04 – Halitta
Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Halitta.
Waɗannan su ne kalmomin Allah Maɗaukaki.
Ba mu da sha'awar maganganun mutane.
Duk wanda yake ƙaunar Allah ... Wannan shi ne abin da Allah ya ce game da shi: Halitta.
A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa.
”Amma Allah yakan ba ƙwayar jiki yadda ya yi niyya, kuma ga kowane irin ƙwaya yakan ba ta irin jikinta. Ba dukan nama ne iri ɗaya ba. Mutane da irin nasu, dabbobi da irin nasu, tsuntsaye da irin nasu, kifaye kuma da irin nasu.
”Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.
”A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa. To, ƙasa dai ba ta da siffa, babu kuma kome a cikinta, duhu ne kawai ya rufe ko’ina, Ruhun Allah kuwa yana yawo a kan ruwan. Sai Allah ya ce, “Bari haske yă kasance,” sai kuwa ga haske. Allah ya ga hasken yana da kyau, sai ya raba tsakanin hasken da duhu. Allah ya kira hasken “yini,” ya kuma kira duhun “dare.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta fari ke nan.
”Allah ya ce, “Bari sarari yă kasance tsakanin ruwaye domin yă raba ruwa da ruwa.” Saboda haka Allah ya yi sarari ya raba ruwan da yake ƙarƙashin sararin da ruwan da yake bisansa. Haka kuwa ya kasance. Allah ya kira sararin “sama.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyu ke nan.
”Allah ya ce, “Bari ruwan da yake ƙarƙashin sama yă tattaru wuri ɗaya, bari kuma busasshiyar ƙasa tă bayyana.” Haka kuwa ya kasance. Allah ya kira busasshiyar ƙasar “doron ƙasa,” ruwan da ya taru kuma, ya kira “tekuna.” Allah ya ga yana da kyau. Sa’an nan Allah ya ce, “Bari ƙasa tă fid da tsire-tsire, da shuke-shuke, da itatuwa a bisa ƙasa masu ba da amfani da ’ya’ya a cikinsu, bisa ga irinsu.” Haka kuwa ya kasance. Ƙasar ta fid da tsire-tsire, da shuke-shuke masu ba da ’ya’ya bisa ga irinsu, ta fid kuma da itatuwa masu ba da ’ya’ya da iri a cikinsu bisa ga irinsu. Allah ya ga yana da kyau. Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta uku ke nan.
”Allah kuma ya ce, “Bari haskoki su kasance a sararin sama domin su raba yini da dare, bari su zama alamu domin su nuna yanayi, da ranaku, da kuma shekaru, bari kuma haskokin su kasance a sararin sama domin su ba da haske a duniya.” Haka kuwa ya kasance. Allah ya yi manyan haskoki biyu, babban hasken yă mallaki yini, ƙaramin kuma yă mallaki dare. Ya kuma yi taurari. Allah ya sa su a sararin sama domin su ba da haske a duniya, su mallaki yini da kuma dare, su kuma raba haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta huɗu ke nan.
”Allah ya ce, “Bari ruwa yă cika da halittu masu rai, bari tsuntsaye kuma su tashi sama a bisa duniya a sararin sama.” Allah ya halicci manyan halittun teku, da kowane mai rai da abin da yake motsi a ruwa, bisa ga irinsu, da kuma kowane tsuntsu mai fiffike bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau. Allah ya albarkace su ya ce, “Ku yi ta haihuwa ku kuma ƙaru da yawa, ku cika ruwan tekuna, bari kuma tsuntsaye su yi yawa a bisa duniya.” Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta biyar ke nan.
”Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa tă ba da halittu masu rai bisa ga irinsu; dabbobi da halittu masu rarrafe, da kuma namun jeji, kowane bisa ga irinsa.” Haka kuwa ya kasance. Allah ya halicci namun jeji bisa ga irinsu, dabbobi bisa ga irinsu, da kuma dukan halittu masu rarrafe a ƙasa bisa ga irinsu. Allah kuwa ya ga yana da kyau.
