuma babban kisa a Edom. Babban bijimin jeji zai fāɗi tare da su, maruƙan bijimi da manyan bijimai. Ƙasarsu za tă cika da jini, ƙura kuma zai cika da kitse. Gama Ubangiji yana da ranar ɗaukar fansa, shekarar ramuwa, don biya wa Sihiyona bukata. Za a mai da rafuffukan Edom rami, ƙurarta za tă zama kibiritun farar wuta; ƙasarta za tă zama rami mai ƙuna! Ba za a kashe ta ba dare da rana; hayaƙinta za tă yi ta tashi har abada. Daga tsara zuwa tsara za tă zama kango; babu wani da zai ƙara wucewa ta wurin.
”“Ku juyo gare ni ku sami ceto, dukanku iyakokin duniya; gama ni ne Allah, kuma babu wani. Da kaina na rantse, bakina ya furta cikin dukan mutunci kalmar da ba za a janye ba. A gabana kowace gwiwa za tă durƙusa; ta wurina kowane harshe zai rantse.
”Nakan sanar da ƙarshe tun daga farko, daga fil azal, abin da yake zuwa nan gaba. Na ce nufina zai tabbata, kuma zan aikata dukan abin da na gan dama.
”Ki kasa kunne! Masu tsaronki sun tā da muryoyinsu; tare sun yi sowa ta farin ciki. Sa’ad da Ubangiji ya komo Sihiyona, za su gan shi da idanunsu.
”“Ga shi, na halicci sabuwar sama da kuma sabuwar duniya. Abubuwa na dā za a manta da su, ba kuwa za a ƙara tuna da su ba.
”“Kamar yadda sabuwar duniya da sabuwar sama za su tabbata a gabana,” in ji Ubangiji, “haka sunanku da zuriyarku za su tabbata.
”Kaito, gama wannan rana za tă zama mai girma! Babu kamar ta. Zai zama lokacin wahala wa Yaƙub, amma za a cece shi daga cikinta.
”“ ‘Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ni kaina zan nemi tumakina. Kamar yadda makiyayi yakan lura da tumakinsa da suka watse sa’ad da yake tare da su, haka zan lura da tumakina. Zan cece su daga dukan wuraren da aka watsar da su a ranar gizagizai da baƙin duhu. Zan dawo da su daga al’ummai in kuma tattara su daga ƙasashe, zan kuma kawo su cikin ƙasarsu. Zan yi kiwonsu a kan duwatsun Isra’ila, a maɓulɓulai da kuma cikin wuraren zamansu a ƙasar.
”Saboda haka yi annabci ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ya mutanena, zan buɗe kaburburanku in fitar da ku daga cikinsu; zan mai da ku ƙasar Isra’ila. Sa’an nan ku, mutanena, za ku san cewa ni ne Ubangiji, sa’ad da na buɗe kaburburanku na fitar da ku daga cikinsu.
”amma akwai Allahn da yake a sama wanda yake bayyana asirai, ya nuna wa sarki Nebukadnezzar abin da zai faru a kwanaki masu zuwa. Mafarkinka da wahayin da ya wuce cikin tunaninka a sa’ad da kake kwance a gadonka su ne,
”“Ya sarki, ka ga wata babbar siffa, mai girma, siffa ce mai haske, abar bantsoro tana tsaye a gabanka. An yi kan wannan siffa da zinariya zalla, ƙirjinta da kuma hannuwanta an yi su da azurfa, cikinta da kuma cinyarta da tagulla ne. An yi ƙafafun da ƙarfe, tafin ƙafafunta kuma an yi rabi da ƙarfe rabi kuma da yumɓu. A lokacin da kake dubawa, sai aka yanko wani dutse, amma ba da hannun mutum ba. Ya fāɗa a kan ƙafafun siffar na ƙarfen da aka haɗa da yumɓu aka kuma ragargaje su. Sai ƙarfen da yambun da tagulla da azurfan da kuma zinariyan suka ragargaje a lokaci ɗaya ya zama kamar ƙaiƙayi a masussuka a lokacin kaka. Sai iska ta kwashe su ta tafi, har ba a iya ganin ko alamarsu. Amma dutsen da ya fāɗo a siffar ya girke ya zama tsauni ya kuma cika dukan duniya.
”“Wannan shi ne mafarkin, yanzu kuma za mu fassara ta wa sarki. Ya, sarki, kai ne sarkin sarakuna. Allah na sama ya ba ka iko da girma da suna; a cikin hannunka ya sanya ɗan adam, da namun jeji da tsuntsayen sama. A duk inda suke zaune, ya maishe ka ka yi mulki a bisansu kai ne kan zinariyan nan na siffar. “A bayanka, za a yi wani mulki, wanda bai kai naka ba. A gaba kuma, za a yi mulki na uku wanda yake na tagulla, zai yi mulkin dukan duniya.
”A ƙarshe, za a yi mulki na huɗu, mai ƙarfi kamar ƙarfe, Da yake baƙin ƙarfe yakan kakkarya, ya ragargaje abubuwa, haka nan wannan mulki zai ragargaje sauran mulkoki Ka kuma ga an yi ƙafafun da yatsotsin da baƙin ƙarfe gauraye da yumɓu, wato, mulkin zai rabu, amma zai kasance da ƙarfi kamar na baƙin ƙarfe da yake gauraye da yumɓu. Kamar yadda yatsotsin rabi na ƙarfe rabi kuma na yumɓu ne, haka wannan mulki zai zama rabi mai ƙarfi rabi kuma marar ƙarfi. Kamar dai yadda ka ga ƙarfen ya gauraye da yumɓu, haka mutanen za su zama a gauraye amma ba za su haɗu da juna ba, kamar yadda baƙin ƙarfe da yumɓu ba su haɗuwa.
”“A lokacin mulkin waɗannan sarakunan, Allah na sama zai kafa mulki da ba zai taɓa rushewa ba, ba kuma za a ba ma waɗansu mutane ba. Zai ragargaje waɗannan mulkokin da kuma kawo su ga ƙarshe, amma shi wannan mulki zai dawwama har abada. Wannan shi ne ma’anar wannan wahayin da ka gani na dutsen da aka yanko daga jikin tsaunin, amma ba da hannun ɗan adam ba, dutsen da ya ragargaza ƙarfen, da tagullar, da yumɓun da azurfar da kuma zinariyar. “Allah mai girma ya nuna wa sarki abin da zai faru nan gaba. Mafarkin gaskiya ne, fassararsa kuma abin dogara ne.”
”Daniyel ya ce, “A cikin wahayina da dare na duba, a gabana kuwa ga kusurwoyi huɗu na sama suna gurɓata babban teku. Sai ga dabbobi huɗu, kowannensu ya yi dabam da sauran, suna fitowa daga teku. “Na farkon ya yi kamar zaki kuma yana da fikafikai kamar gaggafa. Ina kallo, sai aka fizge fikafikanta, aka ɗaga ta sama, aka sa ta tsaya a kan ƙafafu biyu kamar mutum, aka ba ta tunani irin na mutum. “A gabana kuma ga dabba ta biyu, wadda ta yi kamar beyar. Aka ɗaga ta a gefenta guda, tana kuwa da haƙarƙarai uku a bakinta a tsakanin haƙoranta. Aka faɗa mata, ‘Tashi ki cika cikinki da ɗanyen nama!’ “Bayan haka, na duba, a gabana kuwa ga wata dabba wadda ta yi kamar Damisa, a bayanta kuma tana da fikafikai huɗu irin na tsuntsu. Wannan dabbar tana da kawuna huɗu, aka kuma ba ta iko tă yi mulki. “Bayan haka, a cikin wahayina da dare na duba, a gabana kuwa ga dabba ta huɗu, wadda take da bantsoro da banrazana da kuma iko ƙwarai. Tana da manyan haƙoran ƙarfe; ta ragargaje ta cinye abin da ta kama, ta kuma tattaka duk abin da ya rage a ƙarƙashin ƙafafunta. Ta bambanta da dukan sauran dabbobin da suka riga ta, tana kuma da ƙahoni goma. “Yayinda nake cikin tunani game da ƙahonin nan, a gabana kuwa ga wani ƙaho, ɗan ƙanƙani, wanda ya fito daga cikinsu; kuma an tumɓuke uku daga cikin ƙahonin farko kafin wannan. Wannan ƙaho yana da idanu kamar na mutum da kuma bakin da yake maganganun fariya.
”“Ina cikin dubawa, “sai aka ajiye kursiyoyi, sai ga wani wanda yake tun fil azal ya zauna a mazauninsa. Rigarsa ta yi fari fat kamar ƙanƙara; gashin kansa sun yi fari kamar ulu. Kursiyinsa kuma harshen wuta, dukan ƙafafun kursiyin masu kama da keken yaƙin, wuta ne. Kogin wuta yana gudu, yana fitowa daga gabansa. Dubun dubbai sun yi masa hidima; dubu goma sau dubu goma sun tsaya a gabansa. Aka zauna don shari’a, aka kuma buɗe littattafai.
”“Sa’an nan na ci gaba da kallo saboda kalmomin fariyar da wannan ƙaho yake furtawa. Na yi ta kallo har sai da aka yanke dabbar, aka kuma hallaka jikinta a cikin wuta. (An tuɓe sauran dabbobin daga mulkinsu, amma aka bar su su rayu na wani lokaci.)
”“A wahayina na dare, na ga a gabana wani kamar ɗan mutum yana saukowa tare da gizagizan sama. Ya kusaci Wannan wanda yake Tun fil azal aka kuma kai shi gabansa. Aka ba shi mulki, daraja da kuma mafificin iko; dukan mutane, da al’ummai, da mutane daga kowane harshe suka yi masa sujada. Mulkinsa kuwa dawwammamen mulki ne da ba zai ƙare ba, sarautarsa kuma ba ta taɓa lalacewa.
”‘Waɗannan manyan dabbobi huɗu, Masarautai ne huɗu waɗanda za su taso a duniya. Amma tsarkaka na Mafi Ɗaukaka za su karɓi wannan sarauta, za su kuwa mallake ta har abada, I, har abada abadin.’
”“Sa’an nan kuma sai na so in san ma’anar wannan dabba ta huɗu, wadda ta yi dabam da sauran dabbobin da suke da matuƙar bantsoro, da take da haƙoran ƙarfe da kuma farcen tagulla, dabbar ta ragargaje ta cinye abin da ta kama, ta kuma tattaka duk abin da ya rage a ƙarƙashin ƙafafunta. Na kuma so in gane game da ƙahonin nan guda goma da suke a kanta da kuma game da ƙahon nan da ya fito, wanda aka tumɓuke ƙahoni uku a gabansa, ƙahon nan da yake da idanu da bakin da yake furta manyan maganganun fariya, wanda ya yi kamar ya fi sauran girma. Ina cikin dubawa, sai ga wannan ƙaho yana yaƙi da tsarkaka yana kuma cin nasara a kansu, sai da Wannan wanda yake tun fil azal ya zo ya furta hukunci, aka kuma ba tsarkaka na Mafi Ɗaukaka gaskiya, lokaci kuwa ya cika sai suka karɓi mulki.
”“Sai ya ba ni wannan bayani, ‘Dabbar nan ta huɗu, ita ce mulki na huɗu da zai bayyana a duniya. Zai bambanta da dukan sauran mulkoki, zai kuma cinye dukan duniya, yă tattake ta, yă kuma ragargaje ta. Ƙahonin nan goma, sarakuna ne goma waɗanda za su taso daga wannan mulki. Bayansu kuma, wani sarki zai taso, wanda ya sha dabam da waɗanda suka riga shi. Zai rinjayi sarakunan nan uku. Zai yi maganar saɓo a kan Mafi Ɗaukaka, zai kuma tsananta wa tsarkaka yă kuma yi ƙoƙarin sāke lokuta da shari’u. Za a miƙa tsarkaka a hannunsa na wani lokaci, lokuta da kuma rabin lokaci. “ ‘Amma majalisa za tă yi zama, za a karɓe ikonsa, a kuma hallaka shi gaba ɗaya har abada. Sa’an nan za a ba da mulki, iko da girma na mulkokin da suke a ƙarƙashin dukan sammai ga tsarkaka, mutane na Mafi Ɗaukaka. Mulkinsa kuwa mulki ne marar matuƙa, kuma dukan masu mulki za su yabe shi, su kuma yi masa biyayya.’
”Daga cikin ɗayansu kuma wani ƙaramin ƙaho ya fito, ya yi girma ya ƙasaita ƙwarai zuwa kudu da kuma gabas da wajen Kyakkyawar Ƙasa. Ya yi girma sai da ya kai rundunar sammai, ya kuma fid da waɗansu rundunar taurari zuwa ƙasa ya kuma tattake su. Sai ya ɗora kansa ya zama mai girma kamar Sarkin runduna; sai aka ɗauke hadaya ta kullayaumi daga gare shi, aka kuma saukar da wurin masujadarsa ƙasa. Saboda tawaye, sai aka ba da rundunar tsarkaka da kuma hadayar ƙonawa ta kowace rana ga ƙahon. Sai ya yi watsi da gaskiya, ya yi abin da ya ga dama, ya kuwa yi nasara. Sa’an nan na ji mai tsarkin nan yana magana, wani mai tsarki kuma ya ce da wancan, “Har yaushe wannan wahayi zai tabbata, wahayi game da hadaya ta kullayaumi, da tawayen da yake kawo lalacewa, da kuma miƙa wuri mai tsarki da kuma na rundunar da za a tattake a ƙarƙashin sawu?” Sai ya ce mini, “Zai ɗauki safiya da yamma 2,300; sa’an nan za a sāke tsarkake wuri mai tsarki.”
”Yayinda ni, Daniyel, nake duban wahayi ina ƙoƙari in fahimce shi, sai ga wani a gabana wanda ya yi kama da mutum. Sai na ji muryar wani mutum daga Ulai tana cewa, “Jibra’ilu, faɗa wa wannan mutum ma’anar wahayin.” Da ya zo kusa da inda nake tsaye, na firgita na kuma fāɗi rubda ciki. Ya ce da ni “Ɗan mutum, ka gane da cewa wannan wahayi yana magana ne a kan kwanakin ƙarshe.” Yayinda yake magana da ni, barci mai nauyi ya kwashe ni, da nake kwance rubda ciki. Sai ya taɓa ni ya kuma tashe ni tsaye. Sai ya ce, “Zan faɗa maka abin da zai faru a lokacin fushi, saboda wahayin yana magana ne a kan lokacin da aka ƙayyade na ƙarshe.
”“Can wajen ƙarshe mulkinsu, sa’ad da muguntarsu ta kai intaha, wani mugun sarki mai rashin hankali, uban makirci, zai fito. Zai yi ƙarfi ƙwarai da gaske, amma ba da ikonsa ba. Zai jawo mummunar hallakarwa kuma zai yi nasara a duk abin da ya sa gaba. Zai hallakar da majiya ƙarfi da kuma tsarkaka. Zai sa yaudara ta ƙara yin yawa, zai ɗaukaka kansa. Sa’ad da suke ji sun sami mafaka, zai hallaka mutane da yawa sa’an nan kuma yă fara gāba da Sarkin sarakuna. Duk da haka za a hallaka shi, amma ba da ikon mutum ba. “Wahayin nan na safiya da yamma da aka nuna maka gaskiya ne, amma ka ɓoye wahayin, gama ya shafi nan gaba mai tsawo ne.”
”“An ƙayyade wa jama’arka da tsattsarkan birninka shekara ɗari huɗu da tasa’in domin a kawo ƙarshen laifi da zunubi, domin a yi kafarar laifi, sa’an nan a shigo da adalci madawwami, a rufe wahayi da annabci, a tsarkake haikali. “Sai ka sani ka kuma fahimci wannan; Tun daga sa’ad da aka kafa doka don a maido a kuma sāke gina Urushalima har sai Shafaffen nan, mai mulki, ya zo, za a yi shekara arba’in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da mafaka. Bayan shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu, za a datse Shafaffen nan zai kuma kasance ba shi da kome. Mutanen mai mulkin za su zo su hallaka birnin da kuma wuri mai tsarki. Ƙarshen zai zo kamar rigyawa. Yaƙi zai ci gaba har ƙarshe, a kuma hallakar kamar yadda aka ƙaddara. Zai tabbatar da alkawari da mutane masu yawa har na shekara bakwai. A tsakiyar bakwai ɗin nan ɗaya zai kawo ƙarshen duk wata hadaya da baiko. Kuma a kusurwar haikali zai sa abin ƙyama mai kawo hallaka, har sai ƙarshen da aka ƙaddara ya auko wa wanda ya sa abin ƙyama.”,
”Yanzu na zo domin in bayyana maka abin da zai faru da mutanenka nan gaba, gama wahayin ya shafi lokacin da bai riga ya zo ba ne.”
”Sarakunan nan biyu sun sa mugunta a ransu. Za su zauna a tebur guda su yi ta shara wa juna ƙarya, amma a banza, gama lokacin da aka ƙayyade bai yi ba tukuna. “Sarkin Arewa zai koma ƙasarsa da dukiya mai girma, amma zuciyarsa za tă yi gāba da tsattsarkan alkawari. Zai ɗauki mataki a kan wannan abu sa’an nan yă koma ƙasarsa.
