32 – Shahada
Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Shahada.
Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Shahada.
‹Gaskiya nake gaya muku, sai ƙwayar alkama ta fāɗi ƙasa ta mutu, in ba haka ba za tă kasance ƙwaya ɗaya tak. Amma in ta mutu, za tă ba da ’ya’ya da yawa.› ‹Duk mai ƙaunar ransa, zai rasa shi, duk mai ƙin ransa a wannan duniya, zai kiyaye shi har yă zuwa rai madawwami.› ‹Duk wanda zai bauta mini dole yă bi ni, inda kuma nake, a can bawana zai kasance. Ubana zai girmama wanda yake bauta mini.›
”‹Za su kore ku daga majami’a; lalle, lokaci yana zuwa da duk wanda ya kashe ku, zai ɗauka yana yin wa Allah hidima ne.› ‹Za su yi waɗannan abubuwa ne domin ba su san Uba ko ni ba.› ‹Na faɗa muku wannan, domin in lokacin ya yi, ku tuna na gargaɗe ku. Ban faɗa muku wannan tun da fari ba domin ina tare da ku.›
”Sa’ad da ya buɗe hatimi na biyar, sai na ga a ƙarƙashin bagaden rayukan waɗanda aka kashe saboda maganar Allah da kuma shaidar da suka yi. Suka yi kira da babbar murya suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarki da kuma Mai Gaskiya, sai yaushe za ka shari’anta mazaunan duniya ka kuma ɗauki mana fansar jininmu?” Sai aka ba wa kowannensu farin riga, aka kuma faɗa musu su ɗan jira kaɗan sai an cika adadin abokansu masu hidima da kuma ’yan’uwansu waɗanda za a kashe kamar yadda su ma aka kashe su.
”Ana nan sai Kayinu ya kawo waɗansu amfanin gona a matsayin hadaya ga Ubangiji. Amma Habila ya kawo mafi kyau daga ’ya’yan fari na garkensa. Ubangiji ya yi farin ciki da sadakar da Habila ya kawo, amma bai yi farin ciki da sadakar da Kayinu ya kawo ba. Saboda haka Kayinu ya ji fushi sosai, fuskarsa kuma ta ɓace. Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Don me kake fushi? Don me fuskarka ta ɓace? Da ka yi abin da yake daidai, ai, da ka sami karɓuwa. Amma tun da ba ka yi abin da ba daidai ba, zunubi zai yi fakonka don yă rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so yă mallake ka, amma tilas ka rinjaye shi.” To, Kayinu ya ce wa ɗan’uwansa Habila, “Mu tafi gona.” Yayinda suke a gona, sai Kayinu ya tasar wa Habila ya buge shi ya kashe. Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina ɗan’uwanka Habila?” Sai Kayinu ya ce, “Ban sani ba, ni mai gadin ɗan’uwana ne?” Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Saurara! Ga jinin ɗan’uwanka yana mini kuka daga ƙasa.
”Bayan abubuwan nan suka faru, sai Allah ya gwada Ibrahim. Ya ce masa, “Ibrahim!” Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.” Sai Allah ya ce, “Ka ɗauki ɗanka, makaɗaicin ɗanka Ishaku, wanda kake ƙauna, ka tafi yankin Moriya, ka miƙa shi hadaya ta ƙonawa a can a kan ɗaya daga cikin duwatsun da zan nuna maka.” Kashegari da sassafe, Ibrahim ya tashi ya ɗaura wa jakinsa sirdi. Ya ɗauki bayinsa biyu, da ɗansa Ishaku. Bayan ya faskare isashen itace saboda hadaya ta ƙonawa sai ya kama hanya zuwa wurin da Allah ya faɗa masa. A rana ta uku Ibrahim ya ɗaga ido sai ya ga wurin daga nesa. Ibrahim ya ce wa bayinsa, “Ku tsaya a nan da jakin, ni da yaron kuwa mu haura can. Za mu yi sujada sa’an nan mu komo wurinku.” Ibrahim ya ɗauki itace saboda hadaya ta ƙonawa ya ɗora wa ɗansa Ishaku, shi kuwa ya riƙe wuƙa da wutar. Yayinda su biyun suke tafiya, sai Ishaku ya yi tambaya, ya ce wa mahaifinsa Ibrahim, “Baba?” Ibrahim ya ce masa, “Na’am ɗana!” Ishaku ya ce, “Ga dai wuta, ga kuma itace, amma ina ɗan ragon hadaya ta ƙonawa?” Ibrahim ya amsa ya ce, “Ɗana, Allah kansa zai tanada ɗan ragon hadayar ƙonawa.” Sai su biyu suka ci gaba da tafiya. Sa’ad da suka isa wurin da Allah ya faɗa masa, sai Ibrahim ya gina bagade a can, ya kuma shisshirya itacen a kai. Ya ɗaura ɗansa Ishaku, ya kwantar da shi a kan itacen, a bisa bagaden. Sa’an nan Ibrahim ya miƙa hannunsa ya ɗauki wuƙar don yă yanka ɗansa. Amma mala’ikan Ubangiji ya kira shi daga sama ya ce, “Ibrahim, Ibrahim!” Sai Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga ni.” Mala’ikan ya ce, “Kada ka yi wa yaron nan rauni. Kada kuma ka ji masa ciwo. Yanzu na san cewa kana tsoron Allah, gama ba ka hana ni ɗanka, makaɗaicin ɗanka ba.” Ibrahim ya ɗaga ido, ya duba, sai ya ga rago da ƙahoninsa a kafe a wani ɗan kurmi. Sai Ibrahim ya tafi ya kamo ragon ya miƙa shi hadaya ta ƙonawa a maimakon ɗansa.
”Dabbobin da za ku zaɓa, dole su zama bana ɗaya, namiji marar tabo, za ku kuma kamo su daga cikin tumaki ko awaki.
”Ba za ka yi kisankai ba.
”Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je.”
”Sai sarki ya umarci matsaran da suke tsaye kusa da shi ya ce, “Ku kakkashe firistocin Ubangiji, gama su ma sun goyi bayan Dawuda. Sun san yana gudu, duk da haka ba su gaya mini ba.” Amma ma’aikatan sarki ba su yarda su sa hannu su kashe firistocin Ubangiji ba. Sai sarki ya umarce Doyeg ya ce, “Ka juya ka kakkashe firistocin.” Doyeg mutumin Edom ya juya ya kakkashe firistocin. A ranar kuwa ya kashe mutum tamanin da biyar waɗanda suke sanye da efod na lilin. Ya kuma hallaka Nob birnin firistoci, ya kashe dukan mata, da maza, da yara, da jarirai, da shanu, da jakuna, da kuma tumaki.
”Yayinda Yezebel tana kisan annabawan Ubangiji, Obadiya ya ɗauki annabawa ɗari ya ɓoye a kogwanni biyu, hamsin a kowanne, ya kuma tanada musu abinci da kuma ruwa.)
”Ya amsa, ya ce, “Ina kishi dominka Ubangiji, Allah Maɗaukaki. Isra’ilawa sun ƙi alkawarinka, suka rurrushe bagadanka, suka kuma kashe annabawanka da takobi. Ni ne kaɗai na rage, yanzu, ni ma suna ƙoƙari su kashe ni.”
”Ku dogara ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa; ku nemi fuskarsa kullum.
”Sai Ruhun Allah ya sauko a kan Zakariya ɗan Yehohiyada firist. Ya tsaya a gaban mutane ya ce, “Ga abin da Allah ya ce, ‘Me ya sa ba ku yi biyayya da umarnan Ubangiji ba? Ba za ku yi nasara ba. Domin kun yashe Ubangiji, shi ma ya yashe ku.’ ” Amma suka yi masa maƙarƙashiya, kuma ta wurin umarnin sarki suka jajjefe shi da duwatsu har ya mutu a filin haikalin Ubangiji.
”“Amma suka yi rashin biyayya suka kuma yi tawaye gare ka; suka sa dokarka a bayansu. Suka kashe annabawanka waɗanda suka gargaɗe su don su mai da su gare ka; suka aikata saɓo mai bantsoro.
”Da jin haka sai Ayuba ya tashi ya yayyaga tufafin jikinsa, ya aske kansa. Ya fāɗi a ƙasa ya yi sujada ya ce, “Tsirara na fito daga cikin mahaifiyata, tsirara kuma zan koma. Ubangiji ya bayar, Ubangiji kuma ya karɓa; yabo ya tabbata ga Ubangiji.”
”Ko da zai kashe ni ne, begena a cikinsa zai kasance; ba shakka zan kāre kaina a gabansa
”Na san wanda zai fanshe ni yana nan da rai, kuma a ƙarshe zai tsaya a kan duniya. Kuma bayan an hallaka fatata, duk da haka a cikin jiki zan ga Allah. Zan gan shi da kaina da idanuna, Ni, ba wani ba ne. Zuciyata ta cika da wannan tunani!
”Amma ya san hanyar da nake bi; sa’ad da ya gwada ni zan fito kamar zinariya. Ƙafafuna suna bin ƙafafunsa kurkusa; na bi hanyarsa ba tare da na juya ba.
”Me ya sa ƙasashe suke haɗa baki mutane kuma suke ƙulla shawarwarin banza? Sarakunan duniya sun ɗauki matsayi masu mulki sun taru gaba ɗaya suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa. Suna cewa, “Bari mu tsittsinke sarƙoƙinsu, mu kuma ’yantar da kamammu daga kangin bautar Allah.” Mai zama a kursiyi a sama yana dariya; Ubangiji yana musu ba’a.
”Amma bari dukan waɗanda suke neman mafaka gare ka su yi murna; bari kullum su yi ta rerawa saboda farin ciki. Ka buɗe kāriyarka a bisansu, domin waɗanda suke ƙaunar sunanka su yi farin ciki a cikinka.
”Kullum nakan sa Ubangiji a gabana. Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba. Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki; jikina kuma zai zauna lafiya, domin ba za ka yashe ni a kabari ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba. Ka sanar da ni hanyar rai; za ka cika ni da farin ciki a gabanka, da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.
”Amma ni, cikin adalci zan ga fuskarka; sa’ad da na farka, zan gamsu da ganin kamanninka.
”yakan maido da raina. Yakan bi da ni a hanyoyin adalci saboda sunansa. Ko da na yi tafiya ta kwari na inuwar mutuwa, ba zan ji tsoron mugu ba, gama kana tare da ni; bulalarka na dūka da kuma sandanka na tafiya, za su yi mini ta’aziyya.
”Ubangiji ne haskena da cetona, wa zan ji tsoro? Ubangiji ne mafakar raina, wane ne zan ji tsoro? Sa’ad da mugaye suka tasar mini don su cinye ni, sa’ad da abokan gābana da maƙiyina suka kawo mini hari, sun yi tuntuɓe suka fāɗi. Ko da yake mayaƙa sun kewaye ni, zuciyata ba za tă ji tsoro ba; ko da yake ya ɓarke a kaina, duk da haka zan ƙarfafa. Abu guda na roƙi Ubangiji, wannan shi ne na nema, cewa in zauna a gidan Ubangiji dukan kwanakin raina, in dubi kyan Ubangiji in kuma neme shi a cikin haikalinsa. Gama a lokacin wahala, zai kiyaye ni lafiya a wurin zamansa; zai ɓoye ni cikin inuwar tabanakul nasa ya kuma sa ni can a bisa dutse.
”Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji ku kuma yi murna, ku adalai; ku rera, dukanku waɗanda zuciyarku take daidai!
”Mugaye sukan shirya wa adalai maƙarƙashiya su ciji baki a kansu; amma Ubangiji yakan yi dariyar mugaye, gama ya sani ranarsu tana zuwa. Mugaye sukan zare takobi su ja baka don su kashe matalauta da masu bukata, don su kashe waɗanda hanyoyinsu daidai suke. Amma takubansu za su soki zukatansu, kuma bakkunansu za su kakkarye.
”Duk da haka saboda kai mun fuskanci mutuwa dukan yini; aka ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.
”Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala. Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku,
”Gama wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin; zai zama jagorarmu har zuwa ƙarshe.
”Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji zai kuwa riƙe ku; ba zai taɓa barin mai adalci yă fāɗi ba.
”Amma kai, ya Ubangiji, kakan yi musu dariya; kana yi wa dukan waɗannan al’ummai ba’a. Ya ƙarfina, na dogara gare ka; kai, ya Allah, kai ne kagarata, Allah mai ƙaunata. Allah zai sha gabana zai kuma sa in yi dariya a kan waɗanda suke magana marar kyau a kaina.
”A gadona na tuna da kai; ina tunaninka dukan dare. Domin kai ne mai taimakona, ina rera a cikin inuwar fikafikanka. Raina ya manne maka; hannunka na dama yana riƙe da ni. Su da suke neman raina za su hallaka; za su gangara zuwa zurfafan duniya.
”Amma bari adalai su yi murna su kuma yi farin ciki a gaban Allah; bari su yi murna da farin ciki. Rera wa Allah, rera yabo ga sunansa, ku ɗaukaka wanda yake hawa a kan gizagizai; sunansa Ubangiji ne, ku kuma yi farin ciki a gabansa.
”Duk da haka kullum ina tare da kai; ka riƙe ni a hannun damana. Ka bishe ni da shawararka, bayan haka kuma za ka kai ni cikin ɗaukaka. Wa nake da shi a sama in ba kai ba? Ba na kuma sha’awar kome a duniya in ban da kai. Jikina da zuciyata za su iya raunana, amma Allah ne ƙarfin zuciyata da kuma rabona har abada.
”Masu albarka ne waɗanda suka koyi yin maka kirari waɗanda suke tafiya cikin hasken da yake gabanka, Ubangiji. Suna farin ciki a cikin sunanka dukan yini; suna samun ɗaukaka cikin adalcinka.
”Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki.
”A ɗaukaka ka, ya Allah, a bisa sammai, bari kuma ɗaukakarka ta kasance a bisa dukan duniya.
”Ubangiji yana tsare masu tawali’u; sa’ad da nake cikin tsananin bukata, ya cece ni. Ka kwantar da hankali, ya raina, gama Ubangiji mai alheri ne a gare ka. Gama kai, ya Ubangiji, ka ceci raina daga mutuwa, idanuna daga hawaye, ƙafafuna daga tuntuɓe, don in iya tafiya a gaban Ubangiji a ƙasar masu rai.
”Abu mai daraja a gaban Ubangiji shi ne mutuwar tsarkakansa.
”Bari tsarkaka su yi farin ciki a wannan bangirma su kuma rera don farin ciki a kan gadajensu.
”Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka kada kuma ka dangana ga ganewarka;
”Suna mai kyau ya fi turare mai ƙanshi, kuma ranar mutuwa ta fi ranar haihuwa.
”zai haɗiye mutuwa har abada. Ubangiji Mai Iko Duka zai share hawaye daga dukan fuskoki; zai kawar da kunyar mutanensa daga dukan duniya. Ubangiji ne ya faɗa.
”Amma matattunka za su rayu; jikunansu za su tashi. Ku da kuke zama a ƙura, ku farka ku kuma yi sowa don farin ciki. Raɓarka kamar raɓar safiya ce; duniya za tă haifi matattunta.