”Sa’an nan Allah ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, cikin kamanninmu, bari kuma su yi mulki a bisa kifin teku, tsuntsayen sama, da kuma dabbobi, su yi mulki a bisa dukan duniya, da kuma a bisa dukan halittu, da masu rarrafe a ƙasa.” Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa. Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum. Miji da mace ya halicce su. Allah ya albarkace su, ya kuma ce musu, “Ku yi ta haihuwa ku ƙaru da yawa, ku mamaye duniya, ku mallake ta. Ku yi mulki a bisa kifin teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma bisa kowace halitta mai rai wadda take rarrafe a ƙasa.” Sa’an nan Allah ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da ’ya’ya masu kwaya da suke a fāɗin duniya, da dukan itatuwa masu ba da ’ya’ya, don su zama abinci a gare ku. Na kuma ba da dukan dabbobin ƙasa, da dukan tsuntsayen sama, da dukan abin da yake rarrafe a ƙasa, da dai iyakar abin da yake numfashi; haka kuma na ba da ganyaye su zama abinci.” Haka kuwa ya kasance. Allah ya ga dukan abin da ya yi, yana da kyau ƙwarai. Yamma ta kasance, safiya kuma ta kasance, kwana ta shida ke nan.
”Ta haka aka gama yin sammai da duniya da dukan abubuwan da suke cikinsu. Kafin kwana ta bakwai, Allah ya gama aikin da yake yi, saboda haka a kwana ta bakwai, ya huta daga dukan aikinsa. Allah kuwa ya albarkaci kwana ta bakwai, ya kuma mai da ita mai tsarki, saboda a kanta ne ya huta daga dukan aikin halittar da ya yi.
”Wannan shi ne asalin tarihin sammai da duniya sa’ad da aka halicce su. Sa’ad da Ubangiji Allah ya yi duniya da sammai, babu tsiro a duniya kuma ganyaye ba su tsira a busasshiyar ƙasa ko ba, gama Ubangiji Allah bai aiko da ruwan sama a kan duniya ba tukuna, babu kuma wani mutumin da zai nome ƙasar, amma dai rafuffuka suna ɓullo da ruwa daga ƙasa suna jiƙe ko’ina a fāɗin ƙasa. Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mutum daga turɓayar ƙasa, ya kuma hura numfashin rai cikin hancinsa, mutumin kuwa ya zama rayayyen taliki. To, fa, Ubangiji Allah ya yi lambu a gabas, a Eden, a can kuwa ya sa mutumin da ya yi.
”Wannan shi ne rubutaccen tarihin zuriyar Adamu. Sa’ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin kamannin Allah. Ya halicce su namiji da ta mace, ya kuma albarkace su. Sa’ad da kuma aka halicce su, ya kira su “Mutum.” Sa’ad da Adamu ya yi shekaru 130, sai ya haifi ɗa wanda ya yi kama da shi, ya kuma kira shi Set.
”Gama kwana shida Ubangiji ya halicci sama da ƙasa, da teku, da duk abin da yake cikinsu, amma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Ubangiji ya albarkaci ranar Asabbaci, ya kuma mai da ita mai tsarki.
”Zai zama alama tsakanina da Isra’ilawa har abada, gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama da ƙasa, a rana ta bakwai kuma ya daina aiki, ya kuma huta.’ ”
”Duk da haka, muddin ina raye, kuma muddin ɗaukakar Ubangiji ta cika dukan duniya,
”Ku bincika dukan tarihi mana, tun daga lokacin da Allah ya halicci mutane a cikin duniya har yă zuwa yanzu; ku tantambaya daga wannan kusurwa ta samaniya zuwa waccan, ko wani babban abu irin wannan ya taɓa faruwa, ko kuma an taɓa jin labarin irinsa?
”Sammai, har da sama sammai, da duniya, da kome da yake cikinta na Ubangiji Allahnku ne.
”Yakan tā da matalauci daga ƙura, yă kuma ɗaga mai bukata daga tarin toka; yă zaunar da su tare da ’ya’yan sarki; yă kuma sa su gāji mulki na ɗaukaka. “Harsashin duniya na Ubangiji ne; a bisansu ne ya kafa duniya.
”Aka bayyana kwarin teku, tushen duniya suka tonu. A tsawatawar Ubangiji, da numfashinsa mai ƙarfi daga hancinsa.