”“A ƙayyadadden lokaci zai sāke kai wa Kudu hari, amma a wannan karo abin da zai faru zai sha bamban daga abin da ya faru can baya. Jiragen ruwa yammancin bakin teku za su yi gāba da shi, zuciyarsa kuwa za tă yi sanyi. Sa’an nan zai juya ya huce haushinsa a kan tsattsarkan alkawari. Zai komo yă nuna jinƙai ga waɗanda suka juya wa tsattsarkan alkawari baya. “Mayaƙansa za su taso su ƙazantar da kagarar haikali za su kuma kawar da hadaya ta kullum. Sa’an nan za su kafa abin banƙyama da yake lalatarwa. Ta wurin daɗin baki zai gurɓata waɗannan da suka karya alkawari, amma mutanen da suka san Allahnsu za su yi tsayin daka su yi jayayya da shi. “Waɗanda suke da hikima za su wayar da kan mutane da yawa, duk da haka za a kashe su da takobi, waɗansu da wuta, a washe waɗansu a kai su bauta. Sa’ad da suka fāɗi, za su sami ɗan taimako, mutane da yawa za su haɗa kai da su, amma da munafunci.
”Waɗansu masu hikima za su yi tuntuɓe, don a tsabtacce su, a tsarkake su, su yi tsab, har matuƙar da aka ƙayyade ta yi.
”“Sarkin zai yi abin da ya ga dama. Zai ɗaukaka yă kuma girmama kansa gaba da kowane allah zai kuma faɗa munanan abubuwa a kan Allahn alloli. Zai yi nasara har sai lokacin hukunci ya cika, gama abin da aka ƙaddara zai cika. Ba zai kula da alloli iyayensa ba ko wanda mata suke sha’awa, balle ma yă ga darajar wani allah, amma zai ɗaukaka kansa gaba da su duka. A maimakonsu, zai ɗaukaka allahn kagarai; allahn da kakanninsa ba su ko sani ba, shi ne zai miƙa masa zinariya, da azurfa, da duwatsu masu daraja, da abubuwa masu tsada. Zai kai wa kagarai mafi ƙarfi hari da taimakon baƙon allah zai kuma girmama waɗanda suka yarda da shi zai ba su girma, ya kuma shugabantar da su a kan mutane da yawa, zai raba musu ƙasa ta zama ladansu.
”“A lokaci ƙarshe sarkin Kudu zai tasar masa da yaƙi, sarkin Arewa kuwa zai tunzura, yă tasar masa da kekunan yaƙi da mahayan dawakai, da jiragen ruwa da yawa. Zai ratsa ƙasashe, yă ci su da yaƙi, yă wuce. Zai kuma mamaye Kyakkyawa Ƙasa. Ƙasashe masu yawa za su fāɗi, amma Edom, Mowab da kuma shugabannin Ammon za su kuɓuta daga hannunsa. Zai fadada mulkinsa har zuwa ƙasashe masu yawa; Masar ma ba za tă tsira ba. Zai mallaki dukiyoyi na zinariya, da na azurfa, da dukan abubuwa masu tsada na Masar. Zai kuma ci Libiyawa da Kush da yaƙi. Amma labari daga gabas da arewa za su firgita shi, shi kuwa zai ci gaba da yin yaƙi da zafi, yă karkashe mutane da yawa, yă shafe su. Zai kafa tentin mulkinsa tsakanin tekunan da suke a kyakkyawan tsauni mai tsarki. Duk da haka zai zo ga ƙarshensa, kuma babu wanda zai taimake shi.
”“A wannan lokaci Mika’ilu, babban mai mulki wanda yake kāre mutanenka, zai tashi. Za a yi lokacin matsananciyar wahala wanda ba a taɓa yi tun farkon ƙasashe har zuwa yanzu. Amma a lokacin da mutanenka, kowane mutum wanda aka sami sunansa a rubuce a cikin littafin, za a cece shi. Ɗumbun mutanen da suka yi barci cikin turɓayar duniya za su farka, waɗansu zuwa ga rai madawwami, waɗansu zuwa ga madawwamiyar kunya da kuma madawwamin ƙasƙanci. Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar hasken samaniya, waɗanda kuma suka jagoranci waɗansu da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin. Amma kai, Daniyel, ka rufe zancen nan ka kuma liƙe kalmomin littafin nan har sai ƙarshe. Mutane da yawa za su yi ta kai komo don neman sani.”
”Sa’an nan ni, Daniyel, na duba, a gabana kuwa ga waɗansu mutum biyu tsaye, ɗaya a wannan hayen kogi ɗaya kuma a ƙetaren kogin. Ɗayansu ya ce wa mutumin da yake sanye da tufafin lilin, wanda yake a saman ruwan kogin, “Har yaushe waɗannan abubuwan banmamakin za su cika?” Mutumin da yake sanye da tufafin lilin, wanda yake a saman ruwan kogin, ya ɗaga hannun damansa da kuma na hagunsa sama, sai na ji yana rantsuwa da wannan da yake raye har abada, yana cewa, “Zai kasance na ɗan lokaci, lokuta da rabin lokaci. Za a kammala waɗannan abubuwa, sa’ad da aka gama ragargaje ikon tsarkakan mutane.”
”Na kuma ji, amma ban fahimta ba. Don haka sai na yi tambaya, “Ranka yă daɗe, mene ne ƙarshen waɗannan abubuwa?” Sai ya amsa ya ce, “Ka kama hanyarka, Daniyel, domin a rufe kalmomin aka kuma liƙe su har sai ƙarshen lokaci. Za a tsarkake mutane da yawa, za a maishe su marasa aibi a kuma tace su; amma mugaye za su ci gaba da mugunta. Babu wani mugun da zai fahimta, amma waɗanda za su zama masu hikima za su fahimta.
”“Daga lokacin da za a hana miƙa hadayar ƙonawa ta yau da kullum, a kuma kafa abin banƙyama, wanda yake lalatarwa, za a yi kwana 1,290. Mai albarka ne wanda ya jira har yă zuwa ƙarshen kwanakin nan 1,335. “Gare ka dai, ka yi tafiyarka har zuwa ƙarshe. Za ka huta, sa’an nan a ƙarshen kwanaki za ka tashi don karɓi sashen gadon da aka ba ka.”
”“A waccan rana,” in ji Ubangiji, “za ki ce da ni ‘mijina’; ba za ki ƙara ce ni ‘maigidana’ ba.
”Ku busa ƙaho a cikin Sihiyona; ku yi karar amo a tsaunina mai tsarki. Bari dukan mazaunan ƙasar su yi rawan jiki, gama ranar Ubangiji tana zuwa. Tana gab da faruwa rana ce ta baƙin duhu ƙirin, ranar gizagizai ce baƙi ƙirin. Babbar rundunar mayaƙa mai ƙarfi tana zuwa kamar ketowar alfijir a kan duwatsu yadda ba a taɓa ganin irinta ba, ba kuwa za a ƙara ganin irinta ba har tsararraki masu zuwa. A gabansu wuta tana ci, a bayansu ga harshen wuta yana ci, A gabansu ƙasa ta yi kamar gonar Eden, a bayansu kuma jeji ne wofi, babu abin da ya kuɓuce musu. Suna da kamannin dawakai; suna gudu kamar dokin yaƙi. Da motsi kamar na kekunan yaƙi sun tsallake ƙwanƙolin duwatsu, kamar ƙarar harshen wuta mai cin tattaka, kamar runduna mai ƙarfi wadda ta ja dāgār yaƙi. Da ganinsu, al’ummai sun kamu da azaba; kowace fuska ta yanƙwane. Sukan auka kamar jarumawa; sukan hau katanga kamar sojoji. Kowa yana takawa bisa ga tsari, ba mai kaucewa. Ba sa turin juna, kowane yakan miƙe gaba. Sukan kutsa cikin abokan gāba ba mai tsai da su. Sukan ruga cikin birni, suna gudu a kan katanga. Sukan hau gidaje, sukan shiga ta tagogi kamar ɓarayi. A gabansu duniya takan girgiza, sararin sama kuma yakan jijjigu, rana da wata su yi duhu, taurari kuma ba sa ba da haske. Ubangiji ya yi tsawa wa shugaban mayaƙansa; sojojinsa sun fi a ƙirge masu ƙarfi ne kuma su waɗanda suke biyayya da umarninsa. Ranar Ubangiji da girma take; mai banrazana. Wa zai iya jure mata?
”“Daga baya kuma, zan zuba Ruhuna a bisan dukan mutane. ’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci, tsofaffinku za su yi mafarkai, matasanku za su ga wahayoyi. Har ma a bisan bayina, maza da mata, zan zuba Ruhuna a kwanakin nan.
”Zan nuna abubuwan banmamaki a cikin sammai da kuma a kan duniya, za a ga jini da wuta da murtukewar hayaƙi. Rana za tă duhunta wata kuma yă zama jini kafin isowar babbar ranan nan mai banrazana ta Ubangiji. Amma dukan waɗanda suka nemi Ubangiji za su tsira. Kamar yadda Ubangiji ya ce, gama a Dutsen Sihiyona da Urushalima akwai ceto, a cikin waɗannan da Ubangiji ya kira.
”Ku fito da lauje, gama girbi ya nuna. Ku zo, ku tattaka inabin, gama wurin matsewar ruwan inabi ya cika randunan tarawa kuma sun cika har suna zuba, muguntarsu da girma take!” Dubun dubbai suna a cikin kwarin yanke shawara! Gama ranar Ubangiji ta yi kusa a cikin kwarin yanke shawara. Za a duhunta rana da wata, taurari kuma ba za su ba da haske ba. Ubangiji zai yi ruri daga Sihiyona tsawa kuma daga Urushalima; duniya da sararin sama za su yi rawan jiki. Amma Ubangiji zai zama mafakar mutanensa, mafaka ga mutanensa Isra’ila.
”“Sa’an nan za ku san cewa ni, Ubangiji Allahnku, ina zaune a Sihiyona, dutsena mai tsarki. Urushalima za tă zama mai tsarki; baƙi ba za su ƙara mamaye ta ba. “A wannan rana duwatsu za su ɗiga da sabon ruwan inabi, tuddai kuma za su malmalo madara; dukan rafuffukan Yahuda za su yi ta gudano da ruwa. Maɓulɓula kuma za tă fito daga gidan Ubangiji haka ma ruwa a kwarin itatuwan ƙirya. Amma Masar za tă zama kango, Edom kuma hamada marar amfani, saboda kama-karyar da aka yi wa mutanen Yahuda, a ƙasar da aka zub da jinin marasa laifi. Za a zauna a Yahuda har abada Urushalima kuma daga tsara zuwa tsara. Alhakin jininsu, wanda ban gafarta ba, zan gafarta.” Ubangiji yana zama a Sihiyona!
”A kwanakin ƙarshe za a kafa dutsen haikalin Ubangiji yă zama babba a cikin duwatsu. Za a ɗaga shi sama da tuddai, mutane kuma za su riƙa ɗunguma zuwa gare shi. Al’ummai da yawa za su zo su ce, “Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji, zuwa gidan Allah na Yaƙub. Zai koya mana hanyoyinsa, don mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.” Doka za tă fita daga Sihiyona, maganar Ubangiji kuma daga Urushalima. Zai shari’anta tsakanin mutane yă kuma sulhunta tsakanin manyan al’ummai nesa da kuma kusa. Har su mai da takubansu su zama garemani, māsunsu kuma su zama wuƙaƙen askin itace. Al’umma ba za tă ɗauki takobi gāba da wata al’umma ba, ko a yi horarwa don yaƙi. Kowa zai zauna a tushen kuringar inabinsa da tushen ɓaurensa, kuma ba wanda zai tsoratar da su, gama Ubangiji Maɗaukaki ne ya faɗa.
”Babbar ranar Ubangiji ta yi kusa, ta yi kusa kuma tana zuwa da sauri. Ku saurara! Kukan ranar Ubangiji za tă yi zafi, za a ji kururuwan jarumi a can. Ranan nan za tă zama ranar fushi, rana ce ta baƙin ciki da azaba, rana ce ta tashin hankali da lalacewa, ranar duhu baƙi ƙirin, ranar gizagizai da baƙin duhu, rana ce ta busa ƙaho da kururuwar yaƙi gāba da birane masu mafaka, da kuma kusurwar hasumiyoyi. “Zan kawo baƙin ciki a kan mutane za su kuma yi tafiya kamar makafi, domin sun yi wa Ubangiji zunubi. Za a zubar da jininsu kamar ƙura kayan cikinsu kuma kamar najasa. Azurfarsu ko zinariyarsu ba za su iya cetonsu ba a ranar fushin Ubangiji.” A cikin zafin kishinsa za a hallaka dukan duniya gama zai kawo ƙarshen dukan mazaunan duniya nan da nan.
”Saboda haka ku jira ni,” in ji Ubangiji; “a ranar da zan tsaya in ba da shaida, Na yanke shawara in tattara dukan al’ummai, in tattara mulkoki in kuma zuba fushina a kansu, da dukan zafin haushina. Za a mamaye dukan duniya da zafin fushina.
”“Sa’an nan zan tsarkake leɓunan mutanen, don dukansu su kira bisa ga sunan Ubangiji su kuma yi masa hidima kafaɗa da kafaɗa.
”“Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ba da jimawa ba zan sāke girgiza sammai da kuma ƙasa, teku da busasshiyar ƙasa. Zan girgiza dukan al’ummai, marmarin kowace al’umma kuma zai taso, sa’an nan zan cika gidan nan da ɗaukaka,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. ‘Da zinariya da azurfa duka nawa ne,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. ‘Ɗaukakar gidan nan na yanzu za tă fi ɗaukakar gidan nan na dā,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. ‘A wannan wuri kuma zan ba da salama,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.”
”Ranar Ubangiji tana zuwa sa’ad da za a raba muku ganimar da aka washe daga gare ku. Zan tara dukan al’ummai su yaƙi Urushalima; za a ci birnin da yaƙi, za a washe gidaje, a kuma yi wa mata fyaɗe. Rabin birnin zai je bauta, amma ba za a kwashe sauran mutanen daga birnin ba. Sa’an nan Ubangiji zai fita yă yi yaƙi da waɗannan al’ummai, kamar yadda yake yaƙi a ranar yaƙi.
”A ranan nan ƙafafunsa za su tsaya a kan Dutsen Zaitun, gabas da Urushalima, za a kuma tsage Dutsen Zaitun kashi biyu daga gabas zuwa yamma, yă zama babban kwari, rabin dutsen zai matsa zuwa wajen arewa, rabi kuma zai matsa zuwa wajen kudu. Za ku gudu ta wajen kwarin dutsena, gama zai miƙe har zuwa Azel. Za ku gudu kamar yadda kuka guje wa girgizar ƙasa a kwanakin Uzziya sarkin Yahuda. Sa’an nan Ubangiji Allahna zai zo, tare da duk masu tsarki. A ranan nan ba za a kasance da haske ko sanyi ba, ko hazo mai duhu ba. Za tă zama rana ce ta musamman, ba yini ko dare, rana da take sananne ga Ubangiji. Sa’ad da yamma ta yi, za a yi haske. A ranan nan ruwan rai zai kwararo daga Urushalima, rabi zai gangara gabas zuwa teku rabi kuma zai gangara yamma zuwa Bahar Rum, a damina da rani.
”Ubangiji zai sama sarki bisa dukan duniya. A ranan nan za a kasance da Ubangiji ɗaya, ba wani suna kuma sai nasa.
”Ƙasar gaba ɗaya daga Geba zuwa Rimmon, kudu da Urushalima, za tă zama kamar Araba. Amma Urushalima za tă kasance a wurinta, daga Ƙofar Benyamin zuwa sashen Ƙofa ta Farko, zuwa Ƙofar Kusurwa, daga kuma Hasumiyar Hananel zuwa wurin matsin ruwan inabin sarki. Za a zauna a cikinka; ba za a ƙara hallaka ta ba. Urushalima za tă zauna lafiya. Ga bala’in da Ubangiji zai bugi dukan al’umman da suka yi yaƙi da Urushalima. Fatar jikinsu za tă ruɓe tun suna tsaye a ƙafafunsu, idanunsu za su ruɓe a cikin kwarminsu, harsunansu kuma zai ruɓe a cikin bakunansu. A ranan nan Ubangiji zai sa maza su cika da tsoro ƙwarai. Kowane mutum zai kama hannun ɗan’uwansa, za su kai wa juna hari. Yahuda ma za tă yi yaƙi a Urushalima. Za a tattara dukiyar al’umman da suke kewaye, za a tara zinariya da azurfa masu yawan gaske tare da tufafi. Irin wannan bala’i zai auko wa dawakai da alfadarai, raƙuma da jakuna, da kuma dukan dabbobi a wannan sansani.
”Sa’an nan waɗanda suka tsira daga cikin al’umman da suka yaƙe Urushalima za su haura shekara-shekara su yi wa Sarki, Ubangiji Maɗaukaki sujada, su kuma yi Bikin Tabanakul. In waɗansu mutanen da suke duniya ba su haura Urushalima suka yi wa Sarki, Ubangiji Maɗaukaki sujada ba, ba za su sami ruwan sama ba. In mutanen Masar ba su haura sun yi sujada ba, ba za su sami ruwan sama ba. Ubangiji zai kawo masu bala’in da ya aika wa al’umman da ba su haura sun yi Bikin Tabanakul ba. Wannan ne zai zama hukuncin Masar da kuma na dukan al’umman da ba su haura sun yi Bikin Tabanakul ba.
”A ranan nan za a rubuta TSARKI GA Ubangiji a jikin ƙararrawar dawakai, kuma tukwanen dahuwa a gidan Ubangiji za su zama kamar kwanoni masu tsarki a gaban bagade. Kowace tukunya a Urushalima da Yahuda za tă zama mai tsarki ga Ubangiji Maɗaukaki, kuma duk wanda ya zo don miƙa hadaya zai ɗauki waɗansu tukwane yă yi dahuwa da su. A ranan nan kuwa, ba Bakan’ane da zai ƙara kasance a gidan Ubangiji Maɗaukaki.