”kuma fansassu na Ubangiji za su komo. Za su shiga Sihiyona da rerawa; matuƙar farin ciki zai mamaye su. Murna da farin ciki za su sha kansu, baƙin ciki kuma da nishi za su gudu.
”Ku yi sowa don farin ciki, ya ku sammai; ki yi farin ciki, ya ke duniya; ku ɓarke da waƙa, ya ku duwatsu! Gama Ubangiji ya ta’azantar da mutanensa zai kuma ji tausayin mutanensa da suke shan wahala.
”Na ba da bayana ga masu dūkana, kumatuna ga masu jan gemuna; ban ɓoye fuskata daga masu ba’a da masu tofa mini miyau ba. Gama Ubangiji Mai Iko Duka zai taimake ni, ba zan sha kunya ba. Saboda haka na kafa fuskata kamar dutsen ƙanƙara, na kuma sani ba zan sha kunya ba.
”Waɗanda Ubangiji ya fansar za su dawo. Za su shiga Sihiyona da waƙoƙi; madawwamin farin ciki zai rufe kansu da rawani. Murna da farin ciki zai cika su, baƙin ciki da nishi zai ɓace.
”Mutane suka rena shi suka ƙi shi, mutum ne cike da baƙin ciki, ya kuma saba da wahala. Kamar wanda mutane suna ɓuya fuskokinsu daga gare shi aka rena shi aka yi banza da shi. Tabbatacce ya ɗauki cututtukanmu ya kuma daure da baƙin cikinmu duk da haka muka ɗauka Allah ya hukunta shi ne, ya buge shi ya kuma sa ya sha azaba. Amma aka yi masa rauni saboda laifofinmu, aka ƙuje shi saboda kurakuranmu; hukuncin da ya kawo mana salama ya kasance a kansa, kuma ta wurin mikinsa ya sa muka warke. Dukanmu, muna kama da tumakin da suka ɓata, kowannenmu ya kama hanyarsa; Ubangiji kuwa ya sa hukunci ya auko a kansa hukuncin da ya wajaba a kanmu. Aka wulaƙanta shi aka kuma yi masa azaba, duk da haka bai buɗe bakinsa ba; aka kai shi kamar ɗan rago zuwa wurin yanka, kuma kamar tunkiya a gaban masu askinta tana shiru, haka bai buɗe bakinsa ba. Da wulaƙanci da kuma hukunci aka ɗauke shi aka tafi. Wa kuwa zai yi maganar zuriyarsa? Gama an kawar da shi daga ƙasar masu rai; saboda laifin mutanena aka kashe shi. Aka yi jana’izarsa tare da mugaye, aka binne shi tare da masu arziki, ko da yake bai taɓa yin wani tashin hankali ba, ko a sami ƙarya a bakinsa. Duk da haka nufin Ubangiji ne a ƙuje shi yă kuma sa yă sha wahala, kuma ko da yake Ubangiji ya sa ransa ya zama hadaya don zunubi, zai ga zuriyarsa zai kuma kawo masa tsawon rai, nufin Ubangiji kuma zai yi nasara a hannunsa. Bayan wahalar ransa, zai ga hasken rai, ya kuma gamsu; ta wurin saninsa bawana mai adalci zai ’yantar da mutane masu yawa, zai kuma ɗauki laifofinsu. Saboda haka zan ba shi rabo tare da manya, zai kuma raba ganima tare da masu ƙarfi, domin ya ba da ransa har mutuwa, aka kuma lissafta shi tare da masu laifofi. Gama ya ɗauki zunubin mutane masu yawa, ya kuma yi roƙo saboda laifofinsu.
”Za ku fita da farin ciki a kuma bi da ku da salama; duwatsu da tuddai za su ɓarke da waƙa a gabanku, dukan itatuwan jeji kuma za su tafa hannuwansu.
”Mai adalci yakan mutu, ba kuwa wanda yakan yi tunani a zuciyarsa; an kwashe mutanen kirki, ba kuwa wanda ya fahimta cewa an kwashe masu adalci don a tsame su daga mugunta. Waɗanda suke aikata abin da yake daidai sukan shiga da salama; sukan huta yayinda suka kwanta cikin kabari.
”in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona, in maido musu rawani mai kyau a maimako na toka, man murna a maimako na makoki, da kuma rigar yabo a maimako na ruhun fid da zuciya. Za a ce da su itatuwan oak na adalci, shukin Ubangiji don bayyana darajarsa.
”Ina jin daɗi ƙwarai a cikin Ubangiji; raina yana farin ciki a cikin Allahna. Gama ya suturce ni da rigunan ceto ya yi mini ado da rigar adalci, yadda ango yakan yi wa kansa ado kamar firist kamar kuma yadda amarya takan sha ado da duwatsunta masu daraja.
”Cikin dukan damuwarsu shi ma ya damu, mala’ikan da yake gabansa ya cece su. Cikin ƙauna da jinƙai ya fanshe su; ya kuma ɗaga su ya riƙe su dukan kwanakin dā
”Amma sai ga waɗansu Yahudawa waɗanda ka ɗora su a kan harkokin yankin Babilon, wato, Shadrak, Meshak da Abednego waɗanda ba su kula da umarninka ba, ya sarki. Ba su bauta wa allolin ba balle su yi sujada ga gunkin zinariya da ka kafa.” Cikin fushi da hasala, Nebukadnezzar ya aika a kira Shadrak, Meshak da Abednego. Aka kawo waɗannan mutane a gaban sarki, sai Nebukadnezzar ya ce musu, “Gaskiya ne Shadrak, Meshak da Abednego, cewa kun ƙi ku bauta wa alloli kuka kuma ƙi yi sujada ga gunkin da na kafa? Yanzu sa’ad da kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, in kuna a shirye ku rusuna ƙasa ku yi wa wannan gunkin da na yi sujada, to, da kyau. Amma in ba ku yi sujada ba, za a je fa ku yanzu a cikin tanderun wutar nan. In ga kowane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”
”Sai Shadrak, Meshak da Abednego suka amsa wa sarki suka ce, “Ya Nebukadnezzar, ba mu bukata mu kāre kanmu a gabanka a kan wannan batu. In an jefa mu cikin tanderun wutar nan, Allahn da muke bauta wa zai iya cetonmu daga ita, kuma ya sarki, zai cece mu daga hannunka. Amma ko da bai cece mu ba, muna so ka sani, ya sarki; cewa ba za mu bauta wa allolinka ba ko kuma mu yi sujada ga gunkin zinariyar da ka kafa ba.”
”Sai Nebukadnezzar ya husata da Shadrak, Meshak da Abednego, sai al’amuransa a kansu ya canja. Sai ya umarta a ƙara zuga wutar har sau bakwai domin tă yi zafi fiye da yadda take a dā. Kuma ya umarci waɗansu ƙarfafan sojoji a cikin rundunarsa su daure Shadrak, Meshak da Abednego su jefa su cikin tanderun wutar. Waɗannan mutanen suna sanye da riguna, da wanduna, da rawani da waɗansu kayan sawa, aka daure su, aka jefa su cikin tanderun wuta. Sarki ya ba da umarnin da gaggawa kuma wutar ta yi zafi ƙwarai har harshen wutar ya kashe sojojin nan da suka ɗauki Shadrak, Meshak da Abednego, waɗannan mutane uku kuma a daure, suka fāɗa cikin tanderun wutar.
”Sai Sarki Nebukadnezzar ya miƙe tsaye, cike da mamaki ya tambayi mashawartansa, “Shin ba mutum uku ba ne muka daure muka jefa cikin wutar?” Suka amsa, “Tabbatacce haka yake ya sarki.” Sai ya ce, “Ku duba ina ganin mutum huɗu suna tafiya suna yawo a cikin wutar, a sake kuma babu abin da ya same su, na huɗun sai ka ce ɗan alloli.” Sai Nebukadnezzar ya matsa kusa da ƙofar tanderun wutar ya yi kira da ƙarfi, “Shedrak, Meshak da Abednego, bayin Allah Mafi Ɗaukaka ku fito! Ku zo nan!” Sai Shadrak, Meshak da Abednego suka fita daga cikin wutar, Sa’an nan hakimai, da wakilai, da gwamnoni da masu ba wa sarki shawara suka kewaya su. Suka ga wutar ba tă yi musu wani lahani a jikinsu ba, babu ko gashin kansu da ya ƙuna; ko warin wuta ma ba su yi ba. Sa’an nan Nebukadnezzar ya ce, “Yabo ya tabbata ga Allahn Shadrak, Meshak da Abednego wanda ya aiko da mala’ikansa ya ceci bayinsa da suka dogara matuƙa a gare shi, suka ki bin umarnin sarki kuma su na a shirye domin su ba da ransu da suka ƙi bauta ko su yi sujada ga wani allah sai dai Allahnsu.
”To, da Daniyel ya ji labarin cewa an fitar da doka, sai ya tafi gidansa a ɗakinsa na sama inda tagogin ɗakin suke duban wajen Urushalima. Sau uku yakan durƙusa yă yi addu’a yana yin godiya ga Allahnsa, kamar yadda ya saba yi. Sai waɗannan mutane suka tafi a ƙungiyance suka kuma iske Daniyel yana addu’a yana roƙon Allah yă taimake shi. Sai suka tafi wurin sarki suka yi masa magana game da dokar mulkinsa, suka ce, “Ashe, ba ka yi doka cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda aka tarar yana addu’a ga wani allah ko mutum in ba kai ba, ya sarki, za ka jefa shi a cikin ramin zakoki ba?” Sarki ya amsa ya ce, “Dokar tana nan daram bisa ga dokar Medes da Farisa, waɗanda ba a iya sokewa.” Sai suka ce wa sarki, “Daniyel ɗin nan, wanda yake ɗaya daga cikin waɗanda aka kwaso daga Yahuda, bai kula da kai ba, ya sarki, balle fa dokar da ka yi. Har yanzu yana addu’a sau uku a rana.” Da sarki ya ji haka, sai ya damu sosai, ya ƙudura yă ceci Daniyel, ya yi ta fama har fāɗuwar rana yadda zai yi yă kuɓutar da shi. Sai mutanen nan suka je wurin sarki a ƙungiyance suka ce masa, “Ka tuna, ya sarki; cewa bisa ga dokar Medes da Farisa, babu umarni ko dokar da sarki ya yi da za a iya sokewa.”
”Saboda haka sai sarki ya ba da umarni suka kuma kawo Daniyel suka jefa shi cikin ramin zakoki. Sarki ya ce wa Daniyel, “Bari Allahn nan wanda kake bauta masa kullum, yă cece ka!” Aka kawo dutsen aka rufe bakin ramin, sa’an nan sarki ya hatimce shi da zobensa da kuma zoban manyan mutanensa, don kada wani yă canja yanayin Daniyel. Sa’an nan sarki ya koma fadarsa ya kwana bai ci ba, kuma babu wata liyafar da aka kawo masa. Ya kuma kāsa barci. Gari yana wayewa, sai sarki ya tashi ya hanzarta zuwa ramin zakoki. Da ya yi kusa da ramin zakokin, sai ya kira Daniyel da muryar mai cike da damuwa ya ce, “Daniyel bawan Allah mai rai, ko Allahn nan naka wanda kake bauta wa kullum, ya iya cetonka daga zakoki?” Sai Daniyel ya amsa ya ce, “Ran sarki, yă daɗe! Allahna ya aiko da mala’ikansa, ya kuwa rufe bakunan zakoki. Ba su yi mini rauni ba, gama an same ni marar laifi ne a gabansa. Ban kuwa taɓa yin wani abu marar kyau a gabanka ba, ya sarki.” Sai sarki ya cika da murna ƙwarai, ya kuma yi umarni a ciro Daniyel daga ramin zakoki. Kuma da aka fito da Daniyel daga ramin, ba a sami wani rauni a jikinsa ba, domin ya dogara ga Allahnsa.
”Zai yi maganar saɓo a kan Mafi Ɗaukaka, zai kuma tsananta wa tsarkaka yă kuma yi ƙoƙarin sāke lokuta da shari’u. Za a miƙa tsarkaka a hannunsa na wani lokaci, lokuta da kuma rabin lokaci.
”“A wannan lokaci Mika’ilu, babban mai mulki wanda yake kāre mutanenka, zai tashi. Za a yi lokacin matsananciyar wahala wanda ba a taɓa yi tun farkon ƙasashe har zuwa yanzu. Amma a lokacin da mutanenka, kowane mutum wanda aka sami sunansa a rubuce a cikin littafin, za a cece shi. Ɗumbun mutanen da suka yi barci cikin turɓayar duniya za su farka, waɗansu zuwa ga rai madawwami, waɗansu zuwa ga madawwamiyar kunya da kuma madawwamin ƙasƙanci. Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar hasken samaniya, waɗanda kuma suka jagoranci waɗansu da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.
”Ubangiji nagari ne, mafaka kuma a lokacin wahala. Yana kula da waɗanda suka dogara gare shi,
”duk da haka zan yi farin ciki da Ubangiji, zan yi murna da Allah Mai Cetona.
”‹Masu albarka ne waɗanda ake tsananta musu don gani an yi adalci,› ‹gama mulkin sama nasu ne.› ‹“Masu albarka ne ku, sa’ad da mutane suke zaginku, suna tsananta muku, suna kuma faɗin kowace irin muguwar magana a kanku saboda ni.› ‹Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.›
”‹Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku›‹kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a,›
”‹“Kada ku yi wa kanku ajiyar dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda kuma ɓarayi sukan fasa, su yi sata.› ‹Amma ku yi wa kanku ajiyar dukiya a sama, inda ba tsatsa da asu da za su ɓata su, inda kuma ba ɓarayin da za su fasa, su yi sata.›
”‹Ku yi hankali da mutane; za su miƙa ku ga majalisa su kuma yi muku bulala a majami’unsu.› ‹Saboda ni, za a ja ku zuwa gaban gwamnoni da gaban sarakuna domin ku ba da shaida a gabansu, da kuma ga Al’ummai.› ‹Amma sa’ad da suka kama ku, kada ku damu game da abin da za ku faɗa ko kuwa yadda za ku faɗe shi. A lokacin za a ba ku abin da za ku faɗa,› ‹gama ba ku ba ne kuke magana, amma Ruhun Ubanku ne yake magana ta wurinku.›
”‹“Ɗan’uwa zai ci amanar ɗan’uwansa, a kuma kashe shi, Uba ma zai yi haka da ɗansa; ’ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su.› ‹Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya jure har ƙarshe zai sami ceto.› ‹Sa’ad da aka tsananta muku a wannan wuri, ku gudu zuwa wancan. Gaskiya nake gaya muku, kafin ku gama zazzaga dukan biranen Isra’ila, Ɗan Mutum zai zo.›
”‹Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta.›
”‹duk wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai dace yă zama nawa ba.› ‹Duk mai son adana ransa zai rasa shi, duk wanda kuwa ya rasa ransa saboda ni zai same shi.›
”‹“Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu.› ‹Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku.› ‹Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”›
”Amma Farisiyawa suka fita suka ƙulla shawara yadda za su kashe Yesu.