”Hezekiya kuwa ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda yake zaune tsakanin kerubobi, kai kaɗai ne Allah bisa dukan mulkokin duniya. Kai ka yi sama da duniya.
”Girma da iko da ɗaukaka, da daraja da kuma nasara naka ne, ya Ubangiji, gama kome a sama da ƙasa naka ne. Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji; an kuma ɗaukaka ka a matsayin kai a bisa duka.
”Kai kaɗai ne Ubangiji. Kai ka yi sammai, har ma da sama sammai, da dukan rundunar taurari, da duniya da kuma dukan abin da yake cikinta, da tekuna da dukan abubuwan da suke cikinsu. Ka ba da rai ga kome, kuma rundunonin sama suna maka sujada.
”Yana girgiza ƙasa, yana girgiza harsashenta. Yana magana da rana sai ta ƙi yin haske; yana hana taurari yin haske. Shi kaɗai ya shimfiɗa sammai ya kuma yi tafiya a kan raƙuman ruwan teku. Shi ne ya halicci Mafarauci da Kare da Zomo, da Kaza, da ’Ya’yanta da tarin taurari a sama, da taurarin kudu. Yana yin abubuwan banmamaki waɗanda ba a iya ganewa, mu’ujizai waɗanda ba a iya ƙirgawa.
”“Amma ka tambayi dabbobi, za su kuma koya maka, ko kuma tsuntsayen sararin sama kuma za su gaya maka. Ko ka yi magana da duniya, za tă kuma koya maka, ko kuma ka bar kifin teku su sanar da kai. Wane ne cikin waɗannan bai san cewa hannun Ubangiji ne ya yi wannan ba? Ran kowace halitta yana a hannunsa, haka kuma numfashin dukan ’yan adam.
”Ya shimfiɗa arewancin sararin sama a sarari; ya rataye duniya ba a jikin wani abu ba. Ya naɗe ruwaye a cikin gizagizansa, duk da haka girgijen bai yage saboda nauyi ba. Ya rufe fuskar wata, ya shimfiɗa gizagizai a kan shi, ya zāna iyakar fuskar ruwa a kan iyakar da take tsakanin duhu da haske. Madogaran sama sun girgiza, saboda tsawatawarsa.
”Ruhun Allah ne ya yi ni; numfashin Maɗaukaki ya ba ni rai.
”Sa’an nan Ubangiji ya amsa wa Ayuba. Ya ce, “Wane ne wannan da yake ɓata mini shawarata da surutan wofi? Ka sha ɗamara kamar namiji; zan yi maka tambaya, za ka kuwa amsa mini. “Kana ina lokacin da na aza harsashen duniya? Gaya mini, in ka sani. Wane ne ya zāna girmanta? Ba shakka ka sani! Wane ne ya ja layin aunawa a kanta? A kan me aka kafa tushenta, ko kuma wa ya sa dutsen kan kusurwarta, yayinda taurarin safe suke waƙa tare dukan mala’iku kuma suka yi sowa don farin ciki. “Wane ne ya rufe teku a bayan ƙofofi, lokacin da ya burtsatso daga cikin ciki. Lokacin da na yi wa gizagizai riga na kuma naɗe su a cikin duhu sosai, sa’ad da na yi masa iyaka na sa masa ƙofofi da wurin kullewa. Sa’ad da na ce ga iyakar inda za ka kai, ga inda raƙuman ruwanka za su tsaya?
”“Dubi dorina, wadda na halicce ku tare kuma ciyawa take ci kamar sa. Ga shi ƙarfinta yana a ƙugunta ikonta yana cikin tsokar cikinta. Wutsiyarta tana da ƙarfi kamar itacen al’ul; jijiyoyin cinyoyinta suna haɗe a wuri ɗaya.
”Sa’ad da na dubi sammai, aikin yatsotsinka, wata da taurari waɗanda ka ajiye a wurarensu,
”Kwarin teku sun bayyana tussan duniya sun bayyana a fili sa’ad da ka tsawata, ya Ubangiji, sa’ad da ka numfasa daga hancinka.