”Amma wa zai jure wa ranar zuwansa? Wa zai iya tsaya sa’ad da ya bayyana? Gama zai zama kamar wuta mai tace ƙarfe, ko sabulu mai wanki. Zai zama kamar mai tace azurfa da mai tsarkaketa; zai tsabtacce Lawiyawa, yă kuma tace su kamar zinariya da azurfa. Sa’an nan Ubangiji zai sami mutanen da za su kawo hadayu a cikin adalci.
”‹Gonar kuwa ita ce duniya, irin nan mai kyau kuwa suna a matsayin ’ya’yan mulkin. Ciyayin nan kuma su ne ’ya’yan mugun nan,› ‹abokin gāban da yake shuka su kuwa, Iblis ne. Lokacin girbi kuma shi ne ƙarshen zamani, masu girbin kuwa su ne mala’iku.› ‹“Kamar yadda aka tattara ciyayin aka kuma ƙone a wuta, haka zai zama a ƙarshen zamani.› ‹Ɗan Mutum zai aiki mala’ikunsa, su kuwa cire daga mulkinsa kome da yake jawo zunubi da kuma duk masu aikata mugunta.› ‹Za su jefa su cikin wuta mai zafi, inda za a yi kuka da cizon haƙora.› ‹Sa’an nan masu adalci za su haskaka kamar rana a mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yă ji.”›
”‹“Har yanzu, mulkin sama yana kama da abin kamun kifin da aka jefa cikin tafki yă kamo kifi iri-iri.› ‹Da abin kamun kifi ya cika, masuntan suka jawo shi gaci. Sai suka zauna suka tattara kifi masu kyau a kwanduna, amma suka zubar da marasa kyau.› ‹Haka zai kasance a ƙarshen zamani. Mala’iku za su zo su ware masu mugunta daga masu adalci› ‹su kuma jefa su cikin wuta mai zafi, inda za a yi kuka da cizon haƙora.”›
”Ya amsa ya ce,‹“Sa’ad da yamma ta yi, kukan ce, ‘Yanayi zai yi kyau, gama sararin sama ya yi ja,’› ‹da safe kuma, ku ce, ‘Yau kam za a yi hadari, gama sararin sama ya yi ja, ya kuma ɓata fuska.’ Kun san yadda za ku fassara yanayin sararin sama, amma ba kwa iya fassarar alamun lokuta.›
”‹Gama Ɗan Mutum zai zo cikin ɗaukakar Ubansa, tare da mala’ikunsa, sa’an nan zai ba wa kowane mutum lada gwargwadon abin da ya yi.› ‹“Gaskiya nake gaya muku, akwai waɗansu da suke tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba sai sun ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin mulkinsa.”›
”Yesu ya ce musu, ‹“Gaskiya nake gaya muku, a lokacin sabunta dukan kome, sa’ad da Ɗan Mutum ya zauna a kan kursiyinsa mai daraja, ku da kuka bi ni, ku ma za ku zauna a kan kursiyoyi goma sha biyu, kuna yi wa kabilu goma sha biyu na Isra’ila shari’a.›
”Da Yesu yana zaune a Dutsen Zaitun, almajiran suka zo wurinsa a ɓoye. Suka ce, “Gaya mana, yaushe ne wannan zai faru, mece ce alamar zuwanka da kuma ta ƙarshen zamani?” Yesu ya amsa, ‹“Ku lura fa, kada wani yă ruɗe ku.› ‹Gama mutane da yawa za su zo cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne Kiristi,’ za su kuwa ruɗi mutane da yawa.› ‹Za ku ji labarin yaƙe-yaƙe da kuma jita-jitarsu, sai dai ku lura kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru, amma ƙarshen tukuna.› ‹Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki yă tasar wa mulki. Za a yi yunwa da girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam.› ‹Dukan waɗannan fa, mafarin azabar naƙudar haihuwa ne.›
”‹“Sa’an nan za a bashe ku don a tsananta muku a kuma kashe ku, dukan al’ummai za su ƙi ku saboda ni.› ‹A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna,› ‹annabawan ƙarya da yawa za su firfito su kuma ruɗi mutane da yawa.› ‹Saboda ƙaruwar mugunta, ƙaunar yawanci za tă yi sanyi,› ‹amma duk wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.› ‹Za a kuma yi wa’azin wannan bisharar mulki a cikin dukan duniya, yă zama shaida ga dukan al’ummai, sa’an nan ƙarshen yă zo.›
”‹“Saboda haka sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama mai kawo hallaka,’›‹wanda annabi Daniyel ya yi magana a kai, yana tsaye a tsattsarkan wuri (mai karatu yă gane),› ‹to, sai waɗanda suke cikin Yahudiya, su gudu zuwa cikin duwatsu.› ‹Kada wani da yake a kan rufin gidansa, yă sauko don ɗaukar wani abu a gida.› ‹Kada wani da yake gona kuma yă komo don ɗaukar rigarsa.› ‹Kaiton mata masu ciki da mata masu renon ’ya’ya a waɗancan kwanakin!› ‹Ku yi addu’a, kada gudunku yă zama a lokacin sanyi ko a ranar Asabbaci.› ‹Gama a lokacin za a yi wata matsananciyar wahala, wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu ba kuwa za a ƙara yi ba.› ‹“Da ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da babu wani da zai tsira, amma saboda zaɓaɓɓun nan, za a taƙaita kwanakin.›
”‹A lokacin in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko, ‘Ga shi can!’ Kada ku gaskata.› ‹Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu.› ‹Ga shi, na faɗa muku tun da wuri.› ‹“Saboda haka in wani ya ce muku, ‘Ga shi can a hamada,’ kada ku fita; ko, ‘Ga shi nan a ɗakunan ciki,’ kada ku gaskata.› ‹Gama kamar yadda walƙiya take wulgawa walai daga gabas zuwa yamma, haka dawowar Ɗan Mutum zai kasance.› ‹Duk inda mushe yake, can ungulai za su taru.›
”‹“Nan da nan bayan tsabar wahalan nan› ‹“ ‘sai a duhunta rana,› ‹wata kuma ba zai ba da haskensa ba;› ‹taurari kuma za su fāffāɗi daga sararin sama,› ‹za a kuma girgiza abubuwan sararin sama.’› ‹“A sa’an nan ne alamar dawowar Ɗan Mutum zai bayyana a sararin sama, dukan al’umman duniya kuwa za su yi kuka. Za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gizagizan sararin sama, da iko da kuma ɗaukaka mai girma.› ‹Zai kuwa aiki mala’ikunsa su busa ƙaho mai ƙara sosai, za su kuwa tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga wannan bangon duniya zuwa wancan.›
”‹“Yanzu fa, sai ku koyi wannan darasi daga itacen ɓaure. Da zarar rassansa suka yi taushi ganyayensa kuma suka toho, kun san damina ta kusa.› ‹Haka kuma, sa’ad da kun ga dukan waɗannan abubuwa, ku sani ya yi kusan zuwa, yana ma dab da bakin ƙofa.› ‹Gaskiya nake gaya muku, wannan zamani ba zai shuɗe ba sai dukan abubuwan nan sun faru.› ‹Sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za tă taɓa shuɗe ba.› ‹“Babu wanda ya san wannan rana ko sa’a, ko mala’ikun da suke sama ma, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai.› ‹Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum.› ‹Gama a kwanaki kafin ruwan tsufana, mutane sun yi ta ci, sun kuma yi ta sha, suna aure, suna kuma aurarwa, har zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi;› ‹ba su kuwa san abin da yake faruwa ba sai da ruwan tsufana ya zo ya share su tas. Haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum.›
”‹Maza biyu za su kasance a gona; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya.› ‹Mata biyu za su kasance suna niƙa; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya.› ‹“Saboda haka sai ku zauna a faɗake, gama ba ku san a wace rana ce Ubangijinku zai zo ba.› ‹Ku dai gane wannan, da maigida ya san ko a wane lokaci ne da dare, ɓarawo zai zo, da sai yă zauna a faɗake yă kuma hana a shiga masa gida.› ‹Saboda haka ku ma, sai ku zauna a faɗake, domin Ɗan Mutum zai zo a sa’ar da ba ku za tă ba.›
”‹“Wane ne bawan nan mai aminci da kuma mai hikima, wanda maigida ya sa yă lura da bayi a cikin gidansa, yă riƙa ba su abinci a daidai lokaci?› ‹Zai zama wa bawan nan da kyau in maigidan ya dawo ya same shi yana yin haka.› ‹Gaskiya nake gaya muku, zai sa shi yă lura da dukan dukiyarsa.› ‹Amma in wannan bawa mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Maigidana ba zai dawo da wuri ba.’› ‹Sa’an nan yă fara dūkan ’yan’uwansa bayi, yana ci yana kuma sha tare da mashaya.› ‹Maigidan wannan bawa zai dawo a ranar da bai yi tsammani ba, a sa’ar kuma da bai sani ba.› ‹Maigidan zai farfasa masa jiki da bulala, yă kuma ba shi wuri tare da munafukai, inda za a yi kuka da cizon haƙora.›
”‹“A lokacin mulkin sama zai zama kamar budurwai goma waɗanda suka ɗauki fitilunsu suka fita don su taryi ango.› ‹Biyar daga cikinsu wawaye ne, biyar kuma masu hikima.› ‹Wawayen sun ɗauki fitilunsu, sai dai ba su riƙe mai ba.› ‹Masu hikimar kuwa suka riƙo tulunan mai da fitilunsu.› ‹Ango ya yi jinkirin zuwa, sai duk suka shiga gyangyaɗi har barci ya kwashe su.› ‹“Can tsakar dare, sai aka ji kira, ana cewa, ‘Ga ango nan! Ku fito, ku tarye shi!’› ‹“Sai dukan budurwan nan suka farka suka kuna fitilunsu.› ‹Sai wawayen suka ce wa masu hikimar, ‘Ku ɗan sassam mana manku; fitilunmu suna mutuwa.’› ‹“Su kuwa suka amsa, suka ce, ‘A’a, wataƙila ba zai ishe mu da ku ba. Gara ku je wurin masu sayarwa ku sayo.’› ‹“Amma yayinda suke kan tafiya garin sayen mai, sai ango ya iso. Budurwai da suke a shirye, suka shiga wajen bikin auren tare da shi. Aka kuma kulle ƙofa.› ‹“An jima can, sai ga sauran sun iso. Suka ce, ‘Ranka yă daɗe! Ranka yă daɗe! Ka buɗe mana ƙofa!’› ‹“Amma ya amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, ban san ku ba.’› ‹“Saboda haka sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ko sa’ar ba.›
”‹“Sa’ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa, tare da dukan mala’iku, zai zauna a kursiyinsa cikin ɗaukakar sama.› ‹Za a tara dukan al’ummai a gabansa, zai kuma raba mutane dabam-dabam yadda makiyayi yakan ware tumaki daga awaki.› ‹Zai sa tumaki a damansa, awaki kuma a hagunsa.›
”‹“Sa’an nan Sarki zai ce wa waɗanda suke damansa, ‘Ku zo, ku da Ubana ya yi wa albarka; ku karɓi gādonku, mulkin da aka shirya muku tun halittar duniya.› ‹Gama da nake jin yunwa, kun ciyar da ni, da nake jin ƙishirwa, kun ba ni abin sha, da nake baƙunci, kun karɓe ni,› ‹da nake bukatar tufafi, kun yi mini sutura, da na yi rashin lafiya, kun lura da ni, da nake kurkuku, kun ziyarce ni.’› ‹“Sa’an nan masu adalci za su amsa masa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka da yunwa muka ciyar da kai, ko da ƙishirwa muka ba ka abin sha?› ‹Yaushe kuma muka gan ka baƙo muka karɓe ka, ko cikin bukatar tufafi muka yi maka sutura?› ‹Yaushe kuma muka gan ka cikin rashin lafiya ko a kurkuku muka ziyarce ka?’› ‹“Sarkin zai amsa ya ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan’uwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.’›
”‹“Sa’an nan zai ce wa waɗanda suke a hagunsa, ‘Ku rabu da ni, la’anannu, zuwa cikin madawwamiyar wutar da aka shirya don Iblis da mala’ikunsa.› ‹Gama da nake jin yunwa, ba ku ba ni abinci ba, da nake jin ƙishirwa, ba ku ba ni abin sha ba,› ‹da na yi baƙunci, ba ku karɓe ni ba, da nake bukatar tufafi, ba ku yi mini sutura ba, da na yi rashin lafiya kuma ina a kurkuku, ba ku lura da ni ba.’› ‹“Su ma za su amsa, su ce, ‘Ubangiji, yaushe muka gan ka cikin yunwa ko ƙishirwa ko baƙo ko cikin bukatar tufafi ko cikin rashin lafiya ko cikin kurkuku, ba mu taimake ka ba?’› ‹“Zai amsa, yă ce, ‘Gaskiya nake gaya muku, duk abin da ba ku yi wa ɗaya daga cikin waɗannan mafi ƙanƙanta ba, ba ku yi mini ba ke nan.’› ‹“Sa’an nan za su tafi cikin madawwamiyar hukunci, amma masu adalci kuwa za su shiga rai madawwami.”›
”Sai Yesu ya amsa ya ce, ‹“I, haka yake yadda ka faɗa. Sai dai ina gaya muku duka, nan gaba, za ku ga Ɗan Mutum zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gizagizan sama.”›
”‹Duk wanda ya ji kunyata, da na kalmomina a wannan zamani na fasikanci da zunubi, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa lokacin da ya shiga cikin ɗaukakar Ubansa, tare da tsarkakan mala’iku.”›
”Ya kuma ce musu, ‹“Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsattsaye a nan ba za su mutu ba, sai sun ga mulkin Allah ya bayyana da iko.”›
”“Ka gaya mana, yaushe waɗannan abubuwa za su faru? Wace alama ce kuma za tă nuna cewa, duk waɗannan suna dab da cikawa?” Sai Yesu ya ce musu, ‹“Ku lura fa kada wani yă ruɗe ku.› ‹Da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne shi.’ Za su kuwa ruɗi mutane da yawa.› ‹Sa’ad da kuka ji labarun yaƙe-yaƙe da jita-jitar yaƙe-yaƙe, kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru. Amma ƙarshen tukuna.› ‹Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki kuma yă tasar wa mulki. Za a yi girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam, a kuma yi yunwa. Waɗannan dai mafarin azabar naƙuda.›
”‹“Dole ku yi zaman tsaro. Za a ba da ku ga hukuma, a kuma bulale ku a majami’u. Saboda ni kuma, za ku tsaya a gaban gwamnoni da sarakuna, domin ku ba da shaida a gabansu.› ‹Dole sai an fara yin wa’azin bishara ga dukan al’ummai.› ‹Sa’ad da aka kama ku, aka kuma kai ku don a yi muku shari’a, kada ku damu da abin da za ku faɗa. Sai dai ku faɗi abin da aka ba ku a lokacin. Gama ba ku kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne.› ‹“Ɗan’uwa zai ba da ɗan’uwa a kashe. Mahaifi zai ba da ɗansa. ’Ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su.› ‹Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.›
”‹“Sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama, mai kawo hallaka’›‹tsaye inda›‹bai kamata ba (mai karatu ya gane), to, sai waɗanda suke a Yahudiya su gudu zuwa duwatsu.› ‹Kada wani da yake kan rufin gidansa yă sauka, ko yă shiga gida don yă ɗauki wani abu.› ‹Kada wani da yake gona kuma yă koma don ɗaukar rigarsa.› ‹Kaiton mata masu ciki, da mata masu renon ’ya’ya a waɗancan kwanakin!› ‹Ku yi addu’a, kada wannan yă faru a lokacin sanyi.› ‹Domin waɗancan kwanakin za su zama kwanaki na baƙin ciki, waɗanda ba a taɓa yin irinsa ba tun farkon halitta, har yă zuwa yanzu, ba kuwa za a sāke yin irinsa ba.› ‹“Da ba don Ubangiji ya rage kwanakin nan ba, da ba wani da zai tsira. Amma saboda zaɓaɓɓu waɗanda ya zaɓa, sai ya rage kwanakin.›
”‹A lokacin nan, in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko kuwa, ‘Duba, ga shi can!’ Kada ku gaskata.› ‹Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu.› ‹Amma ku kula! Na dai gaya muku kome tun da wuri.›
”‹“Amma waɗancan kwanaki, bayan baƙin azaban nan,› ‹“ ‘rana za tă yi duhu,› ‹wata kuma ba zai ba da haskensa ba;› ‹taurari za su fāffāɗo daga sararin sama.› ‹Za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama.’› ‹“Sa’an nan, mutane za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin gizagizai da iko, da ɗaukaka mai girma.› ‹Zai kuma aiko mala’ikunsa su tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga iyakar duniya har yă zuwa iyakar sama.›
”‹“To, sai ku yi koyi da itacen ɓaure. Da zarar rassansa suka yi taushi, ganyayensa kuma suka toho, kun san cewa damina ta yi kusa ke nan.› ‹Haka ma, in kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku san cewa ya yi kusan zuwa, yana ma dab da bakin ƙofa.› ‹Gaskiya nake gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun faru.› ‹Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.› ‹“Game da wannan rana ko sa’a kuwa, ba wanda ya sani, ko mala’ikun da suke sama, ko Ɗan, sai Uban kaɗai.› ‹Ku lura fa! Ku zauna a shirye! Don ba ku san lokacin da shi zai zo ba.› ‹Yana kama da mutumin da zai yi tafiya. Yakan bar gidansa a hannun bayinsa, kowa da nasa aikin da aka sa shi, yă kuma ce wa wanda yake gadin ƙofa, yă yi tsaro.› ‹“Saboda haka, sai ku zauna a shirye, domin ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko lokacin da zakara na cara ne, ko kuma da safe ne.› ‹In ya zo kwaram, kada ka bari yă tarar da kai kana barci.› ‹Abin da na faɗa muku, na faɗa wa kowa. ‘Ku yi tsaro!’ ”›