”‹Wanda ya karɓi irin da ya fāɗi a wuraren duwatsu kuwa, shi ne mutumin da yakan ji maganar, nan da nan kuwa yă karɓe ta da murna.› ‹Sai dai da yake ba shi da saiwa, yakan ɗan jima kaɗan kawai. Da wata wahala ko tsanani ya auko masa saboda maganar, nan da nan sai yă ja da baya.›
”‹“Mulkin sama yana kama da dukiyar da aka ɓoye a gona. Da wani ya same ta, sai yă sāke ɓoye ta, sa’an nan cikin farin cikinsa yă je yă sayar da duk abin da yake da shi yă sayi gonar.› ‹“Har wa yau dai, mulkin sama yana kama da ɗan kasuwa mai neman lu’ulu’ai masu kyau.› ‹Da ya sami dutse guda mai daraja sosai, sai ya tafi ya sayar da dukan abin da yake da shi ya saye shi.›
”sai ya ce wa fadawansa, “Wannan Yohanna Mai Baftisma ne; ya tashi daga matattu! Shi ya sa abubuwan banmamakin nan suke faruwa ta wurinsa.” To, dā Hiridus ya kama Yohanna ya daure, ya kuma sa shi cikin kurkuku saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa Filibus, gama Yohanna ya dinga ce masa, “Ba daidai ba ne ka aure ta.” Hiridus ya so yă kashe Yohanna, amma yana jin tsoron mutane, don sun ɗauka shi annabi ne. A bikin tuna da ranar haihuwar Hiridus, diyar Hiridiyas ta yi musu rawa ta kuma gamsar da Hiridus ƙwarai, har ya yi alkawari da rantsuwa cewa zai ba ta duk abin da ta roƙa. Da mahaifiyarta ta zuga ta, sai ta ce, “Ba ni a cikin kwanon nan, kan Yohanna Mai Baftisma.” Sarki ya yi baƙin ciki, amma saboda rantsuwarsa da kuma baƙinsa, sai ya ba da umarni a ba ta abin da ta roƙa ya kuma sa aka yanke kan Yohanna a kurkuku. Aka kawo kansa cikin kwano aka ba yarinyar, ita kuma ta kai wa mahaifiyarta. Almajiran Yohanna suka zo suka ɗauki gawarsa suka binne. Sa’an nan suka je suka gaya wa Yesu.
”Tun daga wannan lokaci Yesu ya fara bayyana wa almajiransa cewa dole yă tafi Urushalima yă sha wahaloli da yawa a hannun dattawa, manyan firistoci da kuma malaman dokoki, dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.
”Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, ‹“Duk mai son bina, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa, yă bi ni.› ‹Gama duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi.›
”Sai Bitrus ya amsa masa, “Ga shi mun bar kome don mu bi ka! Me za mu samu ke nan?”
”‹“Za mu haura zuwa Urushalima, za a kuma bashe Ɗan Mutum ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa› ‹za su kuma bashe shi ga Al’ummai su yi masa ba’a, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma a tashe shi!”›
”‹“Ku saurari wani misali. An yi wani mai gona wanda ya yi gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa wurin matsin inabi a ciki, ya kuma gina hasumiyar gadi. Sa’an nan ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, ya kuma yi tafiya.› ‹Da lokacin girbi ya yi kusa, sai ya aiki bayinsa wajen ’yan hayan, su karɓo masa ’ya’yan inabi.› ‹“Amma ’yan hayan suka kama bayinsa; suka dūke ɗaya, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi na ukun.› ‹Sai ya sāke aiken waɗansu bayi wurinsu, fiye da na dā yawa, amma ’yan hayan suka yi musu kamar yadda suka yi wa na farin.› ‹A ƙarshe, sai ya aiki ɗansa a wurinsu. Ya ce, ‘Za su girmama ɗana.’› ‹“Amma da ’yan hayan suka hangi ɗan, sai suka ce wa juna, ‘Wannan shi ne magājin. Ku zo, mu kashe shi, mu ci gādonsa.’› ‹Saboda haka suka kama shi, suka jefar da shi bayan katangar gonar inabin, suka kashe shi.›
”‹Saboda haka ina aika muku da annabawa, da masu hikima da malamai. Waɗansunsu za ku kashe ku kuma gicciye; waɗansu kuma za ku yi musu bulala a majami’unku kuna kuma binsu gari-gari.› ‹Ta haka alhakin jinin masu adalcin da aka zubar a duniya, tun daga jinin Habila mai adalci, zuwa jinin Zakariya ɗan Berekiya, wanda kuka kashe tsakanin haikali da bagade zai koma kanku.›
”‹“Sa’an nan za a bashe ku don a tsananta muku a kuma kashe ku, dukan al’ummai za su ƙi ku saboda ni.› ‹A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna,›
”‹amma duk wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.›
”‹Gama a lokacin za a yi wata matsananciyar wahala, wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu ba kuwa za a ƙara yi ba.› ‹“Da ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da babu wani da zai tsira, amma saboda zaɓaɓɓun nan, za a taƙaita kwanakin.›
”suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci, su kuma kashe shi.
”Bitrus ya furta, “Ko da ma zan mutu ne tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Dukan sauran almajiran ma suka faɗa haka.
”Sai manyan firistoci da ’yan majalisa duka suka yi ta neman shaidar ƙarya a kan Yesu, don su sami dama su kashe shi.
”Sai suka tottofa masa miyau a fuskarsa, suka kuma bubbuge shi da hannuwansu. Waɗansu kuma suka mammare shi
”Da wayewar gari, sai dukan manyan firistoci da dattawan mutane suka yanke shawara su kashe Yesu. Suka daure shi, suka tafi da shi, suka ba da shi ga gwamna Bilatus.
”Sai ya sakar musu Barabbas. Amma ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.
”Suka tattofa masa miyau, suka karɓe sandan, suka yi ta ƙwala masa shi a kai. Bayan sun yi masa ba’a, sai suka tuɓe masa rigar, suka sa masa nasa tufafin. Sai suka tafi da shi, domin su gicciye shi.
”Bayan da suka gicciye shi, sai suka raba tufafinsa a tsakaninsu ta wurin jefa ƙuri’a.
”‹Waɗansu suna kama da irin da aka shuka a wurare masu duwatsu, sukan ji maganar Allah, sukan kuma karɓe ta nan da nan da farin ciki.› ‹Amma da yake ba su da saiwa, ba sa daɗewa. Da wahala ko tsanani ya tashi saboda maganar, nan da nan, sai su ja da baya.›
”Sarki Hiridus ya ji wannan labari, gama sunan Yesu ya bazu a ko’ina. Waɗansu suna cewa, “An tashe Yohanna Mai Baftisma daga matattu ne, shi ya sa yana da ikon yin ayyukan banmamakin nan.” Waɗansu suka ce, “Ai, Iliya ne.” Har wa yau waɗansu suka ce, “Ai, annabi ne, kamar ɗaya daga cikin annabawan dā.” Amma da Hiridus ya ji haka, sai ya ce, “Ai, Yohanna ne, mutumin da na yanke masa kai, shi ne ya tashi daga matattu!” Gama Hiridus da kansa ya ba da umarni a kama Yohanna, ya kuma sa aka daure shi, aka sa shi a kurkuku. Ya yi haka saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa Filibus, wadda ya aura. Gama Yohanna ya yi ta ce wa Hiridus, “Ba daidai ba ne bisa ga doka, ka ɗauki matar ɗan’uwanka.” Saboda haka, Hiridiyas ta ƙulla munafunci game da Yohanna, ta kuma so ta kashe shi. Amma ba tă iya ba, domin Hiridus yana jin tsoron Yohanna, ya kuma kāre shi sosai, da sanin cewa shi mutum ne mai adalci da kuma mai tsarki. Duk sa’ad da Hiridus ya saurari Yohanna, yakan damu ƙwarai, duk da haka, yakan so yă ji shi. A ƙarshe, ta sami zarafi. A ranar murnar haihuwar Hiridus, ya yi biki domin hakimansa, da shugabannin sojojinsa, da kuma manyan mutanen Galili. Sa’ad da diyar Hiridiyas ta shigo, ta kuma yi rawa, sai ta gamshi Hiridus tare da baƙinsa. Sai Sarkin ya ce wa yarinyar, “Ki tambaye ni kome da kike so, ni kuwa zan ba ki.” Ya yi mata alkawari da rantsuwa cewa, “Duk abin da kika roƙa, zan ba ki, ko da rabin mulkina ne.” Sai ta fita ta ce wa mahaifiyarta, “Me zan roƙa?” Ta ce, “Kan Yohanna Mai Baftisma.” Nan da nan, sai yarinyar ta yi hanzari zuwa wajen sarki da roƙon, “Ina so ka ba ni kan Yohanna Mai Baftisma a cikin tasa, yanzu-yanzu nan.” Sai sarki ya yi baƙin ciki ƙwarai, amma saboda rantsuwar da kuma baƙinsa, bai so yă hana ta ba. Nan take, sai ya aiki mai aiwatar da kisa da umarni ya kawo kan Yohanna. Mutumin ya je ya yanke kan Yohanna a kurkuku. Ya kuma kawo kan a tasa ya ba yarinyar. Ita kuma ta ba wa mahaifiyarta. Da almajiran Yohanna suka sami labari, sai suka zo suka ɗauki jikinsa suka binne a kabari.
”Sai ya fara koya musu cewa, dole Ɗan Mutum yă sha wahaloli da yawa, dattawa, manyan firistoci da malaman dokoki kuma su ƙi shi. Dole kuma a kashe shi, bayan kwana uku kuma, yă tashi.
”Sai ya kira taron wurinsa tare da almajiransa ya ce, ‹“Duk wanda zai bi ni, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa yă bi ni.› ‹Domin duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, da kuma bishara, zai same shi.›
”gama yana koya wa almajiransa. Ya ce musu, ‹“Za a ci amanar Ɗan Mutum, a ba da shi ga hannun mutane. Za su kashe shi, bayan kwana uku kuma zai tashi.”›
”Ya ce, ‹“Za mu haura zuwa Urushalima, za a bashe Ɗan Mutum, ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa, a kuma ba da shi ga Al’ummai,› ‹waɗanda za su yi masa ba’a, su tofa masa miyau, su yi masa bulala, su kuma kashe shi. Bayan kwana uku kuma yă tashi.”›
”Sa’an nan ya fara yi musu magana da misalai ya ce, ‹“Wani mutum ya shuka gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa rami domin matsin inabin, ya kuma gina ɗakin gadi. Sai ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, sa’an nan ya yi tafiya.› ‹Da lokacin girbi ya yi, sai ya aiki wani bawa wajen ’yan hayan, don yă karɓo masa ’ya’yan inabin daga wurinsu.› ‹Amma suka kama shi, suka yi masa dūka, suka kore shi hannun wofi.› ‹Sai ya sāke aikan wani bawa wurinsu, amma suka bugi wannan mutum a kai, suka wulaƙanta shi.› ‹Har yanzu ya sāke aikan wani. Wannan kuwa suka kashe. Ya aika waɗansu da yawa; suka bubbuge waɗansu, sauran kuwa suka kashe.› ‹“Sauran mutum ɗaya da ya rage ya aika, ɗa, da yake ƙauna. Daga ƙarshe sai ya aike shi, yana cewa, ‘Za su girmama ɗana.’› ‹“Amma ’yan hayan suka ce wa juna, ‘Aha! Wannan shi ne magājin. Ku zo mu kashe shi, gādon kuma yă zama namu.’› ‹Sai suka kama shi suka kashe, suka jefa shi bayan gonar inabin.›
”‹“Dole ku yi zaman tsaro. Za a ba da ku ga hukuma, a kuma bulale ku a majami’u. Saboda ni kuma, za ku tsaya a gaban gwamnoni da sarakuna, domin ku ba da shaida a gabansu.› ‹Dole sai an fara yin wa’azin bishara ga dukan al’ummai.› ‹Sa’ad da aka kama ku, aka kuma kai ku don a yi muku shari’a, kada ku damu da abin da za ku faɗa. Sai dai ku faɗi abin da aka ba ku a lokacin. Gama ba ku kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne.› ‹“Ɗan’uwa zai ba da ɗan’uwa a kashe. Mahaifi zai ba da ɗansa. ’Ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su.› ‹Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.›
”To, saura kwana biyu ne kaɗai a yi Bikin Ƙetarewa da Bikin Burodi Marar Yisti, sai manyan firistoci da malaman dokoki, suka nemi wani dalili su kama Yesu a ɓoye, su kashe.
”Amma Bitrus ya yi ta nanatawa da ƙarfi ya ce, “Ko da zan mutu tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Duk sauran ma suka ce haka.
”Manyan firistoci da dukan ’yan Majalisa, suka shiga neman shaidar laifin da za a tabbatar a kan Yesu, domin su kashe shi. Amma ba su sami ko ɗaya ba.
”Kun dai ji saɓon. Me kuka gani?” Duka suka yanke masa hukuncin kisa. Sai waɗansu suka fara tattofa masa miyau, suka rufe masa idanu, suka bubbuge shi da hannuwansu, suka ce, “Yi annabci!” Masu gadin kuma suka ɗauke shi, suka yi masa duka.
”Suka yi ihu, suka ce, “A gicciye shi!” Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?” Amma suka ƙara yin ihu suna cewa, “A gicciye shi!” Don son yă faranta wa taron rai, sai Bilatus ya sakar musu Barabbas. Ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.
”Bayan da suka gama yin masa ba’a, suka tuɓe rigar mai ruwan shunayyar, suka sa masa nasa tufafi. Sai suka tafi da shi don a gicciye shi.
”Sai suka gicciye shi. Suka rarraba tufafinsa, suka jefa ƙuri’a a kansu don su ga abin da kowa zai samu. Sa’a ta uku na safe ce kuwa aka gicciye shi.
”Da murya mai ƙarfi, Yesu ya ja numfashinsa na ƙarshe.
”ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona,
”‹Masu albarka ne sa’ad da mutane suka ƙi ku,› ‹suka ware ku, suka zage ku,› ‹suna ce da ku mugaye,› ‹saboda Ɗan Mutum.› ‹“Ku yi farin ciki a wannan rana, ku kuma yi tsalle don murna, saboda ladarku yana da yawa a sama. Gama haka kakanninsu suka yi wa annabawa.›
”‹“Amma ina faɗa muku, ku da kuke ji na, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku yi wa masu ƙinku alheri.› ‹Ku albarkaci waɗanda suke la’anta ku, ku kuma yi wa waɗanda suke wulaƙanta ku addu’a.›
”‹Amma, ku ƙaunaci abokan gābanku, ku kuma yi musu alheri, ku ba su bashi, ba da sa zuciya sai an biya ku ba. Ta yin haka ne kawai, za ku sami lada mai yawa, ku kuma zama ’ya’yan Mafi Ɗaukaka, gama shi mai alheri ne ga marasa godiya da mugaye.›
”Yanzu fa, Hiridus mai sarauta ya ji labarin dukan abubuwan da suke faruwa. Sai ya rikice, don waɗansu mutane suna cewa, Yohanna Mai Baftisma ne ya tashi daga matattu, waɗansu kuma suna cewa, annabi Iliya ne ya sāke bayyana. Waɗansu kuma har wa yau, suna cewa, ɗaya daga cikin annabawa na dā ne, ya tashi. Amma Hiridus ya ce, “Yohanna dai na yanke kansa, amma wanne mutum ne nake jin labarin abubuwan nan a kansa?” Sai ya yi ƙoƙari ya ga Yesu.