”Sammai suna shelar ɗaukakar Allah; sararin sama suna furta aikin hannuwansa.
”Duk da haka muryarsu tana kaiwa ga dukan duniya, kalmominsu zuwa iyakokin duniya. A sammai Allah ya kafa tenti domin rana,
”Duniya ta Ubangiji ce da kome da yake cikinta, duniya, da dukan waɗanda suke zama a cikinta; gama ya gina ta a kan tekuna ya kafa ta a kan ruwaye.
”Ta wurin maganar Ubangiji aka yi sammai, rundunar taurarinsu kuwa da numfashin bakinsa.
”Sammai naka ne, haka kuma duniya; ka kafa duniya da dukan abin da yake cikinta. Ka halicce arewa da kudu; Tabor da Hermon suna rera don farin ciki ga sunanka.
”Kafin a haifi duwatsu ko a fid da ƙasa da duniya, daga madawwami zuwa madawwami kai Allah ne.
”Teku nasa ne, gama shi ne ya yi shi, da hannuwansa kuma ya yi busasshiyar ƙasa. Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada, bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu;
”A farkon fari ka kafa tushen duniya, sammai kuma aikin hannuwanka ne. Za su hallaka, amma za ka ci gaba; duk za su tsufe kamar riga. Kamar riga za ka canja su za a kuwa zubar da su.
”Yabi Ubangiji, ya raina. Ya Ubangiji Allahna, kana da girma ƙwarai; kana saye da daraja da ɗaukaka. Ubangiji ya naɗe kansa da haske kamar riga ya shimfiɗa sammai kamar tenti ya kafa ginshiƙan ɗakin samansa a kan ruwaye. Ya maido da gizagizai suka zama keken yaƙinsa yana hawa a kan fikafikan iska. Ya mai da iska suka zama ’yan saƙonsa harsunan wuta kuma bayinsa. Ya kafa duniya a kan tussanta; ba za a iya matsar da ita ba.
”Ina misalin yawan aikinka, ya Ubangiji! Cikin hikima ka yi su duka; duniya ta cika da halittunka. Akwai teku, babba da kuma fāɗi, cike da halittun da suka wuce ƙirga, abubuwa masu rai babba da ƙarami.
”Ayyukan Ubangiji da girma suke; dukan waɗanda suke farin ciki da su suna tunaninsu.
”Bari Ubangiji yă albarkace ku, shi Mahalicci sama da ƙasa. Saman sammai na Ubangiji ne, amma ya ba da duniya ga mutum.
”Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya yi; bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna a cikinta.
”Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, wanda ya kafa sama da ƙasa.
”Taimakonmu yana a sunan Ubangiji, Wanda ya yi sama da ƙasa.
”Ubangiji yana yin abin da ya ga dama, a sammai da kuma a duniya, cikin tekuna da kuma cikin dukan zurfafansu.
”Wanda ta wurin ganewarsa ya yi sammai, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Wanda ya shimfiɗa duniya a kan ruwaye, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Wanda ya yi manyan haskoki, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Rana don tă yi mulkin yini, Ƙaunarsa madawwamiya ce. Wata da taurari kuma don su yi mulkin dare; Ƙaunarsa madawwamiya ce.
”Gama ka halicci ciki-cikina; ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata. Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki; ayyukanka suna da banmamaki, na san da haka sosai.
”Mahaliccin sama da ƙasa, teku, da kome da yake cikinsu, Ubangiji, wanda yake mai aminci har abada.
”Ya lissafta yawan taurari ya kuma kira kowannensu da suna.