”Yesu ya ce, ‹“Ni ne. Za ku kuwa ga Ɗan Mutum yana zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a cikin gizagizan sama.”›
”‹Duk wanda yake jin kunyana da na kalmomina, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa sa’ad da zai zo a cikin ɗaukakarsa, da ɗaukakar Uban, da kuma ta tsarkaka mala’ikun.› ‹“Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsattsaye a nan ba za su ga mutuwa ba, sai sun ga mulkin Allah.”›
”‹“Ku shirya ɗamara don hidima. Ku bar fitilunku suna ci,› ‹kamar maza da suke jiran maigidansu ya dawo daga bikin aure. Saboda duk lokacin da ya dawo ya ƙwanƙwasa ƙofa, a shirye suke su buɗe masa nan da nan.› ‹Zai zama da albarka in maigida ya dawo, ya tarar da bayinsa suna zaman tsaro. Gaskiya ni faɗa muku, zai sa kayan hidima da kansa, ya sa bayinsa su zauna kan tebur, sa’an nan ya yi musu hidimar abinci.› ‹Zai zama da albarka ga bayin da maigidansu ya iske su, suna zaman tsaro, a duk lokacin da ya dawo, ko da ya dawo a sa’a ta biyu, ko ta uku na tsakar dare ne.› ‹Amma ku fahimci wannan. Da maigida ya san sa’ar da ɓarawo zai zo, ai, da ba zai bari a shiga, a fasa masa gida ba.› ‹Ku ma, sai ku zauna da shiri, domin Ɗan Mutum zai zo a sa’ar da ba ku yi tsammani ba.”›
”‹Zai zama da albarka ga bawan nan wanda maigidan ya dawo, ya same shi yana yin haka.› ‹Gaskiya nake gaya muku, maigidan zai ba shi riƙon dukan dukiyarsa.› ‹Amma da a ce bawan ya yi tunani a zuciyarsa ya ce, ‘Ai, maigidana ya yi jinkirin dawowa,’ sa’an nan ya fara dūkan bayin, maza da mata, ya kuma shiga ci, da sha, har da buguwa.› ‹Maigidan bawan nan zai dawo a ranar da wannan bawan bai yi tsammaninsa ba, kuma a sa’ar da bai sani ba. Maigidan zai yayyanka shi, ya kuma ba shi rabonsa tare da marasa bangaskiya.› ‹“Bawan da ya san nufin maigidansa, kuma bai yi shiri ba, ko kuma bai yi abin da maigidansa yake so ba, zai sha mummunan duka.›
”Ya ce wa taron, ‹“Sa’ad da kuka ga hadari ya fito daga yamma, nan da nan kukan ce, ‘Za a yi ruwan sama,’ sai a kuwa yi.› ‹Sa’ad da kuma iska ta taso daga kudu, kukan ce, ‘Za a yi zafi,’ sai kuwa a yi.› ‹Munafukai! Kuna san yadda za ku fassara yanayin ƙasa da na sararin sama. Ta yaya ba ku san yadda za ku yi fassarar wannan zamani ba?›
”Sai ya ce wa almajiransa, ‹“Lokaci yana zuwa da za ku yi marmarin ganin rana ɗaya cikin ranakun Ɗan Mutum, amma ba za ku gani ba.› ‹Mutane za su ce muku, ‘Ga shi can!’ Ko kuma, ‘Ga shi nan!’ Kada ku yi hanzarin binsu.› ‹Gama Ɗan Mutum, a cikin ranarsa, zai zama kamar walƙiya da take walƙawa, da take kuma haskaka sararin sama, daga wannan kusurwa zuwa wancan kusurwa.›
”‹Amma da fari, dole yă sha wahaloli masu yawa, kuma mutanen zamanin nan su ƙi shi.› ‹“Daidai kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a zamanin Ɗan Mutum.› ‹Mutane suna ci, suna sha, suna aurayya, ana kuma ba da su ga aure, har ranar da Nuhu ya shiga jirgin. Sa’an nan ambaliyar ruwan ya sauka, ya hallaka su duka.› ‹“Haka ma aka yi a zamanin Lot. Mutane suna ci, suna sha, suna saya, suna sayarwa, suna shuki, suna kuma gine-gine.› ‹Amma a ranar da Lot ya bar Sodom, sai aka yi ruwan wuta da farar wuta daga sama, aka hallaka su duka.› ‹“Daidai haka zai zama, a ranar da Ɗan Mutum zai bayyana.›
”‹A ranan nan, kada wanda yake kan rufin gidansa ya sauka don yă kwashe dukiyarsa da take cikin gidan. Haka ma duk wanda yake gona, kada yă koma don wani abu.› ‹Ku tuna fa da matar Lot!› ‹Duk wanda yake so ya ceci ransa, zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa, zai cece shi.›
”‹Ina gaya muku, a daren nan, mutane biyu za su kasance a gado ɗaya, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗayan.› ‹Mata biyu za su kasance suna niƙan hatsi tare, za a ɗauki ɗaya, a bar ɗayan.”› Suka tambaya, suka ce, “A ina ne, ya Ubangiji?” Ya ce musu, ‹“Ai, inda gawa take, nan ne ungulai za su taru.”›
”‹Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke masa kuka, dare da rana adalci ba? Zai ci gaba da ƙin sauraronsu ne?› ‹Ina gaya muku, zai tabbatar sun sami adalci, ban da ɓatan lokaci. Amma sa’ad da Ɗan Mutum ya dawo, zai sami bangaskiya a duniya ke nan?”›
”Sai ya ce musu, ‹“Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki zai tasar wa mulki.› ‹Za a yi manyan girgizar ƙasa, da yunwa, da annoba a wurare dabam-dabam, da kuma abubuwa masu bantsoro, da manyan alamu daga sama.›
”‹“Amma kafin duk abubuwa nan, za a kama ku a tsananta muku. Za a kai ku majami’u, da kurkuku. Za a kuma kai ku gaban sarakuna da gwamnoni, kuma dukan waɗannan saboda sunana.› ‹Wannan zai sa ku zama shaidu a gare su.› ‹Amma ku yi ƙuduri, wato, ku shirya zuciyarku, a kan ba za ku damu ba kafin lokacin, game da yadda za ku kāre kanku.› ‹Gama zan ba ku kalmomi, da hikima waɗanda ba ko ɗaya daga cikin maƙiyanku, za su iya tsayayya da ku, ko su ƙaryata.› ‹Har iyayenku, da ’yan’uwanku maza, da danginku, da abokanku ma, duk za su bashe ku, su kuma kashe waɗansunku.› ‹Duk mutane za su ƙi ku saboda ni.› ‹Amma ko gashi ɗaya na kanku, ba zai hallaka ba.› ‹Ta wurin tsayawa da ƙarfi, za ku sami rai.›
”‹“In kuka ga mayaƙa sun kewaye Urushalima, za ku sani rushewarta ya yi kusa.› ‹A lokacin nan, bari waɗanda suke Yahudiya, su gudu zuwa cikin duwatsu. Bari waɗanda suke cikin birnin kuma su fita, bari kuma waɗanda suke ƙauye kada su shiga birnin.› ‹Gama wannan shi ne lokacin hukunci, saboda a cika duk abin da aka rubuta.› ‹Zai zama abin kaito ga mata masu ciki, da mata masu renon ’ya’ya, a waɗancan kwanakin! Za a yi baƙin ciki mai tsanani a ƙasar, da kuma fushi mai tsanani a kan mutanen nan.› ‹Za a kashe su da takobi, a kuma ɗauke su ’yan kurkuku, zuwa dukan al’ummai. Al’ummai za su tattaka Urushalima, har sai lokacin Al’ummai ya cika.›
”‹“Za a yi alamu a cikin rana, da cikin wata, da cikin taurari. A duniya, al’ummai za su yi baƙin ciki, su kuma rikice don tsoro, saboda ruri da kuma tafasar teku.› ‹Mutane za su suma don tsoro, za su kuma yi fargaba, a kan abin da yake zuwa a bisan duniya, gama za a girgiza duniyar taurarin sararin sama.› ‹A lokacin ne za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin girgije, da iko, da ɗaukaka mai girma.› ‹Sa’ad da waɗannan abubuwa sun fara faruwa, ku tashi tsaye, ku ɗaga kawunanku, domin fansarku yana matsowa kusa.”›
”Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, ‹“Ku dubi itacen ɓaure da dukan itatuwa.› ‹A duk lokacin da sun fara fitar da ganye, za ku gani da kanku, ku san cewa, damina ta yi kusa.› ‹Haka ma, in kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku sani mulkin Allah ya yi kusa.› ‹“Gaskiya nake gaya muku, ba shakka, wannan zamani ba zai shuɗe ba, sai dukan waɗannan abubuwa sun cika.› ‹Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.› ‹“Ku lura fa don kada son jin daɗi na banza, da shaye-shaye, da damuwa na rayuwa su rinjayi zuciyarku, har ranar ta auko muku ba tsammani kamar tarko.› ‹Gama za tă zo a kan kowa da yake kan dukan duniya.› ‹Ku yi tsaro kullum, ku yi addu’a don ku iya kuɓuta daga dukan waɗannan abubuwa da suke kusan faruwa, don ku iya tsayawa a gaban Ɗan Mutum.”›
”‹Gaskiya nake gaya muku, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya zo sa’ad da matattu za su ji muryar Ɗan Allah waɗanda kuwa suka ji za su rayu.› ‹Gama kamar yadda Uban yana da rai a cikinsa, haka ya sa Ɗan yă kasance da rai a cikin kansa.› ‹Ya kuma ba shi iko yă hukunta domin shi Ɗan Mutum ne.› ‹“Kada ku yi mamakin wannan, gama lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke cikin kaburbura za su ji muryarsa› ‹su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta za su tashi zuwa ga rai, waɗanda kuma suka aikata mugunta za su tashi zuwa ga hukunci.›
”‹A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa; da a ce ba haka ba ne, da na gaya muku. Za ni can don in shirya muku wuri.› ‹In kuwa na tafi na shirya muku wuri, sai in dawo in ɗauke ku ku kasance tare da ni don ku kasance inda nake.›
”Bayan ya faɗi wannan, sai aka ɗauke shi sama a idanunsu sai wani girgije ya rufe shi daga ganinsu. Suna zuba ido a bisa, zuwa cikin sararin sama yayinda yake tafiya, nan da nan, sai ga mutane biyu saye da fararen riguna tsaye kusa da su. Sai suka ce, “Mutanen Galili, don me kuke tsaye a nan kuna duban sararin sama? Wannan Yesu, wanda aka ɗauke daga gare ku zuwa sama, zai komo daidai yadda kuka ga ya tafi sama.”
”A ganina, wuyar da muke sha a wannan lokaci ba su isa a kwatanta da ɗaukakar da za a bayyana a cikinmu ba. Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar ’ya’yan Allah.
”A rubuce yake cewa, “ ‘Muddin ina raye,’ in ji Ubangiji, ‘kowace gwiwa za tă durƙusa a gabana; kowane harshe kuma zai furta wa Allah.’ ”
”Allah na salama zai tattake Shaiɗan ba da daɗewa ba yă kuma sa shi a ƙarƙashin sawunku. Alherin Ubangijinmu Yesu kuma yă kasance tare da ku.
”In wani ya yi gini a kan tushen ginin nan da zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja, itace, ciyawa ko kara, aikin zai bayyana kansa, domin za a nuna shi a sarari a Ranar. Wuta ce za tă bayyana aikin, wutar kuwa za tă gwada ingancin aikin kowa. In abin da kowane mutum ya gina ya tsaya, zai sami lada. In ya ƙone, zai yi hasara, amma zai sami ceto, sai dai kamar wanda ya bi ta tsakiyar wuta ne.
”Saboda haka, kada ku shari’anta kome tun lokaci bai yi ba. Ku jira sai Ubangiji ya zo. Zai bayyana abin da yake a ɓoye a cikin duhu a sarari, zai kuma tone nufin zukatan mutane. A lokacin ne fa kowa zai karɓi yabo daga wurin Allah daidai gwargwado.
”Ku miƙa irin wannan mutum ga Shaiɗan, don a hallaka halin nan na mutuntaka, ruhunsa kuma yă sami ceto a ranar da Ubangiji zai dawo. Ku daina taƙama. Ba ku san cewa ɗan ƙanƙanin yisti ne yakan sa dukan curin burodi yă kumbura ba?
”Ina sanar da ku, ’yan’uwa, cewa nama da jini ba za su gāji mulkin Allah ba, haka ma ruɓa ba zai gāji rashin ruɓa ba. Ku saurara, in gaya muku wani asiri. Ba dukanmu ne za mu yi barci ba, sai dai duk za a sauya kamanninmu farat ɗaya, cikin ƙyaftawar ido, da busan ƙaho na ƙarshe. Gama za a busa ƙaho, za a tā da matattu da jiki irin da ba ya ruɓewa, za a kuma sauya kamanninmu.
”don a sunan Yesu kowace gwiwa za tă durƙusa, a sama da a ƙasa da kuma a ƙarƙashin ƙasa, kowane harshe kuma yă furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne, don ɗaukakar Allah Uba.
”Sa’ad da Kiristi, wanda shi ne ranku, ya bayyana, ku ma za ku bayyana tare da shi cikin ɗaukaka.
”ku kuma jira dawowar Ɗansa daga sama, wanda ya tasa daga matattu, Yesu, wanda ya cece mu daga fushi mai zuwa.
”’Yan’uwa, ba ma so ku kasance cikin jahilci game da waɗanda suka yi barci, ko kuwa ku yi baƙin ciki kamar sauran mutanen da ba su da bege. Mun gaskata cewa Yesu ya mutu ya tashi kuma daga matattu, ta haka muka gaskata cewa Allah zai kawo waɗanda suka yi barci a cikinsa tare da Yesu. Bisa ga maganar Ubangiji kansa, muna gaya muku cewa mu da muke raye har yanzu, waɗanda aka bari har dawowar Ubangiji, tabbatacce ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba.
”Gama Ubangiji kansa zai sauko daga sama, da umarni mai ƙarfi, da muryar babban mala’ika da kuma busar ƙahon Allah, waɗanda suka mutu kuwa cikin Kiristi za su tashi da farko. Bayan haka, mu da muke da rai da aka bari, za a ɗauke mu tare da su a cikin gizagizai don mu sadu da Ubangiji a sararin sama. Ta haka za mu kasance tare da Ubangiji har abada.
”To, ’yan’uwa, game da lokuta da ranaku, ba ma bukata mu rubuta muku, gama kun sani sarai cewa ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo da dare. Yayinda mutane suke cewa, “Akwai salama da zaman lafiya,” hallaka za tă auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba. Amma ku, ’yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za tă zo muku ba zato kamar ɓarawo.
”Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi. Ya mutu saboda mu domin, ko muna a faɗake ko muna barci, mu kasance tare da shi.
”Saboda haka, a cikin ikkilisiyoyin Allah muna taƙama game da daurewarku da kuma bangaskiyarku cikin dukan tsanani da gwaje-gwajen da kuke sha. Dukan wannan yana tabbatar cewa hukuncin Allah daidai ne, saboda haka kuma za a lissafta ku a kan kun cancanci mulkin Allah, wanda dominsa ne kuke shan wahala. Allah mai adalci ne, Zai sāka wa masu ba ku wahala da wahala yă kuma sauƙaƙa muku ku da kuke wahala, har ma da mu. Wannan zai faru sa’ad da aka bayyana Ubangiji Yesu daga sama cikin wuta mai ci tare da mala’ikunsa masu iko. Zai hukunta waɗanda ba su san Allah ba da kuma waɗanda ba su yi biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu ba. Za a hukunta su da madawwamiyar hallaka a kuma kau da su daga gaban Ubangiji da kuma daga ɗaukakar ikonsa a ranar da zai dawo don a ɗaukaka shi a cikin mutanensa masu tsarki, yă kuma zama abin banmamaki ga dukan waɗanda suka gaskata. Wannan ya haɗa har da ku, domin kun gaskata shaidar da muka yi muku.
”Game da dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi da game da tattara mu gare shi, muna roƙonku, ’yan’uwa, kada ku yi saurin jijjiguwa ko kuwa hankalinku yă tashi ta wurin wani annabci, rahoto ko wasiƙar da an ce daga wurinmu ne, cewa ranar Ubangiji ta riga ta zo. Kada ku bar wani yă ruɗe ku ko ta yaya, gama wannan rana ba za tă zo ba sai an yi tawayen nan an kuma bayyana mutumin tawayen nan, mutumin da aka ƙaddara ga hallaka. Zai yi gāba yă kuma ɗaukaka kansa a bisa kome da ya shafe sunan Allah, ko kuma ake yi wa sujada, domin yă kafa kansa a haikalin Allah, yana shelar kansa a kan shi Allah ne.
”Ba ku tuna ba cewa sa’ad da nake tare da ku nakan gaya muku waɗannan abubuwa? Yanzu kuwa kun san abin da yake hana shi, wannan yana faruwa ne don a bayyana shi a daidai lokaci. Gama ikon asirin tawaye ya riga ya fara aiki; sai dai wannan da yake hana shi zai ci gaba da yin haka sai an kau da shi. Sa’an nan za a bayyana mai tawayen, Ubangiji Yesu kuwa zai hamɓare shi da numfashin bakinsa yă kuma hallaka shi da darajar dawowarsa. Zuwan mai tawayen nan zai zama ta wurin aikin Shaiɗan da aka bayyana cikin kowane irin ayyukan banmamaki, alamu da abubuwan banmamaki na ƙarya, da kuma cikin kowace irin muguntar da take ruɗin waɗanda suke hallaka. Sun hallaka ne domin sun ƙi su ƙaunaci gaskiya don su sami ceto. Saboda haka Allah zai aiko musu da babban ruɗu don su gaskata ƙarya don kuma a hukunta dukan waɗanda ba su gaskata gaskiyar ba sai dai suke jin daɗin mugunta.
