Sai ya ce musu, ‹“An ba ku sanin asirin mulkin Allah. Amma ga waɗanda suke waje kuwa, kome sai da misalai.› ‹Saboda,› ‹“ ‘ko sun dinga duba, ba za su taɓa gane ba,› ‹kuma ko su dinga ji, ba za su taɓa fahimta ba,› ‹in ba haka ba, mai yiwuwa, su tuba, a gafarta musu!’ ”› Sai Yesu ya ce musu, ‹“Ba ku fahimci wannan misali ba? Yaya za ku fahimci wani misali ke nan?› ‹Manomi yakan shuka maganar Allah.› ‹Waɗansu mutane suna kama da irin da ya fāɗi a kan hanya, inda akan shuka maganar Allah. Da jin maganar, nan da nan sai Shaiɗan yă zo yă ɗauke maganar da aka shuka a zuciyarsu.› ‹Waɗansu suna kama da irin da aka shuka a wurare masu duwatsu, sukan ji maganar Allah, sukan kuma karɓe ta nan da nan da farin ciki.› ‹Amma da yake ba su da saiwa, ba sa daɗewa. Da wahala ko tsanani ya tashi saboda maganar, nan da nan, sai su ja da baya.› ‹Har yanzu, waɗansu kamar irin da aka shuka cikin ƙaya, sukan ji maganar,› ‹amma damuwar wannan duniya, da son dukiya, da kuma kwaɗayin waɗansu abubuwa, sukan shiga, su shaƙe maganar, har su mai da ita marar amfani.› ‹Waɗansu mutane kuwa suna kama da irin da aka shuka a ƙasa mai kyau, sukan ji maganar Allah, su kuma karɓa, sa’an nan kuma su fid da amfani riɓi talatin-talatin, ko sittin-sittin, ko ɗari-ɗari.”›