”Ta wurin hikima Ubangiji ya kafa harsashin duniya, ta wurin fahimi ya shirya sammai inda suke;
”“ Ubangiji ya kawo ni a matsayi na farko na ayyukansa, kafin ayyukansa na tuntuni; an naɗa ni tun fil azal, daga farko, kafin duniya ta kasance. Sa’ad da babu tekuna, aka haife ni, sa’ad da babu maɓulɓulai masu ruwa; kafin a kafa duwatsu a wurarensu, kafin tuddai ma, an haife ni, kafin ya yi duniya ko gonaki ko wata ƙurar duniya. Ina nan sa’ad da ya kafa sammai a wurarensu, sa’ad da ya shata sararin sama a kan fuskar zurfafa, sa’ad da ya kafa gizagizai a bisa ya kuma kafa maɓulɓulan zurfafa daram, sa’ad da ya ba wa teku iyakarsa domin kada ruwaye su zarce umarninsa, da kuma sa’ad da ya shata tussan duniya. A lokacin ni ne mai tsara abubuwa a gefensa. Na cika da murna kowace rana, kullum ina farin ciki a gabansa, ina farin ciki da dukan duniyarsa ina murna da ’yan adam.
”Kunnuwan da suke ji da kuma idanun da suke gani, Ubangiji ne ya yi su duka.
”Suna kiran juna, “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Maɗaukaki ne; duniya ta cika da ɗaukakarsa.”
”Ba za su yi lahani ko su hallaka wani a dutsena mai tsarki ba, gama duniya za tă cika da sanin Ubangiji kamar yadda ruwaye suka rufe teku.
”Kuna birkitar abubuwa, sai ka ce an mayar da mai ginin tukwane ya zama yumɓu! Abin da aka yi zai ce wa wanda ya yi shi, “Ba shi ne ya yi ni ba”? Tukunya za tă iya ce wa mai ginin tukwane, “Ba ka san kome ba”?
”“Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, zaune a tsakanin kerubobi, kai kaɗai ne Allah a kan dukan masarautan duniya.
”Wane ne ya auna ruwaye a tafin hannunsa, ko kuwa ya gwada tsawon sammai da fāɗin tafin hannunsa? Wane ne ya riƙe ƙurar ƙasa a kwando, ko kuwa ya auna nauyin duwatsu a magwaji, tuddai kuma a ma’auni?
”Ba ku sani ba? Ba ku taɓa ji ba? Ba a faɗa muku daga farko ba? Ba ku fahimta ba tun kafawar duniya? Yana zaune a kursiyi a bisa iyakar duniya, kuma mutanenta suna kama da fāra. Ya miƙa sammai kamar rumfa, ya kuma shimfiɗa su kamar tentin da za a zauna a ciki.
”Ku ɗaga idanunku ku duba sammai. Wane ne ya halicce dukan waɗannan? Wane ne ya fitar da rundunar taurari ɗaya-ɗaya, yana kiransu, kowanne da sunansa. Saboda ikonsa mai girma da kuma ƙarfinsa mai girma, babu ko ɗayansu da ya ɓace.
”Ba ku sani ba? Ba ku ji ba? Ubangiji madawwamin Allah ne, Mahaliccin iyakokin duniya. Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba, kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.
”Ga abin da Allah Ubangiji ya ce, shi da ya halicci sammai ya kuma miƙe su, wanda ya shimfiɗa duniya da dukan abin da ya fito cikinta, wanda ya ba wa mutanenta numfashi, da rai ga waɗanda suke tafiya a kanta.
”kowa da ake kira da sunana, wanda aka halitta saboda ɗaukakata, wanda na siffanta na kuma yi.”
”“Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Fansarka, wanda ya yi ka a cikin mahaifa. “Ni ne Ubangiji, wanda ya yi dukan abubuwa, wanda ya shimfiɗa sammai ya kuma kafa harsashen duniya da kansa,
”“Ga abin da Ubangiji yana cewa, Mai Tsarkin nan na Isra’ila, da kuma Mahaliccinsa. Game da abubuwan da ke zuwa, kun tambaye ni game da ’ya’yana, ko kuwa kun ba ni umarni game da aikin hannuwana? Ai, ni ne wanda ya yi duniya na kuma halicci mutum a kanta. Hannuwana ne sun miƙe sammai; na umarci rundunar sararin sama.
”Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya halicci sammai, shi ne Allah; shi da ya sarrafa ya kuma yi duniya, ya kafa ta; bai halicce ta don ta zama ba kome ba, amma ya yi ta don a zauna a ciki, ya ce, “Ni ne Ubangiji, kuma babu wani.