”ka kiyaye wannan umarni ba tare da wani aibi ko abin zargi ba har yă bayyanuwar Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda Allah zai kawo a daidai lokaci, Allah, mai albarka wanda yake kaɗai Mai Mulki, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji, wanda shi kaɗai ne marar mutuwa wanda kuma yake zaune cikin hasken da ba ya kusatuwa, wanda babu wanda ya taɓa gani ko zai iya gani. A gare shi girma da iko su tabbata har abada. Amin.
”Amma fa ka san wannan, za a yi lokutan shan wahala a kwanakin ƙarshe. Mutane za su zama masu son kansu, masu son kuɗi, masu taƙama, masu girman kai, masu zage-zage, marasa biyayya ga iyayensu, marasa godiya, marasa tsarki, marasa ƙauna, marasa gafartawa, masu ɓata sunayen waɗansu, marasa kamunkai, masu ƙeta, marasa ƙaunar nagarta, masu cin amana, marasa hankali, waɗanda sun cika da ɗaga kai, masu son jin daɗi a maimakon ƙaunar Allah suna riƙe da siffofin ibada, amma suna mūsun ikonta. Kada wani abu yă haɗa ka da su.
”A gaban Allah da kuma Kiristi Yesu, wanda zai yi wa masu rai da matattu shari’a, saboda kuma bayyanuwarsa da mulkinsa, ina ba ka umarni. Ka yi wa’azin Maganar Allah, ka zama a shirye a kullum, ko da zarafi, ko babu zarafi, ka yi gyara, ka kwaɓe, ka kuma ƙarfafa, da matuƙar haƙuri da koyarwa cikin natsuwa. Gama lokaci yana zuwa da mutane ba za su jure da sahihiyar koyarwa ba. A maimako, don cimma burinsu, za su taro wa kansu malamai masu yawa, domin su faɗi abin da kunnuwansu masu ƙaiƙayi suke so su ji. Za su juye kunnuwansu daga gaskiya zuwa ga jin tatsuniyoyi. Amma kai, ka natsu cikin kowane hali, ka jure shan wahala, ka yi aikin mai bishara, ka cika dukan ayyukan hidimarka.
”Yanzu kuwa an ajiye mini rawanin adalci, wanda Ubangiji, Alƙali mai adalci zai ba ni a ranan nan ba kuwa ni kaɗai ba, amma ga duk waɗanda suka yi marmarin bayyanuwarsa.
”yayinda muke sauraron begenmu mai albarka bayyanuwar ɗaukakar Allahnmu mai girma da kuma Mai Cetonmu, Yesu Kiristi,
”Ya kuma ce, “Tun da farko, ya Ubangiji, ka kafa tushen duniya, sammai kuma aikin hannuwanka ne. Su za su hallaka, amma kai kana nan; dukansu za su tsufa kamar riga. Za ka naɗe su kamar mayafi, kamar riga za su sauya. Amma kai ba za ka canja ba, shekarunka kuma ba za su taɓa ƙarewa ba.”
”Waɗannan abubuwa hotuna ne kawai na abin da yake a sama, dole kuma a tsarkake su ta wurin waɗannan ƙa’idodi. Amma dole a tsarkake ainihin abubuwa na sama da wani abu mafi kyau. Gama Kiristi bai shiga wani wuri tsattsarka da mutum ya yi ba, wanda yake hoto ne kawai na gaskataccen, a’a sama kanta ya shiga, domin yă bayyana a gaban zatin Allah a yanzu saboda mu. Bai kuwa shiga sama domin yă yi ta miƙa kansa a kai a kai, yadda babban firist yake shiga Wuri Mafi Tsarki kowace shekara da jinin da ba nasa ba. Da a ce haka ne, ai, da Kiristi ya sha wahala sau da yawa tun halittar duniya. Amma yanzu ya bayyana sau ɗaya tak a ƙarshen zamanai domin yă kawar da zunubi ta wurin miƙa kansa hadaya. Kamar dai yadda aka ƙaddara wa mutum yă mutu sau ɗaya, bayan haka kuma sai shari’a, haka aka miƙa Kiristi hadaya sau ɗaya domin yă ɗauke zunuban mutane masu yawa; zai kuma bayyana sau na biyu, ba don yă ɗauki zunubi ba, sai dai don yă kawo ceto ga waɗanda suke jiransa.
”Kada mu daina taruwa kamar yadda waɗansu suka saba, sai dai mu ƙarfafa juna, tun ba ma da kuka ga Ranan nan tana kusatowa ba.
”Mata suka karɓi ƙaunatattunsu da aka sāke tasar daga matattu. Aka azabtar da yawancin mutanen nan, amma suka ƙi a sake su, domin sun tabbata za su sami lada mafi kyau sa’ad da aka tā da matattu.
”Yanzu fa sai ku saurara, ku masu arziki, ku yi kuka da ihu, saboda azabar da take zuwa a kanku. Arzikinku ya ruɓa, asu kuma sun cinye tufafinku. Zinariyarku da azurfarku sun yi tsatsa. Tsatsarsu kuwa za tă zama shaida a kanku, ta kuma ci namar jikinku kamar wuta. Kun ɓoye dukiya a kwanakin ƙarshe.
”Saboda haka ’yan’uwa, sai ku yi haƙuri har dawowar Ubangiji. Ku dubi yadda manomi yakan jira gona ta ba da amfaninta mai kyau, da kuma yadda yake haƙurin jiran ruwan sama na damina da na kaka. Haka ku ma, ku yi haƙuri, ku tsaya da ƙarfi, gama dawowar Ubangiji ya yi kusa.
”Da farko dai, dole ku fahimci wannan cewa a kwanakin ƙarshe masu ba’a za su zo suna ba’a, suna bin mugayen sha’awace-sha’awacensu. Za su ce, “Ina wannan ‘dawowar’ da ya yi alkawari ne? Tun mutuwar kakanninmu, kome yana tafiya kamar yadda yake tun farkon halitta.” Amma da gangan suke manta cewa tun dā can ta wurin maganar Allah sammai suka kasance aka kuma yi ƙasa daga ruwa ta wurin ruwa kuma. Ta wurin waɗannan ruwan ne aka nutsar, aka kuma hallakar da duniya ta wancan lokaci. Ta wurin wannan magana ce aka ajiye sammai da ƙasa na yanzu domin wuta, an ajiye su kuma don ranar hukunci da hallaka ta mutane marasa tsoron Allah.
”Amma kada ku manta da wannan abu guda ɗaya, abokaina ƙaunatattu. Ga Ubangiji kwana ɗaya kamar shekaru dubu ne, shekaru dubu kuma kamar kwana ɗaya ne. Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani yă hallaka, sai dai kowa yă kai ga tuba.
”Amma ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo. Sammai za su ɓace da ruri, abubuwan da suke cikinsu za su ƙone, ƙasa kuma da dukan abin da yake cikinta za su tonu. Da yake za a hallaka dukan abubuwa ta haka, waɗanne irin mutane ne ya kamata ku zama? Ya kamata ku yi rayuwar tsarki da ta tsoron Allah, yayinda kuke zuba ido ga zuwan ranar Allah kuna gaggauta zuwanta. Wannan rana za tă kawo wa sammai hallaka ta ƙunan wuta, abubuwa kuma za su narke don zafi. Amma bisa ga alkawarinsa muna zuba ido ga sabuwar sama da kuma sabuwar ƙasa, inda adalci zai yi zama.
”Duniya da sha’awace-sha’awacenta suna shuɗewa, amma mutumin da yake aikata nufin Allah, zai rayu har abada. ’Ya’yana ƙaunatattu, waɗannan su ne kwanakin ƙarshe; kuma kamar yadda kuka ji cewa magabcin Kiristi yana zuwa, ko yanzu ma abokan gāban Kiristi da yawa sun zo. Ta haka muka san cewa kwanakin ƙarshe sun iso. Waɗannan masu gāba da Kiristi suna cikinmu a dā, amma sun bar mu, don tun dā ma su ba namu ba ne. Ai, da su namu ne, da har yanzu suna tare da mu. Amma sun bar mu, wannan ya nuna a fili cewa su ba namu ba ne.
”Abokaina ƙaunatattu, ba kowane ruhu za ku gaskata ba, sai dai ku gwada ruhohi don ku ga ko daga Allah ne, domin annabawan ƙarya da yawa sun fito duniya. Ga yadda za ku gane Ruhun Allah, duk ruhun da ya yarda cewa Yesu Kiristi ya zo cikin jiki, to, daga Allah yake. Amma duk ruhun da bai yarda da Yesu ba, ba daga Allah ba ne, ruhun magabcin Kiristi ne, wanda kuka ji yana zuwa, har ma ya riga ya shigo duniya. Ku, ’ya’yana ƙaunatattu, ku daga Allah ne, kun kuma yi nasara a kan magabtan Kiristi, domin wanda yake a cikinku ya fi wanda yake a duniya girma. Su daga duniya ne saboda haka suke magana yadda duniya take ganin abubuwa, duniya kuwa tana sauraronsu. Mu daga Allah ne, kuma duk wanda ya san Allah yakan saurare mu. Amma duk wanda ba daga Allah ba, ba ya sauraronmu. Ta haka ne muke gane Ruhun gaskiya, da kuma ruhun ƙarya.
”Masu ruɗi da yawa, waɗanda ba su yarda da zuwan Yesu Kiristi cikin jiki ba, sun riga sun fito a duniya. Duk irin mutumin nan mai ruɗi ne kuma magabcin Kiristi. Ku lura don kada ku yi hasarar aikin da kuka yi, sai dai ku sami cikakken lada. Duk mutumin da bai tsaya a kan koyarwar Kiristi ba, amma ya yi ƙari a kanta, mutumin nan ba shi da Allah. Amma wanda ya tsaya a kan koyarwar Kiristi, yana da Uban da kuma Ɗan. Duk wanda ya zo wurinku bai kuma kawo koyarwan nan ba, kada ku karɓe shi a gidanku ko ku marabce shi. Duk wanda ya karɓe shi yana tarayya da mugun aikinsa ke nan.
”Enok ma, wanda yake na bakwai daga Adamu, ya yi annabci game da waɗannan mutane cewa, “Duba, Ubangiji yana zuwa da dubu dubban tsarkakansa don yă yi wa kowa shari’a, yă kuma hukunta duk marasa tsoron Allah game da dukan ayyukansu na rashin tsoron Allah da suka aikata ta hanyar rashin tsoron Allah, da kuma dukan baƙaƙen kalmomin da masu zunubi marasa tsoron Allah suka faɗa game da shi.”
”Wahayin Yesu Kiristi, wanda Allah ya ba shi yă nuna wa bayinsa abin da lalle zai faru nan ba da daɗewa ba. Ya bayyana shi ta wurin aiko da mala’ikansa zuwa ga bawansa Yohanna,
”“Duba, yana zuwa cikin gizagizai, kowane ido kuwa zai gan shi, har da waɗanda suka soke shi”; dukan mutanen duniya kuwa “za su yi makoki dominsa.” Bari yă zama haka nan! Amin.
”‹Da yake ka kiyaye umarnina ta wurin jimrewa, ni ma zan tsare ka daga lokacin nan na gwaji wanda zai zo bisan dukan duniya don a gwada waɗanda suke zama a duniya.› ‹Ina zuwa ba da daɗewa ba. Ka riƙe abin da kake da shi, don kada wani ya karɓe rawaninka.› ‹Duk wanda ya ci nasara zan mai da shi ginshiƙi a haikalin Allahna. Ba kuwa zai sāke barin wurin ba. Zan rubuta a kansa sunan Allahna da kuma sunan birnin Allahna, sabuwar Urushalima, wadda take saukowa daga sama daga Allahna; ni kuma zan rubuta a kansa sabon sunana.›
”‹Na san ayyukanka, ba ka da sanyi ba ka kuma da zafi. Na so da kai ɗaya ne daga ciki, ko sanyi, ko zafi!› ‹Amma domin kana tsaka-tsaka ba zafi ba, ba kuma sanyi ba, ina dab da tofar da kai daga bakina.› ‹Ka ce, ‘Ina da arziki; na sami dukiya ba na kuma bukatar kome.’ Amma ba ka gane ba cewa kai matsiyaci ne, abin tausayi, matalauci, makaho kana kuma tsirara.› ‹Na shawarce ka ka sayi zinariyar da aka tace cikin wuta daga gare ni, don ka yi arziki; da fararen tufafi ka sa, don ka rufe kunyar tsirancinka; da kuma maganin ido ka sa a idanunka, don ka gani.› ‹Waɗanda nake ƙauna su nake tsawata wa, nake kuma horo. Saboda haka ka yi himma ka tuba.›
”Bayan wannan sai na duba, a can kuma a gabana ga ƙofa a buɗe a sama. Sai muryar da na ji da fari da take magana da ni mai kama da busar ƙaho ta ce, ‹“Hauro nan, zan kuma nuna maka abin da lalle zai faru bayan wannan.”›
”Sa’an nan na ga a hannun damar wannan wanda yake zaune a kursiyin naɗaɗɗen littafi da rubutu a ciki da wajensa an kuma hatimce shi da hatimai bakwai. Na kuma ga wani babban mala’ika yana shela da babbar murya cewa, “Wa ya cancanta yă ɓalle hatiman nan yă kuma buɗe naɗaɗɗen littafin?” Amma ba wani a sama ko a ƙasa ko a ƙarƙashin ƙasan da ya iya buɗe naɗaɗɗen littafin ko ma yă duba cikinsa. Na yi ta kuka domin ba a iya samun wanda ya cancanta yă buɗe naɗaɗɗen littafin ko yă duba cikinsa ba. Sai ɗaya daga cikin dattawan ya ce mini, “Kada ka yi kuka! Duba, Zakin kabilar Yahuda, da kuma Tushen Dawuda ya ci nasara. Ya iya buɗe naɗaɗɗen littafin da hatimansa bakwai.” Sa’an nan na ga Ɗan Rago, yana kamar an yanka, tsaye a tsakiyar kursiyin, halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan an sun kewaye shi. Yana da ƙahoni bakwai da idanu bakwai, waɗanda suke ruhohi bakwai na Allah da aka aika cikin dukan duniya. Ya zo ya karɓi naɗaɗɗen littafin daga hannun dama na wannan wanda yake zaune a kursiyin. Bayan ya karɓa, sai halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi ƙasa a gaban Ɗan Ragon. Kowannensu yana da garaya kuma suna riƙe da kaskon zinariya cike da turare, waɗanda suke addu’o’in tsarkaka. Suka rera sabuwar waƙa, “Ka cancanci ka karɓi naɗaɗɗen littafin ka kuma buɗe hatimansa, domin an kashe ka, da jininka kuma ka sayi mutane wa Allah, daga kowace kabila da harshe da mutane da kuma al’umma. Ka mai da su masarauta da kuma firistoci, don su yi wa Allahnmu hidima, kuma za su yi mulki a duniya.”
”Sai na duba na kuma ji muryar mala’iku masu yawa, yawansu kuwa ya kai dubu dubbai, da kuma dubu goma sau dubu goma. Suka kewaye kursiyin da halittu huɗun nan masu rai da kuma dattawan nan. Da babbar murya suka rera, “Macancanci ne Ɗan Ragon nan da aka kashe, don yă sami iko da wadata da hikima da ƙarfi da girma da ɗaukaka da kuma yabo!” Sa’an nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa, “Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon yabo da girma da ɗaukaka da iko, sun tabbata har abada abadin!” Sai halittu huɗun nan masu rai suka ce, “Amin”, dattawan kuma suka fāɗi suka yi sujada.
”Na kalli yayinda Ɗan Ragon ya buɗe hatimin farko na hatimai bakwai ɗin nan. Sai na ji ɗaya daga cikin halittu huɗun nan masu rai ya yi magana da murya mai kama da tsawa ya ce, “Zo!” Na duba, can kuwa a gabana ga wani farin doki! Mai hawansa yana riƙe da baka, aka kuma ba shi rawani, ya yi sukuwa ya fito kamar mai nasara da ya kutsa don nasara.
”Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na biyun, sai na ji halitta mai rai na biyu ya ce, “Zo!” Sai wani doki ya fito, ja wur. Aka ba wa mai hawansa iko yă ɗauke salama daga duniya yă kuma sa mutane su kashe juna. Aka ba shi babban takobi.
”Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na uku, sai na ji halitta mai rai na uku ya ce, “Zo!” Na duba, can a gabana kuwa ga wani baƙin doki! Mai hawansa yana riƙe da abubuwan awo guda biyu a hannunsa. Sai na ji wani abu mai ƙara kamar wata murya a tsakiyar halittu huɗun nan masu rai tana cewa, “Kwatan alkama don albashin aikin yini, da kuma kwata uku na sha’ir don albashin yini guda, kada kuwa ka ɓata man da ruwan inabi!”
”Sa’ad da Ɗan Ragon ya buɗe hatimi na huɗu, sai na ji muryar halitta mai rai na huɗu ya ce, “Zo!” Na duba, can a gabana kuwa ga ƙodaɗɗen doki! An ba wa mai hawansa suna Mutuwa, Hades kuwa yana biye da shi. Aka ba su iko a kan kashi ɗaya bisa huɗu na duniya don su yi kisa da takobi, yunwa da annoba, har ma da namomin jeji na duniya.