”Ya sāke cewa, ‹“Dole ne Ɗan mutum ya sha wahaloli da yawa, dattawa, da manyan firistoci, da malaman dokoki kuma su ƙi shi, kuma dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a tā da shi da rai.”›
”Sai ya ce wa dukansu, ‹“In wani zai bi ni, dole yă mūsanta kansa, ya ɗauki gicciyensa kowace rana, ya bi ni.› ‹Gama duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni zai same shi.›
”‹“Kaitonku, domin kun gina kaburbura saboda annabawa, nan kuwa kakannin-kakanninku ne suka kashe su.› ‹Wannan ya shaida cewa kun amince da abin da kakannin-kakanninku suka yi. Sun karkashe annabawa, ku kuma kun gina kaburburansu.› ‹Saboda haka, Allah a cikin hikimarsa ya ce, ‘Zan aika musu da annabawa da manzanni. Za su kashe waɗansu, su kuma tsananta wa waɗansu.’› ‹Saboda haka, alhakin jinin dukan annabawa da aka kashe, tun farkon duniya, yana kan wannan zamani,› ‹wato, tun daga jinin Habila, har zuwa jinin Zakariya, wanda aka kashe tsakanin bagade da mazauni. I, ina gaya muku, alhakinsu duka yana kan wannan zamani.›
”‹“Ina dai gaya muku abokaina, kada ku ji tsoron masu kashe jiki, amma bayan haka, ba sauran abin da za su iya yi.› ‹Amma zan nuna muku wanda za ku ji tsoronsa. Ku ji tsoron wanda, bayan da ya kashe jikin, yana da iko ya jefa ku cikin jahannama ta wuta. I, ina gaya muku, ku ji tsoronsa.›
”‹“Ya ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, gama ya gamshi Ubanku ya ba ku mulkin.› ‹Ku sayar da dukiyarku, ku ba wa matalauta. Ku yi wa kanku jakar kuɗin da ba za su lalace ba. Ku yi wa kanku ajiyar dukiyar da ba za tă kare ba a sama, inda ɓarawo ba zai yi kusa ba, asu kuma ba za su iya su lalatar ba.›
”‹“Duk wanda yakan zo wurina, amma bai ƙi mahaifinsa da mahaifiyarsa, da matarsa da ’ya’yansa, da ’yan’uwansa mata da maza, kai, har ma ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba.› ‹Kuma duk wanda ba yakan ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, ba zai iya zama almajirina ba.›
”‹Haka nan fa, kowane ne a cikinku, da ba ya rabu da abin da yake da shi ba, ba zai iya zama almajirina ba.›
”‹Duk wanda yake so ya ceci ransa, zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa, zai cece shi.›
”‹Za a ba da shi ga Al’ummai, za su yi masa ba’a, su zage shi, su tofa masa miyau,› ‹za su yi masa bulala, su kuma kashe shi. A rana ta uku kuma zai tashi.”›
”Sai ya ci gaba da gaya wa mutanen wannan misali ya ce, ‹“Wani mutum ya yi gonar inabi, sai ya ba da hayarta ga waɗansu manoma, sa’an nan ya yi wata doguwar tafiya.› ‹A lokacin girbi, sai ya aiki bawa zuwa wurin masu hayan, don su ba shi daga cikin ’ya’yan inabin. Amma ’yan hayan suka yi wa bawan nan dūka, suka kore shi hannu wofi.› ‹Ya sāke aikan wani bawa, shi ma suka yi masa dūka, suka kunyata shi, suka kuma kore shi hannu wofi.› ‹Har yanzu, ya sāke aikan na uku, amma suka ji masa rauni, suka jefar da shi waje.› ‹“Sai mai gonar inabin ya ce, ‘Me zan yi? Zan aiki ɗana da nake ƙauna, wataƙila za su girmama shi.’› ‹“Amma da ’yan hayan suka gan shi, sai suka tattauna zancen, suka ce, ‘Wannan shi ne magājin, mu kashe shi sa’an nan gādon zai zama namu!’› ‹Sai suka fitar da shi waje, suka kashe shi.› ‹“To, me mai gonar inabin zai yi da su?›
”‹amma su waɗanda aka ga sun cancantar kasancewa a zamanin can, da kuma na tashin matattu, ba za su yi aure, ko su ba da aure ba.› ‹Kuma ba za su sāke mutuwa ba, gama su kamar mala’iku ne. Su ’ya’yan Allah ne, tun da su ’ya’yan tashin matattu ne.›
”‹“Amma kafin duk abubuwa nan, za a kama ku a tsananta muku. Za a kai ku majami’u, da kurkuku. Za a kuma kai ku gaban sarakuna da gwamnoni, kuma dukan waɗannan saboda sunana.› ‹Wannan zai sa ku zama shaidu a gare su.› ‹Amma ku yi ƙuduri, wato, ku shirya zuciyarku, a kan ba za ku damu ba kafin lokacin, game da yadda za ku kāre kanku.› ‹Gama zan ba ku kalmomi, da hikima waɗanda ba ko ɗaya daga cikin maƙiyanku, za su iya tsayayya da ku, ko su ƙaryata.› ‹Har iyayenku, da ’yan’uwanku maza, da danginku, da abokanku ma, duk za su bashe ku, su kuma kashe waɗansunku.› ‹Duk mutane za su ƙi ku saboda ni.›
”‹Ta wurin tsayawa da ƙarfi, za ku sami rai.›
”manyan firistoci da malaman dokoki kuma suna neman yadda za su kashe Yesu a ɓoye, don suna tsoron mutane.
”‹Ku ne kuka tsaya tare da ni a gwaje-gwajen da na sha.›
”Amma ya amsa ya ce, “Ubangiji, ina a shirye in tafi tare da kai har kurkuku, ko mutuwa ma.”
”Mutanen da suke gadin Yesu suka fara masa ba’a da dūka. Suka rufe masa idanu suna tambaya cewa, “Ka yi annabci! Wa ya mare ka?”
”Amma sai suka ci gaba da ihu, suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!” Ya sāke ce musu, sau na uku, “Don me? Wane laifi wannan mutum ya yi? Ni dai ban same shi da wani dalilin da ya isa a kashe shi ba. Saboda haka, zan sa a hore shi, sa’an nan in sāke shi.” Amma suna ihu, suna nacewa, suna cewa, dole a gicciye shi, har ihunsu ya rinjaye shi.
”Da suka isa wurin da ake kira “Ƙoƙon Kai,” nan suka gicciye shi, tare da masu laifin nan, ɗaya a hannun damansa, ɗayan kuma a hagunsa. Yesu ya ce, ‹“Ya Uba ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.”› Suka rarraba tufafinsa ta wurin jefa ƙuri’a.
”Yesu ya amsa, ya ce masa, ‹“Gaskiya nake faɗa maka, yau ɗin nan, za ka kasance tare da ni, a mulkina a sama.”›
”Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, ‹“Ya Uba, na danƙa ruhuna a hannunka.”› Da ya faɗi haka, sai ya ja numfashi na ƙarshe.
”Manyan firistoci da masu mulkinmu sun ba da shi a yi masa hukuncin mutuwa, suka kuwa gicciye shi.
”‹“Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ji maganata ya kuma gaskata da wanda ya aiko ni yana da rai madawwami ba za a kuma hukunta shi ba; ya riga ya ƙetare daga mutuwa zuwa rai.› ‹Gaskiya nake gaya muku, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya zo sa’ad da matattu za su ji muryar Ɗan Allah waɗanda kuwa suka ji za su rayu.›
”‹“Kada ku yi mamakin wannan, gama lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke cikin kaburbura za su ji muryarsa› ‹su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta za su tashi zuwa ga rai, waɗanda kuma suka aikata mugunta za su tashi zuwa ga hukunci.›
”‹Amma ga burodin da ya sauko daga sama, wanda mutum zai iya ci, ba zai kuma mutu ba.› ‹Ni ne burodin rai mai saukowa daga sama. Duk wanda ya ci wannan burodi, zai rayu har abada. Wannan burodin shi ne jikina, da zan bayar don duniya ta sami rai.”›
”‹Ashe, ba Musa ba ne ya ba ku Doka? Duk da haka ba ko ɗayanku da yake kiyaye Dokar. Me ya sa kuke nema ku kashe ni?”›
”‹Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya kiyaye maganata, ba zai ɗanɗana mutuwa ba sam.”›
”‹“Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yakan ba da ransa domin tumakin.›
”‹kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uba, ina kuwa ba da raina domin tumakin.› ‹Ina da waɗansu tumaki da ba na wannan garken ba ne. Dole ne in kawo su su ma. Za su saurari muryata, za su kasance garke guda ɗaya, makiyayi guda kuma.› ‹Abin da ya sa Ubana yake ƙaunata ke nan, domin ina ba da raina, in ɗauko shi kuma.› ‹Ba mai karɓe mini rai, ina dai ba da shi. Ina da iko in ba da shi, ina da iko in ɗauko shi kuma. Wannan umarni kuwa daga wurin Ubana na karɓo shi.”›
”Yesu ya ce mata, ‹“Ni ne tashin matattu da kuma rai. Duk wanda ya gaskata da ni zai rayu, ko ya mutu;› ‹kuma duk wanda yake raye ya kuma gaskata da ni ba zai taɓa mutuwa ba. Kin gaskata wannan?”›
”Saboda haka, daga wannan rana suka ƙulla su ɗauke ransa.
”Saboda haka manyan firistoci suka ƙulla su kashe Lazarus shi ma,
”‹Gaskiya nake gaya muku, sai ƙwayar alkama ta fāɗi ƙasa ta mutu, in ba haka ba za tă kasance ƙwaya ɗaya tak. Amma in ta mutu, za tă ba da ’ya’ya da yawa.› ‹Duk mai ƙaunar ransa, zai rasa shi, duk mai ƙin ransa a wannan duniya, zai kiyaye shi har yă zuwa rai madawwami.› ‹Duk wanda zai bauta mini dole yă bi ni, inda kuma nake, a can bawana zai kasance. Ubana zai girmama wanda yake bauta mini.›
”Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, don me ba zan binka yanzu ba? Zan ba da raina saboda kai.”
”‹Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa.›
”‹“In duniya ta ƙi ku, ku san cewa ta fara ƙin na ne.› ‹Da ku na duniya ne, da ta ƙaunaci abinta. Kamar yadda yake, ku ba na duniya ba ne, na zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku.› ‹Ku tuna da kalmomin da na yi muku cewa, ‘Ba bawan da ya fi maigidansa,’›‹In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun yi biyayya da koyarwata, da za su yi biyayya da taku ma.› ‹Za su yi muku haka saboda sunana, gama ba su san Wannan da ya aiko ni ba.›
”‹Za su kore ku daga majami’a; lalle, lokaci yana zuwa da duk wanda ya kashe ku, zai ɗauka yana yin wa Allah hidima ne.› ‹Za su yi waɗannan abubuwa ne domin ba su san Uba ko ni ba.› ‹Na faɗa muku wannan, domin in lokacin ya yi, ku tuna na gargaɗe ku. Ban faɗa muku wannan tun da fari ba domin ina tare da ku.›
”‹Haka ku ma, yanzu ne lokacin baƙin cikinku, amma zan sāke ganinku za ku kuma yi farin ciki, ba kuwa wanda zai ɗauke muku farin cikinku.›
”‹“Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”›
”‹Na gaya musu maganarka duniya kuwa ta ƙi su, don su ba na duniya ba ne yadda ni ma ba na duniya ba ne.›
”Sa’an nan Bilatus ya tafi da Yesu ya kuma sa aka yi masa bulala. Sai sojojin suka tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa a kā, suka kuma yafa masa wata riga mai ruwan shunayya. Suka yi ta zuwa wurinsa suna cewa, “Ranka yă daɗe, sarkin Yahudawa!” Suna ta marinsa a fuska.
”Nan da nan da manyan firistoci da ma’aikatansu suka gan shi, sai suka yi ihu suka ce, “A gicciye! A gicciye!” Amma Bilatus ya amsa ya ce, “Ku, ku ɗauke shi ku gicciye. Ni dai ban same shi da wani abin zargi ba.”
”Yesu ya amsa ya ce, ‹“Ba ka da wani iko a kaina, in ba a ba ka daga sama ba. Saboda haka wanda ya bashe ni gare ka, ya fi na zunubi.”›
”Amma suka yi ihu suka ce, “A yi da shi! A yi da shi! A gicciye shi!” Bilatus ya ce, “A! In gicciye sarkinku?” Sai manyan firistoci suka amsa suka ce, “Mu dai, ba mu da wani sarki sai Kaisar.” A ƙarshe Bilatus ya ba da shi gare su a gicciye shi. Ɗauke da gicciyensa, ya kuwa fita zuwa wurin Ƙoƙon Kai (wanda a harshen Arameya ana ce da shi Golgota). Nan suka gicciye shi tare da waɗansu mutum biyu, ɗaya a kowane gefe da Yesu a tsakiya.
”Da ya tsotsi abin sha ɗin, sai Yesu ya ce, ‹“An gama.”› Da wannan fa, ya sunkuyar da kansa ya saki ruhunsa.
”‹Gaskiya nake faɗa maka, sa’ad da kake saurayi kakan yi wa kanka sutura ka tafi inda ka so; amma sa’ad da ka tsufa za ka miƙa hannuwanka, wani dabam yă yi maka sutura yă kai ka inda ba ka so.”› Yesu ya faɗi wannan ne, don yă nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi yă ɗaukaka Allah. Sa’an nan ya ce masa, ‹“Bi ni!”›
”Yesu ya amsa ya ce, ‹“Idan na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki? Kai dai bi ni.”› Saboda wannan, jita-jita ta bazu a cikin ’yan’uwa cewa wannan almajirin ba zai mutu ba. Amma fa Yesu bai ce ba zai mutu ba; shi dai ya ce, ‹“In na so yă kasance da rai har in dawo, mene ne naka a ciki?”›
”An ba da wannan mutum gare ku bisa ga nufin Allah da kuma rigyasaninsa, ku kuma tare da taimakon mugayen mutane, kuka kashe shi ta wurin kafa shi a kan gicciye. Amma Allah ya tashe shi daga matattu, ya ’yantar da shi daga azabar mutuwa, don ba ya yiwuwa mutuwa ta riƙe shi.
”Suka kama manzannin suka sa su a kurkukun da ake sa kowa da kowa.
”Da suka ji haka, sai suka yi fushi suka so su kashe su.
”Jawabinsa ya rinjaye su. Suka kira manzannin suka sa aka yi musu bulala. Sa’an nan suka kwaɓe su kada su ƙara magana a cikin sunan Yesu, suka kuma bar su suka tafi. Manzannin suka bar Majalisar, suna farin ciki domin an ga sun cancanta a kunyata su saboda Sunan nan.