”“Ka kasa kunne gare ni, ya Yaƙub, Isra’ila, wanda na kira cewa, Ni ne shi; ni ne na farko ni ne kuma na ƙarshe. Hannuna ne ya kafa harsashen duniya, hannuna na dama kuma ya shimfiɗa sammai; sa’ad da na kira su, duka suka miƙe tsaye gaba ɗaya.
”har da kuka manta da Ubangiji Mahaliccinku, wanda ya shimfiɗa sammai ya kuma kafa harsashen duniya, har kuna zama da tsoro kowace rana saboda fushin masu zalunci, waɗanda sun ƙudura sai sun hallaka? Gama ina fushin mai zalunci?
”Duk da haka, Ubangiji, kai ne Ubanmu. Mu yumɓu ne, kai kuma mai ginin tukwane; dukanmu aikin hannunka ne.
”Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Sama kursiyina ce, duniya kuma matashin sawuna. Ina gidan da za ku gina mini? Ina wurin hutuna zai kasance? Ba hannuna ba ne ya yi dukan waɗannan abubuwa, ta haka suka kasance?” In ji Ubangiji. “Wannan mutum ne nake jin daɗi, shi da yake mai ƙasƙanci da kuma zuciyar yin tuba, yana kuma rawar jiki ga maganata.
”Amma Ubangiji shi ne Allah na gaskiya; shi ne Allah mai rai, madawwamin sarki. Sa’ad da ya yi fushi, ƙasa takan girgiza; al’ummai ba sa iya jure da hasalarsa. “Ka faɗa musu wannan, ‘Waɗannan alloli, waɗanda ba su yi sammai da ƙasa ba, za su hallaka daga duniya da kuma daga ƙarƙashin sammai.’ ” Amma Allah ya yi duniya ta wurin ikonsa; ya kafa duniya ta wurin hikimarsa ya shimfiɗa sammai ta wurin fahiminsa.
”Da ikon mai ƙarfi da kuma hannuna da na miƙa na yi duniya da mutanenta da kuma dabbobin da suke ciki, na ba da ita ga duk wanda na ga dama.
”“A, Ubangiji Mai Iko Duka, ka yi sammai da duniya ta wurin ikonka mai girma da kuma hannunka mai iko. Ba abin da ya gagare ka.
”“Ya halicci ƙasa ta wurin ikonsa; ya kafa duniya ta wurin hikimarsa, ya kuma shimfiɗa sammai ta wurin fahiminsa.
”(Shi wanda ya yi Taurarin nan da ake ce Kaza da ’Ya’yanta da kuma Mai Farauta da Kare, wanda ya mai da duhu ya zama haske ya kuma baƙanta rana ta zama dare, yakan kwashe ruwan teku ya zubar a ƙasa, Ubangiji ne sunansa,
”shi da ya gina kyakkyawar fadarsa a cikin sammai ya kuma kafa harsashenta a duniya, shi da yakan kira ruwan teku yă kuma kwarara su a bisa duniya, Ubangiji ne sunansa.
”Sai ya amsa, “Ni mutumin Ibraniyawa ne, ina kuma bauta wa Ubangiji Allah na sama, wanda ya yi teku da tuddai.”
”Gama duniya za tă cika da sanin ɗaukakar Ubangiji, yadda ruwaye suka rufe teku.
”Annabci, maganar Ubangiji game da Isra’ila. Ubangiji, wanda ya shimfiɗa sammai, wanda ya kafa harsashin duniya, wanda kuma ya yi ruhun mutum a cikinsa ya ce,
”‹Amma a farkon halitta, Allah ya ‘halicce su miji da mace.’›
”ɗan Enosh, ɗan Shitu, ɗan Adamu, ɗan Allah.
”Tun farar farawa akwai Kalma, Kalman kuwa yana nan tare da Allah, Kalman kuwa Allah ne. Yana nan tare da Allah tun farar farawa. Ta wurin Kalman ne aka halicci dukan abubuwa. In ba tare da shi ba, babu abin da aka yi wanda aka yi.
”Yana a duniya, kuma ko da yake an yi duniya ta wurinsa ne, duniya ba tă gane shi ba.