”Sa’ad da ya buɗe hatimi na biyar, sai na ga a ƙarƙashin bagaden rayukan waɗanda aka kashe saboda maganar Allah da kuma shaidar da suka yi. Suka yi kira da babbar murya suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarki da kuma Mai Gaskiya, sai yaushe za ka shari’anta mazaunan duniya ka kuma ɗauki mana fansar jininmu?” Sai aka ba wa kowannensu farin riga, aka kuma faɗa musu su ɗan jira kaɗan sai an cika adadin abokansu masu hidima da kuma ’yan’uwansu waɗanda za a kashe kamar yadda su ma aka kashe su.
”Ina kallo yayinda ya buɗe hatimi na shida. Sai aka yi babban girgizar ƙasa. Rana ta zama baƙa kamar gwado na gashin akuya, wata kuma gaba ɗaya ya zama ja wur kamar jini, taurarin sararin sama suka fāffāɗi a ƙasa, kamar yadda ɗanyun ’ya’yan ɓaure suke fāɗuwa daga itacen ɓaure sa’ad da iska mai ƙarfi ta jijjiga shi. Sararin sama kuwa ya janye kamar naɗaɗɗen littafi, ya yi ta naɗewa, aka kuma kawar da kowane dutse da kowane tsibiri daga wurinsa. Sa’an nan sarakunan duniya, hakimai, jarumawa, masu arziki, masu ƙarfi, da kowane bawa da kuma kowane ’yantacce ya ɓoye a cikin koguna da kuma cikin duwatsun tsaunuka. Suka kira duwatsu da tsaunuka suna cewa, “Ku fāɗi a kanmu ku kuma ɓoye mu daga fuskar wannan mai zama a kan kursiyi da kuma daga fushin Ɗan Ragon nan! Gama babbar ranar fushinsu ta zo, wa kuwa zai iya tsayawa?”
”Bayan wannan, na ga mala’iku huɗu, a tsaye a kusurwoyi huɗu na duniya, suna tsare iskoki huɗu na duniya, domin su hana wani iska hurawa a bisan ƙasa ko a bisan teku ko a bisa wani itace. Sai na ga wani mala’ika yana zuwa daga gabas, yana da hatimin Allah mai rai. Ya yi kira da babbar murya wa mala’ikun nan huɗu da aka ba su iko su cuci ƙasa da teku ya ce, “Kada ku cuci ƙasa ko teku ko kuma itatuwa sai bayan mun sa hatimi a goshin dukan bayin Allahnmu.”
”Sai na ji yawan waɗanda aka sa musu hatimi. Su 144,000 daga dukan kabilan Isra’ila. Daga kabilar Yahuda mutum 12,000 ne aka sa musu hatimin, daga kabilar Ruben mutum 12,000, daga kabilar Gad mutum 12,000, daga kabilar Asher mutum 12,000, daga kabilar Naftali mutum 12,000, daga kabilar Manasse mutum 12,000, daga kabilar Simeyon mutum 12,000, daga kabilar Lawi mutum 12,000, daga kabilar Issakar mutum 12,000, daga kabilar Zebulun mutum 12,000, daga kabilar Yusuf mutum 12,000, daga kabilar Benyamin mutum 12,000.
”Bayan wannan sai na duba, can a gabana kuwa ga wani taro mai girma, wanda ba mai iya ƙirgawa, daga kowace al’umma, kabila, mutane da kuma harshe, suna tsaye a gaban kursiyin da kuma gaban Ɗan Ragon nan. Suna saye da fararen tufafi suna kuma riƙe da rassan dabino a hannuwansu. Suka tā da murya da ƙarfi suna cewa, “Ceto na Allahnmu ne, wanda yake zaune a bisan kursiyi, da kuma na Ɗan Ragon.” Dukan mala’iku suna tsaye kewaye da kursiyin da kuma kewaye da dattawan tare da halittu huɗun nan masu rai. Suka fāɗi da fuskokinsu ƙasa a gaban kursiyin suka kuma yi wa Allah sujada, suna cewa, “Amin! Yabo da ɗaukaka, da hikima da godiya da girma da iko da ƙarfi sun tabbata ga Allahnmu har abada abadin. Amin!” Sai ɗaya daga cikin dattawan ya tambaye ni ya ce, “Waɗannan da suke saye da fararen tufafi su wane ne, daga ina kuma suka fito?” Na amsa na ce, “Ranka yă daɗe, kai ka sani.” Sai ya ce, “Waɗannan su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala; sun wanke tufafinsu suka kuma mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan. Saboda haka, “suna a gaban kursiyin Allah suna masa hidima dare da rana a cikin haikalinsa; kuma wannan mai zaune a kursiyin zai shimfiɗa tentinsa a bisansu. ‘Ba za su sāke jin yunwa ba; ba za su kuma sāke jin ƙishirwa ba. Rana ba za tă buga su ba,’ ko kuma kowane irin zafin ƙuna. Gama Ɗan Ragon da yake a tsakiyar kursiyin zai zama makiyayinsu; ‘zai bi da su zuwa ga maɓulɓular ruwan rai.’ ‘Allah kuwa zai share dukan hawaye daga idanunsu.’ ”
”Sa’ad da ya buɗe hatimi na bakwai, sai aka yi shiru a sama na kusan rabin sa’a. Sai na ga mala’iku bakwai da suke tsayawa a gaban Allah, a gare su kuwa aka ba da ƙahoni bakwai. Wani mala’ika, da yake da kaskon zinariyar da ake zuba turare, ya zo ya tsaya kusa da bagaden. Aka ba shi turare da yawa don yă miƙa tare da addu’o’in dukan tsarkaka a bisa bagaden zinariya a gaban kursiyin. Hayaƙin turaren tare da addu’o’in tsarkaka, suka hau zuwa gaban Allah daga hannun mala’ikan. Sai mala’ikan ya ɗauki kaskon, ya cika shi da wuta daga bagaden, ya kuma wurga shi bisan duniya; sai aka yi ta yin tsawa, ƙararraki, walƙiya, da kuma girgizar ƙasa. Sai mala’iku bakwai ɗin nan da suke da ƙahoni bakwai suka shirya don su busa su.
”Mala’ika na fari ya busa ƙahonsa, sai ga ƙanƙara da wuta haɗe da jini, aka kuma wurga su bisan duniya. Kashi ɗaya bisa uku na duniya ya ƙone, kashi ɗaya bisa uku na itatuwa suka ƙone, dukan ɗanyar ciyawa kuma ta ƙone.
”Mala’ika na biyu ya busa ƙahonsa, sai ga wani abu kamar babban dutse mai cin wuta, aka jefa cikin teku. Kashi ɗaya bisa uku na teku ya zama jini, kashi ɗaya bisa uku na halittu masu rai da suke cikin tekun suka mutu, kashi ɗaya bisa uku kuma na jiragen ruwa kuma suka hallaka.
”Mala’ika na uku ya busa ƙahonsa, sai wani babban tauraro mai cin wuta kamar toci, ya fāɗi daga sararin sama, a kan kashi ɗaya bisa uku na koguna da kuma a bisa maɓulɓulan ruwa sunan tauraron kuwa Maɗaci. Kashi ɗaya bisa uku na ruwaye ya zama mai ɗaci, mutane da yawa kuma suka mutu saboda shan ruwan, don ɗacinsa.
”Mala’ika na huɗu ya busa ƙahonsa, sai aka bugi kashi ɗaya bisa uku na rana, kashi ɗaya bisa uku na wata, da kashi ɗaya bisa uku na taurari, har kashi ɗaya bisa uku nasu ya duhunta. Kashi ɗaya bisa uku na yini ya kasance babu haske, haka ma kashi ɗaya bisan uku na dare. Yayinda nake kallo, sai na ji gaggafar da take tashi sama a tsakiyar sararin sama ta yi kira da babbar murya ta ce, “Kaito! Kaito! Kaiton mazaunan duniya, in an yi busan sauran ƙahonin da mala’ikun nan uku suke shirin busawa!”
”Mala’ika na biyar ya busa ƙahonsa, sai na ga tauraron da ya fāɗo duniya daga sararin sama. Aka ba wa tauraron mabuɗin ramin Abis. Da ya buɗe Abis ɗin, sai hayaƙi ya taso daga cikin kamar hayaƙin matoya mai girma. Hayaƙin nan daga Abis ya duhunta rana da sararin sama. Daga cikin hayaƙin kuwa fāri suka fito zuwa cikin duniya aka kuma ba su iko irin na kunaman duniya. Aka faɗa musu kada su yi wa ciyawa na duniya lahani ko wani tsiro ko itace, sai dai su yi wa mutanen da ba su da hatimin Allah a goshinsu kaɗai lahani. Ba a ba su iko su kashe su ba, sai dai su ba su azaba na watanni biyar. Azabar da suka sha kuwa ya yi kamar ta harbin kunama sa’ad da ta harbi mutum. Cikin waɗannan kwanakin mutane za su nemi mutuwa, amma ba za su samu ba; za su yi marmarin mutuwa, amma mutuwa za tă ɓace musu. Kamannin fārin nan kuwa yana kama da dawakan da aka shirya don yaƙi. A kawunansu kuwa da wani abu da ya yi kamar rawanin zinariya, fuskokinsu kuma sun yi kamar fuskokin mutane. Gashin kansu ya yi kamar gashin kan mata, haƙoransu kuma sun yi kamar haƙoran zakoki. Suna da sulkuna kamar sulkunan ƙarfe, ƙarar fikafikansu kuma ta yi kamar motsin dawakai da kekunan yaƙi masu yawa da suke rugawa zuwa yaƙi. Suna da wutsiyoyi da ƙari kamar kunamai, kuma a wutsiyoyinsu suna da iko su ba wa mutane azaba na wata biyar. Suna da sarkin da yake mulki a bisansu wanda yake mala’ikan Abis, wanda sunansa a harshen Yahudawa shi ne Abaddon, da harshen Hellenawa kuwa shi ne, Afolliyon. Bala’i na fari ya wuce, sauran bala’i biyu suna nan zuwa.
”Mala’ika na shida ya busa ƙahonsa, sai na ji murya tana fitowa daga ƙahonin bagaden zinariya da suke a gaban Allah. Ta ce wa mala’ika na shida da yake da ƙahon, “Ka saki mala’iku huɗun nan da suke a daure a babban kogin Yuferites.” Mala’iku huɗun nan kuwa da aka shirya musamman don wannan sa’a da kuma don wannan rana da wata da kuma shekara aka sake su domin su kashe kashi ɗaya bisa uku na ’yan Adam. Yawan rundunan masu hawan dawakan nan mutum miliyon ɗari biyu ne. Na ji adadinsu. Dawakai da masu hawansu da na gani cikin wahayina sun yi kamar. Sulkunansu ja wur ne, baƙin shuɗi, da kuma rawaya kamar farar wuta. Kawunan dawakan sun yi kamar kawunan zakoki, daga bakunansu kuwa wuta, hayaƙi, da farar wuta suna fitowa. Aka kashe kashi ɗaya bisa uku na ’yan Adam da annobai uku na wuta, hayaƙi da farar wuta da suka fito daga bakunansu. Ƙarfin dawakan nan kuwa yana a bakunansu da wutsiyoyinsu; gama wutsiyoyinsu suna kama da macizai masu kawuna, da wutsiyoyin ne kuma suke yi wa mutane rauni. Sauran ’yan Adam da ba a kashe ta wajen waɗannan annobai ba kuwa har wa yau ba su tuba daga aikin hannuwansu ba; ba su daina bauta wa aljanu, da gumakan zinariya, azurfa, tagulla, dutse da na itace, gumakan da ba sa iya gani ko ji ko tafiya ba. Ba su kuma tuba daga kisankansu, sihirinsu, fasikancinsu ko kuma daga sace-sacensu ba.
”Sai na ga wani babban mala’ika yana saukowa daga sama. An lulluɓe shi da girgije, bakan gizo kuma yana kansa; fuskarsa tana kama da rana, ƙafafunsa kuma suna kama da ginshiƙan wuta. Yana riƙe da ɗan ƙaramin naɗaɗɗen littafi, wanda yake a buɗe a hannunsa. Ya kafa ƙafarsa ta dama a kan teku ƙafarsa ta hagu kuma a kan ƙasa, ya kuma yi ihu da ƙarfi kamar rurin zaki. Da ya yi ihun, sai muryoyin tsawan nan bakwai suka yi magana. Sa’ad da tsawan nan bakwai kuwa suka yi magana, ina dab da rubutawa; amma na ji wata murya daga sama ta ce, “Rufe abin da tsawan nan bakwai suka faɗa kada ka rubuta.” Sai mala’ikan da na gani na tsaye a teku da ƙasa ya ɗaga hannunsa na dama sama. Ya kuma yi rantsuwa da wannan wanda yake raye har abada abadin, wanda ya halicci sammai da dukan abin da yake cikinsu, duniya da dukan abin da yake cikinta, da kuma teku da dukan abin da yake cikinsa, ya kuma ce, “Babu sauran jinkiri! Amma a ranakun da mala’ika na bakwai na dab da busa ƙahonsa, za a cika asirin Allah, kamar yadda ya sanar wa bayinsa annabawa.”
”Sai muryar da na ji daga sama ta sāke magana da ni ta ce, “Tafi, ka karɓi naɗaɗɗen littafin da yake a buɗe a hannun mala’ikan da yake tsaye bisa teku da ƙasa.” Sai na je wajen mala’ikan na ce masa yă ba ni ƙaramin naɗaɗɗen littafin. Ya ce mini, “Karɓa ka ci. Zai sa cikinka yă yi tsami, amma ‘a bakinka zai zama da zaƙi kamar zuma.’ ” Na karɓi ƙaramin naɗaɗɗen littafin daga hannun mala’ikan na kuma ci. Ya yi zaƙi kamar zuma a bakina, amma sa’ad da na cinye, cikina ya yi tsami. Sa’an nan aka ce mini, “Dole ne ka sāke yin annabci game da mutane masu yawa, al’ummai, harsuna da kuma sarakuna.”
”Aka ba ni ƙara kamar sandan awo aka kuma ce mini, “Tafi ka auna haikalin Allah da bagaden, ka kuma ƙirga waɗanda suke sujada a can. Sai dai kada ka haɗa da harabar waje; kada ka auna ta, domin an ba da ita ga Al’ummai. Za su tattaka birni mai tsarki har watanni 42. Zan kuma ba wa shaiduna nan biyu iko, za su kuwa yi annabci na kwanaki 1,260, saye da gwadon makoki.” Waɗannan su ne itatuwan zaitun biyu da kuma alkukai biyu da suke tsaye a gaban Ubangijin duniya. Duk wanda ya yi ƙoƙari yin musu lahani, wuta za tă fito daga bakunansu ta cinye abokan gābansu. Haka ne duk mai niyyar yin musu lahani zai mutu. Waɗannan mutane suna da iko su kulle sararin sama don kada a yi ruwan sama a lokacin da suke annabci; suna kuma da iko su juye ruwaye su zama jini su kuma bugi duniya da kowace irin annoba a duk lokacin da suke so.
”To, da suka gama shaidarsu, dabbar da takan fito daga Abis za tă kai musu hari, tă kuwa sha ƙarfinsu tă kuma kashe su. Gawawwakinsu za su kasance a kwance a titin babban birni, wanda a misalce ake kira Sodom da Masar, inda kuma aka gicciye Ubangijinsu. Kwana uku da rabi mutane daga kowace jama’a, kabila, harshe da kuma al’umma za su yi ta kallon gawawwakinsu su kuma ƙi binne su. Mazaunan duniya za su ƙyaface su kuma yi biki ta wurin aika kyautai wa juna, domin waɗannan annabawan nan biyu ne suka azabtar da mazaunan duniya.
”Amma bayan kwana uku da rabi ɗin numfashin rai daga Allah ya shige su, suka kuwa tashi tsaye, tsoro kuma ya kama waɗanda suka gan su. Sai suka ji wata babbar murya daga sama tana ce musu, “Ku hauro nan.” Suka kuwa haura zuwa sama cikin girgije, yayinda abokan gābansu suna kallo. A wannan sa’a aka yi wata babbar girgizar ƙasa kashi ɗaya bisa goma kuma na birnin ya rushe. Aka kashe mutane dubu bakwai a girgizar ƙasar, waɗanda suka tsira kuwa suka ji tsoro suka ɗaukaka Allah na sama. Kaito na biyu ya wuce; kaito na uku yana zuwa ba da daɗewa ba.
”Mala’ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji muryoyi masu ƙarfi a sama da suka ce, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Kiristinsa, zai kuwa yi mulki har abada abadin.” Sai dattawan nan ashirin da huɗu da suke zaune a kursiyoyinsu a gaban Allah, suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa suka kuma yi wa Allah sujada, suna cewa, “Muna maka godiya ya Ubangiji Allah, Maɗaukaki, wanda yake a yanzu, shi ne kuma a dā, domin ka karɓi ikonka mai girma ka kuma fara mulki. Al’ummai suka yi fushi; fushinka kuwa ya zo. Lokaci ya yi don a shari’anta matattu, da kuma don sākawa wa bayinka annabawa da tsarkakanka da kuma su waɗanda suke girmama sunanka, ƙarami da babba, don kuma hallakar da waɗanda suka hallaka duniya.” Sa’an nan aka buɗe haikalin Allah da yake a sama, kuma a cikin haikalinsa aka ga akwatin alkawarinsa. Sai kuwa ga walƙiya, ƙararraki, tsawa, girgizar ƙasa, da kuma ƙanƙara masu girma.