”“Ku mutane masu taurinkai, da zukata da kuma kunnuwa marasa kaciya! Kuna kama da kakanninku. Kullum kuna tsayayya da Ruhu Mai Tsarki! An yi wani annabin da kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun ma kashe waɗanda suka yi maganar zuwan Mai Adalcin nan. Yanzu kuwa kun bashe shi kuka kuma kashe shi ku da kuka karɓi dokar da aka sa a aiki ta wurin mala’iku amma ba ku yi biyayya da ita ba.” Da membobin Sanhedrin suka ji haka, sai suka yi fushi suka ciji haƙoransu. Amma Istifanus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya dubi sama ya kuma ga ɗaukakar Allah, da Yesu kuma tsaye a hannun dama na Allah. Ya ce, “Ga shi, na ga sama a buɗe da kuma Ɗan Mutum tsaye a hannun dama na Allah.”
”Da jin haka sai suka tattoshe kunnuwansu, suka kuma yi ihu da ƙarfi sosai, suka aukar masa gaba ɗaya. Suka ja shi zuwa bayan birnin suka kuma yi ta jifansa da duwatsu. Ana cikin haka, shaidun suka ajiye tufafinsu a wurin wani saurayi mai suna Shawulu. Yayinda suke cikin jifansa, sai Istifanus ya yi addu’a ya ce, “Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.” Sa’an nan ya durƙusa ya ɗaga murya ya ce, “Ubangiji, kada ka riƙe wannan zunubi a kansu.” Da ya faɗi haka, sai ya yi barci.
”Shawulu kuwa yana can, yana tabbatar da mutuwarsa. Mutane masu tsoron Allah suka binne Istifanus suka kuma yi makoki ƙwarai dominsa. Amma Shawulu ya fara hallaka ikkilisiya. Yana shiga gida-gida, yana jan maza da mata yana jefa su cikin kurkuku.
”Bābān yana karanta wannan Nassin, “An ja shi kamar tunkiya zuwa mayanka, kuma kamar ɗan rago a hannun mai askin gashinsa yake shiru, haka kuwa bai buɗe bakinsa ba. A cikin wulaƙacinsa aka hana masa gaskiya. Wa zai iya yin zancen zuriyarsa? Gama an ɗauke ransa daga duniya.”
”Ana cikin haka, Shawulu ya ɗage yana barazana yin kisa da tsananta wa almajiran Ubangiji. Sai ya je wurin babban firist ya roƙe shi ya ba shi wasiƙu zuwa majami’un Damaskus, don in ya sami wani a wurin wanda yake bin wannan Hanya, ko maza ko mata, yă kama su a matsayin ’yan kurkuku yă kai Urushalima. Da ya yi kusa da Damaskus a kan hanyarsa, ba zato ba tsammani sai wani haske daga sama ya haskaka kewaye da shi. Sai ya fāɗi a ƙasa ya kuma ji wata murya ta ce masa, ‹“Shawulu, Shawulu, don me kake tsananta mini?”› Shawulu ya yi tambaya ya ce, “Wane ne kai, ya Ubangiji?” Ya amsa ya ce, ‹“Ni ne Yesu wanda kake tsananta wa.›
”Bayan kwanaki masu yawa, sai Yahudawa suka haɗa baki su kashe shi, amma Shawulu ya sami labarin shirinsu. Dare da rana suka yi fakonsa a ƙofofin birnin don su kashe shi.
”Ya yi magana ya kuma yi muhawwara da Yahudawa masu jin Hellenanci, amma suka yi ƙoƙarin kashe shi.
”Kusan a wannan lokaci ne Sarki Hiridus ya kama waɗansu da suke na ikkilisiya, da niyya ya tsananta musu. Ya sa aka kashe Yaƙub, ɗan’uwan Yohanna, da takobi. Sa’ad da ya ga wannan ya faranta wa Yahudawa rai, sai ya kama Bitrus shi ma. Wannan ya faru kwanakin Bikin Burodi Marar Yisti. Bayan ya kama shi, sai ya sa shi a kurkuku, ya danƙa shi a hannun soja hurhuɗu kashi huɗu, don su yi gadinsa. Hiridus ya yi niyyar ya yi masa shari’a a gaban mutane bayan Bikin Ƙetarewa.
”Yahudawa da Al’ummai tare da shugabanninsu suka ƙulla shawara a tsakaninsu, domin su wulaƙanta su su kuma jajjefe su da duwatsu. Amma suka sami labari suka kuma gudu zuwa biranen Ikoniyum na Listira da Derbe da kuma ƙauyukan kewaye,
”suna gina almajirai suna kuma ƙarfafa su su tsaya da gaske cikin bangaskiya. Suka ce, “Sai da shan wahaloli masu yawa za mu shiga mulkin Allah.”
”mutanen da suka sa rayukansu cikin hatsari saboda sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi.
”Sai taron suka fāɗa wa Bulus da Sila gaba ɗaya, alƙalan kuwa suka yi umarni a tuɓe su a kuma yi musu dūka. Bayan an yi musu bulala sosai, sai aka jefa su cikin kurkuku, aka umarci mai gadin kurkukun yă tsare su da kyau. Da karɓan irin umarnan nan, sai ya sa su can cikin ɗakin kurkuku na ciki-ciki, kuma ya ɗaura ƙafafunsu a turu.
”Daga mutum ɗaya, ya halicci kowace al’ummar mutane, don su zauna a duk duniya; shi ne kuma ya ƙaddara lokuta bisa ga tsarinsu da kuma inda za su kasance. Allah ya yi wannan domin mutane su neme shi mai yiwuwa kuma su lalluba su same shi, ko da yake ba shi da nisa daga kowannenmu. ‘Gama a cikinsa ne muke rayuwa muke motsi muka kuma kasance.’ Yadda waɗansu mawaƙanku suka ce, ‘Mu zuriyarsa ce.’
”“Yanzu kuma Ruhu ya tilasta ni, za ni Urushalima, ba tare da sanin abin da zai faru da ni a can ba. Na dai san cewa a kowace birni Ruhu Mai Tsarki yakan gargaɗe ni cewa kurkuku da shan wuya suna jirana. Amma ni ban ɗauki raina a bakin kome ba, in dai zan iya gama tserena in kuma kammala aikin da Ubangiji Yesu ya ba ni aikin shaida bisharar alherin Allah.
”Sai Bulus ya amsa ya ce, “Don me kuke kuka kuna kuma ɓata mini zuciya? A shirye nake ba ma a daure ni kawai ba, amma har ma in mutu a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.” Da dai ya ƙi rarrasuwa, muka yi shiru, muka ce, “Bari Ubangiji yă yi nufinsa.”
”Yayinda suke ƙoƙari su kashe shi, sai labari ya kai ga shugaban ƙungiyar sojan Roma cewa birnin Urushalima duk ta hargitse.
”Na tsananta wa masu bin wannan Hanyar har ga mutuwarsu, ina kama maza da mata ina kuma jefa su cikin kurkuku, kamar yadda babban firist da dukan Majalisa za su iya shaida. Na ma karɓi wasiƙu daga gare su zuwa ga ’yan’uwansu a Damaskus, na kuma tafi can don in kawo waɗannan mutane a daure zuwa Urushalima don a hukunta su.
”“Na amsa na ce, ‘Ubangiji, waɗannan mutane sun san cewa na bi majami’a-majami’a na jefa waɗanda suka gaskata da kai a cikin kurkuku, in kuma yin musu dūka. Sa’ad da kuma aka zub da jinin Istifanus mashaidinka, na tsaya can ina ba da goyon bayana ina kuma tsaron tufafin masu kisansa.’
”Kashegari, Yahudawa suka ƙulla makirci suka kuma yi rantsuwa cewa ba za su ci ko sha ba sai sun kashe Bulus. Fiye da mutane arba’in ne suka ƙulla wannan makirci. Suka je wajen manyan firistoci da dattawa suka ce, “Mun yi babbar rantsuwa cewa ba za mu ci kome ba sai mun kashe Bulus. Saboda haka, sai ku da Majalisa sai ku roƙi shugaban ƙungiyar sojan yă kawo shi a gabanku kamar kuna so ku ƙara samun cikakken bayani game da zancensa. Mu kuwa muna a shirye mu kashe shi kafin yă iso nan.”
”“Ni ma a dā na tabbata cewa ya kamata in yi duk abin da zan iya yi domin in yi gāba da sunan Yesu Banazare. Abin da na yi ke nan a Urushalima. Da izinin manyan firistoci na sa tsarkaka da yawa a kurkuku, sa’ad da kuma ake kashe su, nakan ka da ƙuri’ata gāba da su. Sau da dama nakan bi majami’a-majami’a, in sa a yi musu hukunci. Na kuma yi ƙoƙarin tilasta su su yi saɓo. Don kuma tsananin fushi da su, sai da na fafare su har waɗansu garuruwa na ƙetaren iyaka, ina tsananta musu.
”Shi ya sa Yahudawa suka kama ni a filin haikali suka kuma yi ƙoƙarin kashe ni.
”Ga waɗanda ta wurin naciya suna yin nagarta suna neman ɗaukaka, girma da rashin mutuwa, su za a ba su rai madawwami.
”Ba haka kawai ba, amma muna kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri;
”Kun ga, a daidai lokaci, yayinda muke marasa ƙarfi, Kiristi ya mutu saboda waɗanda ba su san Allah ba. Da ƙyar wani yă mutu saboda mai adalci, ko da yake saboda mutumin kirki wani zai iya ƙarfin hali yă mutu. Amma Allah ya nuna mana ƙaunarsa a wannan. Tun muna masu zunubi tukuna, Kiristi ya mutu dominmu. Da yake yanzu mun sami zama marasa laifi ta wurin jininsa, ashe kuwa za a cece mu daga fushin Allah ta wurinsa! Gama in kuwa, sa’ad da muke abokan gāban Allah, aka sulhunta mu da shi ta wurin mutuwar Ɗansa, ashe, da yake an sulhunta mu, za mu sami ceto ta wurin ransa!
”Ko ba ku sani ba cewa dukanmu da aka yi wa baftisma a cikin Kiristi Yesu an yi mana baftismar ne zuwa cikin mutuwarsa? Saboda haka, an binne mu da shi ke nan, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa, domin kamar yadda aka tā da Kiristi daga matattu ta wurin ɗaukakar Uba, haka mu ma mu yi zaman sabuwar rayuwa. In kuwa mun zama ɗaya tare da shi haka a cikin mutuwarsa, tabbatacce mu ma za mu zama ɗaya tare da shi cikin tashinsa daga matattu. Gama mun san cewa an gicciye halayenmu na dā tare da shi domin a kawar da jikin nan mai zunubi don kada mu ƙara zama bayi ga zunubi domin duk wanda ya mutu an ’yantar da shi daga zunubi ke nan.
”To, in mun mutu tare da Kiristi, mun gaskata cewa za mu rayu tare da shi kuma. Gama mun san cewa da yake an tā da Kiristi daga matattu, ba zai sāke mutuwa ba; mutuwa ba ta da sauran iko a kansa. Mutuwar da ya yi, ya mutu ne sau ɗaya tak, saboda yă shafe zunubi, amma rayuwar da yake yi, yana yi ne cikin tarayya da Allah. Haka ku ma, ku ɗauke kanku matattu ne ga ikon zunubi amma rayayyu cikin tarayya da Allah cikin Kiristi Yesu.
”Gama in kuna rayuwa bisa ga mutuntaka, za ku mutu; amma in ta wurin Ruhu kuka kashe ayyukan jikin nan, za ku rayu. Domin waɗanda Ruhun Allah yake bi da su ne ’ya’yan Allah.
”In kuwa mu ’ya’ya ne, to, mu magāda ne, magādan Allah da kuma abokan gādo tare da Kiristi, in kuwa muna tarayya a cikin shan wuyarsa to, za mu yi tarayya a cikin ɗaukakarsa. A ganina, wuyar da muke sha a wannan lokaci ba su isa a kwatanta da ɗaukakar da za a bayyana a cikinmu ba.
”Mun san cewa dukan halitta tana nishi sai ka ce mace mai naƙuda har yă zuwa wannan lokaci. Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu ’ya’yan riƙo na Allah, fansar jikunanmu.
”Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa, yana waɗanda aka kira bisa ga nufinsa. Gama waɗanda Allah ya rigyasani ya kuma ƙaddara su dace da kamannin Ɗansa, don yă zama ɗan fari cikin ’yan’uwa masu yawa. Waɗanda kuwa ya ƙaddara, su ne ya kira; waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar; waɗanda ya kuɓutar kuwa, su ne ya ɗaukaka.
”Me za mu ce ke nan game da wannan abu? In Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu? Shi da bai hana Ɗansa ba, sai ma ya ba da shi saboda mu duka, ashe, ba zai kuma ba mu, tare da shi, dukan abubuwa cikin alherinsa ba?
”Wane ne zai raba mu da ƙaunar Kiristi? Masifa ce ko wahala ko tsanani ko yunwa ko tsiraici ko hatsari ko takobi? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Saboda kai ne muke fuskantar mutuwa dukan yini; an ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.” A’a, cikin dukan waɗannan abubuwa mun ma fi masu nasara ta wurin shi wanda ya ƙaunace mu. Gama na tabbata cewa ko mutuwa ko rai, ko mala’iku ko aljanu, ko abubuwa na yanzu ko abubuwa masu zuwa nan gaba, ko ikoki, ko tsayi ko zurfi, ko wani abu dabam cikin dukan halitta da zai iya raba mu da ƙaunar Allah wadda take cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
”“Ya Ubangiji, sun karkashe annabawanka suka kuma rurrushe bagadanka; ni kaɗai na ragu, suna kuma neman raina”? Wace amsa ce Allah ya ba shi? “Na keɓe wa kaina dubu bakwai waɗanda ba su yi wa Ba’al sujada ba.” Haka ma, a wannan zamani akwai ragowar da aka zaɓa ta wurin alheri.
”Saboda haka, ina roƙonku, ’yan’uwa, saboda yawan jinƙan Allah, ku miƙa jikunanku hadaya wadda take mai rai, mai tsarki abin karɓa kuma ga Allah, wannan ita ce hanyar hidimarku ta ruhaniya. Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.
”Ku yi farin ciki cikin bege, haƙuri cikin shan wuya, aminci cikin addu’a. Ku taimaki mutanen Allah masu bukata. Ku zama masu karɓan baƙi. Ku sa wa masu tsananta muku albarka; ku sa albarka kada fa ku la’anta.
”Ku yi iya ƙoƙarinku, in zai yiwu, ku yi zaman lafiya da kowa. Kada ku yi ramuwa, abokaina, sai dai ku bar wa Allah. Gama a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce; zan kuwa sāka,” in ji Ubangiji. A maimakon haka, “In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ciyar da shi; in yana jin ƙishirwa, ka ba shi ruwan sha. Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta a kansa.”