”Uban bikin kuwa ya ɗanɗana ruwan da aka juya ya zama ruwan inabi. Bai san daga ina ya fito ba, ko da yake bayin da suka ɗiba ruwan sun sani. Sai ya kira angon waje ɗaya ya ce, “Kowa yakan kawo ruwan inabi mafi kyau da fari, sa’an nan marar kyan bayan baƙin sun sha da yawa; amma ka ajiye ruwan inabi mafi kyau sai yanzu.”
”“ ‘Sama ne kursiyina, duniya kuma wurin ajiye tafin ƙafata. Wane irin gida za ka gina mini? Ko kuwa ina wurin hutuna zai kasance? In ji Ubangiji.
”“Ya ku mutane, don me kuke yin haka? Ai, mu ma mutane ne kawai, ’yan adam ne kamar ku. Mun kawo muku labari mai daɗi ne, muna gaya muku ku juya daga waɗannan abubuwa banza, ku juyo ga Allah mai rai, wanda ya yi sama da ƙasa da teku da kuma dukan abin da yake cikinsu.
”“Allahn da ya halicci duniya da kome da yake cikinta shi ne Ubangijin sama da ƙasa, ba ya kuma zama a haikalin da aka gina da hannuwa. Ba a kuma yin masa hidima da hannun mutum, sai ka ce mai bukatan wani abu, domin shi kansa ne ke ba wa dukan mutane rai da numfashi da kuma kome. Daga mutum ɗaya, ya halicci kowace al’ummar mutane, don su zauna a duk duniya; shi ne kuma ya ƙaddara lokuta bisa ga tsarinsu da kuma inda za su kasance. Allah ya yi wannan domin mutane su neme shi mai yiwuwa kuma su lalluba su same shi, ko da yake ba shi da nisa daga kowannenmu. ‘Gama a cikinsa ne muke rayuwa muke motsi muka kuma kasance.’ Yadda waɗansu mawaƙanku suka ce, ‘Mu zuriyarsa ce.’
”Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.
”Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Na mai da kai uban al’ummai masu yawa.” Shi ubanmu ne a gaban Allah, wanda a cikinsa ya gaskata, Allahn da yake ba da rai ga matattu, yake kuma kiran abubuwan da ba su kasance ba su zama kamar sun kasance.
”Saboda haka, kamar yadda zunubi ya shigo duniya ta wurin mutum ɗaya, mutuwa kuma ta wurin zunubi, ta haka kuwa mutuwa ta shafi dukan mutane, domin dukan mutane sun yi zunubi.
”Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar ’ya’yan Allah. Gama an sa halitta a cikin wulaƙanci, ba da son ta ba, sai dai ta wurin nufin wannan da ya mai da ita haka, da bege cewa za a ’yantar da halitta kanta daga bautarta ga ruɓewa a kuma kawo ta cikin ’yancin ɗaukakar ’ya’yan Allah. Mun san cewa dukan halitta tana nishi sai ka ce mace mai naƙuda har yă zuwa wannan lokaci.
”Gama daga gare shi, ta wurinsa, da kuma saboda shi ne dukan abubuwa suka kasance. Ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada! Amin.
”duk da haka a gare mu dai akwai Allah ɗaya kaɗai, Uba, wanda dukan abubuwa suke daga gare shi, wanda kuma saboda shi ne muke rayuwa, kuma akwai Ubangiji ɗaya, Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa ne aka yi dukan abu, ta wurinsa ne kuma muke rayuwa.
”Amma Allah yakan ba ƙwayar jiki yadda ya yi niyya, kuma ga kowane irin ƙwaya yakan ba ta irin jikinta. Ba dukan nama ne iri ɗaya ba. Mutane da irin nasu, dabbobi da irin nasu, tsuntsaye da irin nasu, kifaye kuma da irin nasu.
”Haka yake a rubuce cewa, “Adamu, mutumin farko ya zama mai rai”; Adamu na ƙarshe kuwa ruhu ne mai ba da rai. Ba jikin ruhaniya ne ya zo da farko ba, na mutuntakan ne, daga baya kuma sai na ruhaniya. Mutumin farko daga turɓaya ce ya fito, mutum na biyu kuwa daga sama ne ya fito. Kamar yadda mutumin turɓaya yake, haka ma waɗanda suke na turɓaya. Kuma kamar yadda mutumin sama yake, haka ma waɗanda suke na sama.