”Babbar alama mai banmamaki ta bayyana a sama, mace tana lulluɓe da rana, da kuma wata a ƙarƙashin sawunta, akwai kuma rawani mai taurari goma sha biyu a kanta. Tana da ciki ta kuma yi kuka mai zafi yayinda take gab da haihuwa. Sai wata alama ta bayyana a sama, wani babban jan maciji mai kawuna bakwai da ƙahoni goma da rawani bakwai a kan kawunansa. Wutsiyarsa ta share kashi ɗaya bisa uku na taurari daga sararin sama ta kuma zubar da su ƙasa. Ƙaton jan macijin ya tsaya a gaban macen wadda take gab da haihuwa, don yă cinye ɗanta nan take bayan an haife shi. Ta haifi ɗa, namiji, wanda zai yi mulkin dukan al’ummai da sandar ƙarfe. Aka fyauce ɗanta zuwa wurin Allah da kuma kursiyinsa. Sai macen ta gudu zuwa hamada zuwa inda Allah ya shirya dominta, inda za a lura da ita har kwana 1,260.
”Aka kuwa yi yaƙi a sama. Mika’ilu da mala’ikunsa yaƙi macijin, maciji da mala’ikunsa su ma suka mai da martani. Amma macijin nan ba shi da isashen ƙarfi, har suka rasa matsayinsu a sama. Aka jefar da ƙaton jan macijin ƙasa, tsohon maciji nan da ake kira Iblis, ko Shaiɗan, wanda ya ɓad da dukan duniya. Aka jefar da shi ƙasa, tare da mala’ikunsa a duniya. Sa’an nan na ji babbar murya daga sama tana cewa, “Yanzu ceto da iko da mulkin Allahnmu, da kuma ikon Kiristinsa. Gama mai zargin ’yan’uwanmu, wanda yake zarginsu a gaban Allahnmu dare da rana, an jefar da shi ƙasa. Sun ci nasara a kansa ta wurin jinin Ɗan Ragon da ta wurin kalmar shaidarsu; ba su ƙaunaci rayukansu sosai har da za su ja da baya daga mutuwa. Saboda haka ku yi farin ciki, ku sammai, da ku da kuke zaune a cikinsu! Amma kaiton duniya da kuma teku, gama Iblis ya sauko gare ku! Ya cika da fushi, domin ya san cewa lokacinsa ya rage kaɗan.”
”Sa’ad da macijin ya ga an jefar da shi a duniya, sai ya fafari macen nan da ta haifi ɗa namiji. Sai aka ba wa macen fikafikai biyu na babban gaggafa, don ta tashi sama zuwa inda aka shirya mata a hamada, inda za a lura da ita na ɗan lokaci, lokuta da rabin lokaci, inda macijin ba zai iya kaiwa ba. Sa’an nan daga bakinsa macijin ya kwarara ruwa kamar kogi, don ruwan ya cimma matan yă kuma kwashe ta tare da ambaliya. Amma ƙasa ta taimaki macen ta wurin buɗe bakinta ta kuma shanye ruwan kogin da macijin ya kwarara daga bakinsa. Sai macijin ya yi fushi da macen ya kuma koma wajen sauran zuriyarta don yă yaƙe su waɗannan waɗanda suke biyayya da umarnan Allah suke kuma riƙe da shaidar Yesu.
”Macijin kuwa ya tsaya a bakin teku. Sai na ga wata dabba tana fitowa daga teku. Tana da ƙahoni goma da kawuna bakwai, da kuma rawani goma a ƙahoninta, a kowane kai kuwa akwai sunan saɓo. Dabbar da na gani ta yi kamar damisa, amma tana da ƙafafu kamar na beyar, bakinta kuma ya yi kamar na zaki. Macijin nan ya ba wa dabbar ƙarfinsa da gadon sarautarsa da kuma ikonsa mai girma. Ɗaya daga cikin kawunan dabbar ya yi kamar yana da raunin da zai iya kashe shi, amma raunin nan da zai iya kashe shi ya riga ya warke. Dukan duniya ta yi mamaki ta kuma bi dabbar. Mutane suka yi wa macijin sujada domin ya ba wa dabbar ikonsa, suka yi wa dabbar sujada, suka kuma yi tambaya cewa, “Wane ne yake kama da dabban nan? Wa zai iya yaƙe ta?” Aka ba wa dabbar baki don ta faɗi kalmomin girman kai da na saɓo ta kuma yi amfani da ikonta har watanni arba’in da biyu. Ta buɗe bakinta don tă yi wa Allah saɓo, ta kuma ɓata sunansa da kuma mazauninsa da na waɗanda suke zama a sama.
”Aka ba ta iko tă yaƙi tsarkaka tă kuma ci nasara a kansu. Aka kuma ba ta iko bisa kowace kabila, jama’a, harshe da kuma al’umma. Dukan mazaunan duniya za su yi wa dabbar sujada, dukan waɗanda ba a rubuta sunayensu a cikin littafin ran da yake na Ɗan Ragon da aka yanka tun kafin halittar duniya ba. Duk mai kunne ji, bari yă ji. Duk wanda aka ƙaddara ga bauta, ga bauta zai tafi. Duk wanda aka ƙaddara za a kashe da takobi, da takobin za a kashe shi. Wannan yana bukata haƙuri da aminci a gefen tsarkaka.
”Sai na ga wata dabba tana fitowa daga ƙasa. Tana da ƙahoni biyu kamar ɗan rago, amma ta yi magana kamar maciji. Ta mori dukan ikon dabban nan ta fari a madadinta, ta sa duniya da mazaunanta su yi wa dabba ta farin nan sujada, wadda aka warkar mata da raunin nan da zai iya kashe ta. Ta kuma yi manyan ayyuka da kuma alamu masu banmamaki, har ta sa wuta ta sauko daga sama zuwa ƙasa a gaban idon mutane. Saboda alamun nan da aka ba ta iko tă yi a madadin dabban nan ta fari, sai ta ruɗi mazaunan duniya. Ta umarce su su kafa siffa don girmama dabbar da aka ji mata rauni da takobi duk da haka ta rayu. Aka ba ta iko tă ba da numfashi ga siffar dabban nan ta fari, don tă yi magana tă kuma sa a kashe duk waɗanda suka ƙi yi wa siffar sujada.
”Ta kuma tilasta wa kowa, manya da yara, mawadata da matalauta, ’yantattu da bayi, don a yi musu alama a hannun dama ko a goshi, don kada kowa yă saya ko yă sayar, sai dai yana da alamar, wadda take sunan dabbar ko kuma lambar sunanta. Wannan yana bukata hikima. Duk mai hankali, sai yă lissafta lambar dabbar, gama lamban nan ta mutum ne. Lambarta kuwa ita ce 666.
”Sai na duba, can a gabana kuwa ga Ɗan Rago, tsaye a kan Dutsen Sihiyona, tare da shi akwai kuma mutane 144,000 waɗanda suke da sunansa da sunan Ubansa a rubuce a goshinsu. Sai na ji ƙara daga sama kamar motsin ruwaye masu gudu, kamar kuma tsawa. Ƙarar da na ji ta yi kamar ta masu garaya da suke kiɗin garayarsu. Suka kuwa rera sabuwar waƙa a gaban kursiyin da kuma a gaban halittu huɗun nan masu rai, da kuma a gaban dattawa. Ba wanda ya iya koyon waƙar sai mutanen nan 144,000 da aka fansa daga duniya. Waɗannan su ne waɗanda ba su ƙazantar da kansu da mata ba, gama sun kiyaye kansu da tsarki. Suna bin Ɗan Ragon duk inda ya tafi. Su ne aka saya daga cikin mutane aka kuwa miƙa su kamar ’ya’yan fari ga Allah da kuma Ɗan Ragon. Ba a sami ƙarya a bakunansu ba; su kuma marasa aibi ne.
”Sai na ga wani mala’ika yana tashi sama a tsakiyar sararin sama, yana kuma da madawwamiyar bishara wadda zai yi shela ga waɗanda suke zama a duniya, ga kowace al’umma, kabila, harshe, da kuma jama’a. Ya ce da babbar murya, “Ku ji tsoron Allah ku kuma ɗaukaka shi, domin sa’ar hukuncinsa ya yi. Ku yi wa wannan da ya halicci sammai, ƙasa, teku, da maɓulɓulan ruwa sujada.” Mala’ika na biyu ya biyo yana cewa, “Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi, wadda ta sa dukan al’ummai suka sha ruwan inabin hauka na zinanta.”
”Mala’ika na uku ya biyo su ya ce da babbar murya, “Duk wanda ya yi wa dabban nan da siffarta sujada ya kuma sami alamarta a goshi ko a hannu, shi ma zai sha ruwan inabin fushin Allah, wanda aka zuba da duk ƙarfinsa a kwaf fushinsa. Za a ba shi azaba da farar wuta mai ci a gaban tsarkakan mala’iku da na Ɗan Ragon. Hayaƙin azabarsu kuwa zai dinga tashi har abada abadin. Kuma babu hutu dare ko rana wa waɗanda suke wa dabbar da siffarta sujada, ko kuwa ga duk wanda ya sami alamar sunanta.” Wannan yana bukata haƙuri, a gefen tsarkakan da suke biyayya da umarnan Allah suka kuma kasance da aminci ga Yesu.
”Sai na ji murya daga sama ta ce, “Rubuta, Masu albarka ne matattun da suka mutu cikin Ubangiji daga yanzu zuwa gaba.” “I, za su huta daga faman aikinsu, gama ayyukansu za su bi su,” in ji Ruhu.
”Na duba, can gabana kuwa ga farin girgije, zaune kuma a kan girgijen kuwa ga wani da ya yi kamar “ɗan mutum” tare da rawanin zinariya a kansa da kuma lauje mai kaifi a hannunsa. Sai wani mala’ika ya fito daga haikali ya kuma yi kira da babbar murya ga wannan mai zaune a kan girgijen ya ce, “Ɗauki laujenka ka yi girbi, domin lokacin girbi ya yi, gama amfanin da yake duniya ya nuna.” Sai wannan mai zaune a girgijen ya wurga laujensa a duniya, sai aka kuwa girbe duniya.
”Wani mala’ika kuma ya fito daga haikali a sama, shi ma yana da lauje mai kaifi. Har yanzu, wani mala’ika mai lura da wuta, ya fito daga bagaden ya yi kira da babbar murya ga wannan wanda yake da lauje mai kaifi ya ce, “Ɗauki laujenka mai kaifi ka tattara kawunan ’ya’yan inabi daga kuringar inabin duniya, domin ’ya’yan inabin sun nuna.” Mala’ikan ya wurga laujensa a duniya, ya tattara ’ya’yan inabin, ya kuma zuba su cikin babbar wurin matsewar inabin fushin Allah. Aka tattake su a wurin matsin inabi a bayan gari, jini kuwa ya yi ta gudana daga wurin matsin inabi tsayinsa ya kai kamar tsawon linzami a bakin doki, nisansa kuma ya kai wajen kilomita 300.
”Na ga wata babbar alama mai banmamaki a sama, mala’iku bakwai da annobai bakwai na ƙarshe, na ƙarshe, domin da su ne fushin Allah ya cika.
”Sai na ga abin da ya yi kamar tekun gilashi gauraye da wuta kuma tsaye kusa da teku, waɗanda suka ci nasara bisan dabbar da siffarta da bisan lambar sunanta. Suna riƙe da garayu waɗanda Allah ya ba su suka rera waƙar Musa bawan Allah da kuma waƙar Ɗan Ragon suna cewa, “Ayyukanka suna da girma da kuma banmamaki, ya Ubangiji Maɗaukaki. Al’amuranka suna da aminci da kuma gaskiya, ya Sarkin zamanai. Wane ne ba zai ji tsoronka, yă kuma kawo ɗaukaka ga sunanka ba, ya Ubangiji? Gama kai kaɗai ne mai tsarki. Dukan al’ummai za su zo su yi sujada a gabanka, gama an bayyana ayyukan adalcinka.”
”Bayan wannan sai na duba, a cikin sama kuwa sai ga haikali, wato, tabanakul na Shaida, a buɗe. Daga cikin haikalin mala’iku bakwai tare da annobai bakwai suka fito. Suna saye da tufafin lilin masu tsabta masu walƙiya, suna kuma saye da ɗamarar zinariya a ƙirjinsu. Sai ɗaya daga cikin halittu huɗun nan masu rai, ya ba wa mala’iku bakwai nan kwanonin zinariya bakwai cike da fushin Allah, wanda yake raye har abada abadin. Aka kuma cika haikalin da hayaƙi daga ɗaukakar Allah da kuma daga ikonsa, kuma ba wanda ya iya shiga haikalin sai da aka cika annobai bakwai nan na mala’iku bakwai.
”Sai na ji wata babbar murya daga haikalin tana ce wa mala’iku bakwai nan, “Ku tafi ku zuba kwanoni bakwai nan na fushin Allah a kan duniya.”
”Mala’ika na fari ya je ya juye kwanonsa a bisan ƙasa, sai munanan gyambuna masu zafi suka fito a jikin mutanen da suke da alamar dabbar suka kuma yi wa siffarta sujada.
”Mala’ika na biyu ya juye kwanonsa a bisan teku, sai tekun ya zama jini kamar na mataccen mutum, kuma kowane abu mai rai da yake cikin tekun ya mutu.
”Mala’ika na uku ya juye kwanonsa a bisan koguna da maɓulɓulan ruwa, sai suka zama jini. Sa’an nan na ji mala’ikan da yake lura da ruwaye ya ce, “Kai mai adalci ne cikin waɗannan hukuntai, kai da kake yanzu, kake kuma a dā, Mai Tsarki, saboda yadda ka yi hukuncin nan; gama sun zub da jinin tsarkakanka da kuma annabawanka, ka kuwa ba su jini su sha, yadda ya dace da su.” Na kuma ji bagaden ya amsa, “I, Ubangiji Allah, Maɗaukaki, hukuntanka daidai yake na adalci ne kuma.”
”Mala’ika na huɗu ya juye kwanonsa a bisan rana, sai aka ba wa rana iko ta ƙona mutane da wuta. Aka ƙone su da zafin wuta mai tsanani suka kuwa la’anci sunan Allah wanda yake da iko a kan waɗannan annoban, amma suka ƙi su tuba su kuma ɗaukaka shi.
”Mala’ika na biyar ya juye kwanonsa a bisan gadon sarautar dabbar, mulkinta kuwa ya zama duhu. Mutane suka yi ta cizon bakinsu saboda azaba suka kuma la’anci Allah na sama saboda zafinsu, da kuma saboda gyambunansu, amma suka ƙi su tuba daga abin da suka riga suka yi.
”Mala’ika na shida ya juye kwanonsa a bisan babban kogin Yuferites, sai ruwansa ya shanye don a shirya hanya saboda sarakuna daga Gabas.
”Sa’an nan na ga mugayen ruhohi guda uku da suka yi kamar kwaɗi; suka fito daga bakin macijin nan, da kuma daga bakin dabbar, da kuma daga bakin annabin ƙaryan nan. Su ruhohin aljanu ne da suke aikata abubuwan banmamaki, sukan je wurin sarakunan dukan duniya, don su tattara su don yaƙi a babbar ranar Allah Maɗaukaki. ‹“Ga shi, ina zuwa kamar ɓarawo! Mai albarka ne wanda yake zama a faɗake yana kuma saye da tufafinsa, don kada yă yi tafiya tsirara a kuma kunyata shi.”› Sa’an nan aka tattara sarakuna zuwa wurin da a Ibraniyanci ake kira Armageddon.
”Mala’ika na bakwai ya juye kwanonsa cikin iska, daga haikalin kuwa sai aka ji wata babbar murya daga kursiyin, tana cewa, “An gama!” Sai ga walƙiya, ƙararraki, tsawa da kuma matsananciyar girgizar ƙasa. Ba a taɓa yin irin wannan girgizar ƙasar ba, tun kasancewar mutum a duniya, girgizar ƙasar kuwa gawurtacciya ce. Babban birnin ya rabu kashi uku, biranen al’ummai kuma suka rurrushe. Allah ya tuna da Babilon Mai Girma ya kuma ba ta kwaf cike da ruwan inabin fushinsa. Kowane tsibiri ya gudu ba a kuwa ƙara ganin duwatsu ba. Daga sararin sama manyan ƙanƙara masu nauyin gaske suka fāɗo a kan mutane. Suka kuma la’anci Allah saboda annobar ƙanƙarar, domin annobar ta yi muni ƙwarai.
”Ɗaya daga cikin mala’iku bakwai masu ɗauke da kwanoni bakwai nan, ya zo ya ce mini, “Zo, zan nuna maka hukuncin babbar karuwan nan da take zaune a bisan ruwaye masu yawa. Da ita ce sarakunan duniya suka yi zina mazaunan duniya kuma suka bugu da ruwan inabin zinace zinacenta.” Sa’an nan mala’ikan ya ɗauke ni cikin Ruhu zuwa hamada. A can na ga mace zaune a kan wata jan dabbar da aka rufe da sunayen saɓo tana kuma da kawuna bakwai da ƙahoni goma. Macen tana saye da tufafi masu ruwan ja da shunayya, tana ƙyalli da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai. Tana riƙe da kwaf na zinariya a hannunta, cike da abubuwa masu banƙyama da kuma ƙazantar zinace zinacenta. Sunan da aka rubuta a goshinta asiri ne, Babilon mai girma mahaifiyar karuwai da kuma na abubuwa masu banƙyama na duniya. Na ga cewa macen ta bugu da jinin tsarkaka, jinin waɗanda suka shaida Yesu. Da na gan ta, sai na yi mamaki ƙwarai. Sa’an nan mala’ikan ya ce mini, “Don me kake mamaki? Zan bayyana maka asirin macen nan da dabbar da take hawa, wadda take da kawuna bakwai da ƙahoni goma.