”Dole kowa yă yi biyayya ga masu mulki, gama babu wani iko sai ko in Allah ya yarda. Duk hukumomin da muke su, naɗin Allah ne. Saboda haka, duk wanda ya yi tawaye ga hukuma yana yin tawaye da abin da Allah ya naɗa ne, waɗanda kuwa suke aikata haka, za su jawo wa kansu hukunci. Gama masu mulki ba abin tsoro ba ne ga waɗanda suke yin abin da yake daidai, sai dai ga waɗanda suke aikata laifi. Kana so ka rabu da jin tsoron wanda yake mulki? To, sai ka aikata abin da yake daidai, zai kuwa yabe ka. Gama shi bawan Allah ne don kyautata rayuwarka. Amma in ka aikata mugunta, to, sai ka ji tsoro, don ba a banza ne shugaba yake ɗaukan takobinsa ba. Shi fa bawan Allah ne, ta wurinsa ne fushin Allah yakan hukunta masu laifi.
”In muna rayuwa, muna rayuwa ne ga Ubangiji; in kuma muna mutuwa, muna mutuwa ne ga Ubangiji. Saboda haka, ko muna a raye ko muna a mace, mu na Ubangiji ne. Saboda wannan ne Kiristi ya mutu, ya kuma sāke rayuwa domin yă zama Ubangiji na matattu da na masu rai.
”A’a, muna magana ne a kan asirin hikimar Allah, hikimar da tun dā, take a ɓoye, wadda Allah ya ƙaddara domin ɗaukakarmu, tun kafin farkon zamanai. Ba ko ɗaya daga cikin masu mulkin wannan zamani da ya fahimce ta, gama da a ce sun fahimce ta, da ba su gicciye Ubangiji mai ɗaukaka ba. Duk da haka, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ba idon da ya taɓa gani, ba kunnen da ya taɓa ji, ba kuma zuciyar da ta taɓa tunanin abin da Allah ya shirya wa masu ƙaunarsa.”
”Ashe, ba ku sani ba cewa ku kanku haikalin Allah ne, Ruhun Allah kuma yana zaune a cikinku?
”Gama a ganina fa, Allah ya baje mu manzanni a ƙarshen jerin gwanon, a matsayin mutanen da aka hukunta ga mutuwa a filin wasanni. Mun zama abin kallo ga dukan duniya, ga mala’iku da kuma mutane.
”Har yă zuwa wannan sa’a, yunwa da ƙishirwa muke ciki, muna sanye da tsummoki, ana wulaƙanta mu, ba mu kuma da gida. Muna aiki da gaske da hannuwanmu. In aka la’anta mu, mukan sa albarka. In aka tsananta mana, mukan jimre; in aka ɓata mana suna, mukan mayar da alheri. Har yă zuwa wannan lokaci, mu ne kamar jujin duniya, abin ƙyamar kowa.
”Ba ku san cewa jikin nan naku haikalin Ruhu Mai Tsarki ba ne wanda yake cikinku yake kuma daga Allah? Ku ba na kanku ba ne; saye ku fa aka yi da tsada, saboda haka, sai ku girmama Allah da jikinku.
”Gama a duk sa’ad da kuke cin wannan burodi, kuke kuma sha daga wannan kwaf, kuna shelar mutuwar Ubangiji ne har yă dawo.
”In na ba wa matalauta dukan abin da nake da shi, na kuma miƙa jikina a ƙone, amma ba ni da ƙauna, ban yi riban kome ba. Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai. Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya. Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta, sai dai ta ji daɗin gaskiya. Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum.
”Amma tabbatacce, an tā da Kiristi daga matattu, nunan fari kuwa cikin waɗanda suka yi barci.
”Abokin gāba na ƙarshen da za a hallaka kuwa, shi ne mutuwa.
”Ina fuskantar mutuwa kowace rana. I, kamar yadda yake tabbatacce cewa ina taƙama da ku cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.
”Kai, marar azanci! Abin da kuka shuka ba zai tsira ba sai ya mutu.
”Haka ne tashin matattu zai kasance. Abin da aka shuka yakan ruɓe, abin da aka tā da shi kuma ba ya ruɓewa; akan shuka shi cikin ƙasƙanci, a kuma tā da shi cikin ɗaukaka, akan shuka shi da rashin ƙarfi, a kuma tā da shi da ƙarfi; akan shuka shi da jiki na mutuntaka, a kuma tā da shi da jikin ruhaniya. In akwai jiki na mutuntaka, to, lalle akwai jikin ruhaniya ma.
”Gama dole mai ruɓa yă maye wa mai ruɓan nan, marar mutuwa kuma yă maye wa mai mutuwan nan. Sa’ad da mai ruɓan nan ya maye marar ruɓan nan, mai mutuwa kuma ya maye marar mutuwan nan, sa’an nan ne karin maganar da yake a rubuce zai zama gaskiya cewa, “An haɗiye mutuwa cikin nasara.” “Ya ke mutuwa, ina nasararki? Ya ke mutuwa, ina dafinki?”
”Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya, wanda yakan yi mana ta’aziyya a cikin dukan wahalolinmu, domin mu kuma mu iya ta’azantar da waɗanda suke cikin kowace irin wahala, da ta’aziyyar da mu kanmu muka samu daga Allah. Gama kamar yadda wahalar Kiristi ta cika har tana zuba a cikin rayuwarmu, haka nan kuma ta wurin Kiristi ta’aziyyarmu ta cika har tana zuba. In muna shan wahala, ai, muna shanta domin ta’aziyyarku, da cetonku ne, in mun sami ta’aziyya, ai, mun same ta domin ta’aziyyarku ce, wadda take sa ku jure wa irin wahalan nan, da muke sha. Begen da muke da shi dominku kuwa, tabbatacce ne, domin mun san cewa kamar yadda kuke tarayya da mu a cikin wahalolinmu, haka kuma kuke tarayya da mu a cikin ta’aziyyarmu.
”’Yan’uwa, ba ma so ku zama da rashin sani, a kan wahalolin da muka sha a lardin Asiya. Mun sha wahaloli sosai, har abin ya fi ƙarfinmu, ya sa muka fid da tsammanin rayuwa. Ba shakka, a zuciyarmu mun ji kamar hukuncin kisa ne aka yi mana. Wannan kuwa ya faru ne domin kada mu dogara da kanmu, sai dai ga Allah, wanda yake tā da matattu. Shi ya cece mu daga irin wannan hatsari na mutuwa, zai kuwa cece mu. A kansa muka kafa bege cewa zai ci gaba da cetonmu,
”Amma muna da wannan dukiya a cikin tulunan yumɓu, don a nuna wannan mafificin ikon nan daga Allah ne, ba daga gare mu ba. A matse muke a kowane gefe, sai dai ba a gurgunta mu ba. An rikitar da mu, amma ba mu fid da zuciya ba. An tsananta mana, amma ba a yashe mu ba, an fyaɗe mu da ƙasa, amma ba a hallaka mu ba. Kullum muna ɗauke da mutuwar Yesu a jikinmu, domin ran Yesu yă bayyana a jikinmu. Muddin muna a raye, kullum zaman mutuwa muke yi saboda Yesu, don a bayyana ran Yesu ta wurin jikin nan namu mai mutuwa. Ta haka, mutuwa tana aiki a cikinmu, ku kuwa rai a cikinku.
”Saboda haka, ba mu fid da zuciya ba. Ko da yake a waje, jikinmu mai mutuwa yana lalacewa, amma can ciki, ana sabunta mu kowace rana. Don wannan ’yar wahalar tamu mai saurin wucewa, ita take tanadar mana madawwamiyar ɗaukaka mai yawa, fiye da kwatanci. Domin ba abubuwan da ido yake gani ne muke dubawa ba, sai dai marasa ganuwa. Gama abubuwan da ake gani masu saurin wucewa ne, marasa ganuwa kuwa, madawwama ne.
”Yanzu mun san cewa in an hallaka tentin duniyan nan da muke ciki, muna da wani gini daga Allah, madawwamin gida a sama, wanda ba da hannuwan mutum ne suka gina shi ba. Kafin nan muna nishi, da marmari a yi mana sutura da gidanmu na sama, don sa’ad da aka yi mana sutura, ba za a same mu tsirara ba. Sa’ad da muke zaune a cikin jikin nan na duniya, nishi muke domin matsuwar da muke sha, ba domin muna so mu rabu da jikinmu na wannan duniya ba ne, sai dai don so muke yi a suturta mu da na Sama, domin mai rai ya shafe mai mutuwa. Allah ne ya yi mu domin wannan, ya kuma ba mu Ruhu a matsayin abin ajiya, yana kuma tabbatar da abin da zai zo nan gaba.
”Saboda haka, kullum muna da tabbaci mun kuma san cewa, muddin muna a duniya cikin jikin nan, ana raba mu da Ubangiji. Rayuwa bangaskiya muke, ba ta ganin ido ba. Ina cewa muna da tabbaci, za mu fi so mu rabu da jikin nan, mu kuma kasance a sama tare da Ubangiji. Saboda haka, niyyarmu ita ce, mu gamshe shi, ko muna a duniya cikin jikin nan, ko ba mu nan.
”Ƙaunar Kiristi a gare mu, ita take mallakarmu, saboda haka mun tabbata, da yake wani ya mutu saboda dukan mutane, ashe kuwa, mutuwarsu ce dukansu. Ya kuwa mutu ne saboda dukan mutane, domin kada waɗanda suke rayuwa kada su yi zaman ganin dama a nan gaba, sai dai su yi zaman wannan da ya mutu saboda su, aka kuma tashe shi saboda su.
”Saboda haka, daga yanzu zuwa nan gaba, ba mu ƙara ɗaukan wani mutum bisa ga ganin duniya ba. Ko da yake a dā, mun ɗauki Kiristi haka, amma yanzu mun daina yin haka. Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon al’amari ya shuɗe, sabon ya zo!
”Ba ma sa abin tuntuɓe wa kowa, domin kada hidimarmu ta zama abin zargi. A maimakon haka, duk abin da muke yi, muna yin shi ne don mu nuna cewa mu masu hidimar Allah ne. Muna yin haka cikin jimrewa, da shan wahala, da shan wuya, har da shan masifu. Da shan dūka, da shan dauri, da yawan hargitsi, da yawan fama, da rashin barci, da kuma yunwa. Da cikin tsarki, da fahimta, da haƙuri, da kirki, da cikin Ruhu Mai Tsarki, da cikin ƙauna mai gaskiya, da cikin magana mai gaskiya, da kuma cikin ikon Allah. Muna riƙe da makaman adalci dama da hagu, ta wurin ɗaukaka da ƙasƙanci, da cikin ɓata suna, da kuma cikin yabo. Cikin faɗin gaskiya, an ɗauke mu masu ƙarya, mu sanannu ne, duk da haka an ɗauke mu kamar ba a san mu ba, muna mutuwa, duk da haka a raye muke, an ba mu horo, duk da haka ba a kashe mu ba, cikin baƙin ciki, duk da haka kullum cikin murna muke. Cikin matalauta, duk da haka muna azurtar da mutane da yawa. Ba mu da kome, alhali kuwa kome namu ne.
”Ba na faɗin wannan don in sa muku laifi. Na riga na gaya muku yadda muke ƙaunarku ƙwarai cikin zukatanmu, har babu abin da zai iya raba ku da ƙaunarmu, ko a mutuwa ko a rayuwa. Na amince da ku gaya, ina kuma taƙama da ku ƙwarai. Na ƙarfafa sosai. Duk da wahalce wahalcenmu dai ina farin ciki ƙwarai da gaske.
”Gama sun sha wuya sosai saboda tsananin wahalar da suka shiga, har yawan farin cikinsu ya kai su ga yin alheri ta bayarwa ga waɗansu, ko da yake suna cikin tsananin talauci.
”In su bayin Kiristi ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! Ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan dauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri-iri. Sau biyar Yahudawa suka yi mini bulala arba’in ɗaya babu. Sau uku aka bulale ni da bulalar ƙarfe, sau ɗaya aka jajjefe ni da duwatsu, sau uku jirgin ruwa ya ragargaje ina ciki, na kwana na kuma yini ruwan teku yana tafiya da ni. Na yi tafiye-tafiye da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin ’yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al’ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a teku, na kuma sha hatsarin ’yan’uwa na ƙarya. Na yi fama, na shan wuya, ga kuma rashin barci sau da yawa. Na san abin da ake nufin da jin yunwa da ƙishirwa, sau da yawa kuwa na kasance da rashin abinci, na sha sanyi da zaman tsirara. Ban da waɗannan abubuwa, kowace rana ina ɗauke da nauyin kula da dukan ikkilisiyoyi.
”Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni. Sau uku na roƙi Ubangiji yă raba ni da wannan abu. Amma ya ce mini, ‹“Alherina ya ishe ka, domin a cikin rashin ƙarfi ne ake ganin cikar ikona.”› Saboda haka, zan ƙara yin taƙama da farin ciki game da rashin ƙarfina, domin ikon Yesu Kiristi yă zauna tare da ni. Shi ya sa nake murna cikin rashin ƙarfi, da zagi, da shan wahaloli, da tsanantawa, da matsaloli, saboda Kiristi. Don a sa’ad da nake marar ƙarfi a nan ne nake da ƙarfi.
”Kun dai ji labarin rayuwata ta dā a cikin Yahudanci, yadda na tsananta wa ikkilisiyar Allah ƙwarai, na kuma yi ƙoƙarin hallaka ta.
”An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne nake raye ba, Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina.
”A wancan lokaci, wannan ɗa wanda aka haifa ta wurin ƙa’idar jiki ya tsananta wa wanda aka haifa ta ikon Ruhu. Haka ma yake har yanzu.
”Waɗanda suke na Kiristi Yesu, sun gicciye mutuntaka tare da abubuwan da mutum yake marmari da kuma sha’awace-sha’awacensa.
”Wanda ya yi shuki don yă gamshi mutuntakarsa, daga wannan mutuntaka zai girbi hallaka. Wanda ya yi shuki domin yă gamshi Ruhu, daga Ruhu zai girbi rai madawwami.
”Kada in taɓa yin taƙama ga kome sai dai a cikin gicciyen Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa aka gicciye duniya a gare ni, aka kuma gicciye ni ga duniya.
”Saboda haka, ni Bulus, na zama ɗan kurkuku na Kiristi Yesu saboda ku Al’ummai.
”Don haka, ina roƙonku kada ku fid da zuciya saboda abin da ake yi mini a nan. Ai, saboda ku ne nake shan wahalolin nan, wannan kuwa ɗaukakarku ce. Saboda wannan ne nake a durƙushe a gaban Uba,
”A matsayina na ɗan kurkuku saboda Ubangiji, ina roƙonku ku yi rayuwar da ta dace da kiran da aka yi muku. Kullum ku kasance masu sauƙinkai da kuma hankali; ku zama masu haƙuri, kuna jimrewa da juna cikin ƙauna.
”ku kuma yi rayuwar ƙauna, kamar yadda Kiristi ya ƙaunace mu, har ya ba da kansa dominmu a matsayin sadaka mai ƙanshi da kuma hadaya ga Allah.
”To, ina so ku sani ’yan’uwa, cewa abin da ya faru da ni ya sa cin gaban bishara. Ta haka, ya zama sananne ga dukan masu gadin fada da kuma ga kowa cewa an daure ni da sarƙoƙi saboda Kiristi. Saboda sarƙoƙina, yawancin ’yan’uwa cikin Ubangiji sun sami ƙarfafawa su yi maganar Allah gabagadi da kuma babu tsoro.