”Domin shi Allah wanda ya ce, “Bari haske yă haskaka daga duhu,” ya sa haskensa ya haskaka a cikin zukatanmu, don yă ba mu hasken sanin ɗaukakar Allah a fuskar Kiristi.
”An zaɓe ni in bayyana wa dukan mutane shirin asirin nan wanda Allah, mahaliccin kome, ya ɓoye shekara da shekaru.
”Kiristi shi ne surar da ake gani na Allah wanda ba a iya gani, ɗan fari a kan dukan halitta. Ta wurinsa aka halicci dukan abu, abubuwan da suke cikin sama da abubuwan da suke a duniya, waɗanda ake gani, da waɗanda ba a gani, ko kursiyoyi ko ikoki ko masu mulki ko hukumomi; an halicci dukan abu ta wurinsa da kuma dominsa ne. Ya kasance kafin dukan abu, kuma a cikinsa ne dukan abubuwa suke a harhaɗe.
”amma a waɗannan kwanaki a ƙarshe ya yi magana da mu ta wurin Ɗansa, wanda ya naɗa magājin dukan abubuwa, wanda kuma ta wurinsa ya halicci duniya. Ɗan shi ne hasken ɗaukakar Allah, shi ne kuma ainihin kamanninsa, yana riƙe da dukan abubuwa ta wurin kalmarsa mai iko. Bayan ya yi tsarkakewa don zunubai, sai ya zauna a hannun daman Maɗaukaki a sama.
”Ya kuma ce, “Tun da farko, ya Ubangiji, ka kafa tushen duniya, sammai kuma aikin hannuwanka ne.
”Gama kowane gida yana da wanda ya gina shi, amma maginin dukan abu Allah ne.
”Ta wurin bangaskiya ne muka fahimci cewa an halicci duniya bisa ga umarnin Allah, saboda an halicce abin da ake gani daga abin da ba a gani.
”Da farko dai, dole ku fahimci wannan cewa a kwanakin ƙarshe masu ba’a za su zo suna ba’a, suna bin mugayen sha’awace-sha’awacensu. Za su ce, “Ina wannan ‘dawowar’ da ya yi alkawari ne? Tun mutuwar kakanninmu, kome yana tafiya kamar yadda yake tun farkon halitta.” Amma da gangan suke manta cewa tun dā can ta wurin maganar Allah sammai suka kasance aka kuma yi ƙasa daga ruwa ta wurin ruwa kuma. Ta wurin waɗannan ruwan ne aka nutsar, aka kuma hallakar da duniya ta wancan lokaci. Ta wurin wannan magana ce aka ajiye sammai da ƙasa na yanzu domin wuta, an ajiye su kuma don ranar hukunci da hallaka ta mutane marasa tsoron Allah. Amma kada ku manta da wannan abu guda ɗaya, abokaina ƙaunatattu. Ga Ubangiji kwana ɗaya kamar shekaru dubu ne, shekaru dubu kuma kamar kwana ɗaya ne.
”“Ya Ubangijinmu da Allahnmu, ka cancanci ɗaukaka da girma da iko, domin ka halicci dukan abubuwa, kuma ta wurin nufinka aka halicce su suka kuma kasance.”
”Ya kuma yi rantsuwa da wannan wanda yake raye har abada abadin, wanda ya halicci sammai da dukan abin da yake cikinsu, duniya da dukan abin da yake cikinta, da kuma teku da dukan abin da yake cikinsa, ya kuma ce, “Babu sauran jinkiri!
”Sai na ga wani mala’ika yana tashi sama a tsakiyar sararin sama, yana kuma da madawwamiyar bishara wadda zai yi shela ga waɗanda suke zama a duniya, ga kowace al’umma, kabila, harshe, da kuma jama’a. Ya ce da babbar murya, “Ku ji tsoron Allah ku kuma ɗaukaka shi, domin sa’ar hukuncinsa ya yi. Ku yi wa wannan da ya halicci sammai, ƙasa, teku, da maɓulɓulan ruwa sujada.”
”