”Dabbar da ka gani, a dā ta taɓa kasancewa, a yanzu, ba ta, za tă kuma fito daga Abis zuwa ga hallakarta. Mazaunan duniya waɗanda ba a rubuta sunayensu a littafin rai tun kafin halittar duniya ba za su yi mamaki sa’ad da suka ga dabbar, domin a dā ta taɓa kasancewa, yanzu kuwa ba ta, duk da haka za tă dawo. “Wannan yana bukata hankali da kuma hikima. Kawuna bakwai nan tuddai bakwai ne da macen take zama a kai. Sarakuna bakwai ne kuma. Biyar sun fāɗi, ɗaya yana nan, ɗayan kuma bai zo ba tukuna; amma sa’ad da ya zo, zai kasance na ɗan lokaci. Dabbar da a dā ta taɓa kasancewa, amma yanzu ba ta, ita ce sarki na takwas. Ita ɗaya ce cikin bakwai ɗin, kuma tana tafiya zuwa ga hallakarta. “Ƙahonin nan goma da ka gani sarakuna goma ne da ba su riga sun karɓi mulki ba, amma waɗanda na sa’a guda za su karɓi iko a matsayin sarakuna tare da dabbar. Suna da manufa guda za su kuma ba wa dabbar ikonsu da kuma sarautarsu.
”Za su yi yaƙi da Ɗan Ragon, sai dai Ɗan Ragon zai ci nasara a bisansu domin shi ne Ubangijin iyayengiji, Sarkin sarakuna, tare da shi kuwa kirayayunsa, zaɓaɓɓunsa da kuma amintattu masu binsa za su kasance.” Sa’an nan mala’ikan ya ce mini, “Ruwayen da ka gani, inda karuwan take zama, jama’a ce, taro masu yawa, al’ummai da kuma harsuna. Dabbar da kuma ƙahoni goma da ka gani za su ƙi jinin karuwar. Za su kai ta ga hallaka su kuma bar ta tsirara; za su ci namanta su kuma ƙone ta da wuta. Gama Allah ya sa a zukatansu su cika nufinsa ta wurin yarda su ba wa dabbar ikonsu tă yi mulki, sai lokacin da kalmomin Allah sun cika. Macen da ka gani ita ce babban birnin da yake mulki a bisan sarakunan duniya.”
”Bayan wannan sai na ga wani mala’ika yana saukowa daga sama. Yana da iko mai girma, aka haskaka duniya da darajarsa. Ya yi kira da babbar murya ya ce, “Ta fāɗi! Babilon Mai Girma ta fāɗi. Ta zama gidan aljanu da kuma wurin zaman kowace irin mugun ruhu, wurin zaman kowane irin tsuntsu marar tsabta da mai banƙyama. Gama dukan al’ummai sun sha ruwan inabin haukan zinace zinacenta. Sarakunan duniya sun yi zina tare da ita, attajiran duniya kuma sun arzuta da almubazzarancinta.”
”Sai na ji wata murya daga sama ta ce, “Ku fita daga cikinta, mutanena, don kada zunubanta su shafe ku, don kada wata annobarta ta same ku; gama zunubanta sun yi tsororuwa sun kai sama. Allah kuma ya tuna da laifofinta. Ku sāka mata kamar yadda ta sāka muku; ku sāka mata sau biyu na abin da ta yi. Ku dama mata sau biyu na abin da yake cikin kwaf nata. Ku ba ta isashen azaba da baƙin ciki kamar daraja da kuma jin daɗin da ta ba wa kanta. A zuciyarta takan yi taƙama, ta ce, ‘Ina zama kamar sarauniya; ni ba gwauruwa ba ce, kuma ba zan taɓa yin makoki ba.’ Saboda haka a rana ɗaya annobarta za su cim mata, mutuwa, makoki da kuma yunwa. Wuta zai cinye ta, gama Ubangiji Allah mai girma ne, wanda yake shari’anta ta.
”“Sa’ad da sarakunan duniya da suka yi zina da ita suka kuma yi tarayya cikin jin daɗinta suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi kuka da makoki saboda ita. Don tsoron ganin azabarta za su tsaya daga nesa, su yi kuka suna cewa, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma. Ya ke Babilon, birni mai iko! Cikin sa’a guda hallakarki ta zo!’ “Attajiran duniya za su yi kuka su kuma yi makoki a kanta, domin ba wanda yake ƙara sayen kayayyakinsu kayayyakin zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja da lu’ulu’ai; lallausan lilin, tufa masu ruwan shunayya, siliki da jan tufa; da kowane irin katakai masu ƙanshi da kayayyaki na kowane iri da aka yi da hauren giwa, katakai masu tsada, tagulla, baƙin ƙarfe da dutse mai sheƙi; kayayyakin sinnamon da kayan yaji, na turaren wuta, mur da turare, na ruwan inabi da man zaitun, na gari mai laushi da alkama; shanu da tumaki; dawakai da kekunan doki, da jikuna da kuma rayukan mutane. “Za su ce, ‘Amfanin da kike marmari ya kuɓuce. Dukan arzikinki da darajarki sun ɓace, ba kuwa za a ƙara samunsu ba.’ Attajiran da suka sayar da waɗannan kayayyaki suka kuma sami arzikinsu daga gare ta za su tsaya daga nesa, cike da tsoron ganin azabarta. Za su yi kuka da makoki su ce, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma, saye da lallausan lilin, shunayya da kuma ja, mai walƙiya da zinariya, duwatsu masu daraja da kuma lu’ulu’ai! Cikin sa’a guda irin wannan dukiya mai yawa ta hallaka!’ “Duk matuƙan jirgin ruwa, da dukan waɗanda suke tafiya a jirgin ruwa, ma’aikatanta, da duk masu samun abin zama gari daga teku za su tsaya daga nesa. Sa’ad da suka ga hayaƙin ƙunarta, za su yi ihu su ce, ‘An taɓa samun birni kamar wannan babban birnin kuwa?’ Za su zuba ƙura a kawunansu, da kuka da makoki za su yi ta kururuwa, “ ‘Kaito! Kaito, ya birni mai girma, inda dukan waɗanda suke da jiragen ruwa a teku suka arzuta da ɗumbun dukiyarsa! Cikin sa’a ɗaya ta hallaka!’ “Ki yi murna a kanta, ya sama! Ku yi murna, ku tsarkaka! Ku yi murna, ku manzanni da annabawa! Allah ya hukunta shi saboda abin da ya yi muku.” Sa’an nan wani mala’ika mai ƙarfi ya ɗauki dutse kamar girman babban dutsen niƙa ya jefa cikin teku ya ce, “Da wannan irin giggitawa za a jefar da birnin Babilon mai girma ƙasa, ba za a ƙara ganin ta ba. Ba za a ƙara jin ƙarar kiɗin masu garaya da muryar mawaƙa, da na masu bushe-bushe, da na masu busan ƙaho a cikinki ba. Ba za a ƙara samun ma’aikaci na kowace irin sana’a a cikinki kuma ba. Ba za a ƙara jin ƙarar dutsen niƙa a cikinki kuma ba.
”Hasken fitila ba zai ƙara haskakawa a cikinki ba. Ba za a ƙara jin muryar ango da amarya a cikinki ba. Attajiranki, dā su ne manyan mutanen duniya. Ta wurin sihirinki, dukan ƙasashe sun kauce. A cikinta aka sami jinin annabawa, da na tsarkaka, da kuma na dukan waɗanda aka kashe a duniya.”
”Bayan wannan sai na ji abin da ya yi kamar ƙasaitaccen taron mutane a sama, suna cewa, “Halleluya! Ceto da ɗaukaka da iko sun tabbata ga Allahnmu, gama hukuncinsa daidai ne, mai adalci kuma. Ya hukunta babbar karuwan nan wadda ta ɓata duniya da zinace zinacenta. Ya rama jinin bayinsa a kanta.” Suka sāke tā da murya suka ce, “Halleluya! Hayaƙin yake fitowa daga wurinta ya yi ta tashi sama har abada abadin.” Dattawan nan ashirin da huɗu da halittu huɗun nan masu rai suka fāɗi suka yi wa Allah sujada, wannan da yake zaune a kursiyi. Suka tā da murya suka ce, “Amin, Halleluya!” Sa’an nan wata murya ta fito daga kursiyin, tana cewa, “Ku yabi Allahnmu, dukanku da kuke bayinsa, ku da kuke tsoronsa, babba da yaro!” Sai na ji wani abu mai ƙara kamar ƙasaitaccen taron mutane, kamar rurin ruwaye masu gudu da kuma kamar bugun tsawa mai ƙarfi, suna tā da murya suna cewa, “Halleluya! Gama Ubangiji Allahnmu Maɗaukaki ne yake mulki.
”Bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna mu kuma ɗaukaka shi! Domin lokacin auren Ɗan Ragon ya yi, amaryarsa kuwa ta shirya kanta. Aka ba ta lallausan lilin, mai haske da tsabta ta sanya.” (Lallausan lilin yana misalta ayyukan adalci na tsarkaka.) Sai mala’ikan ya ce mini, “Rubuta, ‘Masu albarka ne waɗanda aka gayyace su zuwa bikin auren Ɗan Ragon!’ ” Sai ya ƙara da cewa, “Waɗannan su ne kalmomin Allah da gaske.” Da wannan sai na fāɗi a gabansa, don in yi masa sujada. Amma ya ce mini, “Kada ka yi haka! Ni ma abokin bauta ne da kai da kuma ’yan’uwanka waɗanda suke riƙe da shaidar Yesu. Ka yi wa Allah sujada! Domin shaidar Yesu ita ce ruhun annabci.”
”Sai na ga sama a buɗe can kuwa a gabana ga farin doki, sunan mahayinsa Mai Aminci da Mai Gaskiya ne. Da adalci yake shari’a yake kuma yaƙi. Idanunsa sun yi kamar harshen wuta, a kansa kuwa akwai rawani masu yawa. Yana da suna rubuce a kansa da babu wanda ya sani sai dai shi. Yana saye da rigar da aka tsoma a jini, sunansa kuwa Kalman Allah ne. Mayaƙan sama suna biye da shi, suna hawan fararen dawakai, saye da fararen tufafi masu tsabta na lallausan lilin. Daga bakinsa takobi mai kaifi ya fito. Da shi zai karkashe al’ummai. “Zai yi mulkinsu da sandan sarautar ƙarfe.” Yana tattake wurin matsin ruwan inabi na fushin Allah Maɗaukaki. A rigarsa da kuma a cinyarsa akwai wannan suna a rubuce, Sarkin sarakuna da Ubangijin iyayengiji.
”Na kuma ga wani mala’ika tsaye a cikin rana, wanda ya yi kira da babbar murya ga dukan tsuntsaye da suke tashi sama a tsakiyar sararin sama cewa, “Ku zo, ku taru don babban bikin nan na Allah, don ku ci naman sarakuna, jarumawa, da kuma manyan mutane, na dawakai da mahayansu, da kuma naman dukan mutane, ’yantacce da bawa, babba da yaro.”
”Sa’an nan na ga dabbar da sarakunan duniya da mayaƙansu sun taru don su yi yaƙi da wannan wanda yake kan farin dokin da kuma mayaƙansa. Amma aka kama dabbar tare da annabin ƙaryan nan wanda ya aikata alamu masu banmamaki a madadinta. Da waɗannan alamun ne ya ruɗe waɗanda suka sami alamar dabbar suka kuma bauta wa siffarta. Aka jefa dukansu biyu da rai cikin tafkin wuta ta da farar wuta mai ci. Sauran kuma aka kashe su da takobin da ya fito daga bakin wannan wanda yake kan dokin. Dukan tsuntsaye kuwa suka ci namansu iyakar iyawarsu.
”Na kuma ga wani mala’ika yana saukowa daga sama, yana da mabuɗin Abis yana kuma riƙe da ƙaton sarƙa a hannunsa. Ya kama macijin, wannan tsohon maciji, wanda yake shi ne Iblis, ko kuwa Shaiɗan, aka kuma ɗaura shi har shekara dubu. Ya jefa shi cikin Abis, ya kuma kulle ya sa hatimi a kansa, don a hana kada yă ƙara ruɗin al’ummai, sai shekarun nan dubu sun cika. Bayan wannan, dole a sake shi na ɗan lokaci.
”Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu. (Sauran matattu ba su sāke rayuwa ba, sai da shekaru dubun nan suka cika.) Wannan fa shi ne tashin matattu na farko. Masu albarka da kuma tsarki ne waɗanda suke da rabo a tashin matattu na farko. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kansu, sai dai za su zama firistocin Allah da kuma na Kiristi za su kuma yi mulki tare da shi na shekaru dubu.
”Sa’ad da shekaru dubun nan suka cika, za a saki Shaiɗan daga kurkukun da yake, zai kuma fito don yă ruɗi al’ummai da suke a kursuyoyi huɗu na duniya, Gog da Magog, yă tattara su don yaƙi. Yawansu kuwa ya yi kamar yashi a bakin teku. Suka mamaye duk fāɗin duniya suka kuma kewaye sansanin mutanen Allah, birnin da yake ƙauna. Amma wuta ta fito daga sama ta cinye su.
”Aka jefa Iblis da ya ruɗe su cikin tafkin farar wuta, inda aka jefa dabban nan da annabin ƙaryan nan. Za a ba su azaba dare da rana har abada abadin.
”Sa’an nan na ga babban farin kursiyi da kuma wannan da yake zama a kansa. Duniya da sararin sama kuwa suka ɓace daga gabansa, babu wuri kuwa dominsu. Sai na ga matattu, babba da yaro tsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne littafin rai. Aka yi wa matattu shari’a bisa ga abin da suka aikata yadda yake a rubuce a cikin littattafai. Teku ya ba da matattu da suke cikinsa, mutuwa da Hades kuma suka ba da matattu da suke cikinsu, aka kuma yi wa kowane mutum shari’a bisa ga abin da ya aikata. Sa’an nan aka jefar da mutuwa da kuma Hades cikin tafkin wuta. Tafkin wutar nan kuwa shi ne mutuwa ta biyu. Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a cikin littafin rai ba, an jefar da shi cikin tafkin wutar nan.
”Sa’an nan na ga sabon sama da sabuwar duniya, gama sama na farko da duniya ta farko sun shuɗe, babu kuma wani teku. Na ga Birni Mai Tsarki, sabuwar Urushalima tana saukowa daga sama, daga Allah, a shirye kamar amaryar da aka yi mata ado mai kyau saboda mijinta.
”Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu. Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe.” Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. “Ina yin kome sabo!” Sai ya ce, “Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma.” Ya ce mini, “An gama. Ni ne Alfa da kuma Omega, na Farko da kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi abin sha kyauta daga maɓulɓular ruwan rai. Duk wanda ya ci nasara zai gāji dukan wannan, zan kuma zama Allahnsa, shi kuma zai zama ɗana. Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.” Ɗaya daga cikin mala’ikun nan bakwai masu kwanonin nan bakwai cike da annoban nan bakwai na ƙarshe, ya zo ya ce mini “Zo, zan nuna maka amaryar, matar Ɗan Ragon.”
”Ya kuwa ɗauke ni cikin Ruhu zuwa wani babban dutse mai tsayi, ya kuma nuna mini Birni Mai Tsarki, Urushalima, tana saukowa daga sama, daga Allah. Ya haskaka da ɗaukakar Allah, haskensa kuwa ya yi kamar lu’ulu’u mai daraja sosai, kamar yasfa, yana ƙyalƙyali kamar madubi. Yana da babbar katanga mai tsayi, mai ƙofofi goma sha biyu, da kuma mala’iku goma sha biyu a ƙofofin. A bisa ƙofofin an rubuta sunayen kabilu goma sha biyu na Isra’ila. Akwai ƙofofi uku a gabas, uku a arewa, uku a kudu, uku kuma a yamma. An gina katangar birnin a kan tushen gini goma sha biyu, a kansu kuwa akwai sunayen manzannin sha biyu na Ɗan Ragon. Mala’ikan da ya yi magana da ni yana da sandan awo na zinariya don awon birnin, ƙofofinsa, da kuma katangarsa. Birnin murabba’i ne, tsayinsa daidai ne da fāɗinsa. Ya auna birnin da sandarsa ya kuwa sami mil 1,400 (wajen kilomita 2,200) tsawonsa, fāɗinsa da kuma tsayinsa daidai suke. Ya auna katangarsa ya kuma sami ƙaurinta kamun 144, bisa ga ma’aunin mutum, wanda mala’ikan ya yi amfani da shi. An yi katangar da yasfa, birnin kuma da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi. Tushen ginin katangar birnin kuwa an yi masa adon da kowane irin dutse mai daraja. Tushe na farko an yi shi yasfa, na biyu saffaya, na uku agat, na huɗu zumurrudu, na biyar onis, na shida yakutu, na bakwai kirisolit, na takwas beril, na tara tofaz, na goma kirisofuras, na goma sha ɗaya yasin, na goma sha biyu kuma ametis. Ƙofofi goma sha biyun nan lu’ulu’ai goma sha biyu ne, kowace ƙofa an yi ta da lu’ulu’u guda. Babban titin birnin kuwa an yi shi da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi.
”Ban ga haikali a cikin birnin ba, domin Ubangiji Allah Maɗaukaki da kuma Ɗan Ragon ne haikalin birnin. Birnin ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi, gama ɗaukakar Allah tana ba shi haske, Ɗan Ragon kuwa shi ne fitilar birnin. Al’ummai za su yi tafiya cikin hasken birnin, sarakunan duniya kuma za su kawo darajarsu cikin birnin. Ba za a taɓa rufe ƙofofin birnin da rana ba, gama ba za a yi dare a can ba. Za a kawo ɗaukaka da girmar al’ummai a cikin birnin. Babu wani abu marar tsarkin da zai taɓa shiga cikin birnin, babu kuma wani mai aikata abin kunya ko ruɗi da zai shiga, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a cikin littafin rai na Ɗan Ragon.
”‹“Ga shi, ina zuwa da wuri! Ladan da zan bayar yana tare da ni, kuma zan ba wa kowa gwargwadon abin da ya yi.›
”