”Ina saurara da marmari da kuma bege cewa ba zan taɓa shan kunya ba, sai dai zan sami issashen ƙarfin hali yanzu kamar kullum, za a ɗaukaka Kiristi a jikina, ko ta wurin rayuwa ko kuma ta wurin mutuwa.
”Gama a gare ni, rai Kiristi ne, mutuwa kuma riba ce. In zan ci gaba da rayuwa a cikin jiki, wannan zai zama aiki mai amfani a gare ni. Duk da haka me zan zaɓa? Ban sani ba! Na rasa wanda zan zaɓa cikin biyun nan. Ina sha’awa in yi ƙaura in zauna tare da Kiristi, wannan kuwa ya fi kyau nesa ba kusa ba;
”ba tare da kun ji tsoron waɗanda suke gāba da ku ta kowace hanya ba. Wannan alama ce a gare su cewa za a hallaka su, amma a gare ku za a cece ku, wannan tabbacin kuwa daga wurin Allah ne. Gama an ba ku zarafi a madadin Kiristi cewa ba gaskatawa da shi kaɗai ba kuka yi ba, har ma ku sha wahala dominsa,
”Aka kuma same shi a kamannin mutum, ya ƙasƙantar da kansa ya kuma zama mai biyayya wadda ta kai shi har mutuwa, mutuwar ma ta gicciye!
”Amma ko da ana tsiyaye jinina kamar hadaya ta sha a kan hadaya da kuma hidimar da take fitowa daga bangaskiyarku, ina murna ina kuma farin ciki da ku duka.
”domin ya kusa yă mutu saboda aikin Kiristi, ya yi kasai da ransa don yă cikasa taimakon da ba ku iya yi mini ba.
”Gama mu ne masu kaciya, mu da muke yi sujada ta wurin Ruhun Allah, mu da muke taƙama a cikin Kiristi Yesu, mu da ba mu dogara da ayyukan da ake gani ba,
”Amma abin da dā ya zama mini riba yanzu, na ɗauka hasara ce saboda Kiristi. Me kuma ya fi, na ɗauki dukan abubuwa hasara ne in aka kwatanta da mafificiyar girman sanin Kiristi Yesu Ubangijina, wanda saboda shi ne na yi hasarar kome. Na mai da su kayan wofi, domin in sami Kiristi a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina wanda yake zuwa daga bin doka ba, sai dai adalcin da yake samuwa ta wurin bangaskiya a cikin Kiristi, adalcin da yake fitowa daga Allah da kuma yake zuwa ta wurin bangaskiya. Ina so in san Kiristi da ikon tashinsa daga matattu da kuma zumuncin tarayya cikin shan wahalarsa, in kuma zama kamar sa a cikin mutuwarsa, yadda kuma ko ta yaya, in kai ga tashin nan daga matattu.
”Amma mu ’yan mulkin sama ne. Muna kuma jira zuwan Mai Ceto daga can, Ubangiji Yesu Kiristi, shi ne mai ikon kawo dukan abubuwa ƙarƙashin mulkinsa. Ta wurin ikon nan nasa zai sāke jikin nan namu na ƙasƙanci, yă mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka.
”Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki!
”Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya. Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.
”Yanzu, ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, don ta wurin wuyan nan zan cika abin da ya rage na wuyar da Kiristi ya sha saboda jikinsa, wato, ikkilisiya.
”Da yake an tashe ku tare da Kiristi, sai ku sa zukatanku a kan abubuwan da suke sama, inda Kiristi yake zaune a hannun dama na Allah. Ku sa hankulanku a kan abubuwan sama, ba kan abubuwan duniya ba. Gama kun mutu, ranku yanzu kuwa yana ɓoye tare da Kiristi a cikin Allah. Sa’ad da Kiristi, wanda shi ne ranku, ya bayyana, ku ma za ku bayyana tare da shi cikin ɗaukaka. Saboda haka, sai ku fid da duk wani abin da yake kawo sha’awa a zukatanku, fasikanci, ƙazanta, sha’awa, muguwar sha’awa, da kuma kwaɗayi wanda shi ma bautar gumaka ne.
”Kun san cewa zai ba ku gādo a matsayin ladanku. Ubangiji Kiristi ne fa kuke bauta wa.
”Har kuka zama masu koyi da mu da kuma Ubangiji; duk da tsananin wahala, kuka karɓi saƙon nan da farin ciki wanda Ruhu Mai Tsarki ya bayar.
”waɗanda suka kashe Ubangiji Yesu da annabawa suka kuma kore mu. Ba sa yin aikin da Allah yake so, masu gāba ne kuwa da dukan mutane
”don kada kowa yă raunana ta wurin waɗannan gwaje-gwajen. Kun sani sarai cewa an ƙaddara mu don waɗannan. Gaskiyar ita ce, sa’ad da muke tare da ku, mun sha gaya muku cewa za a tsananta mana. Haka kuwa ya faru, kamar dai yadda kuka sani.
”’Yan’uwa, ba ma so ku kasance cikin jahilci game da waɗanda suka yi barci, ko kuwa ku yi baƙin ciki kamar sauran mutanen da ba su da bege. Mun gaskata cewa Yesu ya mutu ya tashi kuma daga matattu, ta haka muka gaskata cewa Allah zai kawo waɗanda suka yi barci a cikinsa tare da Yesu. Bisa ga maganar Ubangiji kansa, muna gaya muku cewa mu da muke raye har yanzu, waɗanda aka bari har dawowar Ubangiji, tabbatacce ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba.
”Ya mutu saboda mu domin, ko muna a faɗake ko muna barci, mu kasance tare da shi.
”Ku riƙa farin ciki kullum; ku ci gaba da yin addu’a; ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.
”Saboda haka, a cikin ikkilisiyoyin Allah muna taƙama game da daurewarku da kuma bangaskiyarku cikin dukan tsanani da gwaje-gwajen da kuke sha. Dukan wannan yana tabbatar cewa hukuncin Allah daidai ne, saboda haka kuma za a lissafta ku a kan kun cancanci mulkin Allah, wanda dominsa ne kuke shan wahala. Allah mai adalci ne, Zai sāka wa masu ba ku wahala da wahala yă kuma sauƙaƙa muku ku da kuke wahala, har ma da mu. Wannan zai faru sa’ad da aka bayyana Ubangiji Yesu daga sama cikin wuta mai ci tare da mala’ikunsa masu iko. Zai hukunta waɗanda ba su san Allah ba da kuma waɗanda ba su yi biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu ba. Za a hukunta su da madawwamiyar hallaka a kuma kau da su daga gaban Ubangiji da kuma daga ɗaukakar ikonsa a ranar da zai dawo don a ɗaukaka shi a cikin mutanensa masu tsarki, yă kuma zama abin banmamaki ga dukan waɗanda suka gaskata. Wannan ya haɗa har da ku, domin kun gaskata shaidar da muka yi muku.
”Ta haka za su ajiye wa kansu dukiya a matsayin tushen mai ƙarfi don tsara mai zuwa, don su riƙi rai wanda yake na tabbatacce.
”Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai. Saboda haka kada ka ji kunyar ba da shaida game da Ubangijinmu, ko kuwa ka ji kunyata, ni da nake ɗan sarƙa saboda shi. Sai dai ka haɗa kai tare da ni cikin shan wahala saboda bishara ta wurin ikon Allah, wanda ya cece mu ya kuma kira mu ga rayuwar tsarki ba saboda wani abin da muka yi ba sai dai saboda nufinsa da kuma alherinsa. An ba mu wannan alheri cikin Kiristi Yesu tun fil azal, amma yanzu an bayyana ta ta wurin bayyanuwar Mai Cetonmu, Kiristi Yesu, wanda ya hallaka mutuwa ya kuma kawo rai da rashin mutuwa a sarari ta wurin bishara.
”Shi ya sa nake shan wahalar da nake sha. Duk da haka ba na jin kunya, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata cewa yana iya kiyaye abin da na danƙa masa amana don wancan rana.
”Ka jure wa shan wahala tare da mu kamar soja mai kyau na Kiristi Yesu. Ba wanda yake aikin soja da zai sa kansa a sha’anin mutumin da ba ya aikin soja, domin yakan so yă gamshi wanda ya ɗauke shi soja.
”Ka tuna da Yesu Kiristi, wanda aka tā da shi daga matattu, zuriyar Dawuda, wanda shi ne bisharata, wadda nake shan wahala har ga daurin sarƙa kamar mai laifi. Amma Maganar Allah ba a daure take ba. Saboda haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton da yake cikin Kiristi Yesu, tare da madawwamiyar ɗaukaka. Ga wata magana tabbatacciya, “In muka mutu tare da shi, za mu rayu tare da shi; in muka jimre, za mu yi mulki tare da shi. In muka yi mūsunsa, shi ma zai yi mūsunmu;
”Kai kam, ka san kome game da koyarwata, da halina, da niyyata, bangaskiya, haƙuri, ƙauna, jimiri, tsanani, shan wahala, irin abubuwan da suka faru da ni a Antiyok, Ikoniyum da kuma Listira, tsananin da na jure. Duk da haka Ubangiji ya cece ni daga dukansu. Labudda, duk masu niyyar zaman tsarkaka, suna na Kiristi Yesu, za su sha tsanani.
”Amma kai, ka natsu cikin kowane hali, ka jure shan wahala, ka yi aikin mai bishara, ka cika dukan ayyukan hidimarka. Gama an riga an tsiyaye ni kamar hadaya ta sha, kuma lokacin tashina ya yi. Na yi fama mai kyau, na gama tseren, na riƙe bangaskiya. Yanzu kuwa an ajiye mini rawanin adalci, wanda Ubangiji, Alƙali mai adalci zai ba ni a ranan nan ba kuwa ni kaɗai ba, amma ga duk waɗanda suka yi marmarin bayyanuwarsa.
”Bulus, ɗan kurkuku saboda Kiristi Yesu, da kuma Timoti ɗan’uwanmu, Zuwa ga Filemon ƙaunataccen abokinmu da kuma abokin aikinmu,
”duk da haka ina roƙonka saboda ƙauna, na fi so in roƙe ka, ni Bulus tsoho, a yanzu kuma ga ni ɗan sarƙa saboda Kiristi Yesu.
”Sai dai muna ganin Yesu, wanda aka mai da shi ƙasa kaɗan da darajar mala’iku, yanzu kuwa an naɗa shi da ɗaukaka da girma domin yă sha wahalar mutuwa, domin ta wurin alherin Allah yă ɗanɗana mutuwa saboda kowa. Ta wurin kawo ’ya’ya masu yawa zuwa ga ɗaukaka, ya dace cewa Allah, wanda dominsa da kuma ta wurinsa ne kome yake kasancewa, ya sa tushen cetonsu yă zama cikakke ta wurin shan wahala.
”Da yake ’ya’yan suna da nama da jini, shi ma sai ya ɗauki kamanninsu na mutum domin ta wurin mutuwarsa yă hallaka wanda yake riƙe da ikon mutuwa, wato, Iblis ya kuma ’yantar da waɗanda dukan rayuwarsu tsoron mutuwa ya riƙe su cikin bauta.
”Har yanzu, akwai wani hutun Asabbacin da ya rage domin mutanen Allah; gama duk wanda ya shiga hutun Allah, shi ma yakan huta daga nasa aiki, kamar yadda Allah ya huta daga nasa. Saboda haka, bari mu yi iyakacin ƙoƙarinmu mu shiga wannan hutu, don kada wani yă kāsa ta wurin bin gurbinsu na rashin biyayya.
”A lokacin da Yesu ya yi rayuwa a duniya, ya yi addu’o’i da roƙe-roƙe tare da kuka mai zafi da kuma hawaye ga wannan wanda yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa ji shi saboda tsananin bangirman da ya yi. Ko da yake shi ɗa ne, ya yi biyayya ta wurin shan wahala kuma da aka mai da shi cikakke, sai ya zama hanyar samun madawwamin ceto ga dukan waɗanda suke masa biyayya.
”Ku tuna da kwanakin nan da suka wuce bayan kun sami haske, sa’ad da kuka tsaya daram a tsananin shan wahala. Wani lokaci a fili an tsananta muku aka kuma zage ku aka kuma tsananta muku; a wani lokaci kuma kuka tsaya tare da waɗanda aka yi musu haka. Kuka ji tausayin waɗanda suke cikin kurkuku, da farin ciki kuma kuka yarda ku rabu da dukiyar da aka ƙwace muku, domin ku kanku kun san cewa kuna da madawwamiyar dukiya mafi kyau. Saboda haka kada ku yar da tabbacinku; za a sāka muku a yalwace.
”Duk mutanen nan suna cikin bangaskiya sa’ad da suka mutu. Ba su kuwa karɓi abubuwan da aka yi alkawari ba; sun dai hango su suka kuma marabce su daga nesa. Suka kuma amince cewa su baƙi ne, bare kuma a duniya. Mutane masu faɗin irin abubuwan nan sun nuna cewa suna neman ƙasar da take tasu. Da a ce suna tunanin ƙasar da suka bari a baya, da sun riga sun sami damar komawa. A maimako, suna marmarin wata ƙasa mafi kyau, ta sama. Saboda haka Allah ba ya kunya a kira shi Allahnsu, domin ya riga ya shirya musu birni.
”Ya zaɓa yă sha wahala tare da mutanen Allah, maimakon yă ji daɗin sha’awace-sha’awacen zunubi na ɗan lokaci. Ya ɗauki wulaƙancin da yake sha saboda Kiristi ya fi dukiyar Masar daraja, domin ya sa ido ga ladansa. Ta wurin bangaskiya ya bar Masar, ba tare da jin tsoron fushin sarki ba; ya kuwa jure domin ya ga wannan wanda ba a iya gani.
”Me kuma zan faɗa? Ba ni da lokacin da zan ba da labari a kan Gideyon, Barak, Samson, Yefta, Dawuda, Sama’ila, da kuma annabawa, waɗanda ta wurin bangaskiya ne suka ci nasara a kan mulkoki, suka aikata adalci, suka kuma sami abin da aka yi alkawari; waɗanda suka rurrufe bakunan zakoki, suka kashe harshen wuta, suka kuma tsere wa kaifin takobi; waɗanda aka mai da rashin ƙarfinsu ya zama ƙarfi; waɗanda suka yi jaruntaka wajen yaƙi suka kuma fatattaki mayaƙan waɗansu ƙasashe. Mata suka karɓi ƙaunatattunsu da aka sāke tasar daga matattu. Aka azabtar da yawancin mutanen nan, amma suka ƙi a sake su, domin sun tabbata za su sami lada mafi kyau sa’ad da aka tā da matattu. Waɗansu suka sha ba’a da bulala, har da dauri da sarƙa, da kuma jefa su cikin kurkuku. Aka jajjefe su da duwatsu; aka raba su biyu da zarto; aka kashe su da takobi. Suka yi ta yawo saye da fatun tumaki da na awaki, suka yi zaman rashi, suka sha tsanani da kuma wulaƙanci duniya ba tă ma cancanci su zauna a cikinta ba. Suka yi ta yawo a cikin hamada da a kan duwatsu, da cikin kogwanni da kuma cikin ramummuka.
”Saboda haka, da yake muna kewaye da irin wannan taron shaidu mai girma, sai mu yar da duk abin da yake hana mu da kuma zunubin da yake saurin daure mu, mu kuma yi tseren da aka sa a gabanmu da nacewa.
”Bari mu kafa idanunmu a kan Yesu, tushe da kuma kammalar bangaskiyarmu, wanda ya jure kunyar gicciye da aka yi masa, domin ya san cewa daga baya zai yi farin ciki ya yi haka. Yanzu kuma yana zaune a hannun dama na kursiyin Allah. Ku lura da wannan wanda ya jure da irin hamayyan nan daga masu zunubi, don kada ku gaji, har ku fid da zuciya. Cikin famanku da zunubi, ba ku yi tsayayya har ga zub da jininku ba tukuna.
”Haka ma Yesu ya sha wahala a bayan gari don yă tsarkake mutane ta wurin jininsa. Saboda haka, sai mu fita mu je wajensa a bayan sansani, muna ɗaukar kunyar da ya sha. Gama a nan ba mu da dawwammamen birni, sai dai muna zuba ido a kan birnin nan mai zuwa.
”Ku ɗauki wannan da farin ciki mai tsabta, ’yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje na kowane iri suka zo muku, domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi daurewa. Dole daurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba.
”Mai albarka ne mutumin da yake daurewa cikin gwaji, gama bayan ya yi nasara da gwajin, zai sami rawanin rai wanda Allah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa.
”’Yan’uwa, ku ɗauki annabawa da suka yi magana a cikin sunan Ubangiji, a matsayin gurbi na haƙuri a cikin shan wahala. Kamar yadda kuka sani, mukan ce da waɗanda suka jure, masu albarka ne. Kun ji daurewar Ayuba, kuka kuma ga abin da Ubangiji ya yi a ƙarshe. Ubangiji yana cike da tausayi da jinƙai.
”da kuma cikin gādon da ba zai taɓa lalacewa, ɓacewa ko koɗewa ba, ajiyayye a sama dominku, ku waɗanda ta wurin bangaskiya ake kiyayewa ta wurin ikon Allah har yă zuwa ceton da yake a shirye da za a bayyana a ƙarshen lokaci.
”Da kuka zo gare shi, rayayyen Dutse, da mutane suka ƙi amma Allah ya zaɓa, kuma mai daraja a gare shi ku ma, a matsayinku na duwatsu masu rai, ana gina ku ga zama gidan ruhaniya don ku zama tsattsarkar ƙungiyar firistoci, kuna miƙa hadayun ruhaniya, abin karɓa ga Allah ta wurin Yesu Kiristi.
”Ga wannan ne aka kira ku, domin Kiristi ya sha wahala dominku, ya bar muku gurbin da ya kamata ku bi. “Bai taɓa yin laifi ba sam, ba a kuma sami ƙarya a bakinsa ba.” Sa’ad da suka zazzage shi, bai rama ba; sa’ad da ya sha wahala, bai yi barazana ba. A maimakon haka, ya miƙa kansa ga wanda yake shari’ar adalci.
”Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.”
”Gama Kiristi ya mutu domin zunubi sau ɗaya tak, mai adalci saboda marasa adalci, don yă kawo ku ga Allah. An kashe shi a cikin jiki, amma an rayar da shi a Ruhu,
”Abokaina ƙaunatattu, kada ku yi mamakin gwaji mai tsananin da kuke sha, sai ka ce wani baƙon abu ne yake faruwa da ku. Sai dai ku yi murna cewa kuna tarayya cikin shan wahalolin Kiristi, domin ku kai ga farin ciki mai yawa sa’ad da aka bayyana ɗaukakarsa. In an zage ku saboda sunan Kiristi, ku masu albarka ne, gama Ruhun ɗaukaka da kuma na Allah yana bisanku.
”Amma fa, in kuka sha wahala a matsayin ku Kirista ne, kada ku ji kunya, sai dai ku yabi Allah cewa kuna amsa wannan suna.
”Saboda haka, waɗanda suke shan wahala bisa ga nufin Allah ya kamata su danƙa kansu ga Mahaliccinsu mai aminci, su kuma ci gaba da aikata abin da yake daidai.
”Sa’ad da kuwa Babban Makiyayin ya bayyana, za ku karɓi rawanin ɗaukaka marar koɗewa.
”Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yă ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama. Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku. Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye. Ku yi tsayayya da shi, kuna tsayawa daram cikin bangaskiya, domin kun san cewa ’yan’uwanku ko’ina a duniya suna shan irin wahalolin nan. Allah mai dukan alheri, wanda ya kira ku ga madawwamiyar ɗaukaka cikin Kiristi, bayan kun sha wahala na ɗan lokaci, shi da kansa zai raya ku, yă kuma sa ku yi ƙarfi, ku kahu, ku kuma tsaya daram.
”Kada ku zama kamar Kayinu, wanda ya zama na mugun nan, ya kuma kashe ɗan’uwansa. Me ya sa ya kashe shi? Domin ayyukansa mugaye ne, na ɗan’uwansa kuma na adalci ne.
”Kada ku yi mamaki ’yan’uwana, in duniya ta ƙi ku. Mun san cewa mun riga mun ratsa daga mutuwa zuwa rai, domin muna ƙaunar ’yan’uwanmu. Duk wanda ba ya ƙauna matacce ne har yanzu. Duk mai ƙin ɗan’uwansa mai kisankai ne, kun kuma san cewa ba mai kisankan da yake da rai madawwami a cikinsa. Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, Yesu Kiristi ya ba da ransa dominmu. Ya kamata mu ma mu ba da rayukanmu domin ’yan’uwanmu.
”Ku, ’ya’yana ƙaunatattu, ku daga Allah ne, kun kuma yi nasara a kan magabtan Kiristi, domin wanda yake a cikinku ya fi wanda yake a duniya girma.
”domin duk haifaffe na Allah yana cin nasara a kan duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta ba mu wannan nasara a kan duniya. Wa ya cin nasara a kan duniya? Sai wanda ya gaskata cewa Yesu Ɗan Allah ne.
”“Duba, yana zuwa cikin gizagizai, kowane ido kuwa zai gan shi, har da waɗanda suka soke shi”; dukan mutanen duniya kuwa “za su yi makoki dominsa.” Bari yă zama haka nan! Amin. “Ni ne Alfa da kuma Omega,” in ji Ubangiji Allah, “wanda yake a yanzu, wanda yake a dā, da kuma wanda zai zo, Maɗaukaki.”
”‹Ni ne Rayayye, dā na mutu, ga shi kuwa ina a raye har abada abadin! Ina kuma riƙe da mabuɗan mutuwa da na Hades.›
”‹Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon ci daga itacen rai, da yake cikin aljannar Allah.›
”‹“Zuwa ga mala’ikan ikkilisiya a Simirna, ka rubuta,› ‹Waɗannan su ne kalmomin wannan da yake na Farko da na Ƙarshe, wanda ya mutu ya kuma sāke tashi da rai.› ‹Na san wahalarka da kuma talaucinka, duk da haka kai mai arziki ne! Na san ɓata suna da waɗannan suke yi maka waɗannan da suke cewa su Yahudawa ne alhali kuwa ba haka ba ne, su dai majami’ar Shaiɗan ne.› ‹Kada ka ji tsoron wahalar da kake gab da sha. Ina gaya maka, Iblis zai sa waɗansunku a kurkuku don yă gwada ku. Za ku sha tsanani na kwana goma. Ka yi aminci ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka rawanin rai.›
”‹Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara mutuwa ta biyu ba za tă cuce shi ba ko kaɗan.›
”‹Na san inda kake da zama, inda Shaiɗan yana da gadon sarautarsa. Duk da haka ka riƙe sunana da gaske. Ba ka yi mūsun bangaskiyarka gare ni ba, har ma a kwanakin Antifas, amintaccen mashaidina, wanda aka kashe a birninku, inda Shaiɗan yake zama.›
”‹Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara zan ba shi kaɗan daga cikin ɓoyayyiyar Manna. Zan kuma ba shi farin dutse tare da sabon suna a rubuce a bisansa, sananne kawai ga mai karɓan dutsen.›
”‹Gare shi wanda ya ci nasara ya kuma aikata nufina har ƙarshe, zan ba shi iko a kan al’ummai.› ‹‘Zai yi mulki a kansu da sandar sarauta ta ƙarfe, zai farfashe su, kamar tukwanen yumɓu’›‹kamar yadda na karɓi iko daga Ubana.› ‹Zan kuma ba shi tauraron asubahi.› ‹Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.›
”‹Wanda ya ci nasara, kamar su, za a sanya masa fararen tufafi. Ba zan taɓa share sunansa daga cikin littafin rai ba, sai dai zan shaida sunansa a gaban Ubana da mala’ikunsa.› ‹Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.›
”‹Duk wanda ya ci nasara zan mai da shi ginshiƙi a haikalin Allahna. Ba kuwa zai sāke barin wurin ba. Zan rubuta a kansa sunan Allahna da kuma sunan birnin Allahna, sabuwar Urushalima, wadda take saukowa daga sama daga Allahna; ni kuma zan rubuta a kansa sabon sunana.› ‹Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.›
”‹Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon zama tare da ni a kursiyina, kamar yadda na ci nasara, kuma ina zaune tare da Ubana a kursiyinsa.› ‹Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi.”›
”Sa’ad da ya buɗe hatimi na biyar, sai na ga a ƙarƙashin bagaden rayukan waɗanda aka kashe saboda maganar Allah da kuma shaidar da suka yi. Suka yi kira da babbar murya suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarki da kuma Mai Gaskiya, sai yaushe za ka shari’anta mazaunan duniya ka kuma ɗauki mana fansar jininmu?” Sai aka ba wa kowannensu farin riga, aka kuma faɗa musu su ɗan jira kaɗan sai an cika adadin abokansu masu hidima da kuma ’yan’uwansu waɗanda za a kashe kamar yadda su ma aka kashe su.
”Bayan wannan sai na duba, can a gabana kuwa ga wani taro mai girma, wanda ba mai iya ƙirgawa, daga kowace al’umma, kabila, mutane da kuma harshe, suna tsaye a gaban kursiyin da kuma gaban Ɗan Ragon nan. Suna saye da fararen tufafi suna kuma riƙe da rassan dabino a hannuwansu.
”Sai ɗaya daga cikin dattawan ya tambaye ni ya ce, “Waɗannan da suke saye da fararen tufafi su wane ne, daga ina kuma suka fito?” Na amsa na ce, “Ranka yă daɗe, kai ka sani.” Sai ya ce, “Waɗannan su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala; sun wanke tufafinsu suka kuma mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan. Saboda haka, “suna a gaban kursiyin Allah suna masa hidima dare da rana a cikin haikalinsa; kuma wannan mai zaune a kursiyin zai shimfiɗa tentinsa a bisansu. ‘Ba za su sāke jin yunwa ba; ba za su kuma sāke jin ƙishirwa ba. Rana ba za tă buga su ba,’ ko kuma kowane irin zafin ƙuna. Gama Ɗan Ragon da yake a tsakiyar kursiyin zai zama makiyayinsu; ‘zai bi da su zuwa ga maɓulɓular ruwan rai.’ ‘Allah kuwa zai share dukan hawaye daga idanunsu.’ ”
”Al’ummai suka yi fushi; fushinka kuwa ya zo. Lokaci ya yi don a shari’anta matattu, da kuma don sākawa wa bayinka annabawa da tsarkakanka da kuma su waɗanda suke girmama sunanka, ƙarami da babba, don kuma hallakar da waɗanda suka hallaka duniya.”
”Sun ci nasara a kansa ta wurin jinin Ɗan Ragon da ta wurin kalmar shaidarsu; ba su ƙaunaci rayukansu sosai har da za su ja da baya daga mutuwa.
”Sai macijin ya yi fushi da macen ya kuma koma wajen sauran zuriyarta don yă yaƙe su waɗannan waɗanda suke biyayya da umarnan Allah suke kuma riƙe da shaidar Yesu.
”Aka ba ta iko tă yaƙi tsarkaka tă kuma ci nasara a kansu. Aka kuma ba ta iko bisa kowace kabila, jama’a, harshe da kuma al’umma.
”Aka ba ta iko tă ba da numfashi ga siffar dabban nan ta fari, don tă yi magana tă kuma sa a kashe duk waɗanda suka ƙi yi wa siffar sujada. Ta kuma tilasta wa kowa, manya da yara, mawadata da matalauta, ’yantattu da bayi, don a yi musu alama a hannun dama ko a goshi, don kada kowa yă saya ko yă sayar, sai dai yana da alamar, wadda take sunan dabbar ko kuma lambar sunanta. Wannan yana bukata hikima. Duk mai hankali, sai yă lissafta lambar dabbar, gama lamban nan ta mutum ne. Lambarta kuwa ita ce 666.
”Wannan yana bukata haƙuri, a gefen tsarkakan da suke biyayya da umarnan Allah suka kuma kasance da aminci ga Yesu. Sai na ji murya daga sama ta ce, “Rubuta, Masu albarka ne matattun da suka mutu cikin Ubangiji daga yanzu zuwa gaba.” “I, za su huta daga faman aikinsu, gama ayyukansu za su bi su,” in ji Ruhu.
”Na ga cewa macen ta bugu da jinin tsarkaka, jinin waɗanda suka shaida Yesu. Da na gan ta, sai na yi mamaki ƙwarai.
”Hasken fitila ba zai ƙara haskakawa a cikinki ba. Ba za a ƙara jin muryar ango da amarya a cikinki ba. Attajiranki, dā su ne manyan mutanen duniya. Ta wurin sihirinki, dukan ƙasashe sun kauce. A cikinta aka sami jinin annabawa, da na tsarkaka, da kuma na dukan waɗanda aka kashe a duniya.”
”Yana saye da rigar da aka tsoma a jini, sunansa kuwa Kalman Allah ne. Mayaƙan sama suna biye da shi, suna hawan fararen dawakai, saye da fararen tufafi masu tsabta na lallausan lilin.
”Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu. (Sauran matattu ba su sāke rayuwa ba, sai da shekaru dubun nan suka cika.) Wannan fa shi ne tashin matattu na farko. Masu albarka da kuma tsarki ne waɗanda suke da rabo a tashin matattu na farko. Mutuwa ta biyu ba ta da iko a kansu, sai dai za su zama firistocin Allah da kuma na Kiristi za su kuma yi mulki tare da shi na shekaru dubu.
”Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe.” Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. “Ina yin kome sabo!” Sai ya ce, “Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma.” Ya ce mini, “An gama. Ni ne Alfa da kuma Omega, na Farko da kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi abin sha kyauta daga maɓulɓular ruwan rai.
”Duk wanda ya ci nasara zai gāji dukan wannan, zan kuma zama Allahnsa, shi kuma zai zama ɗana.
”‹“Ga shi, ina zuwa da wuri! Ladan da zan bayar yana tare da ni, kuma zan ba wa kowa gwargwadon abin da ya yi.› ‹Ni ne Alfa da kuma Omega, na Fari da kuma na Baya, Farko da kuma Ƙarshe.›
”